Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 9
Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 9: Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 9. Ai kuwa bata yi wata wata ba, ta tako izuwa…
3,331 words
Ai kuwa bata yi wata wata ba, ta tako izuwa gaban gadon, a hankali ta ja mashi wanan katon bargon nasa, da kyar ma ta iya jawo bargon ta rufa mashi zuwa jirjinsa, yau gata ga shi kuma yana barci, amma ta kasa kare mashi kallo, zuciyarta ta karaya, ba zata iya kallon shi ba, idan ta yi hakan kuma ta san zata yi ihu ne, zata firgita sosai, domin rikita mata kwakwalwar yake yi a duk san da ta kalle shi, wani irin kwarjini Allah ya yi mashi.
Bayan ta rufa mashi bargon, a hankali ta duƙa a gabansa, har lokacin taki kallon shi, hannu tasa tana ƙoƙarin zame wayar nasa, kirjinta sai dukan uku uku yake yi.
Wani irin Mahaukaciyar damka ya kaiwa wuyarta, idanunsa a lumshe bai buɗe su ba, bai kawo cewa ita ba ce, a cikin barci kawai ya ji tana zare wayar a hankali hankali daga hannunsa, shineyasa ya kai mata damƙa, sai kuma ya yi Sa'a ya capki siririn wuyar nan nata.
Tsabar razana bata san time da ta kurma ihu ba, ai kuwa rige rige Imran da Areef suka yi wajen shigowa ɗakin, har lokacin bai saki wuyar tata ba, ganin hakan yasa Areef ya gane abin da ya faru, Rimsha bata san cewa Lion bashi da nauyin barci ko kaɗan ba, zai iya yana barci kuna hira a palo ma yana jinku sama sama, haka yake, baya da nauyin barci, kuma a yadda ta zo zame wayar tasa, ta yi mashi abu kamar ɓarawo, a hankali take zameta, wai dan kada ta tashe shi, shi kuma ya damketa, a yanzu dai ko bai buɗe idanunsa ba, ya san wuyar waye ya damƙa, tun lokacin ma da ya damka ɗin, ya ji wuyar ɗan siriri, bata ma kai kaurin singalalalin hannunsa wajen ɗaura agogo ba, tun da ya ji haka ta gane wuyar kanwar Imran ce, sai dai kuma bai sake ta ba, dan a ganin shi ta raina shi ne, a kan me zata ta taɓa mashi waya ko wani abu nashi, shiyasa ya kara shaƙe ta yana da ga kwance, idanu a rufe kamar mai barci, dama ga yunwa yana ji.
Da sauri Areef ya kariso wajen, bawan Allah da yake yana cikin ciwo, sai ya kasa ɓanɓare hannun Lion ɗin daga wuyar tata, yasan idan ya sanya karfi sosai, wajen ciwonsa zata iya fara yin jini kuma, cikin sanyi murya ya ce "Saif! Saif mace ce fa, zaka kasheta, ba zata iya jurewa ba". Abin da ya sanya ya gaya mashi hakan kuma, Lion da bakinsa lokacin suna school, Aseef zai daki wata yarinya ya hana shi, bayan ya dakatar da shi ya ɗaura da cewa, ai duk mai dukan waƴan nan halittu ba namiji bane, "Idan har zata daki mace to da sauranka a mazantaka, kuma kai Aseef idan ka daki wannan abar ai ba zata saura ba, halittun da su da kansu ma suna tafiya suna faɗuwa saboda tsabar rashin quality, to ina ga kuma ka ɗaura hannu a jikinsu? Ai ka daki namiji, ka sanya namiji dakakken gwarzo kuka, shi ne ka cika namiji, amma waƴan nan halittu, ka sanya masu mahaukacin tsoron ka kawai, wadda ganinka kawai ma zai sanyasu suma". A lokacin da Lion ya yi wannan magana, yana ganinyar tashensa ne, ya ce yafi karfin ya daki mace, sai dai ya sanya kartin maza kuka, idan kuma kuka lura yana daga cikin abin da yasa yake dannewa baya dukan Rimsha, amma bata ji tana kure shi.
Ko da Areef ya yi magana, bai zame hannunsa ba har sai da ya ji yana ƙoƙarin yin kisan kai, a cewarsa yarinyar tana kure iya ɗan hakurin da yake da shi ne, rawan kanta ya yi yawa, yana son saita ta da kyau.
Yana saketa ta karisa zama a wajen tana ƙoƙarin sulalewa kasa ta kwanta, da sauri Imran ya kariso ya riƙe mata hannu tare da miƙar da ita suka nufi waje.
Gefen gadon Areef ya zauna yana mai bin ɗan uwan nasa da kallo. "Saif idan ba damuwa, zan so ka rinƙa yi wa yarinyar nan uzuri, kaga karamar yarinya ce, kuma mace ce, ƙwaƙwalwarta karami ne, kasan ko kallonka ta yi wani mahaukacin razana take yi, idan ka ɗaura hannunka a jikinta wlh daga ranar ba zata sake moruwa ba".
Shiru ya yi bai tanka ba, hannu Areef ɗin ya kai ya toshe mashi hanci da karfi yana faɗin "Har dani zaka yi wa walakancin ne?". Tsawon minti ɗaya yana riƙe da numfashinsa kafin ya sanya hannu ya damki hannun ɗan uwan nasa ya janyo shi da karfi, luuuuuuu Areef ya tafi sai saman kirjinansa, waro blue eyes nasa masu ɗauke da barci ya yi akan face ɗin ɗan uwan nasa, ido huɗu suka yi.
Wani irin kallon Saif ya bi shi da shi kafin ya sake shi. "Tashi mashi a jiki" gently ya yi maganar. Kara hayewa jikin nasa Areef ya yi. "Karfi ya ɗaga ni in gani". Lumshe ido ya yi yana jin Bala'in kaunar ƴan uwan nasa. "Areef kana kure ni ko?". "Au haba dai? To shikenan ka ɗauki mataki!". "Okey zan ɗauka ai yanzu dai tashi mani a jiki ka zuba mani abinci, am felling hungry over". Ya yi maganar can kasan maƙoshinsa. "Nifa ba zan tashi ba, karfi ya tashe ni nace". Tamkar abin haɗin baki, suna a haka sai ga kiran Aseef bawan Allah.
Da yake wayar tana a hannun Saif ɗin, sai ya kawota saitin face nasa, ganin Aseef ne yasa ya sauƙe nauyayyar ajiyar zuciya, shi ma dai Areef ajiyar zuciyar ya sauƙe, bayin Allah nan suna yi wa junansu wani irin mahaukacin kauna ne wadda baki ba zai iya faɗarta ba, duk ɓacin rai ɗin da ɗaya yake ciki, suna ganin juna zasu wastsake.
Areef ne ya sanya hannu ya yi picking call ɗin, har lokacin yana kwance a jikin Lion ɗin.
Wani irin ƙayatattacen murmushi Aseef ya saki lokacin da ya kalli fuskokinsu dukkansu biyu, da yake video call yake kiransu, bai cika kiransu normal call ba, kwance yake a saman gadonsa yana sanye da kayan barci milk color, ya yi kyau sosai.
Shi ma Areef ƙayatattacen murmushi ya saki, shi kuwa Saif bai yi murmushi ba, amma dai ya ɗan saki wannan ɗaurarriyar fuskar tasa, alamar ya ji daɗi kenan, amma murmushi kam, sam babu ko ɗigonta a fuskarsa.
"Wow My TRIPLETS yau kam wace iriyar Sa'a ce dani,? Naga face naku a haɗe waje guda, wlh ina kewarku sosai, ko yaushe na tuno ku sai na yi kuka, shi ma daddy yana kewarku sosai, ni gaskiya zan bar exams ɗin nan na biyo ku, ba zan iya zama ba, i can't gaskiya". Ya kai karshen maganar tamkar zai yi masu kuka.
"My shagwaɓati ba, kai Aseef ban san ya zanyi da kai ba, yanzu dai kuka zaka yi mana kenan? To kayi bari na yi recording na ajiye tarihi, gaskiya your future wife tana da aiki, yaron nan har yanzu ba zaka canza ba ko?". Cewar Areef, ya yi maganar cikin zolaya.
"Serious kewarku nake yi, kuma ni mata mai shagwaɓa zan aura ai, ta yi ta kuka nima ina taya ta, jiya ma na haɗu da wata beb a white house, sai dai bata iya shagwaɓa ba, sai wani juya min ido kamar wata tsuntsuwa ta iya".
Dariya Areef ya kwashe da shi, shi kam Saif kamar wasu Tv haka yake binsu da ido, idan suna irin wannan wasan nasu nishaɗi suke sanya shi, yana son ya kallesu suna farinciki suna dariya, ga shi shi kuma bai iya dariyar ba bare ya yi masu shi ma.
"Aseef shiyasa fa na ce maka zan ɗauko maka mace daga nan Nigeria in kawo maka, matan Nigeria fa the are beautiful wlh, and suna da kirki over, ba kaga Our princess ba Rimsha? Ai tana da kirki sosai, kuma tana da kyau, to irinta zan samo maka".
Ɗan satar kallon Musharraf dake barci a gefensa ya yi kafin ya ce "Idan har Gimbiyar TRIPLETS tana da sister to kawai ka ɗauko mani ita, in dai jinin Uncle Hosain ne, ina so zan aura". Zaro ido Saif ya yi yana jujjuya sunan da suka kira Rimsha da shi, da yake ya san suna kaunar Musharraf, sai ya yi tunanin hakan yasa suke kaunar Rimsha, sai bai kawo komai a ransa ba, bai taɓa kawowa cewa wai Rimsha na haukar son shi ba, dan shi kallon ƴar karamar yarinya yake yi mata, idan ma aka gaya mashi tana son shi ai sai ya sumar da ita, kuma tabbas zai tsaneta, ace yarinya yar karama har ta san soyayya, dududu shekarunta nawa a duniya? Da har zata fara soyayya, ita da ya kamata yanzu ace ta tsaya tsayin daka tana zuba uban karatu kamar ba gobe, amma wai soyayya. TAB LALLAI LION BAI SAN RIMSHA KAM TUN TANA ƳAR SHEKARA 9 TAKE HAUKAR SON SHI BAN, IDAN YA JI TUN WANNAN LOKACIN KUMA SAI YAYA, YANZU MA YA CE KAMAR HAKA BATA KAI SOYAYYA BA, ƳAR JARIRIYA DA ITA........🤣.... TO INA GA KUMA YASAN TA JIMA A CIKIN SOYAYYARSA? TAB AKWAI AIKI.
"Kai Aseef ka kawo good shawara fa, zan tambaya maka Rimsharmu idan tana da sister zan nemota na taho maka da ita, amma kuma sai dai kamar da wuya fa ace tana da sister, domin da uncle ya zo mummynsu kawai ya tambaya, ban ji ya ce ina sister ta ko wani abu makamancin haka ba, amma zan bincika".
Aseef zai yi magana zazzakar murya Lion ya katse su da cewa "Haba Areef ka tashi mani a jiki kada ka karya ni mana, kuma ai na ce maka yunwa nake ji ko?". Cikin sauri Aseef ya ce "Kai Areef ka tashi ka bashi abinci mana, please ka yi sauri, nima har kasa na fara jin yunwa".
Kwafa Areef ya yi. "Ba zan tashi ba karfi ya tashe ni, kuma abinci dai ba za'a ci ba, tun da yau ya shaƙe mani sister ba zai ci abinci a gidan nan ba". Zaro ido waje Aseef ya yi. "Haba mana Lion meyasa zaka shaƙeta? Ai gwara ni kazo ka shaƙeni, ina fa sonta, sister mu ce fa, ƴar uncle ce fa, muna kaunarta ni da Areef, kuma ya kamata kai ma kaso abin da nake so tun da kana so mu, please ka daina shaƙeta ka ji? Saboda ni zaka yi ka ji my pleasure? Our king". Tamkar bai ji su ba, tabbas yasan suna bala'in kaunar Rimsha, dan ya ga irin zaman da suke yi da Areef, ya ga yadda Areef yake bata kulawa ɗazun, abin ma mamaki yake bashi, sai dai shi kuwa bata ma ishe shi kallo ba.
"Areef zan yi maka rashin mutunci fa idan baka tashi mani a jikina ba". Ya faɗa gently.
"Areef please stand up mana, ko so kake ka saka ni kuka ne? Ya ce maka yunwa fa yake ji, please ka tashi, dan kaga muna lallaɓaka baka da lafiya ko, to Allah ka tashi ko kuma muyi sama da kai, kuma ai ba zan sake shaƙe sister taka ba, na ari bakin ɗan uwan, na yi magana a madadinsa, dan haka yanzu dai ka tashi maza". Cewar Aseef
Kin tashi ya yi tamkar bai ji me suke faɗe ba, sai da ya kalli Lion ya lumshe idanu alamar ransa ya ɗan ɓaci, dan a gaskiya yana jin yunwa sosai, kuma baya son ya yi wurgi da Areef ɗin ne, dan saboda ciwon dake jikinsa, hakan yasa yake mugun tausaya mashi, amma Areef na neman kai shi bango.
Ganin ya lumshe idanu ne yasa Aseef ya yi mashi alamar ya tashi ya bashi abinci dan Allah, ko da kuma Aseef bai faɗa ba, to ya zama dole shi ma Areef ɗin ya tashin dan kansa, baya son ɓacin ran ɗan uwan nasa.
Miƙewa ya yi tare da dirowa kasa yana faɗin "Ba dan halinku na tashi ba". Har lokacin wayar tana a hannun Saif ne.
Wucewa ya yi zuwa wajen da Rimsha ta ajiye abincin, tare da zama ya fara zuba abincin a plate.
Miƙewa shi ma Lion ɗin ya yi tare da dirowa kasa ya nufi wajen abincin, sai dariya Aseef yake yi masu, idan Aseef da Areef suka haɗu, kamar wasu tom and Jerry suke komawa, su na wasa da dariya da juna over, kamar wasu ƴaƴan kawu nai, sun haɗe kai sosai, shi kuma Saif sai dai ya yi ta binsu da ido kawai yana jin daɗin yadda suke farinciki.
Zama ya yi tare da ɗaukar spoon zai fara cin abincin, karɓe spoon ɗin Areef ya yi tare da ɗebowa ya kai mashi saitin ɗan bakinsa yana faɗin "Ni zan baka first spoon". Kallon gefen ido mai kama da hararar wasa ya wurga mashi kafin ya buɗe ɗan karamin bakin nasa. Zuba mashi abincin Areef ya yi, sai murmushi Aseef yake yi, karɓar spoon ɗin shi ma Lion ɗin ya yi, ya ɗebo abincin ya kawowa ɗan uwan nasa a saitin bakinsa, buɗe baki Areef ya yi ya karɓa, a tare suka fara taunar abinci, Aseef ji yake tamkar ya yi tsuntsu ya zo ya same su, wayyo yana wani irin mahaukacin kewarsu.
Abin gwanin burgewa, dama idan suka haɗu, tsantsar kula da nuna kaunar juna suke yi wa kansu, ɗauko wani spoon ɗin Areef ɗin ya yi suka fara cin abincin a tare, sai hira Aseef da Areef suke yi, shi kuma abincin kawai yake ci yana saurarensu.
A tare suka cire hannu daga abincin, sun ƙoshi, kusan kuma a tare suka sha ruwa. Miƙewa Areef ya yi tare da kwashe kayan abincin ya fitar, lokacin da ya dawo, Saif ya koma gado ya kwanta tare da ajiye wayarsa a saman bedside drawer yana sauraren Aseef tare kuma da kallonsa.
Hayewa gadon shi me ya yi, suka cigaba da hirarsu mai cike da so da kuma kaunar juna, sai zolayar juna suke yi, har Lion ya yi barci ya barsu, daga ƙarshe dai suka yi sallama har da yi wa wayar kiss kamar wasu masoya, tare kuma da furta kalmar i love you wa junansu, abin gwanin burgewa da ban sha'awa, kowa zai yi fatan samun ƴaƴa irinsu masu bala'in kaunar juna haka koma fin hakan.
Kashe wayar Areef ya yi tare da ɗaurata saman bedside drawer kusa da lamp, daga nan ya kashe musu wutar ɗakin tare kuma da kara gudun Ac ya kwanta, yau dai a ɗakin ɗan uwansa zai kwana kenan.
Yana kwanciya ba jimawa barci ta yi awon gaba da shi.
A ɓangaren Imran kuwa, bayan ya maida ita bedroom nata, na shi bedroom ɗin ya wuce, ya ɗauko ɗayar wayarsa ya kunna domin ya kira Abba, dama ya kasheta ne kawai dan baya son damuwar kiraye kirayen jama'a, shiyasa Ammie ta yi ta neman numbersa bata shiga.
Bugu ɗaya ya yi wa Abba ya ɗaga, a lokacin kuma Ammie ta yi nisa cikin barci, akwaita da nauyin barci sosai.
Cikin girmamawa ya gaida Abban nasa, bayan sun gaisa ne ya ce "Abba dan girman Allah ka gaya mani menene ya haɗaku da bappa Hosain da har ya yi fushi da ku ya baro gida". Shiru Abba ya ɗan yi na ƴan mintoci. "Imran babu komai kawai fushinsa ya yi, kasan shi da bala'in zuciya kamar babanmu, to fa ƴar karamar faɗa ce ta haɗasu da mata a cikin gida, shikenan dan munbi bayan matan munyi mashi faɗa ne ya zuciya ta baro gidan".
Tabbas Imran yasan ba haka bane, domin a iya zaman da ya yi da daddyn Rimsha a baya, ya fahimci mutun ne shi mai zurfin tunani da kuma sanin yakamata, haka kawai dan faɗa na mata a cikin gida ba zai yi fushi ya bar ƴan uwansa ba, dole dai akwai wata a kasa, da alama kuma babbar al'amari ce a kasar da yasa suke ɓoyewa, dole akwai abin da suka yi wa daddyn Rimsha da har ya zuciya haka.
Jin ya yi shiru yasa Abba ya ce "Imran ka fara barci ne?" "A'a Abba ban yi barci ba". "Okey ai naji ka yi shiru ne, to dai shikenan sai da safe ni barci nake ji, da safe ka kirani mu yi magana akan ƴar wajen Maik". Yana kai karshen maganar ya katse kiran domin ya ga Ammie ta fara motsawa, kada ta tashi ta tsayar masu da bala'i, dama kunsan ido rufe take neman Imran ɗin.
A ɓangaren Imran kuwa, ɗaura wayar saman bedside drawer ya yi yana tunanin menene gaskiyar abin da ya faru, waye a cikinsu Abba zai gaya mashi gaskiya? Menene yake faruwa a cikin wannan family'n? Ko dai na tambayi gwaggo Batula ce? No tun da Abba bai faɗa mani ba, ita ma ba zata gaya ba, waye ya kamata na samu ya gaya mani wannan magana.
To masu karatun na san zaku so jin me ya haɗa su, tun da Imran bai sani ba, bari ni na gaya maku, a shekarun baya kusan shekara 35 zuwa da 37 baya, mahaifin su daddyn Rimsha, wato kakansu Rimsha........
❤️❤️TRIPLETS❤️❤️
E7-8
Turo bakin nan ta yi kamar biro. "To gwaggo Batula dan ita ta haifi yaya Imran sai ta ce bata son ganina a fitar da nine? To ni dama waye ya ce ma ta so ni? Ni ma ai ba sonta nake yi ba, kuma ba zan zauna ma a gidan nan ba, dan daddy ya taɓa gaya mani she is wicked".
Sosai Hjy Batula ta buge mata baki da ɗan karfi, kuka ta saka masu, har da birgima a kasa, taɓe maki Ammie ta yi tana ganin ikon Allah, wai wannan mahaukaciyar ce matar ɗan ta? Ta tambayi kanta da kanta.
Ita kuwa Aunty a cikin zuciyarta tana jin da ace Mummy Abla ta kyaleta, bata daketa ba, yanzu ga shi ta sake kwaɓe masu komai.
Tsawa Ammie ta daka masu akan su fice mata daga gida tun ransu bai ɓace ba. Waya Hjy Batula ta ciro wayarta ta kira Abbi dan ta sanar da shi abin da yake faruwa, bugu ɗaya ya ɗauki kiran, ba ɓata lokaci ta sanar da shi ga abin da jellyn ta yi, ita kuma Ammie ga reply da ta bata akan ba zata karɓi jelly ɗin ba.
Shiru Abbi ya ɗan yi kafin ya yi magana kasa kasa dan kar daddyn Jelly ya ji, yasan hakinsa sarai idan ya ji zai ɓata rai ya ce an wulaƙanta mashi ƴa, hakan yasa ya yi magana kasa kasa dan zaman lafiya yake so ba faɗa ba, umarni ya yi masu a kan su dawo da jelly ɗin gida, idan suka dawo daga Katsina za su kira Imran, sai su san abin yi.
To ta amsa da shi, ta yi wa Ammie sallama tare da riƙo hannun jellyn ta miƙar da ita suka nufi waje, wani irin matsiyacin kallon banza Ammie ta bisu da shi, sai da suka ƙurewa ganinta ta koma saman sofa ta zauna tare da ɗauko wayarta.
Number Imran ɗin ta fara laluɓa dan ta kirashi, ta bashi umarnin akan idan ma ya auri jelly to ya saketa ko ta tsine mashi albarka, sai dai kash a kashe ta sami number, ta ji babu daɗi sosai, saman sofa ta ɗaura wayar ta cigaba da kallonta.
Su kuma bayan sun je mota, sosai Hjy Batula ta yi wa Jelly faɗa tare da nasiha, ta kara mata da cewa, in dai bata girmama Ammie ba, to tabbas yaya Imran ba zai taɓa sonta ba, zai dai'na kulata, zai yi watsi da ita, domin yana Kaunar mahaifiyarsa shi ma, shiru ta yi tana sauraron Hjy Batula tamkar wata mumina, yadda kasan an mata sauƙar karatun Al Qur'ani mai girma a kanta, tsit ta yi, sai da mummy Abla ta gama nasihar, ta tada mota dan su tafi.
Suna kama hanya ita kuma Aunty ta ɗaura nata nasihar, dan jelly sai an bita a hankali, ta karfi ba zata taɓa yi wu wa ba, idan ka zare mata ido, ita ma zare maka zata yi, bata da tsoro ko kaɗan, ga uban rashin kunya tamkar a kanta a sauƙe shi.