Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 87
Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 87: Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 87. Shiru ya ɗan yi na ƴan mintocin da ba su wuce…
3,022 words
Shiru ya ɗan yi na ƴan mintocin da ba su wuce biyu ba, sai azalzala mishi Areef yake yi da ya yi magana, amma shi kuma ya yi shiru yana ɗan tunani, can kuma sai ya ce "How comes za'ace matar Aseef ta ci poison? Taya za'ayi ace kowa a gidan ya ci abincin lafiya lou sai ita ce kawai ta ci poison a ciki? Wannan ba laifin masu yin girki ba ne, laifin daga cikin masu cin abincin yake tun da kowa a gidan ya ci abincin lafiya lou! Amma ba tare da Aseef ta ci abincin bane?". A ruɗe Areef ɗin ya amsa mishi da "Wlh i don't know, ina ga kamar tare suka ci abincin, ni bana gidan kirana Aseef ɗin ya yi a waya a kan na yi sauri nazo na ceci rayuwarta kada ta mutu, so ban san ya abin ya kasance ba". "Shi Aseef ɗin kuma yana nan lafiya?" "Yes yana nan lafiya, shi fa ya kirani a waya da kansa!".
Mayar da kallonsa kan Rimsha dake ta faman haɗa spoons waje guda ya yi, ɗan zuba mata idanu ya yi yana kallon yadda take zuba yaji a gabanta tana tsince namar dake cikin abincin tana tarawa a gefe guda alamar bata son ci, dawo da kallonsa saman face nata ya yi, yana kallon yanda take murnar cin yajin da take yi, nan take kwakwalwarsa ya ayyana mishi Akila ce zaune a wannan waje ba Rimsha ba, tunani ya fara yi na yadda akayi ta ci guba ita kaɗai a gidan, yanda Rimsha ta zuba wannan yaji a gabanta zai zamana haka aka zuba guba a gaban Akilar lokacin da suke cin abinci, to waye ya yi hakan? Ta ya za'ayi gabaɗaya family'n suna saman table ɗin cin abincin a tare har a zuba mata guba a gabanta babu wanda ya gani? Wannan abu ne mai wuyar ganewa mai kuma ɗaure kai.
"Where is she?" Ya tambaya yana mai sake jinjina al'amarin a ransa tare da dawo da kallonsa kan wayar. "Tana bedroom ɗin Aseef ɗin". "Okey take da camera to her place let me see her". Okey ya amsa mishi da shi tare da ɗaukar wayar da sauri ya nufi bedroom ɗin na Aseef.
Gabaɗaya ƴan gidan suna cikin bedroom ɗin, harta daddyn Rimsha da Jehan, hankalin kowa ya yi mummunar tashi, musamman ma daddyn Lion ya shiga tashin hankali sosai bare ma da ya ga yanda Aseef ya haukace musu suna neman rasa shi gabaɗaya, ga kuma Akilar tana ta faman ta shake wuyarta tamkar ba zata rayu ba, kowa dake cikin ɗakin sai da ya yi mata hawaye, harta uncle Herry da su Jay, dama shi kam John already yana sonta, dan haka ya sha kuka ba kaɗan ba, ita ma Jehan sai da ta zubarwa da Akilar kwallah sosai yau, Aseef kam ba'a magana, dan haukace musu gabaɗaya ya yi, sai da daddyn Rimsha ya rungume shi sosai ya hana shi taɓata, amma yaki yana ta ƙoƙarin kwace kansa, John ya zo ya haɗu suka rike shi sosai, sai kuka yake yi musu yana faɗin, shi ma dan Allah a bashi poison ɗin yasa su kwanta tare da Heartbeat nasa, idan ma mutuwa ne sai su mutu tare, wlh idan ta mutu shi ba zai iya rayuwa ba, dan girman Allah a agaza shi ma a bashi gubarnan, da farko ma cewa ya yi sam sai ya yi mata kiss sun raba gubar tare, da kyar Areef ya janyesa daga wajen nata ya miƙa shi wa daddyn Rimsha, bawan Allah duk ya birkice ya fita a hayyacinsa, Akila ke ciwo amma ya fita shiga tashin hankali, har wani jiri yake ji kirjinsa na harbawa da karfi karfi, yanzu duk jikinsa ya mutu kamar wani gawa haka ya kwanta a jikin daddyn Rimsha, hawayen da yake fita daga idanunsa ne zai tabbatar maka da bai mutu ba yana da rai.
Daddyn Lion a matsayinsa na babban likita ma ya kasa shawo kan matsalar Akilar, mummunar guba aka bata, wanda ba zai kashe ta a lokaci guda ba sai ya gama nakasata ya wahalar da ita tare da kashe duk wasu kwayoyin halittarta, sannan ya kasheta,
Saman gadon Areef ya haye da wayar tare da juyawa Lion camerar dan ya ganta da kyau, shiru ya zuba mata idanu yana kallonta, sai fama take yi abin gwanin ban tausayi, idanuwanta tamkar zasu fito waje saboda zarosu da take yi, bakinta, hancinta duk suna fitar da jini mai kauri tamkar ba jini ba, tsabar kaurin jinin ma har wani pink pink ya yi, alamar gubar ta fara azabtar da ita, ta fara ratsa jininta da kyau............... WAYE KUKE TUNANIN YA BAWA AKILA GUBA A CIKIN WANNAN FAMILY'N⁉️
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥
KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔 ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne.
KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA, INFECTION KILLER, COLACCA, SAI KAYAN GYARA PAGE. KACA KACA. YALLAGWADA. JIGIDA. RUWA RUWA. BANI BANI. WOMEN JELL BATA BATA. DAFIN KAXA. TANTABARA. XABUWA. CICCIƁI. AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER 09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH, BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI.
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️
👊FATEEMA ZAHRA MUSA (PRINCESS TEEMA OR STAR LADY)✊
*Domin samun karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 09162620621* 69-70
Zuba musu idanu gabaɗayansu Lion ya yi yana karantar face ɗin kowa, dukkansu babu wanda alamar rashin gaskiya yake a tattare da shi, wani irin azababben tari da Akilar ta fara yi ne ya sanya Lion ɗin dawo da kallonsa a kanta, gabaɗaya hankalin kowa ya dawo kanta, dukkansu sun yi shiru suna sauraron su ji me Lion zai ce kuma, shi dai daddy ya yi iya yinsa a matsayinsa na likita shiru, shi ma Areef ya jarraba, amma poison ɗin ma karuwa yake yi sosai.
Almost 2 mins Lion yana kare mata kallo kafin calmly ya ce "Areef kwance mata chain ɗin nan da yake wuyarta ka saka mini shi a cikin ruwa". Miƙawa daddyn Rimsha wayar tasa ya yi a kan ya rike mishi da kyau ta yanda Lion ɗin zai ji daɗin ganin abin da suke yi, matsowa kusa da ita sosai ya yi tare da sanya hannunsa ya ɗan ɗago kanta yana furta Bismillahirrahmanin a cikin zuciyarsa, gabaɗaya sun zaro idanu suna ganin ikon Allah. "John help me with water inside bowl". Cewar Areef ɗin, ya yi maganar yana cire mata chain ɗin.
A sukwane John ya nufi hanyar fita, dakatar da shi Lion ya yi tare da cewa Aseef ya tashi ya kawo ruwan ba John ba, da mamaki su daddyn Rimsha suke kallonsa, me Lion yake shirin aikatawa kenan? Menene yake faruwa? Tambayoyin da suke yi wa kansu kenan.
Shi ma Areef ya ɗan yi mamaki, amma sanin halin ɗan uwan nasa yasa bai wani damu ba, yasan komai sai da dalilin Lion yake yin shi, kuma tun da ya ji haka to fa akwai matsala kenan.
Kallon daddyn Rimsha Areef ɗin ya yi tun bai yi magana ba daddyn ya fara ƙoƙarin tashin Aseef ɗin a kan ya tashi ya kawo ruwa, kasa tashi ya yi dan gabakiɗaya ilahirin jikinsa ya mutu, sai kerma kamar mai zazzaɓi jikin nasa yake yi, ko motsi ba zai iya yi ba, shi kaɗai yasan me yake ji bawan Allah, tabbas idan Akila ta mutu Aseef zai bita, domin kuwa son da yake yi mata ya wuce gaban misali.
"Lion Aseef fa ba zai iya kiƙewa ba". Areef ya faɗa yana ƙoƙarin sauka daga gadon hannunsa rike da chain ɗin da ya kwance daga wuyar tata. Shiru Lion ɗin ya ɗan yi na tsawon 3 mins kafin ya ce "Okey keep the chain behind this your uncle, then ka je ka ɗebo ruwan because da kai da Aseef all abu ɗaya ne". Okey ya amsa mishi da shi tare da ajiye chain ɗin a bayan daddyn Rimsha saman bedside drawer kenan, da yake daddyn yana ta gaban bedside drawer ne saman sofar dake kusa da gadon.
Ruwa ya je ya ɗebo a bowl tare da dawowa cikin ɗakin, kafin ya dawo Lion ya ce da daddynsa ya fara treating na Akilar yanzu za su iya shawo kan matsalar, ana cire mata chain ɗin ta sume a wajen har lokacin kuma bakinta na fitar da kumfa mai haɗe da jini, ba ɓata lokaci daddy ya fara ƙoƙarin ceto rayuwarta, shi kuma Areef ya zo ya sanya chain ɗin a cikin ruwan da ya kawo, kafin ya sanya sai da ya furta Bismillahirrahmanin rahim a cikin ziciyarsa sannan ya saka chain ɗin, da wuya Areef ya yi abu ba tare da sunan Allah a bakinsa ba bawan Allah, komai zai yi sai ya ambaci mahaliccinmu.
Wani irin ajijiya ruwan robar ya yi tare da fallatsuwa sama tamkar an watsa shi, sannan ya koma cikin robar babu ko ɗaya da ya ɗiga a kasa duk irin tashi sama da ya yi, duk cikin ɗakin sun yi matukar tsorata ban da daddyn Rimsha da yake dake yana furta sunan Allah, shi kansa Lion da yake kallonsu sunan Allah ya furta a cikin zuciyarsa, dan kuwa wannan abin sai Allah ne kawai zai iya kare bawansa daga sharrinsu.
Suratul Aaraf Areef ya fara karantawa a cikin ziciyarsa yana mai cigaba da kallon ruwan yanda yake wani irin juyawa da karfi karfi yana fitar da kumfa tamkar mutum ya ci guba, tsit ɗakin ya yi daddy yana ta ƙoƙarin ceto rayuwar Akila, ya ɗan tsaga wutarta kaɗan dan ya samu aikinsa ta yi mishi cikin ƙanƙanin lokaci, idan ba haka ba tana iya mutuwa nan take.
Areef bai matsa daga wajen ba, yana dake yana kiran sunan Allah har sai da ruwan nan ta gama ajijiyarta bakiɗaya ta koma ta natsu tsin, chain ɗin ya kwanta a kasar ruwan, juyowa ya yi yana kallon Lion da ya zuba musu idanu yana kallonsu.
"Waye ya bata wannan chain ɗin?!". Cewar Lion ɗin, ya faɗa a tsawace, ya yi maganar kuma yana mayar da kallonsa a kan Brady da ya shigo yanzu yana ƙoƙarin haukata Rimsha, ya kawo mata wayar Mark ne, ya je ya sami Mark ɗin yana kallon hoton Anaya, shi ne ya kwace wayar ya kawo mata ta gani, dan yasan a wayarta kawai ya taɓa kallon hoton Anaya ɗin, ita kaɗai ya taɓa gani tana kallon hoton, to yau kuma sai ya ga Mark yana kallo, shi ne ya kwace wayar ya kawo mata, ita kuma ta yi muguwar tsorata na hawa jikinta da ya yi yana miƙa mata wayar ta ɗauka cizonta zai yi.
Da gudun gaske ta miƙe daga saman table ɗin ta haye saman bed ɗin wajen Lion tana kuka kasa kasa. Sam bai ji komai ba ko a jikinsa su daddy su Jehan duk suna kallon shi ta cikin camera ya runhumeta yana ɗan bubbuga bayanta, jin kukanta yasa dukka suka ɗago suka zubawa wayar idanu, harta Jehan ɗagowa ta yi cikin sauri dan ta kalli me ya sami ƴar uwar tata take kurma ihu haka, shi ma daddynta ɗagowa ya yi yana kallon wayar da yake Areef ya karɓi wayar dan ya nunawa Lion ɗin yanda chain ɗin ta koma.
Ganin ta haye jikinsa tana kuka ne yasa suka saki baki har su John suna ganin ikon Allah, shi ma daddynta dai mamaki ya yi, har da kara waro idanu yana kallon shin wai da gaske ne Rimsha ce ta haye jikin Lion har haka? To me ya tsoratata da ta hau jikinsa haka? Shi ne abin da daddynta yake tambaya, haurowar Brady saman gadon ne yasa suka fahimci dalilin yin ihun nata da kuma kukan da take yi yanzu.
"Areef i said waye ya bata chain ɗin nan?". Yana magana yana cigaba da bubbuga bayan Meeshar tasa dan ta yi shiru, ya kara ɗaure fuska sosai, sam babu alamar wasa a tattare da shi, nan take kowa dake kallonsa ya sha jinin jikinsa, duk suna tunanin waye ya bata chain ɗin, dan kuwa wannan kara ɗaure fusataccen fuskar nan nasa da Lion ya yi da alama za su ji ne a jikinsu.
"Lion i don't know, ita kaɗai ce zata bamu wannan amsar". Cikin rawar murya John ya amsa da "Ni na bawa Aseef ya bata". Tashin hankali, ya zaɓi ya bada masa ta gaskiya ce, dan kuwa yasan Lion dai ba'a yi mishi karya kuma baka isa ya ɓoye mishi abu ba, idan ma kayi kuskuren yin hakan to ka kwana da shirin tabbas zai gamo koma me ka ɓoye, idan kuma ya gano da kansa to fa zai ninninka maka hukuncin ne a kan wanda ya yi niyar yi maka a baya.
A razane gabaɗaya ɗakin suka mai da kallonsu a kan John ɗin, cikin tsawa tare da ɓacin rai Areef ya ce "Kai ne kenan kake son kashe mini my pleasure? Dan ba matarsa zaka kashe ba, shi zaka kashe, saboda idan ta mutu shi ma ba zai rayu ba!!". Ya kai karshen maganar tare da nufar John ɗin gadan gadan, da karfin gaske ya damko wuyarsa ya shaƙe shi yana faɗin "Before ka kashe shi ni bari na kasheka!!".
Tsawa Lion ya daka mishi yana faɗin ya sake shi, da mamaki ya juyo da ash eyes nasa da suka rikiɗe suka yi jawur Saboda tsantsar ɓacin rai. "Lion cewa fa ka yi na sake shi? Heartbeat namu fa ya yi ƙoƙarin hallakawa, a haka zan kyale shi?".
"Areef i said ka sake shi, calm down mana, ya kamata a ko da yaushe ka yi aiki tamkar jami'i ba mutun kamar kowa ba!". Ciza laɓɓansa ya yi da karfi tare da furzar da iska mai tsananin zafi daga bakinsa, ba haka ya so ba, ya so ne yau ya kashe John da hannunsa, amma tun da Lion ya ce ya sake shi yasan akwai dalili, dan haka sai ya sake shi ɗin yana wani huci tamkar shi ma John ɗin ba ɗan uwansa bane, su dai su ukun nan sune kawai ƴan uwa, a kan junansu zasu iya kisan kai!.
Ita kuma Rimsha jin maganar Areef ne yasa ta ɗago kai daga saman kirjin nasa tana kallon wayar hannunsa, ganin su daddynta bakiɗaya a wajen ne yasa ta yunkura ta gyara kwanciyarta da kyau a saman kirjin nasa tana kallon daddyn nata, shi ma ita yake kallo tamkar ya sa hannu ya jawota ya rungume, tana son ta yi musu magana, amma ba hali domin Lion yana magana da Areef, ba su isa su saka musu baki or su yi wata magana ba har sai sun kammala, ɗagawa daddyn nata hannu kawai ta yi tana sakin kayatatcen murmushi.
Sam daddy bai murmusa ba, dan suna cikin tashin hankali, ta yi mamakin ganin daddyn nata bai yi murmushi ba, Baiwar Allah bata san me yake faruwa ba.
"John who give you this chain?". Cewar Lion, Bawan Allah ya ji shakar manya, tuni ya jiyo kamshin mutuwa, har wani jawur idanunsa suka yi yana fitar da kwallah.
Da kyar ya iya buɗe baki ya ce "Jo....sep....hine ne ta bani su guda uku a kan na bawa matar Michael da kuma wannan da take kusa da kai sai wannan ɗayar." Ya kai karshen maganar tare da nuna Jehan, da kyar ya iya furta sunan Josephine ɗin saboda wani irin azababben shake mishi wuya da aka yi, ji ya yi tamkar ana zare mishi jijiyoyin wuyar nasa, wannan ma dan Allah yasa suna tare da Musulmai ne a cikin ɗakin, da su kaɗai ne kila kashe John ɗin za'ayi. BABBAR MAGANA WANNAN SHI NE TASHIN HANKALI, JOSEPHINE KUMA? TO A INA TA SAN SU AKILA? WAYE YA GAYA MATA ƳAƳAN NATA SUN YI AURE? ME HAKAN YAKE NUFI? WANNAN SHI NE CAKWAKIYA, SHI WAI A TSAKANIN JOSEPHINE DA WILLIAM WAYE MAI GASKIYA NE? MU DAI JE ZUWA.
"Areef ku bashi ruwa ya sha". Cewar Lion, da sauri Jay ya ɗauko ruwan daga cikin fridge ya kawo musu, a cikin zuciya Areef ɗin ya yi bismillahi tare da yin tamkar zai sha ruwan ya tofa ayoyi biyar na farkon suratul baƙara ba tare da sun ankara ba, sannan ya bawa John ɗin dan ya sha, abin da yasa ya yi hakan saboda kowa da yake cikin ɗakin ya lura da irin mawuyacin halin da John ɗin ya shiga na shake shi da aka yi lokaci guda, so shi ne ya taimaka mishi dan su sami abin da suke so.
Kowa da yake wajen ya shiga tashin hankali jin cewa daga wajen Josephine sarkar ta fito, shi kuwa Lion ko a jikinsa, kallon Areef ya yi yana faɗin "Why kake magana da ita a ɓoye ba tare da na sani ba? Kana tunanin na zan gane ba ko?". Ya yi mishi magana ta sigar da ba wanda zai gane nufinsa, dan ya yi maganar ne a matsayinsu na jami'ai wanda ko daddynsu bai gane me ya ce ba, saboda ba baki da baki ya faɗa ba, da laɓɓansa kawai ya motsa suka yi ƴar kurma, da yake Areef ɗin yana kallonsa.
Shi kuwa daddynsu jin John ya ce Josephine ce ta bada chain ɗin ba ƙaramin razana ya yi ba, saukowa kasa daga saman gadon ya yi yana mai kara tambayar John ɗin wace Josephine? Kuma a ina ya ga Josephine ɗin?. Katsesu Lion ya yi da cewa "Its okey dad, komai ya wuce, ni zan yi bincike a kai, dan haka kada ku sake tambayar John, kada wanda ya sake tayar da maganar nan, Areef go out let's talk".