Triplets book 4 Complete - Chapter 27
Triplets book 4 Complete Chapter 27: Triplets book 4 Complete Chapter 27. Abubuwa da yawa sun faru a cikin kwanakin nan da suka shuɗe, ciki harda neman…
3,332 words
Abubuwa da yawa sun faru a cikin kwanakin nan da suka shuɗe, ciki harda neman Aseef da su gwaggo suka rinƙa yi, amma shiru babu shi babu labarinsa, hakan yasa hankulansu ya kara mummunar tashi, nan fa suka dukufa wajen addu'a babu kama hannun yaro, suma fa sauran sojojin da suke a bakin gate, hankulansu ya yi mummunar tashi ba kaɗan ba, dan idan har Aseef baya gidan, to ba shakka sun shiga uku da Lion idan ya dawo, dan sun karya mashi doka na barin wani daga cikin family ya fita, su kuma wlh sam basu ga fitar Aseef ɗin ba, ba su san time da ya fita ba, Allah ya gani, bayin Allan sun shiga tsananin damuwa na wuce misali.
Daular Mutuwa.
Sun shafe kwanaki a cikinta suna neman ƴan uwansu, amma san basu gansu ba, duk wani part da zasu faɗa a cikin Daular, sai su ga kamar sun bar duniya, ga shi su da suke rayenma sun raba hanya, Aseef ya yi gabas, Areef ya yi yamma, sun sha matukar bakar wahala, har shi kansa Aseef ɗin ya wahala, kuma bai gane ina Fadar Queen ɗin take ba.
Areef ne ke a kan wata hanya yana tafiya, sai wuce ɗakuna da abubuwa na ban tsoro da tsafe tsafe yake yi, tunanin ina Lion yake kawai yake yi, wani irin azababben yunwa yake ji, akwai snacks and drinks a cikin jakar dake goye a bayansa, amma ya kasa saukewa ya samu waje ya nutsu ya ci ya ƙoshi, shi burinsa kawai yaga ƴan uwansa. Duk wannan wahala da yake sha, bai dai'na ambato sunan Allah ba, hakan yasa Queen ta kasa ganin wai shin a ina ma yake, ya ɓace daga idanun tsafinta, sai nemansu take yi shi da Aseef, amma ko alamar mai kama da su bata gani ba.
Ya zo dai'dai wata mararraba, hanyoyi ne suka rabu gida biyu, ɗaya ta yi gabas ɗaya ta yi yamma. A dai'dai wajen ya tsaya yana tunane tunane ya zai yi a yanzu? Shi dai ko mutuwa zai yi wlh sai dai ya mutu, amma ba zai taɓa yarda ya bar cikin Daular nan ba tare da ƴan uwansa ba. Idan ma ya ce zai bar cikin Daular ta ina ne hanyar fita?.
A hankali ya fara jin motsi ta hanyar dake kallon yamma, shiru ya surara yana son tantance motsin menene?. Jin kamar sautin numfashin mutane ne yasa ya nufi hanyar babu tsoro ko miskala zarratin a tattare da shi.
Ko da ya isa wajen sai ganin su Mark ya yi gabaɗayansu da sauran sojojin a ɗaure da sarkoki masu karfin gaske, sai dai babu Lion a cikinsu. Hamdala ya yi ga Allah, ko ba komai ya ga wasu daga cikin tawagarsu, saura su Ayla da kuma Lion, sai Heartbeat nasu, wato Aseef shalele ɗan rigima.
Ba tare da ɓata lokaci ba, cikin kwarin gwiwa ya fara ƙoƙarin buɗe kofar karfen, a rufe kofar take ruf da matakan tsaron Queen. Sai kuma me? Yana ƙoƙarin sakawa kofar karfi ya buɗe ta, kamar daga sama ya ji wani uban jijjiga da ginin ya fara yi, kafin nan ya yi wata yunkuri ginin ta rufta, kofar ɗakin ya toshe.
Hakika a wannan karon ba ƙaramar tashin hankali ya shiga ba, ya shiga ruɗu ta yadda kwata kwata baya iya gane ina ya dosa. Da sauri ya bar wajen saboda wani irin turnukin kura da ya taso, dan ma Allah yasa kofofin ɗakunan irin na karafunan nan ne masu kama da prison, so kofar ta tare ginin bai ruguzo a kansa ba.
Da sauri ya fito daga hanyar idanuwansa sun yi jajir tamkar wuta, sai wani huci yake yi, Hakika ya ji takaicin mutuwarsu Mark, har wani pat, pat, pat zuciyarsa take harba mashi, wani irin tukukin bakin ciki ne ya tokare mashi maƙoshi, da kyar yake haɗiyar wahalallen yawu, kansa sara mashi take yi tamkar zata fashi, har wani irin jiri ya fara gani.
Yana fitowa daga wannan hanya ya faɗa cikin wata tapkekiyar waje, wannan waje kuma ba ko'ina bane face wajen da su Rimsha suka taɓa zama, already dama kunsan ya yanayin wajen yake, ga faɗi da girma, ga kuma ɗakuna da yawa a cikinsu.
Zubawa wajen idanu ya yi yana kallon yanda yake, kamar daga sama ya ga dirowan mutane a gabansa. Jiga jigan matsafane masu ji da karfi, dama Queen ta turosu ne su nemo shi, tasbihi da yake yi ne yasa basu iya ganinsa ba, to a yanzu kuma ya dai'na ambaton Allah, saboda bala'in da ya shiga na ganin abin da ya faru da su Mark, a lokacin ne ma ya kamata ya ambaci sunan Allah da kyau, sai kuma tashin hankali ta hana shi, ya shiga ruɗu na ganin yanda wannan gini ta ruguzo.
Ganin mutanen yasa ya kara shiga tashin hankali, dama already bai dawo dai'dai ba.
Kafin ya yi wani yunkuri waɗan nan jiga jigan matsafa, ɗaya daga cikinsu ya sanya hannu ya sunkuce shi sama, wurgi ya yi da shi can gefe, ta fiya ya yi zai bugu da jikin wannan gunki na karfe mai kifiyoyin tsafi a jikinsa.
Tamkar wani walkiya haka Aseef ya bayyana a wajen ya tare shi, a tare suka faɗi kasa ba tare da sun isa ga wannan gunki ba. Ash suka furta a tare. Shi Aseef da Areef ya faɗo a kansa ma yana a cikin hayyacinsa sosai, shi kuma Areef ɗin saboda already yana cikin ruɗani, sai hakan ta kara gusar mashi da hankalinsa daga jikinsa, hakan yasa ya kasa koda motsawa.
Kwantar da shi a gefe Aseef ɗin ya yi tare da mikewa tsaye, a hankali ya ɗago da dara daran brown eyes nasa izuwa kan waɗan nan matsafa, sun kasance su biyarne cif, jibga jibga da su madaka karti. Kallon up and down ya yi masu kafin ya mai do da kallonsa a kan Areef dake motsi yana ƙoƙarin dawowa dai'dai.
Wani irin taunan hakwara waɗan nan matsafan suka fara yi, tare kuma da wani lankwashe kasusuwan jikkunansu, tamkar wasu macizai. Shiru Aseef ɗin ya zuba masu idanu yana kallonsu, har suka gama duk abin da za su yi, sannan suka tunkare shi da nufin su yi kutsi kutsi da su, su cinyesu ɗanye. Dai'dai lokacin shi ma Areef ya mike tsaye, ya dawo cikin hayyacinsa bawan Allah, ga uban yunwa da yake ji.
Wucewa gaba Aseef ɗin ya yi, ya tari waɗan nan matsafa gadan gadan suka fara faɗa babu kama hannun yaro. Areef ya so ya taimaka mashi, sai dai kuma faɗar tafi karfinsa, ta wuce tunaninsa, daga karshe sai ya rabu da su suna faɗar, shi kuma ya fara duba ɗakunan da suke wajen, a cikin zuciyarsa yana ta mamaki tare da tunanin a ina Aseef ya samu wannan karfi har haka, sai dai kuma a baki ya kasa furta hakan, ya kasa iya tambayar Aseef ɗin komai, sai dai kawai ya bishi da idanu, komai zai yi ba zai iya tambayarsa menene yasa ya yi ba....... E lallai da akwai cakwakiyar gaske kenan.
Binciken ɗaku nan da ya fara yi ne, a nan ne ya cikaro da Dr Salman da kuma Ayla a ɗaki ɗaya suna zauna, sun buga uban tagumi, dama idan baku manta ba, Ayla mutuniyar Dr Salman ce sosai, sun saba tun zamanta a Daular a shekarun baya, dan haka ko da ta sake dawowa a yanzu, sai kawai ta koma ɗakinsa ma da zama tun da bata da abokan hira. Bayin Allan, da kallo ɗaya zaka yi masu kasan suna cikin tsananin firgici da tashin hankali, sun wahala over, duk sun yi wani tsuru tsuru da su.
Da kallo ɗaya ya yi wa Dr Salman duk da tsufan da ya yi, ya gane cewa shi ne kakansu, dan babu in da Abbi ya baro shi a kamanni, akwai kaman ƴaƴansa a tattare da fuskarsa.
Bai ɓata lokacin ba ya faɗa cikin ɗakin tare da yi masu bayani a tsaitsaye na cewa sun zo fitar da su ne, sannan ya ce su je ba ɓata lokaci, suma basu ɓata lokaci ba wajen mikewa su bi bayansa, saboda Allah ya gani sun gaji da wannan bakar gida ta bakaken azzaluman.
Kafin su fito Aseef ya kashe waɗan nan mutane dukka, yana tsaye a harabar wajen yana aikin gyara agogon hannunsa da suka kwance mashi a wajen faɗa, ko a jikinsa, bai sha wahalar faɗa da su ba sam sam.
Nunawa su Dr Salman Aseef ɗin Areef ya yi yana faɗa masu su je wajensa, shi kuma bari ya nemo sauran jama'ar da suka zo ɗauka. Ba musu suka amsa da to, suka wuce izuwa wajen Aseef ɗin, shi kuma Areef ya sake komawa yana leƙa ɗakunan.
Suna zuwa Aseef ya rungumi Dr Salman yana faɗin "Welcome ɗan tsoho". Duk da cewa Dr Salman bai san su waye su ba a gare shi, bai hana ya rungumi Aseef ɗin ba shi ma. Yana ƙoƙarin yiwa Aseef ɗin magana ne suka jiyo muryar Areef daga ɗaya daga cikin ɗakunan dake wajen yana faɗin "Aseef come and see something".
Kallon Dr Salman Aseef ɗin ya yi. "Ɗan tsoho ku jirani a nan kada ku motsa ina zuwa". Ya kai karshen maganar tare da sakin Dr Salman ɗin, da sauri ya nufi in da suka jiyo muryar Areef ɗin.
Yana zuwa ya faɗa cikin ɗakin, sai kallonsa Dr Salman yake yi har ya kurewa ganinsa, ɗan tsoho yaga rayuwa iya ganin idanunsa, baki ma ba zai iya faɗar irin abin da Dr Salman ya fuskanta na kalubalen rayuwa ba, sai dai muce Allah ya kuɓutar da su.
Aseef yana faɗawa cikin wannan ɗaki me zai gani? Heartbeat nasa ne a ɗaure cikin wasu sarkoki. Wani irin sanyi ya ji a ransa, da sauri ya karisa gareta, Areef yana ta ƙoƙarin yanda zai yi ya kwance waɗan nan sarkokin, shi kuwa Aseef ɗin yana zuwa ya rungumota yana faɗin ya yi missing nata over. Ita kuwa tana ganinsa ta sa mashi kuka, yi take yi babu kama hannu yaro, haka ya hau rarrashi, sai gaya mashi abin da ta gani da abin da suka yi mata take yi, baya sauraronta ma, shi dai burinsa kawai ta yi shiru, amma ta kiyi sam sam, shi kuma Areef yana ta ƙoƙarin yanke waɗan nan sarkoki.
Can kuma ko me ya tuna, sai ya fara karantawa sarkokin karatun Alqur'ani mai girma, nan take suka fara kwancewa suna zubawa kasa, kan kace me sarkokin duk sun zama gari, hakan kuma tasa ɗakin ya yi wani irin haske, sannan kuma ya fara wani irin rugugi tare da surutai da wasu irin muryoyi marasa daɗin ji.
Cikin hanzari Areef ɗin ya ce "Kai Aseef da matsala fa a dakin nan, ku wuce da wuri mu fita".
Sam Aseef ɗin bai kula shi ba, ya rungume Heartbeat tasa suna kashe juna da shagwaɓa, su gabaɗaya ma sun mance a ina suke, har lokacin sai kuka take zuba mashi, shi ma ya biye mata suna wannan aiki dai da suka saba, wanda already kun san halinsu idan suka haɗu, shagwaɓa babu kama hannun yaro.
"Aseef wai ba zaka barta sai mun fita daga ɗakin ba?".
Ko ajikinsa, babu tsoro ko ɗigo a tattare da shi, cikin kwanciyar hankali ya ce "Kai Areef kasan tun yaushe ban yi kissing nata bane? Kai ba zaka bar mutun ya sakata ya wala ba, Allah ba zanzo ba sai na gama kissing nata har na ƙoshi".
Girgiza kai Areef ɗin ya yi tare da nufarsu, Aseef sai ya sa an yi masu kisan walaƙanci sannan hankalinsa zai kwanta, ban da iskanci ma irin tasa, ana ta rai waye kuma yake ta wani kiss? Ya bari su rayu mana, daga baya ayi komai, yana ganin yanda komai yake ƙoƙarin lalace masu, ga shi har yanzu basu ma san ina Lion yake ba tukunna. Yana zuwa ya ja hannun Akilar yana faɗin "Idan kika biyewa Aseef duk sai mun mutu kamar dabbobi a nan, ke daɗi masoyi ko?".
Janyota Aseef ɗin ya sake yi yana faɗin "Wai kai ka bari mana, ka sani ne ko kiss na karshe zan yi mata, idan bamu kai ga fita ba aka kashe mu kamar yanda aka kashe sauran fa? Ni ka barni na yi abinda zan yi Hai........" Bai rufe baki ba suka fara jin jijjigar ginin ɗakin, alamar suma ruguje ɗakin ake son yi da su a ciki, tamkar yanda aka yi wa su Mark kenan.
Ihu Aseef ɗin ya kurma tare da shagwaɓe murya yana faɗin "Wayyo Areef mun shiga uku, shikenan zamu mutu ba tare da Heartbeat ta haifa mani baby's ba, wayyo ni Aseef naga ta kai'na".
Wani irin harara Areef ɗin ya wurga mashi. Aseef ɗin nan mugun ɗan rainin wayo ne wlh, ji yanda yake kukan shagwaɓa kamar ba yanzu ya gama jibgan karti maza a waje ba!.
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥
*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔 ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.
*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA, INFECTION KILLER, COLACCA, SAI KAYAN GYARA PAGE. KACA KACA. YALLAGWADA. JIGIDA. RUWA RUWA. BANI BANI. WOMEN JELL BATA BATA. DAFIN KAXA. TANTABARA. XABUWA. CICCIƁI. AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER 09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH, BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️
❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)
*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*
E15
Date: 25/4/2024
Wani irin harara Areef ɗin ya wurga mashi. Aseef ɗin nan mugun ɗan rainin wayo ne wlh, ji yanda yake kukan shagwaɓa kamar ba yanzu ya gama jibgan karti maza a waje ba!.
"Areef yanzu me abin yi, ni fa wlh bana son na mutu". Ko kallon arziki Areef ɗin bai yi mashi ba, bare ya sa ran zai amsa mashi, hannun Akilar kawai ya ja suka nufi kofar fita da gudun gaske, da ya ga ba zata iya gudun bama, sai ya ɗauketa cak, shi kuma Aseef ɗin yana tsaye yana zuba kukan shagwaɓa.
Bayan Areef ya fita da Akila sun tsaya a waje ne, sai ya sauketa tare da dafa kansa yana faɗin "Dama na sani ai, Aseef our heartbeat kuma our headache, wato da gaske yana tsaye a cikin ɗakin kenan? Ya zan yi dole naje na lallaɓa shi ya fito, Heartbeat ki jirani a nan". Ya kai karshen maganar tare da juyawa da sauri ya koma cikin ɗakin.
Gabaɗaya bangon ɗakin sai ruguzowa yake yi, amma Aseef yana tsaye yana zuba kukan shagwaɓa, shi dole sai Areef ya zo ya rike hannunsa shi ma, a kan me zai kama hannun Akila kawai, wato yanzu sun fi son Akila a kan shi kenan? Shi ne fushin da yake yi.
Da sauri Areef ɗin ya dawo cikin ɗakin, hannunsa ya zo ya riko yana faɗin "Shikenan muje to". Bubbuga kafa ya fara yi yana faɗin "Yanzu ka dai'na sona, sai da ka fitar da Heartbeat shi ne ni zaka ce nazo daga baya, Allah ba zan yarda ba, ni babu in da zanje, kawai ka barni na mutu tun da kun dai'na sona........". Bai kai karshen maganar ba bangon ɓangaren hagu ta ruguzo. A dubu ɗari ya rungumi Areef ɗin yana faɗin "Wayyo daddyna, wayyo my Lion, na shiga uku zamu mutu, Areef ka ceceni bana son mutuwa".
Gabaɗaya kan Areef ya kulle, wai shin Aseef ɗin nan wani irin mutun ne? Yanzu ka ganshi cikakken jarumi, anjuma kuma ya koma shagwaɓaɓɓe na kin karawa, ji yanda yake kukan baya son ya mutu, ya zo su fita kuma ya ce bai san wannan ba, shi ya yi fushi saboda an fara fitar da AKILA, yanzu kenan an daina son shi.
Shi ma Areef ɗin rungume shi ya yi yana rarrashinsa a kan ya yi hakuri su tafi to. Bai kai ga rufe baki ba kamar daga sama ya ji Aseef ɗin ya sunkuce shi, ya ɗaga shi sama sun yi waje a guje. Suna fita ɗakin ya rufta mai gabaɗaya.
Bai sauke ɗan uwan nasa a ko'ina ba sai a kusa da Akila dake tsaye tana faman sharar kwallah. Mamaki ya hana Areef ɗin yin wani kataɓus, yau kuma ko a ina Aseef ya samo karfin ɗaukarsa kamar ɗan baby kuma oho? Abin mamaki baya karewa.
Shi kuwa Aseef ɗin yana sauke Areef ɗin sai ya faɗa jikinsa yana mai cigaba da kukan shagwaɓarsa kamar ba shi ne yanzun nan ya gwada wata zazzafar jarumta ba.
Ture shi Areef ɗin ya yi ya nufi wajen su Dr Salman yana faɗin "Heartbeat dama kayanki ne, kin fi kowa sanin halinsa a yanzu, sai ku fama, ki rarrashe shi, ni bari na nemo maku hanyar fita daga wannan bakin kazamin gidan, ku fita, idan ya so zamu biyoku daga baya". Ya kai karshen maganar dai'dai lokacin da ya karisa wajen Dr Salman.
Matsowa Akilar ta yi ta faɗa jikin Aseef ɗin tana mai cigaba da zuba mashi kuka babu kakkautawa. Rungumeta sosai ya yi tare da dai'na nashi kukan ya hau rarrashinta, ta tsorata sosai baiwar Allah, ta sha wahala, duk ta fita a hayyacinta, a haka ma fa dan tana matsayin jika ga Queen ɗin kenan, ba dan haka ba, da sai yaya? Taga kaɗan daga cikin abubuwan da Rimsha ta gani, a gaban idanunta aka fasa cikin wasu mutane biyu aka ɗebi wasu abubuwa, a gaban idanunta aka shanya gawa kamar busasshen kifi, a gaban idanunta aka yi abubuwa da dama, ita ma dan Allah yasa tana da tsawon kwana ne, da ita ce a kan layi yanzu, ba dan zuwansu Aseef ba, to da ba makawa ba zata kai gobe ba.
Areef kuwa magana ya fara yi da Dr Salman a kan ko ya san wani abin dangane da gidan nan. Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "Na shafe shakaru sama da talatin da uku a nan, amma har yau ba zan iya ce maka ga takamaimen abin da suke yi ba bayan kashe mutane da ɗibar jini da wasu sassa na jikin ɗan adam, sannan har yau ban taɓa ganin gini na farko ko kuma na karshe na wannan gida ba, sai dai kuma, na san da akwai wata hanya da Duna ya taɓa gaya mani, ya ce ko bayan sun ɗauke shi, idan zan iya na bi wannan hanya zan tsira daga wannan gida, sai dai kuma hanyar tana da haɗari, sannan tana da nisa sosai, kuma a karshen hanyar da kawai kofa da zata fitar da kai waje gabaɗaya, bayan hanyar da su Rimsha suka fita, wannan ita ce hanya ta biyu ta sirri a cikin gidan, sannan ya ce mani idan har ina tafiya a kan wannan hanya, to kada na juya baya, komai zan ji na tafi kawai, abin da yasa ban fita ba, saboda komai ya kare mani, ina jin ko nafita bani da kowa a duniya, kuma ya ce hanyar tana da tsawo sosai, so ba zan iya doguwar tafiya ba, ni kaɗai ne kuma, dan a lokacin, sun ɗauki mai taimaka mani ɗin, wato Mustapha, shi ne mai taimakona dama, to sun rabani da shi, sun mayar da shi cikinsu, suna can suna ƙoƙarin juyar da shi izuwa nasu, a halin yanzu ma ina ga sun mayar da shi ɗaya daga cikinsu ɗin, wannan dalili yasa na ce gara na cigaba da zama a nan ɗin kawai har ranar da rai zata yi halinta".