Kenza eBookz

Turken gida book 2 cmplete by janafty - Chapter 18

Turken gida book 2 cmplete by janafty - Chapter 18

Turken gida book 2 cmplete by janafty Chapter 18: Turken gida book 2 cmplete by janafty Chapter 18. Hmm! Kawai na ce a ƙasan maƙogwaaro na saboda na kasa…

3,359 words

Hmm! Kawai na ce a ƙasan maƙogwaaro na saboda na kasa ma mgana. Wai My Darling Wife Yallaɓai ne har da sauya min suna mai daɗi haka, wai munafunci irin na ɗa Namiji ya kwana da wata macen amma yana ce min wai ya yi kewar mu. Sannan tambayarsa ya zo ya duba mu sai da na ja mata tsaƙi, to yaushe namiji yaushe ya fara neman izinin in zai yi wani abu? Lokacin da ya yi auran ai bai gaya min ba. Sai na zuwa duba mu ne zai turo min wani munafunci, da na so na yi banza da saƙonni ne sai na fasa na rubuta masa gajeren saƙo ina yi ina hararan wayar kamar shi ne a cikin ta.

"Muna nan lafiya. A'a ka yi zaman ka kawai ba gobe ba."

Na yi mamakin yadda daga tura saƙo ko mintina goma ba a yi ba sai ga amsar shi kamar wayar ta na hannun shi ne.

"To sai yaushe?

Haka kawai ya ce, sai kawai na ga kamar so ya ke yi ya yi wasa da hankalina. Nan take na saka wayata a filght mode na dankwafar da wayar ina girgiza kafa, har da su kaɗa harshe takaici ya isheni ni kaɗai. Ina cikin wannan halin Amina ta shigo sai na ɗan saki, kamar ta san in na zauna ni kaɗai tunani zai iya yi mun kutse zaman ta a kusa da ni ya sa sai na maida hankalina kanta muna ta ɗan taɓa hira a kan dai yan gidanmu ne.

"Ya Sadiya Ma'u ta ba ni mamaki. Ni fa in kika ce munafuka ce in yi ta mamakinta."

Mirmishin takaici na yi kafin na ce" Uhm ai wanda bai san halinta ba zai taɓa yarda munafuka ba ce. Ta iya kissa fuska biyu gare ta shi ya sa."

Amina ta jinjina kai kafin ta ce" Na gani kuwa. Ai da Ya Aina ta mata mgana sai ta fara kuka ta na cewa ita ba da wata manufa ta je Gwammaja ba. " Ina dariya na ce" To ko da wata manufar ne za ta nuna ne? Makira ce fa Ma'u ina faɗa muku ba ku yarda. Uhm! Shi ya sa ni ban taɓa son Ma'u ba halayyanta ba su da kyau sam"

Sai Amina ta ja numfashi kafin ta ce" Uhm ai na gani yanzu. Ni dai fatana kar ta je ta rika bin Amaryan Yallaɓai ta rikita muku zama tunda ta shige ma yayar ta sa." "Za ta iya aikata komai domin ta ga ni na yi ƙasa. Amma kuma komai za ta yi na fi karfinta ni Allah na ce ita kuma tunda makirci ta saka ma gaba sai dai ya ƙare a kanta."

"Amin wallahi kuwa ah."

Amina ta faɗa har ta na riƙe baki ita fa Ma'u ce ke ba ta mamaki, ni ko na ce ta ma daina mamaki Ma'u ta wuce tunanin su wallahi nan na ke faɗa mata wasu sirrukan nawa ita ke faɗa ma Anty Bahijja in muka haɗu ta rika zagina ta yada min mgana na ƙarishe da cewa" Ina da ta cewa ne Amina? Ƴar'uwata ce ta ba da ni fa, shi ya sa na ke addu'an Allah ya shiga tsakanina da Ma'u duk mugun nufin ta ya koma kanta."

"Amin in sha Allahu."

Amina ta faɗa lokaci ɗaya ta na cigaba da faɗin" Ita fa abin da ya faru na rashin auran Ya Hamza ne ta riƙe a ranta shi ya sa ta ke jin haushin ki Ya Sadiya." "Sai dai ko ta mutu amma Ya Hamza ya yi mata nisa. Kuma wallahi tallahi ba na nadaman abin da na yi har nan da gaban Abada Amina" Na faɗa ina mai jadadda mganata sannan na ƙara da cewa" Ba ki lura ƙawarta Shema na ta ya ta ba. Ita kuma shegiya ta ki auru ai duk wanda ya ce tunkunyar wani ba za ta tafasa ba ina mai tabbatar miki da na shi ko ɗumi ba za ta yi ba. Kuma ko alaqarsu da Ma'u hali ne ya zo ɗaya amma in kin lura Ma'u ta fita wayau ita kuma har da kwaɗayi gani ta ke yi Ma'un na ba ta duniya ita kuma saboda mijinta na da kuɗi sai ta riƙa yi ma Shema'un abu kamar ita ce uwarta."

Na ƙarishe faɗa ina mai kallon Amina wacce ta jinjina kai kafin ta ce" Kwarai kuwa. Kamar raƙumi da alaqarsa haka Ma'u ke jan Shema." Ƙwafa na yi kafin na ce" Gungun munafukai ai sai munafuncin su ya ci su in sha Allahu." Nan muka cigaba da hira har muka gangaro kan Ya Murja na ce ai ita wannan na daɗe da sanin yadda ta ɗauki Ma'u ba haka ta ɗauke mu ba, sannan kuma da ƙwaɗayin itama, wani cewa halina ne ba ta so duk mgana ce amma jiya ta ɗan samu muhallin afuwa acikin zuciyata a karon farko da ta gano Ma'u ba ta kyauta ba.

Sannan Ya Abubakar ma sai a hankali. Shima raƙumin ne sai abin da ya ga an karkata acan ya ke. Har neman fitan hayyacinsa ya ke yi in dai akan lamarin Ma'u ne. Amina ta bushe da dariya kafin ta ce" Tsohuwar zuma ce Ya Sadiya " Nima ina taya ta dariyan na ce" Shi ya sa wani lokacin na ke yi masa uzuri." Mun daɗe muna hira har aka kira sallar isha'i sannan ta fita ta ce min za ta je falo ta yi kallo nima na ce in na idar da sallah zan fito.

Una ko idarwa na fito na iske suna kallon wani indian Movie a Bolloywood Kuchi kuchi hota hae. Ina son film ɗin tuni na zauna muna kallo har da Saude da Jidda Baby ta kwanta ita da Sultana ɗiyar Amina ƙarama, muna cikin kallon Amina ta je ta ɗumamo mana Tuwo muna ci muna ƙona hannu sannan muna kallo bayan mun gama muka kora da lemu da ruwa, mune har 11pm har sai da aka gama film ɗin nan sannan muka tashi har Jidda ba ta yi barci ba sai da a ka gama sannan muka kora su ɗaki, ni na tsaya na rage hasken duka ɗakunan na duba ko'ina sannan na je na kwanta na iske Amina ta yi shirin barci ta na kwance suna waya da mijinta sai na ba su waje na shiga Tiolet na kama ruwa na yi brush, ko da na fito sun gama wayar sai nima na yi shirin kwanciya na saka kayan barci muka kwanta, mun ɗan fara hira ba daɗe barci ya ɗaukeni ban ƙara sanin kaina ba sai huɗun asuba sannan na tashi na ɗauro alwala na yi nafilfilu, sai da a ka fara kiran sallar farko sanman na fita na ta da su Jidda. Dakyar na idar da sallar asuba saboda barci na cin idona na haye gado ba ni na tashi ba sai tara na safe.

Na iske gida ƙal an gyara ko'ina ya na tashin kamshi har sun karyawa Amina ta shirya sai tafiya Ɗorayi ita da Saude. Ina zama a saman kujera a falon su Jidda na ce" Ke Amina da sassafen nan? Kamar ana koran ki? Amina na gyara ɗaurin ɗankwalinta ta ce" Yau fa zan koma kaduna Ya Sadiya gwara na je na gaida su Alhaji na ɗan zauna zuwa azahar haka."

"To tare da Dattin za ku koma?

Sai ta gyaɗa min kai, ya na iya duk da ba na son tafiyarta haka nan na yi shuru ina laifi an yi min kwana uku. Ni da yara sai rakiya har bakin get muna ɗaga musu Hannu Saude dai gobe ma za ta dawo. Sai ga shi mun dawo cikin gida mun yi tsuru ni da su. Zama kawai na yi a falo ina nazarin rayuwa. Yanzu yau kwanan Yallaɓai biyu ya na cikin garin nan amma ba ya tare da mu sai na ji kwalla sun kawo min amma na yi saurin mayarwa. Tea na ce Jidda ta haɗo min na ci da Dankalin da Amina ta soya da safe. Su daman sum yi wankansu ni ce bayan na gama na tashi na yo wanka yau ma ɗin sabuwat atamfa ta na saka, ban zauna a ɗaki ba fito wajen su Jidda saboda su ɗeɓe min kewa. Baby ta ɗauke mana hankali da rawan drama ɗin da suka yi a makaranta ni da Jidda muna ta dariya.

Haka muka yinin mu kaɗai a gida sai can bayan La'asar Musbahu ya zo ya ce min Yallaɓai ne ya ce ya zo ya duba mu ina mirmiahi na ce" To me zai same mu? Ai dole ma mu saba tunda haka tafiyar za ta miƙa." Ban tambaye shi ba da bakinsa ya ke faɗa min Yallaɓai bai fito Office ba kwana biyu a raina na ce ya fito ya na can ya na cin amarcin sa, ya ɗan daɗe tunda har sai da ya tsaya ya ci abincin da na yi. Da zai tafi Baby sai ta fara rigiman wai ita sai ya kaita wajen Abba da Anty Gimbiya tun jiya ta fara min riginan Ina Abba na ce mata ya na gidan Anty Gimbiya ta ce sai ta je na ce ba yanzu ba, to jiyan ban biye mata ba sai yau ne bayan Tafiyan Musbahu yarinyar nan ta kafa min kuka da rigiman ita sai an kaita wajen Abba da Anty Gimbiya.

Yarinyar nan har da zan shiga salla sai da na yi ma ta jan ido akan ta tashi a saman cafet ɗin ta je ta yi salla amma ba ta ji ba. Har na idar da sallah na fito ta na wajen ta na min kukan banza ba tare da na yi mata mgana ba na koma ɗaki na ɗauko bulalar injin ce wacce na ke dukansu ne, ƙarama ce ma wannan ɗayar babban Yallaɓai ya dauke ta wai ba ta dukan mutane ba ne kamar zan doke dabbobi.

Ta na kwancen nan ta na rigima sai dai ta ji saukan bulala tuni ta fara ihu tun tana kiran Abba sai ta koma Umma ki yi hakuri Ya Jidda Ya jidda. Ta na kuka ta na majina karshenta dai Jiddan ta ƙwace ta, ta na ba ni hakuri.

"Don Allah Umma ki yi haƙuri."

Kwafa na yi kafin na ce"ka ji min yarinya mara mutumci kawai da mangariban nan ki ɗaga min hankali! A'a ba gidan Anty Gimbiya ba saura gidan Sarki." Raina a bace na koma ɗaki ina magana ni kaɗai. "Mata duk ta bi ta gama min da ƴaƴa. Ina dalili." Wayata da ta kwana ma a kashe ban san ko uban na su ma yau ya tuna da su ya neme ni ba. Sai ga shi can ajuma na koma na ganta har ta yi barci a raina na ce ashe ma iskanci ne irin na yara, Jidda ma da wuri ta kwanta ranar amma ni na ɗan dade ina kallo saboda ma kar na kwana ni kaɗai na yi tunani na ce Jidda ta zo ɗakina mu kwana ni kuma na ɗauki Baby na kaita bedroom ɗina na kwantar.

Ranar tare da yara muka yi barcin mu har da su makara domin sai shidda na safe muka farka. Qur'ani na riƙe shi kuma ya kawo min salama da kwanciyar hankali a kwanakin da Yallaɓai ya yi a gidan wata mace ko na ce wata matar ta sa bayan ni, sai a ranar na kunna wayata na kikkira mutane na yi musu ban gajiya Amina ma ta ce jiyan da suka isa gida ta yi ta kirana a kashe haka ma Farida ta ce itama ni dai na ce su yi hakuri wayar ce ta mutu ba chaji ban sani ba.

Ina lissafe da yau kwanan Yallaɓai uku kenan a gidan Gimbiya na ɗan ji ba daɗi da na kunna wayata ban ga saƙon shi ba amma dai ina ji a jikina ya kira ni wayar ce bai samu ba. Ko bai sanar da ni ba na san kwanakin bazawara kwana uku ne yau Yallaɓai zai dawo gidana shi ya sa da yamma na dumama sauran kazar da na siya wajen Hajiya Surayya Halin yau, na ci tare da tsumi karfe bakwai da wani abu na yamma Yallaɓai ya kira ni lokacin ma ina kan darduma ina lazimi ne bayan na idar da sallar mangariba.

Ban ɗauka a lokacin ba sai da ta katse sannan ba daɗewa ya ƙara kira sannan na ɗauka cikin sanyin murya lokaci ɗaya da sallama a bakina. Sai ya amsa min daga can bangaren shima a sanyayen, tambayar ya kuke? Ya yara na ce lafiya lau daga nan shuru muka yi dukkanmu na wani lokaci.

"Me ya faru jiya da yau wayarki a kashe."

"Ta mutu ba chaji ne ban sani ba."

Domin kar ma ya kawo tambayar ba wuta ne? Shi ya sa na ce ban san ta mutun ba.

"Ok. Yanzu ba daɗewa za mu taho nan gida tare da Daugther"

Haka na ji ya faɗa sai da na dan yi jim kafin na samu damar magana ya cigaba da faɗin" ina so zan yi magana da ku gabaɗaya."

Sai da sauke ajiyar zuciya sanna na amsa masa da cewa.

"Shike nan sai kun ƙariso."

Da ga haka muka yi sallama ban tashi ba sai da na gama lazimina na yi salatin Annabi na shafa sannan na miƙe na ninke darduman na ɗora saman gado daman na yi wanka na saka riga da wando. Ban kuma jin zan iya sauya shigata turaren wuta na ɗauka na fita falo na saka Jidda ta kunna Burner gidan ya dan yi kamshi Baby kuma na baje a falo ta ba je littafinta na drowing ta na ta zane zane kuma ta na bin shi da kala a baya in na gani sai na hana ta Yallabai ya ce na kyaleta na sani ko ita ce za ta ga je shi? Tun daga lokacin na saka mata ido daga karshe ma katon drawing ya siya mata mai kama da littafi da pensira na zane da clours ya na zane ni, in akwai makaranta ban barin ta yi amma yanzu da suka samu hutu ba na hana ta.

Muna zaune a falon gabaɗayan mu mu ka ji shigowar Motar Yallabai gidan da ƙaran rufe get, tun da karfe ne dole in an buɗe ko an rufe sai mun ji kara. Jidda ta daka tsalle ta mike ta na faɗin" Baby Abba ne." Daga ita har Baby a guje suka fice baby ta yi falati da kayan zanen ta suka fice da gudu suna kiran oyoyo Abba, na ji buɗe kofar falon da yadda yaran suka naɗe shi da muryan shi ya na faɗin.

"Oyoyo My princess. I miss u."

Ina zaune a in da na ke na kasa tashi. Haka kurum sai na ji gabana na faɗuwa ras! Kamar kuma sai na ji kamar wani tsoro tsoro na shiga ta. Yau ne fa zan hada ido da kishiya? Kishiyar da mijina ya kwana da ita har uku. Ƙilama akwanakin nan ta samu ciki.

"Auzubillahi minal sheɗanir rajim"

Haka na faɗa da sauri domin koran sheɗan ɗin da ya ziyarce ni.

*Janafty* *TKG*

*Assalamu alaikum!* *Ina muku gaisuwa irinta addinin musulunci da fatan masoya labarin ƳAR KARUWA suna cikin ƙoshin lafiya,baya ga haka ina muku albishir da cewa free pages na labarin ya ƙare mun shiga asalin labarin wanda ya kasance shine part 2 na labarin.* *Karku manta bamu ce komi ba a free page's na labarin domin kuwa yanzu nema za a fara wasan,don haka karku bari ayi tafiyar babu ku masoya.Ku hanzarta ku shigo cikin tafiyar ARCH.AMMAR CHIROMA TARE DA HAFSAT KABEER CHIROMA,Tabbas a cikin wannan tafiyar akwai tarin faɗakarwa,zazzafar soyayya,ƙiyayya mai zafi da kuma halacci.* *Paid page's sun fara sauka a manhajar whatsapp da kuma Telegram,masu biyiyar arewabook tuni labarin part 2 ya fara nisa a can,sai ku garzaya domin Shan karatu.*

*Ku biya kuɗinku ta wannan asusun Kamar haka👇🏻*

For VIP on Telegram Pay 1k for Whatsapp group Pay 500 in to this account 👇🏻 7087809778 Aisha Dansabo Ibrahim Opay,evidence of payment to 08167768704.

*Masu buƙatar free pages na labarin ku tuntuɓeni ta wannan line ɗin 08167768704.*

10.

Ina zaune ne amma na kasa tashi domin sai na ke jin gabaɗaya ilahirin jikina na rawa. To in ma na tashi wa zan je tarowa? Kishiya ko miji? Kawai sai na yi zama na amma fa zuciyata bugawa ta ke yi da sauri da sauri cikin lokaci ƙalilan hankalina ya tashi ina neman fita hayyacina saboda wani iri abu na ke ji yana ta so min daga ƙasan zuciyata. Kishi masifa ne, zai iya haifar ma da mata lalura mai karfin da nan ta ke za a iya kai su emergency a yi tunanin ciwon ya daɗe a jikinsu ne ba a sani ba alhalin kishi mai saka ma zuciya ciwo nan take ba tare da mutum ya sani ba.

Idanuwana suna kallon ƙofar falon suka shigo, shi ya buɗe mata kofar ta fara shigowa hannunta na riƙe da na hannun Baby. Sai shi ya biyo bayan su, shima hannunsa na riƙe da na Jidda. Gimbiya fara ce sosai doguwa domin har ta ɗan fini tsawo sannan tana da jikin murjewa kyakyawa ce domin hancin ta har baka. Sanye ta ke da atamfa mai kalan orange shi ya sa mayafin da ke jikinta ma kalan shi kenan, shi kuma Yallaɓai an cakare cikin ƙananun kaya har da zanzaro. Dukkansu fuskarsu tana fitar da wani annuri ne. Annurin da ka na ganin shi za ka san na farinciki ne wanda zuciya ke samu ta hanyar gangan jiki.

Duk ina zaune ne na ƙare musu kallo, ina ganin za mu haɗa ido da su na yi saurin ɗauke kaina ina jin zuciyata na ƙara tsananta bugawa. Ina jinjina ma matan da ake yi musu kishiya sannan a haɗa su zama da su a gida ɗaya. Wallahi in ni ce ba zan iya ba, domin na tabbata wata rana zan iya haɗiyan zuciya na mutu saboda baƙin ciki. Da na so na tashi na tarbe ta amma daga baya kawai sai na fasa sai ma gyara zaman da na yi daga in da na ke zaune na ce.

"Sannun ku da zuwa."

Na faɗa ina ƙara gayyato mirmishi a saman fuskata. Ita ta amsa amma a hankali shi ne na ji amsar ta shi da ƙarfi yaran na maƙale da su, shi ya nuna ma Gimbiya kujeran da za ta zauna na zaman mutum biyu, ta isa ta zauna Baby ta haye jikinta shi kuma sai ya durkusa a gabana lokaci ɗaya ya na mai riƙe duka hannayena cikin tafukan hannunsa so ya ke mu haɗa ido, ni kuma na ki bashi damar haka sai ma Juyawa da na yi ina kallon Jidda da ta zauna gefen Gimbiya sai mirmishi suke yi daga ita har Baby umh yara ai ba ku san dawan garin ba.

"Jidda kawo ma Antyn ta ku ruwa da lemu mana."

"To Umma."

Ta faɗa da saurin ta sannan ta ta shi ta nufi kitchen ɗin.

"Kalle ni mana Sadiya ta."

Ya faɗa ya na leƙa fuskata sai na yi fuska ma maze na kalle shi ta ƙasan idanuwana. Haushi fa ya ke ba ni, hannayena ma da ya riƙe ji na ke yi kamar na ƙwace, domin haskowa na ke yi da waɗanan hannayen na shi fa ya riƙe Gimbiya da su, shi ne nima zai dawo ya na taɓa ni tuni na ji gabaɗaya hannayensa sun zame min kamar lantarki mai ja a cikin hannayena sai ƙokarin kwacewa na ke yi ya na ƙara riƙe ni, ita kuma Gimbiya ba ta kallon mu tana ta hiran ta ita da yara.

"Yallaɓai. Ka bari mana." .

Na faɗa bayan na ƙwace hannayena lokaci ɗaya ina kallon shi.

"Ba ki yi mini sannu da zuwa ba."

Ya sake faɗa yana mai ƙure ni da ido.

"Shi wanda na yi maka fa?

Kawai sai ya buɗe mini hannuwansa yana faɗin" Ba wannan ba irin wannan." Kaɗan ya rage ban danno masa na katsinawa ba amma dai na daure ban yi ba, sai ma hararan shi da na yi na matsa gefe ina kallon Gimbiya.

"Ki sha ruwan mana."

Ta na kallona ta ce" Zan sha."

Readers Also Read