Triplets book 4 Complete - Chapter 7
Triplets book 4 Complete Chapter 7: Triplets book 4 Complete Chapter 7. Banda aikin rarrashi babu wani abin da yake yi. Duk jikinsa ta yi muguwar sanyi,…
3,274 words
Banda aikin rarrashi babu wani abin da yake yi. Duk jikinsa ta yi muguwar sanyi, dan ba karya ta wahala iya wahala, shi ma ya wahala sosai. Sai da ya samu good 3 hours yana aikin rarrashinta da lallaɓata kafin ya samu barci ya ɗauketa. Ganin ta yi barci ne yasa ya fita zuwa word room na gidan. Alluran barci ya haɗa mata tare da dawowa cikin bedroom ɗin.
Alluran ya yi mata kafin nan ya ɗebo kayan aiki, da kansa ya gyara ɓarnar da ya yi tare da duk abin da ya kamata. Bayan ya kammala ya tattare komai ya mayar, sannan ya je ya yi wanka, ya shirya cikin pajama ya dawo kusa da ita ya kwanta tare da jawota jikinsa ya rungume gam yana mai jin tsantsar farinciki tare da godiya ga Allah da ya sanya shi ne ya karɓi budurcin matarsa, dama idan baku manta ba, su da wuya ka sami mace virgin a wajensu, hakan tasa ya ji tsantsar farinciki na wuce misali, ji yake yi tamkar ya mayar da ita cikin cikinsa saboda so da kauna.
Haka suka kasance shi ma barci ya daukesa rungume da ita. Ba su suka farka ba sai da Josephine suka dawo can rana ya yi sanyi wuraren laasar. Josephine ɗin ce ta tashesu dan taga basu yi sallar la'asar ba ga rana na dab da faɗuwa, ita kuwa sallar la'asar ba abar wasa ba ce, Allah ya yi rantsuwa da sallar, duk halin da zaka shiga, kada ka taɓa barinta sai rana ta faɗi kayi ta. Wasu hadisai sun ce idan rana ta faɗi ma ko kayita ba'a karɓa, wasu kuma sun ce sai dai ka hakura gobe ka rama, annabi ya ce munafukai ne kawai suke bari sallar la'asar ta wucesu, dan sallah ce mai matukar muhimmanci, kada ku manta har rantsuwa da ita Allah ya yi, kunga kuwa ba abin wasa ba ce ita ɗin. Allah ka bamu ikon yinta a kan lokaci!!.
Da kuka gwaggo ta tashi mashi, sabon rarrashi ya sake farawa. Sam taki kula shi, sai tambayar lafiya take kuka Josephine take yi, amma bata samu amsa ba, dan shi ma Dr yana ta faman rarrashinta ba ta kan Josephine ɗin yake yi ba.
Da kyar da suɗin goshi ya samu ta yi mashi shiru. Umarni ya yi wa Josephine ɗin a kan ta fita musu a ɗaki. Ba musu ta fita, dan ta san halin yayan nata sarai, yanzu zai iya saɓa mata kamanni.
Sai lallaɓa beautyn tasa yake yi, amma taki kula shi, da alama fushi take yi da shi. Da kyar ya lallaɓata ta yarda ya ɗauketa zuwa toilet dan su yi wanka. Bayan sun fito, da kansa ya saka mata kaya, sai kumbure kumburen kumatu take yi, yau babu zancen my Dr, my Dr ya yi aika aika, haushinsa ma take ji.........NI KUMA PRINCESS TEEMA MALTINA MAI SANYI NAKE SHA, YO ME YAFI RA'INA?🤔 SOYAYYA AI DA DAƊI KO? SU GWAGGO YAU DAI AN GA RIBAR SOYAYYA😂
Bayan sun yi sallah ne ya kawo mata lunch ɗaki da kansa, ƙin ci ta yi, da kyar ya lallaɓata ta sha tea kawai. Bayan ta sha komawa saman bed ta ce zata yi. Cikin hanzari ya dauketa zuwa saman bed ɗin. Haka suka kasance har tsawon kwana uku yana lallaɓata tare da jinyar kayarsa, ita kuwa sai wahalar da bawan Allah take yi.
A takaice dai wannan abin da ya shiga tsakanin, ba karamar son junansu ya kara musu ba, irin soyayyarnan da ake cewa a mutu a kan juna suke yi wa junansu, abin ba'a magana. Haka suka cigaba da rayuwa tsawon shakara ɗaya da rabi. A lokacin saura shekara ɗaya da rabi su kammala school, dan ma sun ɗaura master nasu ne, ai da ba'a haka ba, da sun jima da barin school ɗin. Ga shi karatu suke yi babu wasa, ga ilimi, dukkansu akwai kaifin ƙwaƙwalwa na wuce misali, tamkar su suka bawa kansu. (Ai dole TRIPLETS su kasance suna da basira, ba'a kasa suka tsinta ba, gado suka yi daga wajen iyaye!!)
Yanzu gwaggo kwata kwata ta dai'na samun labarin gida Nigeria, amma ko a jikinta, da alama ta mance da su ma bakiɗaya, abubuwa kuma sun faru da dama a gidan Dr Salman!.
Haka ta yi wa Dr William zanen tattoo mai shegen kyau a bayansa, shi ma ya zana mata a nata bayan, amma ta kasa kusa da mazaunanta, ya rubuta mata sunansa a wajen, ita ma ta rubuta mashi sunata a nasa bayan. Abin gwanin birgewa na wuce misali.
Babu wata matsala a tsakaninsu ko da sunan wasa. Suna rayuwar tsantsar farinciki tare da faranta ran juna. Rana tsaka ciki ya bayyana a jikin gwaggo. Nan fa bala'i ya tashi ya tsaya, nan fa Dr ya ce shi baya son ciki, baya son haihuwa, sai dai su zubar, sam shi bai shirya haihuwa yanzu ba, ita kuwa gwaggo ta ce mai rabata da cikin nan sai Allah Ubangijin da ya bata, shi kaɗai ne zai iya kwatar kayansa. Ba yanda Dr bai yi ba, ta kafe sam wlh ba zata cire cikin ba, ai ba shegu bane, da ubansu, ƴaƴan sunna ne! Dan haka dole ta haifesu kamar yanda aka haifeta ita ma!!. Shi kuma ya kafe ko da sonta ko babu sonta, ko da saninta, ko babu saninta, sai ya salwantar da cikin. Da ta fahimci hakan ne, sai ta dai'na bari suna kusantar juna, kwata kwata ta dai'na kula shi.
Amma fa abin ya yi mugun ɗaure mata kai na cewa da Dr ya yi baya son haihuwa, ta san dai a baya yana yawan maganar yara, to how comes kuma sun sami cikin ya ce shi baya son yara? Ko dai dama a bayan ma yaran uncle's nasu kawai yake so ne? Abin ya sakata cikin tunani, wai baya son yara kwata kwata a rayuwarsa. Babbar magana!!.
(Ashe ba a kasa Lion ya tsinci tsanar yara ba! Kunga kuwa yanzu da Lion ya ce baya son yara ai bashi da laifi ko? Dan ɗan gado ne shi ɗin, ya gada komai tsab, har ma ya ninka mahaifin nasa zafi da tsauri. Lallai akwai cakwakiya, Lion baya son yara, ga shi ya kamu da son Rimsha, ko ya za su kare?🤔 Ni dai PRINCESS TEEMA ina da Maltina mai sanyi a fridge, idan suna bala'in da na ji ba zan iya jurewa ba, sai na kora maltina ta ta kwantar mani da hankali)
Wasa wasa faɗa ya yawaita a tsakaninsu har Dr ya fara ƙoƙarin illatata. Ganin zai iya illatata ita da abin da yake cikin cikin nata ne yasa ta fara ƙoƙarin barin gidan. A nan ne Josephine ta tambayeta me yake faruwa? Bata ɓoye mata komai ba, ta gaya mata, sosai Josephine ta sha kuka, dan ita tana matukar son gwaggo ta haifa musu yara, kullum tana addu'ar Allah ya bawa gwaggon ciki ta haifa musu twins, sai dai ita dama already tasan Dr William baya son yara, sam baya son hayaniya, ta san ba zai taɓa karɓar wannan ciki na gwaggon ba, dan kullum yana yawan faɗawa mum ɗinsu kafin ta mutu, yana gaya mata cewa shi da ya haifi yara, gwara ya mutu bai kula mata ba!!..... Yau ake yin ta kenan, tashin sense.
Haka Josephine ta yi ta bawa gwaggon hakuri a kan kada ta je ko'ina, In Sha Allah Dr zai sauko ya so cikin, amma ina wani muguwar tsana ma ya kara yi wa cikin na wuce misali.
Tsanar cikin ne ma har ya shafi ita ma gwaggon, ya tsaneta sosai. Daga karshe ma sai ya yi yunkurin kasheta ita da abin da yake cikin nata. A ranar Josephine ce ta tseratar da ita daga hannunsa, a in da ta gudu da ita izuwa ɗaya daga cikin gidajen daddynsu, wato Jacob Roshan, suka bar Dr William uncle Herry sai TGA, ita dama Cherish bata san me yake faruwa ba.
A nan suka cigaba da rayuwa da gwaggon da ita Josephine ɗin, dan ta ce wlh ba zata koma wajen Dr ba ita ma, zata zauna ta kula da gwaggon, baiwar Allah tana da tausayi sosai ga kirki na wuce misali. A lokacin Cherish tana kasarsu ta je hutu. Ita kuwa gwaggo bata je hutu ba, kuma ba'a nemeta a gida ba, dan a lokacin gidan nasu ya rushe bata sani ba, tana nan ta biyewa Dr ya kaita ya barota, da ba dan Josephine ba, da bata san in da zata sanya rayuwarta ba, da kila izuwa yanzu ma ta mutu. Allah sarki rayuwa kenan.
Hakika Gwaggo ta sha bakar azabar wahala na rabuwarta da Dr, tamkar ba zata yi rai ba, dan tana tsananin kaunarsa fiye da tunanin mai tunani. Shi kuwa yana can ko a jikinsa, sai ma sharholiyarsa da yake sha, da alama ya mance da ita ma, da alama fa dama ba sonta tsakani da Allah yake yi ba! Kawai ya yaudareta ne!. (Wata kila shiyasa su Lion basu jinsa sam sam a ransu🤔 to lokaci dai zai nuna mana komai, amma ni da ku duk mun san cewa alhaki kwaikwayo ne! Ga mutuwar su Jacob ma dai..hmmmm akwai abubuwa da yawan gaske, wlh wasu cakwakiyar idan aka ɓallo maku sai kun ji kanku ta buga!!)
PRINCESS TEEMA..✍️❤️
Da kyar tare da addu'a da taimakon Josephine gwaggo ta dawo dai'dai, da farko da ta ji wahala na soyayyar Dr dake neman hallakata, sai ta ce wa Josephine ta yarda zata zubar da cikin kawai ta koma wajen mijinta, dan ba zata iya yin nisa da shi ba. Kasancewar Josephine tana bala'in son yaran yasa ta yi ta rarrashinta tare da yi mata dabara har ta yarda ta bar ciki.
After some weeks
A haka Cherish ta dawo hutu ta same su, abin kwata kwata bai yi mata daɗi ba, duk sai ta ji ta tsani Dr sosai, ta kuma tsani maza fiye da tunanin mai tunani.
Zaune ta isko Gwaggon a cikin bedroom saman bed, kusa da ita ta zauna tare da fara bata hakuri. A kule gwaggon ta ce. "Cherish kin san me kike faɗa kuwa? Hakuri fa kika ce nayi? Wlh ba zan hakura ba, sai na ɗauki fansan abin da Dr ya yi mini, wlh sai na kashe shi!".
Zaro kananan idanunta na ƴan China Cherish ɗin ta yi tare da dafe kirji, a ruɗe ta ce "A'isha kisa fa kika ce? Please ki dai'na batun kisa, kin san Allah ya hana hakan". "Cherish idan kika ga ban kashe William ba! To wlh ba Dr Salman ba ne ubana, William ya cuceni! Ya zalunce ni! Yanzu ki gaya mini me zan cewa ƴan uwana da iyayena? Wlh billahi ba zan zubar da wannan cikin ba, sai na haife shi! Kuma ba zan bar Washington DC ba har sai na kashe William! Wai da kike wannan magana ma Cherish kin san waye babana kuwa? Ba makawa kashe ni zai yi idan ya ji abin da ya faru da ni, dan haka kada ma ki sake kawo mini maganar na yi hakuri a nan wajen!!"................SU GWAGGO AN JI WUYA, AN TUNA DA DR SALMAN,😂 WAI SAI YANZU TAKE TUNANIN ME ZATA JE TA GAYWA DR SALMAN?🤔 SOYAYYA RUWAN ZUMA!
Shiru baiwar Allah Cherish ta yi bata sake yin magana ba har Josephine ta dawo ta samesu zaune a wajen, zama ta yi suka cigaba da jira. Ita dai Cherish haka ta wuni sukuku da ita har izuwa dare, sannan ta wuce gidanta.
A takaice dai haka suka cigaba da rayuwa, gwaggo tana zuwa school, sai dai bata bari su haɗu da Dr, har cikinta ya girma ya isa haihuwa, Dr bai sake nemanta ba, bai sake leƙota ba, da alama ya mance da ita, baiwar Allah, ita kuma tana ta faman dakon soyayyarsa, a kullum tana tunaninsa fiye da yanda take tunanin komai na rayuwarta.
A haka har Allah ya sauketa lafiya, tashin farko ta haifo ƴan ukunta tsala tsala da su, lafiyayyun yara masu jini a jika, kyawawan gaske, jinin Roshan. Ba abin da ya fi sakata cikin tashin hankali sama da yanda ɗanta na farkon ya yi mugun kama da Dr William, harta blue eyes nasu. Biyu daga cikin yaran nata sun kasance farare ne over, ma'ana sun fi ɗayan haske, haka zalika su biyun da suka fi hasken, sun kasance kwayar idanunsu iriɗaya ne, sak irin na Dr, shi kuma ɗayan haskensa kamar na Dr ne, sannan yana kama da Josephine sak babu maraba, kai kace ɗanta ne ma, saboda tsantsar kama.
Bayan ta dawo cikin hayyacinta ne ta zubawa ƴaƴan idanu, tana kallonsu, basu da maraba da familyn Dr, dukka babu wanda ya ɗaukota a cikinsu, duk su Josephine ne, jajir da su tamkar tsada, ga bala'in kyau tamkar su suka faɗi irin halittar da suke so ayi musu, abin ba'a cewa komai.
A lokacin ne kuma wani bakin shaiɗani ya shiga cikin tunanin gwaggon, nan ta fara tunanin to akan me zata rike yaran Dr? Ai kawai ta kai mashi kayansa, kada ta shayar da su, dan babansu ya cutar da ita, ya ci amanarta, ya ci amanar yarda da soyayya, tun da Allah yasa sun kammala karatu last month, kawai ta bashi yaransa, ita kuma ta koma Naija, idan har ta rike yaranma ai ya cuceta da yawa............. KUSKURE KU HUKUNTA WASU DA LAIFIN DA WASU SUKA YI MAKU,❌ DR SHI YA YI MAKI LAIFI BA TRIPLETS NAKI BA! KUSKURE KI CE BA ZAKI RUKE SU BA, DAN DR YA YI MAKI BA DAI'DAI BA!!
Wannan banzar tunanin ne yasa ta ɗaukesu tare da haɗa wasu kaya nata da kuma wani farar takarda da ta yi rubutu a kansa da yaren su na tatar, wato yaren Na'urat, ta haɗa da chains ɗin da Na'urat ta bata, dama chain ɗin guda shidda ne, ta bawa Josephine ɗaya, Cherish ɗaya, saura huɗu, sai ta zuba uku a cikin wani ɗan ƙaramin, bayan ta raba tambarin heart na ɗayar sarkar kenan. Sannan ta ɗebesu, sai hanata Josephine take yi tana bata hakuri, amma ina ta zuciya, shaiɗan ta buga mata ganga, kuma ta taka rawa, tukukin bakin ciki na abin da Dr ya yi mata ya dawo mata sabo, ji take yi tamkar ta kashe Dr kawai ma ta huta.
Haka ta ɗaukesu zuwa gidan Dr. Da sauri Josephine ta bi bayanta, dan kada su je su yi ɓatatciya da Dr, saboda ta san halinsa.
Ta kuwa yi sa'a yana gida zaune a palo, ya yi wani fresh da shi, ya yi ɓul ɓul abinsa.
Babu ko sallama ta shiga palon. A saman sofa ta ɗaura yara jariran da ko kwana uku a duniya basu yi ba, nono ma sau ɗaya ta gwada basu, da ta ji zafi ta ce ba zata iya ba, ta koma basu madara, daga karshe ta kwasosu zuwa wajensa.
Murje idanu Dr ya yi ya ce bai san da wannan zance ba, shi ba zai karɓi yaran ba, dan yaranta ne ba nasa ba, ta kwashesu ta fita ko kuma ya yi mata illa, ya sanyata ta yi dana sanin zuwanta duniya.
Kin kwashesu ta yi, ita ma sai ta hau dokin zuciya, a in da ta shiga gaya mashi bakaken maganganu over. Abin dai sam ya zamar musu babu daɗi. Daga karshe Dr ya ɗauko sandar buka horking nasu Uncle Herry, ya ce ko ta ɗauki yaran su fita, ko ya kasheta ita da yaran.
Ta dauka wasa yake yi, sai ta ce wlh ba zata ɗauke su ba, ya yi abin da zai yi!!.
Babu wani tunani, babu tsoron Allah ya ɗaga sandar zai buga mata. A guje ta miƙe daga samar sofar ta nufi waje, shi kuwa yana sauke sandar sai tsakiyar kan ɗaya daga cikin jariran nan nasa. Nan take yaro ya sandare musu, ko motsawa bai yi ba, tamkar rai ya yi halinsa, amma ga jini yana malala daga kansa.
Ganin hanan yasa Dr ya yi wurgi da sandar ya yi kan yaran, dan ya tsorata sosai, yasan cewa idan wani abin ya samu yaron nan, to wlh gwamnati ba zata bar shi ba, duk da uncle nasa ne yake a kan mulki, tabbas sai an hukunta shi idan ya cutar da jariri, hukunci kuma mai tsaurin gaske.
Ita kuma gwaggon ta yi waje bata san me ya faru ba. Da gudu Josephine dake tsaye a bakin kofar palon tana ganin komai ta kariso cikin palon, dan ta duba jariran.
A matukar haukace Dr ya kwashesu zuwa asibiti dan a duba mashi yaron ya mutu ne ko yana raye, ba shi da kwanciyar hankali da zai iya dubasu!!.
Ita kuwa gwaggo, tun da ta bar palon bata sake waiwayo su ba, ta ce idan Dr ya ga dama ya kashe yaran ai nasa ne, dan haka sai ta wuce gida abinta.
Tana zuwa ta hau shirin komawa Nigeria, tun da sun kammala karatu. Sai dai fa, da kyar a daddafe ta yi kwana ɗaya na rashin yaran nan. Washegari ta wuni tamkar mara lafiya. A daddafe ta kai yamma. Zuwa dare ta ji ba zata iya rayuwa babu yaranta ba, dan haka sai ta shirya ta tafi gidan Dr.
Abin mamaki abin al'ajabi, ko da ta je sai Dr ya ce wlh ba zai bayar da yaran nan ba, yara dai yaransa ne! Kuma ta fita mashi a gida dama shi ba sonta yake yi ba, idan har bata fita ba, sai ya sanyata ta yi danasani mai girma.
Da farko ta ki fita, sai da ta ga zai yi mata kaca kaca ne ta kama kanta tana kuka tare da danasanin sanin Dr da ta yi a rayuwarta, tamkar ranta zai fita haka ta bar gidan.
A ranar Josephine ta zo har gidanta suka kwana a tare, dan ta ɗebe mata kewa. Kwana kuka Gwaggon ta yi tana danasani kai mashi ƴaƴanta da ta yi. Ita kuwa Josephine kwana rarrashinta ta yi. Abin gwanin ban tausayi, shaiɗan ya yi mummunar aika aika a tsakanin masoyan guda biyu.
A takaice a cikin satin Gwaggo ta shirya ta dawo Nigeria, dan ta zo ta gayawa Dr Salman abin da yake faruwa, saboda su je su karɓo mata yaranta, ba zata iya rayuwa babu su ba, zata mutu idan ba'a karɓo mata su ba.
Haka ta baro Washington ba tare da ta sake saka yaran nata a idanunta ba, bata san a wani hali suke ba, bata san ya suke a hannun Dr William ba, shin ya karɓesu a matsayin ƴaƴa ne ko yaya? Duk bata sani ba, bata sake sanin komai dan gane da su ba!!.
Tana dawowa gida Nigeria ta tarar da bakin labarin da ta gwammaci mutuwa a kansa. Wato ta tarar da labarin Dr Salman ya rasu da shi da Naurat da Amarya, a yanda aka ce accident suka yi dukkansu suka mutu. Abu kaɗan ya hana ƙwaƙwalwar gwaggo bai juye ba, ga rashin iyaye, ga rashin masoyi, ga kuma uwa uba rashin jariran ƴaƴanta, ga rashin ƴan uwa. Dole ta yi hauka data ga Dr William, dan ya cutar da rayuwarta, duk shi ne silar komai a rayuwarta. Da badan son shi ba, ai da ba zata mance da kowa ba har iyayenta su rasu bata sani ba!.
Tun tana kuka da hawaye, har hawayen nata suka dai'na fita. Cikin raɗaɗi da kunan rai ta nufi ɗaya daga cikin gidajen Dr Salman, in da aka ce mata nan Abba ya yi aure. Tana zuwa ta yi sa'a Abban yana gidan. Tana kuka tamkar zata mutu ta fara bashi labarin abubuwan da suka faru da ita, tun daga farko har karshe. Daga karshe ta rufe mashi da cewa, dan girman Allah ya taimaka ya karɓo mata ƴaƴanta a wajen Dr William, dan ba zata iya rayuwa babu su ba.