Kenza eBookz

Triplets book 4 Complete - Chapter 15

Triplets book 4 Complete - Chapter 15

Triplets book 4 Complete Chapter 15: Triplets book 4 Complete Chapter 15. Suna tafiya su Abba suka kira jama'a, aka yi wa Dr wankar gawa irinta addinin…

3,355 words

Suna tafiya su Abba suka kira jama'a, aka yi wa Dr wankar gawa irinta addinin musulunci, sannan aka shirya shi a cikin likkafani, dan su kai shi makwancinsa kuma gidansa na gaskiya.

A takaice su Abbi suka kai shi kabarinsa, ma'ana su suka yi jana'izarsa, sai dai duk cikinsu an rasa wanda zai iya gayawa Umminsa ga abin da yake faruwa, sai faman nuku nuku suke yi, dan suna tsananin tausayawa baiwar Allah'n nan.

A ɓangaren su Imran kuwa, sun isa Kano lafiya, kuma sun haɗu da baban Muneer a companynsa, a cikin office nasa, ya yi masu iso.

Ba tare da ɓata lokaci ba Areef ya fara jefa mashi tambayoyi, sai dai Areef ɗin da kallo ɗaya zaka yi mashi, kasan yana cikin tsananin tashin hankali, duk da bai san abin da yake faruwa da Lion ba, amma a jikinsa yana jin lallai ba shakka ɗaya daga cikinsu bashi da lafiya, dan bugawar zuciyarsa sauri take yi tamkar yanda na Lion ɗin take bugawa da sauri, duk ya firgice tamkar ba shi ba, har Imran ya iya ganewa, ya tambaye shi ko bashi da lafiya ne? Ko kuma tafiyar da suka yi a mota mai tsayin ne ya jijjiga shi?.

A'a ya amsa masu da shi, sannan ya ɗaura masu da cewa, shi ai idan ya je kasar da bai sani ba, yana yin tafiya mai tsawo a cikin mota, dan ya zagaye wasu daga cikin states na garin, dama dai Aseef ne ko Lion, sune za'a ce ba lallai su iya jure tafiya mai tsawo a mota ba, dan basu saba ba, ko'ina za su je, to wlh suna zaune a cikin gida, basu fita yawace garinma bare sauran states dake makwabtaka da garin, amma shi ai yana yawo sosai abinsa, su kwantar da hankulansu, kawai dai yana jin jikinsa ba daɗi ne.

Bawan Allah bai san cewa Lion yana kwance a gadon asibiti ba, kuma kamar yanda yake kwance bashi da lafiya, haka shi ma Areef ɗin yake tafiya da ciwo a jikinsa, da alama zuciyoyinsu a haɗe take over.

Kafe masu baban Muneer ya yi a kan shi bai ma san waye daddyn Jelly ba, kallon Imran Areef ɗin ya yi, sai ya yi mashi magana da larabci a kan, su kyale shi da mutumin bari ya gyara mashi zama!.

Da baban Muneer ɗin yaga za su matsa mashi, sai ya ɗauko wayarsa ya yi ƙoƙarin ɗaura videon daddyn Jelly da ya ɗauke shi a media kowa ya gani, ya yi ƙoƙarin cin zarafin familyn Dr Salman kenan. Ganin yana latsa wayar jikinsa har wani kerma yake yi, ga shi kuma sai musa masu yake yi a kan shi bai san wanenen ma daddyn Jelly ba, sai yasa Areef a cikin tunani.

Duk cikin office ɗin, cikin Imran da Irfan babu wanda ya lura da abin da baban Muneer ɗin yake yi, shi kuma Areef ya lura da lallai ba abin arziki yake yi da wannan wayar tasa ba, dan kuwa ga jikinsa sai kerma yake yi, hannunsa sai ɓari take yi, dama haka mara gaskiya yake, duk in da za'aje a zo, baya ɓuya.

Shammatarsa Areef ɗin ya yi ya fusge wayar da karfi, har wani miƙewa baban Muneer ɗin ya yi tare da nufin ya kwaci wayar, wani irin wawan mari Areef ɗin ya ɗauke shi da shi, nan take hakwaransa biyu suke fita daga bakinsa. Tsawa ya daka mashi a kan ya koma ya zauna, idan ba haka ba, yanzun nan ya yabawa aya zaƙinta, an gaya mashi su sha'anin wasan sa ne?.

Ƙoƙarin gudu ya yi ya fita daga cikin office ɗin, Areef yana daga zaune yasa kafa ya kwashe kafafunsa, sai ga baban Muneer ya zube a kasa wanwar yana baza babbar riga, ya yi shiga ta mutunci tamkar mutumin kirki, ashe dai babbar rigar ce kawai.

"Prof ɗaure mani shi mu tafi da shi, dan jikina duk a mace, i can't do anything yanzu, ina son in je gida first, dan haka mu wuce da shi gidan kawai". Cewar Areef, yana maganar yana duba wayar baban Muneer ɗin. Ganin abin da yake cikin wayar na shirin yin posting na video a media da ya yi ne ya kara ɓatawa Areef ɗin rai, sannan ya kara mashi shakku da zargin baban Muneer ɗin a cikin zuciyarsa, idan ba rashin gaskiya ba, menene na yin yunkurin posting na video daga tambayarka ina Ayla? Da farko ma cewa ya yi shi bai san daddyn Jelly ba, to a ina ya samo wannan video kuma? Ga shi dai daddyn Jelly ne a cikin videon.

Ƙoƙarin kurma ihu baban Muneer ɗin ya yi, dan ma'aikatansa su kawo mashi agaji, sai dai ina, bakinsa ma ya yi muguwar kumbura, saboda hakwaransa guda biyu da suka fita, ga jini da yake malala kamar me, kun san hakori ba wasa ba, fitarta akwai azaba ga zubar da jini, bare ma shi da hakwaran suka fita ba shiri, dama gasu ba kyan gani, duk sun yi baki, saboda busar sigari, nan take bakin ta sunduma suntum, tamkar ruɓaɓɓen alala.

"Areef ni fa ba zai iya ɗaura mutumin nan ba, wannan aikin sai ku". Cewar Imran.

Harara Areef ɗin ya wurga mashi, da dara daran ldanun nan nasa, kafin ya ce "Prof ba zaka canza ba har gobe, ka yi auren ma baka gyaru ba?".

Shi ma hararar ya wurga mashi yana faɗin "Kai kam da ka yi auren ka gyaru ne? Ko dama akwai wanda ya ce maka aure yana gyara mutun ne? Kai ma ai gaka a yanda kake da shegen mugunta kamar Saif, yanzu kawai ka kama ka cirewa mutun hakwara da mari, dan tsabar zafin zuciya".

"Ka dai'na cewa kamar Saif, just call me Saif ɗin kawai kai tsaye, kuma ni ai ban san me auren bane shiyasa ban gyaru ba, amma kai fa? I think ma your wife has pregnant ma ko?". Cewar Areef ɗin.

"A'a Jelly bata da ciki, muna dai fatan samu, kai ba zaka dai'na saka mani ido ba ko? Wai waye ma ya gaya maka ni ma na san menene aure?".

Allah sarki shi dai Irfan, sai binsu da idanu kawai yake yi, yana ɗan murmushi, dan bashi da ta cewa, bai ma san me auren ba bawan Allah.

"Ka san aure mana, kai ne ma kasa na fara sha'awar yin auren".

"Ni kuma?". Ya faɗa yana zaro idanunsa irin na Jellyn nasa.

"Yeah kai mana, ko na tuna maka wen aka yi hakan ne?".

Ganin abin kamar wasa Imran ɗin yake yi, sai ya ce "Yeah tunan mani".

"Time da ka yi dis virgin na matar taka a gida, a time ɗin ka fara saka mani sha'awar yin aure, and then yan da kuke da matar taka, rigimammiya mara jin magana, tana baka wahala, abin yana yi mani daɗi, ina jin daɗin in ga tana wahalar da kai". Ya kai karshen maganar yana switch off na wayar baban Muneer ɗin.

"Wato Areef har gobe ba zaka canza ba ko Areef? Sai mutun ya kalli kamar baka san meyake faruwa ba, amma ka san komai, wato yanzu duk zaman da na yi da Jelly a gidan kasan komai ko?, Amma ban taɓa tunanin haka ba, sai mutun ya ganka kamar wani malamin islami, har ma jin daɗi kake yi idan Jelly tana wahalar da ni ko?".

Mikewa ya yi yana ɗan bincika cikin office ɗin ko zai samu igiyar da zai ɗaure baban Muneer ɗin, yana tafiya yana faɗin "Ni ai har abada ba zan canza ba, an gaya maka C.I.A wasa ce? Ai ni da ido ma idan naga mutun nasan ina ya dosa, just kawai kai ne ba zaka gane nasani ba, saboda already basaja a cikin jinina take, zan iya yi maka basaja kamar mace, kuma mu zauna da kai a haka".

"Da wannan murɗaɗɗen jikin naka ne zaka iya zama macen". Cewar Irfan, ya yi maganar da mamaki a kan face nasa, ya ga ne damatsan hannun Areef ɗin ma kawai abin kallo ne, sannan ga shi da tsawo da cikar halittar namiji, sannan ya ce mashi zai iya basaja a matsayin mace? Ai dole ya tambaya da mamaki a saman face nasa, dan ba gym na wasa shi ma Areef ɗin yake yi ba, jikinsa ta murɗe sosai.

"No Irfan, idan nace basaja a matsayin mace, ba ina nufin zan ɗauki kayan mata or something like that in yi amfani da su ba, you are not a C.I.A, that's why ba zaka gane ba, i mean zan iya zama da kai cikin raunin zuciya like mace, you will feel like bani da wayo, ina da raunin zuciya, and ina da ragonta, like yanda mace dai take, shi ne nufina". Jinjina kai Irfan ɗin ya yi, sai yanzu ya gane nufin Areef ɗin.

"Kai Prof waye ma ya ce ka ɗauka mani matata jiya ka tafi da ita? Na baka izini ne?". Ya yi maganar yana bubbuɗe drawers dake a cikin office ɗin na wajen ajiyar takardu.

"Waye ya ce maka ni na ɗauke ta?".

Harara ya sake wurga masu kafin ya ce "Ban samu peace of mind a daren jiya ba har sai da na bincika a motar waye ta biku, na san Lion ma ya bincika, kuma sai ka yi mashi bayanin dalilin da yasa ka kwashe mana bebs namu, ka hanamu jin daɗi".

Dariya sosai Imran ɗin ya yi, sannan ya ce "Ka ce jiya na ɓata maka harka? To ni nama san ta biyo ni ne".

"Ka dai ɓatawa Aseef harka, kuma wlh ba zai kyaleka ba, dan tun safe yake rigimar a bashi matarsa, kuma tun jiya da safe ya gaya mani ba zai kyaleta ba, idan suka dawo daga unguwa, sai ya yi dis virgin ɗinta, shi ne ka rusa mashi shirinsa ba? Zaku haɗu ne wlh, kasan halinsa, ni matata yarinya ce ai, sai ta girma, zan dai yi ta tsokanarta".

Wani irin dariyar iyashege Imran ɗin ya yi yana faɗin "Au dama haka aka yi? Kace Allah ya kuɓutar mani da sisterta, baiwar Allah, da yanzu tana can tana fama da azaba, da Aseef ya wahalar mani da ita".

"Au kai ba sister tamu ka azabtar ba kenan?". Cewar Areef

Shi dai Irfan tamkar babu shi a cikin office ɗin, shiru abinsa, sai binsu da idanu yake yi, sai da ya ji sun shigo da hirar Akila da Aseef ne ya ji zuciyarsa ta yi bakinkirin, sai ya ji dama bai biyosu ba, su kuma da alama Imran ya mance da cewa Irfan ɗin shi zai auri Akilar a baya, shi dama Areef bai san waye zata aura aka fasa auren ba!.

"A'a ni ban yi wa sisterku komai ba, ita ta ce mani tana son baby, ni kuma na bata, amma ina da tabbacin Akila bata cewa Aseef tana son baby ba, kawai zai azabtar da yarinya dan mugunta ba? To Allah ya kama shi, ta gudu ta koma gida". Cewar Imran.

Hawa sama table Areef ɗin ya yi yana ƙoƙarin kwance camerar dake a cikin office ɗin, ya ce "Jalilar ce ta ce maka tana son baby? Yarinyar da ita da kanta ma baby ce, wannan a ina zata iya renon yaro? Ita kanta yaushe ta gama kuka ana rarrashinta? Ai da ita da Rimsha ni ban san waye gwamma ba, kai dai prof ka ji tsoron Allah, ka dai'na azabtar da ƴar mutane, kada ka je ka bata ciki, wlh wahala kawai zaku sha".

"Ai jelila ba zata ɗauki ciki yanzu ba In Sha Allah, dan idan ta ɗauki ciki a yanzu, to na shiga uku, ta bakin naka ne, yanzu haka idan ta fara yi mani kuka, to sai na yi zaman rarrashi, ina ga kuma mun sami baby? Ai na shiga uku kawai, barmu dai mu cigaba da soyayya, zuwa gaba, idan ta kara girma, ta rage shagwaɓa, sai mu nemi baby, amma dai Areef kai mugun ɗan sa ido ne, waye wai ya gaya maka halin Jelly?".

Shiru ya yi bai bashi amsa ba, dan tun da yake, bai taɓa tsayawa ya yi hira mai tsawon haka da wani ba idan ba TRIPLETS nasa ba, ba shi da yawan magana, amma da TRIPLETS nasa yana magana, yau ɗin ma abin da yasa ya zage yake yin maganar, saboda yana so ne ya manta abin da take a zuciyarsa na tunanin gida, abin ya tsaya mashi a rai, so yana so ne ya ɗan rage damuwar, shi ne yasa ya biyewa Imran ɗin, ban da haka, ba zaka taɓa jin ya yi magana ta tsawon minti biyu mai kyau ba, zaka gan shi kamar bai san komai ba, amma wlh babu wani abin da bai sani ba, duk zaman da su Imran da Jelly suka yi a gidan, ya san komai, duk abin da suke yi, yana sane da komai, kawai dai baya shiga harkar kowa, kuma baya da yawan magana, shi ne yasa sam yake kamar bai san komai ba.

"Prof ka ji tsoron Allah, dama ni nasan abin da ya sa kayi aure kenan, amma kana musawa friend naka a kan ba auren kashe sha'awa ka yi ba". Cewar Areef.

A wannan gaɓar Irfan ne ya karɓi zancen da cewa "Kowa ya sani mana, auren rage zafi ya yi, amma yana musa mana, yanzu idan ba haka ba, me na hana Jelly ɗaukar ciki? Ai idan ta samu ciki ma dole zata rage shagwaɓa, kuma daga haka zata girma".

Ganin suna neman kure shi ne yasa ya ce "Ni ban hana Jelly ɗaukar ciki ba, ai ciki na Allah ne, idan Allah ya ƙaddara lokacin zuwansa, to kome zamu yi, sai ta ɗauke shi".

"Yanzu mu kenan zaka gwadawa Allah ba? To ai komai sai da sanadi, mun san Allah yake bada ciki, amma ta sanadin sex ko?" Cewar Areef....... Dama wannan magana ta rashin kunya ai sai Areef ɗin, shi da bai san kunya ba.🧐

"Ni ba zan biye maku ba, dan ni nasan gaskiyar tsananina da Jellyna, ni da yanzu gado ma daban daban muke kwana da ita".

Wani irin kallon Areef ɗin ya wurga mashi, irin kallon nan na bashakka haka ne, basu ma kwana ɗaki ɗaya ba iya gado daban daban ba, dakin ma daban daban suke, ɗan rainin wayo kawai.

Irfan ne ya ce "A'a karshe ma dai kana palo tana cikin ɗaki, shi ne karshe ba gado ɗaya kuke kwana ba".

Areef kuwa cewa ya yi "Ni prof sam ban san daga ina ka samu wannan jarabar tsiya ba, Allah dai ya bawa sister hakurin juriya".

Irfan ne ya ce "Kila dai ina ga mata huɗu zai aura, dan wannan mace ɗaya ta yi mashi kaɗan".

Allah sarki yau walaƙanci suke jin yiwa Imran, sun saka shi a gaba, bawan Allah.

Shi kuma Imran ɗin cewa ya yi "Yanzu kai Areef har kana da bakin cewa wani yana da jaraba? To aishekenan, Allah ya kwaci Jehan, dan da kake cewa sai ta girman nan ma, duk na san zance ne kawai, bari ka samu dama, hmmm na dai yi shiru".

"Irfan mata huɗu fa ka ce? A nan ku kuna auran mata huɗu kenan?". Cewar Areef ɗin. Jinjina mashi kai Irfan ɗin ya yi tare da tabbatar mashi.

Girgiza kai ya yi yana faɗin "No, we are marring only one girl, mu ko biyu ma bamu yi, Just 1 is okey, amma why zaku auri mata biyu ma? Ɗaya bata isa ba? Me zaku yi da har guda biyu? I can't share my heart to two girls, i can't share my love to two girls, is better for me to share the love and the heart with my childrens and 1 girl, so that we should get more happiness". Ya kai karshen maganar yana saukowa daga saman table ɗin, ya kammala kwance camerar.

Shi kuma baban Muneer baki sai kara kumbura yake yi, ya yi suntum, raɗaɗi da azaba sun hana shi ko motsawa.

Imran ne ya ce "Ni kai'na ba zan iya auran mata biyu ba, but most a time zaka samu masu auren mata biyu ɗin, jaraba ce ta yi masu yawa, and then suna ganin like matan ba za su iya kula da komai nasu ba, wasu kuma rashin samun soyayya daga wajen matan ne yake kaisu ga ƙara aure, wasu kuma rashin samun farinciki ne yake saka su yin wani auren".

Maimaita kalmar soyayya da farinciki Areef ɗin ya yi kafin ya ce "I think namiji shi ne yake bawa mace farinciki, i think shi ne ya kamata ya koya mata sanya shi farincikin, idan har kana sanya matarka farinciki, kana yi mata soyayya, to dole ita ma zata sanyaka farinciki, ga example a kan ni da my baby, before bata sona, amma yanzu ina mai tabbatar maka, wannan tafiya da nayi tana cikin damuwa, kuma ni na koya mata so na ɗin, ni na koya mata menene so, menene kuma farinciki, so duk abin da ka ɗaura mace a kai tun farko, a haka zata ɗaure, komai jarabar namiji, mace tana iya ɗaukarsa tsab, saboda halittarsu ce a hakan, duk yanda ka rukesu, to a haka zasu ɗaure maka har abada, idan baka bata farinciki ba, ta yaya zata baka ita ma? Idan baka kula da ita ba, ta yaya zata kula da kai? Ni ban ga wani dalili na kara aure a nan ba, is better na yi sharing love ɗina da yarana, na kuma sanyasu farinciki, seriously i love Jehan more than your expectations, then i can't share her love with other girls, she is special in my heart, bazan iya haɗata da kowa ba, dan ba zan yi adalci ba, daga kanta an gama". Ya kai karshen maganar yana ciro wayarsa dake ruri yana neman agaji.

My uncle, shi ne sunan da ya bayyana a saman screen ɗin wayar. Cool murmushi ya saki kafin ya ce "My diramati, ba zata iya rabuwa da ni ba, and then kuma ba zata barni na zauna kusa da ita ba, amma for sure zan yi maganinki". Ya kai karshen maganar tare da ɗaukar kiran.

Kamar yanda ya yi tsammani cewa ita ce ba daddynta ba, haka kuwa ita ɗin ce.

Sallama ta yi mashi cikin nutsuwa, amsa mata ya yi yana mamakin ya aka yi ta nutsu muryarta akwai girmamawa a ciki haka? Bai san cewa mum ce ta yi mata faɗa sosai ba, lokacin da ta yi mashi tsawa a palo a gidansu da safe, bayan ya saketa ta koma sama, da mum ta haura saman, zuwa ta yi ta sameta, ta yi mata faɗa sosai tare da tunatar da ita cewa, Allah yana tsinewa mace mai ɗaga murya sama da na mijinta, sannan kuma yakamata ta sani miji ba abin wasa bane, dan ta samu yana sonta, yana biyemata a duk shirmen da zata yi mashi, to wlh gara ta yi amfani da damarta, idan ba haka ba, lokaci ya kure mata ta dawo tana danasani, Areef yana da hakuri sosai, ta sani mai hakuri fa bai iya fushi ba, fushinsa bashi da kyan gani, to wlh kada ta kuskura ta kure shi, zai yi mata ba daɗi, to shi ne nasihar ta shiga kunnan ta, dama kuma da ni da ku dukka mun san tana tsananin son shi, kawai iyashege ne irin nata, yanzu ma ba wai dan nasihar mum ɗin ce tasa ta kira shi ba, a'a tsananin kewarsa ne ya takura mata har ta ɗauki wayar daddynta ba tare da saninsa ba, ta ɓuya ta kira mijin nata............. Ni ko na ce ana so ana kaiwa kasuwa, ni idan ta yi mashi walakanci na janye shi daga gareta ato, dan samun irin Areef a zamanin nan da kamar wuya, abin sai an tona, ko ya kuka ce masu karatu? In yi wuff da abina, yo meyafi ra'ina? Miji na gari a zamanin nan wasa ne?.

Gaisuwa ta ɗaga mashi cikin girmamawa. Mamaki ce tasa har ya ɗago yana kallon su Imran, tare kuma da ɗan raba wayar da kunnansa, dan ya tabbatar ita ɗin ce, shi dai yasan wannan voice nata ne, dan ko muryar kowa zai ɓace mashi, to muryar TRIPLETS nasa, daddynsa, Rimsha da kuma ita Jehan ɗin, sai gwaggo a yanzu, muryoyinsu ba zai taɓa bace mashi ba.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull