Triplets book 3 complete By teema princess - Chapter 100
Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 100: Triplets book 3 complete By teema princess Chapter 100. Duk jikinta ya yi mugun sanyi tamkar wanda…
3,287 words
Duk jikinta ya yi mugun sanyi tamkar wanda ciwon mutuwar gaɓoɓi ya kamata, ta ji babu daɗin ganin ya yi fushi da ita, ɗaukar ledar pad da kwalin pant ɗin ta yi ta nufi wajen trolleys ɗin. Ajiyesu ta je tayi tare da ɗaukar kayan sakawarta ta nufi toilet.
Jim kaɗan ta fito ta shirya cikin haɗaɗɗun kananan kayanta, wandon jeans ne guntu bai ma karisa rufe mata cinyarta ba, irin wandunan nan ne wanda suke tsayawa a dai'dai tsakiyar cinya, sai ƴar riga mara nauyi da ta tsaya mata a kugunta, rigar tana da ƙaramar hannu zuwa iya kafaɗa. Ɗan kwana biyu da suka yi a cikin ruwan nan, har wani sihirtaccen kyau ta kara, wajen ya karɓeta sosai, soft skin nata ya kara kwanciya luwai luwai, tsantsar tsadadden kalar fatarta wato chocolate color ya kara bayyana da kyau da kyau, ba karamin azababben kyau hakan ya kara mata ba, ga idanu farare tas kamar farin cikin kwai, ga su dara dara kuma sleeping eyes, ai abin ba'a magana, dole ma Lion ya rinƙa kasa ɗauke idanunsa daga kanta, kusamman idan ta motsa kyawawan laɓɓan nan nata, nan take haɗaɗɗun dimples nata suke lotsawa, wow ai dole ya rinƙa kafeta da blue eyes nasa babu ko kyaftawa, bawan Allah ya yi mummunar zurmawa a cikin kogin soyayyarta ba tare da ya ankara ba.
Gyara kyakkyawar gashin kanta ta yi tare da zuba perfume nasa a jikinta tamkar babu gobe. Jiki ba kwari ta nufo wajen bed ɗin, yana kwance irin kwanciyar da ya yi ɗazun. Ta wajen kusa da bedside drawer ta zo ta tsugunna a gabansa, cikin sanyin murya da shagwaɓa sosai a cikin muryar tata ta fara magana tare da riƙo hannunsa ɗaya a cikin nata.
"Ban taɓa tunanin akwai wata bakar rana da zata zo a duniyar nan da zansa ka ji babu daɗi ba, ba zan iya yafewa kaina ba har sai idan ka yafe mini, ina cikin damuwa da kuncin zuciya, kai nake gani nayi farinciki, na tuba ba zan sake ba, ka yi hakuri ka ji Noori? Am so so sorryyyyyyyy, na yi alkawarin ba zan sake ba". Tana magana tana kuka, duk wannan abubuwa da ta faɗa mishi wlh caf kalaman mummynta ga daddynta ta ɗauko, tana jinsu wani lokaci idan daddy ya shigo gida cikin ɓacin rai, mummy ba ita ta ɓata mishi rai ba, amma da yake ita mace ta gari ce, sai ta je ta yi ta bashi hakuri tamkar yanda manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya umarci mace ta gari da ta yi wa mijinta, to shi ne ita ma ta haddace yau take yi wa Noorinta.
Tabbas har cikin ransa ya ji daɗi, bai taɓa jin kalmar sorry ta yi mishi daɗi ba a duniya sai yau da ya fito daga bakinta, ya tsani kalmar fiye da tunanin mai tunani, amma yau da ta faɗa, kalmar ta yi mishi mugun daɗi, dan a tsananin shagwaɓe ta furta kalmar, sai dai ya ɗan yi mamakin a ina ta koyo maganganu masu daɗi da ma'ana haka? A ina ta jiyosu?. Ƴar yarinya da ita amma ta iya abubuwa da zata saye zuciyar mutun duk taurin ransa.......MATA!! MATA!! MATA!! ALLAH YA BAMU BAIWA, DUK TAURIN ABU MUNA IYA SANYA SHI YA YI LAUSHI CIKIN ƘANƘANIN LOKACI IDAN MUKA YI RA'AYI! TO UBANGIJI ALLAH YA KARA MANA HAZAKA DA BAIWA😌🙃
Zazzakar muryarta ne ya sake katse mishi tunani da cewa "Noori na Allah idan baka yafe mini ba yau daga yanzu har sanda zaka yafe mini zan yi ta marin kai'na ne, kuma zanyi ta kuka har sai hawayena sun kare, sannan kuma ba zan yafewa kai'na ba, please mijina ka yafe mini.....". Bata kai karshen maganar ba ta yanketa sakamakon wani irin waro idanun waje da ya yi, bai taɓa tunanin ta san cewa shi mijinta bane, bugu da kari bai taɓa tunanin koda ta sani ma zata iya furta mishi kalmar miji a haka ko shakka babu ba, ko ɗazun da ta ce mishi Noorinta wato haskenta ya bashi mamaki, dan bai yi zaton tana da wannan kwarin gwiwa ba, bai san cewa Akila ta gama ɗaurata a kan hanya ba, ita kuma tun da ta san ba zai taɓa lafiyar jikinta ba, shikenan sai ta saki jiki tana zuba mishi kalamai son ranta.
Wani irin razana ta yi na ganin ya waro idanun nasa waje, har wani kyalli suka kara yi na zarosu da ya yi. A hanzarce ta miƙe dan ta gudu, a tunaninta dukanta zai yi or something like that, shi ne yasa zata gudu.
Tana ƙoƙarin sakin hannunsa da ta rike ya yi maza ya riko nata hannun tare da jawota ta faɗa saman faffaɗar kirjinsa, kara ɗaure fuska sosai ya yi tamkar hadari. Calmly ya furta "Waye ya gaya miki ni mijinki ne?". Da yake tun da ya kamota ta runtse idanunta, sai bata san ya kara ɗaure fuska ba, bataga action da ya ɗauka ba, magana kuma da normal yanda yake yi mata magana a sanyaye ya yi shi, so bata ji wani canji ba, dan haka sai ta turo baki cikin shagwaɓa ta fara magana.
"To.... To.... To Noori kai ba mijin nawa ba ne? Uhm uhm ni Allah ka matse ni da yawa, zaka fasa mini kirji fa". Ya ilahi ya lillahi, ai yanda ta yi wannan magana tamkar ta kwala mishi guduma ne a tsakiyar kansa, amma fa gudumar soyayya, tamkar ta caka mishi mashi ne a kahon zuciyarsa na tsantsar kaunarta, yanda take motsa laɓɓanta tana magana ya ilahi, shi kaɗai yasan irin azababben sha'awarta tare da kaunarta da yake ji. Lumshe idanunsa ya yi ya kasa jurewa har sai da ya matso da face nasa izuwa saman tata.
Idanunta a runtse sai zuba mishi shagwaɓa take yi tare da turo ɗan bakin, ba zai iya jurar ganin yanda take motsa lips ɗin nata ba, dan haka sai ya sanya yatsarsa ɗaya a samansu dan ta yi shiru yana mai lumshe idanu, saƙalo wuyarsa ta yi da hannunta ɗaya tare da ɗaura ɗayar hannun nata a saman kirjinsa daidai saitin ɓul ɓul ɗinsa.
"Noori yanzu maganar ma ba zaka barni na yi ba?". Kara ingiza mishi zuciya ta yi da wannan magana tata, matseta sosai ya yi a jikinsa yana jin wani irin azababben yanayi mai azabar daɗin gaske tana ratsa shi.
"Noori ka bari....." Yatsar tasa ya zura mata cikin bakin nata tare da danne mata tongue yana sauke numfashi a hankali. Cikin natsuwa da sanyin murya, can kasar maƙoshinsa ya furta "Meeesha Keep quiet". Cikin salon da shi kansa bai san ya iya ta ba ya yi maganar. Wani irin daɗin yanda ya yi maganar ta ji. Sam baya son ta cigaba da magana tana daɗa jefa shi cikin yanayi mara misaltuwa, yanzu ma komai ya miƙe mishi, bai san time da gabansa ta tsaya kyam ba, irin hakan yake gudu yasa sam baya son yawan wasa or yawan taɓata, yasan waye shi, shiyasa ko da sunan wasa baya kuskura ya taɓa breast nata ko ya yi wasa mai ɗan tsawo da ita, kallon yarinya sosai yake yi mata, kada ya cika taɓata ya jawa kansa bala'i, Rimsha ba zata iya da jarabarsa ba a ƴan shekarun nan nata, shiyasa sam baya wuce ya yi mata kisa ko ya rungumeta, dan tsaro, kada ya je ya kashe ƴar mutane a banza a cikin jirgin ruwan nan, shiyasa yake kame kansa, amma ita kuma tana son hayewa jikinsa, tana son rungume shi, ba dan komai take yin hakan ba sai dan tsantsar kaunarshi da take yi, ta yi mishi wani irin mahaukaci kuma makawon so a rayuwarta, shi ne yasa yanzu da ya zama mallakinta kuma tasan ba zai yi mata komai da ya shafi duka ko tsawa ba sai tana yawan rumgume shi, ta san gabaɗaya TRIPLETS basu dukan mata, dukan mace sai namiji rago da bai sai ciwon kansa ba, mace bata da wajen duka a jikinta dama.
Shiru ta lafe a jikin nasa, shi ma shiru ya yi yana jin azababben sha'awarta da ta motsa, komai ya tsaya mishi cak, bawan Allah ta jefa shi cikin yanayi.
A ɓangaren Jehan da Areef kuwa, soyayya babu kama hannun yaro Areef yake zuba mata ba karya, haka zai yi mata wayo ta yi ta biye mishi ba tare da ta sani ba, yana yi mata dabara tana kara zurmawa cikin son shi, daddynta kuwa ko a jikinsa, murna ma yake yi sosai da hakan, ya fi kowa farinciki.
Idan muka koma ɓangaren gidan Abbo kuwa, soyayya babu kama hannun yaro Dr da Aafia suke zubawa, Ummi kuwa tana kara musu goyon baya ta hanyar bawa A'afia shawari da sauransu. A ɓangaren su Jelly kuwa, yanzu fa jelly ta ɗan natsu sosai, amma sai dai ba dan Allah fa ta natsun ba, maza take karɓa a hannun Imran, baya ɗaga mata kafa ko kaɗan, morar kayansa yake yi son ransa, Ammie kam aikinta gyara da kasasu da ruwan zafi, hankalinta kwance, da anci abincin dare zata kaɗasu ɗakin mazajensu, kuma dole su tafi ko sunki ko sun so. Umaisha da Akil kam dama kunsan mayun juna ne, Akil ya koya mata, su dama a manne suke tamkar chewing gum, cikin nasu ya fara girma ma basu hakura ba, sai sun murji juna son ransu sannan Akil ya shafa cikin tare da zuba mishi addu'a har da cewa Allah yasa yaron nasu ya gaji babansa.................... (Ni kuwa sai na ce ba Amin ba, wannan jaraba har ina? Idan ya gaji babansa ai mun bonu idan kuka zo TRIPLETS return 🤣🤣 kunsan fa ance ɗan na gada yafi ɗan na koya, to ni dai na ce wlh ba Amin ba, kada ya gaji babansa da mamansa gaskiya, ina zamu tsaya idan ya yi gadon wannan irin ɗanyen aikin nasu? Kufa readers me kuka ce?😌🧐)
Ita kuwa Umaisha da ya yi addu'ar sai ta ce Amin da sauri, su dai su Imran shiru basu sami ciki ba har yanzu. Idan muka koma gidan Lion na Kaduna kuma.......
❤️AFTER SOME DAY'S💋
A ɓangaren Aseef da Akila kuwa sai dai mu ce Alhamdulila, dan fa sauki kam ya samu ba karya, Akila ta warke garau, ta samu kula na musamman daga wajen Dr William jacop, shiyasa cikin ƴan kwanaki kaɗan ta sami sauki, shi ma Aseef daddyn nasa ya kashe lokacin a kansa ba karya, ya kula da shi fiye da tunanin kai tunani, sai da ya tabbatar ya yi treating ɗin duk wata cuta da ya gani a tattare da ɗan nasa. A takaice dai duk sai da ya fitar da su daga cikin haɗari, sannan ne ya ɗan samu natsuwa, yana bala'in kaunar TRIPLETS nasa, yanzu ya fahimci idan wani abin ya sami matansu fa to yana iya rasasu, shi ne yasa ya saduda kawai ba dan yana so ba ya karɓi bakaƙen fatar a matsayin surukai, dole tasa kawai ya hakura dan kada ya rasa ko mutun ɗaya daga cikin TRIPLETS nasa, farincikin rayuwarsa, kuma su ne duniyarsa bakiɗaya.
Areef da Jehan game fa yanata tafiya, yanzu saura ƴan kwanaki da basu fi uku ba a gama game ɗin, ya sanya ta saki jiki da shi sosai fiye da tunanin mai tunani, suna hira, sai dai har yanzu bata dariya kuma bata da yawan magana wanda hakan kuma halittarta ce.
Yau ma dai kamar kullum tana kwance cikin bedroom nata ya iskota, yanzu ta tashi daga barcin safe. Bakinsa ɗauke da sallama ya shigo, cike da kulawa ta amsa mishi sallamar, saman bedside drawer ya zauna. Zuba mata idanu ya yi yana kallon kayan jikinta. Kayan barci ne marasa nauyi a jikin nata, tana da breast masu matuƙar ɗaukar hankali, dan kuwa sun cika kirjin nata fam, idan ta sanya kaya ko ba breziya sai su yi tamkar zasu fasa rigar saboda cika, idan baku manta ba dama fa sun gaji girman breast da kuma hips, so dukkansu kusan hakan suke, A'afia ce kawai ƴar caras a cikinsu, ita ce bata da cika sosai, amma dukkansu ba baya ba wajen cikansu.
Ganin sai kallonta yake yi ne yasa ta ɗan meke daga kwanciyar da take tana faɗin "Kallon fa?". Ɗan matsowa kusa da ita ya yi yana faɗin "Girlfriend ɗita nake kallo mana". Shiru ta yi bata sake ce mishi komai ba na ɗan lokacin, shi ma shiru ya zuba mata idanu yana kallonta.
"Yau kuma ina zaka je?". "Ina dai zamu je ko?". Hararsa ta yi tana faɗin "Ni babu in da zanje". Kashe mata ido ɗaya ya yi kamar yanda ya saba yana ɗaga jera ɗaya, cikin sanyin murya ya ce "To shikenan bari na je na shirya na yi tafiya ta". Adawo lafiya ta bashi amsa, miƙewa ya yi tamkar zai fita sai kuma ya juyo tare da manna mata sumbata a goshinta yana murmushi, yunkurawa ta yi dan ta buge bakinsa, da sauri ya wuce tamkar dama yasan zata yi mishi hakan, ko da yake dama da gangan ya sumbace ta ɗin, dan ya san bata so.
Yana fita bedroom ɗin daddynta ya nufa, kwance ya isko daddy yana tunanin mummy, yana kewarta over to over fiye da tunanin mai tunani, dan ma yana da dakiya ne da kuma jarunta yasa ya iya jure rashin ta, rashin mace kamar mummy ba kowa zai iya jurewa ba, ƴar marainiyar Allah ta iya kula da miji fiye da tunanin mai tunani, ta riga da ta kashe zuciyar daddyn da soyayyarta, baya tunanin kowa sai ita, ba zai iya jure rashinta ba, musamman ma da ya ji tana raye daga bakinsu Jehan, tun daga nan ya shiga damuwar a ina take?.
Saman bed Areef ɗin ya zauna yana ƙoƙarin fara magana sai ga ƴar diramar tasa ta shigo ita ma, dama tun da ta tashi daga barci take son zuwa ta duba daddyn nata, amma ta kasa tashi saboda kasala, sai da mijin nata ya zo ya tasheta sannan ne ta iya fitowa. Still kayan barcin ne a jikinta, duk idan ta yi taku ɗaya sai gabaɗaya ilahirin jikinta ya girgiza saboda yanayin kayan barci nata, kasa jure hakan oga fa ya yi, shi gaskiya ya gaji da dannewa, ya fara sarewa, yana son rungume kayansa suyi barci tare yana jin ɗuminta. Duk abin da suke ciki daddynta yana ganinsu, kawai ya zuba musu idanu ne yana ganin gudun ruwansu, ya san cewa Areef fa ba zai iya jurewa ba, dan fa shi ma Lion part two ne, akwai shi da jaraba sannan kuma yana bala'in sonta fiye da tunanin mai tunani, haka zalika ita ɗin ma sarai daddyn yasan ta kamu da son Areef ɗin, kawai wahalar da kansu suke yi, amma ya zuba musu ido ya ga karshen game ɗin nan nasu sai ya san abin yi, dan ba zai yarda Jehan ta rinƙa ɗaukar alhakin Areef bawan Allah a banza ba, so dole ya san abin yi idan game nan ta zo karshe gaskiya.
Kusa da daddyn ta zauna tana wani yamutse fuska tamkar wanda aka yi wa dole ta fito waje. Kasa jurewa Areef ya yi, yana son ya ɗan rungumota amma haka kawai sai ya ji nauyin daddy yau kuma, hakan yasa ya miƙe yana faɗin "Baby ki kawo mini fruits da ruwa mai sanyi ɗaki na, ki yi sauri fa!" Yana magana yana kallonta.
A hankali ta motsa laɓɓanta ta furta wata kalma ta yadda sautin ba zai fita ba, sai dai mai kallonta ya karanci me ta faɗa daga yadda ta motsa laɓɓan, baza'a kawo ba, shi ne abin da ta faɗa.
Mai da kallonsa kan daddy dake kwance ya yi yana faɗin "Uncle ka dai ji wai ba zata kawo mini ba ko?" Cikin sauri ta ce "Daddy wlh ban ce ba, ai baka ji na yi magana ba ko?".
"E to tashi ki je ki kai mashi kin ji?" Cewar daddy'n. To ta amsa tare da miƙewa tana turo baki.
Gaba ya yi ya fice daga ɗakin yana jin nishaɗi, dan dama idan bai tsokaneta ta turo bakin nan ba, kwata kwata baya jin daɗin rayuwa, ya fi so ya ga ya tasata a gaba yana mata abu tana turo baki, ba ƙaramin daɗin hakan yake ji ba.
A ɓangaren ta kuwa, Allah ya kiyaye ta aure shi take yi a cikin zuciyarta, amma idan ta tuna abu ɗaya sai ta fasa wato daddynta, shi ne duniyarta komai nata....... YARINYA KINA CEWA ALLAH YA KIYAYE KI AURE SHI, BAKI SAN CEWA MIJINKI BANE MA A YANZU.
Palon kasa ta nufa tana turo baki, kanta sam babu ɗanlwali ta saki gashin nan gwanin burgewa, kitchen ta nufa, plate ta ɗauko ta shirya mishi fruits ɗin, tun da take tare da daddynta da mummynta a Abuja, bata taɓa shiga kitchen ba sai da ta rabu da su. Haɗa komai ta yi ta ɗauka ta nufi bedroom ɗin nasa, duk in da ta taka kafa sai jikinta ya yi rawa, musamman mazaunanta da breast nata wanda bata sanya breziya ba, dan idan zata yi barci dama bata sakawa, kuma kunga bata jima da tashi daga barci ba.
Bakinta ɗauke da sallama ta shiga bedroom ɗin nasa tana turo baki irin alamar an yi mata dolennan. Baya cikin ɗakin, saman bedside drawer ta je ta ɗaura mishi plate ɗin a in da ta zauna a gefen bed nasa tana jiransa, tasan cewa ko ta tafi sai ya sake dawo da ita, dan zai ce wlh ba zai sha ko ruwan ba sai ta zo ta zuba mishi da kanta, haka daddy zai sakata ta sake dawowa, to gara ma kawai ta zauna ta jira shi. Ta yi shiru sai kallon ɗakin take yi a ranta tana yaba tsantsar tsabta irin na TRIPLETS, duk tsabtarka idan ka zo gabansu to fa tamkar kazami haka za'a ganka saboda tsabtarsu ya wuce misali.
TO BARI MU LEƘA RIMSHA DA LION WATA KILA KAFIN MU DAWO AREEF YA DAWO DAGA IN DA YA JE.
JIRGIN RUWAN💋
Zaune take a saman bed nasa, tana shirye cikin kayan barci masu tsantsar kyau farare tas, ɗaya ne daga cikin kayan da Josephine ta yi mata sayayya kwana huɗu da suka wuce kenan, kayan suna da matukar kyau, jikinsu tamkar audiga saboda laushi, kusan iri ɗaya ne da na shi.
Shi kuma yana waje yana magana da Mark, ita kuma ta kule saman bed a in da ta rufe rabin jikinta da lallausan bargonsa ta sanya Bluetooth nasa ɗaya a kunnenta hannunta na rike da wayarta a in da ta shiga cikin Vidmate tana duba wakoki.
Har zata wuce sai ta yi play ɗin wani waka, jin cewa ta san wakar ne yasa ta yi downloading nata zuwa kan wayarta, tana gama ɗaukota sai ta fita daga Vidmate ɗin ta shiga gallery, wakar ta yi playing tare da fita ta shiga kan hoton jarumin mijin nata dan ta kafe shi da ido. A hankali ta fara ɗan kaɗa kai tana ɗan bibiye wakar har aka zo wajen wata baiti. Da ɗan karfi ta ɗaga murya tana bibiye wakar tana kaɗa kai "A kanka bani jin kunya, ace na haukace a soyayya, samun irinka akwai wuya a wannan zamani duniya, a kanka zan yi komai, in bada rayuwata, kai ne jarumina....". Bata kai karshen ba juyowa da idonta da zata yi suka yi 4 eyes da shi, yana tsaye a bakin kofar bedroom ɗin, tun ɗazun ya shigo ya tsaya yana kallon yanda ta tasa hotonsa a gaba ta sanya Bluetooth nasa tana bibiye wakar. A ransa ya ce e lallai sauki ya samu ba karya, yau period nata ya ɗauke, amma har yanzu kafin ya fita daga cikin bedroom ɗin sai da ta yi mishi kukan ciwon ciki, magani ya bata kafin ya fita zuwa wajen Mark, amma kafin ya dawo har ta sami sauki ta fara bin waka.