Turken gida book 2 cmplete by janafty - Chapter 19
Turken gida book 2 cmplete by janafty Chapter 19: Turken gida book 2 cmplete by janafty Chapter 19. Muka yi shuru ni da ita, shi kuma sai ya zagayo ya…
3,367 words
Muka yi shuru ni da ita, shi kuma sai ya zagayo ya zauna kusa da ni har kafaɗan shi na gogan nawa, a hankali na ƙara matsawa sai na ga ya ƙara matsoni, ina kuma ɗaga kaina sai na ga ta na kallon mu shi ya sa na barsa ban ƙara matsawa ba.
"Na yi kewar ki sosai Sadiya ta."
Haka ya yi min raɗa a kunne ya faɗa mini, ko kallon shi ban yi ba domin sai na ga kamar rawan jikin Yallaɓai ya ƙaru ne saboda a gaban matar shi ne, ni zai faɗa ma burauba a gaban matarsa. Kallo ma ni bai ishe ni ba sai ma na juya masa ƙeya ina ce ma Gimbiya ta sha ruwa mana.
"Zan sha "
Ta sake faɗa a hankali tana wasa da yatsun hannun Baby.
"Anty Gimbiya ina ta kuka ina so na je wajen ku ke da Abba."
Baby ta faɗa cikin shagwaɓa ita kuma sai ta shafa kanta ta na faɗin" Ban sani ba da kin kirani da gudu zan zo na tafi da ke My Baby." Sai Baby ta fara murna, ni ko gani zaune ina yaƙe ban yi mgana ba.
"To ko Baby za ta ture gwamatin Jidda ne kawai sai ki tafi da ita ta ta ya ki kwana."
Sai ta yi mirmishi ta na kallon shi kafin ta ce" Sai abin da ka ce Daddy" "Duk ɗaya ne ko Baby ko Jidda Daugther. Gwara Jidda ma ba za ta yi rigima ba amma Baby ba za ta yarda ki ta fi da Jidda ita ki bar ta ba." "Sai na tafi da su gabaɗaya mana Daddy." Ta faɗa cikin shagwaɓa ta na yi masa wani kallo. Kawai sai na ga ya yi wani mirmishi, mirnishin da na ɗauka bayan ni Yallaɓai ba zai sake yi ma wata mace irin shi ba sai gashi a gaba na a gaban yara Yallaɓai ke hira da wata mace ta na masa shagwaɓa ya na jin daɗi.
"Daughter.."
Ya faɗa ya na yar dariya sai kuma ya kwantar da kansa jikin kujera ya na faɗin" Ke ma kin cika rigima. Su biyu ai sun yi miki yawa. Ita Madam sai a bar ta ita kaɗai ko su je kawai ni kaɗai na ishe ki ko Sadiya ta? Ya ƙarishe zencensa ya na kallona, ban ko kalle shi ba amma a cikin raina ina jinjina karfin halin irin na Yallaɓai wato ma har ya raba mini yayan nawa amma ni ban da darajan da zai faɗa min, ni fa a baya ne na ke da bakin cikawa a kan Yallaɓai amma a yanzu na shaida munafuki ne na gidi ma, ni fa yanzu ba duka ma mganganunsa ne abin yarda a wajena ba, na tabbata tunda ya ƙara aure zai kulla alaqa da ƙarya da munafunci.
"Ya baƙun ta?
Na katse shurun namu da mganata. Cikin wani karya murya ta ce" Baƙunta ya fara bin jiki." Ta faɗa ta na ƴar dariya, ni kuma sai na yi mirmishi ba tare da na sake yin magana ba amma da za a tona zuciyata baƙinƙirin ta ke, kiran sunan Allah kawai na ke yi domin saura kiris na fallasa a sirin zuciyata. Mun zauna shuru har na tsawom mintina ashirin ita dai sai hira ta ke yi da su Jidda Yallaɓai kuma ya na ta faman latsa waya ni kuma ina zaune abin tausayi E mana abar tausayi ni da gidana amma na kasa sakewa, sai satan kallon Gimbiya na ke yi sai da na ƙara lura dakyau na ga har da kwalliya ma ta yi, to wai ta manta yau mijin ma ya fita ɗakin ta ne? Sai da na lura sosai sai na ga jefi jefi suna kallon juna ita da Yallaɓai suna sakar ma juna mirmishi, ji na yi kamar na tashi na bar musu falon amma na ƙara dai haƙuri na zauna, ina so na duba lokaci amma wayata na baro ta a ɗaki kuma gashi ba na so na tambayi Yallaɓai kawai sai na yi shuru kamar in yi tagumi in fashe da kuka haka na ji, ban yi hakan ba amma acikin zuciyata Allah ya saka min kawai na ke faɗa domin Yallaɓai ya gama cutata.
Kiran sa a ka yi a waya sai ya tashi ya koma falon shi, ba daɗewa ya dawo yadda ya bar mu haka ya dawo ya tadda mu, ita dai ta na ta hira da Baby mai shegen surutu in ta fara ba ta son ta tsayawa gwara Jidda ta fita Aji shi ya sa na ke son ta ba ta cika surutu haka barkatai ba. sai balla mata harara na ke yi ta gefe amma yarinyar nan ba ta ji ba sai zuba ta ke yi kamar ƴaƴan kanya.
"Kun yi shuru abin ku."
Ya faɗa yana mai sake zama gefena sai a lokacin na saci kallon Yallaɓai kwata kwata bai yi min kyau ba a raina ma faɗi na ke yi Yallaɓai an yi girman banza ka rufe arba'in kana wani cin zanzaro. A baya ne in yi ta masa nacin saka ƙananun kaya ya yi ta kuma cewa shi ba ya son sakawa amma sai ga shi yanzu ya saka har da zanzaro saboda ya burge wata tir! Tsaki na ja a hankali amma kuma sautin ya fita tun da shi ya ji har kuma sai ya kalleni na basar na haɗe rai kamar ba ni ba shi ya sa bai samu damar yi min wata mgana ba.
"Jidda kama hannun Baby ku je falona ku kunna Tv ku yi kallo kafin na gama mgana da Ummomin na ku."
Haka ya faɗa ya na kallon Jidda sai ta amsa masa da to. Amma Baby har da ƙin tashi ta makale ma Gimbiya. Shi ya tsaya ya na lallashinta shi da Gimbiyar ni ko tsawa na daka mata kafin na ce" Za ki tashi ko sai na zo nan na tattaka ki ? Na faɗa ina mata wani kallo ai kafin ma na yi wani matsi ta sauko daga jikin Gimbiyar ta na neman yi min kuka.
"Kina ɓare min baki yanzu jikin ki zai gaya miki."
Na faɗa ina kallonta jin haka yasa ta koma bayan Jidda ta raɓe, shi kuma Yallabai ni ya kallah kafin ya ce" Haba! Sai ki da ke ta? "Ta yi kukan sai ka gani." Na bashi amsa a takaice sai na ga kawai ya tsaya ya na kallona ni kuma na ɗaure fuska ina kallon jidda kafin na ce" Kama ta ku je mana." Sai ta riƙe hannun Baby suka wuce wacce ta yi narai narai kamar za ta yi kuka ga shi ba hali kuka Gimbiya na ɗaga mata hannu da alamun ta na nan ba tafiya za ta yi ba.
Sai da suka shige da mintina sannan Yallaɓai ya gyara zama gyara murya ya yi irin na juyo na kalle shi sai ma na ƙara yamma da fuskata. "Wannan hijabin fa? Ki cire shi ki sha iska mana." Ya faɗa ya na kama gefen Hijabin kamar da gayya ya yi maganar ni zai ma mutumci gaban matarsa. Daman hijabin da na yi salla dashi ne ban cire ba, kawai sai na fizge hijabin daga hannun shi kafin na ce.
"Ka bar min kayana. Tun da kuma ba zafi ake yi ba."
Na faɗa ina jin kamar na rufe shi da duka ni fa na kosa ya gama maganarsa na shige ciki zuciyata ta kusa daina ɗaukan munafuncin Yallaɓai kar ta kai mu ga in ya faɗa na maida masa mara daɗi.
"Halima."
Ya kira sunana amsawa kawai na yi ban kalle shi ba saboda ni dai yanzu in Yallaɓai ya kirani da Halima ban wani rawan jiki saboda na san na yaudara ne shi ya sa na daina ma rawan jiki.
"Daughter."
"Na'am. Daddy".
Ta amsa cikin sanyin sauti. Ina zaune ne amma ji na ke yi kamar ina yawo a sararin samaniya saboda hazo hazo na fara gani saboda wulaƙancin Yallaɓai, ni ya kira sunana sunan da ko ubana da ya yankamin rago ba ya kirana da wannan sunan ya na sakayawa saboda girmamawa haka sauran ahalina Sadiya suke kirana amma shi yau sabida cin mutumci ni ya kira ni da Halima ita kuma tunda sunan Nene gare ta ba zai iya kiran ta da sunanta na yanka ma sai ya sakaya kamar yadda ya saba. Wani iska na furzar daga bakina da ya sa sai da suka kalleni gabaɗayan su.
"Lafiya?
Ya faɗa ya na kallona, wani irin kallon sama da ƙasa na yi masa kawai na ɗauke kaina shima kuma ya ga yanayin kallon shi ya sa bai ƙara nema na da wata mgana ba ya kama kan shi.
"Na san kun san dalilin da ya sa na tara ku anan ko?
Daga ni har ita shuru muka yi masa, ni ko a raina na ce to kasan mun sani uban miye kuma za ka taramu? Amma dai ban yi magana ba sai ma na maida kaina ƙasa kawai ina wasa da gefen Hijabina.
"Duk da kun sani amna tunatarwa tana daɗi. A matsayina na wanda kuke zaune domin shi akwai wasu mganganu da ya kamata na sake tunatar daku game da su."
Uhm! A cikin raina na ja sheɗata na fesar ta baki, saboda yau wai ni ce zaune da wata matar a matsayin matar Yallaɓai bayan ni. Na kasa gasgatawa amma yanzu gasgatawa ya zama dole tunda ba mafarki ba ne a zahirin gaskiya ya ke faruwa.
"Sadiya ga abokiyar zama nan na kawo miki. Aurena da Daugther Allah ne ya kaddaro shi, ke ma Daugther ga Yayanan na yi miki. Abun fatana na farko shine haɗin kan ku, ku sani wata ba ta fi wata a wajena ba dukkan ku mata ne da aure ya samar min da ku, ina fatan za ku haɗe kan ku ku zauna da juna lafiya domin samun zaman lafiya ta nima."
"In sha Allahu."
Ta faɗa cikin sanyin murya, ni ko ban ce komai ba sai daga baya da na ga ya yi shuru kenan ni ya je jira na ce wani abu.
"Allah ya ba mu zaman lafiya."
Suka amsa a tare da shi da Amin.
"Sadiya ki sani ban aure Daughter domin kin taɓa gaza min ba. Ki kaddara zaɓin Allah ne sannan ikonsa ne. Ke ma ki sani ba ta rage ni da komai ba kar ki yi tunanin akwai ta bangaren da ta gaza min ne ko ɗaya. Ke ma ki ɗauka a kaddaran Allah ne aurena da ni da ke, ki yi mata biyayya domin wakiliyata ce, in ta yi miki gyara ki gyara in ta kwaɓa miki ki kwaɓu, in ta ba ki umarni ki bi wanda bai saɓa ma shari'a ba. Ba zan lamunci ki yi mata cin zarafi ko rashin kunya ba ba na so na ji wata baraka a tsakanin ku, Ku ba yara ba ne ballatana na ce komai sai na faɗa muku dukkanmu nan mun san komai saboda haka ina roƙon ku ku haɗe kan ku mu zauna da juna lafiya har mu zama abin kwantance a wajen su don Allah."
"In sha Allahu."
Ta sake faɗa ni kuma a yangance na ce" Allah ya sa."
Sai kawai ya juyo kaina.
"Sadiya."
Sai na kalleshi sannan na amsa masa.
"Na'am."
"Na ɗora miki wani girma. Ki sani ki ce ni i don ba na nan ko da ma ina nan ke ce wakilyata. Kin fi ta sanina sosai fiye da ita. Ki riƙe girman ki, ni ma kuma ki riƙe min nawa girman. Don Allah ki yi zama da ita da zuciya ɗaya in wani saɓani ya haɗa ku ku zauna ku warware a tsakanin ku kar ki biye ma masu an ce ka ce domin ya na ɓata alaqa ba na fatan ku samu saɓanin da har ni sai na shiga ciki. Na fi son ku yi zaman lafiya da har ni ba zan ji kan ku ba don Allah."
Ajiyar zuciya na sauke domin na ga ya ƙura min ido sannan na ce" Allah ya ba ni ikon ɗaukan girman." Abin da kawai na ce kenan na yi shuru ita kuma sai ta ce" In sha Allahu ba za ka taɓa samun baraka daga bangarena ba"
"Ma sha Allah na ji daɗin haka. Allah ya yi muku albarka ya kuma zaunar damu lafiya gabaɗaya."
A cikina na amsa da Amin, ya ɗan sake yin shuru kafin ya ce" Sai maganar raba kwana. Wani tsari kuke ganin za ku yi? Ya fada ya na kallon mu, ni ko sai na yi kamar ban ji ba.
"Duk yadda Maman Jidda ta tsara dai dai ne ni a wajena."
Ta faɗa ta na kallona sai nima na kalleta kafin na ce" Ah ke ma kina daman ki tsara ɗin." Sai ta kalleshi kafin ta ce" To kai ka faɗa mana." Kai tsaye ya ce" Ni ba ruwana wannan ai maganar ku ne." Ya faɗa lokaci ɗaya ya na duba wayarsa.
"Ni dai sai na ga gwara ita ta faɗa "
Ta faɗa tana kallona, nima ko ina kallonta na ce" Ke ma kina damar ki faɗa duka ɗaya ne da ni da ke ɗin" Ganin mun fatra ja in ja ya sa ya kalleni kafin ya ce" Sadiya ki faɗa mana ke ce Babba." Zan yi magana ya dakatar da ni da cewa" Ke za ki tsara na ce ko? Sai na ga ya wani haɗe rai ya na kallona a raina na ce daga baya kenan.
"To kamar kwana bibbiyu ya yi ko?
Na faɗa ina kallon su sai ya kalli Gimbiya kafin ya ce" Ya yi ko? Da sauri ta ce" Ya yi." Sai ya juya ya na kallona kafin ya ce" Shikenan kwana biyu ya yi Madam." Ko kallon shi ban yi ba domin ni yaudaran Yallabai wanne ne ban sani ba.
"In ba na gidan ɗaya to haƙƙi ne a kaina na je na duba yadda ta kwana. In kuma wani uzuri ya taso zan iya kiran waya. Kuma duk wacce ke son mgana da ni za ta iya kirana nima kuma a duk in da na ke zan iya kiran kowaccen ku, dukkaa ku mata na ne da Allah ya ba ni ku ta ƙarƙashin inuwar aure saboda haka ba bu shamaki a tsakaninku gabaɗaya ɗaya kuke a wajena."
"Allah ya zaunar da mu lafiya. Madam ɗina yi mana addu'a.".
Sai kawai na yi kamar ba da ni ya ke ba sai na kalli Gimbiya ganin ta na kallona shima sai na ga ya na kallona cikin basarwa na ce" Wai ni? Mirmishi ya yi kafin ya ce" Wace ce na ke kira Madam in ba ke ba? Sai na jinjina kai a raina na ce ai ka ce Madam tun da ka gama da ni ka yo sabuwa na zama cus ba ni da amfani dole na koma Madam ko burgeni sunan bai yi ba domin tabbas na ke da shi wulakanci ne na ɗa Namiji shi ya na kiran ta da Daughrt ni kuma Madam kamar wata inyamura.
Ni na rufe zaman da addu'a sannan ya ce mu yi musabaha da juna, hakanan na mika mata hannu muka yi masabahan shi kuma ya duba lokaci ya ce goma har ta gota bari ya zo ya maida ta gida. Shi da kanshi ya leƙa falo ya ce Baby ta yi barci sai Jidda kaɗai a gaba na ya ce ta je ta haɗo kayanta na kwana biyu ta zo su tafi kamar zan yi magana amma sai na ce ba yanzu ba ba tare da ya yi magana da ni ba ina ji ina gani ya ta sa Jidda tare da Amaryansa da ba zai bari ta kwana ita kaɗai ba ya je maida su gida. Mun yi sallama da Gimbiya kadahan kadahan Jidda kuma na ce ta tafi da azkar ɗin ta da Qur'ani kar ta manta da koyarwa da na yi mata ta ce min in sha Allahu.
Bayan tafiyarsu na kai Baby ɗaki na gyara mata kwanciya tare da yi mata addu'an barci. Sannan na rage mata hasken ɗakin na fito. Heater na kunna ya yi zafi sannan na yi wanka na saka kayan barci na duba agogo Yallaɓai ya fi mintina talatin da fita bai dawo ba, har na je kitchen na sha ruwan zafi daman da rana shinkafa na da fa Jallop. Ban damu da Yallaɓai ba tun da sai dare ya zo min gida ai ya cika cikinsa a can shi ya sa ko tunanin dafa wani abu ban yi ba. Bedroom na koma na kwanta amma na kasa barci tun ina mamakin Yallaɓai har na daina mamakinsa domin lamarinsa ya wuce tunanina da hasashena.
Ba ni na ji karan buɗe get ɗin Yallaɓai ba sai sha ɗaya da mintina na dare, saboda akwai waya a gefe sai da na duba ajiyar zuciya kawai na saki a ƙasan raina ina tausan kaina kar Yallaɓai ya shigo na yi masa dibar albarka, saboda ma kar a samu matsala sai na yi lamo cikin bargo kamar mai barci ina jin sa ya shigowarsa cikin gida da zagayen da ya yi ya rarrage hasken ɗaku nan sannan ya shigo cikin bedroom ɗin ya zube key ɗin motarsa da laptop ɗin a saman madubi ta gefen ido na ke kallon shi shammata ta ya yi ya kamani ina kallon shi sai ya yi min mirmishi kafin ya ce.
"Sorry kin ga na daɗe ko?
"Akwai ruwan Zafi in za ka yi wanka ne."
Na katse shi daga maganar saboda ba na son na ji. Karya ce da renin wayau ne kawai a cikin zencen sa.
"Ok."
Ya faɗa, ya na mai tuɓe kayan jikinsa ya rage daga shi sai gajerun wando sannan ya kalle ni kafin ya ce" Zan samu tea mai zafi Madam? Ya faɗa ya na min wani kallo, da kamar na ce a can ɗin da ka tsaya ba ta ba ka ka sha ba ne? Amma dai na danne zuciyata na mike na zo zan fita ya ja min kumatuna lokaci ɗaya ya na faɗin" Na gode Matata ta kaina." Kai na fara tunanin ƙila dai Yallaɓai ya zauce ni domin ya na ta surutai marasa ma'ana.
Kitchen na shiga na kunna gas na ɗora masa ruwan tea. Ina da shayin goriban da na siya wajen Aisha Lame saboda Yallaɓai shi na zazzaga masa na dafa masa bayan ya tafasa na tace masa a mug na kai masa ciki na iske har ya fito wanka ya na shafa mai, kan madubi na ijiye masa, kamar ina sauri na koma kan gado na kwanta sai ya juyo ya na kallona kafin ya ce.
"Ko taya ni ma shiryawa ba za a yi ba?
Ya faɗa ya na wani mini mirmishin da a baya ya san ya na kunna ni, amma a yanzu da zan fito na faɗa masa yadda na ke ganin baƙin sa in ya yi min wannan mirmishin da tuni ya kama kan shi. Sai da na shige cikin bargo sannan na leƙo kaina ina faɗin" shirin barcin ne sai an ta ya ka? Na faɗa ina masa wani kallo, shi wai ba shi da ganewa ne, ni fa da zai ƙyaleni da ya burgeni bai san bina ma da ya ke wani ƙara min takaicinsa ya ke yi ba.
"Da ko barcin ne ai kina shirya ni ko?
"Da ka ce yanzu kuma kiɗa ya sauya dole ma ruwa ya sauya."
Na faɗa ina hararan shi ta gefen ido, tsabar ma Yallaɓai ya maida ni shashashan madina sai kawai ya kwashe da wata dariya kafin ya ce.
"Me ya sauya? Uhm My Sady Baby?
Bakina ne na yi masa limzani amma na kusa na yi masa wani gimgimeman tsaki, ganin in ma tsaya ina biye masa mahaukaciya zai maida ni nishaɗi ya ke yi shi fa amarcin ya karɓe sa matuƙa sai faman washe baki ya ke yi, baya na juya masa kawai ina ƙokarin ya ƙi da abin da ke taso min daga ƙasan zuciyata ina jin sa har ya gama shirin barcin sa ya kashe mana fitila ya zo ya kwanta na ɗauka zai yi gefen sa ne sai kawai na ga ya matso kusa da ni ya kwanto saman jikina ya na kiran sunana.
"Saddy.."