Turken gida book 2 cmplete by janafty - Chapter 20
Turken gida book 2 cmplete by janafty Chapter 20: Turken gida book 2 cmplete by janafty Chapter 20. Wato saboda ya yi mini kishiya na zama abin dariyan shi…
3,249 words
Wato saboda ya yi mini kishiya na zama abin dariyan shi kaɗan ya rage ban ture shi ba amma na yi masa bakam sai ya fara min cakulkuli tun ina kannewa har na kasa ina dariya na mirgina ina faɗin" Ka bari mana Yallaɓai." Amma bai ƙyale ni, sai da ya ga na kusa fita hayyacina har ina hawaye duk mun birkita gadon sannan ya ƙyaleni shi ma ɗin bi na ya yi ya danne ya na min wasu abubuwan, tun ina ture shi har dai ya fi ƙarfina dole na ba da kai bori ya hau, sai da muka samu natsuwa sannan muka yi wanka muka kwanta da asuba ma bayan ya dawo masallci sai da ya ƙara nema mana wani ɓarnan ruwan
"Yallaɓai da sanyin nan kasan ɓarnan ruwa akwai wahala." Ya na shafa fuskata kafin ya ce" Ya fi daɗi ne. Kuma kin san cewa kin ƙara daɗi Madam? Ya faɗa ya na sumbatar goshina lokacin muna kwance a tare ne, saboda kalamansa sun yi kama da na yaudara yasa na yi masa banza. Wai kin ƙara daɗi! Duk da bai san na ƙara daɗi ba ne sai yanzu da ya je ya ɗanɗano wata? Ɗan renin wayau kawai.
"So na ke yi na sake ajiyar mai sunan Alhajinmu ko Baban Gwammaja"
Ya faɗa ya na shafa cikina zuwa saman marata, nima sai na ɗora hannuna saman hannun shi har na ji tahowar ƙwallah. "Allah ya sa haka Yallaɓai na." Ina so na sake haihuwa ni ko da guda ɗaya ne." Na faɗa ina jin sukan abin daga ƙasan raina.
"In sha Allahu za ki ƙara haihuwa ba ma ɗaya ba dozin."
Mirmishi kawai na yi amma ban yi mgana ba.
"Ya ku ka yi da Likita zuwan ki na ƙarshe asibiti?
Bayani na fara yi masa da cewa gwajin na ƙarshe ma ya na lap on 12 january zan koma in na karɓa sai na je na kai mata na ji me za ta ce tukunna. " In sha Allahu ba matsala." Na amsa da Allah ya sa.
Bai kuma ƙyale nin ba sai da ya saka mu muka sake ɓarnan ruwa da safen nan. Ranar dai a gida ya yini bai fita ba saboda shi ma na ƙi dukan Baby domin tunda ta tashi barci ta ga ba Jidda ta fara rigima da Yallaɓai baya nan da tuni jikinta ya faɗa mata, shi ya zauna ya na lallashinta ni ko kallo ba su ishe ni ba. Sai washegari ya fita ya ce min zai biya ya duba Gimbiya daga nan zai shiga Office. Baby ta nace masa da ita ya tafi da cewa wai zai dawo da ita in zai dawo gida ni dai ban yi magana ba ina jiran na ga iya gudun ruwan shi.
Sai ga shi tare da Gimbiyar suka kawo Jidda da Baby tun da yau ɗin ya na wajen ta ne. Ba su dade ba ni ma kuma ko fuska ban ba su ba muna gama gaisawa na bar su a falo na yi shigewata ciki sai da ya biyo ni muka yi sallama, hug ɗin ma na ƙi yarda na shige tiolet na bar shi nan dole ya wuce sai da na ji sun bar gidan na fito. Baby sun dawo da chaculte sai cincin da su alhaki suna ta budirinsu kallo ba su isheni ba suma ɗin haushin Ubansu ne duk ya shafe su.
Tun ina ganin lamarin Yallaɓai in ya yi kwana biyu a gidana ya je can ya yi kwana biyu a wasa har na tabbatar da cewa gaskiya ne. Ba ni kaɗai ba ce matar Yallaɓai yanzu ba. Yana da wata matar shi ya sa ko cefane yanzu biyu ne Musbahu ya kawo min itama ya kai mata. Ya na kawo ta gidana su zo tare amma ni ban taɓa marmarin zuwa gidanta ba. Kuma in dai ya na gidana sai ya dauki Jidda ya kai mata in kuma ya ma can sai ya dawo da ita yadda bai taɓa min magana kan Jidda ba nima ban taɓa yi masa ba. Kwanaki can ya yi min maganar kan me ya haɗamu da Anty Bahijja.? a lokacin sai na tambaye sa.
"Me ta ce maka hala?
"Kawai ta na ta faɗa ne wai kin yi mata rashin kunya."
Sai na jinjina kai kafin na ce" Ita ya ɗauke shi a rashin kunya amma ni ba haka na ke nufi ba" Sai ya tambaye ni mai ya haɗamu na ɗan faɗa masa da cewa" Na faɗa mata ko kai da na ke zaman ka, in ka matsa min da zuwa haƙuri zan ba ka. Ina ga shi ne ta ji haushi." A lokacin bai ce komai ba amma dai ya ce na kira ta na bata haƙuri ni ko dai na ce masa toh amma ban kira ba domin ban ga abin da na yi mata da zan kira ta na bata hakuri ba in ta so kar Allah ya sa ta haƙura in mun haɗu in na gaisheta kar ta amsa ita ta sani.
Shi daman Yallaɓai ba mai damuwa da bin diddigi ba ne bai ma ƙara ta da mganar ba, ba ni ƙila ma tuni ya manta da batun in dai ba ita Anty Bahijjan ta sake masa mgana ba. Ga shi muna cikin sati na biyilu da tariyan Gimbiya tun ina tunanin zan iya sabawa da sallaman Yallaɓai in zai bar gidana har na fara tunanin har abada ba a sabawa kullum ne lamarin ni sabo na ke kallon shi a idanuwana. Ga shi tun bayan bikin ba wanda ya dawo gidana sai dai mu yi magana da su Hauwa ta waya Suwaiba ma sai da na kirata sannan ta turamin hotunan da ta ɗauke mu ni da Yallaɓai sun yi kyau amma ko status ban yi da su ba amma dai na ga Anty Maimuna ta sassaka hotunan su na bikin tariyan ƙila a lokacin ba ta samu sukunin sakawa ba, duk na kalla daga baya ne na yi ta daman kalla domin har da hoton Yallaɓai da Gimbiya su biyu, ta kwantar da kanta saman kafaɗansa ta na dariya shi kuma ya juya ya na kallonta kamar dai magana ya ke yi mata aka ɗau hoto. A ƙasan hoton ta saka caption.
"Tafida da Gimbiyarsa. Alƙawarin Allah ya tabbata."
Lalle fa Gimbiyarsa. Hoton nan da na gani ya daɗe yana gilmamin a cikin mafarkina da zahirina. Duk in da na zauna ko na kwanta da na runtse ido su na ke gani sai da na yi ta kiran sunan Allah sannan na samu sukuni da salama. Sai a yanzu na ke ganin cewa daman tun can Yallaɓai na son Gimbiya dama ne bai samu ba. Wannan rawan jikin kam ya na yi mata a gaba na kuma sai ya riƙa nuna ni ya ke yi ma rawan jiki, wai ni Yallaɓai zai maida ƙaramar yarinya Allah na tuba wani dare ne jemage bai gani ba ai sai dai daren mutuwarsa.
****
20January 2016.
Tuni na koma asibiti na ga Dr. Aisha Alhandulillah abin farincikina duka na tsallake matakin gwaje gwajen su kuma ta ba ni tabbacin ba wata matsala mai girma. Sai dai kawai side effect ya taɓa ni sannan kuma hormones ɗina sun ɗan yi rauni ne amma ta rubutamin manganganun da za su dai dai tamin al'ada da wanda za su ƙara taimaka min wajen samun ciki suna da tsada domin da na je phamarcy ma kuɗin da Yallaɓai ya ba ni ba su isa ba, na yi ta kiran wayar shi ban samu ba sai na kira na Musbahu shi ya faɗa masa sai shi kuma ya taho asibitin ya same ni, bayan ya biya kuɗin magunguna ya ɗauke ni ya maida ni gida. Duk da ina da kuɗi a cikin acct da gangan na ƙi taɓa su ni fa yanzu na fara jin ƙyashi yin hidimar da nawa ba, ba kamar da ba da shi kan shi ya san wani abun ma ba na jiran shi. Kan jiki kan karfi na dage na fara shan magunguna na saboda fata na da burina ni ma Allah ya sake ba ni wani cikin ko ɗaya ne na sake haifa.
Kwana biyu tsakani na je gidan Hauwa daga can ni da ita muka je gidan Munnira muka haɗu muna ta hira. Sun tambayeni ya yanayin zaman na ce lafiya lau. To me zan ce? Zaman da yanzu aka fara ai sai tafiya ta tafi sannan halin kowa ma zai bayyana. Hauwa ita dai faɗi ta ke yi Yallaɓai ɗan halas ne, ni ko a raina na ce ai ba a yabon ɗan kuturu sai ya shekara da yatsa a hannun shi. Sai yamma muka rabu Hauwa ta hau adaidaita anguwarsu nima na hau ta anguwarmu na koma gida. Ina komawa ma na iske Marwa ta zo daga asibiti ta biyo ba na gida, daman Saude na bari a gida tare da su Jidda sai da dawo suka tafi gabaɗaya.
Tun bayan tariyan Gimbiya sau ɗaya na je Gwammaja na gaishe da Alhajinmu daga nan na ɗauke kafa ina gida mai son ganina ya san in da na ke, iyakata in ina son mgana da mutun na yi masa waya. Ni yanzu ba ma Yallaɓai da Amaryansa ba ne a gabana sauran kudaɗen hannuna na ke son zama na yi tunanin sana'ar da zan fara, kar ma su ƙare a banza ban yi komai da su ba, tun dai na fahinci Yallaɓai zuma kawai ya ke lasamin a baƙi burina da ya ce zai zama sillar cikarsa na cire rai da su. Hankalina ya koma kan wani busineess ɗin da zan fara da zan dogara da kaina har Khaleesat na kira mun yi mgana saboda na ce ko nafara gwada hijabai ne? Sai ta ce wata Akwai ƙanwarta na siyarwa za ta tambaya min ta ji harkan in akwai fita sai ta haɗani da masu ɗinkin Hijaban anan sabon garin Zaria in muka saba ma ba sai na je ba ma. Kololin kawai zan faɗa su za su riƙa siya suna dinka min sai dai kawai a saka a mota a kawo min nan da nan na ce ta yi min ƙokari ko Yallaɓai ban faɗa mawa ba da Amina kawai muka yi mgana ta ce wallahi na fara itama yanzu turaruka ta ke saidawa har ta ba ni shawaran na saro mayukan gyaran gashi tunda ina son bangaren na fara saidawa na ce shima zai zo daga baya mu fara da wannan ɗin dai mu gani.
Ko a raina ban ji zan faɗa ma Yallaɓai ba sai dai in ya gani ya tambaya na amsa masa. Shima yanzu ai hankalinsa kashi biyu ne. Da ni kaina da ita amaryansa, ga su Jidda sun koma makaranta ta shiga Jss2 Ita kuma Baby primary 3, ya biya musu kuɗin makaranta daga nan na san Yallaɓai kuɗi gare shi, ba zan zage shi a yanzu ba tunda iya adalci yana kwatantawa. Sai ɗan abin da ba a rasa ba na halin Ɗan adam. Zama ya yi zama an kwarari wata biyu da tariyan su sannan na fara lura da wani abu.
Duk da Jidda ta koma makaranta ranar da ba ya gidan Gimbiya sai ya kaita. Ita kuma da safe sai in za ta wuce wajen aiki tunda ta na da mota sai ta kai Jidda makaranta in sun tashi ta je ta ɗaukota. Nan kuma Baby ita kaɗai Salisu kai kaiwa sai dai in har Yallaɓai na wajen Gimbiya ne ta ke gida duk da na ga ana ta min gantali da yarinya ban yi magana ba saboda ina ganin akwai sauran lokaci. Sai da na ga in dai zai zo gidan nan ranar da zai bar gidanta sai ta rako shi, kuma tana da mota amma a tashi za su zo bayan nan kuma shi zai maida ta gida ya ɓata lokaci kafin ya dawo duk na kauda kaina ban yi magana ba, sai abu na biyi in dai yana gidana to ta rika kiran waya kenan kamar wani ɗan kasuwan da ya ci mata bashi. Ni ko ba alfahari ba bana kiran shi in na san ya na gidanta. Sai dai in ma ya zama dole na yi masa saƙo in ya gani ya kira amma ita ba haka ba ne a wajenta in abu ne ta nema ba ta gani ba sai ta kira shi ta tambaye shi tun ina ba ta lokaci har dai na fahimci da gangan ta ke yi, ranar dai na ga abin na ta ya isheni da daddare har mun kwanta ta kira shi wai ta kasa kulle ƙofa, ina jin sa ya na faɗa mata key ɗin ne ya lalace gobe da safe zai saka Musbahu ya je da mai gyara sai a sauya key ɗin gabaɗaya.
"Wai shekarun Gimbiya na wa ne?
Sai ya kalleni kafin ya ce" 33 to 34 ina jin ko za ki girmeta da kaɗan ne"
Sai na jinjina kai ban yi magana saboda na gama fahimtar renin wayau ne kawai kamar wata jaririya.
"Me ya sa kika tambaya."
"Na ga ta na yin abubuwa kamar Jidda ne"
Ido ya zuramin alamun ƙarin bayani ni ko ina gyara gashina da tun da na yi tsifa ban kitse shi ba a gaban madubi na yi masa kamar bangane ba.
"Me ya sa kika ce haka?
Sai da na gama abin da na ke yi sannan na zo na kwanta lokaci ɗaya ina faɗin" Ka fi ni sanin dalilin." Da ga haka na yi kwanciyata na juya masa baya. Na san ya yi ta kallona ya kuma kasa mgana saboda ya san abin da na ke nufi. Mata kawai daga zuwanta za ta zo min da makirci a cikin gidana to ba ta isa ba zan taka ma ta burki daga ita har me biye mata.
*Janafty* *TKG*
11.
FHB CLOTHING Muna Dinka kowanne irin nau in dinkunan yara na zamani,Muna bada sari ga masu bukata haka Muna maraba da masu sayen dai dai Muna turawa ko Ina cikin sauki a Nigeria da makotan kasan mu . Amana shine taken mu . wtsapp no.08080266674 or call @08034109622
Yanzu Gimbiya tana cikin wata biyu ne da tarewa. Zaman su ya fara miƙawa tun ina ganin lamarin kamar wasa har dai daga karshe na saka a raina gaskiya ne sannan zan saba ɗabi'ar haka ta zame min jiki ko domin samun zaman lafiya ta. In na buɗe wardrope ɗina na ga cikin kayan Yallaɓai kashi uku babu kashi ɗaya a hankali a hankali ya na ta rage su, suna can gidan Gimbiya, bayan kaya ma hatta ma'ajiyar takalman mu sun yi rauni, wajen gudu huɗu duk babu su a wajen suna gidan Gimbiya bangaren unders ma sannu sannu dai suma ɗin suna ta raguwa, a raina na ce shi kenan duk ikon da na ke dashi a kan Yallaɓai da duk abin da ya mallaka yanzu wannan ikon ya fita daga hannuna saboda ba ni kaɗai ke da shi ba ya na da wata matar kuma itama ta na da iko akan shi da duk abin da ya mallaka.
Iya kauda kai ina yi, saboda ni ce babba kuma na riƙe girmana duk da na san ina saurin fushi da zafin zuciya amma na danne ban bari kishi ya saka ni na yi abin da ba dai dai ba ne. Kwanaki na je na gaida Nene ta ƙara yi min nasiha da ƙara tunasar da ni girman da ake cewa ina da shi kar na ɗauka wani ne ya ba ni. Na saka a raina girma ne da Ubangiji ya ba ni. Na ji kuma na yi kamar ban ji ba sannan na gani na yi kamar ban gani ba. Duk da Gimbiyar ɗiya ta ke a wajenta ni Nene ba ta ƙi ni ba kuma ina ganin girmanta shi ya sa duk abin da ta faɗa min zan ji sannan ina ƙoƙarin yin amfani da shawarwarinta. Saboda haka ne ma na saka ma Yallaɓai ido ya gama mararin amarcinsa da rawan kafansa ƙala ban taɓa ce masa ba.
Na yi ta ƙoƙarin kauda kaina a kan al'amarin sa da Amaryansa shima kuma tun kafin auren nan da muka yi mganar ya daina mini labarinta ya tsaya iya matsayin shi. Iyakata dashi abin da ya shafe ni ko ya shafe shi ko ƴaƴana ni ma kuma bana tsallake hurumin da ba nawa ba domin samar ma kaina zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Ko na sana'ar sai da Hijabai da aka kawo min daga Zariya guda Hamsin sai da ɗan nuna rashin jin daɗin sa saboda ni dai ban faɗa masa sai dai kawai ya zo ya ga an kawo hijabai. Da farko ma ya ɗauka ko na saƙo ne bai tambaya ba sai da ya ji ina waya da Khaleesat anan ne ya fahimci nawa ne zan fara saida wa. Sai da ya bari har mun yi shirin kwanciya sannan ya yi min mgana.
"Kasuwanci kika fara ban sani ba Sadiya?
Sai na kalleshi kafin na ce" E. Ban fara ba zan dai fara in sha Allahu."
Sai ya jinjina kai kafin ya ce" Shi ne ba ki faɗa min? Yaushe kika fara yin wani abu ba tare da na sani ba?
Sai ya ba ni mamaki ji karfin hali ɓarawo da sallama.
"Ina ka samu lokacin zama ballatana na faɗa maka?
"Ban gane ina na samu lokaci ba? Ba nan na ke kwana ba in ban kwana ba, ba na zuwa da safe? Ban kiran ki a waya?
Kai tsaye na ce" Ba wannan ba kai da ka ke cin amarci? Amma ina da niyyar in faɗa maka daman."
Sai kawai ya kasa yi min mgana. Nima daga nan ban ƙara jan sa da wata mgana ba amma washegari na yi masa talla na ce ya siya ma yara tunda akwai na yara sai ya ce na ɗaukan musu guda biyu. Ba tare da ya sani ba na cire ma Nene da Gwaggo ɗaya ɗaya na saka albarka sai kuma bayan ya fita ya kirani a waya ya ce ya faɗa ma Gimbiya ta ce ta na so za ta zo ta duba nima na duba na ɗauka zai biya sannan na duba ma Nene itama. Ban ce masa na ɗaukan mata ba na yi masa godiya. Haka ko aka yi a daren ya kawo ta ta duba guda biyu ta ɗauka nima sai na ɗau biyun nan kuma ta ke ya turamin kuɗina Nene kuma biyu na ɗaukan mata sai na haɗa da na wajen nawa ya zama uku, ba shi ya kai mata ba Musbahu na kira ya zo ya karɓa ya kai mata daga baya na kira ta a waya na yi mata bayani ta ji daɗi ta yi ta saka min albarka.
Kuma an ta siyan Hijaban duk da na ɗan yi kyattuka da wasu. Na ɗaukan ma Saude da Marwa. Sauran kuma na tallata ma su Ya Aina da su Ya Hamza kuma duk sun siya ma matansu. Sannan har group ɗin makarantarmu na shiga na yi musu talla har mutum uku sun aiko da kuɗi sun siya sun kuma aiko har gida an karɓan musu. Duk da mun ɗan samu saɓani da Anty Bahijja amma tuni na yi mata na ƴan duniya da kaina na kira ta na yi mata tallar Hijaban sai ta fara min faɗa wai na gama yi mata rashin kunya zan neme ta yanzu. Ina dariya na wayance da cewa.
"Haba Babbar Yaya. Wace ni Sadiya ai ban isa ba. Rashin fahimta ce. Ke ce ba ki fahimce ni ba."