Kenza eBookz

Triplets book 4 Complete - Chapter 78

Triplets book 4 Complete - Chapter 78

Triplets book 4 Complete Chapter 78: Triplets book 4 Complete Chapter 78. Kara faɗaɗa murmushin dake a saman face nata ta yi kafin ta ce. "Wannan alkawarin…

3,351 words

Kara faɗaɗa murmushin dake a saman face nata ta yi kafin ta ce. "Wannan alkawarin tsoro ne, barazana aka mun na yi shi, dan haka ba zan dai'na ba, ke dai kawai ki tafi abinki".

Ganin motocin su Lion ya danno kai cikin gidan ne yasa Malikar ta ɓace daga kan idanun Rimshar, sai dai bata tafi ba, tana wajen, dan tana jin daɗin ganin diramar Lion da Rimshar.

Ita kuwa Rimshar bata ma san sun shigo cikin gidan ba, dan harabar gidan gari ne guda, parking space yana ta gefe can, bazaka san mutane sun shigo gidan ba idan kana ta gefen shiga ainahin cikin gidan, dan haka da taga Malika ta tafi, sai kawai ta cigaba da sharholiyar tana juyi kamar wata mai tafiyar maciji.

Tana tsaka da juyawa tana rera wakar. Da kai ne zan yi, amma a maimaƙon ta ce da kai ne zan yi wuff, sai dai ta ce da Noorish na zan yi wuff, abin gwanin ban dariya, har yanzu akwai yarinta sosai a kanta.

Bata ankara ba sai ji ta yi ta bugi mutun wanda ko bata ɗago ta kalle shi ba tasan wanene, daga yanayin tsayuwar Lion chest nasa da take kyam har izuwa kamshin perfume nasa, hakan ne yasa ta gane wanene.

A dubu ɗari ta yi baya baya zata faɗi.

In da dai ya saba riƙota idan zata faɗi, wato wuyar rigarta, a yanzu ma nan ya riƙo tare da ɗan daidaita mata tsayuwarta yana kallon face nata.

"Ban hanaki shiga cikin ruwa ba?!" Ya yi maganar tamkar mai jin barci, da alama akwai gajiya sosai a tattare da shi.

Tsuru tsuru ta yi da idanu tana tunanin me yakamata ta ce mashi, dama idan baku manta ba, time da ya hanata shiga ruwan, a cikin zuciyarta ta ce ba zata dai'na ba, ga shi kuwa bata dai'na ɗin ba.

Malika dake laɓe tana kallonsu me zata yi banda dariya, barema da ta ga Rimshar ta yi tsuru tsuru da idanu, abin ba ƙaramin dariya ya bata ba, kamar ba yanzu Rimshar ta gama cika mata baki a kan Lion ɗin ba zai yi mata komai ba.

"Ba dake nake magana ba ne?". Ya sake jefo mata wata tambayar.

Ɗan satar kallon hanyar guduwa izuwa cikin gida ta yi, dan ta samu ta gudu, sai dai kuma ai jikinta akwai ruwa over, tana guduwa zata zame ta faɗi kasa, ya zata yi kenan?. Ta tambayi kanta da kanta.

Kallon gefen ido ya wurgawa Mark dake tsaye a gefensa. Tun bai yi magana ba Mark ɗin ya miƙa mishi jakar Sheikh Sultan ɗin dake a rike a hannunsa tare da sa kai ya wuce abinsa, dama saboda jakar ya tsaya bai wuce ba. Shi kuwa Al Shaikh yana cikin mota ba zai iya fita a cikin ruwan nan ba. Binsu kawai da idanu yake yi babu ko kyaftawa.

Ganin bata da mafita ne yasa ta fara ƙoƙarin magana tana in ina.

"Kayi hakuri na manta ne, kuma na tuba ba zan sake ba ka ji?!". Tana magana kamar da gaske, alhalin karya take yi, gobe ma taga ruwa sake shiga zata yi.

(Wlh Rimsha ƴar dirama ce😂)

Sarai ya sani ba wani mantawa da ta yi, iya shege ne kawai, yasan halinta, ba kasafai ta cika mance abu ba, musamman ma da ya kasance maganarsa ce, ba zata taɓa mancewa ba. Dan haka sai ya kara ɗaure fuska sosai na wuce misali, dan ma ta san yanzu ba da wasa yake yi ba, a kan wannan shiga ruwan zai iya zaneta sosai wlh.

Yana ƙoƙarin yin magana tamkar daga sama ya ji an ambaci sunansa daga bakin kofar shiga parlourn. Ko bai ɗago ba yasan wacece, dan muryarta ita kaɗai ce ba ta biyunta a zuciyarsa.

Kin ɗagowa ya yi su haɗa idanu, sai ma ya yi kamar bai ji ba, dan so yake yi ya hukunta Rimsha.

"Saif ka kyaleta ka zo". Cewar gwaggon dake tsaye a kofar parlourn.

Ita gwaggo tasan amanar da yake a tsakanin Rimsha da ruwan sama, tun suna Dubai haka take, komai sanyin da ake yi sai ta shiga ruwa idan aka yi, yanzu ku duba mani uban sanyin da yake a U.s ɗin nan, amma hakan bai hanata shiga cikin ruwan sama mai uban sanyi ba.

Jin abin da gwaggon ta ce ne yasa ya kama hannun Rimshar kawai suka nufi cikin gida.

Sam ba haka Malika ta so ba, ta so ya bata mari ko guda ɗaya ne, dan Rimsha bata ji, basu son tana shiga cikin ruwan sanyin nan, amma sam bata ji.

A parlourn ƙasa ya saki hannunta tare da wucewa sama, a lokacin shi kuma Mark ya shigar da Sheikh Sultan, dan ya yi mashi amfani da lema ne suka shige ciki.

Shaikh Sultan dattijon arziki dattijon kirki, yana ganin su Areef ya fahimci tsafi ce ta ɗan taɓasu, dan haka sai ya fara aikin zuba masu adduo'i babu kama hannun yaro.

A kusa da su Lion, sir Safwan, and Aseef suka zauna, shi kuma Dr William sai ya fara aikin cirewa uncle Herry bullet ɗin da yake jikinsa.

Gwaggo kuma ta gama aikin Jehan ta zo ta fara aikin duba daddyn Rimsha, dan kafafunsa suna ciwo sosai.

Izuwa yanzu gabaɗaya gidan sun san da cewa su daddyn Rimsha sun dawo, dan haka kan kace me sun cika word room ɗin nan tab.

Ita kuma Hjy Rimsha uwar rigima, da farko da Lion ya barta a parlourn ƙasa ya haura sama, ta so ne ta koma wajen ta ɗan kara shiga cikin ruwan saman, saboda tsabar rashin jin magana, shiyasa Malika ta so Lion ɗin ya bata koda mari ɗaya ne, kila zata rinƙa jin magana.

Amma kuma da ta sami labarin su mummynta sun dawo, ai kuwa da gudu ta haura sama, a gaggauce ta canza kayan jikinta, ta fasa wanka a ruwan saman.

Bayan ta gama canza kayan ne tana ƙoƙarin fitowa waje daga bedroom ɗin nasu, shi kuma Lion yana sako kai, karo suka ɗan yi.

Baya kaɗan ta koma tana faɗin. "Noorish wai su mumnyna sun dawo?".

Hannu ya kai ya tura kofar bedroom ɗin. Yana turata kuma ta rufe kanta, bai ce da ita komai ba ya wuce ya nufi toilet ya barta tsaye a wajen.

Bata damu ba ta nufi hanyar fita, sai dai kuma kofar a rufe, bata iya buɗe kofofin gidan ba, dan dayawansu ma da fingerprint suke aiki, wasu da card, hakan yasa bata iya buɗe kofar ba.

Tamkar zata yi kuka ta koma saman bed ta kwanta tana jiransa ya zo ya buɗe mata ta fita.

Shi kuwa samun tabbacin su Areef zasu iya tashi ko yanzu daga bakin Sheikh Sultan ne ma yasa ya dawo cikin bedroom nasa dan ya yi wanka, Sheikh Sultan ya ce kowani lokaci tsafin zai iya sakinsu, yana sake su kuma zasu koma normal kamar babu abin da ya taɓa taɓasu.

Bayan ya yi wanka, cikin pajamas ya shirya, sannan ya sanar da cewa kada wanda ya dame shi a yau, dan yana da abin yi nasa na kansa.

A saman bed ya iskota, sai latsa mashi waya take yi tana jiransa ya zo ya buɗe mata kofa ta fita.

Kwanciya ya yi tare da kurawa Tv idanu yana kallon kyawawan baby's ɗin Areef, sai ɗaga hannayensu sama suke yi, ga Jehan ɗin kuma sai zuba barci take yi, su gwaggo sun gasa mata jikinta da ruwa mai zafi, sannan suka yi mata alluran barci, dan ta huta.

Ganin yana ta kallon yaran ne yasa Rimshar ta ce. "Noorish mu kuma sai yaushe zamu haifi namu?".

Dogon numfashi ya ja tare da saukewa a hankali kafin ya dawo da kallonsa a kanta.

"Ai ina ganin ma yanzu zaki karɓi naki baby's ɗin, ba dai kin shirya ba?". Ya yi maganar yana ɗaga mata gera ɗaya.

"Wlh Noorish na shirya, ko yanzu ka bani".

"To zo ki karɓa". Ya faɗa tare da jawota jikinsa.

"Noorish iya baby's fa kawai zaka bani, irin na Jehan ko Akila nake so".

Kasa kasa ya ce mata. "Fin haka ma zan baki, mu our baby's special ne". Ya kai karshen maganar tare da haɗe fuskokinsu, cikin salo ya fara aiwatar da abin da yake da niyya.

"Noorish baby fa kawai zaka bani". Ta faɗa a ɗan tsorace.

Katseta ya yi ta hanyar zuwa mata tongue nasa a cikin ɗan bakin nata, hakan yasa ta yi shirun dole ta fara karɓar sako.

Ai yau ma ba shi ya kyaleta ba har sai da ya fanshe kewarta na tsawon watannin nan da ya yi, sannan ya rabu da ita.

Ban da kuka hawaye bibbiyu babu abin da take yi mashi, ta ji a jikinta ne ba karya.

Rarrashi ya hauyi babu kama hannun yaro, sam taki kula shi.

Ganin haka sai ya ce ta yi shiru bari ya je ya yi mata wanka sai suje wajen mummynta.

Jin hakan yasa ta danne ta yi shiru, tana jin raɗaɗin zafi kam, amma a haka ta danne, dan tana son ganin mummynta.

Sumbatar lips nata ya yi yana faɗin. "I really love you my Meesha".

Turo bakin nan ta yi, kamar zata sa kuka ta ce. "Love you too". Ta yi maganar kamar wadda aka saka dole.

Kamar zai sake yin magana, sai kuma ya fasa tare da miƙewa ya ɗauketa sai cikin toilet.

Wanka ya yi mata kamar yadda ya faɗa, sannan ya naɗota a towel ya dawo da ita saman bed, ya koma cikin toilet, dan ya yi nasa wankar, taki yarda su yi a tare ne, har wa yau kunyar yin wanka tare da shi take yi, shiyasa yake fara yi mata kafin ya yi nasa.

Kafin ya fito daga wanka har ta shirya cikin wata abayar, ta haye saman bed ta kwanta, ta yi shiru tana jin raɗaɗin da gabanta yake yi mata.

Har ya fito ya gama shiryawa bata sani ba, ta afka duniyar tunani.

Bayan ya kammala ne ya dawo wajen bed ɗin.

"Let's go". Ya faɗa yana ɗaure dark black curly hairnsa a bayan wuyarsa.

Make mashi kafaɗa ta yi, ta ce sai dai ya ɗauketa cak, dan ita bazata iya tafiya da kafafunta ba.

Bashi da zaɓin da ya wuce ya yi hakan, dan shi ne nan ya ja mata ai. Dan haka sai ya ɗauketa cak suka nufi wajen.

Sai shafa kyakkyawar bakin gashin sajensa take yi tana sumbatar wuyarsa.

Kasa kasa kamar mai raɗa ya ce "Zaki fara ko? Ki cigaba, ai ban yi nisa da bedroom ba, sai na juya na mayar dake ciki, dama ni ban ƙoshi ba, kawai ragwantarki yasa na barki".

Ganin sun ɗan yi nisa da part ɗin nasu ne yasa ta ce. "Allah Noorish ni ba raguwa bace ba".

Cak ya tsaya da tafiyar yana tambayarta. "Are you sure?".

Ganin ya tsaya ne, kuma tasan tsab zai iya juyawa da ita su koma ciki ya bata ajikinta ne yasa ta yi sauri girgiza kai tana faɗin. "Am not sure, wlh yanzu ma wajen ciwo yake yi mu" Ta kai karshen maganar kuma tare da saƙalo wuyarsa ta ɓuye fuskarta a wajen wuyar tasa.

Cigaba da tafiya ya yi ba tare da ya sake ce mata komai ba, ƴar rigima kawai.

Bai direta a ko'ina ba sai a cikin room ɗin, a lokacin kuma Allah da ikonsa mum ta farfaɗo, ta kuma dawo normal kamar yadda Sheikh Sultan ya faɗa, shi kuma Areef bai dawo normal ba, yes ya farfaɗo, amma kuma bai dawo dai'dai ba, dan lokaci da ya farfaɗo ya farfaɗo ne da karfi tare da fara yunkurin barin cikin ɗakin, su Uncle T ne suka danne shi, sai fisge fisge yake yi.

Da kyar suka samu suka dannesa ya nutsu Sheikh Sultan ya cigaba da yi mashi addu'a, daga haka barci ta ɗaukesa bawan Allah.

Mummy kuwa, ta dawo dai'dai sai hira da su gwaggo ma take yi, dama tsafin ne ya taɓata, a wajen faɗar tasu ne ma aka samu akasi su Anderson suna ƙoƙarin jefar daddyn Rimsha da abin tsafin, sai ya taɓata ita, shi ne ya kandarar mata da jiki kamar ta mutu.

Amma da yake babu abin da yafi karfin Allah, ayar Allah ba wasa ba, sai ga shi cikin hukuncin Ubangiji ta dawo dai'dai normal abinta.

Shi kuwa Areef sai washegari suka samu ya dawo dai'dai. Yana dawowa dai'dai kuma Jehan ya fara nema, a nan ne Lion ya gaya mashi tana nan lafiya kuma ta haifa mashi ƴan huɗu jiya, ita ma tun jiyar take ta faman barci kamar me, ta gaji ne over, shiyasa take ta zuba barci kamar ba gobe baiwar Allah.

Mummyn Rimsha baki har kunne, ta ji daɗin samun jikoki QUADRUPLE, sai uban murmushi take yi abinta.

Cikin zumuɗi Areef ɗin ya ce zai je ya kalli Jehan ɗin. Hana shi Lion da sir Safwan suka yi, suna son ya ɗan huta, Lion ya ce da gwaggo a kawo mashi baby's ɗin nan ya kallesu, sai zuwa dare idan ya kara hutawa, sai ya je ya kalli maman babyn.

Haka kuwa aka yi, gwaggo ta je tare da Josephine suka ɗauko baby's ɗin, gwanin ban sha'awa.

Ana miƙa mashi ɗaya ya karɓa yana sakin cool murmushi.

A fili ya furta "Ga takwaran Saif nan, na hannun momma kuma takwaran Safwan, ɗayan na hannun Josephine takwaran Aseef, ɗayan kuma takwaran uncle ne (daddyn Rimsha)". Ya kai karshen maganar yana ɗago da kallonsa izuwa kan Lion ɗin.

"Lion yakamata ka rike takwaran nan naka fa". Ya faɗa yana miƙo mashi babyn.

Sam Lion ɗin bai so ɗauka ba, amma kuma saboda babyn yana tsananin kama da Areef ɗin, ga shi kuma takwaransa ne yasa ya kai hannu ya karɓi yaron, sam baya son ya kalli wannan murmushin dake a saman face ɗin Areef ɗin ta kau, shi ne yasa ya karɓi baby, dan in bai karɓaba tabbas wannan murmushin zata kau daga saman face ɗin Areef ɗin.

Karɓar yaro na biyu daga hannun Josephine Areef ɗin ya sake yi yana kallon babyn sosai, nan take wasu siraran hawaye suka fara bin kuncinsa.

Zuba mash idanu Lion ɗin ya yi yana kallonsa da mamaki.

"Areef meyasa kake kuka kuma?". Cewar sir Safwan, ya yi maganar a ɗan ruɗe.

Nisawa Areef ɗin ya yi kafin ya goge hawayen nasa yana faɗin. "Dole nayi kuka, Allah mai kyauta mai kari, ya bani ƴaƴa maza har guda huɗu, tamkar fa yadda aka haifemu mu huɗu, kamar yadda Allah ya albarkaci daddynmu da samun mu mu huɗu, haka ya sake kara mana da wasu huɗun, wasu suna can suna haukar neman haihuwa, abin da kuɗi, mulki, isa, taƙama, izza, kai komai bai isa ya bada haihuwa ba, Allah shi kaɗai yake bayarwa, dole na zubar da hawayen farinciki".

Gwaggo ce ta ce mashi "Bama iya kai kawai ba, Aseef ma Allah ya bashi TRIPLETS kuma dukka maza".

Zaro ash eyes nasa ya yi yana mamaki, abin kamar a mafarki yake jinsa.

Haka suka kasance cikin tsananin farinciki har Allah ya sauki Anaya lafiya a cikin wannan sati da Jehan ɗin ta haihu, ratarsu kwana huɗu, ita kuma Anaya ta haifo TWINS kamar daddynta kenan, idan baku manta ba daddynta ai ƴan biyu ne da daddyn Rimsha, so ita ma TWINS ta haifa, ta gado kenan.

A nan ne fa gwaggo ta ce yana da kyau su shirya gagarumin walima na murnar samun wannan ni'ima da Allah ya yi masu, dan haka yana da kyau su Abban Imran su Abbi da sauran dangi duk su zo, su zo ayi taron suna tare da wannan walima, idan ya so daga baya sai su koma.

Haka kuwa aka yi, Brr Naurat ta buƙaci kowa da ya zo, harda daddyn Anaya da mum nata sun zo, su Irfan harda Ummin Dr Nawid kowa ya zo, daddyn Adiva shi ma yazo, mummynta ne dai shiru ba'a san in da take ba, ta mutu ko tana raye, Allah masani.

An shirya walima sosai na wuce misali, amma ba'a gidan za'a gabatar da walimar ba, a wani tapkeken hall za'ayi shi, sai shirye shirye suke yi, gobe ne walimar, sai hidima ake yi tamkar baza'a mutu ba. Su gwaggo anje shopping ya kai sau biyar, sai ta sawowa ƴaƴan nata kuma matan ƴaƴan nata kaya, sai taga bai yi mata ba, haka zata sake tasan jiga jigan motoci ta sake komawa shopping ɗin, sai sharholiyarta take yi, tana so ne matan ƴaƴan nata su tashi kan al'umma da haɗuwa ranar walimar.

Da misalin karfe 9 na dare, gabaɗaya familyn sun haɗu a parlourn ƙasa, sai hirar yaushe rabo ake yi. Rimsha ta tada kai da cinyar mummynta, ita kuma Jehan tana kusa da gwaggo, baby suna ɗakin gwaggo tare da Ummin Dr Nawid, ta ce ita ba zata fito parlourn ba, zata zauna a tare da baby's ɗin, uncle Herry ma duk da bai gama samun lafiya ba, ya fito parlourn ana hira da shi, sai tambayar ina matarsa mamansu John yake yi, an rasa wanda zai iya gaya mashi ta mutu bata raye.

Jay da su John duk kowa yana nan, Jellyn Yah Imran dai har yanzu shiru babu ciki, ga yaron su Akil har ya yi wayo, amma su shiru har yanzu, sai more duniyarsu suke yi abinsu, ga wani uban kyau da Jellyn ta kara kamar me.

Umaisha ce ta kunna masu wakar zuri'a guda tsintsiya guda babu mai rabawa, soyayyar gaske ake in da rai da lafiya ba zaku ganmu a rana ba, a wayarta ta kunna wakar. Sai murna suke yi, shi kuma Lion so yake ya tashi ya ɗauki Rimsha su wuce ɗaki, dan fa shi sun takura mashi, yana jinsa a sama, ga Rimshar taki zuwa wajensa, ta wani maƙale a jikin mummynta kamar wata jaririya.

Sai bibiye wakar ƴan matan suke yi. Jin anzo wajen wata baiti yasa Rimshar ta miƙe zaune tare da zuro kyawawan kafafunta kasa ta miƙe tsaye tana bibiye wakar.

Wajen Lion ɗin ta nufa tana bibiye baitin da suke cewa. "Innayo tunawa na tuna cewa kai ne mijinawa ba, sai in ji da sanyi zuciyata ta dai'na yin kuna". Ta kai karshen baitin tare da zama a kusa da Lion ɗin babu ko kunya, yanzu sun koya mata rashin kunyarsu ita ma.

Dama shi Lion jira yake yi su haɗa ido ya ce ta zo, sai ga shi kuma ta kawo kanta dalilin baitin waka, dan haka sai ya miƙe tare da ɗaukarta cancak ya keta gabaɗaya family ya wuce sama da ita abinsa.

Kada ku manta dukka familyn dai jirgi ɗaya ya kwasosu, wato dai jinin turawan ne, dan haka ko a jikinsu, ko kallon Lion ɗin ma basu yi ba, suka cigaba da hiransu.

Akila ce ta sake miƙewa tana bin wata baiti da ake cewa. "Inna sake waigawa naga ƴaƴan dake garemu, dani da kai dole mu gobewa wanda ya bamu, shi ne wanda yasa mun haɗa kanmu ana ganinmu, ni na tabbata bazaka mun abin da bazana so shi ba". Ta kai karshen baitin ita ma tare da zama kusa da Aseef.

(Yaran nan sun zama ƴan duniya🥱😒 duk sun zama marasa kunya, dama ita gwaggo uwar miji sam ba'a jin kunyarta😂 kaka ma suka mayar da ita, ɗan gara Dr William ma suna raga mashi😂)

Ai kuwa Akilar tana zuwa kusa da shi, shima ya capkota, dama tun jiya yake lallaɓata a kan tazo suje bedroom nasu ta ki yarda, ta ce mashi wlh sai ta yi arba'in zata dawo, ya yi ya yi har ya gaji, har kuka sai da ya yi mata, amma ta murje idanu taki yarda ta bishi, ya gaya mata shi fa a gaskiya sha'awarta tana neman kashe shi, sai tace mashi ai tana jini, kuma karya take yi, tun last week ta yi tsarki, kawai binsa ne ba zata yi ba, to ga shi ita ma ta kawo kanta sanadiyar baitin waka, ai kuwa ya capkota, tana ƙoƙarin guduwa ya damketa tare da ɗagata cak yana faɗawa gwaggo sun tafi sai da safe.............(😂 Allah ka shirya mana Aseef, shi harda sai da safe ma ya yi wa family😂)

Ganin haka yasa Umaishar ta miƙe tana dariya tana faɗin. "Wakar zuri'a guda dai ta haɗa wata zuri'ar".

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull