Kenza eBookz

Turken gida book 2 cmplete by janafty - Chapter 31

Turken gida book 2 cmplete by janafty - Chapter 31

Turken gida book 2 cmplete by janafty Chapter 31: Turken gida book 2 cmplete by janafty Chapter 31. Na faɗa ina kallonta, sai na ga ta ɗan sunkuyar da…

3,285 words

Na faɗa ina kallonta, sai na ga ta ɗan sunkuyar da kanta ƙasa sai na dawo ina faɗin" Na manta ya jikin? Yallaɓai ɗazu ya ke faɗa min jiya cikin dare ciwon ciki ya taso miki.? Sai ta kalleni kafin ta yi mirmishi ta na faɗin" Laa ba fa wani abu ba ne, wai sai da ya faɗa miki? Sai na gyaɗa kaina kafin na ce" Allah ya ƙara lafiya. Ina fatan dai ba matsala? "Babu matsala, kawai cikina ne ya ɗan lalace amma ba matsala "

"Ayya sannu. Allah ya ƙara lafiya"

Ta amsa da Amin sai na ce ta kunna Tv mana zaman shuru ba daɗi sai ta ce ba ta son hayaniya. Sai na ƙyaleta na tafi kitchen na ɗora mata ruwan zafin sannan na ɗauko garin kunin na dama, tsamiyar tawa ma kaɗan ta rage ita kenan na yi mata amfani da shi har garin kunin ma ya ƙare daman Maman Saude ce na aika ma gero ta daka min dole itama zan ƙara yi ma mgana ta sake daka min tun da Gimbiya kokon ta ke sha ai saboda ita ne gero har tiya goma Yallaɓai ya siyo ya ijemin ni dai ya san ban cika shan kuni ba in dai ba azumi ba, zai yi wahala na sha kuni sai dai kuma in ba ni da lafiya Yallaɓai ma sai irin shekara bayan shekara gaskiya tun da na ga an kawo gero na san saboda wacce aka kawo shi.

Bayan na dama mata ban saka mata siga ba saboda ba ta so na kuma kawo mata har falo, ta karɓa ta na ta min godiya. Mun ɗan zauna ni da ita muna ɗan taɓa hira sama sama kafin ta gama shan kokon ta ce min za ta je ta sha mgani ta ɗan kwanta na ce mata to. Tun da ta shige ciki sai ni kaɗai a gida sai can da rana sai ga Naja'atu ta zo itama muna gaisawa ta shige ciki, daman haka suke yi da sun zo domin ita daman suka zo za su shige ciki. Ni daman muna ta waya da mai hijabai za a kawo min wasu sannan na saka a ɗinka ma Amina domin ta ce ta yi talla ana so. To shi ne za a aika mata kaduna ni ma za'a aiko min dashi, da daddare tuwon shinkafa na yi miyar ganye Naja'atu sai mangariba Direba ya zo ɗaukanta ashe ƙasar za su bari ita da mijinta shi ya sa ta zo yi ma ƙawar ta ta sallama nima da suka fito ne Gimbiyar ta rako ta ta ke faɗa min na ce Allah ya tsare hanya.

Yallaɓai ya ɗauka na bar maganar sai ga shi ya na dawowa, bayan ya shiga ɗaki na ya yi wanka ya fito falo ya ni da shi da yara har da Gimbiyar muna cin abinci ita kaɗan ta ci tuwon miyan ne ta ɗan sha da yawa. Ni da Yallaɓai ne muke hira ita kuma daman yara ne abokan maganarta, ban sanin musu ba amma ba ta sakin jiki ta yi hira da shi in dai ina wajen gwara shi ma ya na ɗan janta da mgana ita ce za ka ga ta na wani sunne kai, amma na san in sun shiga ciki ba za su rasa yin hiran su ba.

Ni da Yallaɓai mun daɗe a falo muna kallo daman in dai ya ga ana Horror film sai ya ja ni ya ce mu kalla tare. Yara tuni sun shige ciki Gimbiya ma ana fara ta tashi ta ce ba ta kallon fina finan tsoro har ya na zolayanta da cewa" Ke ba Jaruma ba ce Daugther amma zan koya miki kallo kamar yadda na koyar da Sadiya ta." Banza da shi ta yi ta shige ciki ta na yi min sai da safe ta bar ni da shi ya na ta takalata da hira ni ma da na gaji sai na fara yi masa hammar ƙarya, na kuma ce masa ina jin barci zan je na kwanta har na miƙe sai na kalle shi kafin na ce.

"Sai da safe."

"Sai na shigo dai ko?

Ya faɗa hankalin shi na wajen kallo.

"Ka manta! Ai a ɗakin Gimbiya za ka kwana."

Sai ya ɗago ya na kallona kafin ya ce" Ba na ce a bar mganar ba." "Ba za a barta ba. Domin da gaske na ke yi." Kallona ya yi ni kuma sai na juya ina ƙara faɗin" Mu kwana lafiya." Na yi wuceta ciki Tiolet na shiga na kama ruwa sannan na koma ɗaki na sauya kaya zuwa na barci ina shirin kwanciya sai ga shi ya shigo sai na kalle shi kafin na ce" Ba mun yi sallama ba?

Karisa shigowa ɗakin ya yi ya na faɗin" Sadiya me ya sa kika yi hakan? "Saboda hakan ne ya kamata. Ba ta da lafiya gwara ka riƙa kwana a kusa da ita." Sai ya yi shuru bai yi mgana ni kuma sai na zauna a gefen gado ina faɗin" Kar ka damu ba matsala ni na ce ai ka je."

"Kin tabbata ba matsala?

Sai na kalleshi ina jin takaici in Yallaɓai ya yi min tambayar nan daman zai yi min kishiya ne ya ce min kuma ba matsala. Ban nuna masa ba illa ƴar dariya da na yi kafin na ce" Na ce ba matsala ka je kawai." "Na je bakomai? Sai na gyaɗa masa kai sai na ga ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce" Na gode. Allah ya tashe mu lafiya." "Amin."

Takowa ya yi zuwa gaba na ya duƙa ya na sumbatar goshina.

"Sadiya."

Ya kira sunana na ɗago ina kallon shi kafin na yi mgana ya ce.

"Sai da safe."

"Sai da safe."

Na mayar masa da martanin mganarsa har ya juya zai tafi sai gashi ya ƙara juyowa ya na kallona kafin ya ce" Ko za ki ɗauko yara ne? "Bar su kawai yau ni kaɗai zan kwana." Sai na ga ya kalleni ni wannam makircin na Yallaɓai ya fara ba ni dariya wai yau ya saba tafiya ya bar ni? Da ya ke barin gidan ma gabaɗaya fa? Duk bai yi haka ba sai yau.

"Ka je kawai Yallaɓai bakomai"

"Kin tabbata?

Sai kawai na kwashe da dariya kafin na ce" To ko da wani abun akwai abin da za a fasa ne? Sai ya ware min ido ya na kallona ni kuma sai na cigaba da faɗin" Ba abin da zai canza Yallaɓai, mene ne a cikin kwana? Tun da na yi sharing ɗin ka da ita an gama mgana. Kwana a ɗakin ta ba zai rage ni ba kuma ba zai kare ni ba saboda haka ka je kawai sai da safe."

Ina gama faɗin haka na koma na kwanta ina mai rufe kafafuwana da bargo har ina lumshe ido, shima ganin haka ya sa ya ja siraran kafafun shi ya fice na bi shi da kallo daga wutsiyar ido na sai da ya fice ya jawo min kofa sannan na sauke ajiyar zuciya ina mai ƙara jinjina halin Maza in suka ƙara aure. Na daɗe ban yi barci ba sai can kuma barcin ya ɗauke ni har sai da na makara domin sai bayan da Yallaɓai ya dawo sallar asuba sannan ya tashe ni a cewarsa ya ɗauka na tashi ne. Da safen ne bayan Gimbiya ta fito mun gaisa sai take ce min wai Yallaɓai ya ce na ce ya riƙa kwana a wajenta har ta koma na ce haka ne, sai ta kalle ni kafin ta ce

" Ba komai ai na ji sauƙi wallahi."

"Duk da haka dai gwara ya na kusa da ke."

Ina kallonta ta na ta mirmishi amma ba ta ce komai ba a raina na ce munafukai to daga ita har shi ɗin suna ji da munafuci da gulma. Ranar an yi baki daga Rano, Yayarta Mardiya da wasu ƙannen Hajiyar Tafida suka zo duba ta, ni na yi musu girki suna ta min godiya Yayar tata har ɗaki ta same ni ta yi min godiya a kan yadda na ke kula da Gimbiya na ce bakomai ai an zama ɗaya sai La'asar suka bar nan zuwa gidan Nene. Ranar asabar kuma Anty Maimuna ce ta zo da yaran ta nan suka yini a ɗakin Gimbiya ni dai iyakata na girki na ba su shi ne aiki na sun ƙule a cikin ɗaki ana hira ana shewa saboda can da Yamma ma Anty Bahijja ta zo gidan. Ranar lahadi ma an yi baƙi ƙawayen Gimbiyar su biyu sun zo duba ta suna ta min taɓe taben fuska ni kuma ban ba su fuskar da za su rena ni ba ni da gidan mijina ba matar da ta isa. Suma ciki suka bi ta ranar ma Dambu na yi kuma sun ci sai la'asar suka tafi a daran ranar aka kawo min hijabai na Amina ma mun yi waya a ranar aka tura mata na ta.

Washegari litini kuma ina da komawa asibiti kuma magunguna sun kare shi ya sa na shirya na ce ma Yallaɓai zan koma asibiti amsar da ya ba ni lokacin ta ƙara sakani mamakinsa.

"To dole sai kin koma yau ɗin ne?

"E zan koma saboda magunguna sun ƙare gabaɗaya."

Sai na ga ya yi jim bai ce komai ba sai na gyara tsayuwa ina faɗin" Me ya faru? Lokacin ma wanka na ke shirin shiga shi kuma ya na zaune a saman gado ya na aiki a system ɗin shi.

"Ina tunanin in kika tafi wa zai zauna da Daugther?

Sai na buɗe ido ina kallon shi, daman ai a rina an saci zanin mahaukaciya. Kamar ya ɗauke ni aiki na kula masa da mata har da cewa ya na tunanin in na fita wa zai zauna da ita? Kamar wata jaririya mata ta ji sauƙi in ta yi baƙi ta na dariya da shewa in a waya ne haka zan ji ta na ta rera hira rai rei amma ya na faɗa min in na tafi wa zai zauna da ita.

"Ko za ki ɗaga tafiyar ne zuwa Next week?

Kallon shi na yi irin kallon ba ka da adalci, wato na fasa zuwa asibiti na zauna a gida saboda matarsa da na ciki. Kawai sai na juya na hau tuɓe kaya ƙala ban ce ba, shima bai yi mgana ba na jawo towel ɗina na saka na fice na bar masa ɗakin, ina wanka ina jin takaicin Yallaɓai. Gaskiya wasu mazan ba su da adalci, haka kurum na fa sa zuwa ganin likita saboda matarsa? Duk mutumcin da na yi masa baya gani. To lalle ko yau zai sha mamakina daman da safen nan bayan ya dawo kai yara makaranta Salisu ya yi tafiya shi ne ya shigo ɗaki na ya zauna da na yi magana sai ya ce wai ta kwanta barci ne ba ya so ya dame ta, ni kuma tun da likita bai ba ni hutu ba sai ya zo ni ya dame ni shi ya sa na haɗe raina ban sakin masa fuska ba sai da na yi masa mganar zuwa asibiti shi ne zai tare ni da mganar banza.

Ko da na fito wanka baya ɗakin na yi tsaki a raina na ce shirme kawai. Agurguje na shirya na saka hijabina sabo dogo har ƙasa, na ɗauki jakata a hannu da takalmina ina fiowa sai ga shi ya fito daga ɗakin Gimbiya sai muka haɗe.

"Sai ina kuma?

Ya faɗa ya na kallona nima ko ina kallon shi na ce" In da na ce maka zan je" "Asibitin? Sai na ɗaga masa kai, na duƙa ina saka takalmi kafata na saka safa gajera na zamani na mata.

"Ba ki fasa ba kenan?

"Na faɗa maka magunguna na sun ƙare ya kamata na je."

Bai ce komai ba, nima ban ƙara mgana ba, na raɓa ta gefen shi na shiga ɗakin Gimbiyar sai na ganta zaune a gefen gado ta na duba wayarta alamu dai ta ɗan jima da tashi. Gaisawa muka yi ina tambayanta jikin ta, ta ce min ta warke ba ta jin komai.

"Allah ya sauwaƙe."

"Amin Anguwa za ki je ne?

"E asibiti zan je."

"Ba ki da lafiya ne?

Ta faɗa ta na kallona sai na yi mirmishi kafin na ce" A'a kawai dai zan je ganin likita ne." "Allah ya dawo dake lafiya." Na amsa mata da Amin. Kafin na ce" Akwai ragowan shinkar jiya na ɗumama miki sai ruwan zafi in za ki sha ruwan lipto" Sai ta amsa min da to shike nan.

"Za dai ki iya zama ke kaɗai ba matsala ko?

"Ba matsala na fa ji sauƙi Madam yadda na ke jin kaina ko aiki ma zan iya yi."

Sai na yi ƴar dariya kafin na ce" Ai haka muke so. Amma aikin nan ba yanzu ba sai kin fita daga dokar likita."

"To na gaji da zama waje ɗaya.'

"Lokaci ne. Kar ki damu. Sai na dawo."

Ta rako ni har falo sai na ga Yallaɓai zaune ya na kallo dining na nuna mishi ina faɗin" Ga abin karyawan ka nan" "Wa zai zauna da ita? Tambayar da ya ƙara jefa min kenan ni ko kai tsaye na ce. "Ba ga ka fa? Me ka ke yi? Sai ya sake kallona kafin ya yi magana na ce" Sai ka zauna da ita har na dawo tun da kana tsoron kar wani abu ya faru ko?

Kunya ya ji ko nauyi ban sanin masa ba. Bai yi dai mgana ba sai ita ce ta kare mganar da cewa ita fa bakomai za ta iya zama ita kaɗai. Ni dai na wuce na bar su nan har ya na wani mikewa wai bari ya zo ya kai ni, na ko daba masa mgana ina cewa" A'a ka zauna kar ka barta ita kaɗai." Sai ya yi shuru ya kasa mgana na fita haraba shi ne ya biyo ni ya ba ni 5k da cewa in an rubuta mangaguna, na kira shi a waya sai ya yi min transfer. Da a raina na saka da wuri zan dawo gida amma tun da Yallaɓai ya ne mi raina min wayau na ce sai ya ganni shi ya zauna mana ai shi ya yi cikin ɗan renin wayau kawai.

Na samu ganin Dr. Aisha da na ce mata maganina ya ƙare sai ta ce ba matsala. Ta tambayeni al'adata ya daidai ta ko har yanzu ya na min tsallake? Sai na ce gaskiya wattani biyu kenan normal sai ciwo mara amma wannan watan ya zo min da sauƙi.

"Zan sake rubuta miki mgani guda ɗaya shima dai na dai daita jinin al'adan ne kamar wan can"

Sai na amsa ta mata da to. Abin da ke zuciyata na faɗa mata.

"Dr kina ganin zan sake haihuwa?

Ba ta kalleni ba ta na rubutu a saman takarda lokaci ɗaya ta na faɗin" In sha Allahu"

"Dr ni ko ɗaya ne na ƙara."

Na faɗa cikin rauni sai da ta ba ni takardan da ta rubutamin mganin sannan ta ce" Me ya sa kike son ki ƙara haihuwa? Ba kina da wasu ƴa'ƴan ba.?

"Ina da shi Dr amma dai ina so na ƙara ne saboda mijina mai son yara ne."

"Ko dai kina da kishiyoyi ne ana rigiman magaji?

Ta faɗa da sigan zolaya sai kawai na yi mirmishi kafin na ce" Ko ɗaya. Ai shi ya na da wata matar ciki ma gare ta kila ta haifa masa namijin. Ni kawai ina son na sake haihuwan ne Dr namiji ko mace duka ina so."

" Zai ba ki in sha Allahu fiye ma da ɗayan. Ai na faɗa miki ba ki da wata matsalan da zai hana ki haihuwa. Lokaci ne kawai."

Nima na yarda da lokaci ne, kuma lokacin ne bai yi ba, in ya yi zan ƙara haihuwa nima.

Na tsaya a phamarcy cikin asibitin na siya maganin kuma sai da na kira Yallaɓai ya turamin Kuɗi duk da guda ɗaya ne, ni fa na saka a raina duk wani abu na haƙkin Yallaɓai na daina masa kara a kan shi in biyar ne sai na kira shi ya tura, sai da na hau adaidaita sannan na kira shi na ce zan biya gidan Ya Aina sai da ya yi jim kafin ya ce sai na dawo na san ya na so ya ce min na dawo da wuri ne ba fuska, na kusa gidan Ya Aina sai na ga ya turo min saƙo.

"Ni fa na fita, Daughter ita kaɗai ce a gida. Don Allah ki koma gida da wuri."

"Ba zan koma ba."

Na faɗa a fili saboda haushi har mai adaidaitan sai da ya juya ya na kallona tsaki na ja na maida wayata jaka, a bakin titi na sauka na taka zuwa gidan Ya Aina sai dai ta ganni kwatsam ko da na je Marwa ba ta nan tana asibiti mun sha hira duk dai akan Marwa da Kawu Abba Ya Aina na faɗa min cewa ba matsala Marwa dai na so ya kuma kawo mata waya faskekeya ban ga dai wayar ba amma na ga kwalin wayar. Zuwan shi biyu kuma da alamu dai sun fara dai daita kan su da Marwa.

"Ma sha Allah na ji daɗin haka."

Na faɗa ina jin daɗi har cikin zuciyata.

"Ai ya ce ba ya so a ja lokaci suna gama fahintar juna zai turo manyan shi."

"Haka ake so. Allah ya nuna mana "

Ta amsa da Amin mun cigaba da hira a cikin hiran ne ta ke faɗa min Murja fa ta sani. Cikin mamaki na ce" Ke kika faɗa mata? Sai ta ce e, ranar ta zo gidan ta iske Kawu ya zo kuma ranar ya kawo ma Marwa shi ne da ta tambaya ta faɗa mata.

"Murja har ta na jin haushina wai Marwa ta samu miji ban faɗa musu ba, ni dai na yi ta ba ta haƙuri "

Cikin mamaki na ce" Ikon Allah. Kamar an saka ranar ne ba su sani ba? Ya Aina ta ce ai na san halin Murja ni fa a raina na ji ban so Ya Murja ta sani ba, sai ta kai mganar gaba kuma shi ya ce sai sun dai daita ne manya za su sani ko Nene Yallaɓai ya ce bai faɗa mata ba saboda Kawun ne ya ce su dakata tukunna ban dai nuna ma Ya Aina wani abu ba ban jira dawowar Marwa ba na tafi gida wajen uku na rana saboda yara ba kuma saboda Matar Yallaɓai ba, ina hanyar komawa gida Yallaɓai na ta kiran wayata na ƙi dagawa sai da na koma Gimbiya ke ce min Ya na ta kiranta ya na tambayar ta ko na dawo sai na ce zan kira shi, na gane daman gidan ya ke so na koma shi ya sa da matarsa ta faɗa masa na dawo bai ƙara nema ba.

Saboda haushin shi da na ke ji da wuri na kwanta na ce kaina na ciwo, na bar shi da yara da matarsa ko da ya dawo ina ciki kwance ya dai shigo ya duba ni.

"Kin sha mgani?

Na ce masa na sha ya na wani taɓa goshina da wuyana ni ko burgeni bai yi ba na ce masa barci na ke so na yi, na san in na tashi kaina zai daina sara min sai ya fice ya na mai rufomin ƙofa na raka shi da harara, ko washegari a dakune na tashi daga shi matar tashi na riƙa yi musu yatsina ai shima sai ya sha jinin jikinsa ya san halina da na fara haka to ya san an ɓata min rai ne sai ya kiyaye ne da wata mgana sai da ni da kaina na ba ma kaina haƙuri na sauko gabaɗaya.

****

Readers Also Read