Triplets book 4 Complete - Chapter 79
Triplets book 4 Complete Chapter 79: Triplets book 4 Complete Chapter 79. Akil ne ya ce. "Abba muma mun shiga sai da safe". Ya kai karshen maganar tare da…
3,300 words
Akil ne ya ce. "Abba muma mun shiga sai da safe". Ya kai karshen maganar tare da riƙo hannunta suka wuce nasu masaukin, suna tafiya yana gaya mata ita ma yanzu zai bata wani zuri'ar tun da babynsu ya yi wayo.
Jelly da ta ga haka, sai ta lallaɓa ta gudu sama wajen Ummin Dr Nawid abinta, dan dama ta gaji da jarabar Yah Imran ɗin nan nata. Allah sarki Ummin Dr Nawid, akwaita da bala'in son yara, Dr Nawid shi kaɗai Allah ya bata kuma ya karɓi abinsa, kunga kuwa dole yanzu da taga yaran Akila da Jehan dole ta ruɗe baiwar Allah, dole ta ce ita zata zauna tare da su a cikin ɗakin.
Shi kuma Handsome babu kunya babu komai ya ce da gwaggon shi fa yana son wannan karamar yarinyar, ta burge shi sosai, dan haka ya yi mata.
Kallon yarinyar da ya nuna gwaggon ta yi, ita da kanta bata san ƴar wacece bace, amma dai tasan familynsu ne.
"Wacece wannan ɗin?". Ta tambaya tana kara karewa yarinyar kallo.
Daddyn Rimsha ne ya bata amsa da cewa. "Zaira ce kanwar Anaya ƴar Azharuddin".
Kun san halin gwaggo da shegen son fadanci da nuna isa, dan haka sai ta ce. "Ba komai Handsome na baka ita, ko yau kake so sai a ɗaura maku aure".
Jama'a kunji karfin hali wajen gwaggo, dan kawai ita ce yayar su daddyn Anayar, wato ko suna so ko basu so ita ta bada Zaira. (Hjy Gwaggo ikon god😂)
Wani irin daɗi Handsome ɗin ya ji, cike da murna ya zo ya ɗan rungumi gwaggon yana zuba mata godiya.
Ganin haka yasa shi ma Irfan ya ce da gwaggon yana son Pinky.
Aikuwa kara ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya gwaggon ta yi tare da shaida mashi cewa shima ta bashi aurenta, ba kuma wanda ya isa ya hana. Hjy Gwaggo sarkin son mulki.
Dr William kam da yake yasan halin kayarsa, sai ya ce ai bama wanda ya isa ya hana maganarta, dan haka kamar yadda ta bada aure, to ba mai hana wannan auren sai wani ikon Allah, dan haka shima ya bada Pinky ga Irfan.
Miƙewa Irfan ɗin ya yi tare da zuba masu godiya kafin ya wuce nasa masauki, alwala ya je ya yi ya fara sallah tare da rokar Allah da yasa Pinky matarsa ce, kada a fasa bashi kamar yadda aka yi mashi a kan Akila, har ga Allah yana tsananin son Pinky sosai da kallon farko.
Gaskiya Irfan ya more mata, kada ku manta Pinky fa kyakkyawar gaske ce, jinin jajayen kunnuwa, kama da su Lion take yi, ai kuwa ya more......😌
Da haka da haka family suka watse kowa ya yi nasa ɓangaren, dan suje su kwanta su huta gobe suna da gagarumin Walima. Asuba ta gari.
Washegari🤍
LOVE PERIOD❤️🕊️
Tun karfe 7 Rimsha ta farka, dama sun mayar da barci da suka yi sallar asuba, so da yake tana son zuwa wajen walimar, sai ta tashi tun 7, shi dai Lion ya ce ba zai je walimar ba, hakan yasa ma ita ta yi saurin farkawa dan ta shirya.
A hankali ta zame jikinta daga nasa, dan ya rungumeta ne suka yi barci. Cikin dabara a hankali take ƙoƙarin sauka ta bar saman bed ɗin. Sai dai.......
FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA CE.....✍️🔥
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥
*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔 ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.
*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA, INFECTION KILLER, COLACCA, SAI KAYAN GYARA PAGE. KACA KACA. YALLAGWADA. JIGIDA. RUWA RUWA. BANI BANI. WOMEN JELL BATA BATA. DAFIN KAXA. TANTABARA. XABUWA. CICCIƁI. AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER 09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH, BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️
❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)
*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*
E53
A hankali ta zame jikinta daga nasa, dan ya rungumeta ne suka yi barci. Cikin dabara a hankali take ƙoƙarin sauka ta bar saman bed ɗin. Sai dai kuma ta manta da cewa bashi da nauyin barci, dan haka tana ƙoƙarin sauka ya capkota, idanuwnasa a lumshe ya jawota jikinsa.
"Where are you going?".
Ya faɗa can kasan maƙoshinsa, da wata iriyar murya mai matuƙar shegen daɗi, ga shi a sanyaye fiye da yadda yake magana ya yi ta.
"Wanka zan je fa na yi Noorish".
Ta bashi amsa a shagwaɓe.
"To ni kin sallameni ne?".
Ya yi maganar tare da waro idanuwansa a saman face nata. Ta wani tsuke ɗan bakin nan nata kamar ya ce zai yi mata kiss, ita ala dole ta ji haushin ya ganota zata gudu.
Gera guda ɗaya ya ɗaga mata yana mai cigaba da kallonta, idanuwansa sai wani kyalli suke yi.
Turo mashi bakin nan ta ɗan yi kafin ta matso ta shige jikinsa.
Hannunta ya kama tare da ɗaurawa a saman Heronsa dake tsaye kyam. A kunne ya raɗa mata cewa abinci yake son ci.
A shagwaɓe ta ce. "Allah Noorish kai ko, wai shi baya ƙoshi ne?".
A kunne ya raɗa mata. "Tambaye shi mana, baga hannunki a kansa ba?".
Zame hannun nata daga wajen ta yi tare da mayarwa saman mararsa tana shafawa a hankali.
Da ɗan karfi ya furta. "Wash my Meesha". Ya yi maganar tare da kara matseta sosai a jikinsa.
Tana ƙoƙarin yin magana ya yi saurin haɗe bakinsu waje guda, cikin salo ya fara bata zazzafar kiss mai tashin kai.
Cikin so da tsananin kaunarsa ta fara mayar mashi da martani babu kama hannun yaro.
Nan take suka shiga farantawa juna rai babu wasa. Ba shi ne ya rabu da ita ba sai karfe 9:30, nan ma sai da ta saka mashi kuka, sannan ne ya kyaleta yana mai ce mata raguwa kawai.
Bata ce mashi komai ba, dan tasan idan ta ce mashi wani abin ma sake komar da kanta ruwa zata yi, ita kuma sam ba haka take so ba, so take yi ta je ta hau shirin zuwa wajen walimar da za'a gabatar anjuma, tun daga karfe 12 za'a fara har zuwa lokacin da Allah ya yi za'a gama, ba karya Lion and sir Safwan sun kashe maƙudan kuɗaɗe a wajen wannan walimar, saboda iya kaya da motocin da suka tanada za'a rabawa al'umma ma kawai abin ba'a magana, shugaban kasa guda ace Familynsa zasu yi walima ai kunga dole dollars su ci ubansu, dole dollars su yi kuka.
Cigaba da kwanciya shi kuma Lion ɗin ya yi, dan duk jikinsa a mace yake, baya jin kamar zai iya tashi, ita kuma sarkin son zuwa wajen walimar, tuni ta miƙe ta lallaɓa zuwa cikin toilet.
Yana jinta ta yi wanka ta fito, shiryawa ta yi cikin wata abaya kafin ta zo ta gaya mashi ta tafi wajen gwaggo.
Bai amsa mata ba, bai kuma kawar da kallonsa daga kanta ba, ya tsareta da idanu sosai kamar nace zan rabasu.
"Noorish lafiya? Meyasa kake ta kallona haka kaki yin magana? In tafi ne?".
Nisawa ya yi ba tare da ya kawar da kallon nasa ba, a hankali ya motsa laɓɓansa tamkar suna yi mashi ciwo, kasa kasa ya ce.
"Ban ƙoshi bane".
Ya yi maganar yana cigaba da kallonta.
Zama ta yi a gefen bed ɗin tare da juyowa gare shi sosai, cool murmushi ta sakar mashi kafin ta ce.
"Tom bismillah".
Ɗan zaro mata idanu kaɗan ya yi kafin ya jawota jikinsa. A kunne ya raɗa mata ta yarda ya kara?.
Sumbatar kumatunsa ta yi tare da cewa. "E mana Noorish, ka yi har iya yadda ya isheka, In Sha Allah Allah zai baki ikon iya jurewa, da na shiga fushin Mala'iku da tsinuwar Allah na ka buƙaceni naki ba gara na jure ko zan mutu na baka hakkinka ba, na san ko na mutu ta haka zan huta, me aka yi aka yi zuwa wajen walima? Meyasa zan yi zumuɗin zuwa wani waje bayan mijina yana buƙatata a kusa da shi? Kawai ka yi abinda kake so".
Tabbas abin da take faɗa har cikin zuciyarta take faɗarsa. Daɗi sosai ya ji, sumbata ya kai mata a saman ɗan bakin nan nata kafin ya ce.
"I really love you my Meesha, jeki abinki, dama na gwadaki ne naga da gaske zaki iya bani idan na buƙata, da gaske zaki iya daurewa a kowani irin hali kike ciki wanda bai saɓawa Allah ba ki bani, sai kuma ga shi kin bayar ɗin, Allah ya yi maki albarka, jeki ki gaida Momma sai na yi wanka ina zuwa wajen nata nima".
Ya kai karshen maganar tare da manna mata sumbata a ɗan bakin nata again.
Cool murmushi ta sake sakar mashi kafin ta kai ɗan bakin nata ta capko lips nasa na ƙasa. Kissing nasa ta fara yi cikin tsananin so da kauna.
A saman mazaunanta ya ɗaura hannunsa guda ɗaya yana karɓar sakon nata tare da lumshe idanuwansa. A hankali ya fara yawo da hannunsa a saman bayan nata, yana matuƙar kaunar mazaunan nan nata.
Sun ɗan jima a haka kafin ya daure ya saketa, dan baya son ɓata mata rai, ta faranta mashi rai sosai yau da safen nan, so ba zai so ya yi mata abin da zata ji babu daɗi a cikin zuciyarta ba.
Miƙewa ta yi tana mai gaya mashi da ya kula mata da kansa sosai. Sai ta dawo ya yi mata tare da gaya mata ta kula sosai ita ma.
Okey ta amsa da shi tare da nufar kofar fita. Da kallon tsantsar so da kauna ya bita da shi har ta kurewa ganinsa.
Dogon numfashi ya ja tare da saukewa a hankali kafin ya miƙe zaune, wani irin azababben sonta ne yake kara narkuwa mashi a cikin zuciyarsa.
Da kyar ya iya miƙewa ya nufi toilet, jikinsa duk a mace yake, ta saukar mashi da kasala.
Ita kuwa tana zuwa part na gwaggo ta isko Josephine tana ta cancaɗawa su Jehan make up, ga gwaggo ma ta shirya cikin dandatsesiyar Dubai abaya mai bala'in kyau, ta fito a uwar His Excellence ɗin da kansa, kyau iya kyau, yau sai ta yi kama da Aseef sosai, sai nanata kalmar kamar tasu Josephine take yi.
Gabaɗayansu Josephine ta tsara masu kwalliya, har ita kanta Rimshar da gwaggo ta ce ta cire abayar jikintan nan, kayan indiyawa zasu saka yau, sai murna suke yi.
Mazajensu suna nasu bedroom ɗin suma suna shiryawa, Lion ne kawai ya ce shi ba zai je taron ba, ba kuma zai je office ba, kwanciya zai yi a gida, su je sai sun dawo.
Su sir Safwan kam duk sun shirya cikin wasu shegun suit masu bala'in tsada abinsu, sai tashin fitinannen kamshi suke yi, shiga iri ɗaya suka yi a matsayinsu na QUADRUPLE, haka zalika matan nasu ma gabaɗaya kwalliya iri ɗaya Josephine ta yi masu, dukkansu sari Pink color suka sanya.
Rimsha sarkin son ta yi kyau, tuni ta saki dark black curly hair nan nata har baya, ga wani uban sarkar diamond da gwaggo ta ɗaura mata a ƙugunta, abin sai ya tashi kai matuƙa gaya, ta yi wani irin azababben kyau.
Dukkansu Josephine ta feshesu da perfume mai bala'in daɗin kamshi.
Sai santin kyan da suka yi gwaggo take yi, ta yaba ta sake yabawa.
An shirya baby's cikin wasu shegun kaya masu matuƙar kyau, sannan aka jibga masu wasu uban kayan sanyi masu bala'in kyau da tsada a saman kayan nasu, sai wani irin bala'in kamanninsu da iyayensu maza ya bayyana, a cikin baby's ɗin Areef guda ɗaya ya fito mai tsananin kama da gwaggo sosai, ɗayan kuma tamkar Aseef, biyun kuma da shi suke kama, kuma biyu daga cikin baby's ɗin ne suka ɗauki kalar idanuwnasa wato ash color, saura biyun dukka idanunsu irin na Jehan ɗin ne, suma baby's dai sun yi gadon dara daran idanuwan Dr Salman, dattijon nan ya rabar masu gadon idanu kam, akwai su da dara dara ba karya, da wannan idanu ake iya gane cewa jinin Dr Salman ne, dan duk kusan design na idanun nasu iri guda ne, sai dai na wani ya fi na wani girma, amma duk idanun Dr Salman ɗin ne.
Har karfe 11 ana ta wannan uban shirye shiryen, baki ma ya yi kaɗan ya zayyano irin shirin da suka yi wa walimar nan, sun yi kyau na wuce misali.
A cikin waɗan nan sabbin motocin da aka saiwa His Excellence Saif za su tafi, Lion ɗin ne ya ce a ɗaukesu a cikin motocin, duk da cewa already an sayawa mahaifiyar His Excellence nata motar, haka zalika ita ma matarsa, amma ya ce ina su tafi a nasa motocin.
Suna ƙoƙarin fita, wasu ma har sun yi gaba sun sauka parlourn kasa, part ɗin ya rage daga Jehan, Rimsha sai kuma gwaggon, su ne suka yi bayan sauka kasa, ana can kasa an haɗu a parlourn ana jiransu, su kuma sun tsaya jiran Rimsha tana aikin ɗaure igiyar uban high heels da take sanye da su a kyawawan kafafunta.
Bakinsa ɗauke da sallama kasa kasa ya shigo cikin bedroom ɗin.
Wani irin cool murmushi gwaggon ta sakar mashi tana faɗin. "Sai yanzu ka tashi?".
"No sai yanzu dai na iya fitowa, amma tashi kam tun ɗazun na yi shi".
Ya faɗa yana ƙarisowa cikin ɗakin. Tun da ya sako kyawawan kafafunsa cikin wannan ɗakin idanuwansa suke a kan babyn tasa, ta tashi kansa over, sai ya ji ina, ai ba zai ma iya barinta ta tafi ba, wani irin zir zir ya ji a jikinsa, sabuwar tsumi ta tashi mashi.
Ita ma a nata ɓangaren sai kallon shi take yi kamar nace zan kwace mata shi, ya yi matuƙar kyau cikin shigar three cuter fara kal mai bala'in kyau and shirt sky blue, ya ɗaure kyakkyawar dark black curly hairn nan nasa a baya, sai tashin fitinannen daddaɗar kamshin yake yi.
"Good afternoon Momma". Ya faɗa har lokacin ya kasa kawar da idanunsa daga kanta.
Fuska a ɗauke da fara'a gwaggon ta amsa mashi gaisuwar tare da tambayarsa ya ya tashi?.
"Na tashi cikin farinciki da ban taɓa shiga irinsa ba my Momma".
Ya bata amsa yana dawo da kallonsa a kanta.
Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce Alhamdulillah ya Allah, sannan ta yi mashi sallama a kan kowa yana parlourn kasa yana jiranta, to sun wuce.
Addu'ar Allah ya kiyaye hanya a dawo lafiya ya yi masu.
Gaba gwaggon ta yi rike da hannun Jehan, ita ma Rimsha ta rufa masu baya.
Cikin sauri ya riƙo kyawawan hannayenta tare da ɗan jawota jikinsa. Bai yi magana ba sai dai ya zubawa gwaggo da Jehan idanu har sai da suka fita, sannan ya dawo da kallonsa a kan matar tasa.
Cak ya ɗauketa sai cikin bedroom nasu, ko uppan bai ce mata ba, ita ma bata ce mashi ko uppan ba, kawai ta bishi da kallo ne.
Sai saman katafaren bed nasa ya direta. A kusa da ita ya haye ya zauna yana ta kallonta.
Kwantowa ta yi a jikinsa, cikin shagwaɓa ta ce. "Noorish lafiya?".
Hannunta ɗaya ya riƙo cikin nasa kafin ya fara magana.
"Meesha anya zan iya bari ki je wajen walimar nan kuwa? Kin yi kyau over ne".
Kyawawan fararen yatsunsa ta riƙo, a shagwaɓe ta ce.
"To shikenan Noorish ai sai na fasa zuwa! Dama me zan je nayi a wajen da mijina aljannata baya nan? Me zan je nayi awajen da farincikina baya wajen, na san ma kona je wajen tunaninka kawai zan yi ta yi, dan haka gara mun kawai na zauna a tare da kai king of my heart".
Tana magana tana murza mashi ƴan yatsunsa.
"Meesha da gaske zaki fasa zuwa ki zauna da ni?".
Da sauri ta gyaɗa mashi kai tana faɗin. "Mai zai hana my Noorish, ai bama zan fasa zuwa ba, na rigada na fasa zuwa, zan zauna da mijina".
Dogon numfashi ya ja tare da saukewa a hankali. "Me kike so ni kuma na yi maki my wife?".
Nisawa ta ɗan yi kafin ta kamo hannunsa ta ɗaura a saman shafaffen cikinta, cikin nutsuwa ta fara magana.
"Abu biyu nake so, na farko in samu ciki nima in haifi baby's nawa masu kama da kai, abu na biyu kuma shi ne bakin ruwa, kullum da ina ƙarama idan zan yi mafarkinka ina yinsa ne muna a bakin ruwa muna zuba Love, to wajen nake son ka kai'ni Noorish na".
"Iya su kawai?".
Da sauri ta gyaɗa mashi kai.
Ƙanƙameta ya yi a jikinsa sosai tare da gaya mata cewa tabbas zasu je bakin ruwan nan kamar yadda ta buƙata, maganar ciki kuma yana addu'ar Allah ya basu, Allah yasa wasan da zai buga a yanzu ya samu nasarar zura kwallo a raga.
Da amin ta amsa mashi da shi kafin ta gyara kwanciyarta a jikinsa.
Hannunsa ya zuro a ta cikin kayan nata ya fara shafa plat tummyn nata.
Narke mashi ta fara yi tana kara shigewa jikinsa. Kan ka ce me ya birkice mata, tuni ya cire duk wannan uban kwalliya da Josephine ta zauna ta yi mata ɗin, duk ya rabata da komai kafin ya fara aikin juyata son ransa, tamkar ba ɗazun suka hau network suka sauƙa ba.
Ita ma haka ta cigaba da biye mashi babu kama hannun yaro, lamarinsu sai dai mu ce azimun.......🥱
Su kuwa ƴan zuwa walima, sun jima a parlourn ƙasa suna jiran Rimshar ta fito, amma shiru bata fito ba.
Da Areef ya ga haka sai ya ce da gwaggon wai ina Rimshar suka barota ne dama?.
"Tana tare da Saif a part nawa". Gwaggo ta bashi amsa.
Guntun murmushi Areef ɗin ya saki kafin ya ce. "Ku mu tafi abinmu, dan in zaku kwana a nan Rimsha ba zata zo ba, tab Lion fa, ai tun da suka yi wannan kwalliyar suka yi kyau to ita Rimsha sai dai hakuri, kishi ba zai kyale shi ya iya barinta ta fito ba, ai muje kawai".
Da farko Gwaggo ta so ta ce su ɗan kara jira ko kuma Aseef ya je ya dubota, daga baya kuma sai ta ce to su tafi ɗin kawai, idan ma zata je shi Lion ɗin ya kawota da kansa.
Haka suka tafi abinsu, ita kuma Rimsha tana cikin bedroom tana manne da babynta suna aikin da suka saba.
Walima ya yi walima, waje ya yi waje, sun yi rabon kuɗi ba karya, sai dai fa kowa kallon Lion yake yi wa Sir Safwan, saboda ba mai iya banbantasu idan ba Rimsha da kuma su gwaggo ba, su gwaggon ma ba su jima da fara iya banbantasu ba, kunsan idan kana zaune da mutane waje guda, to dole dole a kwana a tashi watarana zaku iya rabesu komai kamanninsu kuwa, to hakan ce tasa su gwaggon ma suke iya rabesu, dan sun zauna da su, shi Areef ma dama already yana iya rabesu, ga kuma Aseef da Mahhir wato Alex, suma kada ku manta kamanninsu ɗaya, banbancin kwayar idanu ne kawai.
Kowa idan yazo kallon Sir Safwan a matsayin Lion suke yi, babu wani bare daga waje da ya iya banbanta su ko ya iya gane cewa ba Lion bane a wajen.