Kenza eBookz

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 99

Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 99

Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 99: Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 99. Hannu ya miƙawa macen sojan a kan ta kawo…

3,373 words

Hannu ya miƙawa macen sojan a kan ta kawo mishi trolleyn ba tare da ya yi magana ba, cikin hanzari tare da taku irin na jaruman sojojin da suka sami tsantsar horo ta kariso gabansa, sai da ta sake kamewa kam ta sara mishi kafin ta miƙa mishi trolleyn, sam bai karɓa ba bai kuma ɗaga ido ya kalleta ba, hankalinsa ya koma a kan wayarsa dake hannunsa, ya barta rike da trolleyn for almost 5 mins, ga trolleyn da bala'in nauyi, ta gaji amma ba damar ta nuna hakan, daurewa ta yi har sai da ya kara tsayuwar 2 mins kafin ya yi mata alama da hannu a kan ta ajiye ta wuce mishi ta bashi waje, sam bai yi magana ba dan nuna tsantsar isa da izza.

A hanzarce ta ajiye mishi ta juya ta koma wajen da ta sauko dan ta jira Helicopter ta dawo ta ɗauke ta, ya ɗauki almost 2 mins ba tare da ya motsa ba yana latsa wayarsa cike da nuna isa, tamkar ba shi ne ya gama cewa Meesha yanzu a cikin ɗaki ba, ko da yake dama Meeshansa kawai ya canzawa, ita kaɗai taga canji a tattare da shi, da ya bar wajen ta, to ya koma ainahin Lion ɗin nasa, sai ya wani kara ɗaure fuska na wuce misali, ga uban nuna isa da izza babu abin da ya ragu.

Ɗaukar trolley ya yi zuwa ciki, gabaɗaya sojojin sun yi mamakin me zai yi da trolley,? Saboda sun san wanene shi, baya sayan kaya a hanya, idan zai yi tafiya yana shirya komai da zata ishe shi, harta ita kanta soja mace da ta kawo trolley bata san menene a ciki ba, ita dai an kawo mata trolley har cikin office nata aka ce ta shiga jirgi zu je zata kaiwa GAR, amma bata san me a ciki ba, duk abin da yake ciki wannan kyakkyawa tsadadden kuma haɗaɗen trolley to Josephine ne ta sayo shi, ita ta je da kanta ta yi sayayya, a lokacin da zata je ita da kanta bata san me zata je saya ba, ita dai tana zaune sojoji biyu suka zo har cikin gida suka ɗauketa zuwa super market, sai da suka shiga super market ɗin ne Lion ɗin ya yi mata massage a kan ga abin da zata ɗauka mishi a super market ɗin, ta sha ruwan mamakin ganin saƙonsa, bata taɓa tunanin ya san da numberta a duniya ba, dole dai ba dan ta so ba ta yi wannan sayayya na abin da ya rubuta mata tas, bata yi mamakin ganin ya rubuta mata ta ɗauka mishi kayan mata har da su pad ba, domin duk wani motsin yaran nata tana iya sani, amma ba kowani lokaci ba, time to time haka dai, Lion shi ne yake yawan zulle mata sosai dama, dan ya fi TRIPLETS nasa riko da addini fiye da tunanin mai tunani, bata iya bincikar halin da yake ciki, kuma bata taɓa iya gane mishi, kullum a siffa ɗaya yanayi ɗaya take ganin shi, Aseef kuwa bawan Allah da yake yanzu ma yake koyan karatun addinin bai yi nisa ba, sai ya zamana duk wata bala'i take farawa ta kansa, shi kuma Areef Allah yana kare shi daga duk wata sharri saboda kyakkyawar zuciyarsa ta zinari kuma shi ma yana da riko da addini sosai duk da bai kai Lion ilimin addinin ba, amma yana iya ka bakin kokarinsa, Lion shi ne ya zurfafa bincike sosai a kan addinin musulunci shiyasa ya fisu ilimi na wuce misali.

So Josephine bata yi mamaki ba dan ya ce ta zaɓo mishi kayan mata, ta san yana tare da mace, abin da ya bata mamaki a nan shi ne karfin izzarsa da nuna isa irin na yaron nata, wato shi ko ana so ko ba'a so idan yana son abu to fa sai an shi, gata dai a nata wawtar wai ita take juyasu, amma shi kuma shi ne yake ainahin controlling nata ko tana so ko bata so, bata isa ta ɗaura wata magana a saman nasa maganar ba, idan ya yi magana dole ne a yi, yanzu dan tsabar isa irin nasa tana zaune a gidanta yasa aka ɗaukota aka kawota super market, kuma ba yanda ta iya dole ne ta yi wannan sayayya idan tana son zamanta lafiya, kuma duk abin da ya rubuta dole haka zata ɗauko mishi su masu kyau ko ranta ya ɓaci a banza, ita dai tana ganin gararin rayuwa, sun haifi ƴaƴan amma ƴaƴan su ne suke juyasu, ko da yake ba laifin ƴaƴan ba ne, laifin su ne dan su suka basu tarbiya irin haka, so dole su ɗauki koma me yaran zasu yi a yanzu, dan sun makaro tunfarko, itace tun yana ɗanye ake tankwara shi, idan aka kuskura aka bari ya bushe to ba zai tankwaru ba sai dai ya karye, Allah ka bawa ko wace mace ikon bawa ƴaƴanta tarbiya irin na koyarwar manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama dan amfanuwan kanta.

A takaice dai Josephine ce ta yi dukkan sayayyar cikin trolleyn nan, bayan ta kammala ta shirya su cikin trolleyn sai ta bawa soja mace dake biye da ita ta ɗauko suka fito, sojan ta wuce office nasu ita kuma Josephine ɗayar sojar ta mayar da ita gida aka cigaba da tsaronta, dan Lion ya hanata fita ko nan da can, kullum tana gida zaratan sojoji biyu suna gadinta.

Wajen da trolleys nasu yake ya nufa ya ajiye trolley, kusa da ita ya dawo, sai zuba barci take yi abinta, hankali a kwance, ɗan zuba mata waƴan nan dara daran blue eyes ɗin nasa ya yi na ƴan mintoci kafin ya sanya hannu ya saɓeta a kafaɗarsa tamkar wata ƴar baby ya nufi toilet da ita. Daddaɗar kamshin perfume nasa ne ya fara kai mata karo a hancinta lokacin da ta farka sanadiyar jin da ta yi an ɗauketa, a hankali ta waro dara daran sleeping eyes nata a saman face nasa, hankalinsa baya a kanata haka zalika kallonsa, yana kan wajen da yake son zaunar da ita, amma ya san tana kallon shi.

Hannu tasa ta saƙalo wuyarsa tana ɗan turo baki, jin saukar hannun nata a wuyarsa ne yasa ya sauko da idanunsa kanta, cikin sauri ta runtse nata idanun, tsayuwa ya yi daga tafiyar da yake yi ya zuba mata idanu. "Open your eyes". Ya faɗa a tsakanin sanyaye.

A hankali tamkar mara gaskiya ta ɗan buɗe idanun nata tana kara turo mishi baki.

Zuba mata ido ya yi na ƴan mintoci kafin ya ɗaurata a saman chair dake cikin toilet ɗin. Ɗan ɗaukanta da ya yi har ta ɓata mishi jiki, da yake idan baku manta ba shi rabin kayansa dukka fararene, shi ne yasa take saurin ɓata shi. Wucewa ya yi ya haɗa ruwan wanka sannan ya nufi hanyar fita yana ce mata ta yi wanka ta zo ta sanya kaya, okey ta amsa mishi da shi, ficewa ya yi zuwa ɗayar ɗakin shi ma dan ya yi wanka.

Ta riga shi fitowa daga wankar, ko da ta fito taga sofar da ta kwanta a kai ya ɓaci da jini, sai ta ɗauko towel fari mai kyau irin na goge sumar kai idan an yi wankar nan, ta ɗauko sabulai masu kamshi sosai, ta zo ta zuba tare da ruwa kaɗan ta goge tas, nan take wajen ta fara zuba kamshi sosai saboda karfin kamshin sabulan, bata sanya kaya a jikinta ba har sai da ta gyare musu ɗakin tsab, air freshener har kala uku ta fesa musu sannan ta ɗan kara gudun Ac, wani haɗaɗɗen kamshi tare da sanyin Ac mai ratsa zuciya ne yake tashi a ɗakin.

Lotions nasa ta je ta fitar tare da zama ta fara shafawa sai ga shi ya shigo ɗakin cikin shigar wando three quarter fari tas da kuma polo t-shirt sky blue, ya yi matuƙar kyau tamkar shi ya yi kansa, ya ɗaure dark black curly hairnsa a baya, ya bar wannan guntu na gaban goshin nasa, face nasa har wani kyalli yake yi, soft skin ɗin nan nasa ya kara kwanciya luff tamkar bai taɓa taka kasa ya fita waje ba, sai wani sheki fatar tasa take yi, alama ce ta ya kara samu kwanciyar hankali over fiye da na baya.

Sosai yau ta zuba mishi idanu tana kallo shi, ya yi wani irin azababben kyau ne na wuce misali, ji take yi tamkar ta tashi ta je ta rungume shi ta kuma sumbaci ɗan bakin nan nasa, dan kuwa lips nasa har wani kyalli suke yi tamkar ya sanya musu lips balm, sun kara ja sosai. Ya tsaya a tsakiyar bedroom ɗin yana ɗan latsa waya. Kasa jurewa ta yi da sauri ta miƙe ta zo ta faɗa jikinsa.

Nauyayyar ajiyar zuciya suka sauke a tare kafin ya buɗe hannunsa ya rungumeta da kyau a saman faffaɗar kirjinsa, sam ta manta ma da cewa towel ne a jikin nata, ga gashin kanta bai gama bushewa ba, akwai ruwa ruwa a jikinsa, shi ma gashin kansa da ɗan ruwa a jikinsa, dan bai busar da shi ba, da ya goge da towel kawai sai ya barta dan yana son ya zo ya bata pad kada ta saka kaya ta sake ɓata jikinta, yasan idan ba shi ya zo ya bata da kansa ba, to ba zata taɓa trolley ɗin ba, kayanta kawai zata ɗauka dan bata da shisshigi a kan abin da bai shafeta ba.

Lumshe idanunsa ya yi yana shaƙar daddaɗar kamshin air freshener da ta fesa musu ga kuma sanyin Ac dake ratsa mishi zuciya, shi kaɗai yasan me yake ji.

Hannu ya ɗaura a saman bayanta kasa kasa ya ce "Muje na baki kayan sakawa". Ya yi maganar a tsananin sanyaye kamar dai kullum, ya kuma yi maganar yana waro idanunsa a kanta. Sakinsa ta yi ta nufi wajen trolleys ɗin tana faɗin "Noori yau kai ne zaka zaɓa mini kaya?". Tana magana cikin tsantsar yarinta, hakan ba ƙaramin burge shi take yi ba, sai dai shiru ya yi bai yi magana ba, ya kariso wajen trolley ɗin.

Wanda sojan can ta kawo mishi ya kwantar a in da ya zuge zip ɗin ya buɗe, manya manyan teddy guda biyu farare kal kal masu matukar kyau da kuma girma sosai ya fara cin karo da shi a cikin trolleyn, kallo ɗaya ya yi musu ya kawar da kansa, shi dai bai cewa Josephine ta saya mishi teddy ba, ita kuma ta saya mishi ne dan ta nuna mishi cewa Rimsha fa baby ce da bata wuce ta yi wasa da teddy ba, sako ta aiko mishi a fakaice, ya gane nufinta sarai amma sai ya yi tamkar bai gane ba.

Yana ciro teddy ya ajiye a gefe Rimshar ta kariso wajen da sauri tana zuba uban murmushi cike da murna ta ɗauki teddy ɗaya, ta ji tsantsar farinciki, rabonta da su tun a Abuja lokacin da daddynta yake sayo musu suyi ta faɗa ita da Jehan akansu. Zancen Josephine ya tabbata, Rimsha fa yarinya ce da bata wuce wasa da teddy ba, ga shi kuwa ta ɗauki abinta tana ta murmushi har da yi wa teddyn magana tamkar da mutun take tare.

Girgiza kai kawai ya yi ya cigaba da duba kayan ba tare da ya fitar dasu daga cikin trolleyn ba, yes komai ya yi, yanda ya rubuta haka ya sayosu, wata ƙatuwar leda mai ɗauke da pad a ciki ya fitar tare da ɗauko kwalin pant guda ɗaya, miƙa mata ya yi yana faɗin ta ajiye teddyn nan ta je ta shirya, karɓa ta yi tana kallon pad ɗin da mamaki, ita fa bata san taya ma ake sanya always a jikin pant ba, bata taɓa ganin yanda ake yi ba, shiru ta tsaya ta kasa motsawa, gyara kayan cikin trolley ya yi tare da jan zip ɗin ya rufe, sannan ya miƙe tsaye da nufin ya bar wajen.

Ganin tana tsaye tana ta kallon always ɗin ne yasa ya ɗan zuba mata idanu, sarai ya gane bata san ya ake amfani da shi ba ne, amma sai ya yi tamkar bai gane ba ya yi wucewarsa ya barta tsaye a nan rike da su ta saki baki ta rasa ta ina zata fara, ita tunani ma take yi na ya akayi a wancan ranar Ayla ta yi amfani da nata ma? Bata sani ba, dan ai Ayla ba'a gabanta take sakawa ba, a toilet take sakawa. Tamkar zata yi kuka ta juyo da kallonta a kansa, yana kwance saman bed ya lumshe idanunsa tare da ɗaura hannu ɗaya a saman goshinsa tamkar mai yin barci.

"Noori Allah ni ban iya saka wannan abin ba". Ta yi maganar tamkar zata yi kuka, tamkar babu shi a cikin ɗakin, sam bai kulata ba, shiru ta yi tana tunanin mafita.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔 ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA, INFECTION KILLER, COLACCA, SAI KAYAN GYARA PAGE. KACA KACA. YALLAGWADA. JIGIDA. RUWA RUWA. BANI BANI. WOMEN JELL BATA BATA. DAFIN KAXA. TANTABARA. XABUWA. CICCIƁI. AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER 09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH, BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)

*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 09162620621*

78

"Noori Allah ni ban iya saka wannan abin ba". Ta yi maganar tamkar zata yi kuka. Tamkar babu shi a cikin ɗakin, sam bai kulata ba, shiru ta yi tana tunanin mafita.

Kukan shagwaɓa ta saka mishi daga baya wanda ya sanya shi buɗe idanunsa ba tare da ya shiryawa hakan ba, bubbuga kafa ta fara yi a kasa tana turo baki tana faɗin "Uhm uhm ni yanzu Noori to ya zan yi? Allah cikina ma ya sake fara ciwo, wayyo mummyna, ina kike ne? Kizo ki koya mini yanda zan saka wannan abin". Ɗan sake lumshe idanu ya yi, ba yanda ya iya, wannan shagwaɓa tata dai tana matuƙar ɗaukar hankalinsa tare da jan ra'ayinsa ya sake jin yana son kasancewa tare da ita a koda yaushe.

Hannu ya miƙe mata a kan ta bashi pad da pant ɗin, cikin wani irin yauki da shagwaɓa ta kariso gabansa, sai turo baki take yi tana kumbura kumatu. Miƙewa zaune ya yi yana kallon face nata, komai yarinyar nan ta yi a duniyarnan burge shi take yi, wai shin me matsalarsa ne? Ya tambayi kansa.

Cikin yanga kamar yanda AKila ta gaya mata ta miƙa mishi pad ɗin, karɓa ya yi tare da ajiyewa a gefensa har lokacin ya kasa kawar da kallonsa daga kanta, yangar tata ma ba ƙaramin burge shi ya yi ba, yarinya karama sai iyayi kala kala, bai san cewa duk Akila take koya mata waƴan nan abubuwa ba.

"Bani kwalin mana". Ya faɗa a sanyaye. Dama da gangan taki miƙa mishi kwalin pant ɗin, ta bari ne ta ji zai iya kiran sunan pant ɗin ne ko ba zai iya ba, sai kuma ta ji bai faɗi sunan ba, kawai ya ce ta bashi kwalin. Turo baki ta yi a tsakanin shagwaɓe ta ce "Noori wai dama me a cikin kwalin ne?".

Ayya Rimsha da gaske yarinya ce, bata san tunaninsa ya wuce nan ba, shi baya sauraron maganar saman harshen mutun, karkashin harshensa yake karanta, hakan da ta yi mishi sai ya ji tamkar ta rai'na shi ne or ta mayar da shi bai san me yake yi ba, abin ya ɓata mishi rai da har yasa hannu ya damko towel ɗin jikinta da nufin ya jawota dan ya dallah mata koda mari ɗaya ne yau ta san shi fa ba abokin wasan ta bane.

Duk yanda kuke da TRIPLETS kada ka kuskura ka bari wata alama ta rainin ta shiga tsakaninka da su, duk mutuncin da kuke yi kuma duk yan da suka kai ga sonka, muddin ka yi musu wargi kaɗan da zata nuna ka rainasu, to wlh nan take za su manta da soyayyar nan su yi maka abin da zaka yi danasanin zuwanka duniya, haka suke tun suna yara, haka kuma suka taso har izuwa yanzu. Lion sam baya dukan mata, amma wlh a yanda Rimsha ta yi mishi wannan magana tsab zai dallah mata mahaukacin mari da zai sata suma ko sau uku ne, maganar tata akwai rainin wayo a ciki, sai dai ita bata kalli hakan ta fuskar rainin wayo ba, rashin sani ne, bata san taya zata sanya shi ya kira mata sunan pant ɗin ba, shi ne ta tambaye shi ta wannan hanyar, tana ganin hoton pant da sunansa a jikin kwalin amma dan rainin wayo zata tambaye shi, dole ya ji haushi.

Ƙoƙarin guduwa ta yi a in da ya fisgota da karfi har sai da ta bugu da jikin bedside drawer, karan azaba ta saka mishi wanda ya sanya shi sakinta. Allah sarki ta rigada ta zama rauninsa, ta shige jikinsa sosai a lokacin da bai sani ba, soyayyarta ya yi mishi over a zuciya, so ba zai iya ganinta cikin wani hali kuma ya sake yunkurin kara mata wani hukuncin ba, ganin ta bugu da jikin drawer ne yasa ya saketa, ya kyaleta ba dan ya so ba, a sonsa kam ya bata mari koda guda ɗaya ne mai rai da lafiya.

Kasa miƙewa ta yi dan ta bugu sosai, kuka ta sanya mai tsuma zuciyar mai sauraro, bai bi ta kanta ba ya ɗauki kwalin pant ɗin, da farko ma ya yi niyar kin sanya mata pad ɗin a jikin pant ɗin, amma da ya tuna zata ɓata mishi waje da jini ne yasa ya ɗauko dan ya sanya mata.

Kuka take yi sosai amma ko a jikinsa, pant ɗin ya fitar tare da ciwo always ɗaya, calmly ya ce ta tashi ta kalli yanda ake yi dan daga wannan ba zai sake saka mata ba, bala'in tsoronsa yasa ta miƙe da kyar dan ta kallah, hawaye wani na bin wani, zantukan AKila kawai take tunawa, in da take ce mata wlh idan kika yi mishi ba dai'dai ba tsab zai manta da soyayyar da yake yi miki ya hukunta hukunci mai tsanani, sai dai daga baya ya ji babu daɗi or ya yi danasani, amma a lokacin kam ba makawa sai ya hukuntaki, dan na lura haka zuciyar TRIPLETS gabaɗaya suke, sun iya canzawa lokaci guda su manta da duk wata alaƙa da take a tsakaninsu da mutun su bashi hukunci mai tsanani, sai da ga baya idan sun sauko daga dokin zuciyar ne kuma sai su ji ba daɗi.

Cire ledar pad ɗin ya yi tare da buɗe pant ɗin ya sanya mata a ciki, kunya tamkar zata shige cikin kasa, shi kuwa da yake jinin turawa, ko a jikinsa, tamkar ma bai san me ya rike ba, sam babu ko ɗigo na alamar kunya a tattare da shi. Ga pant ɗin fari tas da shi mai shegen kyau, jikinsa laushi sosai. Ba ƙaramin kyau ya yi mata ba, sai dai ta yi mamakin yanda aka yi aka sayo mata pant dai'dai size ɗinta, bata san da idanunsa ya aunata a in da ya rubutawa Josephine size da yake bukata ba, hausawa sun ce ido ba mudu ba amma ya san kima, to haka ne, in dai zaka kalli abu da idanu to ba sai ka auna ba, kana iya kimantawa, amma sai masu basira sosai.

Bayan ya kammala sakawa ya miƙa mata tare da komawa ya kwanta ba tare da ya ɗaga idanu ya sake kallon in da take ba.

Readers Also Read