Turken gida book 2 cmplete by janafty - Chapter 16
Turken gida book 2 cmplete by janafty Chapter 16: Turken gida book 2 cmplete by janafty Chapter 16. Iya imu muka ci taron bikin mu, mun ci waina da alele…
3,317 words
Iya imu muka ci taron bikin mu, mun ci waina da alele da zoɓo sai son barka. Ma'u sai wajen uku na rana suka zo ita da Shema'u sun saka kaya iri ɗaya sun chaba kwalliya tare da kanwarta Zainab da Alhaji ƙarami. Ni da ya ke na daina saka sha'anin Ma'u a gabana da fara'a ta na tarbesu lokacin na sanya leshina riga da sikat kayan kuma sun zauna a jikina adon leshin ja ne, domin ni daman ina son jan abu, sai leshin ya yi min kyau na yi kwalliyata mai sauƙi na kashe ɗauri bayan na cire atamfar da na saka da safe na tabbata daga Gwammaja ta ke, kuma a yanayin da suka ganni cikin fara'a da gayu na ya yi musu baza ta sun ɗauka za su zo su ganni cikin kuka da baƙinciki ne, ina lura da su sai bi na suke yi da kallon mamaki ni kuma ina juyi da mazaune na domin akwai su Allah ya ba ni.
Shema'u za ta min shaƙiyanci da cewa" Uwargida a gidan Yallaɓai wannan ba za kalan fa? Ina mata fari na kaɗa mata kugu sannan na juya wuyana gashina da ya sauka ya karkace na baza shi da gyara tsayuwata kafin na ce" Ke ma ba ki ji abin da kika faɗa ne. Uwargida a gidan Yallaɓai fa, kin kuma san cewa daman tun can matar Yallaɓai akwai kashe kala ba sabon abu ba ne wannan." Munnira na gefe ta ranguɗa ta na faɗin" Wannan gaskiya ne ta Yallaɓai ita belbela daman ai da farin gashin ta a ka gan ta." Sai ta mika ma Hauwa hannu suka tafa, Faridan Tariq na gefe ta miƙe ta yi juyi kafin ta riƙe hanci tana faɗin" Jama'a ku ta ya ni rangaɗa ma duk wata uwargida guɗa."
Kafin kace me su Munnira sun rikita falon da guɗa, ni dai ina ta dariya ganin har da Ya Balki a masu guɗan. Ni dai na saka Amina ta zubo ma su Ma'u waina da alele, na ɗauka za ta ce sun ƙoshi sai na ga ta fara cin alalen. Amina ce ta yi mata tsiyan sai da yamma ta ke zuwa bikin gidn su?
"Na ɗan je Gwammaja ne. Kin san ni duka tudun biyun nawa ne Uwargida da Amaryan."
Ta fada ta na wani mirmishi, wanda na tabbata na yake ne, to ba nasara ta ga abin da ba ta yi tsammani n gani ba. Nan ta ke Ya Aina ta ce mata in ta gama cin abinci ta na so za ta yi magana da ita sai ta ce ti, sun yi dai hira da su Ya Murja ba wanda ya nuna mata ko a fuska, ni dai sai faman bina da kallo suke yi ita da Shema'u ganin yadda na ci kunshina baƙi da ja haka ma yara su Jidda su kansu sun sha gayu, suna falon sai ga su Suwaiba da Jamila sun leƙo min biki suna shigowa suka hau faɗin" Ina Uwargida a gidan Ya Tafidan ne! Ta fito mu tantance tun da mun gama gano gayun amarya saura na uwargida."
Sai suka ci karo da ni ai sai suka ɗau shewa daman Jamila shaƙiya ce ta karshe zagaye ni ta fara yi ta na faɗin" Kai jama'a cancanɗi. Ni fa na kasa gane ki. Anty Sadiya kin gama cinye wannan gasar." Ta faɗa ta na buga shewa ta ba ni hannu muka kashe Suwaiba kuma sai zama ta yi kan kujera ta na faɗin" Ke ce ma Amaryan Ya Sadiya to ai ko Gimbiya sai dai ta nuna miki makeup ɗin da mai kwalliya ta yi mata. Amma tabbas Uwargida ta Yallaɓai wanka ya rusuna jama'a."
Sai ta karkace hanci ta saki guɗa su Munnira na ta ya ta falon ya ɗau ihu, ina gefe ina ta dariya. Allah ya ɗauke min hamdala kawai na ke yi a cikin raina ashe da ban yi taro ba haka zan zauna baƙin ciki ya kashe ni kaɗai a gida. Suma nan suka zauna suka ci waina ana ta hira ana shewa yau dai gabaɗaya ranar ta uwargidaye ne, su Ma'u ana gefe duk an muzanta. Wannan muƙamin na manyan mata ne, sai mai nasibi ubangiji ke ba ma wannan sarautar in ji Ya Balki nan ko aka saka mata guɗa ana faɗin kwarai ma da gaske Yayarmu, ni dai ba na mgana sai dariya Suwaiba ke faɗin Yallabai na can Gwammaja ana ta hotuna ta na ma cikin faɗa ne wayata na hannun Marwa ta kawo min ta ce Yallaɓai na kira suna ko jin haka suka ɗau ihu suna faɗin.
"Yallaɓai dai bai manta da matar Yallaɓai ba duk da ya ga Amarya."
"Ita kanta Amarya in ta zo sai dai ta yi mana mubaya'a. " In ji Munnira sai suka ƙara saka shewa suna tafawa ita da Suwaiba daman mutuniyarta ne, Jamila ta mike ta na faɗin" Wai ya ne? Gidan Uwargida ba sauti? Ya Balki yar ta ya ɓera bari ta ce" Shi ne da ya kamata sa kar mana sauti mu yi takun uwar gida ran gida Yallaɓai ya na yi ma Sadiya rawa." Ni kaina wannan karon na kasa rike kaina sai da na fashe da dariya a jikin Tv falon yara akwai wajen saka flash Amina na da shi aka yo dowloading ɗin wakar Uwar gida suka kunna mana sauti, Suwaiba ta ce duk wacce ta san ita ɗin ba Uwargida ba ce ta koma gefe wannan filin na uwargidaye ne.
Sai kawai suka miƙe suna takawa, ni dai na shige ɗakin su Jidda ina amsa wayar Yallaɓai tunda ya sake kira.
"Yallabai na"
Na faɗa har daga ƙarƙashin zuciyata kuma a cikin wayar ma har ya tona asirin halin da na ke ciki na farinciki.
"Matar Yallaɓai."
Ya faɗa daga can bangaren, ina jiyo hayani ya tabbata har lokacin ya na can Gwammaja ɗin.
"Na'am mijin Sadiya."
Shuru ya yi na wani lokaci kafin ya ce" Me kika samu ne? Na ji ki cikin farinciki ne' Ina mirmishi na ce" Farinciki mana. Yan'uwana ke nan suna saka ni farinciki." "Alhamdulillah na ji daɗin jin haka."
"Ya Hidima Yallaɓai?
A amsa min da Alhamdulillah. "Sadiya ta yunwa na ke ji tun fitan mu fa ba mu ci wani abu ba." Da sauri na ce" Me ya sa ba ku ta ho gida ba! Tun ɗazu aka kawo waina alelen ma an gama fa." Da sauri ya ce" To in zo za ki ba ni? Ina dariya na ce" Ni na isa na hana Yallaɓai abinci? Sai kun taho zan shirya muku na ku in sha Allahu."
Da haka muka yi sallama, ko da na fito falo waje ya cika da shewa ga kiɗa. Har da su Ya Balki ana cikin fili ana takawa da, ban ga Ma'u da Ya Aina kenan ta ja ta gefe suna mgana. Amina na yi ma mgana abinci su Yallabai daman an cire musu, tare muka shiga kitchen ɗin ina ganin abin da ta ke haɗawan, ina cikin kitchen ɗin Munnira ta zo ta ja ni ina faɗin ta bari ina zuwa amma ba ta saurareni ba, sai tsakiyar falo ta kuma riƙe hannuna ta na rawa da ni farida ta mike ta na min liki, Shema'u na ga ta na kallona sai kawai na sakin hannun Munnira na fara takawa, suna min shewa da guɗa hana ni saƙat suka yi har su Jidda fa sun shige rawan suma sun ce ba za a bar su a baya ba.
Muna can muna bidiri ko shigowar su Yallaɓai ba mu ji ba, sai da ya leƙo da kansa ya na faɗin" Ku ce shasu kuke yi kenan" Ai su Suwaiba suna ganin shi suka rufe shi da guɗa, ya na kare fuskarshi ya ke faɗin" Wai guɗan nan ba ta ƙarewa ne Suwaiba?
"Wanda muka yi maka a Gwammaja na Amarya ne. Wannan kuma ai sautin na uwargida ne."
Suwaiba ta faɗa ta na ƙara sakin masa guɗaa akai, ya dafe kansa ya na dariya Jamila ma ta kama Munnira na ta ya ta, Sai ga Kawu da Tariq sun shigo. Kawu shi cewa ya yi" Danƙari Tafida ka ce ga in da ake biki." Tariq kuma ya ce" Shi fa Tafida duka amare gare shi."
Ya faɗa ya na kallona ni kunya ma na ji na sauke kaima ƙasa, Suwaiba ta fara yi ma kawu shaƙiyanci wai shima Allah ya sa baɗi uwar haka suna Rano sun je suna ya zabga mata harara kafin ya ce" Sai dai in da cikin ta zo ko? Ni kaina sai da na yi dariya daman kawu akwai yanka mgana gaisuwa suka yi da su Ya Balki da su Inna Mariya ƙin barin shi suka yi suka ce sai an yi mana hotuna, haka nan suka tsaida mu suna ta ɗaukan mu hoto har da Tariq shima da wayarsa shi da Faridan sa, sai da na ce musu su yi haƙuri, Ango fa na jin yunwa a yi masa afuwa na bashi abinci ai sai su Suwaiba suka ƙara ɗaukan shewa suna dariya.
"Allah ya shirye ki Suwaiba."
Haka Tariq ya faɗa ya na girgiza kai. Dakyar Yallaɓai ya samu ya ƙwace suka koma falon shi sai na saka Marwa ta kai musu abincin da komai da komai a falon na Yallaɓai, bayan sun gama ci sun ƙoshi har suka bar ma gidan ban sani ba muna can ana ta hira da shewa, Ma'u dai tun da ta dawo falon ba ta ƙara dariya ba, ga ta nan dai zaune ta na bin kowa da kallo, muna nan tare da su Suwaiba har dare bayan mangariba na sauya kaya na saka material Ya Aina da Ya Balki har da Ya Murja da Zaituna da mutanen Gandun albasa sun koma gida sai aka bar su Rahila, Ma'u ma da kawarta ba su tafi ba, da daddaren Halima ta zo ita da ƙawarta ta ce daga nan gidan Amarya za su wuce domin an tafi da ita tun mangariba ta zo min ne kawai na ce mata na gode. Haka ma Lailan Ya Auwal a lokacin ta zo ita da ƙanwarta na yi mata uziri tun da suna da hidima.
Sai wajen tara na dare gidan ya yi shuru, su Suwaiba sun koma Gwammaja su Ma'u sun tafi, Haka ma su Hauwa da Munnira daga ni sai Amina sai Rahila sai Sameena da ta yini ma kwance ba ta jin daɗi duk shewan da aka yi ta na ɗaki, sai Saude da Marwa sai su Jidda har maman Saude da mai yi mana kitso sun zo min biki. Su suka gyara gidan ma ya yi kintsi sai gidan ya koma ya yi shuru kamar ba shi ba ne ɗazu ya cika da hayaniyar mutane ana ta hidima sai kuma da ya yi shurun na fara jin wani iri a cikin ƙasan raina.
Ranar da na ke gudu ce yau ta zo. Ranar da Yallaɓai zai je ya kwana da wata mace ba ni ba. Tirƙashi.
*Janafty* *TKG*
09.
*Assalamu alaikum!* *Ina muku gaisuwa irinta addinin musulunci da fatan masoya labarin ƳAR KARUWA suna cikin ƙoshin lafiya,baya ga haka ina muku albishir da cewa free pages na labarin ya ƙare mun shiga asalin labarin wanda ya kasance shine part 2 na labarin.* *Karku manta bamu ce komi ba a free page's na labarin domin kuwa yanzu nema za a fara wasan,don haka karku bari ayi tafiyar babu ku masoya.Ku hanzarta ku shigo cikin tafiyar ARCH.AMMAR CHIROMA TARE DA HAFSAT KABEER CHIROMA,Tabbas a cikin wannan tafiyar akwai tarin faɗakarwa,zazzafar soyayya,ƙiyayya mai zafi da kuma halacci.* *Paid page's sun fara sauka a manhajar whatsapp da kuma Telegram,masu biyiyar arewabook tuni labarin part 2 ya fara nisa a can,sai ku garzaya domin Shan karatu.*
*Ku biya kuɗinku ta wannan asusun Kamar haka👇🏻*
For VIP on Telegram Pay 1k for Whatsapp group Pay 500 in to this account 👇🏻 7087809778 Aisha Dansabo Ibrahim Opay,evidence of payment to 08167768704.
*Masu buƙatar free pages na labarin ku tuntuɓeni ta wannan line ɗin 08167768704.*
Ƙarfe tara da rabi na dare sai ga Yallaɓai ya dawo shi kaɗai ya ce min ya ba ro su Tariq a gidan mai za su saka mai amotar shi kuma sai ya hau adai daita ya taho gida ya yi wanka ya shirya kafin lokacin sun taho sai su raka shi can gidan Gimbiyar. Kamar ya sani bai ko neme ni na haɗa masa ruwan wanka ba, ba domin in ya ce na yi ba zan yi ba sai domin zuciyata a lokacin ba ta cikin sukuni, muna gama maganar nan da shi ya shiga wanka ni kuma sai na koma can falo wajen su Rahila ba na so na zauna ni kaɗai tunani da damuwa su taru su ƙara ruguza ɗan sauran kuzarina.
Duk hiran da suke yi na kasa saka musu baki, zaune kawai na ke kamar mutum da mutumu ba na ma fahimtar hiran da suke yi, tun da ni nawa tunanin ya yi zurfin tunanin yau fa Yallaɓai ba anan zai kwana ba, yau ɗin wata rana ne da zai je ya kwana da wata mace ba ni ba, tuna haka kawai in na yi sai na ji numfashina ya sarƙe. Zuciyata na harbawa da sauri sauri ina dai zaune ne ina wasa da yatsun hannuna amma ni kaɗai na san halin da gangan jikina da zuciyata ke ciki, amma ban bari na shagala ba, sai na fara kiran sunan Allah a acikin raina domin na samu natsuwa.
Haka kawai na ji ba na son komawa cikin bedroom ɗin mu, tun da Yallaɓai a yanzu na san ya fito wanka ya na shiryawa. Tun da aka faro wannan al'amarin ban bari Yallaɓai ya ga gazawata ba. In ko na bari ya gani yanzu kamar na yi faɗuwar baƙar tasa ne, shi ya sa da na koma na gan shi raina ya sosa hankalina ya tashi gwara na yi zama na a nan cikin ƴan'uwana a ƙalla dai ko ba na da natsuwar fahimtar hiran su ina kallon fuskokinsu za su iya zame min garkuwa daga bayyana raunina a wannan daren.
Ina nan zaune shuru sai ga Sameena ta fito daga ɗaki har sannu da su Amina suka yi ta mata wallahi ni ban ma ji ba, sai da ta zo kusa da ni ta na taɓa kafaɗata sannan na dawo duniyar da suke, kallona ta yi sai ta ga kamar ina firgice ne, sai ta zagayo kusa da ni ta zauna ta na faɗin" Matar Baba lafiya?
"Ya jikin ki! Sannu"
Na katse wancan tambayan na ta, sai ta amsa min da ta ji sauƙi, daga ni har ita sai muka rasa abin cewa, ni kam ba na rasa ba ne yanayin da na ke ciki ne ya sa kalaman bakina suka ƙare, Faridan Tariq daman ta na ɗakin su Jidda ta je kwantar da su Hassan sai ga ta fito ta na faɗin ga su Tariq can a waje ya ce suna kiran wayar Tafida ba ta shiga suna jiran shi a ƙofar gida.
Lokacin da ta faɗi haka sai gabaɗaya jikina ya fara rawa har Sameena da ke gefena sai da ta fahimci haka, da sauri ta saka hannu ta riƙe hannuna guda ɗaya sai na juya ina kallonta da idanuwana da na ji kamar sun juye, kai ta girgiza min kawai sai na bi ta da kallo domin kamar wata yarinya sai na kasa fahimtar ta, bakina na ji ya bushe na kasa ma haɗiye miyau, maƙogaro na kuma na wani irin zafi kamar wani abu ya karce ni ban sani ba.
"Sadiya ki faɗa ma Yallaɓai suna jiran shi a ƙofar gida."
Farida ta faɗa ta na kallona sai kawai na bi ta da kallo itama kamar irin ban fahimta ba, kuma dukkansu sai suka kasa gane yanayin da na ke ciki, illa Sameena da ke gefena da ta yi saurin cewa" Ta shi Matar Baba." Ta faɗa ta na kallona, lokaci ɗaya ta na ɗan bubbuga hannuna alamun lallashi da ban baki, ina ƙokarin ƙwato numfashina ne na ji muryan Yallaɓai ta korido ya na kiran sunana.
"Sadiya."
"Sadiya.."
"To ai ga Yallaɓan ma can ya na kiran ki Ya Sadiya."
Amina ta faɗa ta na kallona kamar an ja ni tsaye sai ganina na yi na miƙe kan kafafuna duk yadda na so na yi musu mirmishi na kasa illa kaina da na kaɗa ina faɗin" Ba. ba ri na yi masa mgana." Ina gama faɗin haka na juya zan wuce ban ko kallon gabana sai gashi na ci tuntuɓe da cafet na kusa faɗuwa gabaɗaya suka haɗa baki wajen faɗin" Subhanallah."
Na kusa kaiwa kasa na samu na riƙe kujera ban riga na kai ƙasan ba, jikina ba in da ba ya rawa sai kawai na wuce ina tafiya ina ji kamar ina jin sanyi zazzaɓi zai kamani domin ina ta matse jikina a waje ɗaya, da kallo suka bi ni, saboda sai a lokacin dukkansu suka kula da yanayina sai kuma jikinsu ya yi sanyi ina jin Farida daga bayana ta na faɗin" Ki yi a hankali Sadiya kar ki faɗi." Cikin muryan sanyi kamar na tausayi haka na ji a cikin maganarta.
Ina gama shigewa koridon Sameena ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce" Allah ya ƙara ma Matar Baba haƙuri da juriya." Faridan Tariq sai ta koma ta zauna a gefen kujera ta na faɗin"Amin. Amma lamarin ba daɗi." Rahila dai da Amina ba su yi magana ba, amma jikin su duk ya yi sanyi sai falon ya koma ya yi shuru hiran ma sai ta tsaya kowa da tunanin da ya ke yi shi da zuciyarsa.
Ni kuma ina fita daga koridon na buɗe kofa na tsaya a ƙofar bedroom ɗin na kasa shiga, dafe kirjina na yi jin kamar zuciya ta za ta faso ta fito saboda yanayin da na ke ciki, duƙawa na yi ina maida numfashi sama sama kamar wacce ta yi gudun tsere ji na ke yi kamar sheɗata na neman ɗaukewa na ma kasa iya dai daita yanayina ballatana har na tura ƙofa na shiga ɗakin, ina duƙen ban sani ba sai kawai na ji an buɗe kofa Yallaɓai ya bayyana a gabana. Kaina na dago ina duke kan gwiwoyiyina na ɗago ina kallon shi, na ga lokacin da ya ɗan buɗe ido cikin mamakin ganina a wajen, ni kuma kayan jikinsa na ke kallo wata shadda ce sabuwa ce mai ruwan sararin samaniya ɗinkin zamani ne, har saman kaina na ke jin ƙamshin turaran Yallaɓai har kafarsa sabon takalmi ne domin ni ban ma san ya siya takalmi sabo ba, kamar wani cuta ina ganin Yallaɓai sai na ji kawai ina haƙi, daga tsuggune kamar ina ganin hajijiya ne ma.
"Sadiya lafiya? Me kike yi anan?
Ya faɗa yana kallona yana ƙokarin shima ya duka shima da sauri na yi ƙoƙarin na miƙe kawai sai na ji juwwa ta ɗauke ni na yi baya zan faɗi da hanzari Yallaɓai ya taro ni, nima sai gani na ƙamƙame hannayensa ina cigaba da haki kamar mai cutar Asthma saboda na ɗauka zan faɗi ne, ni fa gabaɗaya ji na ke yi kamar wata cuta ta kamani, kuma irin cutar da ban taɓa samun kaina a cikin sa ba, ina tunanin cutar yau ce ta kamani.
"Ba ki da lafiya ne?
"Subhanallah."
Na ji yo Yallaɓai na faɗa Sama sama ni dai ban dawo hayyacina ba sai da na ganni zaune a gefen gado, kitchen ya koma ya ɗauko min ruwa mai ɗan sanyi ya buɗe min ya kuma kafa min a baki ya ce na sha. Na ɗauka ban ji ƙishi sai ga shi na ɗaga roban ruwa na dire bakomai a ciki shi kan shi Yallaɓai da mamaki ya ke kallona Allah ya taimake ni sai na fara dawowa hayyacina na ji numfashina na daidaita sannan na daina hakin nan, kuma bakina bai bushe ba yanzu sannan ina jin maƙogwarona ya daina kartamin ɗin da ya ke yi ɗazu.
"Sadiya."