Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 80
Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 80: Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 80. Bakinta ɗauke da sallama ta shigo cikin…
3,321 words
Bakinta ɗauke da sallama ta shigo cikin ɗakin, shiru babu kowa, a in da ta saba zama ta je ta zauna tare da ajiye abincin tana jiran zuwansa, kamar wanda aka mintsina sai ta ce bari ta buɗe kular yau taga me Mark ya girka musu, dan yanzu abincin Lion ɗin take ci, bata zuwa kitchen ɗiban wani, na kular tasa dai idan ya gama ci shi take ci.
A hankali ta buɗe kular tana leƙawa kamar daga sama taga mutun ya faɗo cikin ɗakin babu ko excuse, ba ƙaramin razana ta yi ba, hakan yasa ta saki marfin kular tare da mikewa kamar wata mara gaskiya.
Ɗaure fuska sosai daddyn ya yi yana kare mata kallo kafin ya daka mata tsawar me ya kawota bedroom ɗin ɗansa? Wacece ita kuma me zata yi mishi a cikin abinci data buɗe? Me tazo yi?.
Baya baya ta farayi dan ta gudu ta fita, daddyn ma ya fara binta tare da kara tambayarta me take yi a cikin ɗakin ɗansa, ta tsorata sosai da ganin shi, musamman da ya zare mata dara daran blue eyes nan nasa irin na Lion ɗin, ga shi kuma an samu akasi ta buɗe kular abincin ne ya shigo, shiyasa ya ce sam wani abin zata yi wa ɗansa, dama bakaƙen fata mugaye ne a cewarsa.
Hawaye ta farayi tana ja da baya bata ankaraba sai ji ta yi ta bugi mutun, ta kasa juyawa ta ga wanene dan saboda bala'in tsoron daddyn, sai dai har cikin ranta ta ji cewa Lion ne, dan daga kamshin perfume nasa ta gane, duk da cewa yanzu su Areef duk da perfume ɗin nasa suke amfani, amma ya fi kama jikinsa shi, idan ya doso waje dole sai kamshin ta bule ko'ina lungu da saƙo.
Tsawa daddyn ya daka mata wanda ya sanyata watsawa a guje da nufin ta fita ɗakin, cikin sauri Lion ɗin ya rikota ta kugunta tare da jawota jikinsa dan ya rabata faɗa da daddyn kada abin da ya faru da Akila na marinta da daddyn ya yi ya faru da ita itama, so is better ya takawa abin birki ya kuma gayawa daddyn cewa shi ya sakata duk wani abin da take yi a cikin bedroom ɗin nasa, dan haka babu ruwansa da ita.
Narai narai ta yi da idanu ta kasa juyowa ta kalli Lion ɗin, ɗan rankwafo da kansa ya yi daidai saitin kunnenta kasa kasa ya ce ta je ta zuba mishi abinci dan yana jin yunwa, ya yi maganar tare da sakinta yana kallon daddyn.
"Dad let's go and eat". Ya faɗa tare da nufar saman bed ya ajiye laptop nasa da duk wasu kayayyaki na mummynsa da ya je ya yi bincike a kansu a garden.
"Romeo ni ba zanci abincin nan ba, kuma kai ma ba zakaci ba, dan ban yarda da abincin ba". Shiru ya yi bai tanka ba, bayan ya gama ajiye kayan ne ya wuce zuwa in da ya saba zama ya zauna, a nitse ya ce "Dad why kake son problem ne? This girl she is our sister, since before now muna tare, and then karamar yarinya ce sosai why are you thinking or expecting cewa zata cutar damu? Me wannan innocent face ɗin ta sani? Gaskiya kana son wahalar da kanka dad, you know cewa tun da ka ganta a bedroom na ai nasan ba zata cutar da mu ɗin bane, so please stop all this thing that you are doing, kazo kawai muci abinci".
Jinjina mishi kai daddyn ya yi alamar ya gamsu da maganarsa yana faɗin "Okey tom i agreed, amma ni zanje naci abinci dasu Herry a saman dinning table kamar yadda muka saba ci". Kai kawai ya gyaɗa mishi ba tare da ya yi magana ba, juyawa ya yi ya fice daga cikin ɗakin ya nufi wajen uncle Herry.
Zuba mishi abincin ta yi ta tura mishi, spoon ya ɗauko ya faraci a nitse ba tare da ya kalli in da take ba, sai dai fa yana tsananin son kallon cikin idanunta, ya yi kewarsu sosai yau, ita ma sai satar kallon shi take yi, tana kewar fine face nasa, sam bai ɗago ya ganta ba har ya kammala cin abincin ya mike ya bar waje ya nufi waje gabaɗaya.
Kayan abincin ta kwashe zuwa waje, kitchen ta mayar da su, ko sannu bata ce da Mark ba, dan ta lura yanzu sam baya son ta rinƙa yi mishi magana, hakan yasa ko sannu bata ce mishi ba ta wuce ta fito abinta.
Bedroom nasu ta yi niyar komawa, tamkar wadda aka cewa ta juya ya kalli cikin bedroom nasa, kai tsaye saman bed nasa ta kallah, kayan da ya ajiye ta gani, sanin cewa baya cikin ɗakin ne yasa bata ji tsoro ba ta shige ciki dan ta kalli menene ya ajiye a wajen.
Gefen bed nasa ta zauna, ko'ina na cikin ɗakin fes yana tashin kamshi, kayan mummyn nasa ta fara dubawa, wannan takarda da yake son sanin wace yarece a rubuce a jiki ta ɗauka tare da hoton Josephine ɗin tana kallo, da yake kowa da yadda yake kallon mutun, sai ita kuma ta kalli Josephine ɗin sak Lion ɗin tamkar an tsaga kara, banbancin kawai kalar kwayar idanu ne, amma ta yi mata muguwar kama da shi, hakan yasa ta fahinci cewa lallai wannan mummynsa ne ko kuma sisters, dan kunga a lokacin da Josephine ɗin ta yi hoton tana budurwa, shiyasa Rimshar ta kirata da sistersa, ta yi kyau sosai a hoton ba karya.
Zubawa sarkar wuyarta idanu ta yi tana kallon shi da mamaki, tunani ta fara yi a kan a ina ta taɓa kallon sarkar nan bayan wuyar TRIPLETS, tabbas sai da ta ganshi yanzu a wuyar Josephine ɗin ne ma ta tuna wlh ta taɓa kallon irin sarkar, to amma a ina? Ta mance dan lokaci bata yi wayo haka ba, matso da hoton sosai ta yi kusa da ita, a nan ne ta fahinci da sarkar wuyar Josephine ɗin da ta wuyar Lion yana da banbanci kaɗan, na wuyar Josephine ɗin akwai rubutu a tsakiyar sannan ya fi nasu girma, tun da Lion yake bai taɓa kurewa hoton kallo har yasan da rubutu a jikin sarkar ba, sai ita yau dan tsabar fitina.
Zubawa rubutun idanu ta yi tana son karanta menene a rubuce a wajen, shiru ta yi tana tariyo sarkar Lion dan shi ma ɗin nasan kamar akwai rubutu wlh, sam dukkansu ba wanda ya taɓa lura da rubutun dake jikin sarkar, dan ba karya rubutun kanane sosai, idan ba ka mayar da hankali sosai ba bazaka gani ba, tabbas tana da bukatar sake kallon sarkar Lion dan taga me aka rubuta, ga dai na Josephine rubutun ba da English bane, da yare ne, hakan na nufin kenan Josephine tana da yare? Dan kuwa wannan sarka dai ita da kanta ta sanya aka buka mata, ba kamar sauran sarkoki yake ba, kuma da alama tabbas akwai dalilin da ya sanya ta sa aka buga mata wannan sarka, alamomi da dama sun nuna hakan, na farko rubutun dake jikin sarkar, na biyu da yare aka yi rubutun, na uku meyasa ta cire tambarin heart na sarka ɗaya ta rike a wajenta, sai ta bawa TRIPLETS babu shi? Meyasa zata yi hakan? Hakan na nufin tabbas akwai sakon da take son isar musu ne wanda ta san da bakinta ba zai isa garesu ba, tasan ba zasu taɓa sauraranta ba idan suka girma, hasashe ta yi hakan yasa ta yi musu haka, ga shi kuma hasashenta ya zama gaskiya, sam sunki bata dama su saurareta, bata wani damu ba, dan tasan duk lokacin da Lion ya natsu, ya kuma mallaki hankalin kansa sosai, ya lura da abubuwan da ta bar musu, to dole shi da kansa zai zo in da take dan neman wasu amsoshi wanda ita ce kawai zata bashi wannan amsoshin, a nata hasashen kenan, kuma hakan ce take shirin faruwa, dan kuwa idan baku manta ba, a dube duben da Lion yake yi kwanaki har yaso yasa a kawo mishi ita dan ya yi mata wasu tambayoyi, case ɗin daddyn Rimsha data kunno kai tasa ya watsar da zancen mummyn nasa, yanzu kuma ya gama da case ɗin daddy, abin da ya rage ɗauko Na'urat ce wanda kuma ya san in da take, sai mummy wanda ita ma yasan in da take, so a takaice ya gama da case ɗin daddy Shiyasa yau ya fito da kayan mummyn nasa yana bincika dan gaskiya yana son sanin gaskiyar abin da yake faruwa a tsakaninta da daddy, yana da bukatar amsoshi da dama daga wajenta, ciki kuma har da fassarar abin da ta rubuta a takardan nan dan shi bai san wani yare bane wannan, shiyasa ma taki rubuta mishi da yaren da zai gane dan dolensa ya je neman faffasar yaren a wajenta, tarko ta kafa musu sosai ta yadda in dai sun mallaki hankalin kansu to dole zasu nemeta a koma ina ne su kai kansu gareta.
Ganin ba zata iya karanta abin da yake rubuce a jikin sarkar ba ne yasa ta ajiye hoton tana santin kyau irin na Josephine, dan fa ba karya kyakkyawace ajin farko.
Takardan sakon wasikar da ta rubuta musu ta fara budewa dan ta kalli me a ciki, wow ta furta ganin wani irin good handwriting, abin mamaki kuma handwriting ɗin sak irin nata, yana ɗaya daga cikin dalilan da ya sanya da suka je Abuja Lion ya ɗauki takardanta na makaranta guda ɗaya ba tare da saninta ba, saboda wlh handwriting nata da wannan handwriting da aka rubuta sakon nan babu banbanci, da yake ita tasan yadda daddynta yake rubutu, sai ta kalli ma handwriting ɗin tafi kama ta tasa sosai, dama gadon rubutun daga wajensa ta yi.
Ƙoƙarin fara karanta sakon ta yi sai ta fahimci bada turanci bane, haka ta rinƙa kwaɓawa tana karantawa, ba abin da ta gane ko ɗaya, dan dama yare idan ba naka ba ai ko haɗa kalma ka karanta ba iyawa zaka yi ba. A karshen rubutun ne da ta karanta sai taga an rubuta da turanci wajen da aka sanya i really love you my pleasures, and i will going to miss you more than your expectations.
Shiru ta yi tana tunanin irin wannan rubutu haka kamar yaren aljanu, ta kasa karanta komai, sai wasu kalmomi take haɗawa kamar tana tsinewa kanta ne da yaren, irin wannan abu haka anya ba yaren aljanu bane kuwa?.
Ta yi nisa cikin tunanin da take yi sai jin motsinsa ta yi a palon sama alamar yana shigowa cikin bedroom ɗin, a guje ta miƙe ta nufi toilet ta ɓuya a bayan wasu kyawawan fararen towals dake gere a wajen kusa da show glass na su mayukan wanke kansa.
Kasa kasa ya yi sallama tare da wucewa dressing room nasa, kayan jikinsa ya cire kafin ya ɗauko wani towel mai azababben kyau fari tas ya ɗaura a kugunsa ya fito ya nufi toilet ɗin da ya yi wanka ya yi shirin barci.
Yana shigowa ta runtse idanunta kirjinta na dukan uku uku, yau tashiga uku ta lalace a cewarta. Wajen brush nasa ya nufa, haɗa mayukan goge bakinsa ya yi tare da fara yi cikin natsuwa, bayan ya kammala sai ya nufi wajen tampatsetsen baf ɗin wankansa dan ya haɗa ruwa, ruwan zafi ya fara zubawa zuwa daidai rabin baf ɗin kafin ya cikata da ruwan sanyi, sannan ya ɗebo sabulansa kala kala ya zuba a cikin ruwan, kunsan dama su Turawa yadda suke wanka, mafiya yawan lokuta sun fi zuba zabulan wankansu a cikin baf ɗin sai ruwan ta yi kunfa over suke shiga, sai su goge jikinsu da kyau kafin su fito idan sun kammala su shiga shower dan ɗauraye jiki, suna son tsunduma cikin ruwan kumfar sosai, suna kuma ɗan jimawa a cikin ruwan idan suka shiga, shiyasa basu cika amfani da sabulai irin namu ba, sun fi yin amfani da sabulai na ruwa.
Bayan ya zuba duk wasu soaps nasa da sauran kayan wankansa, tsab ya kammala komai, duk abin da yake yi tana kallon shi, tsabar dukan uku uku da kirjinta yake yi yasa gabaɗaya gaɓoɓin jikinta sun yi sanyi, sun kasa ɗaukarta, dap take da ta zube kasa dan wlh ba zata iya ba, a hakan ma dan ya bata baya ne yake harkokinsa, ba ta gabansa take kallon ba, da ta gaba ne ina ga sai suma.
Yana ƙoƙarin kwance towel ɗin dake kugunsa dan ya shiga ya yi wanka ne, ta ji ina bazata iya jurewa ba, dan haka sai ta fito daga bayan towels ɗin da gudu gaske ta nufi waje, taku biyu ya yi ya damkota ta shafaffen cikin nan nata, dama tun shigowarsa ɗakin yasan ta shigo mishi, duk kuma abin da ta yi ta taɓa mishi ya gani kuma yasan an taɓa, sai dai bai yi tunanin a toilet ɗin ta ɓuya bane, ya yi tunanin dressing room ta shiga da ta ji motsin nasa, lokacin da ya shigo toilet ɗin ya ji kamshin perfume nata, so ya yi tunanin nan ma shigowa kawai ta yi ta mishi taɓe taɓe kamar a cikin ɗakin, bai kawo ɓuya ta yi a ciki ba, sai da ya je zai ɗauki brush ne ya ganta, amma ya yi kamar bai ganta ba ya yi brush nasa zai fara wanka ko a jikinsa.
"What brought you in to my room?. Me ya kawoki cikin bedroom na?" Ya yi maganar a nutse cikin wannan cool sexy voice ɗin nasa. A hankali ta juyo suna fuskantar juna har lokacin hannunsa a saman flat tummynta ya riketa sosai ta wajen, gabaɗaya ilahirin jikinta kerma yake yi, harta laɓɓanta ɓari suke yi dan bala'in tsoro.
Ya ilahi ya lillahi, wani irin mahaukacin razana ta yi na ganin surar jikinsa a zahiri ba riga, musamman faffaɗar kirjinsa, ga wannan baƙin gashi dake kwance a iya tsakiyar ɓul ɓul ɗin breast nasa, gashi bashi da yawa, ɗan daidai tsakiyar breast ɗin nasa ne, ga breast ɗin ba sai na sake gaya muku ba, suna nan ɓul ɓul saboda training da yake yi, damatsansa kamar zasu fashe, a cike suke tab, ga wasu siraran jijiyoyi ɓaro ɓaro a saman damatsan nasa alamar cikar jarumin namiji kenan.
Datse idanunwanta gam ta yi kirjinta na dukan tara tara, jikinta na kara tsananta kerma da yake yi, iya razana ta yi ba karya, soft skin nasa ma kawai abin kallo ne yadda yake wani sheki tamkar fatar jariri, kamar bai taɓa fita waje ba, ga jikin nasa da tsantsar daddaɗar kamshin perfume nasa da already ya rigada ya kama fatarsa gam, ko bai saka ba yana zuba kamshin.
Duka dukanta bata wuce dai'dai tsakiyar ɓul ɓul ɗin breast nasa a tsawo ba, kanta ya tsaya a dai'dai breast ɗin nasa, dan ba karya Lion yana da tsawo sosai irin daddynsa, biyunsa kuma Areef, Aseef ma yafi Imran tsawo sai dai bai kaisu ba, so tanannan ƴar dai'dai a gabansa, musamman idan ya mannata da faffaɗar kirjinsa da ya ji training ya koshi, sai ta lafe luf a gefe guda.
"Open your eyes". Ya faɗa murya can kasan maƙoshinsa, ya yi maganar kuma yana cire hijabin jikin nata dan sai haɗa uban zufa take yi, ta tsorata over ƴar kaniya, yana cirewa nan take zanen sunansa dake saman tudun breast nata ya bayyana, da yake ta yadda ya damko cikin nata yasa wuyar rigar kayan barcin jikin nata ya yi kasa, tudun breast ɗin nata sun bayyana sosai, zubawa sunan idanu ya yi yana kallon yadda zanen ya zauna ɗas tamkar da shi aka haifeta.
A tsananin shagwaɓe ta ce "Yaya Saif na tuba wlh, ba zan iya buɗe idanuna ba, ba zan iya kallonka a haka ba, na yarda idan ka fito wanka ka shirya, to koma wani irin hukunci ne a lokacin ka yi mini zan karɓa, amma yanzu Allah ba zan iya buɗe idanuna ba, kuma na maka alkawarin ba zan sake taɓa maka komai naka ba, ba ma zan sake shigowa ɗakinka ba idan ba abinci zan kawo ba, wlh tsautsayi ne yasa yanzu ma na taɓa abubuwan da na taɓa, wayyo daddyna nashiga uku yau kam, yaya Areef kazo ka ceceni". Ta kai karshen maganar hawaye na zuba daga idanunta, danasanin abin da ta yi ta farayi, me ma ya aiketa ta taɓa mishi abubuwa? Ga shi har da kayan mummynsa tsab ta buɗe komai.
Yadda ta zuba shagwaɓa over wajen yi mishi magana tasa ya ji gabaɗaya jikinsa ya mutu, ba zai iya yi mata wani hukunci ba, da ya yi niyar hukunta ta sosai, dan babu wanda ya taɓa taɓa mishi abin da ta taɓa yau, ko su Aseef basu san da shi ba, amma sigar da ta yi mishi magana da shi yasa ya ji ya hakura.......... E LALLAI SOYAYYA NA ƊAWAINIYA DA ZUCIYAR LION BA TARE DA YA SANI BA TA BAKIN AREEF, IDAN BA SOYAYYA BA ME ZAISA TA YI MISHI LAIFI YA CE YA YAFE MATA? MUTUMIN DA A BAYA KO BATA YI MISHI LAIFI BA MA IDAN TA BIYO TA HANYAR DA AKAYI MISHI LAIFI SAI TA KARƁI HUKUNCI, BA SHAKKA LION KA FAƊA TARKON KARAMAR YARINYA.
A hankali shasshekar kukanta ya fara ratsa zuciyarsa, ɗan ɗago idanun nasa ya yi daga saman zanen sunan nasa zuwa kyakkywar fuskarta, ganin yadda hawaye wani na abin wani suke zarya a face ɗin nata ne yasa ya ji sam babu daɗi a cikin zuciyarsa, ga shi ta datse idanu gam tamkar zata fasasu, hakan bai yi mishi daɗi ba, baya son ganin hawayen, bai san lokacin daya ɗago hannunsa ya ɗaura saman lallausan kumatun nata ba, a maimakon ya goge mata hawaye, a'a shi salon rarrashinsa daban ne, yasan ko ya goge hawayen ma wasu ne zasu zubo, so kukan ya kamata ya dakatar ba goge hawaye ba, kara jawota jikinsa ya yi da ɗayar hannunsa dake saman cikinta, ta shiga firgici sam bata ma san da hannunsa a saman cikin nata ba.
A hankali ya sanya latsarsa guda ɗaya a........
❤️❤️TRIPLETS❤️❤️
*Duk wace ta karanta mini littafina ba tare da ta biyani hakkina ba Allah ya isa ban yafe ba, sai Allah ya tsayar da mu ranar da bata da abin da zata biyani face ladarta*
E63-64💋
A hankali ya sanya latsarsa guda ɗaya a saman lips nata dake ta faman kerma kamar mai rawan sanyi, ɗan murza lips ɗin nata ya fara yi tare da zame hannunsa dake saman cikinta ya mayar saman mazaunanta ta baya dan ya ji daɗin rikota da kyau. Saukar hannunsa a saman mazaunan nata ne yasa ta waro idanunta ba shiri, kai tsaye sai cikin dara daran blue eyes nasa idanun nata suka sauka, dan kuwa ya tsareta da idanu yana kallonta, wani irin azababben sonta ne yake kara ratsa shi ba tare da ya shirya ba, wani irin daddaɗar yanayi yake jin kansa a ciki mara misaltuwa.
Har lokacin idanunta suna zubar da kwallah zuwa saman face nata bata dai'na ba, zame hannunsa ya yi daga saman lips ɗin nata a hankali ya gangaro da shi zuwa saman lallausan wuyarta, blinking idanunta sau biyu ta yi dan ta tabbatar wa da kanta ba mafarki take yi ba, tunani ta fara yi wai ko dai akwai wani abin da ya shiga kansa ne? Anya yaya Saif ɗin da ta sani ne kuwa? Anya Malika bata yi mishi wani abin ba kuwa?.
Tana can tana tunani sai jin saukar lallausan hannunsa ta yi a saman tudun tula tulan ya sanya yatsa ɗaya babbar cikin yana shafa sunan nasa dai'dai in da ta rubuta GAR, kasa ɗaukar hakan ta yi, bata san lokacin da numfashinta ya tsaya cak ba saboda razana da shiga yanayin da bata taɓa tsintar kanta a ciki ba. Tana ƙoƙarin zubewa kasa ya rikota da kyau da hannunsa dake saman mazaunanta, dawo da kallonsa saman face nata ya yi yana kallon yadda ta sha kuka, ta sume mishi a jiki sarkin tsoro.