Kenza eBookz

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 8

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 8

Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 8: Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 8. Spoon ɗaya ya kai bakinsa, da kyar ya haɗiye…

3,288 words

Spoon ɗaya ya kai bakinsa, da kyar ya haɗiye abinci, kawai ma dan baya son dawo da ita ne yasa ya haɗiye da kyar ɗin, ta lura da hakan, da mamaki take satar kallon shi, ko me ya faru da abincin Oho.

Ajiye spoon ɗin ya yi tare da ɗaukar wayarsa, kasa ya yi da kansa yana latsawa, zuba mashi idanu kawai ta yi tana kallon yadda ya kara ɗaure fuska sosai, dama yaya lafiyar kura bare kuma ta yi zawo, tabbas akwai abin da ya faru da abincin, wannan irin uban ɗaure fuska da ya yi haka ba'a banza ba.

Nan take wani irin tsoron shi ya dira mata a ranta, ji take yi tamkar ta tashi ta gudu, dan ganin ya kara ɗaure fuskar, suna a haka Mark ya shigo ɗakin ya same su, hannunsa rike da bowl mai ɗan girma, gabansa ya zo ya ajiye bowl, ba tare da ya yi magana ba ya juya ya koma wajen hukuncin da aka yanke mashi yanzu, shi mai girkin ma first.

Da mamaki take kallon pepper dake cikin bowl ɗin, an wankesu da kyau, ga su fresh, ta rasa me hakan yake nufi, me kuma za'ayi da su.

Miƙewa ya yi, ya koma saman sofa ya zauna, gently ya ce ta cinye attarugun nan dukka, zaro idanu waje ta yi, yau ta shiga uku laifin me tayi? Ta tambayi kanta da kanta, abin da bata sani ba shi ne, abinci da ta kawo mashi, yau Mark ya yi kuskuren da bai taɓa yi ba, yaji ta kubce a cikin abinci, shi kuma Lion kwata kwata baya cin yaji, komai kankantar ta saboda gym da yake yi, idan har ya ci yaji takan iya yi mashi mummunar illar a jiki, kuma tun kafin ya fara gym ma, shi baya haɗa hanya da yaji, ba'a taɓa yi mashi girki da ya ji ba sai yau, Mark ya yi kuskure, kuma yau kamar ba lafiya ba, sai bai ɗan ɗana abincin ba, haka ya shiryawa ogan nasa, to ita laifin kawowa kawai ta yi shi ne a kace ta ci attarugun, shi kuma Mark na shi hukuncin wa iya zubillah kwakwalwa ba zata ɗauka ba, kuma babban abin haushin shi ne ma zai hukunta kansa, idan kuma ya yi ɗaya ba daidai ba yasan halin ogan nasa, bai ma isa ya tsallake ba. BABBAR MAGANA MAI GIRKA ABINCI DABAN WAƳAN DA HUKUNCI KE SHAFA SU MA DABAN, KENAN KO MAI KANKANTAR SA HANNUN DA MUTUN YAKE DA SHI A WAJEN YI WA LION KUSKURE YA SHIGA UKU TAB ƊI JAM!!!.

Hawaye ta fara yi tare da fara ɗaukar attarugun tana kai wa bakinta, har ga Allah ita ma ba ma abociya cin yaji bane, bata ci ko kaɗan a baya, ɗan zamanta a gidansu Kausar ne ma ta ɗan koyi cin yajin, kunsan Yarabawa da shegen son yaji kamar me, to a nan ta ɗan koya, amma a gida wajen mummynta, bata ci, mummy ma bata ci ne yasa bata sanya masu a cikin abincin, yau ta ga tashin hankali iya ganin idon ta.

Kwara ɗaya ta ci harshenta ya ɗaye ya yi jawur kamar wuta, kai gaskiya punishment ɗin soja Bala'i ne, shi saboda sun wahala wajen horo, sai ya rinƙa ganin kamar kowa ma irin sane, sai ya rinƙa ganin kamar komai ya yi wa fararen kaya daidai ne, saboda shi already ya hororu, abin da bata sani ba, duk abin da kake yi, zakaga kowa ma tamkar haka take yi, walau mai kyau walau mara kyau, shiyasa idan sojoji suna hukunta mutun, zaka samu hukuncin na da bala'in tsauri fiye da tunanin mai tunani, su kuma normal ne a wajensu.

Tana hawaye ta ɗauko na biyu, ga shi har guda goma ne a cikin bowl ɗin, alama ya yi mata da hannunsa ba tare da ya kalleta ba, akan ta ɗebo ruwan tea nasu mai jafi ta rinƙa korawa da shi, TASHIN SENSE bala'i kan bala'i kenan, zafi kan zafi, ruwan zafi haɗe da attarugu, eyya i pity you RIMSHA, Lion ya kware wajen horarwar mugunta, ba kalar da bai iya ba, attarugun ita kaɗan ta ma yaya bare kuma da ruwan zafi, ya ilahi ya lillahi.........😭

Haka ta ɗebo ruwan tea ɗin, ga shi ya haɗu mata da bata son green tea ɗin nan nasu, wlh yarinyar nan ta yi kuka ne har idanunta suka kumbura, shi kuwa tamkar babu shi a cikin ɗakin, Areef Imran suna Palo, kuma shi Areef ya san me yake faru, abin da yasa bai tinkari Lion ɗin ba, yasan idan ya je ba ƙaramin faɗa za su yi ba, saboda Lion ɗin yana jin yunwa sosai, yana son cin abinci ya yi barci saboda ya gaji, sun ɓata mashi rai sosai, a yadda yake nan babu uban da ya isa ya kwaci Rimsha da Mark a hannunsa har sai sun lashe hukuncin nan tas, to yasan idan ya je fa ba ƙaramin faɗa za su yi ba yau, to wai ita Rimsha me laifinta ne? Dan kawai ta kai mashi abin? Ita ta girka ne? Ita da kitchen ɗin ma bata shiga har sai idan zata je ɗaukar abinci, amma saboda bakar zuciya na fitar hankali shi ne har da haɗawa da ita.

Allah sarki duk wanda ya kalleta a halin da take ciki sai ya matsa mata kwallah, lips nata sun tashi daga pink sun yi jawur tamkar nasa lips ɗin, kamar ta sanya masu jan lips stick, sai hawaye take yi, ta kasa sakin kuka mai sauti saboda kada ya ji, idan ya ji zai kara mata wani hukuncin, baiwar Allah idanunta sun yi hawur sun yi luhu luhu.

Haka ta cinye attarugun nan tas, hawayene majina ne duk sun haɗe mata waje guda, da dama ma ina ga hawayen jini zata yi. Hijabinta ta kamo bayan ta gama cinyewa, ta shiga goge hawayen nata tare da majinar tana mai dana sanin zuwanta gidan nan ma baki ɗaya, wani irin azababben ciwo kirji ne ya dira mata lokaci guda, ga attarugun da shegen bala'in zafi, ga su manya ba halin ta haɗiye bata tauna ba, dole haka ta taunesu.

Duk abin da take yi yana same da ita, sai dai kawai shi ya fi karfi ya ɗaga ido ya kalleta ne a nasa cewar, har yau bai san kamannin fuskarta ba, ɗazun da ya juyo ne ma da tana kallon shi to za su iya yin ido huɗu, dan ita ya fuskanta, amma kuma ta yi kasa sosai da kanta, lokacin da ta yi mashi ɓari da rana kenan, hakan yasa bai ma ga face nata ba ya wuce dressing room, so bai san kalar face na ta ba, amma kuma tabbas ya riƙe wadda ta kira shi da sunan GAR a gidansu Imran a lokacin da ya zo, kuma e lallai yana son sani wace ce wannan, sai dai kuma bai tambayi Imran ba, dan gani yake shirme ne, kuma a haka maganar ta tsaya mashi a rai, abin ne da mamaki yadda ta gane ainahin face na shi ba tare da face mask ba, da yanzu Rimsha zata maimaita wannan suna na GAR to tabbas zai gane ita ɗin ce, abin da yasa yanzu bai gane muryarta ba saboda a ranar yadda ta kira sunan GRA daban da yadda take magana, har wani lankwatsa ta yi wa sunan kamar a bakinta a ka halinci sunan nan ranar, so ita ce magana ɗaya da ta tsaya mashi a ransa tun da ya zo Nigeria, yana ganin shirme ne yasa bai tambayi Imran ba, amma ya kasa mancewa da shirmen kuma. TO FA......🤔

Umarni ya sake yi mata akan ta cinye abincin da ta zuba mashi a cikin plate ɗin, idan ta gama ta kwashi kayan abincin ta fitar mashi a ɗaki, ba musu ta fara cin abincin, tasan baya magana biyu, tana ci harshenta tamkar zai ɗaye saboda azabar zafi, ya yi wani jawur da shi kamar jini, azaban balai take yi mata, lips nata ma suka yi ja bare kuma harshe.

Allah ya rufa mata asiri ba dayawa sosai ta zuba mashi abincin ba, hakan yasa ta cinye da wuri, kwashe kayan abincin ta yi tare da nufar waje, har lokacin idanunta na zubar da kwallah sun ki tsayawa.

A palo ta isko su Imran kamar yadda ta tafi ta barsu, taki kallon in da suke bare su fahimci wani abin, shi kam Areef da ya san komai dan ya tambayi Mark da taren Spanish dan kada Imran ya ji, zuba mata idanu ya yi yana kallonta cike da tausayawa, Imran kuwa bai wani damu da ya kalleta ba, yana latsa waya, kafin ya ɗago kuma ta wuce izuwa palon kasa.

Babu kowa a kitchen ɗin, ga wani abinci kuma an ɗaura a saman wuta, ajiye kayan abincin ta yi, ta nufi fridge, a hanzarce ta fara dubawa ko zata sami Madara ta ruwa, ta ko yi Sa'a akwai, sauri sauri ta ɗauko kwara ɗaya, ga sanyi madarar, ta fasa tare da kafawa a ɗan bakinta ta fara kwankwaɗa, azaba tai azaba, bata san time da ta sha kwankwani biyu ba, jin motsin mutun ne yasa ta farga ma ashe gwangwani biyu ta sha.

Mark ne ya shigo cikin kitchen ɗin dan duba girkin da yake yi, idanun nan nasa sun yi jawur, da alama ya sha bakar azaba, kuma shi ma da alama ya ci attarugu over, lips nasa duk da suke jawur yau sun kara ja over, har wani kumbura suka yi, ko kallon in da take bai yi ba, ya wuce gaban gas, mamaki take yi, a ranta tana faɗin "Punishment da zai sanya wannan jibgegen Bature sojan idanunsa su yi ja haka ba karamin abu bane, lallai tabbas Lion ya kware wajen mugunta, fata ɗaya kawai mutun zai, shi ne kada Allah ya haɗa shi da mummunar rana ta haɗuwa da hukuncin Lion, Allah ya rinƙa haɗa shi da ɗayar fuskar Lion ɗin, wato ta adalci ba ta mugunta ba". To amin dai kam, idan ba haka ba, fuskar muguntan Lion ai ko makiyi ba zaka yi mashi wannan mummunar fata ta haɗuwa da face ɗin ba.

Goge hawayenta ta yi tare da wucewa ta fice daga kitchen ɗin, yau dai bata yi amai ba da ta ci abincin nasu, azababben raɗaɗin da harshenta yake yi mata ma, ai ya mantar da ita ta ci wani abu wai abinsu.

Bata bi ta kansu Imran ba, bedroom nata ta wuce, sauri sauri ta shige toilet, fuskarta ta fara wankewa fes, ta fito tare da canza kayan jikinta zuwa goguwar rigar Abaya launin Navy blue, ta yafo mayafin abayar a kanta, ta nufi Palo.

Still a in da ta barsu, a nan ta dawo ta same su, kusa da Imran ta zauna. Ɗan juyowa ya yi ya kalleta. "My first lady yau baki jin barci ne?" Shi ne abin da ya faɗa cikin harshen Hausa, ɗan kwantowa ta ɗan yi a kafaɗarsa, a shagwaɓe ta ce "Yaya Imran dan Allah yaushe zamu je gidan Bappa, wlh tun da naji daddy ya ce su Umaisha ƴan uwana ne ina matukar kaunar ganinsu, dan Allah ka kaina na ga ƴan uwana". Shiru ya yi yana tunani, yanzu ai ko uban Rimsha bai isa ya yi iko da ita ba, yanzu Lion ne sabon uban ta.....🤣

Shi maganar da ta yi ma ta tuna mashi da son tambayar Abbansa da yake yi akan me ya haɗa su faɗa da bappa Hosain, tun da dai sun ce shi bappa Hosain ɗin nasu faɗar daban ne dana su daddyn Jelly, ma'ana shi Daddyn Rimsha tun iyayensu na raye ya yi fushi ya bar gidan, su daddyn jelly kuma, sai bayan auren Abba da Hjy Umaiya, har ma an haifi Imran, sannan suka sami gagarumin matsala a tsakaninsu, amma fa kafin auren Hjy Umaiya ɗin ma akwai wata tangarɗa da suka samu na kin auren, abun dai ya haɗu ne kashi kashi sai ya tadda gaba guda ɗaya.

"Yaya Imran ka yi magana mana? Yaushe zaka kai Ni? Wlh ina bala'i kewar Aunty AKILA". Nishawa ya yi tare da sauƙe ajiyar zuciya. "Rimsha gobe zan kawo maki Akila gidan nan ku wuni, ita ma Umaisha zan samu lokaci na ɗauko maki ita, amma fita kam kema kinsan ba zai taɓa yiwu ba, yanzu kin zama sarauniya sai dai a kawo maki duk wanda ki ke da bukatar gani".

Narai narai ta yi da ido kamar zata yi kuka, shi dai Areef ya zuba masu idanu ne kawai tun da ba jin me suke faɗe yake yi ba, baya jin Hausa ko kaɗan, sai dai kawai ya yi ta binsu da idanu yana murmushi.

"Yaya Imran ya batun zuwa school fa?" Shafa kanta ya yi. "My Rimsha, na gaya maki babu uban da ya isa ya fitar dake daga cikin gidan nan sai idan shi ya bada dama, fitar ki ba zai yi wu ba har sai ya bar Naija, sun kusa komawa ai, na ji jiya yana magana da daddynsu akan maybe next week su shigo Usa ɗin, amma kafin ya koma ma, idan ya sauƙo yana iya barinki ki koma school, abin da nake so dake yanzu shi ne, ki natsu, ki natsu sosai, ki daina rawan kai, ki daina yi mashi laifi, wlh dannewa yake yi, idan kika bari Saif ya yi maki koda bari ɗaya ne, ina mai tabbatar maki sai kin kurmance, to dan haka ki kara natsuwa, ki bi komai a sannu dan ku rabu lafiya, idan ba haka ba kuma, wlh ina mai tabbatar maki zai iya tafiya dake kasarsu ki je kina yi mashi aiki, kuma babu wanda ya isa ya tinkare shi bare ma har ya yi gigin yi mashi maganar ya yi hakuri ya kyale ki, ko daddynki bai isa ba, idan kuka ce kun shigar da shi kara court, to fa court ɗin gabaɗaya ma zai iya ɗaukowa ya kawo maku gida, dan ku ji daɗin shari'ar da kyau, shiyasa kika ga daddynki bai ja da shi ba, saboda bashi da dukiya da kuma power iya ja da shi, to muda gabaɗaya kasarmu ma take a karkashin su, sufa suke juya mu, kinga kuwa ba mu isa ja da shi ba, to kawai shawarar da zan baki, ki natsu ki bi Saif a hankali ku rabu lafiya, Allah ya rabaku lafiya, tun da ya kusa komawa Alhadulillah zamu ce". Ya kai karshen maganar yana shafa kanta.

Shiru ta yi tana tunanin zalunci irin na Saif, mutun tamkar ba mutun ba? Kamar dutsene a jirjinsa, sai izzar bala'i, ka nuna isa a abin da take mallakinka har ma da wanda yake ba mallakin ka ba, wannan ai zalunci ne.

Ganin ta yi shiru ne yasa Areef ya ce "What are you thinking my sister? What prof told you that make you angry like this?".

Kai kallonta kanshi ta yi, tare da ƙaƙalo murmushi dole tana girgiza mashi kai alamar babu komai, da hannu ya yi mata alama akan ta zo, ba musu ta miƙe ta koma kusa da shi ta zauna.

Hannayenta ya riƙe a cikin nasa, cikin zolaya ya yi magana da harshen tunaranci. "What lion did to you ya sa ki angry haka?".

"Yaya Areef ni ai yaya Saif bai yi mani komai ba, kawai barci nake ji ne". Dawo da kallonsa kan Imran ya yi. "Prof ka koya mani wannan yaren naku, dan gaskiya ba zan yarda ba, kuna cutata da yawa, how zaku yi magana ban ji me kuka ce ba, a maganar taku kuma ka sanya sister ta ta ɓata rai, na tambaya kuma all of you kuna gaya mani ba komai ko?". Dariya ta yi mashi tana mai buga hammar barci.

"Serious Areef ba wani magana muka yi ba, ta ce mani ne tana son komawa school, shi ne na ce mata ta yi hakuri Saif ya kusa komawa, idan ya koma shikenan sai ta koma school ɗin". Girgiza kai ya yi, yana mai matukar tausayawa Rimsha, domin kuwa, Lion ba next week zai koma ba, wata aiki ma yake yi a Nigeria, aikin kuma ya shafi Musharraf and gwamnatin Nigeria, albarkacin farincikin da Musharraf yake sanya Aseef yasa Saif kwana biyu da suka wuce ya fara bincike akan tun ainahi menene ya faru da har yarabasu da family'nsa haka, menene ya raba kansu da har yake tunanin family'nsa sun rasu, mutumin kirki kamar haka.

A ka'ida irin ta aikin Lion idan zai yi aiki baya tambayar abun da ya faru, dan yasan kowa kansa kawai ya sani, da wuya mutun ya faɗi gaskiyar komai da ya faru, bare ma kuma idan mutun ya yi laifi, to zai yi kokarin ɓoye laifin nasa ne ya bayyana na abokin faɗar nasa, hakan yasa ma baya tambaya, bincikensa kawai yake yi, da kansa yake gano gaskiyar ko wace ɓangaren, ya kuma yanke hukunci da ta dace da ko wace ɓangaren, ɗazun da yamma da suka zauna da Rimsha, ya so tambayarta went last ta rabu da su mummynta, sai kuma ya fasa, dan ya fuskanci kan Rimsha na rawa sosai, shi kuma baya son mutun haka, ba ya zama inuwa ɗaya da mutun mara natsuwa, idan bata gyara ba 1 day 1 time zai yi wurgi da ita waje kawai kowa ya huta.

Shi Areef ɗin abin da ya sanya ya gane Saif ya fara bincike a kan case ɗin Musharraf ɗin, jiya ne da ya shiga bedroom ɗin na ɗan uwan nasa, a nan ne ya gani cikin laptop nasa, ya sha mamaki shi ne ya fara binciken tun yaushe Lion ɗin ya fara aikin, sai ya ga ma kwana ɗaya ne da ta wuce, ba wani jimawa bane, sai dai kuma Areef ya sa a ransa Lion zai barta ta cigaba da zuwa school, bari dai su samu ya ɗan sauƙo, idan baku manta ba, Lion yana son karatu, yana son yaga kowa yana karatu, baya son jama'a su zauna a cikin duhun jahilci, so da wuya idan zai hanata zuwa school.

Shiru suka yi kowa da abin da yake tunani, suna a haka har Mark ya kammala girki, ya zo ya sanar da Areef ya gama girkin oga, bayan ya gaya masu kuma ya koma kan punishment da Lion ya bashi, yau kwana zai yi a waje, Allah sarki, shima bada son shi bane hakan ta faru, bai so ba, bai ma san ya akayi ya sanya yaji a abincin ba, tun da suke yau shekara almost 10 kenan suna tare, bai taɓa yin kuskure maka mancin haka ba, sai yau, amma Lion bai yi mashi afuwa ba, domin a tsarin Lion babu kuskure sai dai ganganci. TAB DA ALAMA AKWAI ABUBUWA DA DAMA DA ZA'A KAMA LION DA SHI, BAI YARDA AKWAI RAUNI A DUNIYA BA, HAKA BAI YARDA DA KUSKURE BA SAI DAI GANGANCI, BAYA SON YARA BARE SHI YA HAIHU, BAYA SON KALMAR SO, KAI SHI DUK WATA ABIN ARZIKI BAYA SO, A LALLAI DA AKWAI BABBAR RINA A KABA.......🤔

Rimsha dai bata so ba, amma haka ta miƙe ta nufi palon kasa, babu kowa a kitchen ɗin, wanke hannunta ta yi before ta ɗauki abincin.

Kamar yadda ta saba, da sallama ta shigo cikin ɗakin, bawan Allah ya yi barci da yunwa, dama barci yake ji tun ɗazun, da alama kuma barcin ɗaukarsa ta yi ba tare da ya shirya ba, ga wayarsa a hannunsa da alama latsawa yake yi barcin ta zo.

In da ta saba ajiye mashi abincin, a nan ta ajiye mashi, ta juya ta nufi hanyar fita. Har ta kai tsakiyar ɗakin sai kuma ta nuyo dan ta sake kallon shi, nan take ta ji zuciyarta na ingizata akan ta zo ta rufa mashi bargo ta kashe mashi wutar ɗakin, ta kuma zame wayar nan nasa da ya riƙe ta ajiye mashi a saman bedside drawer.

Readers Also Read