Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 91
Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 91: Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 91. Ɗaukarta ya yi cancak suka nufi saman bed…
3,359 words
Ɗaukarta ya yi cancak suka nufi saman bed yana tambayarta menene ya sameta. "Yaya Saif to ba kai ne ba?". Tsareta ya yi da idanu ba tare da ya sake yin magana ba. "Na ce maka ni bana son Mark ya rinƙa kawo mana abinci, zan je in rinƙa ɗaukowa, amma shi ne ka bari yanzu ma ya shigo mana da abincin, kuma ka ce ya zo ya kwashe kayan abinci, shiyasa na yi fushi kuma ba zan ci abincin ba". A tsananin shagwaɓe ta yi maganar, yanda ta yi maganar kuma dole shi ne ya amsa mata da okey ba dan ya so ba, saboda ta saukar mishi da kasala, ta sanya shi shiga cikin yanayi, ta rikita mishi kwakwalwa da shagwaɓar tata, uwa uba da ta kai karshen maganar sai da ta sanya ɗan bakinta a saman kumatunsa ta ɗan ciza dan ta huce haushi, hakan da ta yi ba ƙaramin kara birkita mishi lissafin ƙwaƙwalwa ta yi ba.
Saman bed ɗin ya sauketa tare da nufar toilet yana faɗin, to ta je ta ci abinci, Mark ba zai sake shigowa ba, shi zai ɗauko abincin da kansa tun da haka take so. Sosai ta ji daɗi, shi dai Lion akwai tsananin kishi, ba zai iya barinta ta fita ta keta cikin sojojin nan ta shiga kitchen wajen Mark ta ɗauki abinci ba, gara mishi Mark ɗin ya kawo mishi abincin kofar bedroom nasu shi ya fita ya karɓar, e lallai Rimsha ta ciri tuta ko a iya haka, dalilinta ne yau zai rinƙa karɓo musu abinci da kansa?!! Abin da mamaki, kishi dai yau ta yi amfani.
Wanka ya yi ya shirya cikin kayan barci ya zo ya kwanta tare da jawo wayarsa yana tunanin me zai hana ya fara bincike a kan Josephine yanzu tun da baya aikin komai?. Ita kuma abincin ta ci ta gama, sannan ta wuce toilet ta yi wanka tare da yin shirin barci sannan ta hau saman sofa ta kwanta sai zuba kamshi take yi, ga kayan barcin nata ma wasu irin kaya ne wanda suke ƴan sharara sharara marasa nauyi, riga ce mai ƙaramar hannu kamar na vest, sai dogon wando har kasa.
Har ta kwnata ta sake miƙewa ta feshe musu cikin bedroom ɗin nasu da air freshener mai bala'in daɗin kamshi wanda Lion ya ɗauko musu, bayan ta kammala ta zo ta kwanta a saman sofa, shi kuma Brady yana wajen Mark, dama shi yawonsa yake tafiya sai lokacin da ya ga dama yake shigowa, yau kam ma da gangan Mark ɗin ya rike shi su yi hira tare, dan yau ba'a gida suke ba, babu su Tyrone, ba abokan hira, shi ne ya rike Bradyn dan ya rage mishi kewa.
Yana ƙoƙarin miƙewa ya ɗauko laptop nasa dan ya fara bincikar tsakanin daddynsa da Josephine wai waye ne mai gaskiya a cikinsu? Wannan abin ya fara damun shi sosai gaskiya, yana da bukatar sanin gaskiya a yanzu kam. Bai kai ga miƙewa ba Malika ta fito a siffar dodo ta tsorata Rimshar, tana tsaka da tunanin Lion ɗinta kawai taga abu ya fito kamar wani shaiɗani ga kawo ɗaya a tsakiyar kai, idanu kamar zasu zazzago waje, wani mahaukacin ihu ta kurma tare da mikewa a guje ta nufi saman gadon, ta san dai duk wani bala'in da ya ta so Lion ɗinta ne kawai zai iya tare mata, shiyasa shi kaɗai take nufa idan wani abin ya taso.
Yana ƙoƙarin miƙewa ta haye jikinsa tana ihu, shi kuma bawan Allah bai ga komai ba, dan Malika wa iya Rimshar kawai ya fitowa, da yake tasan ba zasu ji ta ba, sai ta yi dariya tana faɗin "Ƴar kaniya kawai, zaki wani zo ki kwanta a saman sofa ki bar mana angon mu shi kaɗai a saman gado, wato baki ji nasihar Akila ba kenan? Mu samu da kyar mun tayaki yaki a kan soyayyar taki ne har kika samu nasara shi ne kike kokarin watsa mana kasa a idanu ki ruguje komai ta hanyar yin nesa da shi ko? To mu zuba da ni da ke ƴar nema". Ta kai karshen maganar tare da kwashewa da dariya sannan ta ɓace ɓat kamar wata walkiya.
Ita kuwa Rimsha ta kankame shi sosai tamkar zata koma cikin jikinsa, sai ihu take kurmawa kamar ba lafiya ba, su kansu sojojin Lion ɗin sai da suka yi mamakin irin ihun da take yi, yarinya kamar kanta akwai motsi, basu san cewa Malika ce ke yi mata tsiya wani lokacin ba, ta razanata tasa ana yi mata kallon mahaukaciya ko tana da matsala a kwakwalwa.
Ganin yanda jikinta yake kerma sosai ga kuma kuka da take yi ne yasa ya ɗago kai dan ya ga ko dai Brady ne ya tsoratata, bawan Allah shi bai ga komai ba, ɗago haɓarta ya yi dan ya rarrasheta ta yi shiru ta gaya mishi menene, amma ina ta ki yin shiru, dan fa ba karya ta tsorata iya tsorata, irin wannan halitta da daddare haka ya fito maka ba tare da ka shriya ba, dole kwakwalwa ta juye.
Sai ambatar sunanta Meesha yake yi, amma ina sam bata jin shi, sai ihu sosai take yi, hakan yasa ya haɗe bakinsa da nata dan ya sata ta yi shiru, kara kankame shi ta yi tana jan numfashi da kyar da kyar. Sai da ya tabbatar da ta sami natsuwa ta yi shiru sannan ya saketa yana mai ɗago haɓarta, ta runtse idanu gam hawaye na zuba daga idanun nata.
"Meesha why are you crying?" Cikin kuka murya a dashe ta fara magana da kyar da kyar "Yaya Saif dodo na gani fa". Sake ɗago idanu ya yi yana bin ɗakin da kallo, ganin ba komai ne yasa ya fara tofa mata addua'o'i kawai, dan a tunaninsa tsorata ta yi, dama ya san ta da shegen tsoro, ga shi kuma ta ga a cikin ruwa suke, kila ta fara barci ne ta yi mafarkin sun nitse cikin ruwa, shi ne ta farka take yi mishi ihu wai dodo ta gani, ko a ina taga dodon ƴar rigima kawai, haka yake ta tunani a ransa.
Yana tofa mata addu'a yana shafa bayanta a hankali hankali alamar ta yi barci to.
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥
KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔 ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne.
KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA, INFECTION KILLER, COLACCA, SAI KAYAN GYARA PAGE. KACA KACA. YALLAGWADA. JIGIDA. RUWA RUWA. BANI BANI. WOMEN JELL BATA BATA. DAFIN KAXA. TANTABARA. XABUWA. CICCIƁI. AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER 09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH, BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI.
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️
👊FATEEMA ZAHRA MUSA (PRINCESS TEEMA OR STAR LADY)✊
*Domin samun karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 09162620621*
73-74
Yana tofa mata addu'a yana shafa bayanta a hankali hankali alamar ta yi barci to. Cikin ɗan ƙanƙacin lokaci ta samu natsuwa sosai saboda karfin addu'a, sai sauke ajiyar zuciya take yi tana jan hanci, ta ci kuka ba karya.
Jin ta samu natsuwa ta kara lafewa a jikin nasa tamkar mai jin barci ne yasa ya ɗan rankwafo da kansa a kanta tare da dakatawa daga addu'ar da yake tofa mata. Can kasan maƙoshinsa tamkar mai raɗa ya furta "Meesha". Ɗan ɗago kanta ta yi tana kallon lallausan laɓɓansa, ta kasa kallon cikin kwayar idanunsa, "Are you okey now?". Jinjina mishi kai ta yi tana faɗin "Yes am okey, amma kuma ina jin sanyi sosai yaya Saif". Kallon yanda take aiki tura ɗan bakin nata ya yi. "Meyasa kika cike tsoro har haka ne?".
A shagwaɓe ta ce "Ni fa yaya Saif ba tsoro nake ji ba, da gaske ne naga dodo irin wanda gwaggo take bamu labarin shi a tatsuniya". Sam bai gane in da zancen nata ya dosa ba, wai ana basu labari a tatsuniya, kai Rimsha duniya. Canza topic ɗin maganar ya yi da cewa "Anywhere, yanzu dai a duk lokacin da kika tsorata, ki kasance sunan Allah shi ne abu na farko da zaki fara ambata ba ihu ba, idan kina ihu a duk lokacin da kika tsorata hakan zai bawa shaiɗanun aljanun dake kawaye da ke su iya shiga jikinki har su cutar dake, so be careful". "Tom yaya Saif zan kiyaye". Ya ji daɗin amsar da ta bashi, bata yi ƙoƙarin kare kanta ta hanyar yi mishi musu ko wani abin ba, yasan ita mai addini ce, yasan ta tsorata sosai ne da har ta manta bata furta sunan Allah, amma sam bata yi ƙoƙarin gaya mishi ta tsorata ne yasa ta kiɗime bata yi hakan ba, sai kawai ta amsa mishi da to zata gyara, ya ji mugun daɗi, dayawa daga jikin maza haka suke, sun san komai, amma zasu rufe idanu suyi ta faɗa a kan abin da suka san bake kika yi shi ba, idan baki yi masu musu ba, kika basu hakuri, wlh ba ƙaramin daɗi suke ji ba, zai wuni a cikin zuciyarsa yana sanya miki Albarka, idan kuwa kika yi ƙoƙarin kare kanki dan ki gaya mishi gaskiya, to zaku yi faɗa ne a banza dan ba zai karɓi kuskurensa a wannan lokaci ba, so yana da kyau mata ku lura a kan hakan, ba ko wani lokaci zaku yi musu da su wajen sawa su gane baku da laifi ba, sun san komai, wannan hallitta ce da Allah ya yi musu na ba zasu nuna sun sani ɗin ba, zasu ga kamar idan suka yi hakan zaki renasu ko makamancin haka, ya kamata mata mu waye a kan karatun maza, mu karancesu tsab.
"Why are you always looking my lips?". Ya tambayeta yana ɗauko wayarsa da ta yi ƴar kara alamar shigowar saƙo. Massage ne da ɓoyayyiyar number, gargaɗi ake yi mishi da babbar murya a kan kada ya yarda ya tonowa kansa abin da zai bin ne kansa da kansa, guntun tsaki ya ja tare da goge saƙon ya ajiye wayar a ransa yana faɗin Wai su kam basu sam shi abin da ba'a so shi yake aikatawa ba ne? To wlh sai ya yi bincike ya gano wasu kungiyar matsafa ne Josephine take ciki, yana da yakinin sune suka turo mishi wannan shirmen banzan da wofin, sun ja ma ya ji yana bala'in kaunar binciken yanzu, kuma sai ya yi idan sun isa kada su bari ya kwana yau, iskancin kawai, har shi za'ayiwa barazana, to wlh sun ma taɓowa kansu ne, sai ya yi abin da basu taɓa zato ba, amma ya ɗan yi mamakin a in suka samu numbersa, sai dai bai damu ba dan yasan number Nigeria ne, da numbersa na Usa ne wlh wane kaniyarsu su iya turo mishi saƙo kuma har ta shigo, ba zata shiga ba ko sun tura, dan ba kowani shirme yake shiga wayarsa ba.
Yana tunani yana shafa bayan matar tasa yana jiran ta bashi amsar meyasa take yawan kalle mishi lips. "Allah yaya Saif lips ɗin naka ne suna yi mini kyau". "Serious?" Ya yi maganar yana ɗaga gera ɗaya, tamkar walkiya ta ga ɗaga gerar tasa, dan ta wutsiyar idanunta ta ga hakan, cikin sauri ta ɗago da kallonta zuwa saman face nasa da kyau, dan ta tabbatarwa da kanta da gaske gera ɗaya ya ɗaga irin na Areef ne?.
Tana ɗago idanu ya sake ɗaga mata gera ɗaya ba tare da ya yi magana ba, ba ƙaramin ruwan mamaki ta sha ba, wato shi ma ya iya ɗaga gera guda kenan? Lallaima yaya Saif ɗin nan, wato dai babu abin da bai iya ba shi ma, kawai yi ne ba zai yi ba, amma yanzu ga shi da lokacin yi ɗin ya yi ai yana yi.
Number Sultan ya kira dan ya gaya mishi su fara sauke mishi Alqur'ani mai girma dan zai sake komawa wannan shegen case ɗin na matsafa, a ko da yaushe shiyasa Lion yake nasara a rayuwarsa, ga shi dai shi Bature ne kuma krista ne ya musulunta, amma duk abin da zai yi Allah yake fara sakowa a gabansa kafin komai, Allah kaɗai yake kaiwa kukansa, baya tsoron wani mahaluki a duniyar nan, baya shakkar kowa. Sai dai fa abin mamakin duk da wannan abin da ya faru sun fi jin Josephine ɗin a ransu sama da daddy, sun rasa meyasa suka fi kaunarta.
Bugu ɗaya Sultan ya ɗauka, cikin sanyin murya suka gaisa, sannan ya gaya mishi buƙatarsa, shiru Sultan ɗin ya ɗan yi kafin ya ce mishi "Amma Saif da ka bari sai ka koma tukun nan, akwai haɗari sosai, saboda kaga in da ka nufa yanzu waje ne mai haɗari, sannan tafiya kake yi a cikin ruwa, kasan kuma a cikin ruwan nan babu abin da babu, akwai shaiɗanun aljanu sosai, kuma aiki ne da ya shafi tsafi da shaiɗanun aljanu, ni dai a nawa shawarar zan so ka bari sai ka fita daga cikin ruwan nan, ka koma gida lafiya lou, sai mu ɗaura ko?". Kallon Rimsha dake ta faman kallosna ya yi yana tunanin wannan ƴar rigimar tasa ma ba zata iya ɗaukar wannan kasada ba, tana jin motsi zata zunduma mishi ihu ta hana shi yin aiki, so Sultan yana da gaskiya, ko dan ma Rimsha zai hakura sai ya koma ɗin, kuma yana ganin girman Sultan sosai, dattijo ne sosai wanda a kallah zai iya kai shekaru 60 zuwa 70, sai mai taimakinsa wato ladan ɗinsa wanda sunansu iri ɗaya da Sultan ɗin, shi ma baban mutun ne, so ba karya Lion yana ganin mutuncin Sultan tun lokacin da ya musulta.
Hakan ta sa ya ce "Okey uncle i will think about it". Addua'o'i sosai kamar yanda ya saba Sultan ɗin ya yi mishi, shiru ya yi yana sauraron addua'o'i suna ratsa shi tare da sanyaya mishi zuciya, har sai da ya kai karshe sannan ya amsa mishi da Amin uncle......... Ai ko dan addua'o'i da Sultan yake zuba mishi ma dole zuciyarsa ta yi ta sanyi tana rage zafi, dole ya sauƙo, ai addu'ar manyan malamai ba wasa ba. Karin wata haske na abin da baku sani ba, perfume ɗin Lion Sultan yake haɗa mishi ita, shiyasa basu shiri da duk wani shaiɗanin aljani, basu haɗuwa waje guda, to Sultan yake haɗa mishi ita haɗi na musamman, shi ya zaɓi irin kamshin da yake so, sannan Sultan yake tofe mishi ita da addua'o'i masu karfin gaske kafin ya bashi, ainahin turaren daga Dubai yake sayosu ya kawowa Sultan ɗin, idan ya gama haɗa mishi su sai ya kira shi a waya a kan ya aiko a ɗauka mishi, to kun ji tushen perfume ɗin nan, duk wani shaiɗanin aljani ba zai taɓa zama kusa da wannan perfume ɗin ba, ko aljanune a jikinka in dai masu cutarwa ne shaiɗanu da an shaka maka zasu gudu.
Da haka suka yi sallama ya ajiye wayar yana mai dawo da kallonsa a kanta, cikin sauri ta runtse idanu tana murmushi, ba ƙaramin kyau ta yi ba, hannunta ya riko cikin nasa yana kallon ƴan yatsun nata, tunanin maganarta na ɗazun ne ya faɗo mishi a ransa, a in da take cewa yaya Saif lokacin fa da aka yi mini wannan zanen ina yarinya ce, tunani ya yi wato ita yanzu ji take yi ta girma kenan ko? Wai da tana yarinya, kai wannan ƴar rigimar tasa akwai ta da iya magana da son girman, yanzu ma bata wuce a goyata ba wai da tana yarinya yanzu ta girma tab su babba manya.
"Yaya Saif nace maka sanyi fa nake ji?". Ta yi maganar a shagwaɓe sosai, shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Har a jikin nawa da kike kwance ma?". Jinjina mishi kai ta yi alamar e tana faɗin "To ai yaya Saif kai ma kayan narci ne a jikinka ba jacket ba, shiyasa nake jin sanyi, da Jacket ne zan shiga ciki ba zan ji sanyi ba". Shiru ya yi bai yi magana ba sai dai ya gyara kwanciyarsa da ita a jikin nasa tare da ja musu bargo zuwa wuyanta shi kuma karjinsa.
Tamkar mai yi mata raɗa ya furta "To sauka mini a jikina". Make kafaɗa ta yi tana faɗin "Ni a'a gaskiya, ina tsoron dodan can Allah, haka kawai na sauka ya kamani, gara mini dai jikin naka duk wuya". Yanda take magana ba ƙaramin gigita shi ta yi ba, zuro hannunsa waje ya yi daga ta cikin bargon ya kashe wutar ɗakin ta hanyar yin amfani da remote dake saman bedside drawer, sannan ya kunna green light dake manne a sama kusa da farin wutar.
"Yaya Saif in tambayeka?". Shiru ya yi bai amsa mata ba, dan sam baya jin yin magana. "Uhm uhm yaya Saif ka amsa mini mana". Yatsarsa manuniya ya sanya mata a cikin ɗan bakin nata yana wasa da harshenta dan ta dai'na damun shi da surutu, tsotsar yatsan nasa ta fara yi tana ɗan cizawa, kwace kayansa ya yi dan kada ta jefa shi cikin wani hali, kukan shagwaɓa ta saka mishi mara dalili.
Shiru ya ɗan yi na ƴan mintocin da ba su wuce 2 ba, kafin nan ya ɗan juya kaɗan da ita a in da ya sauketa daga saman kirjin nasa ya zamana suna fuskantar juna, matso da face nasa daf da tata ya yi yana yi mata wani irin mayen kallon, da yake darene sai idanun nasa suka kara haske, ga kuma hasken green light na ɗakin. Cikin sauri ta runtse idanunta dan ba zata iya gani shi ba.
Haɗe fuskokinsu ya yi waje guda yana mai lumshe idanunsa shi ma, a hankali ya fitar da harshensa izuwa saman lallausan laɓɓanta na kasa yana ɗan tattaɓa lips ɗin nata, wani irin yanayi ta shiga, buɗe ɗan bakin nata ta yi da nufin ta kama harshen nasa, janyewa baya ya yi yaki bata, idanunta a datse gam ta turo mishi ɗan bakin alamar shagwaɓa, bata ji daɗi ba da yaki bata.
Sake zuro harshen nasa ya yi zuwa saman lips ɗin nata, a hankali yake ɗan wasa da harshen a saman lips ɗin ba tare da ya kai cikin bakinta ba, sake kokarin kama harshen nasa ta yi, ina nan ma janyewa baya ya yi bai bari ta kama ba, kukan shagwaɓa ta saka mishi tana ɗan bubbuga kirjinsa, sam bai kulata ba a karo na uku ma ya sake zuro harshen nasa zuwa saman lips ɗinta, a wannan karon ta ci alwashin sai ta kama harshen, ƙoƙarin kamawa ta yi yana ɗan janyewa kaɗan kaɗan yana janta da wayo har ta matso kusa da shi sosai, a in da ya ɗaga kai daga rankwafowa da ya yi a kanta, ya zamana yana miƙe.
Kuka ta saka mishi tana kokarin barin jikin nasa, rikota ya yi tare da zura harshen nasa cikin ɗan bakin nata yana tsotar lips nata na kasa, nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke tare da cizan harshen nasa dan ta huce takaicin wasa da hankalin da ya yi mata, bai san time da ya furta wash ba jin yanda ta cije shi, zame harshen nasa ya yi tare da kara mannata sosai da jikinsa yana shafa bayanta, har cikin ransa yake jin irin sokinsa da breast nata suke yi a kirjinsa, a da ya rainasu sosai, yanzu kuwa ga shi suna tsokale mishi zuciya, musamman ma idan ya matseta sosai a jikin nasa, shi kaɗai yasan me yake ji, dama kun sani ita ba saka breziya take yi ba, to yau ko vest ɗin ma bata saka ba dan kayan barci ne a jikinta.