Kenza eBookz

Triplets book 4 Complete - Chapter 6

Triplets book 4 Complete - Chapter 6

Triplets book 4 Complete Chapter 6: Triplets book 4 Complete Chapter 6. A lokacin da za'ayi jana'izarsu su mum, za'a kaisu mutuware, wato jana'izar…

3,320 words

A lokacin da za'ayi jana'izarsu su mum, za'a kaisu mutuware, wato jana'izar kiristoci, an buƙaci da Dr William ya zo ya wuce gaba a matsayinsa na babban ɗansu, amma sam baya wajen, hasalima bai san da zancen mutuwar ba, duk da cewa labarin ya baza gari, abin ku da manyan mutane, sai dai shi bai sami labari ba, dan yana babbar masallaci jumma'ar musulmai dake garin, tun da ya bar gidan suka wuce can da gwaggon, kafin ya tafi kuma sai da ya kashe wayarsa, a cewarsa kada ma su mum ɗin su kira shi, dan confirm sai ya musulunta. TASHIN SENSE.

Kasancewar ba'a sami Dr William ko a waya ba, haka aka ce Uncle Herry ya wuce gaba, Josephine ta bi bayansa, dan da aka tambayesu ina Dr William, sai suka cewa jama'a ai Dr William baya nan, sun dai ki faɗar gaskiya. Haka aka kai gawarwakinsu mum ɗin mutuware, sai kuka su Josephine ɗin suke yi tamkar ransu zai fita.

A ɓangaren Dr William kuwa, suna fita Masallaci ya wuce da gwaggon, a in da ya je ya gayawa liman ga abin da yake tafe da su, ya gaya mashi aure suke son yi, kuma iyayensu basu son aure, saboda iyayensa sun ce a'a, kuma sun hana shi musulta.

Duba da yanayin kasar tasu, ba musu limamin ya bashi kalmar shahada tare da tambayar gwaggo shin da gaske tana son Dr William, sosai ta tabbatar musu da hakan, ba ɓata lokacin limamin ya ɗaura musu aure bayan an fito sallar azzahar, a cewarsa, ai sun fi shekaru goma sha takwas, dan haka suna da ƴanci da kansu, suna da ƴanci su yi abin da suka ga dama, shi ne yasa aka ɗaura musu aure bayan musultar Dr.

Ita kuma gwaggon a lokacin idanunta sun rufe, tana ganin kamar iyayen Dr William za su zo su rabata da shi, ba zata iya rayuwa babu shi ba, shi ne kawai yasa duk abin da liman ya ce mata, sai ta ce mishi e, dan a lokacin bata da burin da ya wuce Dr William ya musulunta, a ɗaura musu aure, su mallaki juna, shi ne yasa ta yarda, bata bi ta kan iyayenta ba, dan tana ganin suma zasu tsaya ɓata mata lokaci ne har a rabata da Dr.

Bayan an ɗaura musu aure, kai tsaye gidan Gwaggon suka wuce abinsu, yau sun zama sabbin mutane. Ko da suka je gidan, komai na kayan kallo a kashe, basu sami labarin abin da yake wakana a gari ba. Rungume juna suka yi suna tsananin murna da farinciki, yau sun mallaki juna na har abada.

Kissing nata ya fara yi, cike da so da kauna ta fara mayar mishi da martani. Sun ɗan yi nisa cikin abin da suke yi, tamkar wanda aka muskula ta miƙe tana faɗin "My Dr bari na kira mum ɗina na gaya mata yanda aka yi komai, dan kada asamu matsala ka ji?".

Idanuwansa a runtse ya jawota jikinsa yana faɗin "A'a kada ki gaya musu yanzu, kada suma su rabani da ke, ki bari sai mun sami hutu a school, sai mu je gidan a tare ko?".

Jinjina mashi kai ta yi cike da gamsuwa da kuma yarda da shi ɗari bisa ɗari, dan ta faɗa makauniyar soyayya, baiwar Allah, ba laifinta bane, laifin so ne, da bashi da adalci idan ya shiga mutun.

"My Dr ka bari, bari na je nayi wanka nazo ko?". A kunne ya raɗa mata yau kam a tare za su yi. Bata yi mashi musu ba, dan sun mallaki juna, kafin su mallaki juna ma, dama wani lokaci ko tana toilet yana shiga ya yi abin da zai yi, bare kuma yanzu, ai sai abin da hali ya yi.

A tare suka wuce cikin toilet ɗin. After some minutes suka fito rungume da juna, tamkar wani ya ce zai kwace musu junansu. Yau dai a tare suka yi komai, kama daga shafa lotions, shiryawa cikin kananan kaya, da yake da akwai kayansa sosai a gidan, dan idan baku manta ba, wani lokaci a gidan nata yake kwana a baya, hakan tasa ya sayi wasu kaya ya zuba a dressing room nata. Komai suke yi suna yi ne suna wasan masoya cike da so da kauna.

Da zata shiga kitchen ma, a tare suka shiga da shi. Duk da cewa bai iya aikin komai na kitchen ba, amma ya tayata da hira na kalaman soyayya masu daɗi, tare kuma da tana aiki yana rungumeta, ko ya shafi mazaunanta. Kayan kwalama ta haɗa musu tare da green tea mai zafi sosai.

A palo suka baje abinsu, a lokacin kuma har an kaisu Jacob mutuware an dawo, duk basu da labari. Sai da suka fara shan tea ne ta ɗauko wayarta tare da kunna data dan ta yi wa Cherish massage a Whatsapp na yau sun yi aure da Dr, sun mallaki juna, ta zo ta tayata murna.

Tana kunna data sakon Cherish ɗin ya shigo wayar nata na tayata alhinin rasa iyayen saurayin nata Dr William wanda yake a matsayin mijinta a yanzu kenan. Wani irin ihu ta kurma wanda bata san time ɗin da ya fito daga bakinta ba, jikinta na kakkarwa ta yasar da wayar kasa.

Cikin tashin hankali ya riko kafaɗunta yana tambayarta lafiya? Ihun me take yi. Kasa magana ta yi, nan take hawaye suka cika mata idanuwa, domin tasan Cherish ba zata taɓa yi mata karya ba, tun da ta yi mata wannan massage ɗin, to gaskiya ne, iyayen Dr William sun mutu. TASHIN SENSE!!!.

Ganin taki amsa mishi tambayar da yake yi mata ne, yasa ya ɗauki wayar tata dan ya duba me ta gani take wannan ihu. Dubawa da zai yi bai san time da ya saketa ya wani irin mikewa a razane ba.

Ita ma mikewa ta yi tana hawaye jikinta duk sai ɓari yake yi, abin mamaki yanzu bai fi awa biyar da suka rabu da su ba, amma ace sun mutu dukkansu biyu? Wannan dole bawa ya shiga tsananin tashin hankali.

A hanzarce Dr ya wuce ya ɗauko wayarsa, cikin tashin hankali, idanuwansa suna gani bibbiyu, ya fara ƙoƙarin kunna wayar. Ya kasa saboda kerma da jikinsa yake yi, wayar ta kasa tsayuwa waje guda a hannun nasa.

Daga karshe ita ta karɓa ta kunna mashi. Number uncle Herry ya fara kira, bugu ɗaya ya ɗauka. Cikin tsananin tashin hankali da razana ya fara magana yana haɗe word, a in da ya tambayi uncle Herryn ɗin ina dad da mum.

Ba ɓoye ɓoye ya gaya mashi sun mutu. Ya ilahi ya lillahi, bai san time ɗin da ya saki wayar tasa ta faɗi kasa ba. Kasa tsayuwa waje guda ya yi a in da ya zube gwiwowinsa a kasa a wajen, yana wani irin numfashi mai kama da gurnanin zaki.

Tsugunnawa ta yi a kusa da shi tare da ɗan rungumo shi a jikinta, sai ruwan hawaye take yi. Muryarsa tamkar mara lafiyar da ya yi shekara cikin mawuyacin hali ya ce mata. "My.....my beauty.... Don't tell me that what i heard now about my dad and mum is true, say it's not a true to me".

Rarrashinsa ta fara yi tare da kara mashi karfin gwiwa. Ina ai kasa hakura ya yi, zuciyarsa ba zata iya ɗauka ba, idanuwansa sun yi jajir da su. Ta yi ta yi a kan ya tashi su je gidan, amma ina ya kasa koda motsawa, dan yana bala'in kaunar iyayen nasa fiye da tunanin mai tunani, sune duniyarsa, duk abin da yake yi musun nan yana tsananin sonsu, ace lokacin guda ya rasasu? Kai abu ne wanda zuciyarsa ba zata iya ɗauka lokaci guda ba, dan ma dai yana da taurin zuciyar ce, ai da abin ya wuce hakan.

Sai da ya ɗauki almost 1 hour a durkushe a wajen, sannan ne ya iya ɗan motsawa. Da kyar ya mike. Da dafa bango ya fito palo. Da sauri ta ɗauki bakullin mota ta biyo bayansa.

A takaice ita ta ja motar suka nufi gidan. Har lokacin jama'a na cike taf a gidan. Bai kula kowa ba ya wuce ciki, yana tafiya tamkar zai faɗi kasa, ya rike hannun gwaggo gam dan kada jama'a su rabasu, ta je ta ɓace mashi kuma.

Kai tsaye hawa na biyu suka wuce, a nan suka sami su uncle Herry da su yayyun dad ɗin nasu, sun sha kuka tamkar ba gobe, shi kuwa Dr William ya daure, idanuwansa sun yi jajir kamar wuta, amma sam bai yi kwallah ba.

Sai bayan sati biyu da mutuwar iyayen nasu ne ya fara gane kansa, nan ma da taimakon gwaggo da take kwantar mashi da hankali, ba karya ya shiga tsananin damuwa da tashin hankali na wuce misali, har wata iriyar mummunar rama ya yi, tamkar ba shi ba, iyaye ba wasa ba! Kuma dukkansu a lokacin guda, a hakan ma su Uncle Herry basu gaya mashi cewa sanadiyarsa ne yasa hawan jinin dad ɗin nasu ya tashi har ya mutu ba, sun ɓoye mashi, wata kila da sun gaya mashi shi ne sula, tashin hankali ne shi ma zai kashe shi.

Haka suka kasance a daddafe har tsawon wata da rasuwar iyayen nasu, sannan ne ya ce shi ba zai iya zama a wannan gidan ba, dan idan har ya zauna, kullum zai rinƙa kwana ne cikin kunci da bakinci tare da ganin tamkar iyayensu suna tare da su a gidan kamar baya, dan haka shi zai koma ɗaya daga cikin gidajen daddyn nasu ya zauna tare da gwaggon, za su ɗauki Tga su rike tun da a lokacin shekararsa biyu da ƴan watanni.

Uncle Herry da Josephine suka ce suma za su bishi, ba za su iya zama ba. Tambayar gwaggo ya yi a kan zata iya zama da familynsa, cike da murna ta ce mashi e, dan haka sai suka tattara duk wani abin da za su buƙata, suka rufe gidan tare da sallamar gabaɗaya ma'aikatan, sannan suka tafi zuwa wani gidan bene mai hawa ɗaya, shi ma ɗaya ne daga cikin gidajen daddyn nasu, ba karya ya kawatu iya kawatawa gidan.

A nan suka fara sabuwar rayuwa, gwaggo da Josephine sun zama very close friend, dan a lokacin shekarunsu kusan ɗaya. Cherish tana zuwa suna rayuwar farinciki.

Da Josephine da Uncle Herry duk sun karɓi musulci, gwaggo ta musultar da su, daga baya ita ma Cherish ta musulta. Rayuwa mai tsabta da farinciki suke gudanarwa a gidan. Har tsawon wata ɗaya da dawowarsu gidan sam Dr William bai kusanci gwaggo ba, dan har lokacin bai warke daga raɗaɗin rashin iyayensa ba. Ita ma Gwaggo bata wani damuwa na rashin soyayya da basu yi, dan ta san halin da yake a ciki.

A tare suke yin aiki da Josephine, komai tare tamkar twins, Uncle Herry kuma kullum yana tare da TGA yana koya mishi wasu abubuwa na rayuwa. Idan suka tashi tafiya school, akwai wata mai aikin TGA ɗin da take kula da shi, dukkansu suna tafiya su bar shi.

Sosai Dr da gwaggon suka mayar da hankali a kan karatu, dama already kun san basu wasa da karatu..........

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️❤️🔥

*KINDADE KINA NEMAN ABUN DA ZAI SANYAKI QIBA,QIBA MEKYAU KIYI DIMIMI DUK INDA KIKA SHIGA BABU RAINI KINYI TA SIYA KINA ASARAR KUDINKI🤔 ALBISHIRINKI NAZO MIKI DA ABUN DA ZAKISHA BA TARE DA KINYI ASARAR KIDINKI BA 💃 Yana da matiƙar kyau sosai ko'ina naki zai chiko ki xama abar sha'awa duk mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09067614054, kada ki bari ayi babu ke, kayanmu tested and trusted ne, guarantee ne*.

*KINDADE KINA NEMAN ABUNDA ZAI SANYA KISAMU XAMAN LFY TARE DA KWANCHIYAR HANKALI? TO BABYN HABIBI KIXO UMMU AFFAN TAXO MIKI DA SHAHARARRUN KUMA INGANTATTUN MAGUNGUNAN MATA, KAMA TUNDAGA KAN HUMRA, TURAREN WUTA, INFECTION KILLER, COLACCA, SAI KAYAN GYARA PAGE. KACA KACA. YALLAGWADA. JIGIDA. RUWA RUWA. BANI BANI. WOMEN JELL BATA BATA. DAFIN KAXA. TANTABARA. XABUWA. CICCIƁI. AND EXCLUSIVE, XUMA TASTED AND TRUSTED INA FARIN CHIKIN SANAR DA KU MUN FARA RAMADAN PROMO GAME BUQATA XA A IYA TUNTUBA NA TA WANNAN NUMBER 09067614054 JIGAWA STATE MUNA AIKAWA KO'INA CIKIN AMINCI DA YARDAR ALLAH, BABYN HABIBI KARKIMANTA DA KAYANMU FIRST CLASS NE, DAGA KANSA AN RUFE KOFA, YANA DA INGANCI NA WUCE TUNANINKI*.

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S

❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥❤️🔥

TSARAWA DA RUBUTAWA......✍️

❤️FATEEMA ZAHRA MUSA (💫PRINCESS TEEMA💋)

*Domin samun damar karanta littafin nan daga farko har karshe zaki iya nemana ta wannan number 08161390581*

E4

*Ina yi wa ɗaukacin al'ummar musulmi ta duniya barka da sallah, Allah Ubangiji ya maimaita ma, ya karɓi ibadunmu ya sa kuma muna daga cikin ƴantattun bayi, wannan page sadaukarwa ce, barka da sallah ce ga ƴan comments section group na, ina farincikin kasancewa a tare da ku, kuma dukkanku ina ganin comments na kowa, tare da adduo'inku da yaba mani da kuke yi, tare da kwarin gwiwan da kuke kara mani, ba abin da zan ce maku face Allah ya bar zumunci, hakika kuna sakani farinciki da comments naku, hakika kuna cikin tunanina a koda yaushe ❤️*

Sosai Dr da gwaggon suka mayar da hankali a kan karatu, dama already kun san basu wasa da karatu. A takaice sai da suka ɗauki almost wata biyar da aurensu kafin Dr William ya dawo dai'dai na rashin iyayen nasu da suka yi, a lokacin ma ya dawo dai'dai ne sakamakon adduo'i da kuma karatun Alkur'ani mai girma da gwaggon take yawan yi mashi. Shi ma yana koyan hadda sosai a wajen limamin da ya bashi kalmar shahada, haka su Josephine ma suna karatun addini sosai. A lokacin Josephine sunanta A'isha, dan ta ce sunan gwaggo take so a saka mata, shi kuma Uncle Herry sunansa Muhammad, TGA kuma Sudais. Suna rayuwa cikin tsantsar farinciki.

Har lokacin gwaggo bata san da abin da yake faruwa a gida Nigeria ba, ita dai soyayya ya rufe mata idanu, sabgar gabanta kawai take yi. Bayan Dr William nata, bata tunanin kowa, shi ne a ranta dare da rana. A haka almost shekara guda kenan da aurensu.

Yau ta kama Sunday, babu school, duk suna haɗe a gida suna hira. Cherish ma ta zo gidan nasu. Da Josephine wato A'isha da gwaggo suna kitchen suna haɗa kayan makulashe, karfi da ya ji gwaggo ta koyawa Josephine shiga kitchen, ita ma Gwaggon ba wani abin da ta iya yi face dafa tea sai ɗan snacks da ba'a rasa ba haka. Idan ta shiga kitchen hada even tea, sai ta fi 40 mins ana abu guda, amma a haka take zagewa ta shiga dan ta yi wa Dr tea da kanta, bata son ƴan aiki su yi mashi tea ɗin.

After some minutes.

Zaune take a saman bed nata a cikin bedroom nata tana duba wasu takardunsu, dan sun kusa fara exams, daga ita sai wando zuwa iya santala santalan cinyoyinta, da kuma ƴar riga da bata gama rufe cibiya ba, ta saki gashi har baya, tana aikin taunar chewing gum.

Josephine da Uncle Herry sun ta fi yawon shakatawa, dan yau week, Cherish na palon kasa, ita da TGA, tana aikin bashi hot milk, tana bala'in kaunar TGA kamar me, sai dai shi kuma, tun yana yaro, yana da bakar zuciya na wuce misali, ga saurin fushi da taurin kai, tun yana karami idan ya ce ba zai yi abu ba, to kamar Lion yake, ba zai yi ɗin ba, sai dai a kashe shi, abin dai ba'a cewa komai. Amma da yake Cherish ta san halinsa, sai ta koyi zama da shi, tana yi mashi abin da yake so, har tasa ya saba da ita sama da yanda ya saba da su Josephine, har ɗaukarsa take yi su je gidanta su wuni, ya zama kamar ɗanta, tun Dr yana hanawa, har ya saduda, ya kyalesu kawai.

Dr William, sanye yake da short irin masu kama jikin nan, kwata kwata wandon a iya rabin cikyarsa ta tsaya mashi, babu riga a jikinsa. Daga cikin ɗakin maratunsu ya fito, hannunsa na rike da wayarsa, sai aikin sauke ajiyar zuciya yake yi.

Cike da so da kauna ta kalle shi tare da sakar mashi cool murmushi kafin ta ce "My Hero ya ka ji karatun?". Gera ɗaya ya ɗaga mata yana faɗin "Normal beauty, what about you?".

Rufe takardun dake a gabanta ta fara yi tana bashi amsa da komai normal.

"Akwai wani abin da zan kara maki ne?". Ya tambaya yana tsareta da waɗan nan shegun blue eyes ɗin nasa masu rikitar da mai kallonsu.

Girgiza mashi kai ta yi kafin ta ce "Nothing gaskiya, saboda komai dai'dai nake ji, ko yanzu a fara exams kawai". "Are you sure?". Ya faɗa yana mai canza kallon da yake yi mata izuwa wani irin kallo na azababben so da kauna.

Jin yanda ya yi tambayar yasa ta ɗago da dara daran idanunta izuwa kansa. Ɗan zuba mashi idanu ta yi na ƴan sakanni kafin ta ce "Are okey kuwa?".

Nisawa ya yi tare da ɗan kashe mata ido ɗaya yana faɗin "Am not sure, but you have to be check me very well, so that you should now am okey or not". Ya yi maganar cikin wata iriyar murya da take nuna tsantsar so da kauna.

Ƴar murmushi ta yi kafin ta ce "Okey come and sleep, let me see what to do".

A hankali ya nufota, yana tafiya yana wani yarfar da hannu kamar wani ɗan baby.

"My Dr, yau fa like you're feeling shagwaɓa more for me ko?".

Ɗan turo mata ɗan bakin nan nasa ya yi kafin ya sake ciza ɗan red lips nasa, sannan ya ce "Ba dole ba, gabaɗaya you forget about me, kawai kina ta kula da su A'isha, ni babu mai kula da ni". Ya kai karshen maganar tare da kwanciya a saman bed ɗin ya kuma tada kai da cinyarta yana turo baki.

Hararar soyayya ta wurga mashi kafin ta ce "E lallai yau rigimace ma kake ji da ita ba shagwaɓa ba, amma na san maganinka".

Hannu ya kai ya ɗan shafo breast nata yana faɗin "Ga abin da zaki bani na sha sai na dai'na rigimar".

A takaice ta ce "Da a baya da kake sha ni nake baka ne?". Gera ɗaya ya ɗaga tare da ɗan zaro idanu kafin daga bisani kuma ya miƙe zaune a in da ya rungumota suka kwanta tare yana faɗin to bari ya sha kayansa. Murmushi kawai take binsa da shi. Da ya fara wasa da su kuma, sai ta fara taya shi kamar yanda suke yi a baya. Nan take ta fara gigita shi da salonta.

Romancing na juna suka fara yi babu kama hannun yaro, an jima ba'a haɗu ba, ya kware wajen iya wasa, duk ƙoƙarin gwaggo sai ta sakar mashi ragamar idan suka fara, bata ma wani iya jurewa su yi nisa zata sakar mashi, ta dai'na biye mashi, sai dai ta yi ta zuba mashi kukan shagwaɓa, hakan kuma kara rikita shi yake yi, yasa ya yi ta kara birkita mata ƙwaƙwalwa har ta yi kukan gaske.

A takaice dai Dr bai rabu da ita ba yau sai da ya kawar da budurcinta. Ta sha bakar wahala a hannunsa, har da suma ta yi, duk ta yakushe mashi fuska, saboda ta tara faratun hannu, kun san dama turawa suna tarasu sosai, to ita ma ta tarasu zara zara, hakan tasa duk ta ji mashi ciwo a fuska da bayansa kamar ya yi faɗa da damusa. Sai dai shi kuwa sam sam bai ji tana yi ba, har sai da ya kammala abin da yake yi ne, da ya sami nutsuwa, a nan ne ya ga ɓarnar da ya yi.

Ya tsorata ainun, sunanta ya rinƙa kira, amma sam bata ko motsa ba, duba da sun yi karatu mai zurfi, duk abubuwa irin haka sun karanta, hakan tasa ya sauko daga saman bed ɗin ya nufi toilet. Ruwa mai zafi ya haɗa mata kafin ya dawo cikin bedroom ɗin, ya ɗauketa zuwa toilet ɗin. Shi ya yi mata komai da kansa, sai zuba mashi kuka take yi tamkar wanda aka cewa ubanta ya mutu.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull