Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 81
Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 81: Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 81. Ranƙwafo da kansa sosai ya yi daidai saitin…
3,366 words
Ranƙwafo da kansa sosai ya yi daidai saitin face nata, shiru ya ɗan yi kamar mai tunanin wani abin, can kuma sai ya ɗan ɗaga kai tare da sanya hannu ya goge mata hawayen kafin ya ɗauketa cak a saman kafaɗarsa ya fito da ita zuwa cikin ɗakin. A saman bed nasa ya ahinfiɗeta kafin ya koma cikin toilet ɗin dan ya yi wanka.
After 45 mins, ya fito shirye cikin tsadaddun kaya barcinsa farar tas, sai shaki soft skin nasa yake yi sosai, yana ta zuba kamshi. Saman bed ɗin ya nufa kamar zai zuba mata ruwa, kome ya tuna sai kuma ya fasa ya nufi waje dan ya duba ƴan uwansa da kuma daddy.
After some minutes ya dawo, sai da ya bisu ɗaya bayan ɗaya ya duba su sannan ya dawo, har Aseef sai da ya yi musu knocking suka buɗe ya duba lafiyar Aseef ɗin kafin ya dawo bedroom ɗin nasa.
Saman bed ɗin ya haye bayan ya ɗauko ruwa roba ɗaya daga cikin fridge, ya buɗe robar ruwan yana ƙoƙarin tarbowa a hannunsa dan ya zuba mata ta tashi ta koma bedroom nata, bai kai ga yin hakan ba daddynsa ya shigo bedroom ɗin dan yana son ya yi magana da ɗan nasa, ganin daddyn yasa ya tsaya bai zuba mata ruwanba yana bin daddyn da kallo.
"Son me yarinyar nan kuma take yi a saman bed naka?". Shiru ya yi bai tanka mishi ba. "Son ka tasheta ta fita magana nazo in yi da kai, kuma kasan cewa nace bana son yarinyar nan since before nazo nan ko? To dan haka bana sonta! Bana son ganinta a kusa da kai! Dan haka yanzu ba sai anjuma ba ka tasheta ta fita a ɗakin nan, kuma kada ta sake zuwa dan bana sonta kusa da kai". Yanayin yanda daddyn yake magana sai ya ga kamar daddyn yana wani nuna mishi isa da izza ne, shi kuma kun sani ba sai na sake faɗa ba, baka isa ka nuna isa a gabansa ba, kuma shi daddyn shi ya basu wannan tarbiya, dan haka iyaye ku ji tsoron Allah ku bawa ƴaƴanku tarbiya da zata sanya su yi abin alkhari, ku sani duk abin da kuka koya musu wlh sai sun yi muku shi a kwana a tashi, to dan haka ku koya musu alkhari dan kuma kuga alkhari, kada ki yarda ko irin gulmar da yara suke kawowa irin idan sun je gidan mutane duk abin da ya faru suzo suna gaya miki, kada ki yarda, tun wuri ki taka musu birki, da sun fara ki hanasu ki ce waye ya tambayeku? Idan ba haka ba, wlh haka zasu tashi da wannan kananun maganganu da gulma da munafurci, a kwana a tashi kema sai sun yi miki, Allah dai ya dafa mana ya bamu ikon aikata alkhari a duniyarmu dan muga lahira mai kyau.
Jin yanda daddyn ya yi mishi magana cikin nuna isa ne yasa ya fasa zuba mata ruwan ma bakiɗaya, tare da yin kwanciyarsa bayan ya ajiye ruwan a saman bedside drawer, ya jawo bargo zuwa dai'dai cikinsa, ganin bargon ya rufe har kanta ne yasa ya mike ya gyara mata kwanciya a in da ya ɗaura kanta a saman pillow dake manne da jikin headboard na gadon, sannan ya ja musu bargo dan shi bashi ma da lokacin yin wata magana da daddaren nan bare ya biyewa daddy su yi.
Ganin hakan yasa daddy ya ɓata rai sosai ya fara faɗa babu kama hannun yaro, shiru ya yi bai tanka ba tamkar babu shi a ɗakin.
Sai da yaji surutun daddy fa yana neman sanya shi ciwon kai, a fusace ya miƙeq zaune, cikin nuna isa da izza ya fara magana "Daddy do you know what? She is my wife yanzu da nake maka magana matata ce, a da bani da niyar kulata, amma tun da ka ce baka son ganinta a kusa da ni, as from today ta dawo bedroom ɗin nan da zama kenan, ko waje ba zata fita ba idan ta dawo school, kuma zan kula da ita saboda baka sonta, wai ka manta cewa ni abin da ba'a so ne ni kuma nake so? To idan ka manta na tuna maka, tun da baka sonta dole zan kulata, zaka iya tafiya yanzu barci nake ji, ita kuma matata ce babu wanda ya isa ya canza hakan!".
Tashin hankali, a tsananin razane daddyn ya miƙe, cikin fushi shi ma ya fara magana "Romeo ni fa na haifeka ba kai ka haifeni ba, to ina mai baka umarni da ka fitar da yarinyar nan daga cikin bedroom naka, in fact daga gidan nan baki ɗaya, na ce bana sonta ko?". Shiru ya yi bai sake yin magana ba, sai ma kwanciyarsa da ya yi tare da jawota jikinsa tun da daddyn ya ce baya son ta zo kusa da shi, to barima ya rungumeta suyi barci tare sai ya ga karshen tsiya, shin daddyn zai mutu ne ko yaya? Mutun sam baya son zaman lafiya?.
Bakin ciki tamkar daddyn ya haɗiyi zuciya ya mutu, Allah dai yasa yanzu ya sami sauki sosai, da yanzu ciwonsa ya tashi saboda tsananin azabar ɓacin rai, ko kallon in da yake Lion ɗin bai sake yi ba, hannu ma ya ɗaura a saman bayanta yana shafawa a hankali tare da lumshe idanuwansa kamar mai barci.
Daddy bashi da zaɓi dole ya juya ya fita daga ɗakin, domin kuwa babu yanda ya iya da Lion, dole dai ya hakura ne. Daddyn yana fita ya rabata da jikinsa tare da juya mata baya ya yi kwanciyarsa, batun bedroom nasa kuma ta dawo kenan kamar yadda ya faɗa, dan baya magana ya canza, bare ma kuma da ya zamana daddyn yana gidan, ai ko dan ya cika maganar tasa dole ta zauna a bedroom ɗin.
Yana juyawa ba jimawa barci ta yi awon gaba da shi, dama ita kam already tana sume baiwar Allah.
A ɓangaren Aseef kuwa bayan sun yi sallah sun ci abinci ne suka wuce kasa abinsu. Suna shiga bedroom nasu ya rufe kofar da key dan ma kada daddy ya caza mishi kai, Lion ne ya ce mishi ya sanya key a kofar dan kada su tayar mishi da hankali ba lafiya gare shi ba.
Wanka ya yi tare da shiryawa cikin kayan barcinsa launin ash color masu bala'in kyau da tsada, kafewa ya yi a kan lallai sai ya yi wa Akila wanka, ita kuma ta ki yarda, kuka ya saka mata shi gaskiya ba zai yarda ba, ai ita matarsa ce to me zata ɓoye mishi? Ba kayansa bane wai?.
Cikin shagwaɓa ta ce "Kai my shagwaɓatina, kayan kane mana, amma ai yanzu baka da lafiya ne, ni gaskiya ka bari sai ka warke". Kin yarda ya yi ya cigaba da zuba mata kukan shagwaɓa tare da kwanciya a saman gadon ya bata baya ya yi ruf da ciki wai ya yi fushi.
Lallaɓawa ta yi, cikin salon so ta haye saman bayansa tare da kawo bakinta saitin kunnensa tana hura mishi iska a hankali, kara tsananta shagwaɓar tasa ya yi yana faɗin "Kome zaki yi mini ba zan saurareki ba har sai kin barni nayi miki wanka". Kumatunsa ta sumbata tare da ɗan jan gemunsa tana faɗin "Yanzu ka tashi daga shagwaɓati ka koma rigimati Allah, wlh ka cika rigima sosai, ni Allah ba zan yarda ba". Shiru ya yi bai tankata ba.
Hannu ta cusa cikin gashin kansa ta fara shafawa har zuwa fuskarsa wuyarsa dukka, cikin salo mai ɗaukar hankali ta zuro harshenta waje ta fara yi mishi tafiyar tsutsa a wuya, tuni ya manta da fushi ya juya da ita ta koma saman bed ɗin, jawota jikinsa ya yi tare da fara bata sakonni na musamman, kukan shagwaɓa ta sanya mishi tana faɗin ya barta bari ta yi wanka, haɗe bakinsu waje guda ya yi tare da fara bata hot kiss, cikin dabara ya zura hannunsa cikin rigarta ya fara aikin matsa abubuwan da yafi kauna, biye mishi ta yi tana yi mishi kiss ɗin ita ma, nan take ta ruɗa bawan Allah ya fara zuba mata shagwaɓa babu kama hannun yaro.
Da kyar ta samu ta kwaci kanta ta nufi toilet ɗin, tana shiga ta rufo kofar da key dan ma kada ya biyota, kwanciya ya yi yana jiranta ta dawo dan shi kiss ɗin bai ishe shi ba gaskiya.
After some minutes ta fito ɗaure da towel a kirjinta, kiranta ya yi a kan ta zo haka da towel ɗin, make mishi kafaɗa ta yi tare da nufar dressing room nasa, kayan barcinsa riga da wando ta fitar dan tasa, saboda ta manta bata ɗauko kayan daga ɗakin su Rimsha ba.
Tana ƙoƙarin sanya kayan ne kamar daga sama ta ji ya zuro hannunsa daga ta bayanta zuwa ta gaba ya kwance towel ɗin, ko yaushe ya taso ya zo? Ta tambayi kanta, damke towel ɗin ta yi tare da juyowa gare shi, rungumota ya yi yana zuba mata shagwaɓa a kan shi ta daina hana shi taɓa kayansa, idan ba haka ba gaskiya zai yi mata kuka.
"Wace kuka kuma bayan wanda kake yi mini yanzu?" Ta faɗa a shagwaɓe, hannunsa dukka biyu yasa ya riko breast nata bakiɗaya tare da kawo bakinsa saitin kunnenta kasa kasa ya ce "Yanzu ai kukan soyayya nake yi miki, idan kika cigaba da hanani kukan gaske zan yi". Ya kai karshen maganar tare da sumbatar wuyarta. "To dan Allah my shagwaɓatina ka bari na sanya kaya sai mu koma bedroom saman gado, a nan sai kayi duk abin da kake so". "Promise?" Gyaɗa mishi kai ta yi, sakinta ya yi tare da juyawa zuwa cikin bedroom ɗin.
Saurin sauri ta shirya ta fito zuwa gaban mirror, kayan nasa sun yi mata kyau sosai duk da cewa sun fita, sun yi mata yawa, amma ba karya ta yi kyau, Lotion nasa ta shafa a jikinta tare da perfume irin na Lion daya ɗebo musu daga ɗakin Lion ɗin, sai tashin kamshi take yi ta dawo saman bed ɗin.
Kamar jiranta yake yi ya fara murzata son ransa, bata hana shi ba, dan tasa idan ta hana shi ma kuka zai saka mata, to gara kawai ta bar mishi kayansa ya murza son ransa, babu in da bai yi wasa da shi ba a jikinta har gabanta, sai dai bai yi yunkurin shigarta ba, a iya wasa ya tsaya, tana kwance tana jinsa, duk yanda ya juyata haka take juya mishi, sai da ya sami natsuwa sannan ya rabu da ita tare da kwanciya ya jawota jikinsa yana zuba mata albarka har barci ya yi awon gaba da su.
Shi kuwa Areef sai da ya tsokani Jehan sosai kamar yanda suka saba sannan ya nufi bedroom ɗin daddy, bayan ya duba shi suka yi sallama ya wuce nasa bedroom ɗin dan kwanciya. Asuba ta gari.
Washegari kamar kullum, haka suka tashi, sai da Lion ya dawo sallar asuba ne ya shafawa Rimsha ruwa ta farfaɗo, ta sha ruwan mamakin ganinta a bedroom nasa, wanka ya ce ta yi sannan ta yi sallah ta shirya zuwa school, okey ta amsa tare da dirowa kasa daga saman bed ɗin ta nufi waje, calmly ya ce mata a toilet nasa zata yi wanka, dan kuwa kamar yanda ya gayawa daddy ta dawo bedroom nasa nan, to hakan ce, baya saɓa maganarsa.
Mamaki kamar zata cinye ɗan yatsanta, yau me ya shiga kansa ne? Ta tambayi kanta, bata san diramar da suka sha daren jiya shi da daddy bane, ita dai tana mugun mamakin abin ne. Toilet ɗin nasa ta dawo ta shige, shi kuma kwanciya ya yi tare da jawo bargo ya lumshe idanunsa dan ya mayar da barci, ba jimawa barci ta yi awon gaba da shi, ita kuma bayan ta yi wanka ta fito, bedroom nasu ta nufa, da yake ya yi barci, bai san fita ta yi ba, ya ji motsinta, yana tunanin dressing room ta shiga, shiyasa bai buɗe idanu ba, ya cigaba da barcinsa, bata san ya ce ba zata sake fita daga bedroom ɗin ba idan ba school zata je ba. BABBAR MAGANA LALLAI AKWAI CAKWAKIYA ZAMAN CIKIN ƊAKI YA KAMATA KENAN, DADDY YA JA MATA AIKI.
Shiryawa cikin uniform nata ta yi, sun sha guga sosai, ita tun da take a gidan bata taɓa sanin waye mai yi musu wanki ba, kullum idan ta dawo gida zata cire uniform nata, amma kafin nan da awa biyu an wanke uniform ɗin an goge an dawo mata da shi cikin bedroom nata, haka duk kayan da ta cire, tun abin yana bata mamaki har ta dai'na mamakin, komai ya zama mata jiki.
Kitchen ta nufa ta sami Mark, abinci ta ce ya zuba mata bari ta ci su tafi, bai amsa mata ba sai dai ya zuba mata kawai, saman table ɗin palon sama ta koma ta zauna, a nan Areef ya iskota, yana zama daddynta ya fito shi ma, gaishe su ta yi cike da fara'a tana faɗa musu su tayata da addu'a yau zasu rubuta Exams na karshe, okey suka amsa mata tare da yi mata fatan alheri.
Zama suka yi kusa da ita suna tayata hira, a nan ne ta cewa daddy idan ta dawo school zai kaita shopping dan ta sayi kayan partynsu da sauran abubuwa, ita Indian dressing zata yi, dan ana yawan ce mata hakan a school, saboda dark black curly hairnta irin na Naurat, shiyasa suke ce mata ƴar india, to gobe dressing na Indiyawa za ta yi, daddy ya kaita shopping ta sawo sari mai kyau da sauran kayan indiyawa.
Kallon Areef ya yi, while shi ma Areef ɗin shi yake kallah, babu wanda ya isa a gidan nan ya ce zai ɗauketa su je shopping ba tare da izinin Lion ba, kai ai da wuya ma ya yarda koda sun tambaya. Shiru suka yi mata an rasa mai bakin yin magana, cike da damuwa ta ce "Daddy lafiya kuka yi shiru kuna kallon juna?".
Ƙaƙalo murmushi dole suka yi dukkansu biyu Areef yana faɗin "Ba komai yanzu dai idan kin gama cin abinci ki je ki sami Lion ki tambaye shi zamu je shopping anjuma, idan ya barki to, idan bai barki ba kada ki ji tsoro ki saka mishi kuka, ki ce kowa zai yi shiri mai kyau ya je school amma ke baki da kaya, ki yi mishi kuka sosai har da hawaye zai barki". Shiru ta yi tana tunano abin da ya faru daren jiya, abin ya ɗaure mata kai ta yadda akayi yanzu baya son ganin kukanta sam.
Ganin ta yi shiru ne yasa daddyn ya ce "Ba komai tun da Areef ya ce kiyi hakan ki yi kinji ko?" Gyaɗa musu kai ta yi tana ƴar murmushi, amma zuciyarta cike yake fal da tunanin abin da ya faru jiya a tsakaninta da masoyin nata, tunani take yi wannan abin sam ba dai'dai bane, bai kamata yaya Saif ya rinƙa taɓata haka ba, ita ai ba muharramarsa ba ce, sai yanzu karatun mummynta suke dawo mata cikin ƙwaƙwalwarta, da duk ta manta, sai dai kuma abin haushi kome zai yi mata bata isa ta yi mishi wani magana ba, solution a nan kawai shi ne ta rinƙa gudunsa, ya zama suna wasar ƴar ɓuya, kada ta bari suna haɗuwa, idan ta kai mishi abinci ta rinƙa kawar da kanta gefe tana kuma sanya hijabi har kasa, bayan haka da ya gama cin abinci ta kwashe kayan da wuri ta bar ɗakin, idan ba haka ba zata kauce hanyar Allah a nata tunanin.
Tuna hakan yasa duk ta ji babu daɗi, istigifari ta fara yi na yardan da ta yi a baya yana taɓata itama tana kwanciya a jikinsa, nan take idanunta suka cika tap da kwallah, ita da take faɗa kada ayi saɓon Allah wai yau ita ce har ta yarda wani ya taɓata, sam bata ji daɗi ba kuma shaiɗan bai yi mata adalci ba, bakin azzalumin.
Daddy da Areef suna ta zuba hira basu lura da ita ba har ta mike ta bar wajen ta nufi bedroom nata, sai zuba barci ta sami Jehan tana yi, hijabi har kasa ta ɗauko ta sanya a jikinta tare da wucewa zuwa bedroom ɗin nasa dan ta yi mishi magana a kan zuwansu shopping ɗin.
Bakinta ɗauke da sallama ta shigo cikin bedroom ɗin, yana balcony ta hangosa, wucewa ta yi zuwa wajen, yana sanye da three quarter zuwa gwiwa da polo t-shirt, dukkansu fararene tas, tana mamakin irin yanda yake kaunar white color a rayuwarsa.
Yana zaune saman ɗaya daga cikin kyawawan tsadaddun sofas dake wajen, hannunsa rike da robar ruwa, ya yi shiru kamar mai tunani. Gefensa ta zo ta zauna tana faɗin "Good morning yaya Saif". Bai amsa ba kuma bai ɗago ya kalleta ba, ɗan sunkuyar da kanta kasa ta yi cikin girmamawa ta ce "Yaya Saif dama a kan batun partynmu da zamu yi a school ne, to ni bani da kayan da zan saka, shi ne nake son su yaya Areef su kaini shopping na zabi kayan, ton shi ne nake neman izini". Shiru bai tanka mata ba, tamkar babu shi a wajen.
Ganin hakan yasa ta saka mishi kukan shagwaɓa sosai tana faɗin "Allah kai yaya Saif ɗin nan sai mutun ya yi maka magana ka share shi". Yadda ta yi maganar ne yasa dole sai da ya juyo gareta ba tare da ya shirya ba, hawayen da ya gani a saman face nata ne yasa sam ya ji babu daɗi, zuba mata idanu ya yi bai ce komai ba. Ganin hakan yasa ta kara tsananta kukan shagwaɓar tata tare da miƙewa da nufin ta bar wajen.
Hannunta ya riko tare da jawota jikinsa, ɗago haɓarta ya yi can kasan maƙoshinsa ya furta "Yaushe kika zama rigimammiya haka ne?". Ɗan turo baki tayi kamar yanda take yi wa Aseef, tuni ta manta da cewa yanzu ta gama istigifari a palo, kai jama'a shaiɗan la'ananne ne, makiyin mu ne, dan haka kuyi taka tsantsan da shi, kurinƙa yawan neman tsari da shi daga wajen Allah, duk da cewa mijinta ne ba ta sani ba, amma har shaiɗan ya mantar da ita tuban da ta yi a palo, da yanzu ba mijinta bane haka shaiɗan ɗin zai yi ta amfani da damarsa har ya cinwa burisan na ganin ya sanyasu saɓon Allah, Allah ka kare mu daga sharrin la'ananne shaiɗan.
"To ba kai ne sai mutun yana yi maka magana sai kaki kula shi ba". Yadda ta turo baki ta yi maganar cikin shagwaɓa sosai, ba ƙaramin burgesa ta yi ba, hannu ya kai saman face nata ya goge mata guntun hawayen da suka zubo. "Idan kin dawo daga school Areef zai kai ki shopping ɗin, shikenan?" Gyaɗa mishi kai ta yi tana sakin cool murmushi, nan take kyawawan dimples nata masu tafiya da hankalinsa suka lotsa, yatsa ɗaya ya sanya a ciki yana kallon face nata, bata san time da wani sabon murmushi ya sake kubce mata ba, shi dai yana jin daɗi idan tana murmushi, amma bai iya yi ba, bai taɓa kwatantawa ba, bata burge shi ma ya yi, sai dai ita ɗin.
Wayarsa ce ta buga musu time karfe bakwai dai'dai ta cika, rankwafowa da kansa ya yi cikin sanyin murya a nitse ya fara magana "Daga yau bedroom nan shi ne ya zama naki, idan kin dawo daga school a nan zaki zauna ban yarda ki fita ko palo ba, idan abinci ne ma zan sanya Aseef yasa matarsa ta kawo miki, akwai waya a cikin dressing room na idan kin dawo ki ɗauke shi saboda idan kina son wani abin sai ki kira number Aseef or Areef or daddynki, amma ke ban yarda ki fita ko palo ba".
Zaro idanu waje ta yi sosai, bazata fita ko palo ba kuma? Wannan wani irin abu ne? Wai shin ita matarsa ce? Ko dai yaya Saif aljanu sun shiga kansa ne? Anya kuwa lafiya? Haka ta rinƙa jerowa kanta tambayoyi. Ganin ta zaro idanu ta shiga duniyar tunani ne yasa ya hura mata iskar bakinsa a fuska, lumshe idanun nata a hankali ta yi tare da sake buɗesu a kan face nasa, wani irin kunyarsa ma ta ji ganin yanda yake kallonta.