Kenza eBookz

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 77

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 77

Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 77: Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 77. Da misalin karfe 10:30 Lion yana zaune a…

3,298 words

Da misalin karfe 10:30 Lion yana zaune a gefen bed nasa, Aseef kuwa Areef ya mayar da shi bedroom nasa, Akila tana tare da mijinta, Areef da daddyn Rimsha suna zaune a palon sama suna hira, ita kuma Jehan tana ɗaki dan bata son fitowa Areef ya takura mata, haushi ma yake bata ɗan rainin wayo a cewarta.

Kiran number Areef Lion ya yi dan ya zo su yi magana, ganin kiran yasa ya miƙe yana faɗin "Uncle ina zuwa ka jirani". Okey ya amsa da shi, duk abin da suke faɗe Lion yana jinsu sarai dan a palon sama suke kusa da bedroom nasa.

Da sallama ɗauke a bakinsa ya shiga bedroom ɗin, kallo ɗaya Lion ɗin ya yi mishi ya kawar da kansa izuwa saman wayarsa, laptop nasa tana garden sun barota a can.

A gefensa Areef ɗin ya zauna yana yi mishi good morning, cikin mutunci da kaunar juna suka gaisa, sai murmushi Areef yake zubawa daddy ya bashi auren Jehan.

"Areef zan yi tafiya zuwa kasar Russia nan da kwana uku, so ka kula da su daddy da kowa, zan tafi da ɗaya daga cikin yaran nan, ko ƙaramar ko babbar, nafi son ma na tafi da babbar dan ita ce mai kama da ubanta, na gaya maka tun yau ne dan iya yau ɗin ne kawai nake da time na zaman magana, akwai sauran abubuwan da zan kammala kafin na tafi, so ina busy". Zaro idanu ya yi yana faɗin "Lion Russia kuma?!". Shiru bai amsa mishi ba.

"Amma dai kasan bamu shiri da kasar Russia ko kaɗan ko? Kana jami'e zaka shiga kasar, to mema zaka je yi a can?".

Ya ɗan ɗauki lokaci kafin ya amsa mishi da "Kakansu zan ɗauko, ƴar Russia ce ai, so tana wajen iyayenta sun kamata sun rufeta a ɗaki dole dole sai ta zama kafura kafin su saketa tayi rayuwa kamar ko". Shiru Areef ya yi yana tunanin wannan bala'i da Lion yake neman jefa kansa, ya sani basu ko ga maciji da kasar Russia, ƙasar America da Russia sam basu shiri ko kaɗan, babu mutunci a tsakaninsu, sannan ya ce zai shiga cikin kasar ya ɗauko ƴar cikin kasar, dama ga shi family'nta a kule suke da Family'n Dr Salman, ya je su sauke haushin a kansa, dan cewa ma zasu yi ko shima ɗin family'n Dr Salman ɗin ne, tun daga nesa su harbe shi da bindiga ko su yi mishi wani abin, lallai kam akwai ƙura, amma kuma yana da kyau a ɗauko Na'urat ɗin dan kada su sanyata ta yi ridda, sai dai fa daddy ba zai taɓa yarda ayi wannan tafiya ba, barema idan ya ji akan abin da ake rikici ƴan uwan Naurat sun hasala sun fusata an musuluntar musu da ƴar uwa, idan baku manta ba ya tsani musulmai, ya ji labarin sun kamata sun rufe tsawon shekaru taki yarda ta zama krista, haushi kamar su rataye kansu ne Lion ya ce zai shiga har cikin gidansu ya ɗaukota, anya kuwa hakan zai yiwu? Akwai babban haɗari gaskiya, da wuya ma gwamnatin kasar ta barshi ya shiga cikin kasar, ina bama zai yiwu ba.

"Kai sarkin tunani, ta ruwa zan shiga kasar, kuma na gaya maka zan tafi da yarinya ɗaya dan mu sami jituwa tsakanina da matar, so ka kula sosai". Da yake yasan Lion idan ya yi magana baya canzawa sai ya ce "Allah ya bada sa'a ya kare mana kai, amma fa Lion to sai dai ka tafi da Rimsha ba dai Jehan ba, ni ba zan iya yin kwana ɗaya ban ga baby ba". "Dama da farko da ita naso tafiya, amma tsoronta ya yi yawa shiyasa nace zan tafi da babbar".

Tsuke fuska ya yi yana faɗin "Wlh hakuri zaka yi ka tafi da ita ɗin dai, baby kam babu in da zata je gaskiya, idan ba kana son wlh nabi bayanku ba in ka tafi da ita". Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Bari na sanya Mark ya shirya sojoji biyar da shi Mark ɗin shida kenan, sun isa dan kula da jirgin ruwan da zamu tafi da shi".

Nan take wani tunani ya faɗowa Areef, to in dai haka ne ta jirgin tuwa zasu bi ai ya sami hanyar da zai sanya Lion ya yi aure cikin sauki, amma bari ya gwada duk da yasan da wuya ya amince.

Nisawa ya yi tare da fara magana a tsantsar nitse kamar wani malami mai yin wa'azi. "Lion in dai haka ne to bai kamata ka tafi da Rimsha a haka ba, kasan dai ba ta yadda za'ayi ta zauna a cikin sojoji ko? Dole a kusa da kai zata zauna, duk da akwai wasu ɗakuna a cikin jirgin, amma a kusa da kai zata zauna dan tsaron lafiyarta da kuma kula da ita, ba zai yiwu ka barta a wani ɗaki daban kai kana wani daban ba, dole a ɗakinka zata zauna, kuma kasanta dama da bala'in tsoro sosai, baza ta taɓa yarda a cikin waƴan nan tabka tabkan takun da zaku keta cikin jirgin ruwa yana tafiya ta yarda ta kwanta a ɗaki ita kaɗai ba, zata yi ta ganin kamar mutuwa zata yi ko zata nitse cikin ruwa, kasan tafiya a cikin ruwa fa sai wanda ya daure, ruwa yana da giggiwar ɗibar mutun kamar jiri idan yana da yawa, so zata tsorata sosai, idan kuma a ɗakinka zata zauna kaga a matsayinta na mace ba muharramarka ba haramun ne a addini, so yanzu kawai a ɗaura muku aure yadda zata zauna a ɗakin naka ba tare da wani tsinuwar mala'iku ya sauka a kanku ba, idan kun dawo daga tafiya zaka iya sakinta tun da kun gama aikin".

Guntun tsaki ya ja tare da ɗaukar wayarsa ya fara latsawa dan Areef bashi da hankali ya lura, aure kuma shi? Abu kamar hauka ko wasan yara, haba ai shi bashi da lokacin yin aure, bashi ma da lokacin mace, gani yake yi Areef ya samu matsala ne a kwakwalwarsa, so bai kamata ma ya bashi amsar wannan shirme da hauka ba.

Shi kuwa Areef dan ya karawa abin armashi da kara haɓakata dan ya tabbatar da zancensa har da mikewa ya nufi waje yana faɗin "Bari na fara yin magana da uncle zan dawo mu karisa maganar mu".

Ko kallon in da yake bai yi ba, dan bama da Rimshar zai tafi ba, da Jehan ɗin zai tafi dan tafi dakiya da rashin tsoro, Rimsha tana ganin wani bala'in ai rungume shi zata yi ta hana shi cetansu da kuma cetanta, ta ja a ci galaba a kansu, yasan kuma ba ƙaramin yaki za'ayi ba kafin ya shiga kasar Russia, akwai cakwakiya, ya yi alkawarin kuma sai ya kammala case ɗin Nawazudden tas zai koma kasarsu, yana son haɗa shi da kowa da kowa nasa su koma kamar da ne. Wannan aiki idan ba General Of Army ba waye zai iya shi? Su kansu su daddyn basu san in da mahaifiyarsu take ba, amma har ya nemota zai je ɗauko ta, zai shiga gagarumin haɗari saboda su, gaskiya daddyn Rimsha ya ciri tuta, Lion ya yi mishi abubuwa da yawa, sai dai shi kuma daddyn yana kullace da Lion ɗin na abin da ya faru a tsakaninsu, bawan Allah bai san gagarumin taimakon da Lion ɗin ya yi mishi bane, da ya sani ba zai kulkace shi ba.

Zama Areef ya yi kusa da daddy yana faɗin "Uncle ina so ne ka bawa Lion auren Rimsha zasu yi tafiya, idan suka dawo zai saketa, kaga bai dace su yi tafiya a haka ba suna matsayin da sukenan, Rimsha ta girma ai".

Areef ya tabbaka babban kuskure a maganarsa da ya ce a bawa Lion auren Rimsha zasu yi tafiya ne, idan ya dawo zai saketa, sai kace wata kayan wanki ko kayan gwanjo, wani uba ne zai yarda da hakan? Ƴar cikinsa fa, Rimsha 14 years a mayar da ita bazawara ne kenan ko yaya? Haba maganar ta yi muni over, ai wlh koda ba zai saketa bama daddy ba zai bashi aurenta ba bare kuma har da wani cewa idan suka dawo zai saketa kamar wata kaza, maganar ta konawa daddy rai over, shi kuma Areef bai yi mishi bayanin Lion da wuya ya saketa ɗin ba, tarko Areef ɗin ya kafa mishi dan ya kamu da sonta ai, shi kawai ya faɗi maganar ne dan yana tunanin daddyn yasan komai da yake wakana, bai san cewa tun da ya zo ai bai samu zama dasu Rimshar ba bare ya fahimci akwai kusanci tsakaninta da Lion ɗin.

Rai a matukar ɓace shi ma daddyn ya tabbaka babban kuskure wanda ya dawo yana danasani mara amfani, dan kuwa cikin fushi ya ce "Wlh Allah ya sauwaka na bawa Saif auren ƴata, koda ma yana sonta ba zan bashi ita ba bare kuma baya sonta, tafiya zasu yi idan ya dawo ya sake ta, ita ɗin an gaya maka kayan wanki ce? Ko kaza ce? Wlh ba zan bashi ba, ko namutu sai na bada wasiha kada a bashi ƴata".

Dama kuma duk wani uba na kirki zai ji zafin magana irin haka idan akayi ta a kan ƴarsa, sai dai daddyn a in da ya yi kuskure yasan halin Lion ɗin, amma yana bari zuciya ta ɗebesa tasa ya yi abin da zai na danasani daga baya, ya san cewa idan Lion ya ce abu to ba yadda ya iya da shi sai hakuri, amma haka wani lokaci idan ya hau dokin zuciya idanunsa suka rufewa ya faɗi kalamai masu zafi.

To a wannan rana ma tarihi ce ta maimaita kanta, domin kuwa Lion ya ji duk abin da suka faɗa, hakan ta sanya shi ya fito cikin kunan rai ya yi wasu maganganu masu zafi ga daddyn. "Ba zan auri ƴar ka ba saboda baka so ko? To wai kai baka san ni duk abin da ba'a so shi nake yi ba ne? Bani da ra'ayin yin aure a rayuwata, amma a yau yanzu ba sai anjuma ba za'a ɗaura aurena da ƴarka, sannan ka sani zan yi tafiya da ita kamar yadda Areef ya faɗa, da ba da ita zan tafi ba, amma yanzu da kayi magana da ita zan tafi, sannan kuma kai ne waliyin da zaka karɓi wannan auren kuma ka bayar ko kana so ko baka so! Daga karshe kuma sai ka fara azumin kaffara na rantsuwar da kayi ba zan aureta ba!!". Tashin hankali, danasani daddy ya farayi na maganganun da ya yi, domin kuwa ya sani auren Rimsha da Lion yau babu fashi kamar yadda Lion ɗin ya faɗa, shikenan yanzu ya ɓatawa ƴarsa rayuwa da kansa da kalamansa? Magana kalilan ta sanya ya cuci yarsa, yana shirin ko ace ya jefata cikin wahala? La ilahi ya lilliahi.

Shi kam Areef sam bai so abin ya zo musu a karo na biyu ma da haka ba, ya so ne su fahimci juna, bai san meyasa sam daddyn Rimsha da Lion basu shiri ba, basu haɗuwa inuwa ɗaya, daddy zuciya da saurin hawa, idan ya hau kuma baya iya controlling kansa, sannan bugu da kari shima yana da izza, shi kuma Lion duk balai idan ka ɗaga mishi murya tofa sai ya sanya kayi laushi, bare kuma daddy da yake faɗan maganganu masu zafi akan Lion ɗin, ai dole bazasu shirya ba, dole kullum idan suka haɗu sai ta kwaɓe musu, idan bai yi sa'a bama ya jawa Rimsha bala'i kenan, dan da wuya idan Lion ba zai azabtar da ita ba, dan daddynta ya ji kunan rai sosai, sai dai kuma ta wani ɓangaren Areef ɗin ya ji daɗi da Lion ɗin ya amince zai aureta, babban abin jin daɗi na gaba kuma, Lion idan ya yi niyar yin abu fa to baya fasawa, saboda kayi niya ka sake fasawa ma shi yana ganin ai kaskanci ne da nuna faɗuwa, ka zubar da girmanka, dan haka wannan hatsaniya data faru a tsakaninsu bai sa ya ce zai fasa ɗauko Naurat da haɗa daddyn da family'nsa ba, laifin wani baya shafan wani, idan ya ɗauko Na'urat ba iya daddy kawai ya yi wa ba harda surukansa wato su Abbi.

Makudan daloli wato dollars ya ɗebo daga ɗakinsa wanda shi kansa bai san adadin yawansu ba, yazo ya zubewa daddyn a kan shi ne sadakin Rimsha, wayarsa ya ɗauko ya kira Sultan limamin masallacinsa na Washington DC, ya sanya wayar a hand-free, Sultan ya zama mishi waliyi, daddy dole ba dan ya so ba ya bada auren Rimsha Sultan ya karɓa aka ɗaura aure take a wajen a Washington DC wato cikin Masallacin su Sultan ɗin. TASHIN HANKALI, YAU AKE YINTA, DADDY KA JAWO BABBAN AIKI, ALLAH YA CECI ƳAR TAHALIKAN NAN KADA YA CE ZAI HUKUNTATA DAN UBANTA YA JI HAUSHI DA ƁACIN RAI.

Wannan shi ne tashin hankali Rimsha tana school suna rubuta Exams, sam bata san me yake faruwa ba, ita ma Jehan tana can tana zuba barci, bata san ƴar uwarta ta zama matar aure ba, ba wanda ya sani daga daddyn, Areef, sai Lion ɗin, murna a wajen Areef kam ba'a magana, yau ransa fes, bai wani damu ba, dan yasan Lion ɗin ya fara sonta, dan haka yana sa ran wannan tafiya da zasu yi su kara samu kusancin da zai kamu da tsantsar kaunarta ta yadda ba zai iya rabuwa da ita ba dole ya dawo ya bawa daddynta hakuri in dai yana sonta, tashin hankali Lion da bada hakuri! Anya kuwa Areef baka manta waye shi ba? Mutumin da ya tsani ma a ce mishi sorry shi ne zai ce sorry? To dai zamu gani, amma da kamar wuya gaskiya.

Aseef yana can yana zuba barci Akila tana kwance a gefensa tana tunanin rayuwa, sam basu san ne yake faruwa ba, basu san an ɗaura aure a palon sama ba, daddy ya bada auren Rimsha a dole ba dan yana so ba, an nuna mishi fin karfi da isa. E lallai, Lion ya nuna fin karfi da isa da izza ya aurawa Aseef AKil, yanzu kuma da karfi ya nuna isa ya auri Rimsha. GASKIYA INA JIYEWA LION WLH HMM.

Lallai akwai gagarumin matsala, anya William jacop zai yi accepting na Rimsha da Akila kuwa a matsayin surukai? Kun dai sai tun farko ya nuna ya tsani Rimsha over, tab lallai daga Rimshar har Akilar suna tsaka mai wuya kuwa, dan William jacop ba taya baya bane! *DANGEROUS BOSS* ɗin ne da gaske idan baya son abu, akwai dai matsala, akwai yaki, ache acikin TRIPLETS nasa sanyin idanuwansa biyu daga ciki sunyi aure kuma ba Turawa suka aura ba bakaƙen fata? Tab akwai gagarumin matsala ba kaɗan ba wlh.

LION

Bedroom nasa ya koma bayan an ɗaura auren ya yi kwanciyarsa abinsa hankakinsa kwance yana tunanin ta hanyar da ya kamata ya shiga cikin kasar Russia, zai iya zuwa da private jet nasa, amma ra'ayinsa ne ya zaɓi tafiya da jirgin ruwan saboda wasu dalilai nasa na kansa, gaskiya bai so tafiya da Rimsha ba, da Jehan ya so dan bata da tsoro, daddy ya canza komai da wasu banzayen kalamansa. Yau saura kwana uku ya yi tafiyar ga daddy yana hanyar zuwa, Rimsha saura kwana uku suma su kammala Exams, zai zama ranar da zasu kammala a ranar zasu tafi, amma anya daddy zai aminta da tafiyar nan kuwa? Akwai fa kura? Dan kuwa wannan tafiya babbar haɗari ce ga Lion, sai dai shi dama duk abin da aka ce ba'a so, shi kuma shi yake so, zaman ka lafiya ma kada ka ce mishi baka son abu, kana ce mashi to fa sai anyi wannan abin sai dai ka mutu, gaskiya akwai gagarumin matsala tsakaninsa da daddynsa, dan ba zai taɓa yarda ya shiga wannan kasada ba........

❤️❤️TRIPLETS❤️❤️

*Duk wace ta karanta mini littafina ba tare da ta biyani hakkina ba Allah ya isa ban yafe ba, sai Allah ya tsayar da mu ranar da bata da abin da zata biyani face ladarta*

E61-62💋

A ɓangaren Rimsha kuwa, wato school, sun rubuta Exams na farko lafiya, sai murna suke yi sun kusa kammalawa, sai dai fa yau tun da ta je school bata cikin mood mai kyau, har sai da Anaya ta gane ta tambayeta dalili, kaƙalo murmushi dole ta yi. "Anaya babu wani abin da yake damuna, kawai kai'na ne yake yi mini ciwo sosai". Ta faɗa tana ƙoƙarin miƙewa dan ta je cikin mota ta ɗauko ruwa, da sauri Anayar ta miƙe ta bi bayanta tana yi mata sannu Allah ya sawwaka.

Suna tafe suna hira saura musu paper ɗaya su koma gida, sai murna Anaya take yi zata ga Mark. Kamar dai kullum yana aikin latsan waya, sannu ta yi mishi, ɗago idanu ya yi ya sauƙesu a kanta, har wani irin yarr ya ji a jikinsa, sai murmushin take yi abinta, ita kuma Rimsha ta buɗe gidan baya ta zauna tana shan ruwan da ta ɗauko a gaban motar, zama ta yi ta kyau dan babu kyau shan ruwa a tsaye, Annabi ya hana, ka samu waje ka zauna kasha, dan ruwa cikin ƙanƙanin lokaci yana iya kashe bawa idan kayi mishi shan garaje.

Ɗan kawar da kansa ya yi ba tare da ya amsa sannun ba, har cikin zuciyarsa yake jin yarinyar tana mugun burgesa, bare ma idan tana murmushi, da dimple nata irin na Azharuddeen Bature wato daddynta, idan baku manta ba, da daddynta da daddyn Rimsha duk suna da dimple, Rimsha ta gado, ita ma Anaya ta gado, ba ƙaramin kyau kuma ya yi musu ba, sai ma idan suna magana ko suna murmushi, dayawa daga cikin student suna tsananin ganin kamanninsu, sai dai da yake su basu kula kowa, ba wata student da ta taɓa tinkararsu ta ce suna kama.

Suna tsaye a wajen sai ga Fadila ta kariso wajen rai a matukar ɓace cikin fushi, da yake Rimsha tana cikin mota sai Fadilar bata ganta ba ta ga iya Anaya kawai.

Damko wuyar rigar Anayar ta yi tana faɗin "Ke dan ubanki a baki wani ɗan iskan kika ji cewa ina zuwa office ɗin Mr Emmanuel na zauna muyi romancing juna da har da zaki gayawa su Zee? Dan sun ce a bakinki suka ji". Da yake ita ma Anayar ƴar yi ce, ba tayar baya bace sai ta ce

"Da kika rena tsoho shi ne kika zo nan kina kwashe mishi albarka ko? To ki sani tsoho kika zaga ba ni ba, kuma da kike magana a kan office ɗin Mr Emmanuel karya akayi baki je ɗin bane? Bani na gayawa su Zee ba, amma tun da kin ce ni ne, to ni ɗin ne ki yi abin da zaki yi, angaya miki..." Bata kai karshen maganar ba ta dakata sakamakon ɗaga hannu da Fadilar ta yi zata zabga mata mari.

Runtse idanuwanta ta yi tana jiran saukar marin, ta tsuke fuska sosai alamar ta tsorata, jin shiru marin bai sauko bane yasa ta yi yunkurin buɗe idanunta dan taga me ya dakatar da Fadilar, bata kai ga buɗe idanun ba, sai ji ta yi Fadilar ta sakar mata wuyar rigar tata da ta rike, da sauri ta waro idanun dai'dai lokacin ta ji kara mai sauti na saukar mari.

Tana buɗe idanu sai kan face ɗin Mark da Rimsha dake tsaye a gefensa tana zaro waƴan nan dara daran sleeping eyes ɗin nata, ga kuma Fadilar a baje a kasa kamar kayan wanki bata numfashi, da alama ta suma ne, da sauri ta dawo da kallonta kan face ɗinsa, daidai lokacin shi ma ya ɗago Hazel eyes nasa ta cikin glass yana kallonta, bata san yana kallonta ba, dan yana cikin bakar glass, dan haka sai ta tsare shi da ido, shi ma ya tsareta da idanu yana kallon razananniyar face nata, yadda ta tsorata dan ta sadaukar marinta Fadila za ta yi.

Readers Also Read