Kenza eBookz

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 97

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 97

Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 97: Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 97. Bai zame ko'ina ba sai wajen Lion, jikinsa ya…

3,299 words

Bai zame ko'ina ba sai wajen Lion, jikinsa ya haye yana yi mishi nuni da cikin bedroom ɗin yana haushi da karfi karfi, da yake sun san halinsa, shi ya reni kayansa sai ya gane karatun nasa, ya fahimci akwai matsala a cikin ɗakin, rungume shi ya yi tare da juyawa suka nufi ɗakin a tare, sai haushi yake yi da karfi karfi.

Suna shigo Bradyn ya sauka daga jikin nasa ya haye saman bed ɗin yana cigaba da yin haushinsa, karisowa wajen Lion ɗin ya yi, hayewa saman bed ɗin shi ma ya yi tare da sanya hannu ya ɗagota, kuka take yi sosai ta dafe cikinta, hannunta dake saman cikin nata ha zame tare da ɗaura nashi a wajen yana kallon face nata. "Meesha menene yake damunki?". Ya faɗa yana mai cigaba da kallon face nata yana kuma shafa mararta a hankali hankali.

Da kyar cikin kuka ta amsa mishi da cikinta ne yake yi mata ciwo. "Kin taɓa yin period ne?". Ya tambaya. Girgiza mishi kai ta yi alamar a'a, ɗan rungumota ya yi a kirjinsa yana shafa bayanta a hankali dan ya san matsalar kenan, yanzu sai dai su jira lokacin zuwan shi kafin ya bata magani da allura.

Kankame shi sosai ta yi tana kuka shi ma Brady yana tayata kuka, Allah sarki yaji tausayinta, duk da yake kare ya ji ba daɗin ganinta tana kuka kuma cikin wani hali, duk sai shi ma ya shiga cikin damuwa, yau abokiyar faɗa bata da lafiya.

Kun sani a duniya babu kalmar da Lion ya tsani ji kamar sorry, ya tsani wannan kalmar, ko a faɗa mishi ita ko shi ya faɗa, bai taɓa cewa wani sorry ba, idan kuma wani ya ce mishi to sai ya hukunta shi mummunar hukunci ma, amma yau an wayi gari shi da bakinsa yake cewa Rimsha sorry yana shafa marar tata a hankali hankali, haƙiƙa ya tausaya mata dan yanda take murkusoso sai ta baka tausayi, ita kuma da azababben ciwon mara ya zo mata. Cigaba da kukanta ta yi tana kara shigewa jikinsa tare da kankame shi.

Almost 40 mins tana a wannan hali kafin period ɗin nata ya zo, ta jigata ainun, ta wahala ba karya, ta sha kuka kamar ba gobe, duk da ya zo kuma marar tata bai dai'na ciwo ba, sai sambatu take yi mishi a kan ita wlh bata son period ɗin nan, dama ai lokacin da Ayla zata fara period ita ta ce bata so, dan Allah yaya Saif ya ce period ɗin ya tafi, mutuwa zata yi idan bai tafi ba, ciwo cikinta yake yi, wayyo mummynta, daddynta, ita yau ta shiga uku zata mutu. GA ABIN DARIYA GA ABIN TAUSAYI.

Banda sorry hard luck babu abin da yake ce mata, sai dai ya shiga damuwa mara misaltuwa na ganinta cikin ciwo har haka, shi kansa ya ji ya tsani period ɗin nata dan da alama zai wahalar da ita over, shi kuma yanzu zuciyarsa ba zata iya jure ganinta cikin wahala ba, ga shi ba yadda zai yi, dole dai wannan sorry shi zai yi ta ce mata yana rungume da ita, dan shi dai period dole ya zo ato, ya barta tanata sambatun nata dan zai rage mata raɗaɗi ba kaɗan ba.

Ganin jinin ya zo ne yasa ya kwantar da ita tare da miƙewa ya sauko kasa, duk ta ɓata mishi jiki, sam bai damu ba, a matsayinsa na babban soja jini ba bakon abu ba ne a wajensa, abin da ya fi jini ma ya tsallake kafin ya taka matsayin da yake kai a yanzu, so duk wani soja da zai ce baya son ganin jini or yana kyamar jini ma to ba soja bane, ragon namiji ne! Su da suke fasa mutun da bindiga ma jininsa ya wanke musu fuska!, Me dan jinin mace ya taɓa su? Amma dai baya son ganin jinin a jikinsa, ya so ya canza kayan amma sai ya ce bari ya gama dubata ya tabbatar ta ji sauki kafin ya yi wanka, idan ba haka ba ko da ya yi wanka ya canza kaya ya sake dawowa wajenta ma sake ɓaci da jinin zai yi, dan ba always ba ne garesu a cikin jirgin!.

A box ya ɗauko ya dawo saman gadon, nan fa suka fara rikici da ita, dan kuka ta saka mishi a kan wlh ita bata son allura, jinjina kai ya yi yana faɗin e lallai ta sami lafiya ba shakka, da farko kamar zai yi mata tsawa, amma kuma sai ya danne dan tana cikin ciwo ne, lallaɓata ya yi cikin dabara ya yi mata alluran tare da bata magunguna dan ta sha, da kansa ya ɗauko mata ruwa ta sha maganin sannan ya ɗauketa zuwa toilet, har lokacin tana fama da ciwon ciki, sai dai ya ragu ba kamar na ɗazun ba.

Haɗa mata ruwa ya yi ya ce ta yi wanka, fita ya yi ya bata waje, da kyar ta iya cire kayan jikinta ta yi wankar, shi kuma cikin bedroom ɗin ya dawo a in da da kansa ya cire bed sheet ɗin da ya ɓaci shi ma da jini saboda kwantar da ita da ya yi ya je ya ɗauko A box, ba zai iya sanya Mark ya yi wannan aiki ba saboda tsananin kishi, to gara mishi ya yi da kansa dan ma kada wani ya kalli jinin nata........ LION DUNIYA SARAKAN KISHI, DAGA KANKA AN RUFE KOFA IN DAI FAGEN KISHI NE!!.

Canza bed sheet ɗin ya yi dai'dai lokacin ita kuma ta fito wanka ɗaure da towel tana wani layi ta dafe ciki saboda azaban ciwo da yake yi mata, bai ce mata komai ba ya wuce ya shiga cikin toilet ɗin, wanka ya yi ya fito, kwance saman sofa ya iskota ta sanya kaya, ta yi shiru tana sauraron yanda marar nata yake murɗa mata tamkar zata mutu, hawaye wani na bin wani a face nata, kayansa ya ɗauka tare da komawa cikin toilet ɗin ya shirya, pajama ce fara tas ya sanya a jikinsa.

Bayan ya fito kuma sai ya tsaya shiru yana tunanin yanda zai yi da ita, basu da always a cikin jirgin, ga shi kuma jirgin nasu ne su kaɗai ba na kasuwa ba ne bare ya ce ko su tambayi wasu, wani ɓangare na zuciyarsa ce ta ce mishi to ya aika Mark ya sayo musu a ɗaya daga cikin garuruwan da suke kusa da su mana, sai Mark ɗin ya yi amfani da mashin na ruwan dake ciki kin jirgin ya je ya sayo ya dawo ya samesu. Girgiza kai ya yi kishi ba zata iya barinsa ya aiki wani ya sayo mishi always da pant nata ba, haƙiƙa idan har Mark ya rike su da hannunsa to wlh ba zata yi amfani da su ba, tunani ya yi to ko dai ya je da kansa? Nan ma kishi ba zai barshi ya iya tafiya ya barta ita kaɗai cikin zaratan sojojin nan ba, to shi ya zai yi yau? Ya tambayi kansa, bai isa kuma ya ce zai ɗauketa su tafi ba, dan bata da lafiya sosai, kuma a gaskiya ba zai iya yin nisa da ita ba yanda take wannan murkusoso na ciwon marar......... TO JAMA'A SAI KU BAWA LION SHAWARA, KISHI BA ZATA BARSHI YA IYA AIKAN MARK YA SAYO ALWAYS DA PANT BA, HAKA ZALIKA KISHI BA ZATA IYA BARIN SHI YA JE DA KANSA YA BARTA ITA KAƊAI CIKIN SOJOJI BA, GA SHI BATA DA LAFIYA, BA ZAI IYA NISA DA ITA BA, TO YAKENAN ZAI YI? KU BASHI MAFITA, NI DAI NA HAƊA KAYANA ZUWA GIDAN ABBI DAN NA DUBA SU AYLA SUKE.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔 ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA, INFECTION KILLER, COLACCA, SAI KAYAN GYARA PAGE. KACA KACA. YALLAGWADA. JIGIDA. RUWA RUWA. BANI BANI. WOMEN JELL BATA BATA. DAFIN KAXA. TANTABARA. XABUWA. CICCIƁI. AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER 09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH, BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)

*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 09162620621*

https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S

77

❤️GIDAN ABBI💋

Mu koma baya dan jin abubuwan da suka faru, a lokacin da su Abbi suka kai A'A SALAHUDDEEN Asibiti, sum kira babban yayansa KABIR SALAHUDDEEN a kan ya zo ya ga halin da kaninsa yake ciki, waya ya yi wa maman Anisa da take cikin Kd a kan ta yi sauri ta isa asibitin dan ta duba halin da A'A ɗin yake cikin kafin su zo tun da su a Abuja suke, idan baku manta maman Anisa ba, ita ce wanda A'A ya gayawa su Rimsha Ayla tana kama da kanwarsa Anisa da take cikin KD, to ita ce Kabir ɗin ya kira dan ta zo ta kula da shi.

Sai da maman Anisar ta zo sannan su Abbi suka dawo gida suka barta da A'A. Bayan sun dawo gida sun ci abinci sun ɗan huta, sai Abbi ya buƙaci maman Ayla da ta zo ta basu labarin abin da ya faru da yaya kuma akayi ta san *ABUBAKAR SALAHUDDEEN* ita dai Ayla baiwar Allah sai barcinta take yi abinta, Aunty da ƙoƙari har da rufa mata bargo ta zo ta yi tare da rage mata gudun Ac palon.

Haɗuwa suka yi a palon da Abbi da daddyn Jelly sai maman Aylar, Ayla kuwa tana saman sofa tana barci, Aunty kuma miƙewa ta yi ta bar musu palon dan ita bata son jin labari mai taɓa zuciya, ita irin mutanen nan ne masu saka abu a rai, idan har labarin maman Ayla yana da taɓa zuciya to wlh idan ta ji zata jima bata manta da shi ba, shi ne yasa rufin asirrinta kawai ta bar palon dan zaman lafiyarta da abin da yake cikinta, ita kuwa Hjy Hadiza tana can cikin bedroom nata tana aikin kullewa da warwarewa na yanda zata yi da Abbi, ta dai ki barin gidan, ɗan balaraben mijinta kuma sai kiranta yake yi a waya a kan shi zai biyota Nigeria, kullun cikin waske mishi take yi, tana kwantar mishi da hankali da duniyancinta a kan ta kusa dawowa, ba dan yana so ba yake hakura, amma yana bala'in son ta dawo dan ƴarta Suhana ta kamu da ciwo wanda yana tsoron kai ta aisbiti dan kada asirinsa ya tonu, shi ne yasa yake son maman ta dawo, a haukarsa idan ta dawo zata san yanda zata yi ta yi jinyar ƴarta ba sai sun kaita asibiti ba, ya kuma ki yarda ya gaya mata basu da lafiya, sai dai ya yi ta damunta a kan ta dawo kawai.

Abbi ne ya yi gyaran murya a in da ya ce da maman Ayla ta basu labarin abin da ya faru, shi dai daddyn Jelly labarin ma bata dame shi ya ji ba, shi dai yanzu tun da ya gano alaƙar da take tsakanin Ayla da mummyn jelly to Alhadulillah, yanzu ya fahimci akwai aure a tsakaninsa da Aylarsa, to shi bai ma son jin wani labari na bakin ciki, amma da yake Abbi ne ya ce ta basu labarin sai ya hakura ya zauna yana sauraro.

Labari ta fara basu kamar haka, "Ni dai asalina ƴar garin Bauchi ce, karatu ne ya kawoni Zaria Kaduna state, iyayena masu kuɗi ne dai'dai gwargwado, mahaifina babban malami ne, mu uku iyayenmu suka haifa, ni ce ta biyu bayan yayana babba sai autarmu Aliya wanda na mayar mata da sunan Ayla kenan, a kullum idan aka yi hutu ina komawa gida, ina zaune ne a hostel namu, ina karatu babu kama hannun yaro, iyaye na kuma kullum idan muka yi waya suna yi mini faɗa a kan na kula da mutuncin kaina, a duk in da nake na ji tsoron Allah, na sani mutuwa zata iya riskana a kowani lokaci, na sani abin da na aikata ko a gaban idanunsu ko a baya to a baya ɓuyarwa Allah, yana ganin komai kuma a ranar tashin alkiyama tamkar Tv haka za'a buɗe rayuwata wa jama'ar duniya bakiɗaya su kallah, to dan haka na kula da duk abin da zan aikata, ina ɗaukar maganarsu sosai musamman mahaifiyata da ta kware wajen iya nasiha mai ratsa jiki.

So wasa wasa na fara yin kawaye a makarantar, da farko bani da ko ɗaya, daga baya na yi wata kawa malama nitsatsiya mai sunan Maryam, mun cigaba da rayuwa tare da ita muna karatunmu lafiya Lou, bamu kula kowa.

Akwai wani malami da ya nemi ya samu kusanci da mu, amma mun ki bashi kofa, harkar gabanmu kawai muke yi, a taikaice dai har Abida ta zo ta shiga cikin rayuwarmu, Abida ita ce mafarin rugujewar rayuwarmu, ita ta fara koya mana shan kayan maye irin su kwaya da sauransu, yanda akayi ta fara koya mana kuwa shi ne, idan mun je class mun dawo, irin muna complain na mun gajin nan, to sai ta bamu ta ce mu sha rabin kwalba gajiyar zata sakemu, tun muna ki dan bamu ma san menene ba har muka fara sha, abin ku da kayan shaye shaye, fara shi ne wahala, da ka fara zaka ji ba zaka iya dai'na wa ba, zaka ji idan baka sha ba zaka iya mutuwa, to muma haka ce ta kasance da mu, ba mu iya wuni bamu sha ba, abin har ya zama mana jiki.

Kwance tashi babu wuya a wajen Allah har wani matashi ya shigo cikin tafiyar ta mu mai suna Anwar, mun yi rayuwa da Anwar na tsawon watanni da basu fi biyu ba, to ashe shi kam ba tsakani da Allah ya shiga cikinmu ba, ashe irin mazannan ne masu kaiwa manyan masu kuɗi ƴan mata dan su yi lalata da su, a hankali ya fara yi mana inviting na harkar, sam muka ki yarda, a lokacin kuma ya turawa Abubakar salahuddeen hoto na, tun da ya ganni kuma ya ce na yi mishi yana bukatar a kawo mishi ni.

Ba irin kuɗin da Anwar bai nuna mini ba, amma naki yarda dan ina bala'in tsoron iyaye na da kuma yayana, a barni dai a iya kayan mayen nawa, to da suka ga wannan hanya yaki shi kuma Abubakar ya kwallafa ransa a kai'na, sai ya fito da kansa ya nuna yana so na ne da aure, da yake ni ban san cewa shi ne Anwar yake yi wa aiki ba, sai na karɓi soyayyarsa, mun yi soyayya sosai amma kusan zan ce muku soyayyar ta sirri ce, dan har mamaki nake yi watarana a kan baya taɓa zuwa wajena da rana sai da daddare, yana yin abu tamkar mara gaskiya, kuma a lokacin sam bai shiga siyasa ba.

A hankali yana jana da kalamai na yaudara irin na mazan banza da idan suna son abu a wajen mace ba irin kwatar da murya da marairaicewa da basu yi, tun ina ɗari ɗari da shi har na saki jiki muna hira tare da zuba soyayya, karatuna ya ja baya sosai saboda kayan mayen da nake sha, sam kwakwalwata bata ɗaukar karatu, da anyi karatu after 10 mins na mance komai, na zama wata iri da ni, haka zalika ita ma Maryam ta zama sai a hankali, ita kam Abida dama ai ta saba, so bata jin komai, su mamana kuwa, sai na fi sati ban nemesu a waya ba, sai idan su suka gaji da kansu suka kirani, idan na ɗauka sai nayi musu karya na ce musu wlh lectures ne suka ɗauki zafi yanzu, abubuwa ne sun sha kai'na, suna yi mini uzuri, haka mama zata yi ta yi mini nasiha duk a banza, dan a wannan lokacin nasihar ma sam bata shiga kai'na, a yanda nake ma ji nake yi mama fa tana takura mini, idan kuma ta cigaba to watara zan buɗe mata aiki ko da tawayar ne.

Haka muka cigaba da rayuwa har Abubakar ya fara cewa na raka shi shopping da sauransu idan ya zo Zaria, ba a Zaria yake ba zuwa yake yi, ni ban san garin shi ba daga farko, sai daga bayana na san cewa shi ɗan Kano ne, da tafiya ta yi nisa ne ya gabatar mini da kaninsa Farooq duk dan na kara yarda da shi sosai, ya kuma yi sa'a dan na kara yarda da shi over, na saki jiki aurena zai yi da gaske kamar yanda yake faɗa, haka zan raka shi shopping muje mu dawo lafiya lou, wani lokaci ma tare da Farooq ɗin muke zuwa, so yana da gidan hutawa a Zaria, a lokacin sau ɗaya da muna dawowa daga shopping ya ce mu biya ta gidan dan mu ɗan huta, to a nan ne nasan da gidan.

In takaice muku labari Abubakar da Farooq sai da suka yaudareni suka zuba mini kwaya a cikin abin sha a cikin school namu da ya zo muna hira da shi, tare da Farooq suka zo ranar, sun saka mini kwayar barcin bayan na sha na yi barci a cikin motar ne suka ɗauke ni muka fita zuwa gidansa, ban taɓa kawowa zai sanya mini kwaya a abin sha ba, na yarda da shi sosai da sosai, hakan yasa nake karɓar abin hannunsa na sha.

Ban sake sanin in da kaina yake ba tun da na sha lemun da ya bani sai farkawa na yi na ganni a cikin ɗakinsa na gidan hutawarsa, shi kuma yana kwance kusa da ni yana barci abinsa, ya bani kwaya na sha na yi barci ya lalata mini rayuwa, ya yi mini fyaɗe, na yi kuka sosai, ban da mamana babu wanda nake tunani, na san idan ta san da haka zata iya mutuwa, ta bamu tarbiya iya karfin iyawarta. Ko da na tashe shi daga barci sai ya nuna mini ai ba wata matsala ni matarsa ce In Sha Allah, yaudara ta ɗan bariki, da naki yarda ina ta kuka sai ya kira Farooq ya zo suka haɗu suka yi mini daɗin baki har na sake yarda da shi.

Haka muka cigaba da rayuwa, mun cigaba da zuba soyayya tamkar ba gobe, bayan shi ni bana kula kowa, bai canza mini ba bai kuma gujeni ba har sai da ciki ya bayyana a jikina, nan fa rikici ya ɓarke a tsakaninmu, ya ce shi wlh ba cikinsa ba ne, ni kuma nasan shi kaɗai ne na taɓa kwanciya da shi, nan fa ya ce shi wlh ba cikinsa ba ne na nemi uban cikina kuma shi ya fasa aure na dan ba zai auri ragowar wasu ba, amma taimako ɗaya zai yi mini shi ne ya bani makudan kuɗaɗe na kuma zubar da cikin ko zan sami mijin aure, dan babu wanda zai aure ni idan ya ganni da ciki ko kuma ya ji labarin na taɓa yin ciki, to rufin asirina shi ne na zubar, ni kuma na kafe na ce wlh ba zan zubar ba, nan ne fa ya yi yunkurin kashe ni, ya aiko wasu maza biyu dan su kashe ni, Allah ya tseratar da ni, na sha da kyar.

Readers Also Read