Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 96
Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 96: Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 96. Ya fahimci in da zancen nata ya dosa, dan…
3,356 words
Ya fahimci in da zancen nata ya dosa, dan haka sai ya yi mata yanda zata gane, ya ce mata Areef ba zai taɓa yin abin da bai da ce ba, ba zai taɓa sakata ta kauce hanyar Allah ba, shi mutun ne ma da idan ya ga zata kauce hanyar Allah zai tsawatar mata idan ta kama ma zai haɗa mata da duka, dan haka kada ta damu ta yi duk abin da ya ce kawai ba tare da ɗarɗar ko shakka ba.
Shi dai Areef bawan Allah sam baya jin Hausa bayan waƴan can kalmomi, dan haka sai ya zuba musu idanu yana kallon ikon Allah, sai magana daddy yake yi, shi gani ma yake yi kamar basu san me suke faɗe ba, abinku da ba yaren shi ba.
Sai da daddy ya gama yi mata faɗa tsab sannan ya yi musu addu'a da fatan alkhari daga nan suka fito, tana gaba yana binta a baya, sam taki yarda ta jera da shi.
Bedroom ɗin Aseef ya nufa, bayin Allah har lokacin barci suke zubawa, daga shi har Akilar tasa ba wanda ya motsa daga cikinsu, sun ci wahala kamar ba gobe. Saman bed ɗin nasu ya hau a in da ya tofa musu addua'o'i sosai da sosai, ita kuma tana tsaye a gefe tana kallon shi da mamaki, sai yanzu ne ta gasgata zancen daddynta da yake yawan cewa Areef ba zai cutar dake ba, ashe bawan Allah ne, yana da addini sosai, da a ɗan iska take ɗaukarsa, bata san shi kam na kwarai ne da samun irin shi ma akwai wahala ba, mai zuciyar zinari.
Sai da ya kammala ne ya sauko tare da riko hannunta yana faɗin "Gaskiya yanzu kam a tare zamu jera, ai haka boyfriend and girlfriend suke yi, suna tafiya suna zuba love, to kema haka zaki rinƙa yi mini kin ji ko?". Gyaɗa mishi kai ta yi ba tare da ta yi magana ba.
Wucewa suka yi waje har wajen mota, gidan gaba ta shiga shi ma mazaunin driver ya zauna, sun yi matukar kyau over abinsu. Kunna motar ya yi suka bar gidan, ta yi shiru tana tunanin duniya, yau Adiva da Maryam kawai take tunani, tunaninta ɗaya lokaci ya yi da ya kamata ta san abin yi dan wargaza gidan Hjyr daɗi, to amma waye take da shi wanda zai tallafa mata a duniyarnan? Sam ko daddynta bata son gayawa, dan a cewarta bata son ta sake jefa shi cikin bala'i, a bayama lokacin da yake da kuɗi yake harin mulkar kasan ma dan ya yi takun saka da su Abubakar jaja shi ne aka ne mi ɓatar da shi da kuma shafe babinsa bakiɗaya, bare yanzu kuma da komai nasa ya ruguje babu hukuma a hannunsa babu komai, idan ta gaya mishi ma wlh zata sa ransa ne kawai ya ɓaci a banza kuma babu yanda zai yi, domin kuwa gidan Hjyr daɗi dai su Abubakar jaja ne suka kafa, to a karo na biyu bata son daddynta ya sake shiga bala'in su, kuma tana da gaskiya aka ce idan maciji ya sareka, to ko igiya ka gani dole ka tsorata, kada ku manta shi Farooq yana raye, so tana tsoron sake jefa daddynta cikin bala'i, shi ne yasa ta kasa gaya mishi, a hakan ma bata san cewa ba iya takarar siyasa ce kawai tasa Abubakar jaja ya yi niyar shafe daddynta a doron duniya ba, akwai tsama a tsakaninsu na kamasu da daddy ya yi suna safaran mata da kananan yara, suna fitar da yara waje ba da izinin iyayensu ba, a sayar musu da koda, sai su zaɓi matasanmu masu jini a jika, waƴan da suke fama da talauci suna neman abin da zasu ci a fujajan, talakawa waƴan da basu da ilimi basu san darajar kodarsu ba, su yaudaresu da sunan zasu basu kuɗi gida da sauransu, su fitar da yara waje a je a cire musu koda ɗaya, sannan suna safarar mata su fitar da su kasashen Turawa su kai su gidan karuwai su karɓi kuɗi, su yaudaresu da sunan aiki, kuma duk mafiya yawan aiki Hjyr daɗi take gudanar da shi, zata yi shiga ta mutunci ta je ta yaudari mata da sunan aiki, daga kin yarda shikenan sai idan Allah ya ƙaddara zaki dawo lafiya, wata ma sai ta kamu da cuta suke kwasota su dawo da ita, kananan yara suna yi musu alluran shakafashe su sanyasu karuwanci, ga safarar kayan maye su shigo da shi ta ɓarauniyar hanya, haka zalika suna shigo da mugayen makamai ta ɓarauniyar hanya su sayarwa ƴan ta'adda ayi ta kashe talakawa, so daddy ya taɓa kamasu a kan wannan aiki, a lokacin kuma kowa shi yake so, shi za'a zaɓa, ya ci alwashin idan har ya hau mulki wlh sai ya tarwatsasu, ba yanda Abubakar ɗin bai yi ba a kan daddyn ya dawo cikinsu, amma sam ya kafe yaki yarda, ya ce shi talakawa zai yi wa aiki kuma sai ya tarwatsa azzalumai da yardan Allah, kuma sun san batun zaɓe shi zai ci, sun kuma san shi da zuciya idan ya ce zai yi abu to fa sai ya yi, tabbas sai ya wargazasu, hakan tasa suka nemi ɓatar da shi su shafe babinsa baki ɗaya a duniya, amma da yake Allah ba azzalumin bawansa ba ne, komai daren daɗewa zalunci bata tabbata sai ta ruguje, sai Allah yasa Jehan ce ma ta zama sanadiyar mutuwar Abubakar ɗin wanda ko a mafarki ya yi mafarkin ƴar Nawazudden ce zata kashe shi idan ya farka sai ya yi ta dariya dan ba zai yarda ba, sun yi niyar kashe Nawazudden lokacin da uncle Shitu ya biyosu, da gindin bindiga suka daki uncle Shitun a kai sanadiyar haka kansa ya fashe, shi ma sun so kashe shi, amma Allah bai yi ba ya kuɓuta da kyar, ya juya kan motarsa ya samu ya gudu, Allah ya yi yana da rabon shan ruwa a gaba shi ma, a dai'dai lokacin ne kuma daddy ya yi wa mummy massage a kan su gudu dan ba sojoji ba ne suka kama shi, abokan hamaiya ne, mum tana cikin ruɗu bata ga saƙon ba har sai da suka bar Abujan.
Kafin su yi yunkurin kashe daddyn sai da Abubakar jajan ya zo har gabansa ya sake yi mishi ta yi na shiga cikinsu a karo na karshe, nan ma saboda karfin zuciya irin na daddyn da karfin imani ya riki Allah yana ganin mutuwa amma ya ce shi ba zai yarda ba, shi gaskiya kawai ya riƙe, ya riki Allah kuma ba zai ci amanar talakawa ba, hakan tasa Abubakar ɗin ya ce a kashe shi kuma a kashe family'nsa, dan idan familynsa suna raye ya san su sarai gwaggo ba zata taɓa yarda ba, ko an kawo gawarsa zasu shigar da kara kuma dama kunsan gwaggon Jehan da iya faɗa, zata ce sai an binciko mata ya akayi ya mutu, idan ma ance mata accident ne zata ce sai an bincika, ita ma mummy ba zata bari ba, zasu kafe sai an bincika, idan kuma ba'a dawo da gawarba, nan ma zasu fito duniya wa ƴan jarida su yi sanarwa Nawazudden ya ɓata, ga shi kuma su suke da goyan bayan al'umma a lokacin, za a bi bayansu sosai, za'a bazama nemansa har gaskiya ta bayyana, shi ne yasa ya ce a kashe gabaɗaya harda family'n nasa.
Wani maharbi ne ya ceci daddy daga hannunsu, da sun kashe shi, wannan maharbi ya jima a wajen yana taimakon mutane da ake kawosu za'a kashe, tsohon maharbi ne sosai wanda baya saɓa saiti, da ba'a nan yake da zama ba, daga baya ya dawo wajen da zama, shi ya ceci daddy a in da ya harbesu da kwari da baka ya kuma fito suka yi fito na fito da shi, a lokacin Abubakar jajan ya bar wajen dan ya ce a kashe daddyn sai ya tafi, wannan maharbin ya kashe su gabaɗaya, suma sun yi ƙoƙarin harbinsa da bindiga, amma ina bindiga bata cinsa, ko bullet ɗaya bata iya taɓa shi ba, kowa yasan dayawa daga cikin maharba suna tsafi, ba dukkansu bane akwai waƴan da basu yi, to shi yana yin tsafi shiyasa bullet bata cinsa, kuma ya dai'na harbin ma yanzu, ya koma wajen ne kawai da zama abinsa dan ya rinƙa taimakon mutane, daddy ya yi kwana biyu a wajensa kafin su rabu a in da daddyn ya ce mishi zai dawo zuwa nan da wani ɗan lokacin, to ya amsa mishi da shi suka yi sallama cikin mutunci, yana bala'in kaunar daddyn, idan baku manta ba dama shi daddy da daddyn Anaya bala'in shiga rai ke garesu, to haka daddy ya shiga ran wannan maharbi sosai in da suka yi zaman mutunci kuma rabuwar mutunci cike da kaunar juna.
Daga nan da daddy ya bar wajen ya dawo Abuja a in da maharbin ne ya taimaka mishi da kuɗin mota, lokacin da ya dawo babu su mummy, uncle Shitu ya saka su a motar Katsina, ganin basu nan ne yasa ya ji ba zai iya zama ba, komai nasa ya lalace, idan babu su mummy ai babu shi, ba zai iya zama ba, sune komai na shi, dan a tunaninsa kashe su akayi, yasan babu in da za su je a duniyar nan, basu da kowa, hakan tasa ya je banki ya ciri kuɗi dayawa ya fita kasarnan ta ɓarauniyar hanya dan komai na shi na cikin gida su passport da sauransu, so dole sai ta ɓarauniyar hanya zai bi, dan gidan nasa an sanya mata kwaɗo da sarka an rufe. WANNAN SHI NE ABIN DA YA FARU DA DADDY BAYAN RABUWAR SHI DA SU MUMNY, KO BAN TSAYA NA YI DOGON BAYANI BA NASAN KUN FAHINCI IN DA ZANCEN YA DOSA KO? TO MU CIGABA DA STORYN MU.
❤️AREEF and JEHAN💋
Wani katafaren wajen shakatawa ya yi parking na motarsa, waje ne na ƴaƴan shugaban kasa, gwamnoni, ministocin, ƴan majalisu, sarakuna da sauran manya kusoshin gwamnati, wajen ya kawatu iya kawatu ba karya, ba zaka taɓa tunanin a cikin Nigeria kake ba idan ka shiga wajen, zaka yi tunanin irin a Dubai or saudiyan nan kake, an narka dukiya na kin karawa wajen kawata wannan waje ba karya, tsayawa zayyana muku kawatuwar wajen nan ma sai ya cinye mana ɗan space ɗin da ya rage mana, dan haka ku kawata a ranku kawai abin sai wanda ya gani.
Mamaki ta rinƙa yi a kan yaushe ya san wannan wajen kuma? Sai ka ce wani ɗan Kasa, ya wani kawosu nan?. Manya manyan dankara dankaran shegun shadaddun motoci ne suke shawaji a wajen, sai kaga wata shegiyar mota wanda sai ka rantse da Allah ba'a kan kasa take tafiya ba saboda haɗuwa, da ta yi parking sai kaga wata ƴar figaggiyar yarinya ce zata fito daga ciki wanda bata wuce ka hureta ta faɗi ba, irin yarannan masu zubin taliya, sai aukin taunan chewing gum suna wani yi wa mutane kallon kaskanci da walaƙanci.
Fitowa ya yi abinsa tare da ce mata ta zo su je, ita dai duk ta tsorata da ganin wajen, har da su pool a cikin wajen, ga abubuwan more rayuwa tamkar baza'a mutu ba, tun da ya sako kafarsa waje mata da maza suke kallon shi tamkar zasu cinye shi saboda kallo, ba karya ya yi kyau sosai.
Jingina da jikin motar ya yi yana jiran ta fito, sam taki fitowa, sai da ya ji shiru ne ya zagaya ta side nata, duk in da ya yi motsi idanuwa ne rututu na mata da maza a kan shi, sun ga masu jajayen kunnuwa, akwai fafare da dama a wajen, amma kunsan Turawa da shegen farinjini a wajen mu, kuma uwa uba ga shi kyakkyawa matashi lafiyayye mai jini a jika ɗaya tamkar da dubu, ai tuni kallo ya dawo kansa babu ko kyaftawa, wasu ma har cewa suke yi basu taɓa kallon kyakkyawa irin shi ba, mata dayawa sun afka tarkon kaunarsa, sai haɗiye yawu suke yi kamar wasu kanne mayu, sun ga ɗan achan achan, ga kuɗi ga mulki, kyau tamkar shi ya yi kansa.
Buɗe mata kofar side ɗin nata ya yi yana faɗin ta fito su tafi, ya yi maganar yana miƙa mata hannu, cikin sanyin jiki ta bashi hannunta ya rikota ta fito, nan fa kallo kuma ya dawo biyu, dan da dama daga cikin jama'ar wajen Jehan da Areef sun yi musu muguwar kama, idan baku manta ba ita dai Jehan farace tas tamkar Naurat, sai dai fa duk da haka a gabansa ita ɗin baka ce, haskensa yana dishashe nata, dan shi ziryan Bature ne babu mix, ita kuma akwai.
Sai kallonsu a akeyi, tamkar bai san menene murmushi ba haka Areef ya zama yau, ya ɗaure fuskar nan tamau kai ka ce ba shi ba ne, babu alamar annuri a tattare da shi, duk waƴan da suke wajen sun sha jinin jikinsu, kuma kallon da ya ga suna yi musu ne yasa ya ɗaure fuska babu wasa, ita kanta Jehan ɗin ta tsorata da ganin yanda ya wani ɗaure fuskar nan tamau tamkar bai san menene ma murmushi ba, sai ya dawo mata sak Lion.
Cikin wajen cin abincinsu suka shiga, wasu shegun tsadaddun kujeru ne waƴan da suka amsa sunansu kujeru, ga bala'in laushi kamar menene, komai na cikin wajen launin ash da baki ne, Jehan fa yau ta sha jinin jikinta, ta ga manyan mata masu class yanda suke kallon Areef kamar su cinye shi ɗanye, ko kyafta idanu daga kansa sun kasa yi, sun ga kyau iya kyau, shi kuma bawan Allah, ko kallon in da suke ma bai yi ba, ya kafe kallonsa a kan Jehan ɗinsa, ita kaɗai yake so babu canji, duk sai ta ji wani iri a jikinta.
Kayan cima kala kala da dama aka kawo musu, kusa da juna suka zauna sosai, sai kallon yanda mata suke kalle mata shi take yi, duk matan dake cikin wajen cin abincin ma idanunsu ya dawo kansa.
Ɗauko kankana ya yi daga cikin fruits da aka kawo musu, cikin zolaya ya ce "Mu bamu cin abincin restaurant or wani waje, mu abincin gida kawai muke ci, amma dalilin Rimsha mun ci a restaurant ranar, yanzu kuma dalilinki zan sake ci". Ɗan kasa ta yi da kanta tana faɗin "Au dama kun taɓa zuwa nan da Rimsha ne?". Girgiza mata kai ya yi yana faɗin "A'a muna zuwa yawo dai, amma bamu taɓa zuwa nan ba, wajen nan ai na boyfriend and girlfriend ne or something like that, Rimsha kuma sisterta ta ce ai, ya za'ayi......". Bai karisa ba wata figaggiyar yarinya ta yi musu sallama a kansu, sam bai ɗago idanu ya kalleta ba, Jehan ɗin ce ta ɗago idanu tana kallonta.
Hannu ta miƙa mishi tana mai gabatar mishi da kanta, ita kam Jehan sake baki ta yi tana kallon wannan yarinya mai tallar kai haka, dama tun da ta shigo ta ji wasu ƴan mata su uku da suke zaune kusa da su ta baya suna magana cikin harshen Hausa a kan ɗaya ta ce wlh sai ta tinkare shi ko me zai faru ya faru, ɗayar ta ce Allah da budurwarsa yake tare, musa mata suka yi a kan sam Jehan ba budurwarsa ba ce kanwarsa ce, dan sun yi kama kuma wannan yarinyar ai ta yi karama ace budurwarsa, kina ganin matashi lafiyayye kyakkyawa ga kirar karfi da lafiya mai class kamar wannan me zai yi da wannan ƴar yarinyar a budurwa? Caraf ɗayar ta capke tana faɗin "Amma ai kinsan yarinyar tana da kyan da dole zai sota ko? Ni fa duk cikin wajen nan idan gaskiya za'abi wlh ban ga mai kyan yarinyar nan ba". Tsaki ɗayar ta yi tana faɗin koma wacece wlh ita sai ta je ta kula shi, to shi ne ta zo, saura sun ce wlh ba zasu iya ba, suna tsoron dan sunga face nasa babu alamar wasa a tattare da shi, ita dai ta ce ko za'a kasheta sai ta zo.
Kankanar hannunsa ya kaiwa Jehan ɗin saitin ɗan bakinta yana faɗin ta karɓa ta sha, kallon yarinyar da take tsaye musu a kai ɗin kawai take yi, hannu ya kai ya rufe mata idanu yana tura mata kankana a baki, sam tamkar bai san da yarinyar a wajen ba, wani irin kunya yarinyar ta ji, ya yi mata kalakanci na karshe da cin fuska, ya tsinkata a cikin mutane, shi kuma lokacin yin magana da ita ne ba shi da shi, bai ga abin kulawa a wajen ba, bata kai ya ɗaga idanu ma ya kalleta ba a cewarsa.
Haka ta juya jiki ba kwari kunya kamar ta shige cikin kasa ta bar wajen, shi kuwa cigaba da bawa ƴar diramarsa fruits ya yi tare da zame hannunsa daga saman idanun nata, kashe mata ido ɗaya ya yi yana faɗin "Ni ba zaki bani a baki ba ne? Ko kin manta am your boyfriend ne?". Girgiza mishi kai ta yi tana faɗin "A'a ban manta ba, ai kai ne baka ce na baka ba". Ɗan matso da face nasa daf da tata ya yi yana faɗin "Ai ba sai nace ba mana, haba baby".
Salar yankar apple ta ɗauko ta kai mishi saitin ɗan bakin nasa ba tare da ta yi magana ba, buɗe baki ya yi ya karɓa ba tare da ya barɓa dukka a cikin bakin nasa ba, sai ya ɗan ciza kaɗan ya rike, kallon shi ta yi tana kallon yanda ya ɗan rike apple ɗin da fararen hakwaransa yaki kaiwa cikin bakinsa, bata ankara ba sai ji ta yi ya jawota jikinsa tare da haɗe fuskokinsu ya kai mata apple da ya rike da kyawawan hakwaransan bakinta, hakan da ya yi ya sanya mata da yawa a wajen sun zubar da abin sha da yake hannunsu, yasa samari da dama jin kunya dan basu iya soyayya ba!.
Ita kuwa ya tashi kanta, dan bata taɓa tunanin zai yi mata hakan ba, bata da zaɓi dole ta karɓa ko dan kada ta tsinka shi a cikin mutane, amma ya bata kunya, ko da ta karɓa kuma sam bai rabe fuskokin nasu ba, ya zuba mata idanu yana kallon yanda take taunar apple ɗin. "Baby to bani apple ɗina, dama na baki ne ki tauna mini". Ya faɗa cikin sanyin murya, batasan time da murmushi ya kubce mata ba. "Apple naka dai na cinye, sai dai ka ɗauki wani". Ita ma ta bashi amsa a sanyaye. "Ni bana son wani na cikin bakinki nake so". Make mishi kafaɗa ta yi tana fito mishi da harshe dan ya gani ta taune ta kusa haɗiyewa, shammatarta ya yi ya kama harshen nata da bakinsa, da sauri ta kwace kayanta tana turo baki. Cool murmushi ya saki tare da raba fuskokin nasu, tamkar wasu film aka mayar da su a cikin wajen, tsantsar madarar soyayya yake zuba mata, ya kuma yi mata wayo ta biye mishi ba dan ta so ba, haka suka kasance cikin tsantsar farinciki a wannan wajen, suna ta tashin kan masoyan da suke wajen.
A ɓangaren Rimsha da Lion kuwa yau ma dai kamar jiya, sai misalin karfe 10 na safe ta farka daga barcin nata, sai dai fa yau ba dan ra'ayin kanta ta farka ba, wani azababben ciwon ciki ne ya tasheta, kuka ta fara yi tana juyi a saman bed ɗin, shi kuma Lion baya nan yana waje kamar dai jiya yana kallon hanya, sun yi nisa sosai a tafiyar tasu, sun kusa isa in da yake son su kai.
Juyi take yi a saman bed ɗin tana hawaye, a haka Brady ya shigo ya sameta, ta kasa buɗe murya ma bare ta yi kuka mai sauti da zai sa Lion or wani ya jita. Ganin yanda take juyi yasa Bradyn ya haye gadon da gudu yana tattaɓata, yau duk tsoronta da shi sai da ta yi la'asar, ta ji tana gani yana taɓata amma ta kasa motsawa ma bare ta gudun mishi, shi kuwa ya shiga damuwar ganin halin da take ciki, sai ƙoƙarin janta yake yi dan ta miƙe, amma ta kasa, da gudu ya diro kasa daga saman gadon ya nufi waje.