Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 71
Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 71: Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 71. Dukar wasa Rimsha ta kai mata a kafaɗa tana…
3,374 words
Dukar wasa Rimsha ta kai mata a kafaɗa tana faɗin "Ki dai'na hararar mini yaya na gaya miki, idan ba haka sai mun cire idonki ɗaya". Guntun tsaki ta ja tare da miƙewa ta nufi toilet abinta ta barsu a wajen, dawo da kallonsa kan Rimshar ya yi yana faɗin "Me kika ce mata? Wai ku ba zaku dai'na magana da yaren nan naku da bana ji bane?".
Murmushi ta sake idanunta ɗauke da sauran ruwan hawaye ta gaya mishi abin da ta ce wa Jehan ɗin, murmushi shi ma ya yi kafin ya ce "Ni kam tana burgeni sosai idan tana wannan tsare gidan nata, haka idan tana faɗa ba karamin burgeni take yi ba, ina jin daɗi sosai, ki kyleta zata sha tsokana a wajena ba kaɗan ba ai, tun da na san me bata so, bari ma uncle ya zo gobe zaki ga abin da zan yi mata, da idonta irin wanda nake so a wajen". Dariya Rimsha ta yi, wannan wai ya zageta kenan, wai da idonta irin wanda yake so, kai Areef duniya.
Haka suka kasance cikin farinciki, wunin wannan ranar dai cikin tsantsar farinciki suka wuni, ko palo Jehan bata leƙa ba, tana bedroom ɗin Rimsha tana kudundune cikin bargo abinta, tana faman sauke gajiya da wahala bayan ta yi wanka ta ci abinci kenan, ta sha barci kamar ba gobe dan ta tsallake rijiya da baya wlh, Rimaha kuwa tana fita ta kaiwa Lion abinci da sauransu, da ta gama zata dawo wajen ƴar uwarta su zauna, duk da ba hira suke yi ba amma ta fi son ta ganta tare da ita, idan baku manta ba, Jehan bata da yawan magana, shi ne yasa basu yin wani hira, shiru suke zama kamar kurame, sai idan Rimshar ta gaji ne ma zata jefo mata tambaya ɗaya biyu, wani lokaci ta amsa, wani lokaci kuma sai ta ce "Wai ke Rimsha ba zaki bar bakinki ya zauna shiru bane? To idan ke baki gaji da tambaya ba, ni na gaji da bada amsa, dan haka ki kyaleni, idan kina cigaba da takura mini zan kai miki duka gaskiya!". Sai dai ta yi dariya ta yi shiru, dan idan da sabo ta saba da Jehan ciki da bai, tsab ta san halinta, bata son yawan surutu kamar daddy da Gwaggo, basu da yawan magana, idan ka cika matsa musu da magana ma mari zasu kai maka, to ita ma hakan take, ita kuma tana son jin labarin in da Jehan ɗin ta yi rayuwa, amma sam taki bata haɗin kai ta gaya mata, dole ta hakura ba dan ta so ba, haka suka yi kwanan tsantsar faricniki.
Washegari da safe, Rimsha ta shirya ta tafi school dan yau saura kwana huɗu su gama exams, ita kuma Jehan ta kule a cikin ɗaki, da Rimsha ta zo tafiya ta fito waje ta yi mata rakiya zuwa wajen mota, suka rungumi juna suka yi sallama, Areef yana yi mata magana, sam taki kula shi ta wuce ta koma ɗaki ta yi kwanciyarta, da yake ya shirya nemanta da tsokana sai ya bita ɗakin, haka ya tasata a gaba ya rinƙa yi mata duk wani abin da bata so, har sai da ta kusa yin kuka sannan ya kyaleta ya fito.
Shi kuma Aseef a lokacin ne ya shirya ya tafi wajen Akila kenan.
Lokacin da daddynta ya sauƙa a airport, har bedroom nata ya zo ta ce mata ta shirya suje ɗauko daddy, kamar zata ce mishi ba zata je ba, amma sai ta kasa dan a matukar yunwace take da son ganin daddyn nata, haka ta shirya tsab suka nufi airport ɗin.
Lokacin da suka yi parking na motarsu a Airport ɗin basu ga daddyn ba, fitowa ya yi dan ya duba shi, Donal ne ya kawo su airport ɗin, can ya hango shi tsaye shi da Tyrone, da sauri fuska ɗauke da fara'a ya karisa wajensu, rungumar juna suka yi shi da daddyn kafin Tyrone ya ɗaga hannu ya sara mishi, sai murmushi suke yi dukkansu.
Ganin ya ga daddyn ne yasa ta fito da sauri, tsabar farincikin bata san lokaci da ta tafi da gudu zata rungumi daddyn ba, shi kuma daddy bai ganta ba, kwata kwata bai ma san tana tare da su ba, hankalinsa yana kan Areef, da gudu ta zo zata rungune shi, cikin sauri Areef ɗin ya shiga tsakaninsu ta rungume shi, haushi kamar ta kifa mishi mari, shi kuma daddy dariya abin ya bashi, ga kuma tsantsar murnan ganinta, yaso shi ta runguma, sai dai ba zai iya cewa Areef meyasa ya yi mata haka ba, sai ya danne yana dariya.
Tashi ta yi daga jikin nasa a fusace ta ɗaga hannu zata kai mishi duka dan ya kureta ba kaɗan ba, kada ku manta daga ta ciki bala'in tsoronsa take ji. Cikin sauri daddy ya riƙe hannun nata tare da jawota jikinsa yana faɗin "Yi hakuri babyn daddynta". Juyowa Areef ɗin ya yi yana dariya sosai har da riƙe ciki, dan yau ya kureta, zuba mishi ido daddy ya yi yana mamaki, tun da yake da su bai taɓa kallon Areef ya yi dariya irin wannan mai sauti haka ba, yana dai murmushi, ya ma fisu dukka yawan murmushi kafin Aseef ya sami lafiya, amma dariya haka mai sauti har da rike ciki gaskiya bai taɓa gani ba.
Shi kuma Jehan ce ta bashi dariya, yadda ta ɗaure fuska har da ɗaga hannu wai zata kai mishi duka, to a ɗan hannun nan nata ma idan ta dake shi me zai ji ne wai? Ya tambayi kansa, abin da hannun nata ɗan siriri kamar muciya shi ne zata kai duka, gaskiya ta bashi dariya, daddy ya rungumeta yana ta kallon Areef, yau yaga abin mamaki, kuma Areef ɗin ya yi mugun kyau da yana dariya, harta Tyrone sake baki ya yi yana kallonsa ga trolleynsa dana daddyn a hannunsa.
Shi kam daddy ya kotsa ya ji labarin a ina suka sami Jehan? Yana son suje gida ya haɗa ƴaƴansa ya rungume, yau murna a wajensa ba'a magana, ji ya yi kamar ya zuba ruwa a kasa ya sha dan daɗi.
Sai da Areef ya yi dariyarsa mai isarsa kafin ya tsagaita ya ce "Uncle let's go, wannan babyn ƴar dirama ce". Kallon banza ta watsa mishi tare da jan guntun tsaki, shi dai daddy yana ganin ikon god yau, Jehan sarkin faɗa, Areef sarkin neman tsokana wannan abin yana bada sugar.
Hannunta ya kama suka nufi mota, daddy, Jehan da shi Areef ɗin, a baya suka zauna, Tyrone ya zauna a gidan gaba, Donal ya tashi motar sai gida, sai hararsa take yi, ga shi ita ce a tsakiya.
Sai zuba hira daddy da Areef ɗin suke yi tamkar wasu abokan juna, cikin hiran nasu ne ya ce "Uncle this our baby ta iya faɗa over". Murmushi daddy ya yi yana faɗin "Gadon faɗar ta yi ai, dole ne ma a samu masu faɗa a family'nmu da yawa, dan kuwa babana mafaɗaci ne number ɗaya, ta gefen mamana akwai su Trump wanda sun kasance ƴan uwanta ne, dukkansu sarakan faɗa da zafin rai ne sosai, duk ma mamanmu ita ce kaɗai bata da faɗa cikin ƴan uwan nata, haka babban yayanmu Abban su Imran, yana da faɗa sosai ga bala'in zuciya, yanzu ne ya yi sanyi, amma da, tab ba'a magana, shiyasa shi ma ya samu mafaɗaci ɗaya wato Akil, Abbi ma yana da faɗa, duk yanzu da girma ya kamasu ne suka yi sanyi, ban da haka ai ba'a magana, haka sisterta A'isha ita ma number ɗaya ce a faɗa, ina ga ma ita Jehan ta biyo, ga Jalilan Maik ma ta gada, so kaga faɗa ai gadon shi ta yi, ita dai My Rimsha ba ruwanta da faɗa, shiru take abinta, kowa nata ne".
Capke zancen ya yi da cewa "Yes uncle our Queen bata da faɗa, shiru take ma, sai da na koya mata yawan magana". Mamaki Jehan take yi wato dama shi ya koyawa Rimsha ɗan banzan surutun nan kenan, shigen ɗan ƙaramin bakinsa a wajen, ba zakaga baki ba sai rashin mutunci da surutu yana takurawa ƴaƴan mutane, da wani idonsa kamar ball ɗin mota, wlh zan yi maganin shi ne, sai zancen zuci take yi su kuma suna ta zuba hirarsu har suka isa gida.
A tare suka fito suka jera zuwa cikin gida, Areef ne ya riƙe trolleyn daddyn. Bedroom na sama in da Jehan ta fara zama farko, wato ɗakin Imran na farko, nan Areef ya kai daddy, kusa da ƴaƴansa abinsa, zata shiga bedroom ɗin ya tare mata baki kofa ya ce ta koma, kallon sama da kasa ta yi mishi kafin ta ce "Ni ka bani hanya na wuce hai". Kwaikwayar maganar tata ya yi yana murmushi, ji tayi kamar ta shakesa dan haushi, ga kuma bala'in tsoronsa da take ji.
"Wuce ki bani guri a nan, ba zaki shiga bedroom ɗin nan ba, uncle zai yi wanka ne ya kwanta ya huta, dan haka ki wuce naki bedroom ɗin ko na ɗauke ki na kai ki". Bata da zaɓi dole ta koma, dan tasan ƙaramin aikinsa ne ya ɗauketa cak ya kaita ɗin kamar yadda ya faɗa, dan haka sai ta shafawa kanta lafiya ta wuce abinta.
Tana shiga bedroom ɗin ta haye gadonsu ta kwanta, ba jimawa barci ya ɗauketa, shi kuma daddy wanka ya yi, ya shirya cikin kananan kaya abinsa, dan yanzu kwata kwata baya wani saka manyan kaya, ya zama irinsu sak, kuma dama yana sanya kannanan kayan sosai, sai dai zama dasu yasa ma gabaɗaya ya manta da manyan kaya ma a duniya. Bayan ya kammala sai ya fito palon saman, zaune a saman sofa ya isko Areef ga abinci ya jera mishi a kasa saman carpet yana jiransa.
Da fara'a ya kariso wajen suka zauna suna hira suna cin abinci a tare, bayan sun kammala Areef ɗin da kansa ya kwashe kayan ya mayar kitchen, duk abin da suke yi Lion yana ciki yana jinsu, amma tamkar babu shi a gidan, yana can yana harkar gabansa. A lokacin ne kuma su coper suka fara kuka suna daka haushi da karfi, fitowa Lion ɗin ya yi yana tambayar ina Aseef yake? Kowa sai dai ya ce bai san in da yake ba, hakan yasa ya kira numbersa network babu kyau bata shiga, shi ne ya ɗauki mota ya fita nemansa, su kuma su Areef suka zauna a palon suna jiran dawowarsa, dan Lion ɗin ya ce kada su fita. TO WANNAN SHI NE ABIN DA YA FARU DAGA JIYA ZUWA YAU, MU KOMA KAN LABARINMU TUN DA KUNJI YADDA AKA YI KOMAI.
Sai jiran Lion suke yi, amma shiru, Areef dai bawan Allah tamkar zai yi hauka, ya kira Lion har ya gaji ya yi wurgi da wayar, sai rarrashinsa tare da kwantar mishi da hankali daddyn Rimsha yake yi, duk da shi ma dai ya kasa ɗaukar abin, amma yana ƙoƙarin ganin ya jure, yau duk tsiwa irin na Jehan sai da ta yi sanyi ta rinƙa rarrashin Rimsha, ta kwanta a jikinta ta yi lamo, ban da ruwan hawaye ba wani abin da take yi, gida fa yau ya girgiza, gabaɗaya sojijin gidan sai da suka sha jinin jikinsu suka yi laushi, Mark idanun nan nasa sun yi jawur tamkar wuta, alamar shi ma ya shiga tsananin tashin hankali, domin kuwa duk wanda ya zauna da TRIPLETS ko da na kwana ɗaya ne, dole a yau idan ya ji labarin abin da ya faru zai yi musu kuka, dan dole zai san tsananin kaunar da suke yi wa junansu, dole a tausayawa Areef da Lion.
Da misalin karfe 1 Tyrone ya shigo cikin bedroom ɗin ya kira daddyn Rimsha suka fita waje, har lokacin gawar Aseef tana kwance a saman gadon, ba wanda ya taɓa shi, dole sai Lion ya dawo.
A ɓangaren Lion ɗin kuwa yana barin gidan kai tsaye gidansu Imran ya nufa, maza cike a kofar gidan ya samu suna kokarin ɗaura aure, bai bi ta kan kowa ba, ya yi parking na motarsa ya fito cikin takun katsaita, izza da kuma isa, idanuwansa tamkar wuta aka sanya a cikinsu saboda tsananin ja da suka yi, yau gabaɗaya fuskarsa a hargitse take, ganinsa kawai sai ya sanya mai karamin zuciya suma, babu alamar annuri ko tausayi ko kaɗan a face nasa, yau yana cikin tsantsar tashin hankali na wuce misali wanda babu mix ko kaɗan.
Bai bi ta kan kowa ba ya wuce cikin gida kai tsaye tamkar gidansa ne, baki su Abba suka buɗe suna ganin ikon Allah, daga ganinsa Abba yasan dole ɗan uwan Aseef ne, shi ma Akil hakance, yasan ɗan uwan Aseef ne, dan haka sai suka miƙe a tare shi da Abba suka nufi cikin gidan dan suga me Lion kuma zai yi, da sauri su Abbi suka rufa musu baya, shi kuma Imran yana gidan Lion ɗin bai dawo ba.
Kai tsaye cikin palo Lion ya wuce, ya wuce kowa dake wajen bai ce ko sannu ba, ko sallama ma bai yi ba, dan yau babu mutunci a tattare da shi. Mata ne cike a cikin palon, ba sallama ya faɗa, da kallo ɗaya ya yi wa Ammie dake tsaye a wajen bene zata haura sama ya gane ita ce mahaufiyar Imran, dan akwai Kamanni.
Cikin wata iriyar murya ta nuna isa da izza ya ce "Ke ina ƴarki?". Da yake ita ma taga kamanin Aseef a tattare da shi sai ta ce mishi "Tana cikin ɗakin can". Ta yi imanin su Aseef ba zasu cutar da su ba, kuma ita ma Aseef take son ƴar tata ta aura tun da shi ne zaɓinta, gabaɗaya palon ya yi tsit tamkar waƴan da ruwa ya ci su, sun zuba mishi ido suna ganin ikon Allah, ba wadda ta iya buɗe baki bare ta yi magana, dan basu ga wajen wargi ba, ko jaruman maza a yanayin da yake nan basu da kwarin gwiwar iya yi mishi magana bare mata.
Bai sake cewa komai ba ya nufi bedroom ɗin Akil da Ammie ta nuna mishi, babu ko sallam ya faɗa cikin ɗakin, tana kwance saman gado tana kuka kamar ranta zai fita, har wani irin shassheka take yi kamar mai numfashin fitar rai, ma'ana mai magagin mutuwa kenan.
Yana zuwa ya damƙo hannunta ya jata, miƙewa ta yi, ta diro kasa, jan hannunta ya yi suka fito ba tare da ya ce komai ba, da yake ita tana ganin hotonsa a wajen Aseef ta san shi, hotonsu su ukun ne ma a kan screen ɗin wayar Aseef ɗin, sannan ya turo mata hotunansu da dama, so ta san fuskar Lion sosai, bata musa ba ta bishi dan a tunaninta wajen Aseef zai kaita, shiyasa ta bishi dan bata da burin da ya wuce ta san wani hali Heartbeat ɗin nata yake ciki.
A tsakiyar palon kasa yaci karo da su Abba da suka shigo yanzu, ko kallon in da suke bai yi ba, ya nufi waje da ita, duk cikinsu an rasa mai karfin zuciyar tare gabansa ya tambaye shi ina zai kaita, duk rashin kunya da zafi irin na Akil yau ya kasa tare gaban Lion ya tambaye shi ina zai kai mishi sistersa, ido kawai suka bishi da shi dan basu ga alamar imani or tausayi ko wargi a tattare da Lion ɗin ba, basu ga fuskar da zasu iya tinkararsa ba.
Sai bayan ya fita da ita ne suka bi bayansa, shi dai Abbi yau yaga ikon Allah bawan Allah shi bai san komai ba, su Abba da suka sani basu yi mamaki sosai ba, abu ɗaya ne ya ɗaure musu kai a nan shi ne ina zai kai ta? Me zai yi mata.
Yana zuwa ya turata gidan baya na motarsa, shi kuma ya shiga mazaunin driver tare da ciro kuɗi mai uban yawa ya dubi su Abba da suke nufo motar tasa, rai a matukar ɓace da suka iso ya dubesu can kasa kasa ya ce "A cikin wanene ubanta?" Kallon juna suka yi.
Daddyn Jelly ne ya yi ta maza ya ce "Lafiya? wai me yake faruwa ne?" Ko kallon in da suke bai sake yi ba, ya mai da hankalinsa yana ƙoƙarin kunna motar, shi ma Abba fa bai wani damu ba, dan yana son ƴarsa sosai, yana son farincikinta, yana son ta auri wanda take so, kawai dai dan ba yadda zai yi ne, ɗan uwa ba wasa ba, ba zai iya hana Irfan ya bawa Aseef ba bayan ya bata Irfan ɗin, amma abin na yi mishi ciwo, shi ne ya danne ya hanata zaɓin nata, shiyasa yanzu da Lion ya zo bai wani damu sosai ba, abu ɗaya yake son ji shi ne ina za'a kai ta?.
"Tun da ba zaku gaya mini waye ubanta ba, ku karɓi wannan kuɗin shi ne sadakin ƴarku, zan ɗaura mata aure da gawar Aseef, aurenta shi ne burinsa na karshe dole na cika mishi, bayan haka ku saurari dawowata a karo na biyu dan sai kun biya ran Aseef wlh". Ya kai karshen maganar tare da watsa musu kuɗin ya ja motar da gudu ya yi gaba abinsa ya barsu tsaye sun kasa magana.
Ita kuma Akila tun da ta ji ya ambaci gawar Aseef numfashinta ya ɗauke diff tamkar an ɗauke wutar nepa, ta sume, tamkar ba mutun ya ɗauko ba, ko kallon in da take bai yi ba, kai tsaye babban masallaci ya nufa da ita, bayan ya je ne ya kira Tyrone a kan ya kawo mishi daddyn Rimsha ya zo ya zama waliyinta, shi kuma zai zama waliyin gawar Aseef. BABBAR MAGANA WANNAN SHI NE NUNA TSANTSAR ISA A KAN ABIN DA BA MALLAKINKA BA. Shi dai TRIPLETS nasa ne kawai mutane? Baya ɗaukar kowa da daraja bayan su ɗin? Lallai akwai aiki babba ma kuwa, daddy ya yi kuskure babba na irin tarbiyar da ya basu.
Bayan an kawo mishi daddyn Rimsha ya gaya mishi abin da yake da buƙata, sosai daddy ya ji daɗi dan kuwa shi ma ya ji muguwar zafin raba su da Abba ya yi, sai dai kuma da ya tuna Aseef ɗin ya rasu, sai wasu zafafan hawaye suka fara gangaro mishi a saman kuncinsa, shikenan yanzu Aseef ya tafi ya barsu? Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun, tunani ya fara yi wai shin an taɓa ɗaura aure da gawa ne?. Amma ya zai yi, ya zama mishi dole ya yi accepting dan ba'a yi wa Lion musu.
Haka ya zo ya zama walinta aka ɗaura auren, yau ga ikon Allah Lion ba shi ya haifi yarinya ba, amma saboda isa da izza ya fi karfin ya nemi alfarma ya roƙa a bashi cikin salama, kawai ya ɗauko yarinya tana sume ya ɗaura mata aure, wannan izza anya akwai biyunta a duniya kuwa? Daga karshe dai an ɗaura aure Akila da gawar Aseef wannan shi ne tashin sense da ba'a saka mishi date.
Sadaka ya yi mai tarin yawa a Masallacin bayan an ɗaura auren, kafin su shiga mota da nufin su koma gida a je a yiwa Aseef sutura, gidan baya daddyn Rimsha ya shiga in da Akilar take, shi kuma ya shiga gidan gaba.
Suna shiga daddyn Rimsha ya ga Akilar tana sume, hakan yasa ya ɗauko ruwan dake gaban motar ya yayyafa mata, shi kuma Lion ya kunna motar da nufin su wuce gida.
A razane ta farka tana ambatar "Heartbeat bai mutu ba, ni nasan bai mutu ba, wlh yana raye, ya yi mini alkawarin zai rayu dani, ni nasan ba zai karya mini alkawarina ba, wlh ba zai mutu ba, dan girman Allah ku ce mutuwa ta barshi ni ta zo ta ɗauke ni, Wayyo Abbana nashiga uku!". Da alama ta fita a hayyacinta sosai, riketa daddyn Rimsha ya yi yana rarrashinta sosai, shi kuwa Lion jin surutanta yasa ya kara gudun motar, kamar yadda zuciyarsa take tafasa haka yake kara taka motar shi ma, ba ƙaramin tsorota daddy ya yi da irin gudun da yake shararawa ba, kada su je su yi accident.
Shi kuma bawan Allah zuciyarsa ne take tamkar zata fashe yasa yake taka motar da karfi, Allah dai ya tsare sun isa gida lafiya, yau dai gabaɗaya gidan daga kan sojiji har cikin gida kowa jugum jugum yake kamar ruwa ya cinyesu.