Kenza eBookz

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 85

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 85

Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 85: Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 85. Yana damko vest ɗin da nufin ya cire, bata…

3,368 words

Yana damko vest ɗin da nufin ya cire, bata san lokacin da a sukwane ta sanya hannunta ta rike dan kada ya cire ba, ko a jikinsa ya sake mata ya juya ya fice abinsa, saman bed ya haye bayan ya ɗaura sarin nata a saman sofa, wayarsa ya ɗauko ya yi wa Mark text a kan ya kawo musu abinci, yana gama rubutawa ya kwanta yana tunanin irin nasa kaddarar kenan, wai tunanin wannan halitta a cikin zuciyarsa tab, babban bakin ciki shi ma ɗaya shi ne wai wannan ƴar yarinyar, wannan kam renonta kawai zai yi ne ko ya ya? Ya rasa me ma yake tunani a kanta, shi dai face nata kawai ne yake yi mishi yawo a kwakwalwarsa, idan kuma ya yi ƙoƙarin tilastawa kansa rabuwa da tunaninta to fa ba makawa zai cutar da kansa ne a banza, kuma ba dai'na tunanin zai yi ba............ Eh to lallai Lion har yanzu da sauranka ba kaɗan ba, wato har yanzu baka dai'na ganin mata a halitta ba, to dai ga karamar halitta na neman zautar da kai😌🙃

Da gudu Brady ya shigo ya haye jikinsa, Mark ya bashi abinci ya ci ya ƙoshi abinsa, sai murna yake yi, shafa gashinsa ya fara yi, ita kuma tun da ta shiga toilet ɗin sai ta fahimci ba'a toilet na gida take ba, mamaki ne cike fal ranta, haka ya lallaɓa ta karisa wajen baf ɗin wankar, shiga ciki ta yi tare da fara yin wanka.

After some minutes Mark ya shigo musu da abinci cikin wasu tsadaddun kayan abinci masu tsananin kyan gaske, akwai table na cin abinci ɗan madaidai ci a cikin ɗakin, sai tashin kamshi abincin yake yi tun ma ba'a buɗe shi ba, a saman table ɗin ya ɗaura musu abincin, yana fita ita ma ta fito daga cikin toilet ɗin daure da towel fari kal mai bala'in kyau da tsada, da yake towel nasa ne yana da ɗan girma, sai ya saukan mata har zuwa gwiwa, tsayuwa ta yi tana tunanin wai a ina ma suke ne? Sam bata lura da glass ɗin dake gefe ba, ƴan waige waige ta fara yi can ta hango trolleys guda uku, ɗago kai da zata yi idanunta suka sauka a kan glass ɗin, baki ta saki tana kallon tabkeken ruwan da suke ciki, a hankali ta ɗaga idanu sama tana kallon saman ɗakin nasu, ta rasa gane a ina suke, tunani ta fara yi ta saka kaya ta shirya sai ta fita waje ta duba, da wannan tunani ta nufi kusa da gadon.

Idanunsa a lumshe kamar mai barci, kusa da shi ta zauna cikin natsuwa ta ce "Yaya Saif kayan sakawa". Tana tsoron taɓa mishi trolleys ɗin nasa ne kada ya yi mata faɗa, shiyasa gara ta tambaye shi, dan yanzu ma tasan tabbas ta ɓata mishi rai, taga hakan a face nasa, so tana gudun kara yin wani laifi.

Shiru bai amsa ba kuma bai ɗago kai ba, sai Brady ne sarkin gulma ya ɗago kai yana kallonta, harara ta watsa mishi ta tsani karen nan tun da yake takura mata.

Haushi ya daka mata shi kuma yana ƙoƙarin tashi daga jikin Lion ɗin dan ya yi kanta, rike shi Lion ɗin ya yi ba tare da ya buɗe idanu ba, can kasan maƙoshinsa ya ce "Me kika yi mishi?" Mamaki ne ya kamata, lallai Brady ya cika munafukin, yanzu dan ta harare shi, shi ne dama zai mike ya yi kanta? Wato har Lion ma ya gane anyi mishi wani abin kenan? Wannan kare akwai ɗan iska, ɗan bala'i ne, abu kamar wani mutun, yasan komai.

"Babu abin da nayi mishi fa". Ta faɗa tana kumbura kumatu ita a dole ta ji haushi. Haushi ya kuma dakawa irin kamar karya take yin nan, baki ta saki tana ganin ikon Allah wajen karen nan, shi kuma Lion rungume shi ya yi yana shafa jikinsa alamar lallarashi, harara ta watsa musu dukkansu biyu a cikin zuciyarta tana faɗin "Kasan yanda zaka bi da kare a hankali, kasan yanda zaka rarrashi kare da yake dabba, amma saboda mugunta da zalinci baka san ta yanda zaka yi magana da mutane cikin girmamawa da tausasawa ba, ba abin na sami bulala wlh na zaneka ba, iskancin kawai".

A fili kuma shagwaɓe murya ta yi tamkar zata yi kuka ta fara magana "Yaya Saif wlh garin akwai sanyi sosai, kayan sakawa, Allah sanyi nake ji ba kaɗan ba". Mikewa zaune ya yi tare da Bradyn nasa a jikinsa, waro idanuwansa ya yi a kanta, kasa ta yi da kallonta, shi kuma zubawa dogon wuyarta idanu ya yi yana mata wani irin kallo, murza yatsun hannunta ta shiga yi tana wasu ƴan kame kame kamar mara gaskiya, duk kunya ta isheta, bata yi tunanin zai tashi ba, da yake tasan halinsa sai dai ya yi magana daga kwance idanu a rufe, so bata yi tunanin zai tashi ba, shi kuma ya tashi ne ma dan ya sauka kasa ya ci abinci bayan ya gaya mata ga in da kayanta suke kenan, yunwa shi ma yake ji.

Ganin bai yi magana bane yasa ta ɗan ɗago kallonta dan ta saci kallonsa, karaf suka haɗa idanu, wani irin azababben kunya ta ji, da sauri ta miƙe dan ta bar wajen ta koma cikin toilet ɗin kawai, hannu yasa ya riƙota a kugu, kasa ta yi da kallonta tana jin kirjinta na bugawa da sauri da sauri, kasa jurewa ya yi har sai da ya jawota jikinsa, kusa da Brady ta kwanta a gefen kirjin nasa kenan, haushi Brady ya fara yi alamar ta tashi mishi a jikinsa, ai jikin Lion nasa ne shi kaɗai, cikin faɗa ya tashi yana daka haushi tare da yin kanta da nufi zai cijeta da gaske, ihu ta kurma tare da rike Lion ɗin kam, zubawa Bradyn idanu ya yi yana kallon haukan da yake yi.

Sai da ya ga da gaske zai kai mata cizo ne ya hana shi ta hanyar yi mishi magana, da sauri ya dawo kusa da face nasa yana wani buɗe baki shi ala dole cizo zai yi. Magana Lion ɗin ya yi mishi a cikin kunne ta yadda Rimsha ba zata ji me suka ce ba, wani girgiza ya yi tare da daka tsalle ya diro kasa ya koma saman sofa ya kwanta kamar mai jin barci.

Ita kuma ta kankame shi sosai tana kuka kasa kasa, shiru ya yi yana jin kukan nata, har ga Allah bashi da yawan magana, bai ma iya dogon magana ba, so ba zai wani iya magana da ita da baki ba wajen rarrashi, sai kawai ya ɗagota da kyau ya gyara mata kwanciya a kirjin nasa yana ɗan bubbuga bayanta alamar rarrashi, rike shi ta yi a gefen kafaɗarsa tana sauke ajiyar zuciya, hannu ya kai yana goge mata hawaye.

Ganin taki dai'na kukan ne yasa ya ce "Ya isa haka to sarkin rigima". Ya yi maganar kasa kasa, ɗago idanunta ta yi tare da kan nata gabaɗaya daga saman kirjin nasa, ƴan waige waige ta fara yi tana neman Bradyn, zuba mata idanu kawai ya yi tamkar kurma haka ya yi yana kallonta.

Ganin Bradyn baya saman bed ɗin ne yasa ta sauke nauyayyar ajiyar zuciya tare da ɗan ɗagowa dan ta saci kallonsa, 4 eyes suka yi da blue eyes nasa, tana ƙoƙarin kawar da kallonta daga kansa ya sanya hannu ya tallaɓo haɓarta yana mai karewa face nata kallo, runtse idanu ta yi gam. "Meesha". Ya furta kasa kasa, na'am ta amsa mishi amma taki buɗe idanu, shi kuma sleeping eyes ɗin yake son kallah ta kama ta rufe mishi kayansa.

Shiru ya yi yana tunanin me zai yi mata ta buɗe idanun nan ya yi ta kallonsu, ranƙwafowa kanta ya yi tare da haɗe gashinsa da nata, wani irin tsorata ta yi, nan take jikinta ya fara kerma, tunani take yi wai me kuma zai yi mata?. Zazzakar muryarsa ne ya katse mata tunani da cewa "Open your eyes".

Turo ɗan bakin nan ta yi har sai da ya taɓa nasa lips ɗin da yake fuskokinsu a haɗe, a tsananin shagwaɓe ta ce "Allah yaya Saif ni ba zan iya ganin cikin idanunka ba, sai dai ka rufe ido ni kuma na buɗe". Jikinta na kerma take maganar, kamar yanda jikinta yake kerma kuma haka laɓɓanta suke kerma, ba ƙaramin tsuma shi suka yi ba yanda suke kerman nan, ga shi yanayin yanda take motsasu tana magana, ya ilahi ya lillahi har wani irin shock yake ji a jikinsa, uwa uba ga shagwaɓar da take zuba mishi wajen yin magana, ta gama kwance mishi lissafin ƙwaƙwalwa.

Sam bai san time da ya ɗaura lallausan lips nasa a saman..........

*Assalamu alaikum warahmatullahi taala wa barkatuhu, ɗin bin gaisuwa da fatan alkhari a gareku masoyana, fatan kuna lafiya? A duk in da kuke alkharin Allah ya kai muku, masu yi mini ya jiki ina tsananin godiya, ina ganin addua'o'i ƴan amana ƴan comments section, ina tsananin godiya Allah ya bar zumunci, ku ɗin na daban ne a cikin zuciyata, sanarwa ce zan yi muku, ba zaku rinƙa samun update long page kamar da ba, da farko ma hutu zan ɗauka saboda tsananin ciwon yatsa da nake fama da shi, ko baki taɓa yin ciwon yatsa ba nasan an taɓa yi a kusa dake, kin san azabansa ko kin ji labari, wlh wayarma da kyar nake riƙewa, so dan Allah ku yi mini uzuri, a min afuwa, hutu naso ɗauka amma sai nace bari dai na daure ko ba yawa ina yi muku, da babu ai gara babu daɗi, dana barku shiru shiru kamar kurame, na barku cikin tunani gara nayi muku koma yaya ne, ina barar addua'o'i ku, Allah ya bani lafiya cikin ƙanƙanin lokaci, Allah ya bar zumunci 🥰*

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥

KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔 ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne.

KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA, INFECTION KILLER, COLACCA, SAI KAYAN GYARA PAGE. KACA KACA. YALLAGWADA. JIGIDA. RUWA RUWA. BANI BANI. WOMEN JELL BATA BATA. DAFIN KAXA. TANTABARA. XABUWA. CICCIƁI. AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER 09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH, BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

👊FATEEMA ZAHRA MUSA (PRINCESS TEEMA OR STAR LADY)✊

*Domin samun karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 09162620621* 67-68

Sauka kasa Bradyn ya yi ya nufi wajen Mark abinsa, ita kuma har lokacin kuka take yi ta kankame mijin nata gam kamar nace zan kwace mata shi, hannu ya ɗaura saman bayanta yana ɗan bubbugata alamar rarrashi. Meesha, ya amsaci sunanta a hankali, cikin kuka ta amsa mishi da na'am.

"Why baki son ku zama friend da Brady?" Hannunta ɗaya ta ɗaura a saman kirjin nasa tana faɗin "Wlh mugu ne, baka ga ranar abin da ya yi wa su yaya Areef ba ne? Ni nasan ko mun zama friend watarana sai ya cijeni tun da ya jiwa yaya Areef da suka saba ma ciwo". "To amma ai baya yiwa mutun komai har sai idan ni na ce ya yi, ko Areef ɗin da ya jiwa ciwo ma ai ni nasaka shi ko?". Yana magana yana shafa bayanta da hannu ɗaya, ɗayan hannun nasa kuma ya kai saman face nata yana goge mata hawayen nata.

"Uhm ni gaskiya yaya Saif bana son shi koma dai yaya". Cigaba da share mata hawayen ya yi yana faɗin "It's okey, tashi to tun da Bradyn ya tafi". Make mishi kafaɗa ta yi ba tare da ta yi magana ba "Bazaki tashi ba?". Jinjina mishi kai ta yi alamar e bazata tashi ba. "Why ba zaki tashi ba?". Tamkar zata ce saboda jikin mijinta ne, sai kuma ta fasa ta ce "Ba zan iya tashin bane, jikina duk a mace yake". Zuba mata idanu ya yi yana kallon yanda take faman turo baki tana magana.

Yatsa ya ɗaura a saman lips ɗin nata yana ɗan murza su, kara turo bakin nata sosai ta yi tana wasa da hannunta a saman kirjinsa, tana yi mishi tamkar tana zana zane a wajen, ɗan gyara mata kwanciya ya yi a jikin nasa ta yanda zai sami damar buɗe tula tulanta, hannu ya kai ya ɗan yi kasa da wuyar rigar zuwa saman tudunsu, a hankali ya shafa zanen sunan nasa, can kasan maƙoshinsa ya furta "Waye ya zana miki wannan zane?".

Ɗan ɗago idanu ta yi dan ta saci kallonsa saboda yanda ta ji ya ya kuke maganar alamar baya cikin mood mai kyau. Tana ɗagowa karaf suka haɗa idanu, kasa ta yi da nata tana faɗin "Wata mata ce a garinsu Kausar". "Kuma sai kika buɗe mata jikinki ta yi zanen? Sannan a rasa ina za'a buɗe mata ta zana sai nan wajen?".

Ɗan saƙalo wuyarsa ta yi dan ta miƙe ta bar jikin nasa saboda ta ji yanayin maganarsa ya fara sauyawa, kada ya je ya zaneta ko ta sha mari, gara mata ta yi nesa da shi idan ya so ta amsa mishi tambayar a can, idan ta kama duka ne kafin ya miƙe ya capkota ta zunduma waje a guje abinta, sai dai ina tana ƙoƙarin miƙewa ya ɗaura hannu a saman bayanta tare da mayar da ita ta kwanta dan dole ba dan ta so ba.

"Ba yanzu kika ce ba zaki iya tashi ba? Amsa my question first ma dai". Har lokacin hannunta na a sakale a wuyarsa bata saki ba, ɗan shafa wuyar tasa ta fara yi tana tunano shawarar da gwaggo take gayawa mummy idan ran daddy ya ɓaci abin da zata yi mishi ya sauko cikin ƙanƙanin lokaci, yau karatun gwaggo take tunanowa, nan take zuciyarta ta amince mata da shi ma ta yi mishi hakan ko zai sauko yanda ya fara yi mata magana da zafan nan, kishinsa ya motsa.

Tuna hakan yasa ta cigaba da shafa wuyan nasa a hankali tana haurawa zuwa baki bakin gashin kansa ta sake sauko da hannunta zuwa saman bayansa. "Yaya Saif lokacin fa da aka yi mini zanen ina karama, ban kai haka ba, lokacin kamar ma ban cika 13 years ba". Ta yi maganar tana ɗago da dara daran sleeping eyes ɗin nan nata, ga su sun kara wani irin fari tas da su kamar audiga.

Tana ɗago idanu ya ɗago haɓarta shi kuma ta yanda zasu ji daɗin ganin juna da kyau, hannunsa dake saman bayanta ya zura cikin rigarta yana shafa lallausan bayan nata, kwanciya ya yi da ita a jikinsa har lokacin yana kallon cikin kwayar idanunta da ta saukesu kasa tana ɗan kallon gefe hannunta na saman wuyarsa, cikin ɗarɗar ta ɗaura hannu a saman ƙashin maƙoshinsa, wani irin zirr ya ji a jikinsa, bai san time da ya rungumeta sosai a jikin nasa kamar wani ya ce zai kwace mishi ita ba.

"Meesha" Ya ambaci sunanta a hankali, ɗago kai ta yi da nufin ta amsa, tana ɗagowa ya haɗe ɗan bakinsa da nata, wani irin guguwace ta ɗebeta zuwa wata duniya, dan kuwa a kiss da ya yi mata yau karo na uku, biyun dukka bata cikin hayyacinta, ba zata iya wani gane me ma ta ji ba, yanzu kuwa tana cikin natsuwarta, sai jinta ta yi tamkar wanda aka zarewa laka, sumar kwance ta yi tana jin lallausan lips nasa dake yawo a tsakanin laɓɓanta na sama da na kasa, jin abin take yi tamkar a mafarki ko a tunani.

Sai da ta ji saukar hannunsa a saman mazaunanta ne ta dawo daga duniyar da ta afka, nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke cikin tsoro jikinta na kerma ta yi ƙoƙarin kissing na shi ita ma dan laushin lips nasa sun kiɗimata over, tana son ta ji, dama idan baku manta ba, ɗan bakin nan nasa yana ɗaya daga cikin abin da take bala'in kauna a face nasa.

Hannunta dukkan biyu tasa ta tallabo kumatunsa tare da capko lips ɗin nasa ta datse idanunta gam dan ma kada ta ga wani irin yanayi ne zai bayyana a saman face nasa. Tana fara kissing nasa bai san time da ya waro dara daran idanunsa waje sosai ba, ga idanun nasa sun yi jawur kamar wuta. Ganin da gaske ita ce take kissing nasa yasa ya lumshe idanunsa saboda wani azababben daɗi dake ratsa shi, ji yake yi tamkar ya mayar da ita cikin cikinsa, duk wannan abin da yake faruwa sam baya cikin hayyacinsa, ya jima da afkawa duniyar sama jannati, ga shi ta zo ta kara rikita masa ƙwaƙwalwarsa da kissing nasa da ta fara yi.

Ita ma kuma laushin laɓɓansa ya jata zuwa duniyar da ya faɗa wato duniyar sama jannati, sam bata ji bata gani ta fita a hayyacinta, kissing nashi take yi babu kama hannun yaro, hannunta ya kama ya ɗaura a kansa, watsa gashin nasa ta shiga yi tana kara lafewa a jikinsa, nan take sautin numfashinsa ya sauya, hannu ɗaya ya ɗaura a saman gashin kanta yana ɗan shafawa izuwa bayanta.

Call ɗin daddynsa ne ya dawo da su daga duniyar da suka faɗa, sakin lips ɗin nasa ta yi tana ƙoƙarin sauka daga jikin nasa, rikota ya yi idanunsa a lumshe ya mayar da ita saman kirjin nasa yana sauke numfashi a hankali hankali, call na farko ya katse na biyu ya sake shigowa, sam baya ji kamar zai iya ɗaukar kiran, cigaba da shafa bayanta ya yi yana wani sauke nauyayyar ajiyar zuciya.

"Yaya Saif ana kiran wayarka, in ɗauko maka ne?" Ta yi maganar cikin sanyin murya, shiru bai amsa mata ba, kira na uku ne ya sake shigowa da alama dai daddy yana bukatar yin magana da shi cikin gaggawa ne. "Yaya Saif kayi magana mana, sai mutun ya yi ta yi maka magana amma ka share shi". A wannan karon ta yi maganar a shagwaɓe sosai.

Waro idanunsa da suke jawur da su ya yi, can kasan maƙoshinsa ya furta "Ni ban san yaushe kika zama irin Aseef ba a wajen magana". Turo baki ta yi tana faɗin "Kai yaya Saif ni dama haka nake maganata". Tana magana idanu a rufe ruf, shiru ya yi bai sake yin magana ba ya zubawa face nata idanu yana jin wani iri a cikin zuciyarsa, tabbas face ɗin Rimsha da Jehan suna gefa shi cikin yanayi a duk lokacin da ya kallesu, musamman ita Rimsha ya rasa me dalilin da yasa yake jinsu a cikin zuciyarsa.

Call ɗin daddy na biyar ne ya sake shigowa, hannu ya miƙa saman bedside drawer ya ɗauko wayar, video call ne, dad ya kira ne dan ya ga ɗan nasa ya ji kuma ya tafiyar tasu ta kasance, ko a jikinsa ya ɗauki kiran tana kwance a saman kirjin nasa yana shafa kanta zuwa bayanta da hannunsa, ta lafe abinta idanu a rufe.

Lokacin da ya ɗauki kira suka yi 4 eyes da dad ɗin, wani irin murje idanunsa daddyn ya yi dan ya sake ganin wai shin abin da yake ganin nan gaskiya ce ko mafarki ne, mace a kwance a saman kirjin Lion, bayan haka kuma yana shafa lallausan gashin kanta? Anya ba mafarki yake yi ko kuma gizo idanunsa suke yi mishi ba kuwa? Ya tambayi kansa da kansa. Shi kuwa Lion ko a jikinsa, ita ma bata san cewa ya ɗauki kiran ba, bata san cewa Video call bane, haka zalika bata san cewa daddynsa ba ne, idan baku manta ba idanunta a rufe ruf.

"Why are you looking at me like that daddy?". Ya tambaya yana dawo da kallonsa a saman face ɗin uncle Herry dake kusa da daddyn.

Readers Also Read