Triplets book 4 Complete - Chapter 8
Triplets book 4 Complete Chapter 8: Triplets book 4 Complete Chapter 8. Nan fa taga bala'i a karo na uku, dan kuwa Abba a lokacin ma bai gama dawowa cikin…
3,362 words
Nan fa taga bala'i a karo na uku, dan kuwa Abba a lokacin ma bai gama dawowa cikin hanyacinsa na abin da amarya ta yi mashi ba. Dan haka sai ya yi wa gwaggo tatas, ya koreta daga gidan, wai ta zubar masu da kimar gidansu, ta je wata ƙasa ta haifi yara, shi sam bai yarda da aure ta haifesu ba, dan haka ba zai karɓo ƴaƴan shegu ba, da ace ta zo da su ma, wlh karɓarsu zai yi ya mayarwa da ubansu su, dan babu ƴaƴan shegu a kaf zuri'ar Dr Salman. Haka dai ya yi ta surfa ruwan bala'i, ta in da yake shiga, ba ta nan yake fita ba. Daga karshe ya korata waje tare da rufo gate ɗin gidansa, ya ce ta je ya yafeta a matsayin kanwa!!.
A lokacin da yammane, wuraren karfe 6:30, bai yi wani tunani ba ya daketa ya koreta. Tana kuka tana rantse mashi da Allah wlh ba shegu bane ƴaƴanta, ƴaƴan sunna ne, dan Allah ya dai'na shaigantasu, amma ina haka ya sa kafa ya yi ball da ita. Ya ce bai san wannan ba.
Ganin zai yi mata illah ne yasa ta baro bakin gate ɗin gidan a guje kamar mahaukaciya, tana gudu tana kuka, Ammien su Imran ta yi ƙoƙarin dakatar da Abban, amma ina, sam abin ya ci tura, yaki sauraronta, ya hau dokin zuciya, dama idan baku manta ba, a baya na gaya maku, shi mutun ne mai bala'in zuciya da zafin rai!.
Bazama cikin gari gwaggo ta yi kamar mahaukaciya, da kamar zata je gidan Abbi, amma da ta tuna cewa, da Abbi da Abba halinsu iri ɗaya, sai ta gwammaci gara ta shiga duniya. Tamkar zautatciya haka ta zama. Tun tana iya gane hanyar da take tafiya a kai, har ta dai'na ganewa, ta fara ganin dishi dishi, da alama hankali ya gushe a tattare da ita. Daga karshe ma sai ta zube kasa a kasar wata bishiya ta bakin titi, kan ka ce me ta sume a wajen, saboda tukukin bakin ciki da yake cikin zuciyar baiwar Allah nan!!.
Nisawa ta yi tare da goge hawayen fuskarta, sannan ta ce "Tun daga wannan suma da na yi, ban sake sanin in da kai'na yake ba, sai da na shafi shekara kwance a gadon asibiti, lokacin da na farka kuma, da fuskar kanina Nawazuddeen na fara cin karo, shi ne yake gaya mani shakarata ɗaya a sume a gadon asibiti, tsabar bakin ciki ban ko tambaye shi daga ina ya tsintoni ba, kawai na bar maganar, shi ya cigaba da kula da ni, na bashi labarin komai na daga auren da na yi, har da yayana TRIPLETS, hakuri ya yi ta bani, ya kuma biya kuɗin jirgi muka je har Washington DC, sai dai bamu sami su Dr William ba, mun yi tambayar duniyar nan, basu ko ɗaya daga cikin gidajen iyayensu da suka bari, kowa sai ya ce bai san in da suke ba. Daga karshe dai muka hakura muka dawo, zuciyata cike da kaunar yarana, ina jin tamkar zan mutu. Kullum Nawazuddeen ajiye duk wani abin da zai yi yake yi, ya dawo gida ya zauna ya yi ta bani hakuri, yana kwantar mani da hankali, a lokacin ko aure bai yi ba, shi kaɗai yake rayuwarsa shi ma. Haka muka cigaba da rayuwa a tare, na zama tamkar mahaifiyarsa, yana yi mani biyayya over, ban taɓa yin magana ya saɓa ba, ya mayar dani islami, a nan na sami ilimin addini sosai da sosai, daga nan kuma nayi danasanin abubuwa da dama na rayuwar da muka yi da Dr, da na sami ilimin addini sosai, na fahimci wani abin, na fahimci da ni da Dr mun aikata saɓon Allah sosai a cikin soyayyarmu, kila shi ne yasa Allah ya jarrabeni da wannan kaddara, dama irin wannan saɓon da muka aikata ai ba zai taɓa yiwuwa aurenmu ta yi albaraka ba". Ta kai karshen maganar tana goge hawayen fuskarta.
Kowa da yake cikin palon sai da zuciyarsa ta raunata, ta kuma taɓu sosai, daddyn jelly kam kuka ya yi sosai, dan kun san shi dama, akwai shi da saurin kuka. Dayawa daga cikin jama'ar palon sun zub da hawaye.
Gyaran murya Brr Naurat ta yi, cikin dattaku da girma ta ce "Dr William ka ji bayanan A'isha ko? Me zaka ce kai kuma? Bayan A'isha ta baka yaran, ka gaya mana ya ka yi da su? Ina suke? Menene kuma ya faru bayan barin A'isha gidan? Ina yaron da ka illatar da sanda? Meyasame shi? Muna jiran bayananka kai ma!!". Nan fa gabaɗaya kallo ya koma kansa. Harta ƴaƴan nasa ma shi suke kallo.
Ya ɗan ɗauki ƴan mintoci kafin ya ce "Ni duk abin da ta faɗa ban sani ba, ni ban santa ba! Kuma ban taɓa ganinta ba sai yau, wata kila da wani Dr William ɗin take yi ba ni ba!"........TASHIN SENSE
Brr Naurat tana ƙoƙarin sake yin magana Areef ya daka musu tsawa cikin tsananin ɓacin rai tare da tashin hankali. "Daddy kada ka mayar da mu mahaukata mana? How comes zata bada dukka wannan labari kuma ka ce karya ne? How comes ta san su kaka? How comes ta zayyano sunayen unguwar da gidajen kaka yake da sauransu?Kawai daddy ka gaya mana gaskiya!!". Ya kai karshen maganar tare da miƙewa tsaye yana huci tamkar wani mayunwacin zaki. Tamkar ba Areef mai saukin kai da wasa da dariya ba.
Miƙewa shi ma daddyn ya yi yana faɗin "James a said a don't know her, what do you want me to tell you again?!". Ya yi maganar cikin tsawa shi ma.
Buɗe baki Areef ɗin ya yi da nufin ya yi magana. Bai kai ga yin maganar ba sai ganin Lion suka yi ya damki wuyar daddyn nasu da hannu ɗaya, ya maka shi da jikin bango tare da matse shi. Gabaɗaya ya canza lokacin guda, tamkar ba NooRin Meesha ba, idanuwansa sun yi jajir da su kamar wuta, har wasu jijiyoyi sirara ne suka fito mashi a damatsan hannunsa da kuma wuyarsa, sai wani irin numfashi yake yi mai kama da gurnanin zaki, jikinsa sai wani tsuma yake yi, ran maza ya ɓaci!.
Shi kuwa Aseef miƙewa ya yi daga kwanciyar da ya yi daga saman cinyar daddyn Rimsha, ya kifa kansa da jikin hannun sofa yana hawaye, sam baya son ganin abin da yake faruwa.
Sosai Lion ya shake daddy har sai da idanunsa suka juye, harshensa ya zazzago waje, yana daf da bakontan lahira. Ga shi Lion ɗin yaki ko da sassauta mashi, kuma ya ki yin magana, saboda tsananin ɓacin rai, dan daddy yana neman raina masu wayo.
Can kuma cikin tsawa ya ce da daddyn nasa. "Tell us the truth, if not I'll make you regret! Me muka yi maka da zaka yi mana haka? Me bamu yi maka ba? Saboda kai muka ɓoye cewa mun musulta na tsawon shekara ɗaya yanzu, duk gudun kada mu sa ciwonka ya tashi, dan mun sanka da kishin addininka, zaka iya mutuwa idan ka ji mun zama musulmai, saboda kai muka ɓoye hakan! Duk dan mu faranta maka rai, mu kuma sauke hakkin iyaye da yake a kanmu, amma kai kuma ka gaya mana meyasa ka yi mana haka? Meyasa ka bari muka taso cikin kafurci? Ka yi mana karya! Ka ɓoye mana ainahin mahaifiyarmu, ka haɗamu da wata banza a matsayin uwa, bayan kuma sisterka ce uwa ɗaya uba ɗaya! Ka cutar da rayuwarmu! Ka cusa mana tsanar abubuwa da dama a rayuwarmu wanda bai kamata mu tsanesu ba! Ka ɓoye mana gaskiya, amma da yake, ita gaskiya komai daren daɗewa sai Allah ya bayyanata, sai ga shi Allah ya haɗani da Imran, na kaunace Imran sosai! Bana son kowa bayan TRIPLETS na, amma rana tsaka na tsinci kaina da son Imran, ta dalilinsa na dawo ainahin addinina, ta dalilinsa na tako kafata na zo Nigeria, wanda a baya ban taɓa tunanin zan zo ba, da Allah ya tashi kamaka daddy, kai ma da kafarka ka tako kazo Nigeria, ba wanda ya sanyaka dole, daga kan Imran kuma ban sake kaunar wani ɗan adam ba sai Uncle ɗin James, haka kawai shi ma rana tsaka na kaunace shi, har mamaki nake yi wani lokaci, na kasa banbance da shi da Imran wa ye na fi so a cikinsu, ashe dan Allah ya gwada mana wani aya ne yasa muke kaunarsu......". Da kyar ya kai karshen maganar saboda wani tukukin bakin ciki daya tokare mashi maƙoshi. Daga haka ya yi shiru bai sake yin magana ba, sai dai sauke dogon numfashi tamkar gurnanin zaki da yake yi, ya kuma kara shake daddyn da karfi sosai!!.
Kallon Areef Abban Imran ya yi cike da tsananin tashin hankali ya ce "Areef ka dakatar da ɗan uwanka, idan ba haka ba, zai yi kisan kai, dan daddynku dab yake da ya mutu!".
Ganin da gaske hakan ne yasa Areef ɗin ya nufi Lion ɗin da sauri dan kuwa da gaske ne daddyn nasu na dab da mutuwa.
"Lion wlh zai iya mutuwa, dan girman Allah ka sake shi haka nan ya isa, ba kaga yanda yake numfashi ba ne?".
A wani irin haukace ya damko wuyar Areef ɗin ma, da ɗayar hannunsa, ya haɗesu su dukkansu biyu yana jin wani bakin azaba a cikin zuciyarsa, tafarfasa zuciyarsa take yi tamkar an ɗaura dalma a wuta! Sam baya ji kuma baya gani, idanuwansa sun rufe, yau ne ya fito da ainahin zuciyarsa fili! Duk wajen an rasa mai iya gigin yi mishi magana, dama Areef ɗin ne kawai yake da ɗan kwarin gwiwar tinkararsa a irin wannan yanayi da yake ciki, to shi ma ga shi ya haɗa da shi ya shake. Aseef kam dama tun ɗazun daya kifa kansa da jikin hannun sofa, bai sake ɗagowa ba, duk abin da suke yi yana jinsu, amma ba zai iya ɗagowa ba, bakinciki zata iya sanyawa ya haɗiyi zuciya ya mutu idan ya ga halin da suke ciki, to gara mishi ya cigaba da runtse idanuwansa kawai zai fi mashi alkhairi, Rimsha, Jehan da Akila dukkansu guduwa suka yi, suka fita daga palon, ko wace ta san halin masoyin nata sarai, sun san me zai biyo baya idan suka tsaya, gara musu su gudu abinsu.
Yau su Abba sun ga tashin hankali, an rasa mai bakin magana a cikinsu, su Imran duk sun haɗa malaman jikinsu waje guda, dan faɗar ta manya ce!!, TGA da yake jarumi ma, kirjinsa sai dukan uku uku yake yi, cikinsa na murɗawa, bare kuma saura, ai su tsoronsu a tsananin bayyane ma yake.
Daddyn Rimsha ne kawai mai ɗan kwarin gwiwan da ya kalli Gwaggo ya ce mata ta yi wa Lion magana wata kila zai ɗan sassauto ya sakesu, idan ba haka ba to tabbas dukkansu zasu mutu, wlh har Areef ɗin, dan ba shakar wasa ya yi musu ba.......
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥
*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔 ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.
*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA, INFECTION KILLER, COLACCA, SAI KAYAN GYARA PAGE. KACA KACA. YALLAGWADA. JIGIDA. RUWA RUWA. BANI BANI. WOMEN JELL BATA BATA. DAFIN KAXA. TANTABARA. XABUWA. CICCIƁI. AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER 09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH, BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S
❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥
TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️
❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)
*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*
E5
Daddyn Rimsha ne kawai mai ɗan kwarin gwiwan da ya yi ta maza, ya kalli Gwaggo ya ce mata ta yi wa Lion magana, wata kila zai ɗan sassauto ya sakesu, idan ba haka ba, to tabbas dukkansu zasu mutu wlh har Areef ɗin, dan ba shakar wasa ya yi musu ba.
Ganin da gaske har da Areef zai iya mutuwa ne yasa ta miƙe da sauri ta isa wajen nasu.
Shi kuwa Areef ɗin sam bai yi ƙoƙarin kwatar kansa ba, dan yasan duk bala'i Lion ba zai taɓa kashe shi ba! In yaga zai mutu da gaske, dole ya sake shi, sai kawai ya zuba mashi idanu yana kallonsa, kuma dama hakan shi ne dai'dai a cewarsa, ya kamata su koyawa Lion ɗin tausayi ne, idan Areef ɗin ya zuba mashi idanu yana kallonsa, to zai ji tausayinsa ya sake shi, a haka zai koyi tausayi sosai a cewarsu.
Daga ɗan bayan Lion ɗin ta tsaya, gabaɗaya idanun jama'ar palon yana a kansu, kowa so yake ya ga ya Lion zai yi idan gwaggo ta yi mashi magana....... Ni ma PRINCESS TEEMA so nake yi naga ya zai yi😂
"Saif" ta ambata a hankali, tamkar bata son yin magana, kuma kamar tana jin tsoron yi mashi maganar.
Hakika ya ji sunan har cikin ransa, duk fushi da yake ciki bai hana ya ji muryar mahaifiyar tasa ta ratsa dukka ilahirin jikinsa ba, dama shi already zuciyarsa ta yardan mashi cewa ita ce mahaifiyarsu!.....
Ganin bai amsa ba, kuma bai sakesu bane, yasa ta ɗan kara mastowa, gabaɗaya a tsorace take da ganin yanayin da ɗan nata ya shiga, kirjinta sai dukan uku uku yake yi, amma hakan bai hana ta daure ta dafa kafaɗarsa da hannu ɗaya ba. Cikin sanyin murya ta ce "Saif ka sakesu, kada ka yi masu illa ka ji ko?".
Wani irin dogon numfashi ya ja tare da saukewa a hankali, har cikin kashi da ɓargonsa ya ji sakonta! Ya ji sautin muryarta!. Ba musu ya zame hannayensa daga wuyoyin nasu. Nan take suka zube kasa, shi daddy ya suma already dama, shi kuma Areef tari ya fara yi da karfi karfi ba kakkautawa.
Uwa kenan, yau Lion ne yana cikin tsananin fushi haka har ayi mashi magana, kuma ya ji maganar ta ratsa shi? Lallai dai kam, uwa ta wuce wasa wlh!!.
Da sauri daddyn Rimsha ya yi kan Areef ɗin bayan ya ɗauko mashi ruwa a cikin fridge mai sanyi. Cike da kulawa ya dafa shi tare da kafa mashi robar ruwan a baki yana yi mashi sannu.
Shi kuwa Lion juyawa ya yi da nufin ya bar wajen, ya nufi bedroom nasa. Riko hannunsa ɗaya gwaggon ta yi, tana mai sake ambatar sunansa kirjinta na bugawa, dan tana tsoron kada su ce ba za su karɓeta a matsayin uwa ba, idan hakan ta kasance ba makawa zata iya mutuwa, dan tana bala'in sonsu, ko wani rana na duniya sai ta yi masu addu'a da fatan alkhairi tare da fatan Allah ya tsare mata su a duk in da suke, daidai da second guda basu taɓa barin cikin tunaninta ba, suna ranta fiye da tunanin mai tunani..... Allah sarki abin tausayi!.
Juyowa ya yi gareta cikin natsuwa, zuba mata idanu ya yi na ƴan sakanni kafin kuma ya tsinci kansa da rungumeta a jikinsa.
Rungume shi ita ma ta yi, tare da sauke wani nauyayyar ajiyar zuciya mai cike da tarin abubuwa kala kala a cikinsa. Nan take kuma ta fara ruwan hawaye. Wani irin sanyi shi kuma ya ji tana ratsa zuciyarsa da ya rungumeta, hakan ce ta kara tabbatar mashi da cewa lallai ita ce mahaifiyarsu, domin kuwa tun da ya taso har izuwa yau, ba'a taɓa rana guda da ya shiga cikin fushi da ɓacin rai, ace zuciyarsa ta yi sanyi lokaci guda ba, ba'a taɓa ba! Wani lokaci ma, idan ya fusata sai ya zubawa tsakiyar kansa ruwan mai tsananin sanyi, saboda ya sami sauki, dan tamkar ci da wuta zuciyarsa take yi idan ransa ya ɓaci. Amma yau rana ta farko, ya shiga ɓacin rai, daga jin voice na gwaggo kuma ya sauko cikin sauki haka, dole ba'a banza ba! Dole ita ce mahaifiyarsu ta gaskiya! Ya sami nutsuwa sosai a kanta! Yana tsananin jinta a ransa ne fiye da tunanin mai tunani! Ji yake yi tamkar ya ɗauketa a saman kafaɗarsa su yi ta kewaye duniya kawai, saboda tsantsar so da yake yi mata, ashe ba'a banza yake kaunar Rimsha ba! Ashe ba'a banza ba duk da basu son mutane, amma suka yarda da daddyn Rimsha ya zauna a wajensu, sannan kuma suka kaunace shi sosai! Ashe ba'a banza ya ji cewa dole ya tsaya tsayin daka wajen ganin ya kwatarwa da daddyn Rimsha hakkinsa na zaluntarsa da aka yi ba. Ba'a banza su Areef suke tsananin kaunar daddyn Rimsha ba, ko dan kula da mahaifiyarsu da ya yi tamkar ba gobe, ai dole ma su ji kaunarsa, uwa ta wuce wasa!!. Daddyn Rimsha ya kula da gwaggon over, shiyasa Allah dan ya saka mashi, ya jarrabi TRIPLETS ɗin da kaunarsa over!. Allah sarki rayuwa kenan, Allah mai kyauta mai kari, mai saka maka ta in da baka yi zato ba, Shiyasa ake son komai zaka yi, to ka yi shi domin Allah, dan idan ya tashi saka maka, zai yi maka babbar sakayyar da baka taɓa zato ba, a gaskiya daddyn Rimsha ɗan uwa ne na kirki da kowa zai yi fatar samun irinsa, duk bakinciki da kunci da su Abban Imran suka jefa shi a ciki, suka raba shi da mahaifinsa da Hassan nasa da suka kwanta ciki ɗaya, duk da hakan bai hana shi yana taimaka masu ba, kuma dan Allah yake yi, shiyasa da ya gamu da jarabawa na rabuwa da familynsa, sai Allah ya kare mashi familyn nasa, suka shiga hannun na gari, duk in da suka je, an rukesu hannun biyu tsakani da Allah, dan shi ma ya ruke mutane da yawa tsakani da Allah, bugu da kari, sai Allah ya bashi surukai ɗaya tamkar da million, wanda ko wani uba zai yi wa ƴaƴansa fatan samun mazajen aure irinsu, Allah ka cigaba da dafa mana, kasa komai zamu yi, mu yi shi domin ka, dan mu samu rahamarka a koda yaushe.❤️
STORY
A hankali ya kwantar da kansa a saman kafaɗar gwaggon, yana sauke numfashi mai kama da gurnanin zaki. Hannu ta kai ta fara shafa lallausan gashin kansa, da yake ya rage tsawonsa ne, ya ɗan kwanto a kafaɗarta, to tana iya taɓa kansa.
Jin sautin kukan gwaggon yana tashi a hankali hankali ne yasa ya ɗan ɗago kan nasa daga saman kafaɗar tata. Ganin da gaske take kuka ne yasa ya sanya hannu ya fara goge mata hawayen nata ba tare da ya yi magana ba.
Tamkar jira take yi wani sabon kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro ne ya kubce mata. Zafafan hawaye ne wasu suna bin wasu a kuncinta. Hakika an cuceta ba kaɗan ba, an cutar da rayuwarta ba karya, kuma a duk wannan abin da ya faru, sam bata da laifi, duba da yanayin karantar shekarunta a lokacin, ga ƙarancin ilimin addini, sannan bata wani rayuwa da mahaifiyarta sosai ba, bata taɓa haihuwa ba sai a kan TRIPLETS ɗin, a lokacin da ta mayarwa da Dr yaran, bata gama sanin zafinsu ba, sannan zuciya ce ta ɗebeta, wanda kuma dama wannan dole ce, tama yi namijin kokarin da ta hakura ta haife cikin, duk cin amanar da ya yi mata, ta daure ta haife cikin, gaskiya ta yi namijin kokari, abin a jinjina mata nema!!.
Ganin haka yasa ya ɗan raba jikinsu kaɗan tare da ɗan duƙawa ya ɗauketa cancak tamkar karamar yarinya, ya nufi bedroom nasa da ita. Gabaɗaya palon binsu da kallo suka yi, shi ma Areef binsu da kallo ya yi ya kasa motsawa, dan shi kaɗai yasan raɗaɗin da yake ji a cikin zuciyarsa. Shi dama Aseef bawan Allah sam bai ɗago kai ba ma, bare yasan me suke yi, yana kife yana kuka, Allah sarki bayin Allah!.