Kenza eBookz

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 76

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 76

Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 76: Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 76. "A'a ka bari sai ka samu sauki, yanzu dai ka…

3,325 words

"A'a ka bari sai ka samu sauki, yanzu dai ka bani na ci a nan, idan ka samu sauki sai na rinƙa zama a kafar taka kana bani a baki ina baka". Shagwaɓe murya ya yi yana faɗin "Wai ba yanzu su Abba suka gama cewa kada ki yi mini musu ba? Ba sun ce komai nace ki ce okey ba? Shi ne daga tafiyarsu zaki fara ce mini a'a ko?". Girgiza mishi kai tayi alamar a'a tare da miƙewa ta zauna a saman cinyar tasa tana faɗin "Kayi hakuri ba zan sake ba".

"Tom Allah ya yi miki albarka". Murmushin ta saki wato ya ɗauki nasihar daddyn Jelly kenan, dan daddyn Jelly ne ya ce mishi ya kasance mai yawan sakawa matarsa Albarka dan addu'arsa a gareta mai karɓuwa ce, idan yana saka mata albarka, to zata yi Albarka sosai, idan kuma ta yi Albarka gidansa ne ta gyaru, dan mace ita ce gida, idan ta yi albarka gida, arziki da komai na miji zai yi albarka, idan kuma ta lallace, to fa miji ko da babban malami ne zaku ganshi sai a hankali, yana tafiya yana magana shi kaɗai kamar zararre dan matar ta haukata shi saboda rashin albarka, Allah kasa maza su zama masu sanyawa matansu Albarka kamar yadda Annabi yake sanyawa su nana A'isha a kullum, Allah kasa mazanmu gabaɗaya ban cire kowa ba da masu aure da marasa aure har yara, Allah kasa su rinƙa koyi da annabin rahma a dukkannin lamuransu dan gyara gobensu.

Abincin ya fara bata a baki, cikin natsuwa ta fara karɓa tana ci, sai kallonta yake yi yana murmushi, ita ma yau ba zata iya misilta farincikin da take ciki ba. Ta ci abincin mai ɗan yawa dan tun safe rabonta da abin, cin abinci ta ƙoshi kuma tun ranar da Abba ya ce ya bawa Irfan aurenta, daga ranar ta dai'na cin abinci ta koshi sai dai ta ɗan tsakura kawai dan kada yunwa ya kasheta, yau kuma gata a zaune a saman cinyar Heartbeat nata, yana bata abicni a baki, kai Allah iko kenan, wannan rana ba zasu taɓa mantawa da shi ba dukkansu biyu.

Sai da ya tabbatar ta ƙoshi sosai sannan ya kyaleta tare da bata ruwa ta sha. "My shagwaɓati zan je in yi brush, amma bani da brush ɗin ma a nan gidan". Sumbatar kumatunta ya yi kafin ya ce "Jeki bedroom na kiyi, sai ki yi amfani da brush na ko?".

"To ban san ina ne bedroom ɗin naka ba ai". Yadda ta yi maganar a shagwaɓe, kwaikwayon muryarta ya yi tare da yi mata kwatancen bedroom ɗin nasa. Miƙewa ta yi tare da ɗaukar kayan abincin ta nufi waje, binta da kallo ya yi yana faɗin kada fa ta jima, okey ta amsa mishi da shi, kwanciya ya yi tare da jawo bargo zuwa cikinsa, yana son tashi ya sanya ɗaya daga cikin kayan barcin Lion ya yi brush amma ba zai iya ba saboda jiri, dole haka ya kwanta da jallabiyar ba dan ya so ba.

After some minutes ta dawo bakinta ɗauke da sallama hannunta rike da brush ɗin nasa da wani kwano mai ɗan girma sai roban ruwa guda ɗaya, ba ƙaramin daɗi ya ji ba dama yana tunanin yadda zai yi ya shiga toilet ɗin Lion ya yi brush tun da akwai brush da dama a ciki sabbi.

Saman bedside drawer ta zauna tana faɗin "My shagwaɓati naga akwai brushs dayawa a cikin toilet ɗin naka, kuma dukka sabbi ne". Ɗan shagwaɓe murya ya yi. "E na sani amma da nawa wanda nake amfani da shi nake son ki goge bakin ai". Cool murmushi ta saki dan kuwa da shi ɗin ta yi amfani abinta, ga na mijinta me zata yi da sabo? Ai babu.

Miƙa mishi brush ɗin ta yi tana faɗin "To kai ma ga shi nan ka yi". Make mata kafaɗa ya yi. "No ni ke zaki yi mini idan ba haka ba ba zan yi ba". A tsananin shagwaɓe ya yi maganar.

Ba musu ta miƙe ta dawo gefen gadon tare da sanya mishi kwanon a saitin gemunsa kafin ta sanya mishi brush ɗin ta fara goge mishi kyawawa kuma fararen hakwaran nasa, farare tas dasu kamar audiga, ga su a shirye kamar shiryayyun masara, datsan datsan da su gwanin ban sha'awa.

Tas ta goge mishi tare da bashi ruwan roban da ta kawo ya kurkure baki, mikewa ta yi ta nufi wajen dressing room ɗin Lion ɗin bayan ta ajiye kwanon a kasa ta bashi brush ɗin a hannunsa ya rike mata, ta sha ruwan mamakin ganin dressing room ɗin, ƴar kauye ta zama a ciki, da kyar ta iya dannewa ta ɗauko wani ɗan karamin towel fari ta ciro shi daga cikin ledarsa tas da shi.

Bakin nasa ta zo ta goge mishi da towel ɗin kafin ta karɓi brush ɗin ta haɗa da kwanon ta ɗauka ta nufi waje, Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke yana binta da kallo tare da yiwa Ubangiji godiya daya mallaka mishi ita, tana da hankali ga sanin darajan mijinta, ta san ta yadda zata kula da kayanta.

Bakinta ɗauke da sallama ta dawo cikin ɗakin, saman bedside drawer ta zauna tana kallon shi, hannu yasa ya nuna mata gefensa a kan ta zo ta zauna, da farko kamar zata ce mishi a'a, sai kuma ta tuna nasihar su Abba kada ta yi mishi musu, dan haka sai ta miƙe ta koma kusa da shi ɗin.

A hankali ya kai hannu ya cire mata hijabin jikinta tare da ɗaura shi saman bedside drawer. "Meyasa zaki wahalar mini da kanki wajen saka wannan abin kuma?" Murmushin kawai ta yi ba tare da ta yi magana ba.

Ɗan taɓata ya yi ganin tana hamma tare da nuna mata saman kirjinsa a kan ta kwanta, kallon shi ta yi tana turo baki, shagwaɓe murya ya yi tamakar zai saka mata kuka "Wai ba Areef ya ce na baki kulawa bane? Yanzu ki zo ki kwanta na baki kulawa har ki yi barci mana, dan naga barci kike ji". Ɗan kallon ɗakin ta yi kafin ta ce "My shagwaɓati ina cewa wannan ɗakin Lion ne?". Jinjina mata kai ya yi alamar e ɗakin Lion ne. "To meyasa zamu kwana a ciki? Shi kuma a ina zai kwana?".

Hannu ya kai ya jawota jikinsa, kasa kasa ya ce "Shi Lion ai yana da wajen kwana da yawa a gidan nan, kada ki damu, yasan muna nan ba zai dawo ba, baki ga ya sanya jacket kafin ya fita bane? Har kayan barci ya sanya kafin ya fita, baya sanya kayan barci har sai idan zai kwanta, ko garden zai je da normal kaya yake zuwa, amma yau da kayan barci ya fita, so ya sallami ɗakin nan kenan, ya bar mini ni da ke, sai gobe zamu koma bedroom namu, yau dai muna nan.

Lafewa ta yi a kirjin nasa tana shakar daddaɗar kamshin perfume ɗin Lion dake jikinsa, dan yau da shi ya yi amfani, sauke bargon kasa ya yi tare da ɗan gyara mata ta kwanta da kyau a jikin nasa kafin ya hauro da bargon ya rufesu zuwa kirjinsa, iya kanta kawai ya bar mata a waje, ɗauko remote na Ac ya yi tare da kara gudun sannan ya kashe wutar ɗakin ya kunna lamp mai bada sky blue light.

"My rigimati". Ya ambaci sunanta kasa kasa, a shagwaɓe ta amsa mishi da na'am my shagwaɓati, "Barci zaki yi baki bani hot kiss ba?" Ɗan ɗago kanta ta yi tana kallon shi. "Ni ɗazun da safe ma waye ya ce kayi mini kiss?". "Lips naki ne ko nawa?" Ya faɗa a shagwaɓe, mayar da kanta ta yi ta kwantar a saman kirjin nasa tana murmushi sosai, tana bala'in kaunar mijin nan nata shagwaɓatin ta.

Hannunsa ya ɗaura saman hulan kayan barcin dake kanta, a hankali ya zame hular daga kan nata ya ajiye a gefe, shafa lallausan gashin kanta ya fara yi yana gangarowa har zuwan bayanta, cikin shagwaɓa yake gaya mata kalamai masu daɗi tare da tayata murnar yau sun mallaki juna, hannu ita ma ta ɗaura saman kansa tana shafa gashinsa tare da bashi amsar duk wata kalma ta so da ya gaya mata, sai murmushi suke yi, ransu fes, a hankali yake ta juyar da ita tana komawa rabin jikinta a saman bed ɗin har suka zama irin kwanciyar nan na suna fuskantar juna, matso da face nasa daf da tata ya yi yana faɗin "Da nace ki bani hot kiss kin ki yanzu ai zan sha kayan".

Ɗan turo bakin nata ta yi tana faɗin "Ni bari ma na tashi na tafi ɗakin mu, sai da safe, ai na tayaka hira haka ya isa". Hannu ɗaya ya sanya ya rufe mata idanu tare da ɗaura lips nasa saman tata ya fara bata kiss, nauyayyar ajiyar zuciya suka sauke su dukkansu biyu a tare, kara jawota jikinsa ya yi ita kuma ta ɗaura hannunta ɗaya a saman bayansa tana mai mayar mishi da martanin kiss ɗin da yake yi mata.

Shafa bayanta ya fara yi har zuwa saman mazaunanta, harshenta ta zura cikin bakinsa tana wasa da nasa harshen, shafa mazaunan nata ya fara yi yana kara narke mata, a hankali ya same hannunsa dake saman idanunta ya mayar saman breast nata, caraf ta capke hannun nasa tare da kwace bakinta tana faɗin "Uhm uhm kai my shagwaɓatina, wai ba zaka barni nayi barci bane? Na gaji fa". Kukan shagwaɓa ya sanya mata "Ni to kiyi barcin ki mana na hanaki me? Ni ki barni na taɓa kayana". Ita ma kukan shagwaɓar ta saka mishi. "Ni gaskiya ba zan barka ba, ka taɓa ganin ana taɓa mutun kuma ya yi barci ne? Ai idan kana taɓani ba zan yi barci ba, please mana my shagwaɓati, barci nake ji sosai, Allah na gaji dayawa".

Lumshe idanuwansa ya yi yana faɗin "To ki barni na taɓa sau ɗaya zan barki, kinga da safe ma kin hanani taɓawa ko? Da safe ba mallakina bane, yanzu kuma mallaki na ne, please mana My rigimati, sau ɗaya fa". Sakin hannun nasa ta yi tare da kwantar da kanta a gefen kirjin nasa. "Kin yarda na taɓa?" Ya tambayeta a tsananin shagwaɓe, bawan Allah sam baya son ya yi mata abin da bata so, shi farincikinta ya fi mishi komai.

Jinjina mishi kai ta yi almar ta yarda, sumbatar goshinta ya yi. "I really love you my wife, my heartbeat, My rigimati". "I love you too my shagwaɓati". Ta faɗa cikin muryar barci, dan barci sosai take ki baiwar Allah, ta gaji, ta sha wahala, hannu ya kai ya ɗan shafa bayanta kafin ya dawo da hannun nasa saman breast ɗin nata, Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke jin su irin wanda yake ra'ayi, suna cike ɓul ɓul tamkar an hura balo balo. A hankali ya ɗan matsa mata su kafin ya sakesu ya jawota jikinsa sosai yana sauke ajiyar zuciya, a hankali ya fara shafa bayanta har barci ya yi awon gaba da su bakiɗaya, suna cikin tsantsar farinciki na wuce misali.

A ɓangaren daddyn Rimsha da Areef kuwa, hira suka rinƙa zubawa suna kwance har barci ya kwashe su, yau dai Areef a ɗakin daddy ya kwana.

A can waje kuwa wato garden, bayan ta gama zamanta sai ta miƙe da taga babu sarki sai Allah, lokacin kuma Already duk sun hi barci, kusa da shi ta zo ta zauna, sai zuba barcinsa yake yi cikin kwanciyar hankali ya jingina kansa da jikin headboard na sofar. "Yaya Saif dan Allah ɗan bani wayarka bari na kira yaya Areef ya zo ya buɗe mini kofa, ko na buga kofar nasan ba zasu ji ba". Shiru bai amsa mata ba, ya ji duk abin da ta ce, dan tana zama a kusa da shi ya farka, sai dai bai buɗe idanunsa bane kawai, amma ya farka.

Miƙewa ya yi ya gyara kwanciyarsa a saman sofar tare da laluɓar wayar tasa idanu a rufe ya cire mata password ɗin wayar ya miƙa mata, miƙewa ta yi daga saman sofar dan ta bashi damar mike kafafunsa da kyau, duk da cewa ma yafi sofar tsawo dama, amma idan ya miƙe kafafun dai zai fi jin daɗin kwanciyar.

Karɓar wayar ta yi, gabaɗaya babu app ko guda a cikin wayar, sake baki ta yi tana tunanin ina apps ɗin kuma suke? Ina wajen contact da sauruansu? Bata san wayar muguwar security ke gareta ba, apps ɗin suna nan, amma sai idan shi ya fitar mata da wanda zata yi amfani da shi, duk suna karkashin tsaro ne, babu mai ganinsu sai idan ya fitar mata da contact ɗin zata ganshi, idan yana so kuma dukka zai iya fitarwa lokaci guda, duk yadda yake so zai iya sarrafa wayarsa.

Tsugunnawa ta yi a kusa da shi cikin sanyin murya ta ce "Yaya Saif ban kalli contract ɗin ba". Shi gabaɗaya ma ya manta bai fitar mata ba, karɓar wayar ya yi har lokacin idanunsa a lumshe, babbar yatsansa ya daura a saman screen ɗin ya ɗan ja kasa sai ga apps ɗin gabaɗaya sun fito, karɓa ta yi tare da shiga contact, My pleasure ta gani, shi ta kira, number Aseef ne, wayar tana cikin mota a rufe, ta yi ringin har ya kaste ba'a ɗaga ba, sake kira ta yi, nan ma shiru, har sau huɗu tana kira ba'a ɗauka ba, shiga can cikin contracts ɗin nasa ta yi dan ta duba number Aseef, a tunaninta na Areef ta kira, ta san cewa su biyu ne a duniyar nan zai yi saving numbersu da haka.

Out heartbeat ta sake cin karo da shi, murmushi ta saki dan a tunaninta number Aseef ɗin kenan, ta yi gaskiya tunaninta gaskiya ne, number Aseef ɗin ne, amma numbersa na Washington DC ne, wanda ta kira da farko kuma na nan Nigeria ne, number a kashe take, guntun tsaki taja jin bata shiga, yanzu a tunaninta ta kira Aseef da Areef kenan, bata san dukka number Aseef kawai ta kira ba.

Number daddynta ta fara rubutawa dan ta haddace a kanta, ga mamakinta sai taga ya yi saving da sunan Uncle, shiru ta yi tana tunanin kenan shi ma ya ɗauki daddynta uncle nasa kamar yadda su Aseef suka ɗauke shi ne? Abin ya bata mamaki, kiran number ta yi, a kashe dan number Washington DC ne ba zata yi amfani a Nigeria ba, shiru ta yi tana tunanin waye zata kira kuma.

Ganin babu ne yasa ta fara bincika mishi contact nasa tana ganin sunayen da ya yi saving numbobi mutane, daga uncle T, uncle Herry, Jay, John, General, su Major, Captain Peter da sai sauransu, su ne dai a wayar babu wata suna mai daɗi bayan nasu Aseef, shi ma Imran Prof ya sanya mishi, Josephine kuwa mummy ya sanya mata, amma kuma baya kiranta mummyn a baki, sai dai ya ce mata Josephine, duk da ma da wuya kaji ya yi maganar ta, amma idan zai yi Josephine ɗin yake faɗe a baki, amma ya yi saving num ɗinta da mummy, da alama lokacin da ya musulta ne ma ya sanya numberta a wayarsa har ya sanya mata mummyn, dan kuwa a baya bashi ma da numberta sam, kuma tun da ya musulta bai yi maganarta ba, wata kila yanzu tun da ya musulta zai iya ce mata mummyn kamar yadda ya yi saving numberta, shi ɗin ne baka gane mishi!.

Ta wuce number Areef da ya yi saving da My pleasure, sai dai ta ɗauka number da ta kira da farko ne, sai bata gwada kira ba, yana barci tana yi mishi bincike a contracts nasa. Sai da ta ji wayar ta buga karfe 11 daidai sannan ta ajiye mishi a kusa da shi tare da komawa ɗayar sofar ta takure waje guda danma yau akwai hijabi a jikinta, duk da ba mai girma bane bai kai gwiwowinta ba, amma ya ɗan tare mata sanyi kaɗan, ta takure saboda tsoro, da kyar ta iya samu barci ya yi awon gaba da ita, gabanta sai faɗuwa yake yi.

Can wuraren asuba irin karfe huɗun nan ta farka tare da waro idanunta waje, a hankali ta miƙe zaune tana kallon in da yake kwance, ga mamakinta sai bata ga jacket a jikinsa ba, ɗan waigawa da zata yi, sai taga jacket ɗin a jininta ya rufa mata, shiru ta yi tana tunanin yaushe aka yi hakan kuma? Bata san cikin dare irin karfe 1 nan ta dame shi da rawan sanyi ne ya je ya rufa mata jacket ɗin nasa ba, sai kakkarwa take yi hakwaranta na garuwa waje guda, shi kuma hakan yana hana shi yin barci, dan komai kankantar motsi yana farkar da shi daga barcin nasa, hakan yasa ya farka ya cire jacket ɗin ya sanya mata, shi ne ta samu ta cigaba da barci cikin salama, shi ma ya samu barci mai daɗi cikin salama ba tare da takurarta ba.

Wani irin daɗi ta ji ganin hakan, ɗaukar jacket ɗin ta yi ta manna mishi kiss tare da sanyawa a jikinta tana bin garin da kallo, akwai hasken farin wata, tun farkawarta ta farkar da shi, motsinta ya tashe shi, sai dai bai buɗe idanu ba. Ai dama dole Lion ba zai yi nauyin barci ba, General Of the army fa, ai ba'a barci ya kai wannan mukami ba, tun bai kai mukamin ba suka saba da rashin nauyin barci saboda jiran harin abokan gaba a koda yaushe, lokacin da suke bakin iyaka, a kowani lokaci abokan gaba suna iya farmakansu, hakan yasa basu da nauyin barci, komai kankantar motsi zai tashe su, abin tun daga training suka samo shi, shi yanzu ba wani aiki yake yi bama ya kai mukamin hutu, sai dai aikin da ya ga dama ya saka kansa zai yi, amma rashin nauyin barcin tabi jikinsa, ya zamar masa jiki abin, ko yaya ka motsa kusa da shi sai ya ji, sai dai ya basar ya cigaba da lumshe idanunsa kawai har barcin ta sake ɗaukarsa.

Haka suka kasance har asuba, sai da ya fara jin kiraye kirayen sallah ne ya miƙe ya nufi cikin gida, da sauri ta bi bayansa, bedroom na kasa ɗaya sabon da ba'a taɓa shiga ba, nan ya shiga dan ya yi wanka da alwala, akwai bedroom a kasa wanda mutun bai taɓa shiga ba, komai na ciki sabo ne, amma yaki zuwa ya kwana a ciki, gara mishi garden, dama kuma already kwanan garden kam ya saba, dan raba dare yake yi a wajen, wani lokaci sai karfe 2 yake shiga cikin gida, kusan za'a ce kawai kwana a ciki yake yi.

Wanka da alwala ya yi tare da fitowa ya nufi bedroom nasa dan ya canza kayan jikinsa zuwa jallabiya, shi ba ruwansa dan su Aseef suna ciki, matsalarsu ce, dan ya ga Aseef ɗin yana son bedroom ɗin nasan ne ma yasa ya bar musu. Sai zuba barcinsu suke yi rungume da juna a cikin bargo, ko kallon in da suke bai yi ba ya wuce dressing room.

Jim kaɗan ya fito sanye da jallabiya fara tas ya fito ya nufi masallaci, a palon kasa ya cikaro da Areef da daddyn Rimsha, ko kallon in da suke suma bai yi ba ya wuce abinsa zuwa masallaci.

Ita kuma bedroom nasu ta koma, Jehan na ta zuba barci, toilet ta nufa, tsarki da alwala ta ɗauro tare da fitowa ta shinfiɗa dadduma bayan ta saka katon hijabi ta tada sallah.

Sai bayan ta idar ne ta tashi Jehan dan ta yi sallah, da kyar ta tashi tana yatsine fuska, ita kuma hawa gado ta yi ta kwanta zuwa karfe 6 ta tashi ta yi shirin zuwa school, Mark ne ya kaita kamar kullum, har ta tafi school ɗin kuma basu haɗu da Lion ba.

Yau jirginsu daddyn Lion ya ɗaga da misalin karfe 10 na safe daga Washington DC zuwa Naija, to sai dai muce Allah ya kawo ku lafiya, sun bar uncle T a gida yana jinya.

Readers Also Read