Turken gida book 2 cmplete by janafty - Chapter 15
Turken gida book 2 cmplete by janafty Chapter 15: Turken gida book 2 cmplete by janafty Chapter 15. Haka na faɗa ina huci Munnira na dariya, mun rabu ta ce…
3,326 words
Haka na faɗa ina huci Munnira na dariya, mun rabu ta ce min wallahi itama ba za ta je ba sai dai Hauwa ta je, kai tsaye na ce" Hauwa za ta je mana. Kin san tsoron su ta ke ji." Kamar daman na sani tafiyan Munniran ba daɗewa sai ga Hauwa, da farko ba ta faɗa min ma za ta je wajen walima ba sai daga baya wai ta na faɗa min Anty Bahijja ta kira ta ta ce ta zo, ni ko mirmishi na yi kafin na ce" Bakomai Hauwa sai kin dawo."
Saboda ni na san za ta je domin ta na jin tsoron kar ba ta je ba Anty Bahijja ta yi mata faɗa. Hauwa dai har yau ta kasa sama ma kanta ƴanci ni ko da na ke amarya a baya ban zauna wata shegiya da sunan yayar miji ko ƙanwarsa ta ta ka ni ba, kowa da matsayin shi, iya girmamawa ina ba su amma fa ba zan zauna ina jin tsoron su kamar na bauta musu ba, ba kuma su ke aurena ba ballatana su riƙa ba ni umarni ina bi cikin rawan jiki ba a baya ma ban yi haka ba ballantana yanzu da shekaru suka tura an riga an gogi jigida kowa ya san kowa.
Zuwa bayan La'asar ba kowa a gidan daga ni sai Amina sai Marwa da Firdausi da Saude sai yara sai can ne Ya Balki ta zo, da yamma Yallaɓai ya aiko Musbahu da kayan miya da sauran cefane sai Ya Balki ta karɓi gyaran Miyan kafin ma ta fara sai ga Ya Aina ta zo sai suka haɗu gabaɗaya suna yi Amina kuma sai ta dau naman ta na tafasa gefe ɗaya kuma ni ina dafa zoɓo saboda na ce a yi saboda mutane duk da Yallaɓai ya saka an kawo mana lemun kwali da ruwa amma ni ina so ne shi ya sa na ce a yi, daman kuma daga Yashe an ba mu ganye zoɓo ni da Rahila itama sai mangariba ta shigo da ya ke ta sha tsiya a wajena na ce sai ta kwanan min da ko shirin kwananta ta zo tare da yaran, sai ɗan iface ifacen yaran ya ƙara ɗan raya gidan hayaniya da hada hada ya sa na ji zuciya ta yi sauƙi ina ta harkokina.
Wajen bakwai da wani abu na yamma mai ɗinkinmu ya kawo mana kamar sun haɗa baki tare suka ƙwankwansa min gida da mai wanki, kayan Yallaɓai ne sai nawa, na yara daman kananun ni na ke wanke musu sai atamfofinsu ne da less na ke saka su a wanki ghana guda ne da kaya ya ce min Yallaɓai ne ya kira shi ya ce a kawo kayan, su Saude na kira suka kama min kayan zuwa cikin gida ina shigowa Amina ta kawo mini waya ta ce Yaya Auwal ne ya ce ya na ta kiran waya ta a ba na ɗauka sai a lokacin na tuna ta na cikin ɗaki na baro ta.
Falon Yallaɓai na shige ina waya. Ya ce min Laila ta shigo gari amma sun yi mgana ita da yara sai gobe za ta zo gidana na ce bakomai ai itama biki gare su. Mun yi shuru na wani lokaci Ya Auwal ya san ni da hira da mgana amma yau gabaɗaya na yi sanyi. Tunani na ke ni ba uwa ba, ba kakanni baa dukan ya yi mini yawa. Aka ce ɗan uwa rabin jiki ko da ya ke namiji ya fahimci ina cikin damuwa sai na ji ya kira sunana a hankali.
"Sadiya."
Na amsa da Na'am ina ɗaga idanuwana sama domin sai na ji kamar zan fashe masa da kuka.
"Ba ki bukatar wani abu?
"Ba na bukatar komai Ya Auwal kiran ka mean alot to me. Na gode" Na faɗa muryata na rawa sai kawai ya ce" Ko Yallaɓan ya yi miki wani abu ne?. Da sauri na ce" A'a ba abin da ya yi min Ya Auwal." "Kin tabbata? Sai na gyaɗa masa kai kamar ya na ganina ina ta share kwalla da gefen rigana
"E. Bakomai."
Na amsa masa cikin muryan kuka.
"To shike nan zan saka miki 50k ki kara wani abun kin ji ko?
Kamar daman ina jira ne kawai sai na fashe da kuka cikin kukan na ke faɗa min" Na gode Ya Auwal. Allah ya kara ma nema albarka Allah ya ra ya maka zuru'a. Ita kuma Mama Allah ya jiƙan ta da Rahama." Kamar mutuwar ce ta dawo min sabuwa kawai sai na ƙara volume ɗin kukana ya na ma lallashina da min mgana ba na jinsa har ya kashe wayarsa ni kuma sai na sulale a ƙasan kujera ina ta kuka ina cikin kukan nan Jidda ta zo ta ganni hankali tashe ta je ta kira su Rahila suka taho da gudu ganin yadda na saka kaina acikin gwiyoyina ina ta kuka mai sauti sai tausayina ya kama su Rahila da Amina suka rumgumeni suna lallashina Ya Aina ta kori yaran can falo domin sun tsaya akan mu suna ta kallo Jidda duk ta damu sai faman faɗi ta ke yi.
"Umma ko ba ki da lafiya ne?
Baby ko har ta fara kuka da Rigima sai Marwa ta bi su can falon su ta na lallashin su, Ya Aina ta tsaya a kaina ta na faɗin"Me ye haka Sadiya? Har na saka miki suna jarumtar mata kuma sai ki ba ni kunya! Don Allah tashi ki bar kukan nan ki yi haƙuri ki ƙara daurewa da ikon Allah alheri ne za ki yi ta gani in sha Allahu." Amma na kasa iya yin wannan jarumtar kamar ana tunkuɗo kukan daga cikin zuciyata ya na zuwa ta bakina.
Ya Balki kuma cewa ta yi" Ku bar ta don Allah ta yi kukan ta ko za ta samu sauƙin zuciya." Rahila da saurin kuka har ta fara tayani hawaye. Ni kuma ganin sun damu ya sa na ɗago ina faɗin" Ni fa ba kukan auren Yallaɓai na ke yi ba. Ina kuka ne na tuna da Mama ne."
"Allah ya jikanta da Rahama."
Suka haɗa baki gabaɗayansu wajen amsawa da Amin bayan kuma sun yi addu'a Amina sai ta fara kuka sai kawai ta tashi ta bar falon tana sharen ƙwalla ganin na ki daina kuka ya sa Yaya Aina ta kira Gwaggo a waya ta faɗa mata ba zato kawai Alhajinmu na gefe ya karɓe wayar ya kuma ce ma Ya Aina ta ba ni wayar zai yi mgana dashi.
Sai na yi saurin tsaida kuka na ina gaishe da Alhajinmu. Cikin yanayin maganarsa ya ce" Dubu in na ce ki zo gida yanzu ina son ganin ki, za ki iya zuwa? Muryata a shake na ce masa in sha Allahu, shi kuma sai ya ce na taho yanzu ya na jirana, bayan na bama Ya Aina wayar sai ta ce ko ta rakoni ne, amma Alhajimu ya ce ni kaɗai ya ke son gani. Jin haka yasa na tashi na shiga ciki ina shiryawa ina cikin ne sai ga Faridan Tariq da Sameena da Hauwa sun shigo gidan ina ta jin hayaniya sai da na sako hijabi da takalmi bayan na dauko wayata da kuɗi na fito na gansu, muka rumgume da Sameena, Farida kuma muka gaisa cikin fara'a sai ta yi min mgana ko ban jin daɗi ne ta ga idona duk ya ta sa ga muryata a shake.
"Mura na ke yi kaɗam."
Na ba ma Farida amsa daga Walima suke domin ga kayan waliman nan sun taho da shi. Hauwa na kallah kafin na ce" Hauwa zan je Ɗorayi Alhajinmu na son ganina." Tare suka haɗa baki wajen tambayan lafiya na ce lafiya ƙalau, kafin na wuce sai da na gaya musu gidan Munnira za a yi waina gobe sai Hauwa ta ce Mutaƙƙa zai zo ya ɗauke ta da safe sai ta fara sauka a gidan Munnira in sun gama sai su taho da shi Sameena ma ta ce A Gwammaja za ta kwana amma da safen za ta je can gidan Munnira su yi aikin tare Farida dai nan za ta kwana ita zan dawo na same ta, Ya Balki da Ya Aina sun ce gida za su ta fi sai zuwa gobe, nan muka yi sallama Hauwa kuma har waje ta rako ni muka taka har bakin titi na samu abun hawa shi ne ta ke faɗa min ta ga yar uwata Ma'u da ƙawarta a wajen Walima su ne gaba gaba
"Allah ya kyauta."
Shi ne abin da na ce kawai saboda Ma'u daman ni na san duk in da za ta ga gazawata can ta ke sha'awa sai ta yi ta yi dadin abun ma itama kishiyar gare ta, kuma ba fata na ke yi mata ba Alhajin nan na ta sai ya ƙara aure ba kuma domin ina yi mata fata ba, na san zafin kishi ba zan taɓa fatan ko maƙiyina a yi masa kishiya ba. Sai da na kusa ma isa Ɗorayi sannan na tura ma Yallaɓai saƙon na taho Ɗorayi Alhajinmu na kirana ina gama tura masa saƙon na maida wayata cikin ƙaramar jakata. Ko da na shiga gida an ta salla isha'i a masallatai Alhajinmu ya tafi masallaci shi da Datti ashe ɗazu ya dawo garin.
Nima alwalan na yi na gabatar da salla, Gwaggo ma haka bayan mun idar itama ta yi ta min nasiha ta fi jadaddamin na yi hakuri na zauna da abokiyar zama ta lafiya na kuma zauna da ita da zuciya ɗaya in ma ta na da wata manufan Allah zai maida mata kayanta. Ta na cikin yi min nasihan ne sai ga Alhajinmu ya shigo ya na jin mu a cikin ɗakin Gwaggo da kanshi ya shigo nan, ita kuma Gwaggo ta fita ta bamu wuri. Kalaman da Alhajinmu ya yi amfani da su wajen yi mini nasiha ko na ce tunatarwa su suka haɗe min da gyambon zuciyata na yi ta kuka ina shessheƙa. Alhajinmu ya hore ni da abubuwa masu yawa masu girman ciki shi ne na yi hakuri na yi haƙuri na yi hakuri wata rana zan ci riba.
Alhajimmu ya kalleni ya kira sunana. "Dubu" Na ɗago fuskata ina kuka ga hawaye shaɓe shabe na amsa da "Na'am Alhajinmu." Sai kawai ya gyara zama ya na faɗin" Ki saka a ranki abokiyar zama alheri ce. Ba ri na ba ki misali da mahaifiyarki lokacin da na faɗa ma Maimuna ga ta nan Gwaggon ku zan ƙara aure, duk da zafin kishi irin na mata ba ta nuna min ba, nan ta ke ta yi addu'an Allah ya sa mu riba ci junan mu da alheri dukkan wani sharri Allah ya tsare mu matsayinta na babba ta yi haƙuri kuma ta ci riba kina gani a cikin gidan nan ba su taba faɗa ba, ba wai kuma ba sa kishi ba ne a'a suna yi amma cikin ilimi da tarbiya. Har Rukayya ta koma ga Allah Gwaggonku da ni kaina Alherin ta muke faɗa kuma har gobe ba za mu daina tuna ta muna kuka ba. Bayan ba ta a duniya Maimuna ita ce uwa a gare ku ta taɓa nuna muku bambamci da su Murjanatu? Ina kuka ina girgiza ma Alhajinmu kai, shi kuma sai ya cigaba da faɗin" To kin ga falalar alherin da ke cikin abokiyar zama. Ni ma ki saka misali a kaina Dubu. Mahaifiyarmu ta rasu ni da babarku Hasiya ta bar mu hannun Hajiya Allah ya jikanta itace ta zame mana uwar da har ta koma ga Allah muna alfahari da ita. Shin Hajiya kafin ta rasu ta taɓa nuna bambamci tsakanina da su Aminu? Ko ku ta taɓa nuna muku bambamci tsakanim ku da su Muntari? Duka ɗaya ne a wajenta to shima ya na daga cikin misalin alherin abokiyar zama saboda haka ya ke ƴa ta Halimatu mai babba suna ki yi gadom mai sunan ki yi rangwame ga haƙurin ki, ki danne zuciyarki ki yi fatan alheri a cikin wannan auran na mijinki, ko da rana ɗaya kar ki bari sheɗan ya saka miki sharri a kanta. Ki yi ƙoƙarin azaman da zai gudana a tsakaninku kar ki taɓa cutar da ita, in ita ta zo da niyar cuta Ubangiji da zuciya ya ke amfani sai ki ga ya yi miki sakayya. Ki daina kuka ina da kyakyawan yaƙini a kan Yusufa zai zama adalin namiji a gare ku, kuma zai yi muku adalci dai dai gwargwardo. Saboda haka ki rike girmanki ki yi ma Ubangiji godiya, in wani abu ya taso miki acikin zuciya ki kira sunan Allah, in kuma kin tuna da mahaifiyarki ki yi mata addu'a amma ki daina kuka, ki na damu kina da sauran ƴan'uwanki kina da mijinki da ƴaƴanki to ki ɗauka Ubangiji ya gama yi miki dukkan Ni'ima."
Yallaɓai ya ɗauko ni a motarsa misalin tara na dare. Ina gidan gaba mai zaman banza amma kuka kawai na ke yi. Yallaɓai na ta kiran wayata ban ɗauka ba, wayar na cikin jaka sai ya kira ta Alhajinmu shi ya ce ya zo ya ɗauke ni, ni dai bayan Alhajimmu ya gama min nasiha ya sallame ni na fito Yallaɓai ya shiga ciki kuma ya ɗan daɗe sannan ya fito ni dai ina kuka na baro gidan Datti har bakin mota ya rakamu sai faɗi ya ke yi" Ya Sadiya kamar Alhajinmu ya saka miki duka?
Ya faɗa ya na dariya Yallaɓai ne ya kula shi amma ni kuka kawai na ke yi, saboda ma kar Yallaɓai ya ji kansa ya yi girma ina kuka saboda auran shi mun kusa isa gida ina share hawayena na kalle shi ina faɗin" Mama na tuna. Mutuwar ta ce ta dawo mini kamar sabuwa."
Bai ce komai ba sai ma kai da ya girgiza ya riƙe hannuna guda ɗaya da shima hannunsa ɗaya ya na faɗin" Na gane. Ki yi ta mata addu'a kin ji ko? Allah ya yi mata rahama." Na amsa da Amin ina jinjina kai, mun shiga gida tara da rabi da wani yara duk sun yi barci har da Faridan Tariq ma ta yi barci Rahila ce kawai da Amina zaune a falon yara suna kallo, sai ga mu mun dawo suka yi mana sannu da zuwa, Yallaɓai ya shige ciki ni kuma na zauna wajen su yadda ba su tambayi me ya faru a can ɗorayi ba, nima ban faɗa musu komai ba, zama muka yi muna ta hira ni tea ma na sha saboda cikina ya warware. Yallaɓai ma tea ɗin ya sha ya na dai can ɗaki mu kuma muna falo muna hira an tuna da ana ta dariya da shewa su suka ɗeɓe min kewa sai wajen ɗaya saura na dare muka je muka kwanta.
Faridan Tariq daman ɗakin dake gefen namu ta sauka ita da Amina Rahila kuma sai ta ce ta kwana ɗakin su Marwa ina da katifa yara ta kasa sai Marwa da Saude daman sun shimfiɗa sun kwanta sauran yaran kuma sun kwanta tare da su Jidda. Ni kuma na shige ɗakin mu na kwanta gefen Yallaɓai da har ya yi barci ma.
***** Asabar. 28. Dec 2015.
Ranar asabar mun tashi da taron biki, ni dai kamar muka tsara haka tsarin ya tafi. Su Munnira su ka yo waina su Amina kuma suka yi miya da zoɓo anan gida sai kuma Alele ba dai da yawa ba na ce su Saude su wanke wake a yi. Da safe dai Tea muka sha sai buredi sannan aka soya ƙosai. Da ya ke ba wasu jama'a na gayyata ba ƴan'uwana ne, dangin miji kuma suna can Gwammaja suna na su taron
Tun 11am na safe muka yi wanka gabaɗaya gidan kowa ya shirya. Tun da tun safe an gama komai, zuwa sha ɗaya da rabi su Munnira sun iso da waina Yallaɓai kuma tun safe Kawu Abba da Tariq suka zo suka fita tare da shi, ashe Tariq tare suka zo da Farida anan garin ya kwana ni ban ma sani ba sai da safen da suka zo gidan ya ke faɗa min, anan ma suka karya sannan suka fita, Yallaɓai an sha wanka da fararen kaya har da babban riga, ni kaina na jinjina ma kaina kamar an ƙwara min ƙwarin gwiwa na yi mamakin yadda na tashi cikin kuzari da dakiya. Kawu Abba ya ce min na kwantar da hankali na su suna bayana kuma matukar Tafida ya yi min wani abu da ban gane ba kawai na kira shi zai yi min mganin shi, na ce an gama mgana zan ko kira shi suna ta dariya shi da Tariq.
Abin mamaki Ya Murja da wuri ta zo ita da yaranta gabaɗaya Anti ce ba ta zo ba amma ta ce ta je makarantan hadda ne in sun ta so ta ce mata ta same ta a gidana abin da ya ƙara ba ni mamaki da ita shi ne har awara ta yo min mai yawa ta zo min da shi, har sai da idanuwana suka ciko da kwalla da Ya Balki ta ba ni kula cike da awara ta ce Ya Murja ta yo min ta zo da shi.
Na kalleta cikin wani yanayi kafin na ce" Ya Murja ashe dai ba Ma'u kaɗai ki ke so ba. Nima kina so na." Na faɗa cikin wani yanayi a muryanta su Ya Aina suna ta mana dariya ita ko harata ta yi kafin ta ce" Ji wata magana mutun ya taɓa kin ɗan'uwansa ne Sadiya? Ni fitinarki ne ya ba ma shiri amma ki sani ke ɗin fa jinina ne, jinin da ke gudana a jikinki da jikina bai kai wanda ke gudana a jikin Ma'u ba Ki daina gasa da ita ni duka ɗaya na ɗauke ku." Sai kawai na rumgume Ya Murja ina ƙokarin maida ƙwallar da ta kawo min
"Na gode Ya Murja. Allah ya bar zumunci."
Ta amsa da Amin Amim ta na dariya su Rahila na ta ya mu, haƙiƙa ba abin da ya fi ka ga ɗan'uwanka ya zo ta ya ka farincikin ko aka sin shi, duk da dai ba ma shiri da Ya Murja yau sai ta nuna ma duniya ni ɗin jininta ne Ma'u ce bare domin da ake mganar jiya ba ta zo ba, Amina ta yi karaf ta ce an ce ta je can gidan dangin mijina Walima, kuma ni na faɗa mata yau da safe da na ji ta na cigiyar Ma'u.
"Gaskiya ba ta kyauta ba. Duk zumuncin da ke tsakaninta da yayar mijin Sadiya ba kai kwatan alaqan da ke tsakaninta da Sadiya ba. Maganar gaskiya ba ta kyauta ba."
In ji Ya Murja, Ya Aina ko cewa ta yi" To in ma an gayyaceta can ɗin me ya hana nan ɗin ma ta leƙo? Kome ke tsakaninsu Sadiya zumumci ya wuce wasa" Rahila ta karɓe da cewa" ballatana ita Sadiya ma tun da Alhaji ya yi sulhu shike nan ta daina faɗa da Ma'u. Ta kira ta a waya ta faɗa mata tana gayyatan ta ita da shema'u.
Amina ta kaɗa kai kafin ta ce" To gulma ce ya kai ta amma in ba haka me ya sa sai ta je! Wannan ma fa kamar cin mutumci ne wallahi." Ya Balki kuma tace wallahi in ta zo sai ta yi mata mgana Ya Aina ta ce ta ƙyaleta ita da kanta za ta yi mata mgana, ni dai ina gefe sun tare min faɗa ban ce komai ba ina ta mirmishi. Daman muna cikin bedroom ɗina ne mun bar su Hauwa acan falon su Jidda suna hira tare da su Farida. Jama'an da na gayyata sun yi min kara sun zo min kaf iyalan Inna mariya da na yan gandun albasa sun zo min, har da matan su Kawu Tasi'u kuma da wuri suka zo, Sameena da wuri ta baro Gwammaja ta dawo gidana da kayanta ta ce nan za ta kwana sai gobe za ta je Rano daga can za ta koma gidan mijinta haƙika na yaba da karamcinta.