Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 78
Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 78: Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 78. "Anaya mu tafi ko?" Rimsha ta katse musu…
3,323 words
"Anaya mu tafi ko?" Rimsha ta katse musu kallon juna da suke yi, ta kuma yi maganar a tsorace na ganin Mark ya mari Fadila har ta suma. Hannu ya miƙawa Anayar alamar ta zo, sake baki Rimsha ta yi tana ganin ikon god, ko me zai yi mata da zai ce ta zo kuma. Ita ma Anayar ta tsorata bare ma yadda taga face nasa a ɗaure sosai, dama haka yake kullum, amma yau da ya mari Fadila ya kara ɗaure fuskar sosai, sai ta ji tsoron kada ya daketa ko ya yi mata wani abin.
Hakan yasa ta kasa yarda ta miƙa mishi hannunta, gabaɗaya ma sai ta kawar da kallonta daga kansa tana ƴan kame kame, ganin hakan yasa shi ya riko hannun nata tare da janta suka nufi office ɗin shugaban makarantar dan ya sumar da Fadila, ya san cewa case ɗin zai iya shafar su daga ita har Rimshar, idan kuma ya shafesu gida zasu sami labari, dole su Aseef zasu tuhumesa har Lion ya ji, case ɗin zai iya zama babba, shiyasa ya zaɓi ya kashe wutar da kansa kamar yadda ya kunna ba sai ta girma ba.
Waye ya lura da Mark ya ki yarda ya rike hannun Rimsha sai dai Anaya⁉️
Da sauri Rimsha ta rufa musu baya suka bar Fadilar a wajen ga kofofin motar a buɗe, wani irin daɗi sosai yau Anaya take ji, hannunsa laushi sosai kamar baya wani aiki, ga skin ɗin nasa sai sheki yake, jawur da shi kamar ka taɓa jini ya zuba, a nashi ɓangaren ma laushin hannunta ba ƙaramin daɗi ya yi mishi ba.
Abin da ya faru dukka ya sanar da shugaban makarantar tare da gaya mishi ya san yadda zai yi da Fadila, idan ta farfaɗo ya yi mata iya ka da su Rimsha, tun wuri ya taka mata birki kafin gida su sami labari, idan ba haka ba, ya kuskura ya bari gida suka ji ana takurawa Queen nasu, to tabbas wannan makaranta za'a iya rufeta na har abada a dalilin taɓa Rimsha, sannan su Rimshar babu ruwansu a sumar da Fadila da ya yi, hasalima basu san komai ba, dan yasan za'a iya cewa su suka ja komai ya faru, to dan haka su babu ruwansu, okey ya amsa musu da shi, fitowa suka yi Mark ɗin ya tambayesu sun kammala paper ne su wuce gida?.
Rimsha ce ta bashi amsar a'a, shiru ya yi bai sake yi mata magana ba, dan kamar tsoron yin magana da ita yake yi, ya fi mishi alkhari da jin daɗi idan ya yi magana Anaya ta bashi amsa ba Rimsha ba, dan kuwa tabbas ya gano ogansa yana son yarinyar nan, yanayin yadda yake ganinsu suna gudanar da rayuwarsu a cikin gidan, tsab ya fahimci so ne a tsakaninsu kamar yadda a yanzu ya gane cewa shi ma fa ya kamu da son Anaya ba karya, kwata kwata baya son idanuwansa su yi mishi kuskure ganin ko da in da Rimsha take, baya son ta yi mishi magana, haka zalika shi ma baya son ya yi mata, sai idan ya zama dole, ya san wanene Lion, ya san shi da mahaukacin kishi na bala'i, so ba zai so wani abin da zata haɗosa da shi ba, dan bai shirya mutuwa ba gaskiya......WLH MARK DA GASKIYAR KA INA DALILI IRIN WANNAN KISHI AI HMMM.
Class nasu suka wuce shi kuma ya koma wajen motar, zubawa Anaya idanu ya yi yana kallon yadda take tafiya tana juyowa ta saci kallonsa, duk in ta yi tafiya ɗaya biyu sai ta juyo ta kalle shi, yana kallonta bata san yana kallonta ba saboda glass ɗin face nasa, wani irin sonta ne yake kara shigansa, da yake shi ya san so, ya ma taɓa yin soyayya da wata Baturiya ƴar kasar London da suka haɗu a school tun kafin ya kai wannan mukami da yake kai, lokacin suna school ne ma, ya so yarinyar sosai, amma mutuwa ta rabasu, ya sha kukan mutuwarta kamar ba gobe, accident ta yi da motarta da babban mota a hanyarta ta zuwa school, tun daga kanta kuma bai sake ɗaga idanu ya kalli wata mace ba har ya fara aikin soja, daga nan ya mayar da hankalinsa a kan aikinsa ya watsar da komai, kokarinsa yasa Lion ya dawo da shi kusa da shi, sai dai fa iyayen Mark ƴan ƙasar Russia ne ba ƴan Usa bane, zama ya zaunar da su tun lokacin kasashen biyu suna shiri, har dai suka zama ƴan kasa, to shi dai Mark ɗan Usa ne dan a nan aka haifesa ya girma, a takaice ma bai taɓa zuwa Russia ba, sai dai iyayensa su bashi labarin ƴan uwansu, amma bai taɓa zuwa ba har iyayensa suka mutu, dan haka shi bai san kowa na daga family'n iyayen nasa da ido ba, amma yana da hotonansu da dama a wajensa, ba karya Mark mutumin kirki ne sosai, baya shiga harkan kowa, baya da surutu shiru shiru, ga rikon amana kamar me, yanayin rayuwarsa zaka rantse da Allah cikakken musulmi ne ba krista ba, amma krista ne, wannan shi ne tarihinsa.
Yana zaune a wajen har wasu student suka zo suka ɗauki Fadila daga wajen aka wuce da ita zuwa hospital na cikin makarantar.
Bayan sun kammala Exam ɗin ne Anaya ta rako Rimsha zuwa wajen mota dan ta sake kallon Mark, bye bye ta yi musu kafin ta ce da Mark ta gode, jinjina mata kai ya yi tare da cire glass ɗin face nasa ya ɗago idanunsa ya saukesu a kanta, abin da ya sanya ya cire glass ɗin dan ta san yana kallonta, yana da bukatar haɗa idanu da ita.
"What is your name?" Ya tambaya yana ɗaura glass ɗin nasa a saman wayarsa, "My name is Anaya". "Anaya wow nice name, my name is Michael amma ana kirana da Mark, Long story ne sunan Mark tun daga school ya samo asali, nice to meet you beb". Ya kai karshen maganar tare da miƙa mata hannunsa dan su gaisa, miƙa mishi hannu ta yi tana murmushi, shi ma ɗan motsa ɗan ƙaramin bakin nan nasa ya yi ya ɗan yi yake na gefen fuska, alamar ya ji daɗin kenan fa, hakan shi ne ya ji tsantsar farinciki kenan tab.
Ita dai Rimsha ko a jikinta, dan kuwa dama Anaya tana takura mata da wlh tana son shi, so yanzu ai ga shi nan sun gaisa kila zata barta ta huta, tunanin Lion ɗin ta ma ta shiga yi, nan take abin da ya faru daren jiya ya dawo mata cikin ƙwaƙwalwarta, shiru ta yi, shi ne ma abin da ya sanyata yau tun da ta zo school bata wani jin daɗin jikinta, abin ya tsaya mata a ranta sosai.
Gaisawa suka yi kafin ya yi mata sallama tare da mayar da glass nasa ya kunna motar, har zasu bar wajen kome ya tunane ya sake ɗauko wayarsa ya miƙa mata a kan ta sanya mishi numberta, ba musu ta karɓa ta sanya mishi, karɓa ya yi tare da yi mata bye bye ya ja motar suka bar school ɗin, sai daɗi take yi, baki yaki rufuwa, haka ta yi ta ɗaga musu hannu har suka bar school ɗin, sannan ta koma wajen da take tsayuwa ta jira daddynta ta tsaya a wajen.
Dai'dai lokacin da Mark ya yi parking na motarsa a cikin gida, shi kuma Lion ya danno hancin nasa motar sun dawo daga airport ɗauko su daddy, mota biyu suka yi, Lion shi da daddy suna zaune a gidan baya Tyrone ne ya tuka su, Jay, John da kuma uncle Herry suna ɗayar motar wani soja ne yake tukasu, sam su daddy basu lura da ita ba dan Mark yana kashe mota ta fito ta shiga cikin gida da sauri dan tana jin fitsari, shi kuma Lion ya kalleta dan tun da suka shigo gidan ya zubawa motar da Mark ɗin ya ja ido, tunani yake yi a kan ya kamata su sayi sabbin motoci, wannan da Mark yake kaita school ma ya tsufa.
Aseef bai je airport ɗin ba sakamon bashi da lafiya, basu ma gaya mishi daddy na hanya ba, sun kyale shi kawai, shi kuma Areef Lion ya aike shi Abuja gidansu daddyn Rimsha a kan ya kwaso mishi wasu daga cikin takardu na Naurat, dan ya gansu a ɗakin daddy, takardun makarantarta har da katin ƴar kasa na Nigeria da kuma na Russia, duk ya gansu, shi ne ya aika shi ya kwaso mishi su dan zai yi amfani da su, da Donal suka tafi, so bai san su daddy sun iso ba.
Cikin gida suka nufa daddy burinsa kawai yaga shalelensa wato Michael a idonsa mu kuma Aseef a idanunmu.
Suna shiga palon kasa ya fara tambayar Lion ina Michael nasa? Dama Lion ɗin ya gaya mishi Michael ɗin bashi da lafiya ne yasa bai zo Airport ba, shiyasa ma ya matsa ya ganshi ya ga a wani hali yake ciki.
Nuna mishi bedroom ɗin Aseef ɗin ya yi tare da wucewa ya haura sama abinsa, dan shi baya son ciwon kai wato hayaniya, yasan kuma idan daddy da Aseef suka haɗu, ciwon kai zasu saka mishi da surutu kamar ba gobe.
Bedroom ɗin Aseef ɗin daddyn ya nufa da fara'arsa da kuma zafansa na son yaga ɗan nasa farincikinsa, rufa mishi baya su Jay suka yi dan suma su kalli Michael ɗin.
Babu ko excuse ya faɗa cikin bedroom ɗin, Akila na gyaran gado shi kuma Aseef yana cikin toilet yana wanka, yanzu suka tashi daga barci rana da ya ɗebesu, shi ne ta hau gyaran musu ɗaki shi kuma ya wuce toilet.
Ganinta yasa daddy ya ɗaure fuska over, duk da take fara tas kuma fari irin na turawar, amma da yake akwai mix na jinin bakar fata, wato Ammie a jikinta, sai ta zamana baka a gabansu, hakan yasa daddy ya tsaneta sosai, barema da ya kalli ba Rimsha ba ce sai ya kara jin haushi over, kenan hakan yana nufin bayan Rimsha da take tare da Lion wanda ya zo da niyar raba su akwai wata? Kenan dukka ƴaƴansa suna tare da bakaƙen fata? To kuwa ba zai yiwu ba, shi dai dole ƴaƴansa da Turawa kawai zasu yi hulɗa.
Tsawa ya daka mata a kan wacece ita?! Sautin zubar ruwan da yake zuba a toilet ɗin ne yasa Aseef bai ji me yake faruwa ba, ganin face ɗin daddy ba ƙaramin razana ta ya yi ba, domin kuwa shi ma dai Tiger face gare shi wajen ɗaure fuska, akwai shi da zuciya da iya tsare gida ba kaɗan ba, bare ma idan aka ci karo da abin da baya so, ai ba'a magana.
Cikin girmamawa da rawar murya ta yi musu sannu da zuwa, domin kuwa, ko ba'a gaya mata waye su ba, ta san dole mahaifin TRIPLETS ne, dan jini ba karya ba, akwai kamanni na wuce misali a tsakanin fuskar daddyn da yaran nasa, ga idanunsa irin na Lion sak, ai ga maihankali ma da gani babu tambaya zai san ubansu ne.
Tsawa ya sake daka mata a kan wacece ita? Me kuma ya kawota gidan ɗansa har cikin bedroom ɗin ɗaya daga cikin ƴaƴan nasa? A iya saninsa ko sojojin Lion basu shiga musu ɗaki dan rashin yarda da mutane da suke yi, sun tsani mata, mace bata taɓa raɓarsu ba, yau rana tsaka mace a ɗakin Michael tana gyara mishi gado, ai dole ya ji ko ƴar uban wanene?!.
Murya na rawa ta amsa mishi da ita matar Heartbeat ne, dan a gaskiya ba karya Akila bata rike sunan Aseef ba, sau ɗaya ya taɓa gaya mata sunansa, kuma ta manta, Heartbeat take kiransa tun farko, kuma sunan ne ya zauna a bakinta, dan haka sai ta ce ita matar Heartbeat ne.
Da yake shi ma daddyn haka yake kiran Michael ɗin nasa, wato Heartbeat, sai ya gane wato ita matar Michael ne, tab lallai akwai rikici. Cikin fushi ya ɗauketa da wani wawan mari wanda ya sanyata juyi ta faɗa saman gadon, wani irin azababben ihu ta saki dan ta maru ba karya, nan take yatsun daddy biyar reras suka fito ɓaro ɓaro a saman kumatunta, dan ita ma a Nigeria fara ce tas, a gabansu ne take baka dan su babu mix a jininsu tarr suke.
Jay, Uncle Herry da suke tsaye a bayansa duk sun ji daɗin abin da daddy ya yi dan suma suna kyamar bakaƙen fata, shi kuma John har cikin ransa bai ji daɗi ba, dan kuwa tun da ya ganta a ɗakin Michael yasan cewa Michael yana sonta kenan, to duk abin da Michael yake so shi ma yana so, ba ruwansa da kabilarci or faɗar addini, shi dai yana kaunar Michael dan tare suka taso, komai tare suke yi a baya, dan haka kaunar a jini take.
To masu karatu a yanzu dai dole mu mayarwa da su Michael sunansu na farko, domin su daddy basu san sun musulunta ba, kuma kunga dama basu son su daddyn su sani, bamu san dalilinsu ba, za dai muji komai a gaba, yanzu dai shi daddy Michael yake kira, so dole bakinsa zamu rubuta ba namu ba.
Da sauri John ya karisa wajen da take kwance ta dafe kumatunta tana kuka, cikin sauri ya sanya hannu ya ɗan ɗagota yana faɗin "Haba daddy why zaka mareta haka? You know fa tun da ka ganta a nan Michael yana sonta ne, to kuma bai kamata ka daki abin da Michael yake so ba gaskiya, ni wlh ina sonta tun da Michael yana sonta".
Wani irin mahaukacin tsawa ya dakawa John ɗin wanda ya sanya shi razana har ya saki hannunta da ya riƙe, wannan tsawar ce kuma ta sanya Aseef dake toilet ya ji abin da yake faruwa, tsaida ruwan da yake zuba ya yi yana son jin menene yake faruwa?.
Faɗa daddy ya fara yi a kan lallai Akila ta tashi ta bar gidan nan yanzu! Babbar magana, Me ya kawo hakan? Duk tsana ce? To ina ga kuma ya ji shi ma Lion ya auri bakar fatar? Akila da take fara tas kamar Naurat ma ya kira ta baka ina ga kuma Rimsha da take da kala mai tsada a duniya wato chocolate color? Ita kam kamar gawayi zai kalleta kenan? Ina ga ita tsanar da zai yi mata ma sai yafi na kowa, dan ita ce kawai chocolate a cikinsu dake gidan, Jehan ma fara ce tas irin farar fatar Naurat, e lallai da akwai case ba kaɗan ba, dan kuwa bana jin Aseef dai zai rabu da Akila, bama zai yiwu ba, dan ana rabasu mutuwa zai yi, sai dai Akila ta hakura ta jure azaban daddy, dan yadda ya tsanesun nan zasu wahala da alama!!.
Jin voice na daddynsa ne yasa ya ajiye brush dake hannunsa, dama already ya gama wanka yana shirya brushs dake wajen ne da AKila ta watsasu da safe bata gyara ba, ruwa kuma yana ta zuba bai kashe ba, dama sai ya gama zai kashe ya fita, jin voice ɗin na daddyn ne yasa ya ajiye brush ɗin tare da ɗauko karamar towel ya ɗaura a saman kansa dan goge gashinsa, dama already ya ɗaura babba a kugunsa.
Da kyar ya fito wajen, har lokacin bai gama warwarewa ba, ya dai samu jirin ta sake shi, yana iya shiga toilet da kansa, amma jikinsa babu wani kwarin kirki.
Ganin abin da yake faruwa ne yasa ya kariso wajen da sauri tare da kama hannun Akilar ya mikar da ita yana kallon face nata yadda yatsun daddy ya fito ɓaro ɓaro, hakan kuma ya yi daidai da shigowar Lion da Areef da ya dawo daga Abuja yanzu, jin daddyn na surfa masifa ne yasa suka shigo dan su ga me yake faruwa.
Rungume matarsa Aseef ya yi yana bata hakuri ba tare da ya ce da daddy komai ba, ya san dai wlh babu abin da ta yi wa daddy ya mare ta, dan haka ba sai ya tambayi ba'asi ba. Daga Lion har Areef sun san cewa wlh babu abin da Akila ta yi wa daddy ya shinfiɗa mata yatsunsa biyar ɗin nan a face nata har haka, already dama sun san shi da tsanar bakaƙen fata, to a tunaninsu hakan ce tasa ya wanke mata fuska da mari, Baiwar Allah har wasu taurari ta gani, ta sha marin Dr William Dangerous Boss.
Tsawa ya dakawa Aseef ɗin a kan ya saketa ta zo ta bar gidan nan, da sauri ya ɗago brawn eyes nasa da suka yi ja ya saukesu a kan Lion dake tsaye yana ganin wannan iko irin na daddy, sai ka ce shi zai zauna da ita.
Areef ne ya katsesu da cewa "Daddy what is happening here? Why are you shouting like that? Kabi komai a hankali mana". A kule ya jiyo ga Areef ɗin yana tambayarsa au tsawa ma kenan yake shi, ihu yake yi ma kenan? E lallai sun raina shi.
"James ina son wannan yarinyar ta bar gidan nan yanzu nan, I don't want to see her close to my son". "Sorry daddy, I can't live without her, gaskiya ni a bar mini matata". Cewar Aseef, ya yi maganar da kyar saboda tsananin ciwo da kansa yake yi mishi.
Ganin yadda yake faman ciza laɓɓansa ne yasa Lion ya fahimci har yanzu fa akwai ciwo a tarrare da shi sosai, so bai kamata su ɗaga mishi hankali ba, dan haka sai ya dubi daddyn nasa ya ce "Daddy babu abin da zai raba Michael da matarsa, yana sonta, ita ma tana son shi, so banga abin da zai rabasu ba, ko da Michael ya ce baya sonta yau, to wlh dole ya zauna da ita dan kuwa tana son shi, a kansa ta kusa mutuwa, bai isa ma ya ce ba zai zauna da ita ba, ko ya dai'na sonta, so daddy kowa ya wuce bedroom nasa bana son wata hayaniya!!".
Tsawa ya daka musu tare da buga saman bedside drawer yana faɗin ba zai yiwu ba, dole yau wannan munafukar yarinyar ta bar gidan nan.
Banza da shi Lion ya yi bai sake yin magana ba tamkar babu shi a wajen, ba zai wani ɓata bakinsa ba wajen yin wani magana, saboda bai ga uban da ya isa ya raba Aseef da matarsa ba, ba daddy ba yau ko Jacop Roshan ne zai fito daga cikin kabari to sai ya barwa Aseef matarsa. Tashin sense, Jacop Roshan da kansa kuma yau? E lallai Lion ya yi nisa.
Nisawa Areef ya yi kafin ya ce "Dad please and please ka dai'na faɗin haka, seriously Michael yana son matarsa, and then....." Wani irin razanannen tsawa daddyn ya daka mishi wanda ya sanya shi dakatawa da maganar, sam Areef baya son ganin ran daddyn ya ɓaci, amma kuma yana kure shi, sai danne zuciyarsa yake yi dan kada ya zama ya yi mishi irin abin da Lion yake yi mishi, idan aka ce sun haɗu sun zama iri ɗaya waye zai taushi daddyn kenan? Amma kuma daddyn yana neman kure hakurinsa gaskiya, taya zai yi ya ce shi baya son matar Aseef sai dai su rabu? To shi zai zauna masa da matar ne? Wlh tsohon nan ɗan neman bala'i ne, to sun ce basu son turawa ƴan uwan nasu bakaken fata suke so ana dole ne? Dama ya samu Aseef ɗin ya yi auren ne zai wani takura musu, idan da irin Jay Aseef ɗin ya yi musu ya kawo musu ɗan shege ba shikenan ba?!.
Shi kuwa Aseef ya rungume Akila dake ta faman kuka ta sha mari yau, sai rarrashinta yake yi.
"Michael ɗauketa ku je zuwa bedroom na dan na ga kamar zaka faɗi, idan kun je ka rufe kofar with key". Cewar Lion, dan ya luran Aseef ɗin kamar zai zube kasa saboda rashin kwarin jiki, ga kuma hayaniyar daddy sannan ga Akila a rungume a jikin nasa tana kuka, abubuwan sun yi mishi yawa bawan Allah.