Turken gida book 2 cmplete by janafty - Chapter 30
Turken gida book 2 cmplete by janafty Chapter 30: Turken gida book 2 cmplete by janafty Chapter 30. "Nufina na ɗan lokaci saboda kin san dai na faɗa miki…
3,315 words
"Nufina na ɗan lokaci saboda kin san dai na faɗa miki dokar likita ko? To ba a samu wacce za ta je gidanta domin ta zauna da ita ba. An ce ta koma wajen Nene ni kuma na ce a'a Nene ma ba ta da lafiya sai na yi tunanin duk duniya bayan iyayena ba ni da kamarki. Za ki kula da Daugther a gaban idona haka kuma za ki kulata da ita a bayan ido na shi ya sa na yanke shawaran za ta dawo nan gidan ta zauna tare damu har ta fita daga dokar likitoci."
Har ya gama mgana kallon shi na ke yi cikin mamaki. To yanzu kuma abin da ke shirin tunkaro ni kenab? Gimbiya a gidana? Ban taɓa tunanin haka ba shi ya sa na zama kawai ina kallon Yallaɓai na kasa mgana."
"Ki yi magana mana Sadiya."
Ya faɗa ya na matse hannayena cikin na shi.
"Me kake so na ce? Ka na so na ce a'a ne?
Na faɗa ina kallon shi sai ya yi saurin girgiza kai kafin ya samu zarafin mgana na tare shi da cewa" Na ce a'a mutane su je su ce kai da gidan ka na hana ka yin abin da kake so?
"Ba haka ba ne. Haƙƙin ki ne na sanar da ke. Kuma muhimmanci ki ne ya sa na ce ta zo gidan ki ta zauna tare damu."
Kallon shi kawai na ke yi na ma kasa mgana saboda mamaki.
"Aiki zan riƙa yi ma matarka Yallaɓai?
"Aiki kuma? Haba wani irin aiki kuma? Ko ni da na gina gidan nan da sunan ki na gina shi saboda haka duk wacce za ta zo ta zauna alfarman ki za ta ci. Ita Daugther rigar alfarman da kika yi min za ta shiga ciki amma in har kin ce a'a shike nan ba ni da zabi sai ta koma Rano kawai."
"Ka san zan iya cewa a'a me ya sa ka kawo mini mganar?
"Na san ma ba za ki ce Aa ɗin ba ne shi ya sa."
Shuru kawai na yi ban yi mgana ba, uhm ni fa namiji ya daina mamaki ya zo ya na yaudarata da mgana yanzu na ce ban yarda ba magana ta fita a gari a ce na hana ta zama a gidan mijinta gida ba na uwata ba kuma ba na ubana ba. Gidan shi ne ya na da damar da ko kare ya kawo ya sauke ba zan yi magana ba. Abu ɗaya ne ba zan ɗauka cin zarafi da wulakanci. Sai na kalle shi na ga shima ni ya ke kallo ya na jiran ya ji me zan ce.
"Shike nan bakomai ai gidan ka ne itama gidanta ne."
Na faɗa ina danne wani abu daga ƙasan zuciya. Rumgumeni ya yi daga zaunan ya na faɗin" Na gode Abar ƙaunata" Kallon shi kawai na yi ba tare da na yi masa mgana ba.
"Amma ina da mgana."
Sai ya ɗago ya na kallona ni kuma sai na gyara zama ina faɗin" Ta zo ta zauna ban damu ko yau ko gobe ko sai ta shekara ko kuma anan ɗin ma zata zauna gabaɗaya ba. Ai gidan ka ne itama tana da iko da shi saboda haka ba ni da hurumin na ce wani abu akan haka, abu ɗaya ne ba zan ɗauka ba a zo har gidana a ce za a ci min mutumci, in hakan ya faru ba zan yi shuru ka san halina ba ni da hakuri matukar aka taɓa min mutumcina."
"In sha Allahu ba abin da zai faru. Daughter tana girmamaki ina da tabbacin ba abin da zai faru."
"To wai kar ma ya farun ne na yi mgana ka ce na cika cewa an yi min kaza."
"Ba zai faru ba in sha Allahu."..
Ya faɗa ya na min mirmishi. Hannuna na zare a na shi kafin na miƙe ina faɗin" Wani ɗaki za mu sauke ta? "Wanda kika ce Madam" Sai na kalle shi kafin na ce" Ko ɗakin nan nawa na baƙi? Tun da kusa ne da namu." "Ba matsala? "Babu mana."
"To shike nan a yi haka ɗin."
Sai na jinJina kai kafin na ce bari in na gama da yara sai na shiga na dan ƙara gyara ɗakin Sai ya riƙo hannuna na juyo ina kallon shi. Shima ya na kallona har ya na wani sauke ido.
"Na gode Abar ƙaunata"
"Yallaɓai ni kuma yaushe na koma Abar ƙaunar ka kuma?
Ya na mirmishi ya miƙe ya rumgumeni ya na faɗin" Tun a ranar farko da na fara ɗora idanuwana a kan na san cewa tabbas ke ɗin Abar ƙaunar Yusuf ne." Ni dai ina ta dariyan yaudaran Yallaɓai saboda na yarda da zaman matarshi a gidana shi ne zai zaunar da ni ya na min ruwan kalamai. Kai jama' a Maza na abin da suke so ranar kusan raba dare muka yi muna hira da Yallaɓai da na yi magana jikinsa na rawa saboda wata macen sai na ke tunanin in da na yi boren ban yarda ba ya na gaba gaba wajen ci min mutumci ko ba a yau ɗin nan ba nan gaba sai ya yi min gori kuma dangin sa su ji labari su tsine min.
Da safe ya ke faɗa min sun yi waya da Gimbiyar an yi ma sallama saboda haka yanzu daga nan asibitin zai je ya ɗauko su. Na ce to ni kuma zan ɗan kara gyara ɗakin. Wanka ya yi muka karya tare su Jidda sun tafi Tahfeez da wuri tun da jiya ba su je ba. Ɗan gyara gidan na yi na saka turare daman ɗakin da Gimbiyar za ta zauna tun jiya na gama gyara shi daman kuma a gyare ya ke sai dai ƙura.
Karfe sha ɗaya da wani abu na safe na ji ƙaran buɗe get da shigowar mota. Ban fita ba domin ba zan iya zuwa tarban kishiya ba ai na yi iya abin da zan iya yi. Ina falon yara suka shigo Gimbiya ne da Anty Bahijjja sai Maman farko Yallaɓai daga baya ya shigo ɗauke da kayan su. Na karɓe su faram faram kamar yadda na saba na yi musu kuma jagora har ɗakin da zata sauka Maman farko na ta yi min sannu da godiya ina amsawa na je na kawo musu ruwa suka ce sun ƙoshi fita na yi na ba su waje Yallaɓai bai zauna ba ya fice tare da Maman farko da zai maida ta gida ita dai na rakata har haraba sai bayan tafiyar su ne na dawo cikin gida na yi zamana a falo can ba daɗewa sai ga Anty Bahijja ta fito ta kalleni daga sama har ƙasa kafin ta ce.
"Wai ashe kin ji haushin hana Gimbiya shan faten nan da kika yo mata ranar a asibiti Sadiya ?
Na kalleta ban yi mata mgana ba sai ta cigaba da faɗin" Ni ban san kin ji haushi ni fa har a zuciyata ba da wata munafa na yi ba kawai sai ga shi kin turo Tafida ya zo ya na min faɗa tun da an taba uwarsa ba."
"Ni ban turo shi ba."
Na faɗa ina kauda kaina gefe sai ta basar kafin ta ce" Koma da mene ne ni ban ce haka domin na ci zarafin ki. gwara ma ki daina jin haushina." Mirmishi kawai na yi ban yi magana ba to me zan ce? In yi magana ta ce na zageta ko na yo mata rashin kunya.. Ta gama zagayen gidan ta koma ciki ba daɗewa sai ga Naja'atu ta zo kamar kayan Gimbiyar ta je ta kwaso mata. Wajen uku na rana suka tafi lokacin har na gama abinci amma ba su tsaya sun ci ba Anty Bahijja har ta na ƙara jadaddamin likita ya ce ko botiki kar Gimbiya ta ɗaga ta rika cin wake da abinci mai allayahu, hutu kawai ta ke bukata kuma shi za ta yi, na ji tsoron Allah tun da dai Tafida ya na ce sai an kawo ta gidana na kula da ita sosai
Mamaki bar bar ni na yi mgana ba har suka fice daga gidan. Na saki a tsaki a fili na ce" Tun da ni na yi mata cikin ba.' ko kuma ni mahaifata ba ta taɓa ɗaukan cikin ba." Daman ni na san za a rina an saci zanin mahaukaciya ko ita Gimbiya ba ta munana min ba irin su Anty Bahijja yan kanzagi ai za su munana min. Zuciyata na kai nesa na riƙa shiga ina duba Gimbiya ba saboda Anty Bahijja ba sai saboda Allah da kuma Yallaɓai. Na samu bayan ta ci abiinci ta sha mgani sai ta kwanta barci sai bayan la'asar ta tashi ta yi salla.
Saboda ita na yi mana Tuwon semo da miyar kuka mai naman rago tun da ta ce min ta na so. Da yamma da su Jidda suka dawo makaranta ya sa sai ga ta fito falo ma muna ta hira da ita. Sai dare Yallaɓai ya dawo yadda ya ganmu tare ya sa bakin sa ya ƙi rufuwa sai washe haƙora ya ke yi ina lura da shi. Kamar magungunanta akwai na barci ta na sha ta ce min za ta shiga ta kwanta sai na ce ma Yallaɓai ya je wajenta ya kwana saboda makirci har ya na ce min.
"Ba matsala."
"Babu."
Na amsa masa a takaice saboda ni nasan can ya ke son ya ce zai kwana kunya ce ta hana shi mgana. Ina gidan a gaban idanuwana Yallaɓai ya shige da Gimbiya ɗaki suka sakayo ƙofa sai da na yi kuka karshenta dai Jidda da Baby na ɗauko zuwa ɗaki na suka taya ni kwana amma ji na ke yi kamar ba zan iya ba. Muna gida ɗaya kusa da ɗakin juna amma Yallaɓai ba ya tare da ni ya na tare da wata matar ba ni ba, lalle mata suna ƙokari matan da ake yi musu kishiya suna zama da su a gida ɗaya ya tabbata za a kira su Jarumai.
*Janafty* *TKG016*
Tun dawowar Gimbiya gidana na ke ta ganin ikon Allah a wajen Yallaɓai da dangin shi, su rawan ƙafa shima rawan ƙafa, ni dai ina gefe ina ganin komai kamar al'amara kamar mafarki. A ce yau wai a gaban idanuwana Yallaɓai ke ririta wata macen ba ni ba, kuma a cikin gidana ƴan'uwansa ke zarya saboda wata ba ni ba. Rayuwa kenan abin da ya baka dariya wata rana shi zai koma ya na ba ka tsoro.
Anty Bahijja ku san kullum sai ta zo gidan nan sai ka ce ni ɗin zan cutar da Gimbiyar ne. Kuma in ta zo ta riƙa bibiya kenan me Gimbiya ta ci? Kar a riƙa ba ta abincin da ba ta so kar a riƙa tashin ta daga barci in ta kwanta daga ta ce wannan sai ta ce wannan, ni dai ba na wahalar da kaina wajen mgana, saboda duk abin da zan faɗa ba shi zai sa komai ya koma yadda ya ke a baya ba shi ya sa kawai na kawo ido na saka musu daga shi har ƴan'uwan na shi.
Abu ɗaya na ke yi shi ne ina girki sannan in zan dafa na kan shiga na ji ra'ayinta in ma na dafa abin da ba ta so in har ta ce min ga abin da ta ke so ina dafa mata ba zai gagare ni ba. Don Allah na ke yi don kuma ita da Yallaɓai sannan in ya fita ina shiga na duba ta in na ji ta shuru saboda kar wani abu ya faru a ce ai ina gidan amma ban sani ba, ba ta cika fitowa falo da rana ba sai dare shima sai Yallaɓai ya matsa mata, yara kuma suna shiga wajenta suna ɗeɓe mata kewa ni dai tsakanina da ita sai mutumtatawa na kama girmana na riƙe gam ko da na gani ɗin ba na ma nuna na gani ɗin amma domin ba a yin abubuwa ba ana yin abubuwa, kawai dai ina kauda kaina ne, in na ga Yallaɓai na wani ɓare ɓare a kan Gimbiya kawai kai na ke girgizawa, sannan nima sai ki ga ya na wani min rawan baki ba saboda komai ba ne saboda matarsa ce ya ga ta na zaune damu ina kula da ita da zuciya ɗaya. Kallon shi kawai na ke yi amma ni a idanuwana kar na ke kallon shi ba wani abin da Yallaɓai zai yi da ban gane manufarsa ba Allah na tuba ai jiya ba yau ba.
Kowa ya ji Gimbiya na gidana sai ya yi mamaki Munnira ta doka min kira ta na min kumfar bakin a gida ne zan sama ma kishiya wajen zama ta na kwance ina yi mata aiki? Ina dariya na ce" To miye a ciki Munnira? "Akwai mana. Kuma miji ya kwana da ita? "E" Na faɗa ina dariya wata ashar ta laulayo da sai da na ce"Ke Munnira ko ni da haɗa iri da katsina ban iya wannan ashar ɗin ba."
"Abin ne na ji kamar ma na yi zage zage" "Me ye a ciki? To ai ta aure shi to gida kuma don ta zauna ai duk abu ɗaya ne Munnira. Ni dai fata na mu rabu lafiya kawai " Duk yadda ta so ta nuna min kar na yarda ta zauna ba ta aiki kuma ina bata miji ban nuna na gane ba, ni yanzu me zai dame ni? Abin da na ke ma gudu da kishi tuni ya faru to me ya yi saura? Ciki gare ta fa kuma cikin ba na kowa ba sai na Yallaɓai to me ya yi saura? Babu saboda haka mganar gida ko kwana ƙaramin abu ne a waje na tunda na iya hakuri na bari muka raba mijin da ita ai kuma an gama mgana.
Daman ni a raina na yi niyyar na ce Yallaɓai ya yi sati a ɗakin Gimbiya ban dai riga na furta masa ba amma ina da niyyar haka har a cikin raina. Ranar da ya cika kwana uku a ɗakin Gimbiya ina shirin sai ya dawo da daddare na ce masa kawai ya yi mata sati kafin ya dawo wajena amma sai na ga da safiyar Allah Yallaɓai ya fito min da munafuci wai ni Yallabai zai mayar ƙaramar yarinya muna karyawa a saman dining ni da shi yara sun tafi makaranta. Gimbiya kuma ta na ciki ba ta tashi ba tukunna. Sai ya kalleni ya na min duniyan cin da ya koya tun da ya yi aure nan.
"Abar ƙaunata."
Sai na kalle shi amma ban yi magana ba.
"Na gode."
"Wannan godiyar fa?
"Ta ki ce, ki karɓa da martabawa."
Sai na yi mirmishii kafin na ce" To shike nan na karɓa." Tun da na ga yanayin shi na san cewa tabbas wani abu ya ke so, shi ya sa sai wani kashe murya ya ke yi ya na wani ja na da hira, sai faɗa min ya ke yi yanzu kwangila biyu ne a kan tuburin shi akwai na gina wani ƙaramin ma'aikata sannan akwai ma na Kaduna again faɗa min ya ke yi wattanin nan ya na ta samun aiki sai godiya.
"Ma sha Allah. Allah ya sa albarka ya kuma ba da sa'a."
Ya amsa min da Amin ya na faɗa min zuwa gaba in komai ya dai dai ta, ya na so shima ya gina kamfanin shi ko ƙarami ne kafin zuwa gaba, ni kuma sai na ce ai hakan ya yi saboda komai na son cigaba, kuma babbar cigaba ne a gare shi tun da ya na samun manyan kwangiloli mun daɗe muna tattauna abin da ya shafi aiki sannan muka ganganro kan maganar Gimbiya wai ni Yallaɓai zai zaunar ya na kallo na ya na min bariki da munafuncin su na maza.
"Ina faɗa miki jiya fa Daugther sai ciwon ciki cikin dare."
"Subhanallah me ya faru?
"Ni ma ban sani ba, ta ɗan yi kukan cikin ne amma ina ba ta mganinta sai kuma ya lafa sannan ta yi barci."
"Allah ya ƙara lafiya. Ko dai za ku je asibiti ne?
Sai ya girgiza min kai kafin ya ce" Na ce mu je asibiti ta ce min wai cikin ya bari." Sai na kalle shi amma ban yi mgana ba sai na ji ya cigaba da cewa" Ni tunani ma dare Sadiya. Amma dai na ce ga waya nan tun da muna tare in wani abu ya faru kawai sai ta kira ni ko? Ƙura masa ido na yi ina kallon shi sai ya ƙara cewa" Ko? Na ce ai ga waya ma da ta ji wani abu ta kirani ko ta kira ki."
Har Yallaɓai ya gama lissafin kwanakin shi ya ƙare a ɗakin Gimbiya ba ya so ya ce min zai riƙa kwana a can saboda kar cikin dare wani abu ya faru kai tsaye shi ne zai shiryamin alaye kamar ni ɗin ƙaramar yarinya ce.
"Ba ki ce komai ba?
Ya faɗa ya na goge bakin shi da Tissue, sai na yi masa wani irin kallo kafin na yi mirmishi. "Me zan ce! Ai ba sai ta kai ga haka ba. Daman ina shirin na faɗa maka cewa ka yi zaman ka a ɗakin Gimbiya har ta samu lafiya ta koma gidan ta." "Saboda mene? Ya faɗa ya na kallona irin me ya sa kika min haka ɗin nan. "Saboda cikin dare mana? Ba fata mu ke yi ba in wani abu ya faru kiran waya zai yi wahala gwara dai ka na kusa ɗin zai fi."
"Ban gane ba."
Ya faɗa ya na kallona ni kuma sai na miƙe ina tattara kwanakun da muka yi amfani da su lokaci ɗaya ina faɗin" Shi ne na ce ka cigaba kawai da kwana tare da ita har ta samu lafiya ta koma gidan ta." Ina gama faɗin haka na kwashi kayan hannuna na bar masa falon, ni sai ma ya ba ni dariya daman wai Yallaɓai ya iya alayen magana haka? Ai ban taɓa sani ba sai yau ƙwalla suka cika min ƙwarmin idanuwana yau har an yi lokacin da Yallaɓai ba ya son kwana dani sai da wata macen. Har an zo gabar da zai ji gwara ya riƙa kwana da mataras sama da ni. Ni ce fa Sadiya. Sadiyar shi da ban taɓa tunanin wata rana da za ta so Yallaɓai ya ririta wata mace bayan ni ba, sai ga shi ya na faruwa a lokacin kusan ma da ban yi tunani ba.
Ina kitchen din ya biyo ni ya na borin kunya. To borin kunya mana Yallaɓai ya kalli tsabar idanuwana ya na faɗin" ban gane na koma wajen ta gabaɗaya ba? Da wa kika yi shawara kafin ki yanke hukunci? Ni ko na ce ai maganar ba ta bukatar shawara shi ya sa ban faɗa masa ba. Sai ya fara kunyata kan shi ya na faɗin" To ni ban amince ba. Ki ma bar wannan mganar."
Shuru na yi masa kawai saboda ba na so maganar ta yi nisa. Ya zo ya rumgumeni ya sumbace ni a goshi ya na faɗin" Sai na dawo." Na yi masa fatan dawowa lafiya ina ganin shi sai da ya shiga ciki ya duba Gimbiya sannan ya fice, ina aiki ina danne abin da ke ta so min a ƙasan raina ina ƙara karfafama kaina gwiwan da komai ma zai wuce in sha Allahu, duk rashin son aikina yanzu na zage Saude na makaranta sai al'hamis zuwa lahadi ta ke zuwa. Ko kafin Gimbiya ta tashi barci na gama duka aikina har na yi wanka sai da na fita falo na ganta zaune muka gaisa cikin faram faram ɗin da muka saba. Maaganar abin da za ta karya na yi mata sai ta ce.
"Madam in da zan samu kunu da na so."
"Ina da sauran garin kunun ai bai ƙare ba sai na dama miki."
"Na gode Allah ya saka da alheri."
"Amin. Bakomai."