Kenza eBookz

Triplets book 4 Complete - Chapter 26

Triplets book 4 Complete - Chapter 26

Triplets book 4 Complete Chapter 26: Triplets book 4 Complete Chapter 26. "A lokacin da na fita gida, hotel na fara kamawa, ina shiga ɗakin nawa, na zauna…

3,348 words

"A lokacin da na fita gida, hotel na fara kamawa, ina shiga ɗakin nawa, na zauna na ci kuka na son ra'ina, a wannan rana na kwana ban yi barci ba, sai dai kuma na kudurci niyar duk wuya duk daɗi ba zan koma gida ba, ba zan sake waiwayar kowa ba, na kudurta a zuciyata zan yi rayuwata ni kaɗai'na, zan kuma tsaya tsayin daka na nemi ilimi, zan shiga siyasa, daga karshe kuma ina rokon Allah da ya bani iko da dama na samu na taimaki ƴan uwana a duk in da za su kasance, yin wannan tunani yasa ya sami karfin gwiwa, dan haka sai na tashi na yi wanka, na daura towel ɗin hotel ɗin na ɗan kwanta na huta, sai dai tunanin mummy da cikinta ya hanani sukunin, haka dai a daure ina yi mata addu'a. A washegarin ranar na nemi gida na saya, kuɗin da Mommy ta bani suna da mugun yawa sosai, da su na cigaba da yin rayuwata, na koma makaranta, na kuma fara sana'a, ko kaɗan bana tunanin komawa gida, a duk abubuwan nan da na saya kuma ko rabin kuɗin da mum ta bani ban taɓa ba, saboda kuɗin dollars ne, idan na canza kaɗan suna da yawa a kuɗin Nigeria, haka na cigaba da rayuwata ni kaɗai tsawon lokaci, ina zuwa makaranta, kuma ina juya kuɗina, akwai lokacin da ta kama dole na je gida, haka na shirya na je gidan, sai dai ban bari kunsan naje ba, takardun makarantata na je na ɗauka, a lokacin na sami mum tana zaune a garden, na tsaya tsawon lokaci ina laɓe ina ganinta, sai dai ita bata ganni ba, daga karshe na ɗauki abin da zan ɗauka na fita gidan, haka na kammala karatuna ni kaɗai na, ina kuma bibiyar ƴan uwana, ranar da aka ce daddy ya rasu, har gida nazo dan na tabbatar, amma babu wanda ya ganni, komai da yake wakana a gida ina sane da shi, har auren yaya babba duk ina sane da komai, kuma na tura mashi da gudumawata, sai dai bai san cewa ni ne na bashi ba, auren yaya Deen duk ina sane da su, har haihuwar Imran da matar yaya babba ta yi, duk ina sane, kafin haihuwar Imran ma korin Aunty Aisha da babban yaya ya yi daga gidansa duk ina sane, shi ne na je na ɗauketa, amma fa kafin na yi rayuwa da Aunty Aisha, na ruke Maik tukun nan, lokacin da naje gida dan tabbatar da mutuwar daddy, a lokacin na samu labarin cewa har da mum suka rasu, maganganun mutane ya kasu kashi biyu ne a lokacin, wasu sun ce ban da ita, wasu kuma sun ce har da ita, to ni dai da ban ganta a gidan ba, sai na ɗauko Maik muka dawo da shi gidana, ya yi rayuwa mai ɗan tsawo a wajena, ina ganin su baban yaya suka rinƙa nemansa, amma naki bayyana masu yana wajena, sai da ya ɗauki tsawon lokaci a wajena, sai tafiya ta kamani zuwa Dubai a kan harkar kasuwancina, bani da zaɓi dole na mayar da Maik gidan yaya babba, haka na shirya na ɗauke shi zuwa gidan, na bawa mai gadi shi, sannan na juya na koma, sam ban so rabuwa da Maik ba, na so na rene shi ne ya taso a hannuna, amma ba hali, da na tafi Dubai na ɗauki tsawon shekaru uku a can, a lokacin ne kuma Allah ya kara bunkasa mani arzikina, komai na taɓa kuɗi, har mamaki nake yi, abubuwa suka kara haɓaka, lokacin da Aunty Aisha ta baro gidan yaya babba ta suma a kan hanya, a lokacin ina Dubai, amma na sami labari ta hanyar security dana sanya yana yi mani gadin gidajen ƴan uwan nawa, dan ya gaya mani me yake faruwa, ina daga can nasa aka kai mani ita asibiti, satin ta ɗaya a asibiti na diro Nigeria, ni na cigaba da kula da ita na tsawon shekara ɗaya, bayan ta sami lafiya, sai na ɗauketa muka je har Washington, dan ta bani labarin abin da ya faru da ita, da muka je bamu sami waɗan da muke nema ba, sai na wuce da ita Dubai, a nan muka cigaba da rayuwarmu, ina sane da duk irin nemana da ƴan uwana suke yi, amma ko kaɗan ban ji cewa zan koma cikinsu ba, mun yi rayuwa mai tsawo a Dubai da Aunty Aisha, rabon auren Maryam ya dawo damu Nigeria, kafin mu dawo na sa an shifiɗa mana shinfiɗaɗɗen gini na alfarma, gini na gani na faɗa, muna dawowa na cewa Aunty Aisha zan je Niger in duba yanayin yanda ƙasar take, dan ina son buɗe company a can, a lokacin ina da wani aboki ɗan Niger ɗin, shi ne yake yawan bani labarin kasarsu, a makaranta muka haɗu, shi ne nace to bari naje ziyara na duba mu gani, ashe rabon auren Maryam ne ya kai ni, a hanyata muka haɗu da Shitu wanda ya kasance ɗan uwane ga ita Maryam ɗin, in takaice maku labari da na je ƙasar Niger, na so mu sauka a hotel, amma abokina ya nuna baya son hakan, ya nuna ba zai ji daɗi ba idan har ban sauka a gidansu ba, dan yana bawa ƴan uwansa labarina, iyayensa duk suna son ganina, yin hakan yasa na ce mashi to shikenan mu je gidan nasu, haka kuwa aka yi, lokacin kankanin na yi sabo da Shitu, muka zama kamar ƴan uwa, yana da kirki sosai, har muka karɓi number juna. Saukata a gidansu abokina naga karamci, suna da karamci sosai, mutanen Niger adilan mutane ne masu kirki sosai da sosai, suna da karamci over, haka suka karramani, suka mutuntani, a tare da abokina muka kwana, washegari da safe, bayan na yi wanka na shirya zamu je yawace gari da motar abokin nawa, muka shiga wajen mahaifiyarsa dan mu gaisheta, a nan na fara ganin Maryam, tana zaune kusa da mahaifiyar abokin nawa, da alama aikota aka yi, tana sanye da hijabinta har kasa, duk da cewa hijabin da kuma kayan jikinta duk a koɗe suke, amma ta yi shiga ta mutunci wanda duk wani ɗa namiji mai hankali zai sota, kuma zai yi sha'awar ta zama matarsa. Muna shigowa ta ɗaga mana gaisuwa cikin sanyin murya tana sunkuyar da kai kasa, kyakkyawar gaske ce sosai da sosai, sai dai alama akwai wahala sosai a tattare da ita, dan duk fatar jikinta a koɗe. A gaban idanunmu maman abokina ta bata sakon da ta zo karɓa a leda, ta tashi ta tafi abinta, mu kuma muka gaisa da maman abokin nawa, sannan ta zuba mana adduo'i tare da fatan alkhairi, daga nan muka fito, muna shiga cikin mota abokina ya kai mani duka yana faɗin malam ya naga sai kallon Maryam kake yi? Dariya na yi ina cewa kai kuma sarkin sa ido ba, dan Allah ƴar wacece? Ko kanwarka ce?. Bai yi kasa a gwiwa ba wajen gaya mani cewa ita marainiya ce, kuma ga in da take rayuwa, ya bani labarin komai da irin wahalar da take sha a hannun ƴan uwan mahaifiyarta da sauransu, na ji babu daɗi sosai, kuma na tausaya mata sosai, dan haka sai nace to muje gidansu, ko da muka je sai muka tarar da Shitu a gidan, shi ma ashe ya je dubata ne, ɗan uwanta ne ta gefen mahaifinta daga Nigeria kenan, na ji daɗi sosai na ganinsa, a lokacin yarinya ce sosai, dan ba zata wuci irin 13 to 14 years ba, hakan ce ta bani kwarin gwiwar naji cewa ina son na aureta, dan na tsamota daga wahalar da take ciki, kuma bata wuce shiga school ba, in takaice maku labari zuwana Niger dai shi ne silar aurena da Maryam, Aunty Aisha da kuma abokan arziki sune suka tsaya mani akan komai, da yake a lokacin ba wani ɗaukar Maryam ɗin da muhimmanci ƴan uwan nata suka yi ba, saboda rashin iyayenta, sai suka bani aurenta ba tare da bincike ko bin diddigin wanene ni ba, na auri Maryam, bayan ganina da ita na farko da wata biyar dai'dai, sannan na dawo da ita Nigeria, na kuma kaita har garin Maiduguri wajen ƴan uwan mahaifinta, dan naji labarin komai a kansa daga bakin Shitu, daga nan muka sake komawa Dubai da zama, ban yi zaman Nigeria sosai ba, mun yi rayuwa cikin tsananin farinciki, na sanya Maryam a makaranta, ta yi karatu sosai, dan tana da kaifin kwakwalwa da basira, kuma nima ina kara koya mata karatu sosai, Aunty Aisha ma tana kara mata wani duk da cewa ita ma tana zuwa ismaliya sosai a lokacin, aurena da Maryam ya ɗauki tsawon lokaci kafin mu sami haihuwa, cikin mu na farko yaron bai zo da rai ba, mun ji tsananin rashin daɗi, amma mun fawwalawa Allah komai, haka muka cigaba da rayuwar farinciki, cikinmu na biyu yana da wata bakwai ta haife shi, shima ɗa namiji ne, ya zo da rai, an saka shi a kwalba kasancewar bakwaini ne, kwanansa uku a duniya ya koma ga mahaliccinmu, munji babu daɗi, saboda mun ɗauki son duniyar nan mun ɗaura mashi, amma ba yadda zamu yi tun da haka Allah ya ƙaddaro mana, a cikin Maryam na uku ma yana da wata uku cikin ya zube, daga nan na fara shiga damuwa sosai a kan hakan, na ce sai dai muje asibiti, ko da muka je ma babu wata matsala, kawai dai Allah ne bai kawo mai tsayuwa ba, haka Aunty Aisha ta rinƙa kwantar mani da hankali, da har na fara tunanin shikenan ni ba zan sami magaji ba, a lokacin fa Hassan na ma ya yi aure, ɗansa Feroz har yana gudu ko'ina, ya girma, ga su Imran ɗin yaya babba duk sun girma, amma ni kuma shiru, abin kullum da shi nake kwana da shi nake tashi, ita ma Maryam tana cikin tsananin damuwa a kan hakan, sai dai bata bari na gane ba, kullum sai ta yi kuka, bata san ina sane da komai ba, damuwar da take shiga ne ma yake kara tsananta mani tawa damuwar, haka na cigaba da ƙoƙarin faranta mata rai ko dan maraicinta, in takaice maku sai da muka sami ciki har sau biyar dukka basu zama, wasu ta haifesu da rai su koma, wasu babu rai, a ciki na shidda ne muka haifi ƴan biyu dukka maza, kuma dukka Allah ya barɓi abinsa, shi na farkon, wato Hassan ɗin satinsa ɗaya a duniya ya rasu, na biyun kuma sai da ya yi wata biyar a tare da mu, sannan Allah ya karɓi abinsa, ni nasan mumini baya rabuwa da jarabawa ta Ubangiji, amma wlh wannan jarabawa ta ƴaƴa ya yi matuƙar girgiza mu, badan Aunty Aisha da take tare da mu ba, wlh da mun tabbaka babban kuskure, dan har cewa muka yi zamu sami wata mata mu biyata maƙudan kuɗaɗe, sai a sanya mata kwan haihuwata ta haifa mana yara ko uku ne, Aunty Aisha ce ta tsawatar mana sosai a kan hakan, a lokacin dai na bi umarninta ne kawai matsayinta na babba a kai'na, kuma ko ba komai Aunty Aisha ta nuna mana so da kauna nida Hassan fiye da tunanin kowa a lokacin da muke ƙasar Russia, amma banda haka wlh da a lokacin sam ba zan ɗauki maganarta ba, haka dai muka jure, ina ji ina gani dukka ƴan uwana daga mai yara uku sai mai yara biyu, shi babban yaya har matarsa ta haifi Imran, Akil, da kuma Akila, shi kuma yaya Deen, matarsa ta haifi Irfan, Aafia, and Umaisha har ma matar ta bar gidan a lokacin, ta bar Umaisha tana karama, Hassan matarsa ta haifi Feroz tana da cikin na biya, autanmu Maik dana rena da hannuna ma matarsa tana da ciki a lokaci, abin fa ba ƙaramin ɗaga mani hankali ya yi ba, Maryam da kanta ta ce na kara yin wani auren ko zamu sami ƴaƴan, naki yarda da zancenta, saboda bana son nayi mata kishiya, bana son kowa yazo ya takura mata, ina so ne ta yi rayuwar farinciki, ita kaɗai a cikin gidana, saboda mace ce ta gari, macece ƴar albarka, ta bani farincikin da ban taɓa tunani ba, tana da hankali da nutsuwa, ina tausayawa maraicinta, yanzu kuma ga rashin haihuwa, mun binne yara almost 7, amma shiru, a ƴan tsakanin nan muka sake samun ciki, a lokacin cikin matar Maik bai wani girma sosai ba, dan bai wuce 3 months ba, ita ma matar Hassan haka nata cikin bai fi wata uku ba, shiyasa ƴaƴan namu suka kasance shekarunsu ɗaya, sai dai ratan watanni, wato da Jalila, Anaya, da kuma Jehan kenan, sai dai fa ko da muka haifi Jehan ɗin, bamu wani jata a jiki sosai ba, dan muna ganin kamar ita ma mutuwa zata yi, amma da yake uwa da ƴa ba mai shiga tsakani, ita Maryam ta jata a jiki sosai, ni kam baya baya nake yi da ita, dan rasuwar Hussainin namu ya girgizani, na saba da shi sosai, ko ina zanje muna tare, yaro ɗan wata biyar amma ya san yawo, saboda fita da nake yi da shi, lokacin da ya rasu nasha wahala, har firgita nake yi a cikin barci ina kiran sunansa, to shi ne yasa na ki yarda na ja Jehan sosai a jikina, dan kada na sake shan wata wahala, sai da na ga Jehan ta cika shekara guda bata mutu ba, sannan ne na jata a jiki sosai, na fara nuna mata soyayya, mun so Jehan fiye da kanmu, baki ma ba zata iya faɗar adaddin soyayyar ba, haka muka cigaba da bata kulawa tamkar kwai a saman bajajjen faranti, Aunty Aisha ta fi mu nuna kula a kan Jehan, daga karshe ma haka muka hakura muka bar mata Jehan ɗin tana kwana a ɗakinta, dan ta kwace mana ita, shiyasa kuke gani a yanzu sun fi shakuwa, shakuwa ce da suka yi ta tun tile tile, ba ta yanzu bace ba, tun daga kan Jehan ɗin kuma bamu sake samun haihuwa ba har matar Hassan ta haifi Zaira, bayan haihuwar Zaira da wata ɗaya muma muka sami ciki, nan muka fara tattalin kayanmu, har Allah ya sauketa lafiya muka sake samun ƴa mace, a baya duk ƴaƴan da muka binne maza ne, yanzu kuma mata muka samu, ƴarmu ta biyu wato Rimsha, kama take da Maryam sak, while ita kuma Jehan kama take yi da ni sak, haka muka ɗauki son duniya muka ɗaurawa ƴaƴan nan namu guda biyu, muka cigaba da basu kulawa na wuce misali, sai dai sun fi shakuwa da Aunty Aisha, dan sun fi zama a wajenta, ni kuma ina kyale mata su ne dan su ɗebe mata kewar TRIPLETS nata da ta rasa, kullum maganar Aunty Aisha ɗaya idan tana yi wa su Jehan wasa, shi ne idan ta ga TRIPLETS nata, to sune mazajensu Jehan ba makawa, kuma zata yi ta addu'a a kan hakan, in dai tana raye ta gane ƴaƴan nata, to wlh ko sun yi aure sai sun auri su Jehan, kullum shi ne zancenta, a hankali hankali har ta zo ta fara dai'na zancen TRIPLETS ɗin nata, kamar wasa duk zancen ya bar bakinta baiwar Allah, haka muka rayu cikin farinciki, kullum muna waya da Shitu, shi ma ya jima da yin aure, suna da ƴarsu ɗaya Adiva, sa'ar Jehan ce yarinyar. Bamu tashi dawowa Nigeria ba har sai da su Jehan suka yi wayo, sai da Jehan ta kai primary 4 a school, wannan dalilin yasa sam basu jin Hausa, daga larabci, sai English da kuma yaren mamansu wato shuwa Arab, sai kuma kanuri da take yi masu kaɗan kaɗan, nima time to time ina yi masu fullanci, dan na koya wajen daddyna, sai dai Rimsha ce kawai ta ɗan iya fullanci, ita Jehan ko yaren mummyn nasu ma taki ta koya sosai, ita dai a barta da English, da shi kawai take magana, larabcinma sai taga daman yi, ga kafiyar bala'i, ga zafin rai, akwaita da iya tsare gida sosai, kuma dukka Aunty Aisha take zugata, ni dai bani da ta cewa, idan nayi magana Aunty Aisha ta hau surfa mani masifa, haka na zuba masu idanu, sai da muka dawo Nigeria ne na shiga harkar siyasa, da farko ina tsananin son siyasar, daga baya dana shiga cikinta, naga kazantar dake cikinta, sai naji ba zan iya ba, naso na barta, amma Maryam ta hanani, ta kuma kara mani kwarin gwiwa a kan lalllai na yi siyasa, lallai siyasa tana da bukatar mutun irina, zai tallafawa kasa ba kaɗan ba, ta dai nuna mani alfanonta sosai, na kuma gamsu, dan haka sai na sake zage dantse sosai, ina da abokan hamayya sosai, amma ban taɓa mayar da hankali nabi ta kansu ba, kawai harkar gabana nake yi, a lokacin ne Allah ya haɗani da Abubakar Salahuddeen, muka fara takun saka da shi, in takaice maku labari shi ne ya zama sanadiyar rugujewar farincikina da ni da familyna bakiɗaya, saboda na kama shi yana dillanci kayan maye da kuma mata izuwa kasashen waje, ya yi ya yi na rufa mashi asiri, dan takarar da zai tsaya, naki yarda na rufa mashi asiri, sai ya bukaci da na shigo cikin tafiyar tasu, nan ma naki yarda, to shi ne ya nemi salwantar mani da rayuwata da ta familyna, a lokacin da na shiga siyasa sunana ya fito, kamar hauka haka su yaya Deen suka yi ta nemana, har gida sun zo wajena, amma sai nece masu ni ban sansu ba, bani da wata alaƙa da su, dan haka su kama kansu, shi ma Hassan yazo har gida, naki yarda da shi, kuma sarai na san komai ma da yake tafiya a rayuwarsu, dan ina aika masu da makudan kuɗaɗe tun ina Dubai, har na dawo Nigeria ban dai'na idan suna cikin matsala ta kuɗi na taimaka masu ba, wannan shi ne labarina da abin da ya faru da ni a takaice kenan, kun san komai ba zai faɗu lokaci guda ba, amma ku ruke wannan ɗin kawai". Ya kai karshen maganar yana mai gyarawa ya kwanta, tare kuma da tada kansa da laps na Brr Naurat.

Ajiyar zuciya kowa dake cikin wajen suka sauke, Brr Naurat ce ta ce "Sannu ɗana, kasha gwagwarmaya kai ma". Tana magana tana shafa kansa.

Abbi ne ya kai mashi duka yana faɗin "Kana ji muna nemanka a lokacin, amma sai ka sheremu ko?". Jinjina masu kai ya yi alamar e ɗin ya share.

Nan fa kowa ya fara tofa albarkacin bakinsa, shiru ya yi masu kamar baya wajen. Haka suka kasance cikin tsantsar farinciki da kuma yi wa ƴaƴansu dake Daular Mutuwa addu'a.

After some minutes gwaggo ce ta ce "Ni kam wai Aseef bai dawo daga shopping ɗin da ya ce mani zai je bane?".

Daddyn jelly ne ya amsa mata da "Gaskiya fa kamar bai dawo ba, wata kila ya wuce wani wajen ne".

Da mamaki Abban Imran ya ce "Kai ba Saif ya ce kada kowa ya fita daga cikin gidan nan ba? Ya za'ayi A'isha ki barshi ya fita? Suma sojojin ya za'ayi su karya maganar Saif? Ko da yake sun fi kusa da shi, kila ya ce masu idan Aseef zai fita su bashi hanya ne"

"Hmmm yaya babba kenan, Aseef ɗan rigimar ne za'a hana fita, ai idan suka hana shi fita,to wlh gidan nan babu zaman lafiya, ni kai'na idan na ce ba zai je ko'ina ba, to babu ni babu zaman lafiya, shi ne yasa kawai na ce mashi sai ya dawo". Cewar gwaggo.

"Gaskiya kam Aseef ɗan rigima ne wlh". Cewar Abbi.

Abba ne ya tari nunfashinsu da cewa "Ni ne nan zan baku labarin rigimarsa, yaron da ya je ya tasani a gaba ya rinƙa kuka lokacin da na ce ba zan bashi auren AKILA ba, Irfan ya riga shi, hmmmm ni zan gaya maku rigimar Aseef wlh".

Murmushi gwaggon ta yi, ita kaɗai tasan me take tunawa take sakin wannan murmushi. Haka dai suka cigaba da hirarsu na tsawon mintocin kafin nan a kira sallar azzahar kowa ya watse, dan suje su yi sallah.

After some days.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull