Turken gida book 2 cmplete by janafty - Chapter 17
Turken gida book 2 cmplete by janafty Chapter 17: Turken gida book 2 cmplete by janafty Chapter 17. Yallaɓai ya faɗa yana durƙushe a gabana lokaci ɗaya…
3,341 words
Yallaɓai ya faɗa yana durƙushe a gabana lokaci ɗaya kuma ya na kallona sai na ɗago ina kallon shi, yadda kuka san na gaji haka na ke jin duk jikina ya yi sanyi kamar an yi min dukan tsiya. Fuskata ya saka hannu ya na shafawa har ya na ɗan tapping ɗin shi da hannun shi sai na ƙara buɗe idanuwana ina kallon shi amma ban yi magana ba.
"Me ke damun ki?
Haka ya faɗa cikin kulawa, a cikin zuciyata na ke maimaita Hasbunallahi wa'imal wakel. Sai kuma na ji nauyin jikina ya ragu sannan bakina ya saki numfashina ya dai daita, Yallaɓai ya tashi tsaye ya saka hannunsa guda biyu ya ɗago duka kafaɗuna tsaye lokaci ɗaya ya sakani a jikinsa ya rumgumeni ƙamƙam a cikin jikinsa nima ban san lokacin da na miƙa hannuwana na zagaye bayan shi na shige jikinsa sosai kamar zan tsaga jikinsa na koma ciki, shi kan shi ya ji yanayin riƙon da na yi masa duk yadda na so kar kuka ya zo min duk yadda na so kada yau ɗin nan na raunana sai da raunin zuciyata ya rinjayeni sai kawai ji na yi ina kuka har da shessheƙa, hawayena suna sauka a saman kafaɗan shi, ko bai faɗa min ba ni na san jikin Yallaɓai ya yi sanyi, domin kansa na saman kafaɗata kawai ya na riƙe da ni amma ya kasa iya mgana ni kuma ina ta kuka yi yi har da kamar zan shiɗe, kuma in za a kashe ne ba zan iya cewa ga dalilin kukana ba kawai ni dai a raina ji na ke yi kamar na fi kowa na duniya nan shiga matsala, kuma ina ji kamar Yallaɓai zai yi min nisan da tun da muka yi aure bai taɓa min irin shi ba.
Bai hana ni kuka ba sai da muka yi kusan mintina goma a haka, daga ni har shi muna ji ana ta kiran wayarsa da ke saman side drower ɗin gadonmu. Amma bai sake ni ba har sai da na gaji da kukana na yi shuru ni ce ma na sake shi tuna cewa ana can ana jiran shi a waje sannan ita kanta Gimbiyar ta na can ta na jiran sa. Ban kalle shi ba da sauri na juya baya murya ta shaƙe ina faɗin.
"Su Tariq na waje suna jiran ka."
Na faɗa lokaci ɗaya ina goge hawayena da hannuna guda ɗaya. Ƙaramar jakarsa na gani a saman gado alamun ya gama haɗa kayan shi da zai bukata acan ina kallon jakar sai ga hawaye sharr, amma ina ƙokarin tare su, ya na ƙokarim sake riƙe ni na yi saurin kaucewa ina faɗin.
" Yallaɓai ka je kawai sai da safe."
Na faɗa ina ƙokarin maida kukana da ya taso min amma zuciyata sai da ta rinjayene na fashe masa da kuka na ma kasa iya kallon shi, sai kawai na juya da sauri zan fita amma bai bar ni ba da sauri ya riƙo ni amma ina ƙokarin zamewa daga riƙon shi cikin kuka kamar ina masa magiya na ke faɗin
"Don Allah."
Ina kuka maganar ta tsaya mini na kasa cigaba da magana sai ya sassauta riƙon da ya yi min ya na kallona wai ni Yallaɓai ke yi ma kallon tausayi saboda ya san ɗin abar tausayi ce.
"Don Allah ka ƙyaleni."
"Don Allah."
Na faɗa ina masa magiya kuka na ke yi kamar raina zai fita, sai kawai ya sake ni na juya zan fita daga ɗakin sai ya kira sunana.
"Sadiya."
Sai na dakata amma ban juyo ba, sai dai na saka hanuna guda ɗaya na dafe bakina har sautin kukana ya fito.
"Ki yi hakuri."
"Kin ji."
Wai haƙuri ya ke ba ni? In na ce ban hakura ba zai fasa tafiya ne? Ko kuwa zai iya maida hannun agogo baya ne, ko juyawa ban yi ba na buɗe kofa na fice sai na rasa ina zani kawai sai na buɗe kofar tiolet na shige na rufe ƙofar da sakata na sulale sai ga ni na yi zaman dirshan a saman tayels ɗin Tiolet ina mai fashewa da kuka da karfin gaske, suya zuciyata ke yi, har hancina na ke jin ya na fitar da wani yaji yaji, idanuwana sun yi min mugun nauyin da na kasa iya juyawasu, kaina na wani irin saramin da ƙarfin gaske, kaina na kasa a cikin gwiyoyina ina cigaba da kukana mai sauti, roƙon da na yi masa ne ya sa ya ƙyaleni na ji fitowarsa daga bedroom sannan jikina ya ba ni ya daɗe a ƙofar tiolet ɗin kafin ya buɗe kofar korido ya fice, ba jimawa na ji buɗe get din sa tunda shima window ɗin makewayin na ta haraban gidan ne, ban san ko shi ya faɗa musu ga in da na ke ba domin can ba jimawa sai ga Farida ta zo har ƙofar tiolet ɗin ta na kiran sunana ban amsa ba, sai ga Sameena Amina da Rahila kar su yi tunanin wani abu ya sa daga ciki na yi musu gyaran murya.
Ban san suna tsaye a ƙofar Tiolet ɗin ba, har sai da na wanke fuskata ina fitowa na gansu tsatsaye cikin damuwa sai kawai na yi mirmishi na fito ina rufe ƙofar Tiolet ɗin lokaci ɗaya ina faɗin" Lafiya ta kalau fa kar ku ɗaga hankalin ku." Na faɗa ina raɓawa ta gefen Rahila na buɗe kofar Bedroom ɗin mu na shiga sai na juyo ina rike da kofar ganin duk sun bi ni da kallon Tausayi sai na ƙara yin mirmishi da kumbararrun idanuwana kafin na ce.
"Da gaske na ke yi lafiya ta ƙalau. Sai da safe ina so na zauna ni kaɗai ne."
"Kin tabbata?
In Farida ita kuma Amina sai cewa ta yi" Ko na zo na taya ki kwana ne Ya Sadiya? Sai na gyaɗa mata kai alamun toh, sai Sameena ta ce hakan ma ya yi, na juya na shiga cikin ɗakin Farida ce kaɗai ta biyo bayana sauran kuma suka koma a gefen gado na zauna ina yarfe ruwan fuskata. Ta na tsayen ba ta zauna ba ta ce" Ki yi ta kiran sunan Allah, in natsuwar ba ta samu ba ki kunna karatun Qur'ani in sha Allahu za ki samu salama da Aminci."
Sai na amsa mata da toh, bayan na ce ta ɗauko mini wayar a can falo, sai ga shi ta fita ta kawo mini ta kuma fice bayan ta yi mini sai da safe, kayan jikina na sauya domin sun jiƙe, na saka riga da wando na barci da hula sai kuma na saka wani ƙaramin hijabi domin ina jin sanyi, sai da na kwanta na rufe kafafuna da bargo sannan na ɗauki wayar tawa sai na ga Yallaɓai ya tura mini saƙo yanzu ba daɗewa.
"Ki yi haƙuri Sadiya ta. Ki sani auran da na ƙara ba shi ne zai cire ƙaunar da na ke yi miki a cikin zuciyata ba. Ki sani ke ce Yusuf haka Yusuf ne Sadiya mun zama Hanta da jini ɗaya ba zai iya rayuwa ba ɗaya ba. Kar ki ji a ranki cewa matsayin ki ya sauya ke ce a jiya kuma har da gobe ma ke ɗin ce. Ina ƙaunarki Sadiya ta ƙauna mara yankewa. Na gode da dukkan sadaukarwarki gare ni, na gode da karamci da mutumtawa, na gode da yaƙana da martabawa ba, na yi miki alƙwarin adalci mai yawan da zan kwantata a tsakanin ki da Saudatu. Ki yi barci cikin salama Amintattaciya ta."
In a baya ne Yallaɓai ya turo mini waɗanan kalaman yini zan yi ko kwana cikin farinciki amma yau sam sai na ji ba su yi mini tasiri ba, ban goge saƙon ba amma na yi saurin fita daga kan sunan shi, domin sai na ji kamar zuciyata na zugani da na rubuta masa cewa in har ya na sona kuma adalci zai yi mini to ya saki Gimbiya ya dawo gareni, abin da ba zai taɓa faruwa ba kenan shi ya sa na yi saurin fita daga wajen na shiga cikin wayata na lalubo karatun Qur'ani baƙara na kunna na ɗan rage ƙara na saita shi dai dai kunnuwana sannan na koma na kwanta ga casbaha a hannuna ina ja, daman na rage hasken ɗakin sai duhu, ina kwance ina ta hailala da salati lokaci ɗaya karatun na shiga kaina duk yadda sheɗan ya so ya fassara tunanina na kasa barcin ayoyin Allah sun fattake shi, haka na ji iskar natsuwa na shiga jikina da zuciyata sai ga ni na yi luf a kwance ina lumshe ido barci na son kamani barcin da ban taɓa tunanin zai iya ɗaukata a wannan daren ba.
Sai ga shi kuma ya ɗauke ni, ba ni na farka ba sai uku na dare har lokacin karatun Qur'anin ya na ta yi, sai da na juya sai na ga Amina a gefena ta na barci da waya ta daman na duba lokaci uku ta gota sai kawai na sauko daga kan gadon na yaye bargo karatun na kashe sannan na yi amfani da wayar na haska tunda na ga sun ɗauke wuta Tiolet na shiga na ɗauro alwala na dawo ɗaki na shimfiɗa sallaya sannan na saka dogon hijabina na kabbarta salla sai da na yi raka'a takwas sannan na rufe da shafa'i da wuturi, bayan na idar na tashi na ɗauko Qur'ani na fara karatu daga suratul Tauba, a hankali na ke yi karatun saboda kar na ta da Amina, ba ni na tsaya da karatu ba sai da aka fara kiran salla na biyu daga msallatan kusa damu sannan na dakata na ɗaga hannayena sama na roƙi Ubangiji juriya da hakuri sannan na roƙe shi da ya iya yi min a dukkan lamarin da ni ba zan iya ba ya cire min kishi da kyashi ya ba ma zuciyata aminci da salama na daɗe ina kai ma Allah kukana sanman na shafa, na kuma koma ina neman gafaran Allah da casbahan hannuna lalle Ubangiji shi ne ke saukar da duk waraka sai ga ni zuciyata wasai sai ma wani iskar da na ke ji ya na shigata na salama da aminci.
Ni na ta da Amina na ce lokacin sallah ya yi sai kawai ta juya ta ce min ba ta yi, fita na yi zuwa ɗakin kusa da ni sai na ga har sun ta shi ma Sameena ce kaɗai cikin bargo Farida ta ce min ta na hutu, na san da ga ita har Rahila sun yi mamakin ganina kamar ba ni ba, Farida ta kalleni lokacin da na ce ba ri na je na ta da su Marwa har na juya sai ta kira sunana na juyo ina kallonta.
"Ina ta jiyo karatun ki ɗazu." Sai na mirmishi kafin na ce" Wai har kin jiyo? Sai ta gyaɗa min kai kafin ta ce" Nima da na kasa barci, fitan ki na ji ya sa bayan kin fito da ga tiolet ɗin nima na tashi na shiga na ɗauro alwala na yi nafiloli." Sai na jinjina mata kai ban yi mgana ba itama kuma sai ta ta da salla, Rahila daman sallar ta ke yi lokacin da na shigo. Fita na yi zuwa ɗakin su Jidda suma sun ta shi manyan sai yaran ne ke ta barci ni na ta da Baby ta na mutsike ido na ce ta shiga tiolet ta wanke ido ta yo alwala, na fita da cewa in na idar da salla zan dawo mu yi azkar, haka ko aka yi ina idar da salla na koma ɗakin yaran na tattara su gabaɗaya baƙi da yan gida har da su Saude, na ce mu fara karanta azkar da karfi a tare, bayan mun gama na ce kowacce ta ɗauko Qur'ani mu yi karatu. Ni ce fa har wajen bakwai na safe a ɗakin yaran sai da na yi musu karatu gabaɗaya har Marwa sannan muka shiga kitchen tun da ta ce min yau za ta je asibiti, ta re da saude mu uku muka ɗan gyara kitchen din sannan na ce su fere doya a soya sai kunu da za a dama a yi ƙosai Rahila ce ta fara tasowa ita ta karɓe ni daman kunin Saude na gyaran wake Marwa na fere doya.
Daga baya har Sameena da Farida sun fito sai aka kama gabaɗaya aikin, kafin lokaci an gama tunda hannun da yawa. Mai son shan kuni ya sha in tea ne ga shi nan in ƙosai ne ga shi nan, in kuma doya ne duk dai ga shi nan bayan an gama karyawa sai suka gyara min gidan su Rahila kenan yara kuma Saude ta yi musu wanka su Jidda kuma da suke manya suka yi ma kansu. Ni kaina tun safe na yi wanka na saka cikin sabbin atamfofina, zuwa azahar kowa ya yi wanka ya shirya har na fara kewa aka ce baƙo raba duk yau ɗin za su ta fi su bar ni ni kaɗai daɗin abin ma yara sun samu hutun makaranta kaɗaicin ba zai yi min yawa ba.
Da rana Tuwo aka yi miyar agushi ina da sauran manshanu sai aka juye shi sai ƙashin naman ragon ragowan na jiya aka yi amfani da shi, akwai ma ragowan waina da safe Rahila ta ɗumama ta saka masa siga ta sha da kuni da safe, alele daman ragowan balaraba na kwashe ma sauran da za ta wuce gida na ce ta kaima yara ban bari abinci ya kwanan min a gida ba. Sai da aka ci abincin rana sannan Farida ta yi shirin tafiya tun da ta ce Tariq ya kira ta ya ce ta je Gwammaja daga can za su wuce Sameena ma can Gwamnajan za ta je shi ya sa suka shirya za su tafi tare. Na yi musu godiya ƙwarai da karamci na yi musu rakiya har haraba gidan muka rumgume juna ɗaya bayan ɗaya.
"Na gode sosai. Allah ya mai da ku gidajen ku lafiya."
"Haba. Bakomai a yi ta dai hakuri a kauda kai Allah ya zaunar da ku lafiya ya kaɗe fitina."
Farida ke faɗin haka ni kuma ina amsawa da Amin Amin, Sameena kuma hannuwana ta rike kafin ta ce" Matar Baba ni fa ba na jin ki, sannan Baba ma ya na sonki zuwan wata ba zai rage ki da komai ba in sha Allahu." Sai na yi mata mirmishi kafin na gyaɗa kai ina faɗin in sha Allahu. Ga su dai suna na kusa da Gimbiya amma ni sun nuna min ƙauna ƙwarai kuma na yi ta musu godiya na kuma yaba da karamcin su.
Sun tafi ba daɗewa sai ga Hauwa da Munnira suka ce suma daga Gwammaja su ke, suka leƙo ni kafin su wuce gida har ina musu tsiyan ko daga gidan Amarya suke? Munnira na tabe baki ta ce min" Wani gidan Amaryan! Allah ya kyauta. Mu ba ma mu ce za mu je ba, masu zuwa dai sun je tun jiya yau ma da na ji wasu na mganar komawa Anty Bahijja ta hana ta ce a bar Amarya da ango su huta kar wanda ya je domin ya dame su."
Cikin mamaki na ce" Topha. To su waye daman ke son zuwa? "Can dai ahalinsu na Rano ne. Naja ce kawai aka ce za ta je itama sako za ta kai mata. Wai kar a dame su ki ji fa." Munnira ta faɗa ta na kallona, muna zaune daman a falon yara ne sai kawai na jinjina kai kafin na ce" Ba shakka." Hauwa dai na gefe sai ta muskuta kafin ta ce" Su Ayshe tun safe suka koma ɗazu da muka yi waya ta ce min tun jiya Anty Bahijja ta ce duk wanda ke son ganin gidan Amarya ya je a jiya domin in Ango ya shiga ɗaki ba mai yi musu sintiri a dame su. Na ce kamar wata budurwa? Anty Bahijja akwai kambama abu wallahi."
Ina ta dai kallonsu amma ban yi magana ba, Munnira ta ja tsaki kafin ta ce" Ita ce uwar Gimbiyar ba ki ga alama ba? Gani na yi hiran ta su za ta iya dawo min da damuwar zuciyata ya sa na katse hiran su da tambayan ko a zubo abinci? Sai suka ce sun ƙoshi amma ƙila kafin su tafi su ɗan taba tunda tuwo ne, muna tare da su har Yamma, suna ma gidan Ya Muntari ya zo ɗaukan Rahila da yara. Na matsa masa sai da ya shigo har falon Yallaɓai muka gaisa na kawo masa ruwa ya sha har su Jidda suka zo wajen sa suna masa hira ya na biye musu, shi daman akwai son yara in dai yara ne haka za ka gan shi da su ya na biye musu ba ruwan shi.
"Ashe kuma kin samu abokiyar zama?
Ya faɗa ya na kallona, kaina na ƙasa sai na gyaɗa masa kai. "To sai haƙuri Allah ya zaunar da ku lafiya ban da dai ɗaukan zuga." Na ce in sha Allahu, har ya na min tsiya wai Allah ya ƙara min haƙuri domin ya san halina ba ni da haƙuri.
"Kai Ya Muntari."
Na faɗa ina ƴar dariya, shima dariyan ya ke shi da Rahila ya na ce min ai ya san halina, kamar kar Rahila ta tafi amma ina ji ina gani ta wuce gida ita da yara ni da Amina har waje muka raka su, da Amina ta so ta je Ɗorayi ta kwana yau na marairaice na ce ta bari gobe da safe don Allah sannan ta yarda ta zauna na ce sai ma ta tafi tare da Saude kawai. Su ma su Hauwa suna yin sallar mangariba suka yi min sallama suka wuce mun rabu akan zan bi su har gida na yi musu bangajiya sai gida ya rage daga ni sai Amina sai Saude sai yara.
Nima sallar mangariban na yi sannan na natsu a ɗaki wayata tun safe ta na saman gado ban bi ta kanta ba sai da na gama azkar sannan na tube hijabin jikina na yi zaune gefen gado sannan na jawo wayar ina ganin an kirani, da ya ke a silent na saka wayar kuma ban bi ta kanta ba. 7 missed calls aka yi min Yallaɓai huɗu ya yi min sai Anty Zabba da ta yi min guda biyu sai wata lamba da ban san ko ta wacece ba sannan ga sako na an turamin tun kafin na buɗe jikina ya ba ni Yallaɓai ne shi ya sa ban yi ma rawan jikin buɗewa ba, sai da na kira Anty Zabba muka yi magana ita ke faɗa min ta ga hotunammu ni da Yallaɓai su Suwaiba sun ɗora a waya mun sha kyau.
"Sadiya gaskiya kin burgeni ba domin kar a ce na so ki na ƙi amarya ba. Da na ce ko da ranar auranta ne amma kin fita kyau."
Ina ta dariya na ce" Kin ko so ni Anty Zabba. Amma ina ni na fita kyau? "Allah da gaske na ke yi. Kun yi kyau sossi dukkan ku. Allah ya ba ku zaman lafiya da hakuri da juna." Ba mu jima muna mgana ba muka yi sallama, ni ban ma da hotunan ban ko hau online ɗin ba ballatana in gani, ba na ma som hawa domin na san sun ta ɗora na Gimbiya da Yallabai ni kuma ba na son ganin abin da zai ɓata min rai shi ya sa na haƙura da kunna data sai ƙura ta lafa.
Sai da na kira lambar da aka kirani na ga ba a ɗauka ba sannan na duba saƙon Yallaɓai, saƙon har guda biyu ɗaya da safe ne ya turomin wajajen goma na safe ɗayan kuma da yamma nan ne, kamar yadda kiran na shi suke a jere. Biyu da safe biyu nan kuma da yamma nan ne ya sake kira.
"Good morning My Darling Wife! Kun ta shi lafiya? Ina kewar ku. Ki gaida mini da Jidda da Baby."
Sai Ɗayan kuma cewa ya yi.
"Sadiya ta kuna lafiya ko? Gobe in zo na duba ku? Na kira ba ki ɗauka ba ko har yanzu akwai baƙi ne a gidan?