Kenza eBookz

Triplets book 4 Complete - Chapter 17

Triplets book 4 Complete - Chapter 17

Triplets book 4 Complete Chapter 17: Triplets book 4 Complete Chapter 17. Har sun kusa isa gida, kome Lion ya tuna, sai ya karɓi wayar Aseef ɗin ya turawa…

3,357 words

Har sun kusa isa gida, kome Lion ya tuna, sai ya karɓi wayar Aseef ɗin ya turawa Areef massage a kan ya tsananta addu'a sosai a duk in da yake, kada ya bari askar ta kubce daga bakinsa, dan fa akwai gagarumin matsala ba kaɗan ba.

Motarsu na yin parking a cikin gida, motar su daddyn Rimsha ma ya shigo cikin gidan, gabaɗaya familyn sun haɗu waje guda, ita ma Akilar sun ganta, ashe makwabtansu ta shiga, ta je su gaisa ne, dan kunga tun da ta yi aure, ai bata je ba, shi ne yanzu da dama ya samu, sai ta leƙasu. Ita kuma Ayla shiru, babu ita babu labarinta.

Mark yana kashe motar Lion ya fita daga cikin motar, bai bi ta kan kowa ba ya wuce cikin gida da sauri. Kai tsaye bedroom nasa ya nufa, ya sha ruwan mamakin ganin Rimsha tana zuba barci har iyanzu, kai kallonsa a kan agogon bangon dake manne a cikin ɗakin ya yi. Almost 4 to 5 hours tana zuba barci, anya barcin nan na lafiya ne kuwa? Ya tambayi kansa.

Karisawa cikin ɗakin ya yi, cikin nutsuwa ya haye saman bed ɗin, hannu ɗaya ya sanya ya tallabo kanta, sannan ya sanya ɗayar hannunsa ya shafa kyakkyawar face nata.

Cool murmushi ta saki har sai da dimples nata suka yi wani irin lotsawa mai matuƙar ɗaukar hankali. Cikin magagin barci ta fara faɗin "Kai Noorish ka bari mana". Kamar tasan shi yake taɓata.

Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya kai ɗan bakinsa ya sumbaci lallausan lips nata, sannan ya kankameta gam a kirjinsa, yana mai jin wani irin tsananin kaunarta tana ratsa shi. Ya ɗan ɗauki lokaci a hakan kafin ya mayar da ita a hankali ya kwantar, sannan ya diro kasa ya nufi toilet, ita kuma, cigaba da barcinta ta yi cikin kwanciyar hankali.

Hakika tabbas an so ɗaukar Rimshar kamar yanda Lion ɗin ya yi tunani, Malika ta ɓoyeta, ko da aka zo ɗaukarta ba'a ganta ba, Malika ta lulluɓeta da nasu siddabarun na aljanu, a gaskiya Malika tana kaunar Rimsha sosai, sannan kuma tana kula da ita sosai, sau da dama tana tare mata abubuwa da dama wanda idan ba ta gaya maku ba, ba zaku taɓa zaton ita ce ta tare ba, so ake ta karfi da ya ji a ladabtar da Lion, so suke su rufe mashi baki a kan case ɗin, so dole suna son yin amfani da rauninsa, dan su sanya ya rusina, sai dai kuma kash, dukka raunin nasa baza su taɓu ba, barema Rimsha da take tare da Malika, ba zata taɓa taɓuwa ba, sai dai idan shammatar Malikar aka yi, tun da dukka abune na tsafi da aljanun, so babu abin da ba zai iya faruwa ba.

Wanka Lion ɗin ya yi, sannan ya fito ya shirya cikin kanana kaya, wando three cuter fara kal, da T-shirt sky blue bara nauyi, bai ɗaure gashin kansa ba, ya saketa.

Wayarsa ya zo ya ɗauka a saman bed, number Areef ya sake gwada kira, still dai bata shiga, zama ya yi a bakin bed ɗin, number Mark ya kira a kan ya zo ya gyara mashi bedroom nasa, ya kwashe laptop da ya fasar nan.

Yana katse kiran ya ji saukar hannayenta a saman kugunsa ta wajen flat tummynsa, ta rungume shi ta baya, a hankali ta kwanto da kanta a saman bayansa, da murya irin na mai barci ta fara magana. "Noorish shi ne baka tashe ni daga barci ba ko?".

Nisawa ya yi, har cikin ransa ya ji sassauci na abin da yake ji, ya ji sanyi sosai, hannun nata ya riko ba tare da ya yi magana ba.

"Noorish na yi mafarkin wani waje, in gaya maka ina ne?". Tana magana kamar wadda barci bai isheta ba.

Juyowa ya yi a hankali, sannan ya jawowata ta dawo saman kirjinsa, zubawa face nata idanu sosai ya yi. Idanunta a rufe ruf take zuba surutu, sai guntun murmushi dake a saman face nata, ga dimples nata duk sun lotsa sosai, sai ta kara kyau matuƙa.

"Meesha tun da na bar gidan nan baki tashi daga barci ba?". Ya faɗa cike da tantamar irin barcin da ta rinƙa zubawa kamar ba gobe, abin da bai sani ba shi ne, Malika ce ta sakata yin wannan barci, dan da ta farka, to babu abin da zai hana Josephine bata ɗauketa ba! Saboda yanzu farautar rayuwarta suke yi tamkar ruwa mai sanyi a sahara mai tsananin zafin rana, a gefe guda, ga Queen of Daular Mutuwa tana nemanta ruwa a jallo, daga ɗayan gefen kuma, su Josephine suna nemanta ko ta halin kaka ne su ɗauketa, dan hawai su karyar da zuciyar Lion ɗin, hakan tasa Malikar ta sakata wannan uban barci kamar ba goben, har sai da ya dawo, sannan ta tafi ta basu waje, shi ne ma Rimshar ta iya farkawa.

"Noorish ban tashi ba, nifa yanzu na tashi, dama ka fita ne? Shi ne baka tashe ni na raka ba? Na ɓata da kai to". Ta kai karshen maganar tana haɗe mashi fuska, irin ta yi fushin nan.

"Open your eyes first, sai ki kalli cikin idanuna ki ce mun ɓata". Make mashi kafaɗa ta yi.

Hannu ya kai ya shafi lallausar wuyarta dake kara ɗaukar hankalinsa a koda yaushe. "Open your eyes". Ya faɗa yana gangaro da hannun nasa izuwa kirjinta.

A hankali ta waro idanun bata tare kumbura kumatu. Zubawa juna idanu suka yi, yau ɗaya ta iya dakewa ta kalli cikin kwayar idanunsa, anya ita ce ta iya wannan juriya na kallon cikin idanunsa kuwa? Anya babu sa hannun Malika a ciki kuwa? Shi ma ya ɗan yi mamakin yanda ta zuba mashi idanu tana kallon shi, babu ko kyaftawa.

"Noorish meyasameka?". Ta yi maganar tana kai hannunta a saman kumatunsa. Riko hannun nata ya yi tare da manna shi da jikin kumatunsa ba tare da ya saki ba, ya haɗe hannayen nasu waje guda a wajen, shiru bai yi mata magana ba, ita kuma sai kallon mamaki take yi mashi, taga ya yi wani irin rama ne, ita dai tasan kafin ta yi barci, ba haka ta barshi ba, ga idanunsa sun kara girma, alamar ya rame kenan.

Baki ɗauke da sallama Aseef ya shigo cikin ɗakin. Juyawa ta yi tana kallonsa, sai kuma ta yunkura zata bar jikin Lion ɗin, sai dai bai sake ta ba, yana rike da ita, yana ta kallon face nata, shi kaɗai yasan me yake ji a duk lokacin da yake kallonta.

Sam Aseef bai bi ta kansu ba, saman bed ya haye abinsa, ya kwanta tare da ciro wayarsa ya fara aikin latsawa, sai dai fa ya sha ruwan mamakin na ganinsu a manne da juna, kawai baya son ya yi magana ne, dan kada ya katse masu jin daɗinsu.

Mark ne ya sake shigowa cikin ɗakin, kallo ɗaya ya yi masu ya kawar da kansa gefe, sannan ya wuce dan ya yi aikin da ya kawosa.

"Meesha zaki raka ni ƙasar China?". Ya faɗa a sanyaye, tamkar bai san da Mark da kuma Aseef a cikin ɗakin ba.

Jinjina mashi kai ta yi tana faɗin "E zan raka ka".

Shiru ya yi yana tunanin a ina zai sami Cherish? Dan ba shakka duk yadda aka yi, tana da sa hannu a duk abubuwan da suke faru, saboda very close friend ɗin gwaggo ce, ya za'ayi daga haihuwar gwaggon shikenan ace Cherish ta ɓace? Ko dai dama ita ma ba mutun ba ce? Wannan abin da akwai ruɗani, dole ya nemo jigon haɗa wannan rikicin dukka.

Sallamar Areef ce ta dawo da shi daga duniyar tunanin da ya afka, tun da Areef ɗin ya shigo, ya tsare shi da idanu har ya kariso cikin ɗakin, a saman bedside drawer ya zauna yana faɗin "Kai Aseef momma tana nemanka kana nan ko?".

Turo baki ya yi yana faɗin "Ni ba zan je ba, kuma fushi nake yi da su, saboda sun ce wai ba zan yi punishing na Heartbeat ba, a kan me zata fita bata tambaye ni ba? Ni gaskiya ba zan kyaleta ba!".

Sake Rimshar Lion ɗin ya yi yana mai dawo da kallonsa a kan Areef dake kare mashi kallo shi ma. "Me kake zuwa yi a wajen Josephine time da kake zuwa wajenta?". Shi ne tambayar da Lion ɗin ya wurga mashi.

Miƙewa daga jikinsa Rimshar ta yi, sannan ta nufi kofar fita. Hannunta Areef ɗin ya riko yana tsokanarta "Sister yau kin mance da ni ko? Wato ma fita zaki yi kamar baki ganni ba ko?".

Katse shi Lion ɗin ya yi da cewa "Saketa ta wuce, sannan ka juyo ka bani amsa ta".

Kasa sakin nata Areef ɗin ya yi, dan shi ya ji ne ma kamar bai san wacece Josephine ɗin ba, baya son a kawo mashi maganarta, dan haka sai ya ce "Wai kai Lion ka bari mu gaisa da ita mana".

Sosai Aseef ya yi mamakin abin da Areef ɗin ya yi, shi dai a iya saninsa ya san cewa Areef ɗin yana yawan tsawatar mashi a kan kada ya kuskura ya rinƙa rungumar Rimsha, or ya kamata hannunta a gaban Lion, idan ba haka ba, to za su yi babu daɗi da Lion ɗin, dan wannan uban kishin nasa, to ya aka yi yau shi kuma Areef ɗin da kansa ya rike mata hannu, kuma har Lion ɗin ya ce ya saketa, amma yaki, anya kuwa babu wata alamar tambaya a nan?.

Shi kuwa Lion ɗin sam bai ɗauki zafi ba, saboda ya lura, yanzu koma ta halin ƙaƙa, so ake a kai shi ƙasa, so ake a rinƙa fusata shi, yana ɗaukar zafi, har ta kai ta kawo zuciyar ta kasa ɗauka, ta buga ya mutu kowa ya huta, tun da ya fahimci haka kuwa, to ba shakka zai yi taka tsantsan wajen ganin ya danni zuciyarsa ba zai ɗauki zafi ba!! Wannan shi ne yaki sunkuru, Lion dai yana faɗa da aljani, shi baya ganinsu, amma su kuma suna ganin duk wani motsinsa.

Hannun Rimshar ya riko tare da jawota ta dawo jikinsa, cikin sanyin murya ya ce da Areef ɗin "Now amsa me".

Ita dai Rimsha yau tana ganin abin mamaki, ta lura yau gabaɗaya TRIPLETS ɗin a tsai tsaye suke magana da junansu, kamar ba lafiya ba, magana suke yi kai tsaye kawai.

"Saif ni ba wani abin da nake zuwa yi gidanta face gaisuwa, shi kawai nake zuwa yi".

Aseef ne ya amsa da cewa "Ba wani gaisuwa, akwai dai abin da yake kaika, Allah gara ma ka rabu da matar nan, duk da cewa ta taimakawa Momma a baya". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa zaune yana wani yamutse fuska.

"Anywhere zamu koma Washington gobe idan Allah ya kai mu, kuma gabaɗayanmu zamu tafi, saboda mun gama abin da ya kawo mu Naija, so idan mun bar Naija, mun barta kenan har abada!". Cewar Lion.

Da sauri Rimsha ta ɗago kai tana kallonsa, da mamaki fal a face nata ta ce "Noorish to ita kuma gwaggo fa?".

Shiru ya yi bai amsa mata ba. Areef ne ya amsa mata da cewa "Da Momma da ke da my baby, Heartbeat, dukka zamu tafi da ku mana, ai ku kun sallami Naija kenan".

Zaro dara daran idanuwan nan nata ta yi, a tsorace ta ce "To daddyna da mummyna fa?".

Aseef ne ya amsa mata da "A nan zaki barsu mana".

Sam bata san time ɗin da ta furta, "Na shiga uku na! Wlh ni ba zan je ko'ina ba, sai dai ku tafi ku barni". Bata san time ɗin da ta furta hakan ba, sai da ta ga irin kallon da Lion ya wurga mata ne, nan ne ta fara tunanin wai shin me ta faɗa nema?.

Gwaggo ne ta katsesu ta hanyar shigowa cikin ɗakin bakinta ɗauke da sallama. Ita ma tun da ta shigo Lion ya tsareta da idanu yana kare mata kallo, wani irin tausayinta ma yake ji a yanzu, an cuceta ba kaɗan ba.

Da sauri Rimsha ta bar jikinsa, ta nufi gwaggon tana dariya. Rungume juna suka yi, a tare suka kariso cikin ɗakin. A gefen gado kusa da Lion ta zauna, ita kuma Rimsha ta zauna a gefenta tare da kwanto da kanta a saman kafaɗunta.

"Saif kuzo muje palo, akwai maganganu da zamu tattauna da su Abban Imran and Brr". Cewar gwaggon kenan.

Jinjina mata kai ya yi yana faɗin "Ki shirya gobe zamu koma ƙasarmu".

Har tana haɗe word wajen cewa "Wace ƙasa kuma?!". Shiru ya yi bai bata amsa ba. Areef ne ya amsa mata da kasar da ake nufi, wato Usa.

"A'a ni zan zauna a cikin ƴan uwana, ku dai ku koma, duk time ɗin da kuka sami lokaci, sai ku kawo mani ziyara".

Miƙewa Lion ɗin ya yi ba tare da ya sake yin magana ba, ya nufi waje abinsa, dan ya san babu abin da zai hana su tafi da ita, ta gama zantukanta dukka, Nigeria kam sai ta barta..........Babbar magana.

Miƙewa suka yi dukkansu suka rufa mashi baya. A palo suka isko su Abba gabaɗaya, sai hira suke yi, amma ga dukkan alamu, suna cikin matsananciyar damuwa.

Saman sofa Lion ya zauna yana kallon baban Muneer dake a tsakiyar palon, Areef ya ɗaure shi da igiya kamar ba lafiya ba, ga bakinsa a kumbure suntum. Da kallo ɗaya ya yi wa baban Muneer ɗin ya fahimci koma me wannan dai ba mai laifi bane, amma sai bai tambayi meyayi suka ɗaure shi haka ba, ya zuba idanu kawai yana kallonsu, dan shi ciwo ma kansa take masa.

Tun ɗazun Akila sai jin sautin Muryar Ablah kanwar Haroon take yi ana kiranta, tun ana kiranta daga nesa har ta ji an matso kusa, sai ta ji kamar a harabar gidan ma ake kiranta.

Mikewa ta yi tare da gaya masu tana zuwa, tana fita daga palon shikenan ɓat ta ɓace tamkar wata aljanna, an ɗauketa. To fah.

Su kuma jama'ar cikin palon, Brr Naurat ce ta yi gyaran murya tare da fara yin magana cikin dattaku da nutsuwa. Nasiha ce mai ratsa jiki ta yi wa Ummin Dr Nawid, sannan ta ce mata ko sun ɓuyo mata yanzu, gaba dole zata sani, to gara su gaya mata kawai, ta yi hakuri Allah ya yi wa Dr Nawid rasuwa.

Yadda suka yi tunanin Ummin zata ɗauki abin, sai ya zamana ba haka ta ɗauka ba, sai ma wani irin murmushi wadda da ka ganta, kasan dole aka ƙaƙalota, shi ta saki kafin ta ce "Dama ni bani na bawa kai Nawid ba, Allah ne ya bani shi, kuma duk yanda nake son shi, na san Allah ya fini son shi, ni ba zan taɓa butulcewa Ubangijina wajen yin kuka ko makamancin hakan dan ya karɓi rayuwar Nawid ba, na yi imani ya fi kowa sanin zuciyata, kuma a hakan ya ɗauki ran Nawid, ina farinciki da hakan, kuma ina kara godiya ga Allah, duk wanda bashi da yaro, ina rokan mashi Allah da ya bashi masu albarka, ni kuma ina rokan Allah daya kara mani hakuri, ina farinciki cewa ɗana ya rasu a ranar jumma'a, yanzu kawai ku kai ni naga gawarsa, zan yi mashi addu'a". Baiwar Allah, kowa yasan maganar nan ma da take yi, da kyar take fita, karfin imani ne kawai, da kuma yarda da ƙaddara, ta yarda da Allah shi ne mai yi, tana tawassuli da sunayensa tsarkaka, Allahu Akbar, a gaskiya samun uwa irinta a wannan zamani, zai yi matuƙar wahala, Imran da yake iya matsayin aboki a wajen Dr Nawid ma, sai da ya shiga tsakanin tashin hankali na wuce misali, bare kuma uwar da ta haifesa, kuma shi ne kawai ɗanta, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allah ya kara mata hakuri, a gaskiya ta nuna jarumta da karfin imani.

Sosai suka tausaya mata, kowa sai addu'a yake yi mata, ita kuma Aafia, sai da suka samu aka yi mata alluran barci, sannan ne suka sami zaman lafiya, in ba haka ba, sai buge buge take yi masu.

Brr Naurat ɗin ce ta sake shigo da maganar case ɗin daddyn Jelly bayan ta sanar da Ummi ai an rigada an kai Dr Nawid makwancinsa, sai dai su je makabartan Ummin ta ziyarce shi a can kawai.

Tambayar baban Muneer Brr Naurat ta yi, a kan shi ya ɗauki Ayla ko ba shi ba? Idan shi ne, ya dubi girman Allah ya dawo da ita, dan tana da karamin ciki wlh. Girgiza masu kai ya rinƙa yi a kan shi wlh ba shi bane, amma bakinsa bata iya yin magana, dan ya kumbura sosai.

Rimsha ce ta katse su da cewa "Nashiga uku, Ayla ta sake ɓata?! Allah dai yasa ba Daular Mutuwa suka mayar da ita ba, shikenan wlh kasheta za su yi, dama Duna ya gaya mana in dai muka kuskura muka bari muka dawo wannan gida, to wlh babu mai iya fitar da mu, wayyo mummyna!!". Ta kai karshen maganar tare da mikewa da sauri ta faɗa jikin daddynta tana sakin wani irin kuka mai tsuna zuciyar mai sauraro.

Tabbas an shafewa Rimsha tunanin Daular Mutuwa a cikin ƙwaƙwalwarta, yanzu ba ita ce ta yi maganar ba, Malika ce ta yi maganar, dan ita ta san Ayla tana can, bata da wata hanya da zata bi ta gaya masu Ayla tana can, dole sai ta hanyar shiga jikin Rimshar, saboda ita ce kaɗai ta taɓa zuwa Daular Mutuwar bayan Aylar, kuma tana son su san cewa head of the familynsu gabaɗaya wato Dr Salman yana can, shi ne yasa ta bi masu ta wannan hanyar ta shiga jikin Rimshar kawai.

Kowa na cikin palon mamakin jin sunan Daular Mutuwa yake yi, nan take Imran da Areef suka tuna da labarin da ta taɓa basu a baya, tabbas sun tuna da zancen, dan haka sai suka fara bawa jama'ar palon labarin irin ukubar da su Rimshar suka sha a wajen, shi ma daddyn Jellyn, sai a lokacin ya tuna da cewa tabbas Ayla ta taɓa gaya mashi zancen Daular Mutuwar nan, sosai abin ya dawo masu cikin kwakwalensu. Ganin hakan yasa Malikar ta fita daga jikin Rimshar, tun da sun tuna komai, sai ta kyalesu ta koma gefe kawai tana kallonsu.

Jin sunan Daular Mutuwa yasa Hjy Umaiya ta yi wani irin firgita sosai, a tsananin razane ta fara tambayar ina Akila, Akil, da kuma Imran?.

Da mamaki suke tambayarta lafiya, bata iya bawa kowa amsa ba, ita dai kawai tambaya take yi ina yaranta. Imran ɗin ne ya ce "Ammie gamu nan ai, lafiya meyake faruwa?".

Banda girgiza kai babu wani abin da take yi.

"Kai ina Akila? Ya ban ganta a nan ba?". Cewar Akil. Nan fa suka fara waige waige. Shi dai Lion binsu da idanu kawai yake yi, ya rasa meyasa gwaggo ta ce sai dai yazo anyi magana da shi, suna ta surutu suna kara mashi ciwon kai a banza.

Wasa wasa suka fara neman Akila, shiru babu ita babu labarinta, nan fa Hjy Umaiya ta birkice masu, ta yi masu karamar hauka, faɗi take yi wlh Queen ta dawo mata da ƴarta, idan ba haka ba, to a wannan karon za su yi kare jini biri jini!!.

Zuba mata idanu kawai suka yi suna kallon ikon Allah. Brr Naurat ce ta tambayi Abban Imran wai matar nan tasa lafiyarta kuwa?.

Shiru shi ma ya yi ya kasa yin magana, dan kuwa bai san me zai ce ba.

Gwaggo ce ta miƙe ta riko Ammien tana tambayarta lafiya? Wacece kuma Queen?.

Cikin kuka ta basu amsa da mahaifiyarta ce, kuma ita ce shugabar wannan Daular Mutuwar da Rimsha ta ambata a yanzu.

Daga Imran har Areef sai da suka zaro idanu tamkar idanun nasu zai faɗi kasa, irin wannan bala'i na cikin Daular Mutuwar dukka Ammie ta ce uwarta ce shugabansu? Lallai kuwa, akwai cakwakiya.

Ita kuwa Rimsha miƙewa zaune ta yi tana karewa Ammien kallo, sai a yanzu komai yake dawo mata sabo, sai a yanzu take kallon tsananin kama na Ammien da kuma Duna, hakan na nufi duna ɗa ne ga Queen? Ko kuma ɗan uwanta ne? Dan sun yi kama sosai......WATA SABUWAR CAKWAKIYA KENAN, ME KUMA YA HAƊA AMMIEN DA DAULAR MUTUWA?.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull