Triplets book 4 Complete - Chapter 28
Triplets book 4 Complete Chapter 28: Triplets book 4 Complete Chapter 28. Shiru Areef ɗin ya yi yana jinjina wannan al'amari na Dr Salman, abin gwanin ban…
3,375 words
Shiru Areef ɗin ya yi yana jinjina wannan al'amari na Dr Salman, abin gwanin ban tausayi, shekara ɗai ɗai har talatin da uku a cikin wannan bakin azzalumin gidan? Gaskiya Queen ta azabar da bawan Allah nan, ko da ace iya ajiye shi kawai ta yi, bata yi mashi komai ba, wlh masifar da yake gani wanda suke aikatawa kawai ya isa ya kashe shi idan da kwanansa ta kare, Allah sarki, da Allah ya ƙaddara kwanansa na gaba, shi ne har ya kawo iyanzu duk da irin masifu da yake gani, Allah ne kawai zai bi masu hakkinsu, dan kome aka yi wa Queen a yanzu, wlh ba'a biya ko mutun ɗaya abin da ta yi mashi ba, yanzu a kalla ba'a akasaraba wannan Daular Mutuwar ta haura shekaru hamsin da kafata, sai Allah ne kaɗai zai iya kiyaste rayukan da aka salwantar a cikinta, ya ilahi ya lillahi.
Rugujewar sauran ɗakunan dake gefe da gefensu ne ya dawo da Areef ɗin daga duniyar tunanin da ya afka, da mamaki ya ɗago kai yana bin ɗakunan da kallo, sai rugujewa suke yi tamkar waɗan da ake jijjigewa. Anya lafiya kuwa? Areef ɗin ya tambayi kansa. Aseef kuwa kara kankame Akila dake kankame da shi gam ya yi, saboda tsoro, ta tsorata ne da ganin yanda gine ginen suke jijjigowa da kansu, sai ruguzowa suke yi, tamkar katafila ce take watsi da su.
"Aseef let's go, saboda ina ganin gabaɗaya ruguje arean nan ake son yi, so tsayawarmu a nan babban haɗari ne, ka kawo Heartbeat ta tafi da su baba ta hanyar da ya gaya mani yanzu, zamu cin masu a hanya idan mun gane a in da Lion yake". Cewar Areef kenan.
Kankameta ya kara yi yana faɗin "No Areef su baba ɗin su je kawai, ita Heartbeat tana nan tare da ni". "Aseef ba da wasa nake yi ba, kada ka yi ka salwantarwa da yarinyar nan rayuwa, ka barta ta bisu". "Nima ai Areef bada wasa nake yi ba, babu in da zata je, muna tare da ita".
Dr Salman ne ya sa baki ta hanyar cewa "Jikana da ka bari mun yi abin da ɗan uwanka ya ce, dan wannan gida ya wuci tunaninka".
"Baba ni fa ba zan rabu da Heartbeat ba, ai dama ta ce zata soni komai wuya komai daɗi, kuma idan ma aka bata zaɓi a kan mutuwa, to zata zaɓi mu mutu a tare, dan haka kunga ita already a shirye take da ta mutu a tare da ni, please kada ku dame mu, ko ba haka ba Heartbeat?". Tana daga kwance a saman kirjinsa ta amsa mashi da cewa "Haka ne, a tare zamu mutu".
Girgiza kai kawai Areef ya yi, waɗan nan sun yi nisa, sam ba zasu ji kira ba, idan ka biyewa Aseef sai ya sanyaka hawan ruwa ba na jini ba.
Tsananin jijjigar da gine ginen wajen suke yi ne yasa suka dawo cikin hayyacinsu, da sauri Aseef ɗin ya riko hannunta tare da raba jikinsu, cikin hanzari ya nufi su Dr Salman ɗin yana faɗin "Wayyo Areef menake ji da gani haka? Kada fa waɗan nan gine gine dukka su faɗo mana a kanmu, ya kamata mu gudu, dan ni dai gaskiya ban shirya mutuwa a yanzu ba, sai na sami magaji tukun nan........" Bai gama rufe baki ba gine ginen suka fara ruguzowa tamkar waɗan da karapila take jijjigewa.
Cikin hanzari da zafin nama suka yi maza suka fara ƙoƙarin barin wajen. Dr Salman ne ya nuna masu hanya, a in da suka bi ta wata kofa dake ta yamma. Suna tafiya da sauri sauri, gine ginen ɗakunan bayansu na rugujewa kamar ba lafiya ba.
Ganin Ayla zata basu matsala ne yasa Areef ya sauke jakar bayansa, a in da ya dawo da jakar ta gaba, sannan ya goya Aylar a bayansa, dan ba karya ta galabaita iya galabaita, ta sha bakar wahala, da kyar baiwar Allah take iya jan kafafunta, hakan kuma zai sanya har gine ginen su ruguzo a kansu ba tare da sun fita daga wajen ba, shi ne yasa Areef ɗin ya goyata, shi ma Aseef goya Akila a bayansa ya yi.
Sun yi tafiya mai nisa kafin su cikaro da wani ɗaki, ƴan mata guda uku ne rufe a cikin ɗakin, buɗe masu kofa Aseef ya yi, duk da basu san su ba, amma sun taimaka masu. Haka suka cigaba da tafiya, duk wani ɗaki da zasu gani, in dai da akwai mutane a ciki, to sai sun buɗewa mutanen, su ce su biyo bayansu, tun suna su kaɗan, har suka kai kusan su 40 a wannan tafiya tasu, har a lokacin kuma basu cinma wannan hanya da Dr Salman yake son nuna masu ba, wanda kuma ta nan ne kawai za su bi su fita.
A can gida kuma, abubuwa sai ƙoƙarin rikece masu yake yi, yau da wani irin azababben zazzaɓi Rimsha ta tashi, ga tsananin ciwon kai, tun safe take zuba barcin wahala, har misalin karfe 4, shi ma sai da gwaggo ta ga barcin ya yi yawa, sannan ne ta tasheta.
Tana tashinta sai kuma me? Wani sabon tashin hankali suka afka, dan kuwa Rimshar tana tashi ta fara tambayar gwaggon wacece ita? Babbar magana. Zaro idanu waje sosai gwaggon ta yi, idanuwan nata tamkar za su faɗi kasa, cike da mamaki a samar fuskanta ta ce "Rimsha ni yau kuma kike tambaya wacece ni?".
Wani irin harara ta watsawa gwaggon da waɗan nan dara daran fararen Sleeping eyes ɗin nata, ta ɗauki tsawon a kallah minti biyar kafin ta amsa mata da "E mana wacece ke? Kin wani zo ki zaunawa mutane a waje".
Shiru gwaggon ta yi, ta rasa me zata sake ce da Rimshar. A haka Brr Naurat ta shigo ta samesu. Da mamaki take tambayarsu lafiya suka yi wani cirko cirko da idanu haka.
Nisawa gwaggo ta yi tare da gyara zamanta, sannan ta ce "Mummy wai Rimsha ce take cewa bata sanni ba yau kuma".
Murmushi kaɗan Brr ta saki tana faɗin "To kin dai san halin masu ciki, wata kila yau kuma da irin halin da ta tashi kenan, ai sai ki rabu da ita ki kama wani abin ko? Idan lokacin da ta dawo dai'dai ya yi, sai ki zo ki yi mata maganar da dama zaki yi mata ɗin". Ta kai karshen maganar tare da zama a gefen bed ɗin.
Hakika dukkansu basu ɗauki zancen Rimsha na cewa da ta yi bata sannu ba da mahimmanci, gani suke yi dukka shirmene da kuma laulayin ciki, ita kuma ba wani shirme, har ga Allah da gaske take yi, bata sansu ba, gabaɗaya ƙwaƙwalwarta an ɗauke shi ne aka kifa shi, ta mance da komai na rayuwarta, da kuma kowa, ita kanta ma ta mance da ita wacece. Tashin sense!!.
Komawa ta yi ta kwanta tana wani irin ɓata rai tare da ɗaure fuska sosai. Daga gwaggon har Brr Naurat ɗin babu wanda ya sake kulata a cikin ɗakin, da haka barci ya sake yin awon gaba da ita, yau tun da ta yi sallar asuba, bata sake yin wani sallah ba, dan ita kanta bata san wacece ita ba bare ta san cewa ita musulmace ko Kristar, wannan shi ne tashin hankali, to meyasameta kuma? Wanene ya juyar mata da tunani? Meyasa aka yi mata hakan?. Ku kasance da Alkalamin FATEEMA ZAHRA MUSA, PRINCESS TEEMA, alkalamina ne kawai zai iya warware maku wannan cankwakiyar.
Hira Brr Naurat da gwaggo suka fara zubawa, ita kuma Rimsha ta mayar da barci. Baki ɗauke da sallama Jehan ta shigo cikin ɗakin.
Saman bed ɗin ta haye tare da tada kai da laps na gwaggo, da kallo ɗaya zaka yi mata kasan cewa tana cikin tsananin damuwa, har ƴar rama ta yi, ta yi wani fiki fiki da ita, tamkar ba Jehan D.P.O kuma jarumarmu ba.
Shafa kanta gwaggon ta fara yi tana faɗin "Babyn daddynta waye kuma ya taɓo mani ke?".
Tamkar jira take yi a yi mata tambaya, sai kawai ta sa kuka, hawaye wani na bin wani, Allah mai iko, yai Jehan ce take kuka da hawayenta? A lallai abu ya yi tsamari.
"Subhanallahi, Jehan lafiya kike kuka?". Cewar gwaggon. Brr Naurat ma dai abin da ta tambaya kenan, lafiya take kuka?.
Cikin kuka ta fara magana kamar haka "Gwaggo ko na kira number Yah Areef bata shiga, kuma yau tsawon kwanaki fa basu dawo ba, babu wani zancensu ma, ni na rasa ya zan yi, wlh kirjina ciwo yake yi mani, please gwaggo ki ce ya dawo, ba zan iya ba..........." Kasa karisa maganar ta yi, saboda wani kuka daya kubce mata. Soyayya muguwar wasa, ta yi mata mummunar kamu, Allah sarki baiwar Allah, ba zata iya jurar rashin shi a kusa da ita ba.
Rarrashinta gwaggo ta fara yi, yau ga uwar miji tana rarrashin matan ɗanta a kan matar tana kewar ɗan, Allah mai iko, abin mamaki dai baya karewa, sam babu kunyar gwaggo a tattare da Jehan, babu wani abin da ya sauya a yadda suke da, ita bata yi mata ma kamar gwaggonce ta haifi TRIPLETS ɗin ba, ita dai iya abin da ta sani shi ne, Gwaggo, gwaggonta ce, kuma abokiyar rigimarta, ta zuba mata shagwaɓa san ranta, ita kuma gwaggon ta biye mata, bayan haka ita bata wani san da cewa ana jin kunyar uwar miji ba.
Da kyar da suɗin goshi gwaggon ta samu ta shawo kanta, da kyar ta yi shiru, ta hakura ta dai'na kukan, sai dai fa na ciki na ciki, kewar dai babu abin da ya ragu, har wani zazzaɓi take ji.
Haka suka kasance har Anaya ma ta shigo ta same su, ita ma nata sabon babin kukan ta zo ta buɗe masu, yau dai suna ganin ikon Allah, haka suka fara rarrashinta ita ma, har sai da ta hakura ta yi shiru, daga haka kuma barci ne ya yi awon gaba da ita. Ba su suka farka ba har sai da gwaggo ta tashe su a kan lokacin sallar mangariba ta yi, su tashi su yi sallah su yi wa mazan nasu a addu'a. A nan ne Gwaggo ta ga abin mamaki abin al'ajabi. Wannan abin mamaki ba komai bane face Rimsha, tana tashi ta barci da aka ce ta je ta yi sallah, buɗar bakinta sai cewa ta yi menene kuma Sallah? Babbar magana.
Zaro idanu suka yi, gwaggon zata daka mata tsawa, Brr Naurat ta yi saurin dakatar da ita, saboda ta lura tamkar da kawai matsala a tattare da Rimshar, abin ku da manya, ƙwaƙwalwarsu da tunaninsu ba irin na yara bane, har ta harbo da akwai gagarumin matsala a tattare da jikar tata, wanda su gwaggon kuma basu gane ba.
Dan haka sai ta ce kowa ya je ya yi sallah, ita kuma Rimsha ta kwanta ta cigaba da yin barcinta, su kyaleta kada su sake yi mata magana. Da mamaki cike fal a fuskar gwaggon ta ce "Mummy sallah fa zata yi, kuma kice a barta kada ta yi? Ya haka kuma? Ai Rimsha yanzu idan ta ce ba zata yi sallah ba, to wlh da itace zamu karya mata kafa, dan ai ba yarinya bace tun da har da ciki a jikinta, uwa fa take shirin zama".
Jama'a ina ganin ikon Allah, karfi da ya ji gwaggo ta mayar da Rimsha mai ciki, ko me ta gani a jikinta da har ta dage a kan lallai ciki ne da ita? Ku tayani dubawa my readers, ita dai Rimsha bata taɓa yin sunna da Lion ba, har yanzu virgin ce ita, amma an zage a kan tana da ciki, to koma me dalilinsu na cewa hakan, lokaci zai nuna mana komai.
"Aisha tun da na ce ku bar Rimsha, to ku kyaleta kawai, idan kika cika matsawa, to ba makawa zaki tabka danasani mai girma, dan haka ku kyaleta ki je ki yi sallarki". Cewar Brr Naurat.
Okey kawai gwaggon ta amsa mata da shi, sannan ta miƙe tsaye tare da nufar toilet, ita kuma Brr Naurat ta karisa tashin su Jehan a kan su je su yi sallah.
In takaice maku wannan labari, Rimsha dai bayan wannan uban barci, to bata iya aikata komai, ko wanka bata yi, baiwar Allah, sai Allah ne kaɗan yasan menene matsalarta!.
Haka Brr Naurat ta rinƙa lallaɓata tana ririta ta, sai dai kuma ba abin da take cewa face su gaya mata su waye su? Bata sansu ba. Abin ya ƙullewa gwaggo kai, ita kuwa Brr Naurat sam bata damu ba, dan izuwa yanzu ta gama yardanwa kanta cewa jikar tata ba lafiya take ba, da akwai gagarumin matsala a kasa, hakan yasa bata wani damuwa.
Su Abba kuwa, suna can hankalinsu a tashe, sai adduo'i suke yi tare da bincikar ina Aseef, securitynsa Abban Imran ya kira a waya, ya sanyasu suka je suka shigar da report a kan ɓatar na Aseef, su kuma suna gida Lion ya hana fita.
A ɓangaren Aafia dai babu wani sauki, sai ma abin da ya cigaba na rashin lafiya, duk ta kara ramewa, ta bushe sosai, ta yi wani irin duhu mai munin gaske, abin gwanin ban tausayi, kuma har yanzu bata amsawa kowa komai, daga ido sai ido.
Akil, Imran da Irfan gabaɗaya tarewa suka yi a masallaci suna zubawa TRIPLETS addu'ar fatan nasara a tafiyarsu, Allah ya karesu ya dawo da su lafiya.
A ɓangaren Katsina gidansu Sadiq kuwa, Allah mai iko, shagon Yusuf dai sai kara bunƙasa take yi, yanzu har da fridge ya sanya a ciki, yana sayar da kayan sanyi, abubuwa sun cigaba, shi ma Sadiq Alhamdulillah, abubuwa suna tafiya mashi yadda ya kamata, sai dai kuma kullum yana cikin tunanin Jehan, bawan Allah, yana tsananin sonta, bai san cewa matar wani ce a yanzu ba. Maman Sadiq a yanzu abubuwa sun saukaka mata, girkinta har da nama da kifi, sau uku take girki a rana, gabaɗaya ta fita daga harkar baban Sadiq ɗin, dan dama baya tsinana mata komai, yanzu Allah yasa ƴaƴanta sun fara tsayuwa gam da kafafunsu, abu dai sai dai muce Alhamdulillah, wani lokaci har kaji biyu Sadiq yake sayo mata, ya yanka mata, ta gyara masu, ta zuba mashi miya mai shegen daɗi, Allah ya taimaketa ya bata ƴaƴan masu zuciyar nema da kuma zuciyar taimaka mata dukka biyu, dan wani yaron yana da zuciyar nema, amma kuma kuɗinsa bata ciwuwa, ba zai taimaka ba, ita dai ta yi sa'a, daga Sadiq ɗin har Yusuf ɗin burinsu kawai suga sun yi mata abu, su ganta a cikin tsananin fariniki suna kyautata mata, shi ne muradinsu, kuma hakan ce tasa Allah yake taimaka masu, komai suka saka a gaba, sai sunga dai'dai, dan uwa ba wasa ba!!! Uwa ba wasa ba!!! Uwa ba wasa ba!!! Ku ruke wannan da kyau, duk mai son yaga dai'dai, to ya sanya mahaifiyarsa farinciki, ko da iya murmushi kawai kasanya mahaifiyarka a rana, to ba makawa wannan rana ba zata wuce ba har sai wani abin alkhairi da zai sanyaka farinciki ya wanzu a gareka, bare kuma ace ka yi wa mahaifiyarka abin da har zata buɗe baki ta zuba maka albarka da ruwan adduo'i, haba ai ranar abin alkhairi da zaka fuskanta sai Allah ne kawai zai san adadinsa, ina mai kara jan hankulanku ƴan uwa, a kula da uwa, abi umarninta koda babu daɗi matuƙar bai kaucewa dokar Allah ba, hakan zai sanya muga dai'dai a dukkan al'amuranmu, mu jikanta, mu tausaya mata, iyayenmu sun yi mana komai a duniyarnan, komai muka yi ba zamu taɓa biyansu ba! Sai dai mu kwatanta iya abin da zamu iya sanyasu farinciki kawai.
To haka dai rayuwar su Sadiq take a yanzu, shi kuma baban nasu, gaula wanda ya rako maza duniya, yana can har iyanzu yana tare a gindin amarya, sai yadda ta ce haka za'ayi, yadda ta dama haka zai sha, naira na aiki, duk zaginsa da ƴan unguwa suke yi, wlh ko a jikinsa, haka Amarya zata yi mashi ɗinki, ko kunya baya ji zai saka kayan a jikinsa yana washe baki, Sadiq bakinciki kamar ya haɗiyi zuciya ya mutu, yana ji yana gani idan baban nasa ya yi wa Amaryar ba dai'dai ba, a tsakar gida zata kwashe mashi duk wasu albarka dake a tattare da shi, ta tsine mashi, ta yi mashi zagin kare dangi, amma dan rashin zuciya, zuciya ta mutu, haka zai yi ta bata hakuri, kuma bata hana shi ya sake komawa gindinta ya tare, abin dai ba'a cewa komai, Sadiq dai ba dan mamansa ba, da yaronnan ya haɗiyi zuciya ya mutu, saboda kunci da bakin cikin irin wannan hali na babansa, yarinya karama kamar amaryar nan da bata wuce sa'arsa a wajen shekaru ba, ta tsaya tana cin mutuncin mahaifinsa, ai kunsan dole zai ji zafi, dan fa uba uba ne komai lalacewarsa, Allah Ubangiji ka bawa kowa iyaye masu zuciya, masu sanin yakamata, masu sanin darajar kansu, masu sanin mutuncin kansu, ba masu kwaɗayin duniya ba, Allah ka karawa namu muku iyayen lafiya, ka kuma saka masu da mafificin alkhairi.
Wannan shi ne rayuwar su Sadiq kuma. Idan muka dawo Kaduna kuwa, bayan sallar issha, Brr Naurat ce ta taka da kanta har izuwa part nasu daddyn Rimsha.
A lokacin suna tare da mum suna hirar duniya. A palo ta zauna tare da yi masu sallama. Jin cewa ita ce yasa dukkansu har su Abba basu ɓata lokaci ba wajen fitowa. Da mamaki suke kallonta har suka kariso izuwa in da take, a saman sofa kowannansu ya zauna, sai binta da idanu suke yi, suna jiran karin bayani.
Ta ɗan ɗauki mintina da a kallah za su kai biyar tana tunani ba tare da ta yi magana ba. Can kuma sai ta fara magana a nutse. "Nawazuddeen a gaskiya Rimsha tana cikin gagarumin matsala, kuma ga halin da muke ciki a yanzu, babu wanda aka yarjewa ya shiga gidan nan ko ya fita sai su Imran, Akil da kuma Irfan, suma dan tarewa da suka yi a masallaci ne, amma yana da kyau mu san matakin da zamu ɗauka, ba zai yi wu mu barta a cikin ciwo har haka ba, babban tashin hankalin ma shi ne rashin sallah, ba zai taɓa yiwuwa mu barta bata sallah ba har zuwa su Saif su dawo, dole kafin su dawo mu san abin yi". Ta kai karshen maganar tana jan doguwar numfashi tare da saukewa a hankali.
Har suna haɗa baki wajen cewa "Me kuma yake damunta?".
Nan ma shiru Brr ɗin ta ɗan yi, sai jinjina al'amarin a ranta take yi, abin ya bata mamaki kuma ya ɗaure mata kai. "To bana ce ba, amma yanzu abin da za'ayi kuzo muje ku yi mata karatun Alqur'ani mai girma, ko Allah zai sa a samu sassauci, dan fa ikirari take yi ma na cewa ita bata sanmu ba, mun ce mata to shikenan mun ji bata sanmu ɗin ba, kuma mun yarda, amma ta tashi ta yi sallah, shi ne ta ce bata san shi ba, kunga kuwa ai akwai gagarumin matsala, da farko ma na ɗauka dukka laulayin cikin nata ne yasa ta ce bata sanmu ba, amma da ta ce bata san menene sallah ba, sai na fahimci ba batun laulayin ciki bane, wata matsa ce ta daban".
Shiru daddynta ya yi yana tauna zantukan na Brr, shi kuma Abban Imran cewa ya yi. "Gaskiya wannan matsala ce babba, bata san me sallah ba kuma? A dole mu nemi mafita, yanzu dai ina take? Muje sai muga me yakamata mu yi mata".
Haka suka rankaya izuwa ɗakin gwaggon, suka baro su mum ko wacce a ɗakin mijinta, bama su san me yake faruwa ba.
Har lokacin barci Rimshar take yi, tun abincin safe da ta ci, ƴar tahalikan nan bata sake sanya komai a cikinta ba, ko ruwa, da alama ciwon bayan ta yi breakfast ne ya bugeta, dan ba shakka ta yi sallar asuba lafiya lou.
Tana barci basu tasheta ba, dan Brr ta ce kada a tashe ta, su yi mata addu'ar a haka, dan haka sai suka fara yi mata topi ta ko'ina, duk suka haɗu a kanta. Ko motsawa bata yi ba, tamkar wadda babu rai a jikinta, ba dan sauƙar numfashi kaɗan kaɗan da suke ji nata ba, to da sai su ce babu rai a tattare da ita.