Kenza eBookz

Triplets book 4 Complete - Chapter 37

Triplets book 4 Complete - Chapter 37

Triplets book 4 Complete Chapter 37: Triplets book 4 Complete Chapter 37. A ɓangaren Lion kuwa, a cikin waɗan nan kwanaki uku da suka wuce, ya aikata…

3,311 words

A ɓangaren Lion kuwa, a cikin waɗan nan kwanaki uku da suka wuce, ya aikata abubuwa da dama, ciki kuma har da rubuta takardar ajiye aikinsa na soja da ya yi, wannan abin ya yi mugu mugun ɗagawa jama'ar kasar hankali, saboda Lion soja ne wanda kowace kasa take buƙatar jarumi kuma jajirtartce irinsa, tsayayye namiji ne kuma jajirtartce a kan aikinsa, yana da adalci da gaskiya, ga rikon amana, babu zancen cin hanci a lamuransa, kuma babu ɗaga kafa a wajen yanke hukunci, ko kai ɗan uban waye idan ya kamaka da laifi, ba shakka sai ya hukuntaka, babu uban da ya isa ya taka mashi burki, ko his excellence baya ɗagawa kafa, kaifi ɗaya ne shi, babu mai iya tankwara shi, rashinsa a hukumar soja babbar ci baya ne ga kasar U.s gabaɗaya, yana da matuƙar farinjini, al'umma suna tsananin kaunarsa saboda gaskiyarsa, da sama masu kwanciyar hankali da cigaba da yake yi, kowa begensa yake yi, jin cewa ya ajiye aiki yasa wasu har suma sai da suka yi, saboda shiga tashin hankali, wasu kuwa har da rashin lafiya, kowa sai tambayar dalilinsa na ajiye aiki yake yi, amma sam yaki yarda ya fito daga gida ma bare ya yi hira da wasu, duk sojojin dake gidansu ya tarkatasu ya mayar da su headquartersu, sannan ya ɗauko wasu jibga jibgan bodyguards lafiyayyu masu jini a jika ya jibge a cikin gidan nasu, bodyguards ne masu lafiya karfafa masu kiran samudawa, abin ya ɗaurewa jama'a kai, his excellence ya shiga ruɗe sosai, yasan Lion sarai, shi mutun ne da baya yin abu haka kawai, dolen dole sai da kwaƙkwaran dalili, to menene dalilinsa na ajiye aiki? Meyasa? Wannan shi ne tambayar da His excellence ɗin yake ta yi wa kansa, ya haɗa taron gaggawa a white house, ya kuma turawa Lion ɗin saƙon gayyata, amma ya ki zuwa, ko kallon takardar gayyatar ma bai yi ba, dan ya ce bata da amfani a wajensa, his excellence yana tsoron ya sanya karfin mulki ya tursasa Lion ɗin a kan yazo taron dole, dan shi dai yasan waye jikansa, idan ya gwada mashi karfin mulki, to shi kuma ba shakka zai gwada mashi karfin jini, dan Lion baya barin ko ta kwana, dan haka sai His excellence ɗin ya haɗa malaman jikinsa, bai tursasawa Lion ɗin zuwa taron dole ba, haka suka ɗan yi maganganunsu suka watse, anyi anyi da Lion ɗin ya fito ya yi magana a kan meyasa ya kashe kakansa, nan ma yaki buɗe bakinsa, da his excellence ya ga dai Lion fa wani abin yake shirya masu, sai ya lallaɓa ya wankesa a kan zagin kashe kakan nasa da ake yi mashi, duk Lion ɗin yana ganin komai da yake faruwa, amma sam bai yi yunkurin saka baki ba, ya tada kura, a jijiiga gari ya koma gefe ya lafe shiru kamar babu shi, daga shekaran jiya zuwa yau ko'ina idan ka zaga a cikin birnin Washington da kewayenta, maganar Lion ake yi, ko ta ina zancensa ne kawai yake tashi, gidan jaridu kafafen yaɗa labarai, da ko'ina, ya tada tarzoma ba kaɗan ba.

Ya koma gefe guda ya yi shiru kamar ba shi ba, abin da ya sanya ya ajiye aikin soja, saboda ya san ta hakan ne kawai his excellence zai yi ƙoƙarin horar da shi, yasan cewa zasu yi ta ce mashi zasu tuɓe mashi kaki, ko kuma su saka shi yin wani abin a gwammatance, to shi ne yasa kafin ma su fara wannan diramar ya ajiye aikin, yanzu ba kaki da gwamnati ce zasu yi faɗar ba, farar hula ce da gwamnati. Wannan shi ne cakwakiya, shi ne ake kira da ainahin game. Tsafinsu ba zai iya kama shi ba, babu abin da suka isa su yi mashi, dole ne sai sun ajiye tsafi sun yi ta kulla mashi manakisa, shiyasa shi kuma ya biyo masu ta karkashin kasa, Allah ne kaɗai yasan shirin da yake shirya masu!!.

His excellence ya so haɗuwa da Lion ɗin a koma ina ne, sai dai ina bai samu damar haɗuwa ba, hasali ma Lion ɗin ko waje baya fita, yana cikin gida abinsa, gabaɗaya faɗin U.s ta ɗauka a kan ajiye aikin nan nasa, ta girgiza kasar girgiza mafi girma, amma shi ko a jikinsa, sai ma barci da yake shararawa, yana hutawa, har wata ƴar kiba ya kara abinsa, ban da tunanin gwaggo, TRIPLETS nasa da kuma Meeshansa, to baya tunanin komai a rayuwarsa, hankalinsa a matuƙar kwance, kai daga gani kasan ba karamar abu yake shiryawa ba, komawa da baya ga zaki ba tsoro bane, shirin yaki ne, his excellence ya san da hakan, shi ne yasa hankalinsa ya yi mummunar tashi, shi kansa Anderson a tsorace yake.

Wannan shi ne kaɗan daga cikin abubuwan da suka faru a cikin wannan kwana uku da suka wuce, yau ta kama kwana na huɗu, Sheikh Sultan ya kammala aikinsa, Rimsha ta samu lafiya sumul, tamkar bata taɓa yin ciwo ba, yau ta dawo cikin hayyacinta fes, tana dawo dai'dai kuma abinci ta tasa a gaba, ci take yi babu kama hannun yaro, sai kallonta su gwaggo suke yi, baiwar Allah ciki ya buɗe, a kallah yau ta ci abincin da ya kai kusan ukun wanda take ci a baya, sai kallonta Dr Salman da Sheikh Sultan suke yi.

Bayan ta kammala ɗirkar abincin ne ta ɗago idanuwanta tana faɗin "Gwaggo ina yaya Saif? Ko basu dawo daga Daular Mutuwar bane?".

Shiru gwaggo ta ɗan yi kafin ta ce "Sun dawo, amma shi baya nan, sai dai ki kirashi a waya".

Shiru ta ɗan yi tana ji tamkar wadda ta yi tafiya ta je ta yi kwana biyu a wata duniyar.

"Gwaggo ina wayata? Jiya da daddare na barta a nan, bani bari na kirashi". Ta kai karshen maganar tare da miƙewa tsaye ta nufi saman bed ɗin, ta bar kayan abincin da ta ci a wajen.

Mikewa Dr Salman da kuma Sheikh Sultan suka yi, suka fita suka basu waje, sai Hamdala suke yi ga Allah an samu nasara Rimsha ta dawo dai'dai. Ɗakin ya rage daga gwaggo sai Brr Naurat da kuma Jehan dake ta zuba barci ta tada kai da cinyar gwaggon, ita kuma Akila tana can tana gyaran bedroom nasu, Aseef da Areef basu nan, kwana biyun nan ma sam basu zama a gidan, da alama wani aiki Lion yake saka su, dan a tare da Tga suke fita, idan suka fita tun safe, sai dare suke dawowa, da sun dawo kuma zasu yi barci, dan zasu sake fita da sassafe, mummynsu Rimsha kuma tana can boys quarters tana barci, daddynta baya nan, ya fita zuwa gidansu Abban Imran.

Kusa da gwaggo ta zo ta zauna tana faɗin "Gwaggo ina wayar tawa take? Ina so ne na ɗan yi abu da ita". Miƙa mata sabuwar wayarta da Areef ya saya mata gwaggon ta yi, tana faɗin "Nasan Saif zaki kira, to ki kirashi da wayata, numbersa ita ce a farko, dan ba jimawa muka yi waya da shi".

Okey ta amsa tare da karɓar wayar tana wani sunkuyar da kai na rashin kunya. Miƙewa ta yi ta nufi waje, da idanu suka bita suna mamakin yadda ta dawo dai'dai cikin hukuncin Ubangiji.

Kai tsaye bedroom na Lion ɗin ta nufa, ko'ina a gyare tsab tamkar yana nan. Saman bed nasa ta haye tare da rungumo pillow a kirjinta tana danna mashi kira. Wayar tana fara ringing ya katseta, dan ya ɗauka gwaggoce, shi bai san Meesharsa ta dawo dai'dai ba, yana kwance a saman katafaren bed nasa, daga shi sai singlet fara kal and short, sai wani lumshe idanu yake yi tamkar mai jin sha'awar wani abin, ya kara yin fresh da shi over, bin kiran ya yi tare da manna wayar a kunnansa...........

Kiran na shigowa ta ɗauka cikin zumuɗi, a nutse ta ce.........

*KADA KU MANTA BABU POSTING A WEEKEND, NA YI CANCEL NASA, IYA MONDAY TO FRIDAY ZAN RINƘA YI KAWAI YANZU.*

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔 ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA, INFECTION KILLER, COLACCA, SAI KAYAN GYARA PAGE. KACA KACA. YALLAGWADA. JIGIDA. RUWA RUWA. BANI BANI. WOMEN JELL BATA BATA. DAFIN KAXA. TANTABARA. XABUWA. CICCIƁI. AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER 09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH, BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)

*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*

E21

Date: 1/5/2024

Kiran na shigowa ta ɗauka cikin zumuɗi, a nutse ta ce "Hello Noorish". Yana kwance bai san time da ya mike zaune ba, kasa yarda da abin da ya ji kunnuwansa suka ji ya yi, anya ba gizo kunnuwansa suke yi mashi ba kuwa? Anya ita ce kuwa?.

Katse mashi tunanin nasa ta yi da cewa "Noorish ka fara ko? Sai mutun ya yi magana kaki amsa mashi da wuri ko?". Ta yi maganar a tsananin shagwaɓe sosai.

Calmly ya furta "My Meesha". Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke, jin voice nasa ta yi tamkar an zuba mata zuma a baki, saboda daɗi, wani irin sanyi ne ya ratse zuciyarta, kara kankame pillow hannunta ya yi, cikin sanyin murya ta fara magana a shagwaɓe. "Noorish ka dawo daga Daular Mutuwa kuma ka fita baka tasheni daga barci ba, to ni yanzu kawai ka dawo gida ina son ganinka". Tana magana tamkar zata sanya mashi kuka.

"Meesha bana kasar ne, amma zamu rinƙa yin waya kin ji?". Jin abin da ya ce yasa ta fashe mashi da kukan shagwaɓa tana faɗin "Shi ne ka tafi ka barni ko? Allah ni ban yarda ba, koma ina kake ka dawo na ganka, kewarka nake yi sosai". Tana magana tana kuka hawaye bibbiyu.

"My Meesha why kike son yin kuka ne? Do you know how sad am feeling idan kina kuka kuwa?". Girgiza mashi kai ta yi. "Sorry Noorish, amma ai ina son ganinka ne".

Nisawa ya yi kafin ya ce "Same here, nima ina kewarki sosai my wife".

"To Noorish ka dawo mana kawai". Shiru ya ɗan yi mata kafin ya ce "My Meesha, dawowata yanzu ba zai yiwu ba, kuma zamanki a Nigeria yafi mani sauki da samun kwanciyar hankali, ina son kasancewar ki kusadani matuƙa, amma dole na barki a can".

Hawayen da suka cika mata idanu ne suka cigaba da gangaro mata a saman face nata, yanzu ta yaya zata iya yin barci ita kaɗai a wannan ɗakin? Ta tambayi kanta da kanta.

Jin ta yi shiru ne yasa ya ce "Meesha kuka kike yi ko?". Da sauri ta kai hannunta tana ɗan goge hawayen nata, cikin shagwaɓa da sanyin murya ta fara yi mashi magana a nutse, cike da so da tsantsar kauna. "Noorish ba kuka fa nake yi ba, kawai ina kewarka ne, amma shikenan zan tayaka da addu'a sosai, Allah ya tsare mana kai a duk in da kake, Allah Ubangijin ya dawo mana da kai lafiya, ka kula sosai ka ji?". Yanda ta yi maganar tamkar wata babbar mace mai yawan shekaru.

Har cikin ransa ya ji sanyi da daɗi matuƙa, nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da komawa ya kwanta yana jawo pillow izuwa kirjinsa ya rungume, tamkar ita ya ƙanƙame, Allah ya gani yana tsananin kewarta, yana son ganinta a kusa da shi, amma dole ya barta a in da take tukunna, dan shi kansa wannan masifa da yake ƙoƙarin jijjigowa kansa ba ƙaramar wahala zai sha wajen iya tsaida ta ba, bugu da kari kuma idan tana a kusa da shi zata hana shi yin wasu abubuwa, zata sanya mashi tausayi a ransa, kuma dole zai rage wasu abubuwa da ya yi niyar yi saboda ita, shi ne yasa gara mashi suna nesa da juna ɗin, sai su rinƙa yin waya kawai suna jin muryar juna, hakan zai fi sama mashi kwanciyar hankali, zai kuma sanya ya yi aikinsa a yadda ya tsara yin komai ba tare da wata matsala ba.

"I really love you my Meesha, pray for me sosai, because nafi bukatarsa sama da komai a yanzu".

Tana goge hawayen face nata wasu suna gangarowa, Rimsha sarkin soyayya, tattabara uwar soyayya kuma uwar ruke alkawari, tana tsananin kaunar Lion ta yadda baki ma bai isa ya zayyano irin wannan kauna ba.

"Amma Noorish kafin ka tafi ka sumbace ni ko?".

Shiru ya yi na ƴan sakanni kafin ya amsa mata. "Yeah my Meesha, i kissed your lips".

Cool murmushi ta saki ga guntun hawaye a fuska.

"I really like your smile, you're looking so beautiful idan kina yi". Ya faɗa yana ɗago idanuwansa, dan ya duba time, akwai in da zai je da misalin karfe 4 na yamma, fita ce ta sirri!.

"Kai Noorish waye ya ce maka nayi murmushi to? Ko dai ka saka mani camera ne?".

"Ba wani camera da na saka mani, just na san halin kaya na ne, nasan sai kinyi murmushi a wannan time ɗin da nace nayi kissed naki, that's why na ce hakan".

Sake sakin cool murmushi ta yi tana mamakin kwakwalwa irin na Lion, wato shi har ya kammala haddace halinta tsab, yasan duk wani abin da zata aikata da wanda ba zata iya aikatawa ba, ko a bayan idanuwansa, lallai ya cancanci a jinjina mashi.

"Noorish ka ci abinci?". Ta tambaya tana lumshe idanu tare da kara lumewa a saman bed ɗin, dan sanyin A.cn dake a ɗakin ya fara yi mata yawa.

"Yeah na ci, what of you?". A hanzarce ta ce mashi "Nima na ci, sai dai kuma yanzu ma wani yunwar nake ji".

"Okey go and eat another one now, bana son ki rinƙa zama da yunwa, because bana son ki rame, I want to see you the way you are now, ƴar dai'dai".

Ɗan turo baki ta yi, a shagwaɓe ta ce "To Noorish kenan baka son na kara yin ƙiba?".

Jinjina mata kai ya yi tamkar yana a gabanta, sannan ya amsa mata da Yeah.

"To Noorish idan na kara ƙiba fa komai zai kara girma a jikina, ni ina son na kamo Jehan gaskiya". Ta kai karshen maganar tamkar zata yi kuka.

Lumshe idanuwansa ya yi, har cikin farfajiyar zuciyarsa ya ji wannan muryar shagwaɓar da ta yi mashi, da tana kusa da shi ai da ya rungumota ya bata hot kiss, abin ya ratsa zuciyarsa da kyau da kyau, Meeshansa nan ta iya zuba shagwaɓa mai tsayawa a rai, a kowani lokaci da irin sabon salon shagwaɓa da take zuba mashi, bata yarda ta rinƙa yi mashi salo ɗaya kullum, na yanzu daban na anjuma daban, tana ratsashi sosai.

Calmly ya ce "Wato kin sakawa matar Areef idanu ko?". Murmushi ta yi tana faɗin "Kai Noorish bafa idanu na saka mata ba, just kawai tafi ni girma ne baya yi mani daɗi hakan".

Girgiza kai kawai ya yi, Rimsha akwai rigima, idan ya biye mata ba zai je ya yi abin da yake a gabansa ba, wannan yana ɗaya daga cikin abin da yasa sam sam baya son ta dawo Washington a yanzu, sai ya kammala abin da zai yi, idan ta dawo kusa da shi a yanzu, ta rinƙa ɓata mashi lokaci da shiririntanta kenan, ta hana shi yin komai.

"Meesha zamu yi waya da daddare, ki kula mani da kanki sosai ko?".

Turo baki ta yi tana faɗin "To shikenan, kai ma ka kula sosai". Okey ya amsa mata da shi tare da mannawa wayar tasa sumbata sannan ya katse kiran ya miƙe, a gurguje ya nufi toilet dan ya yi wanka, yanzu ta sami lafiya, hankalinsa ya kara kwanciya. Ita kuma gyara kwanciyarta a saman bed ɗin nasa ta yi, ta lumshe idanunta tana tunaninsa.

After some hours, da misalin karfe 9 na dare Aseef da Areef suka dawo gidan, a tare da Tga suke, gaisawa da Alex suka yi a harabar gidan kafin su nufi ciki. Areef da Tga ne suka nufi ciki, shi kuma Aseef ya wuce wajensu Brady a in da suke kulle. Dubasu ya je ya yi ya tabbatar suna cikin ƙoshin lafiya, sannan ya fito ya nufi cikin gida, Lion bai tafi da Brady ba, ya baro shi a nan Naija, so Aseef ya haɗesu da su copper ya rufesu, dan kada su takurawa ƴan gidan, yasan halin matan nan sarai da tsoro, ga shi basu nan, sai su kusa haukatasu a cikin gidan, shi ne yasa ya rufesu.

A palon kasa ya isko Tga da Areef suna magana, wucewa ya yi izuwa nasa bedroom ɗin yana faɗin "Am really tied, bari naje na huta, good night". Ya kai karshen maganar tare da wucewa cikin ɗakinsa, Areef yana tambayarsa ba zai je ya gaishe da momma bane?. E ya amsa da shi, dan ya gaji, ya ce sai da safe kawai zai dubata. Jinjina kai kawai Areef ɗin ya yi.

Bakinsa ɗauke da sallama ya shigo cikin bedroom ɗin nasa, dai'dai lokacin ita kuma Akila ta fito daga cikin toilet ɗaure da towel a kirjinta, wanka ta yi.

Ko sannu bata ce mashi ba, da alama faɗa suke yi, shi kuma ya tsaya ya zubawa santala santalan cinyoyinta da suke jajir da su idanu.

Kallon up and down ta yi mashi da waɗan nan dara daran idanuwan nata kafin ta wuce ta nufi dressing room nasa, lotion ɗin ma ta fasa shafawa, saboda yana tsaye a cikin ɗakin, sai ta wuce dressing room kawai zata sanya kaya, da alama fa Heartbeat ranta a ɓace yake sosai.

Pajamarsa launin sky blue ta ɗauko, a saman show glass na jera watchs nasa ta ɗaura wandon pajamar tana ƙoƙarin warware rigar ta sanya a jikinta. Kamar daga sama ta ji saukar hannunsa a saman shafaffen cikinta, ya kwanto da kansa a saman shoulder ɗinta, a hankali ya kai ɗayan hannunsa ya karɓi rigar dake hannunta take ƙoƙarin sanyawa, ya ɗaurata a saman show glass ɗin.

Ƙoƙarin ture hannunsa daga jikinta ta yi, tana turo baki. Kara kankameta ya yi, a hankali ya ɗan matso da ɗan bakinsa kusa da kunnenta, calmly ya fara yi mata magana a tsananin shagwaɓe. "Why my heartbeat? Ba nace maki sorry yau da safe ba, daga yau fa ba zan ma sake fita ba bare har naje na kai dare, please my pleasure kada kiyi fushi dani, idan kika yi fushi zan iya kamuwa da ciwo, nasan nayi laifi sosai, amma kiyi hakuri".

Ture hannunsa ta yi tana faɗin "Ni ka barni, mun yi hannun riga da kai, wai ma meyasa baka kwana a wajen ba kawai".

Ta kai karshen maganar tana ture hannunsa tare da janye jikinta dan ta bar wajen. Jawota ya yi mai gabaɗaya ta faɗa jikinsa, ɗaukarta cak ya yi suka fito daga cikin room ɗin. Kai tsaye sai saman bed ya sauketa. Tana ƙoƙarin mikewa ta diro kasa, ya yi maza ya rikota tare da kai hannunsa ya kashe wutar ɗakin.

Kwanciya ya yi tare da rungumota sosai a jikinsa tamkar wani ya ce zai kwace mashi ita.

Sai ƙoƙarin kwace kanta take yi, amma ina ya kankameta sosai. Da yaga ba zata nutsu ba, sai ya laluɓi lips nata ya haɗe bakinsu waje guda tare kuma da kara kankameta.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull