Kenza eBookz

Turken gida book 2 cmplete by janafty - Chapter 29

Turken gida book 2 cmplete by janafty - Chapter 29

Turken gida book 2 cmplete by janafty Chapter 29: Turken gida book 2 cmplete by janafty Chapter 29. Kamar yadda na yi alƙwari na sake yi mata faten…

3,278 words

Kamar yadda na yi alƙwari na sake yi mata faten Yallaɓai ya kai mata ta kirani ta na ta min godiya na ce bakomai ranar ban je asibitin ba sai washegari na iske Naja'atu da wasu ƙawayen Gimbiya har da abokan aikinta haka na ji Najan na faɗa ma Maman farko na dai shiga mun gaisa na fito domin na ga ana ta nuna ni, ko ba a yi mgana ba na san sai na fita za a ce ita ce kishiyar ta ki? Ranar ma mun sake haɗewa da Anty Bahijja ina kuma asibitin sai ga Ma'u ta zo tun ina mamakim munafunci Ma'u har na zo na daina amma ta ba ni mamaki da na ganta sanin ni dai ban faɗa ma kowa ba sai Ya Aina ita ma Marwa ce da muka yi waya na faɗa mata sai ta sanar da ita shi ne ta kira ta ji, har ta ce ko za ta yi ma su Ya Balki mgana ne su zo asibitin su duba ta na ce su yi zaman su ai ta ji sauƙi haba abin sai ya yi yawa gani ni ina ta zarya sai kuma na gayyato dangina.

Na san za ta sani tun da ta na tare da Anty Bahijja amma zuwan na ta ne ya fi ba ni mamaki kuma ita kanta ta ɗan yi wani iri da ta ganni. Mun gaisa da ita sama sama ina mai mamakinta Anty Bahijja ta yi mata jagora zuwa ciki ba daɗewa sai ga su sun fito har da ma wasu ƙawayen Gimbiyar da ita Naja'atun a gabansu Anty Bahijja ta kalleni ta na faɗin.

"Sadiya ashe ba ki faɗa ma kowa a gidanku Gimbiya ba ta da lafiya ba?

Sai na kalleta amma ban yi magana ba saboda na ga renin wayan ne ya yi yawa. To Gimbiyar uwata ce da zan yi she ɗan ciwonta a dangi ko Yallaɓai ne ai sai na ga daman na faɗa ballantana ita.

"Sai da na kira Ma'u ina ta mata tsiyan ba ta zo ba shi ne ta ke min rantsuwan ba ta sani ba. Kai tsaye na ce to laifin Sadiya ne wannan ita ce ba ta sanar da ku ba."

Ma'u na yi ma wani kallo kafin na sauke kallona kan Anty Bahijja kafin na ce" Ban faɗa ba amma tun da ita ta sani gashi har ta zo na wakiltata ta sanar da su." Daga haka na juya fuskata ina kallon wani bangaren raina kawai na ji yana tafasa ji na ke yi kamar na je na shake Ma'u.

"Ai ko zan faɗa ma su Ya Murja. Don dai dubiya mene a ciki? In sha Allahu na san za su zo" Ni dai ƙala ban ƙara ce musu ba har suka gama mganan da ƙawayen Gimbiyar za su tafi kamar Anty Bahijja ta kwanta musu haka ta raka su ta na yi musu godiya ni fa matar nan har mamakinta na ke yi, ba ta da yadda za ta yi dani ne da tuni ta saka an koreni Gimbiya ta mamaye komai sai dai kuma ta Allah ba ta ta ba na riga na zame mata ciwon ido. Ma'u da za ta tafi har da ba da kuɗi ina zaune ina ganin ikon Allah da ta yi min sallama ina ji amma ban amsa mata ba na haɗe rai suka fice ita da Anty Bahijja na raka su da harara kafin na ja tsaki.

Ranar kafin na bar asibitin nan sai da raina ya ɓaci Anty Bahijja daga ganin sauran fate da na yi ma Gimbiya jiya ta ce a bata ta shanye ta fara faɗa ba fa komai ne za ta riƙa sha ko ci ba kar ta manta ta na da juna biyu kuma ta na ƙarkashin kulawan likito ci ne.

"Ke Bahijja to ai fanten ne ta ke samu ya zauna mata. Kuma Sadiya ce ke yo mata ta na aikowa dashi wani zubin ma da kanta ta ke kawowa."

"Koma wace ce dai bai kamata a barta ta sha ba. Abu tun jiya duk ya yi sanyi sai kuma a bar ta tasha? Ai sai ya jawo mata wani illar Allah na tuba" Sai ta ɗanɗana faten da sauri ta furzar ta na faɗin" Tabɗijan wannan kaifin tsamin kawai ya isa ya zubar da ciki." Ina tsaye a ɗakin ina kallonta kuma ina jin ta amma matar nan ba ta fasa yada min mgana ba.

"Anty Bahijja ni na ke son tsamin fa.'

Gimbiya ta faɗa a hankali ita Maman farko shuru ta yi ba ta ƙara mgana ba.

"Kuma Likitoci sun ce ba wata matsala ko Mama?

Naja'atu ta faɗa ta na mai kallon Maman farko da ta yi kamar ba ta ji ba saboda abin ya ba ta haushi. Amma Anty Bahijja ƙiri ƙiri ta hana Gimbiya shan faten nan ta ce ba za ta sha ba.

"To wanne zan sha?

"Ba dai fate ba. Zan saka Suhailat ta yo miki ba shikenan ba"

Har Gimbiya sai da ta kalleta amma ba ta yi mgana ba. Nima ban ce komai ba na tattara kololina na saka a kwando na yi musu sallama shi ne Anty Bahijjan ta ke ce min" Ba raina ƙokarin ki na yi ba. An gode amma ya yi tsami da yawa ne kin gane? "Kar ki damu. Ki cigaba da yi mata mara tsamin wanda ba zai zubar da ciki ba." Ina gama faɗin haka na fice ina yi ma Maman farko sai anjuma ta amsa min da cewa na gaida gida.

Muna tafe acikin adaidaita ina jin ƙuna a raina na kuma ce tunda shi alheri ya koma sharri shike nan kuma an gama daman ni saboda Allah na yi da kuma Yallaɓai amma tunda lamarin ya zo da cin mutumci an gama mgana. Tun daga ranar ban ƙara dafa wani abu da sunan Gimbiya ba amma kuma ban fasa kai ma Maman farko. Gimbiyar da kanta ta kirani a waya ta na bani haƙuri na ce kar ta damu bakomai. Kawai ranar da Gimbiya ta cika sati a asibiti sai ga kiran Yallaɓai a waya wai don Allah na taimaka na yi ma Gimbiya faten wake kai tsaye ba kwana kwana na ce.

"Gaskiya ba zan yi ba Yallaɓai. Amma ka kira Anty Bahijja ta yi mata daga gidan ta."

"Saboda mene?

Ya tambaya cikin mamaki kai tsaye na ce" Saboda ba na son ƙananun mganganu ka kuma sanni ba ni da haƙuri kamar zawo na ke yi in raina ya ɓaci"

"Me ya faru?

"Komai ma ya faru. Na yo fate Anty Bahijja ta hana Gimbiya sha ta ce ya yi tsami da yawa wannan zai iya zubar mata ciki ma."

"Ita Anty Bahijjan ta ce?

"Ya wuce wai."

Na faɗa ina kaɗa kafa kamar ya na ganina.

"To ina ruwanki da ita? Ai ba don ita kike yi ba."

"Don Allah na ke yi amma ba shi zai saka na zauna ana ci mun mutumci ba. Daga alheri sai ya koma tsiya kuma? Na ƙarishe faɗa a fusace shi kuma ganin na fusata ya sa ya sassauta murya ya na faɗin" Na ji to ki yi hakuri kin ji ko? "Na yi haƙuri amma girkin ne ba zan yi ba." "To ni ne na ce ko Daughter? Bai kamata ki damu da mganar Anty Bahijja kin san halinta."

"Dole fa na damu. In wani abu ya zo ya faru ba fata ake yi ba mganganu suka tashi fa? Kasan ba zan zauna a ci zarafi ba in kuma na yi magana a ce na cika ƙorafi daga na ce an yi min kaza sai na ce an yi min kaza." Da gayya na daba masa mgana kuma na san ya san dashi na ke yo ina dalili daga abin arziki ban da ma ina da zuciyar Imani ni har wata kishiya ne zan zauna ina ma girki ina zuwa kai mata asibiti duk wannan sadaukarwan da na yi ba ta gani ba ta na neman ci min mutumci to ba ta isa ba mganin ayi ma to kar ma a fara shi.

"Ki yi hakuri na ce ko?

"Na faɗa maka na haƙura."

"To za ki yi ɗin?

"A'a."

"Me ya sa?

"Ai na faɗa maka dalilina."

Ina ji ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce" Duk na ji kuma zam mata mgana amma dai yanzu ki yi hakuri saboda ni saboda Daugther ki yi mata don Allah." Sai na yi shuru ban yi magana ba amma ina ta ƙunƙuni.

"Abar ƙaunata ki yi don Allah. Ni na yarda dake shi ya sa a komai nawa na ke sakawa a ciki. Da gaske na ke ke ɗin amintattaciya ta ce Sadiya."

Nan ma na yi masa shuru har dai ya gaji ya ce" Kin ji ko? "Na ji." "Za ki yi ɗin? "Uhm." Ina jin sautin mirmishin shi kafin ya ce" Yauwa Abar ƙaunata. Allah ya yi albarka." "Amin." Na amsa da Amin aciki ciki shi kuma har da yo min kiss ta cikin waya kafin ya ce" Sai na dawo."

Ko amshi ban yi ba na kashe wayata ina ƙunƙuni ina dalili Yallaɓai na neman ya maida ni yar aikin matarsa daga abin arziƙi ban so yi ba amma haka nan na tashi zan yi mata ban kalli kowa ba sai shi. Mijina ne a kowani hali zan cika Umarninsa, ko faɗa muka yi da Yallaɓai sai dai na yi gaba dashi da kaurace masa amma ba na hana shi abinci zan yi masa komai da na saba, ina bin Umarnin shi saboda na san haƙƙin mijina a kaina shi ya sa na danne komai na yi mata fanten wake ya aiko da hanta da allayahu na saka mata a ciki da ya dawo bayan isha'i ya yi wanka ya ci abinci ya je ya kai mata a wayar ma ya kira ni ta karɓa ta na ta min godiya na ce mata bakomai an zama ɗaya. Bayan mun gama wayar na daɗe zaune ina tunani sai na tuna mganar Alhajinmu da ya ce na yi mata alheri na kuma zauna da ita da alheri in ma ta na da wani sharri Allah zai mayar mata da kayanta.

Kuma ni dai ba ta min komai ba. Laifinta ɗaya ta aure min miji amma ko bayan auran ta na girmamani ta na sona ta na son ƴaƴana ko da ya ke dole ta so ƴaƴana tun da ta na son ubansu sannan nima ta na girmamani sosai sai dai kishi na yau da gobe amma ba zan ce ga wani laifin da ta taɓa yi min ba, tunanin haka ya sa na watsar da mganar Anty Bahijja a cikin raina kuma Yallaɓai in dai bai manta ba sai ya yi mata mgana daman gashi ba shiri ita ta saki nono ya kama akwai faɗan saƙo da saƙo a tsakanin su.

Kafin Yallaɓai ya dawo Marwa na kira da wayar Ya Aina ina tambayanta yadda suke ciki da Kawu nan ta ke faɗa min ma gobe ya ce zai zo ya kawo mata waya ina dariya na ce" To Madalla haka na ke son ji." Ita kunya ya hana ta mgana sai Ya Aina ta ba ma wayar muka gaisa.

"Ya jikin abokiyar zaman ki? Ɗazu Murja ta kira ni wai Ma'u ta faɗa mata kishiyarki ba ta da lafiya ta na kwance a asibiti ya kamata mu leƙa."

Ban yi mamakin abin da Ma'u ta ce ba kuma ban yi ma Ya Aina munafunci ba kai tsaye na ce" Ya Aina kar ku wani zo don Allah ta ji sauki kuma ga ni ina zuwa Ma'un ma ta je duk bai isa ba! Sai kun zo?

"Kuma fa haka ne. To shikenan kya mata sannu. " Na amsa mata da zan faɗa mata. "Me ke damun ta hala? "Ciki gare ta sai ya ɗan samu rauni an dai ce ta samu cikakken hutu." Ya Aina ta ce Allah ya ingata ya raba lafiya. Daga nan muka yo sallama ba daɗewa Yallaɓai ya dawo ya na faɗa min na ga yadda Gimbiya ta sha fanten waken nan kuwa?

"Ko?

Na faɗa ina kallon shi, ya na zama saman kujera ya ke sake faɗin" Wallahi. Ta yi ta santi ta ce na ƙara gode miki." "Ayya ai bakomai." Na faɗa kai tsaye akwai sauran ragowan faten wake sai na kawo ma Yallaɓai ya sha kaɗan sai ya ɗan sha ruwan zafi ko da ya dawo su Jidda sun yi barci ni da shi ne muka yi ta kallo muna hira sai wajen sha biyun dare muka kwanta.

Da safiyar asabar ba makaranta Tahfez kuma yara sun makara ya sa na ce su haƙura sai gobe kawai. Yallaɓai ya fita ba daɗewa sai ga shi ya dawo ina kitchen ina wanke wanke Saude ba ta nan sun je ƙauyen Gwarzo biki, Jidda na can ɗakin su na ce ta gyara Baby kuma na gaban Tibi ta na kallon Cartoon Ashe mantuwa ya yi ya dawo ɗauka a lokacin ne ya ke faɗa min suna saka rai yau ko gobe za a sallami Gimbiya na ce Allah ya sa domin ta fi sati a asibitin kuma ta ji sauƙi alhamdulillah.

Ranar ban ma saka a raina zan je asibitin ba sai da Hauwa ta zo ta ce ba ta je ba, saboda ba ta nan taje Rano, jin haka ya sa na ce bari na shirya muje tare har ma Hauwa ta kira Munnira ita kuma sai ta ce shekarajiya Jamila ta biyo mata suka je amma tun da za mu je ba ri ta shirya mu jira ta sai mu tafi gabaɗaya. Haka ko aka yi sai da muka jira ta ta zo muka tafi tare na bar ma Jidda gidan ita da Baby.

Mun je mun iske asibitin cike da mutane su Anty Bahijja ne da su Anty Maimuna. Halima Suwaiba, Nasara sai Jawaherr da ta ce jiya ta zo gida hutun semister, Maman farko ba ta nan ta koma gida ta yi wanka ta huta, mun gaggaisa da kowa da kowa cikin sakewa amma ita Anty Bahijja sai da ta saƙa mana mgana.

"Uwargida da tawagan ta."

Ta faɗa ta na dariya ni na san da sigan cin mutumci ne ta yi maaganar shi ya sa nima na mayar mata da martani. "Uhm Anty Bahijja yar tawagan Amarya kuma ba " To zan zauna ne ta na gaya min mgana me na yi mata? Da na faɗi haka sai ta wayance da dariya aka yi dariyan gabaɗaya kowa na ciki na ciki mun gaisa da Gimbiyar ta ji sauki itama ta sake faɗa min yau ko gobe likita ya ce za a sallameta na ce Allah ya ƙara lafiya.

An cika ɗakin ana ta hira shi ne ma muka ji Anty Bahijja na waya da Hajiyar Tafida ana mganar wanda za a samo daga rano zai zauna tare da Gimbiya amma kamar ba a samu ba kowa na da iyalai da abin yi, bayan ta gama wayar ta kalli Anty Maimuna ta na faɗin" Kin ji ita kanta Baaba Asma'un da na hango ba ta da lafiya.'

"Topha. Ba dai a samu mai zuwa ya zauna da itan ba kenan?

"Ba a samu ba kam."

"To ta koma wajen Nene kawai ta zauna ba shike nan ba."

Anty Bahijja ta ce" Nima haka na ce da farko to kin san halin Tafida da taurin kai ya ce wai Nene na fama da kanta itama. Kuma na kawo hujjan ga su Maman farko ga iya ai duk za su kula da ita ya ce a'a a samo wacce za ta zauna da ita."

"Wallahi kuwa. To da ya ce bai yarda ba yanzu da ba a samu mai zaman ba ya zai yi?

"Shi dai ya sani. Abin haushin ma ita Mimisco ta goya masa baya. Shi fa shegen nuna iko ne da shi."

Ni dai ina gefe in jin su ban tofa ba daga karshe ma ni da Hauwa muka fara tafiya salla tun da ana ta kiran sallar azahar Munnira ba ta yi ta na hutu shi ya sa ba ta biyo mu ba. Bayan ma mun idar da sallar mun zauna a wajen cikin asibitin muna ta hira da Hauwa. Ta na gaya min ba in da labarin cikin Gimbiya bai za ga ba na ce ai ya za ga tun da su Anty Bahijja na raye.

"Ji fa suke yi kamar Tafida bai taɓa haihuwa ba sai yanzu."

Ina murmishin takaici kafin na ce" Bai taɓa ba mana. Ni ai bare ce saboda haka ƴaƴana ma bare ne. Ita kuma ta su ce haka ma ƴaƴan da za ta haifa ma kin ga ai na su ne." Hauwa ta rike baki kafin ta ce" Lalle kam" Ban ƙara mgana ba amma ina ƙokarin danne wani abu dake ta so min a ƙasan zuciyata.

Bayan mun koma ɗakin har dai lokacin Anty Bahijja na ta buge bugen waya amma ba a dace ba. To kowa na da abin yi wata mata ce za ta yarda a ɗaukota a zaunar da ita waje ɗaya sama da wata ɗaya tun da na ji Halima na faɗin likita ya ce bedrest za ta yi na sati biyar ko botiki ba a yarda ta ɗauka ba ai neman mai zaman akwai wahala Yallaɓai kuma ba mace ba ne ballatana su ce ya zauna ya kula da ita dole dai ƙanwar naƙi wata macen za su nema. Har muka baro asibitin gabda mangariba ba a dace ba ina jin Anty Maimuna har Nene ta kira ta na faɗa mata ba a samu mai zama ba kowa suka kira sai ya ce ga uzurin shi kila Nenen ta ce a dawo da Gimbiyar wajenta sai na ji ta na cewa.

"To Nene Tafidan ya hana. Sai dai ki yi masa mgana ƙila ke ya saurare ki."

Daga karshe na ji ta na cewa to shikenan. Mun rabu da su Hauwa a bakin asibiti na hau adaidaita zuwa gida ban san abin da ya faru ba, can bayan isha'i Yallaɓai ya na dawowa wanka kawai ya yi ko abinci bai ci ya ce mu je ɗaki zai yi magana da ni, ina falo ne ma ina koya ma Baby aikin da aka ba ta a makaranta da na ce ma ya bari mu gani sai gani na yi ya ƙariso ya kama hannuna ya mikar da ni tsaye ya kuma nufi har korido ya na faɗin.

"Ƙarisa mata aikin Jidda."

"To Abba."

Ta faɗa cikin sanyin ta damam ta na gefe itama ta na yin nata.

"Mene ne ya faru Yallaɓai?

Na faɗa ina biye da shi a baya bai direni ko'ina ba sai da muka shiga cikin bedroom ɗin mu, kan gado ya zaunar da ni tun da na ga ya jawo stool ɗin madubi ya zauna na san akwai mgana ko wani abu ya faru.

"Mene ne ya faru Yallaɓai? Ka fara ba ni tsoro."

Na faɗa ina kallon shi ganin kamar ba ya cikin natsuwarsa.

"Sadiya."

"Na'am me ya faru?

Na amsa shi a gaggauce sai ya sauke ajiyar zuciya ya riƙe hannayena duka biyu tun da na ga haka jikina ya ba ni cutavta Yallaɓai zai yi tun da na ga wannan ladabin na shi.

"Me kake so?

Na katse mishi tunani sai ya ɗago yana kallona kafin ya ce" Alfarma zan ƙara roƙa a wajen ki." "Ina jin ka" "Kin san ina sonki ko Sadiya ta? "Na san wannan ka tafi kai tsaye? Me kake son na yi maka?

"Izinin ki na ke nema."

"Izini kuma? Izinin me?

Na faɗa cikin ƙanƙance ido ina kallon Yallaɓai.

"Ina so Daughtet ta dawo gidan nan da zama"

Sai na zaro ido ina kallon shi cikin mamakin kalaman shi.

Readers Also Read