Kenza eBookz

Turken gida book 2 cmplete by janafty - Chapter 32

Turken gida book 2 cmplete by janafty - Chapter 32

Turken gida book 2 cmplete by janafty Chapter 32: Turken gida book 2 cmplete by janafty Chapter 32. Kimanin satin Gimbiya uku a tare damu. Ta warke garas…

3,283 words

Kimanin satin Gimbiya uku a tare damu. Ta warke garas ba wata matsala muna kuma zaune lafiya ba abin da ya taɓa faruwa tsakanimmu amma fa ina ganin bariki domin tun da ta ji sauƙi ta fara shan gayu ana ma miji kwalliya da karairaya, da daddare kuma su shige ciki suna shagalinsu ni kuma ina nan ina musu wahala, duk ina gani fa amma na nuna ban gani ba, ni abin da ya ke ba ni mamaki shi ne Yallaɓai har zai iya tsawon sati biyu bai neme ni ba amma kuma bai damu ba, ni fa a da na ɗauka Yallabai ba zai iya kwana biyu ba ni ba sai ga shi ya wuce tunanina ko a jikinsa. An ce ciki ya samu rauni bedrest ta ke yi amma suna ɓarnan ruwa ni na sani kuma suna sun sam ni ba yarinya ba ce ba su isa su yi min wayau ba. Na faɗa ma zuciyata Yallaɓai ma ya daina ba ni mamaki, domin ko ajikinsa ya na cin amarcin sa, tun da ga boyi boyi sun samu a gida na dai lallashi kaina tun da sati biyar ne in ya cika ta koma gidan ta, ban ji ba kuma ban gani ba saboda haka can su ƙarata.

Yau ta kama laraba ne, Gimbiya da Yallaɓai sun je asibiti bayan sun dawo ya kawo ta gida shi ya fita muna falo muna hira ta tashi ta shiga ciki shigan ta ba dafewa sai na ji ana buga get ina zuwa na buɗe sai na ga Inna Mariya ce ban yi mamakin ganin ta ba saboda daman shekaranjiya mun yi waya za ta aiko min da wani mganin gargajiya na sanyi wanda ke wanko mahaifa. Aneesa ɗiyarta ta yi aure shekaru bakwai ba haihuwa shi ta karɓo mata ta yi amfani da shi ga shi yanzu ta haihu shi ne da na ji na ce ina so. Mun yi waya za ta karɓo min amma ban ɗauka za ta zo da kanta ta kawo min ba.

Muka shigo cikin gida tare ina mata sannu da zuwa na kawo mata ruwa da lemo. Lokacin sha biyu ta gota anan falon yara muka zauna ta fito min da mgamin ta na nuna min. Akwai wanda zan sha da koko akwai kuma na ruwa har da na cin a abinci. Ta ɗauko ƙullin mganin ta na nuna min ta na kuma faɗa min magungunar arraɓi ne a ciki haɗe haɗen ganyeyyeki, shi zan rika sha a koko ta ɗauko ɗayan ta na faɗin.

"Wannan kuma a ruwa za ki saka. Ina mai tabbatar miki in sha Allahu za a da ce."

Ni ban san Gimbiya ta fito ba, da ya ke muna falon yara ne ashe ta daɗe a tsaye ta na kallon mu sai Inna Mariya ce ta ganta sai ta yi min mgana a hankali ta na cewa bakuwa na yi? Sai na juya na ga Gimbiya ganin na ganta ya sa ta ƙariso abin da ya ba ni mamaki ganin ta na ta kallon magunguna da Inna Mariya ta kawo min ni kuma har ga Allah ban kawo komai ba sai na gabatar musu da juna.

"Inna ta ce ƙanwar Mama. "

Na faɗa ina kallon Gimbiya nan da nan ta rankwafa ta na gaishe ta.

"Abokiyar zama na ne, ba ta jin daɗi ne sai ta zo ta na zaune damu na wani lokaci."

Na faɗa ma Inna Mariya itama cikin fara'a ta amsa mata gaisuwa ta yi mata ya jiki.

"Bari na shiga ciki tunda kin yi da baƙuwa"

Sai na amsa mata sai bayan wucewarta ne Inna Mariya ta ce min" Ke Sadiya na ga ta na ta mana wani kallo ne? "Ba ta da wata matsala Inna" Sai ta jinjina kai kafin ta ce Allah ya sa ba ta wani daɗe ba na yi na yi ma ta tsaya ta yi sallar azahar ta ce min daga wajen karɓo min mganin ta wuto gidana ba za ta zauna ba, har haraba na rakata na ba ta kuɗin mota da kuɗin mganin da ta karɓo min ta ce 5k ne gabaɗaya mun yi sallama na dawo cikin gida na tattara mganin nawa na kai kabinet ɗin kitchen na ajiye na daga nan tiolet na shiga zan kama ruwa sai na ga jini yanzo min yanzu in zan yi al'ada ko ciwon mara ba na ji sai dai na gan shi cikin salama ba kamar baya ba, da sai ya yi watanni bai zo ba kuma bayan ya zo ya yi ta min wasa.

Kawai sai na wanke fuskata na fito. Ban san abin da ya faru ranar Gimbiya ba ta sakar min fuska ba da na ma shiga duba ta a daƙile ta amsa min tun da na ga haka na kama kaina. Abinci ma da na shiga na ce ko na zubo mata ne sai cewa ta yi ta ƙoshi. Ni dai na ga ban yi mata wani abu ba amma duk da haka na yi mata uziri saboda ta na da ciki daman a san yanayin masu ciki sai a hankali shi ya sa ban saka komai a cikin raina ba. Na cigaba da harkan gaba na.

Kwana biyu tsakani ranar asabar kenan Jidda ce kaɗai ta je tahfez Baby na gida ba ta jin daɗi. Awara na saka aka yo mana daga gidan su Saude to ba a kawo mana ba sai na tambayi Gimbiya me za ta ci na dafa mata? Sai ta ce fanten wake haka na miƙe na dafa mata fentan waken nan na zuba na kai mata, Saude ma na gidan ta kawo min awarar ni da Baby tun ya na ɗanyen shi na mu ke ci na fara suyan kenan sai na ji ƙara daga ɗakin Gimbiya kamar ta na kiran sunana, saboda sauri har ina wurgar da ludayin hannuna mai ya na zubar min a kafa amma ban ji zafi ba ni da Saude da Baby muka iske Gimbiya a jigace a bakin tiolet ta na ce min maranta na ciwo sannan kuma ta ga jini hankalina ya tashi na koma ɗaki da gudu na kira Yallaɓai a waya bai ɗauka ba sai kawai na ce Saude ta fita ta taro mana adaidaita mu je asibiti.

Ni na taimaka mata ta saka Hijabi da takalmi ni Baby ce ma ta rarumomin hijabin Jidda na saka kafata da silaf ɗin tsakar gida, muka tafi asibiti Saude ta rufe mana gidan gabaɗaya muka tafi asibitin da ta kwanta da farko na kaita ina zuwa aka amsheta suka shiga da ita saboda ruɗewa ban ɗauko waya ta ba sannan ban ɗauko kuɗi ba sai da na fita haraban asibitin na ari wayar wata Nurse na saka lambar Yallaɓai na kira shi sai lokacin ya ɗauka hankalina tashe na faɗa masa ga halin da ake ciki ya ce muna wani asibti ne na faɗa masa ya ce ga shi nan zuwa.

Shi ya fara zuwa kuma har lokacin likitoci ba su ce komai ba, shi ya kira Anty Bahijja ya faɗa mata ita kuma ta yaɗa ma Dangi Yadda Yallaɓai ya ga na ɗaga hankalina sai na bashi tausayina shi ya koma ya na lallashina da cewa ba abin da zai faru, a gigice Anty Bahijja ta zo asibitin kuma ta na nan aka kira Yallaɓai ofishin likita sai ta bishi ni ban san me ya faru a ciki ba ta dai fito ta na ta faɗan mganganu.

"Ni fa shi ya sa tun farko ban so Gimbiya ta je gidan Sadiya ta zauna ba. Saboda ba kamar gida wajen Nene ba. Yanzu to ga shi nan an ce ta ci wani abu da cikinta ba ya so ta kusa yin ɓarin cikin jikinta."

"Duk fa ba wata matsala ba ce. Tunda dai cikin na lafiya itama tana lafiya ai shikenan ko?

Amma ba ta bar mganar ba, an kira ta a waya ta ɗauka ta na surutu ni dai na yi zaune shuru kawai ban yi mgana ba.

"Sadiya me kika ba ma Gimbiya ta ci ya kusa saka ta ɓarin cikin ta?

Tambayar ta zo min a ba za ta na ma kasa mgana, sai kawai na kalleta ma juya ina kallon Yallaɓai cikin rawan baki na ce" Ni ko me zan ba ta? Awara na saka aka yi mana yau shi ne ita Gimbiyar ta ce na dafa mata fenten wake kuma ai na saba dafa mata ta ci kuma ba a taɓa samun matsala ba."

"Uhm Allah ya iya faten waken ne?

Sai na ji raina ya ɓaci a fusace na miƙe ina faɗin" Me kike nufi da mganar ki? Ta ta so ta yi min mgana Yallabai ya tare ta da cewa" Don Allah Bahijja ki bar wannan mganar. Yau Daugther ke zaune da Sadiya? Kuma duk a baya komai bai faru ba sai yau? Za ta yi mgana ya sake tare da cewa ba ya son wata mgana kuma kar ya ƙara jin ta ƙara min wata tambaya ganin ya harzuƙa sai ta yi shuru ni kuma na koma na zauna ina tunanin manufar Anty Bahijja ko ta na zargina da ni ce na ba ta wani abu ta ci da ya sa ta shiga wannan halin? Lalle ne ma matar nan, ganin Yallaɓai ya tare mgamar ya sa nima na yi shuru, sai Allah ya sa ma Gimbiya ta farka lafiya cikin ma bai fita ba amma dai likita ya ce ya na cikin risk sai an kiyaye.

Yallaɓai ya maida ni gida ni da Baby da Saude saboda su Anty Maimuna duk sun zo, har a cikin zuciyata na yi murna da ba abin da ya faru. Da wani abu ya faru ai da na shiga uku ashe na gudu ban tsira ba ne, kwanan Gimbiya uku a asibiti aka sallameta nan ta ke aka wuce da ita wajen Nene. Ban yi magana ba amma a raina na ce gwara haka can ɗin in wani abu ya faru sai su ce uwar su ce sila. Ni dai na ga tun ana gobe za a sallami Gimbiya da na je asibitin duk ba wacce ta yi min wata mgana amma na ga suna yi mini wani kallo har da Halima da ita kanta Gimbiyar ta sauya min sai ban kawo komai a raina ba shi ya sa ana sallamota na shirya washegari da safe na je Gwammaja daman mun yi da su Hauwa suma za su je duba ta sai na ce kawai mu haɗu a can. Musamman na yi dambun shinkafa da zogale sanin Nene na so ya sa na diɓa na tafin mata da shi na je Ɗakin Nene cike da su Anty Bahijja kaf da ƴaƴanta Anty Maimuna Halima, Su Suwaiba ina gidan Hauwa ta ƙariso daman na iske Munnira.

Na shiga har ɗaki na gaida Nene na kuma kai mata Dambun da na zo da shi, ta karɓa ta yi godiya Bayan na fito na shiga ɗakin da Gimbiya ke ciki, su Anty Bahijja na ciki da na yi sallama ba wacce ta amsa har ita Gimbiya sannan suna ganina suka yi shuru. Na gaishe su suka amsa min a daƙile, Gimbiya ina cewa ya jiki ko kallona ba ta yi ba a laɓanta ta amsa da.

"Da sauƙi."

"Allah ya ƙara lafiya."

"Amin."

Ta faɗa kamar ba ta so, sai jikina ya yi sanyi wulaƙanci ƙiri ƙiri suka yi min a ciki sai na fito na koma falo wajen su Hauwa ina ƙirkiran mirmishi ban nuna musu ma wani abu ya faru ba. muna zaune Anty Bahijja ta zo ta wuce ɗakin Nene ba jimawa sai ga shi ta fito da kulan Dambun da na kawo ma Nene muna ji Nene na ƙwala mata kira har sai da ta fito da kanta.

"Bahijja magana fa na ke yi miki."

"Nene ba za ki ci dambun nan ba fa Kawai ke ma ta saka miki mgani ta kashe mana ke kamar yadda ta so kashe abin da ke cikin Gimbiya. Tun da daman ita ɗin dangin asiri ne an saba shige shige."

"Bahijja ba na ce ki bar mganar nan ba ne?

Har ta na wani jijiyan wuya wajen faɗin" Nene to sai a ƙyaleta bayan kowa ya san gaskiya? Ta faɗa ta na hararana ni fa da farko ban ma gane in da ta dosa ba ne sai da na ga ta na kallona sannan na fara dawo da abin da ya faru tun shigowata gidan nan, ban san lokacin da na miƙe ba haka ma su Hauwa saboda sai yanzu na gane in da Anty Bahijja ta dosa.

"Ban ga ne ba? A kan wa kike mgana?

Na faɗa ina kallonta sai kawai a gabana ta ɗaga kulan dambun ta sake shi ta a ƙasa murfin ya buɗe dambun ya Zube ƙasa idanuwana har sun ƙanƙance saboda ɓacin rai.

"Me kenan kika yi?

"Abin da idanuwanki suka gane miki."

Ta faɗa ta na kallona ai sai na ƙarisa gabanta Hauwa na riƙe min hannu na fizge ita kuma Munnira na faɗin"Subhanallah zubar da abinci me ya yi zafi Anty Bahijja? Sai gabaɗaya har su Gimbiyar suka fffito Nene kuma faɗi ta ke yi" Sadiya ƙyaleta kin ji."

"Ke dai za ki faɗa min abin da kike nufi da zubar da abinci da na kawo. Sannan da mganganun da kike a kaina?waye zai kashe muku uwa? Sannan waye ya so kashe abin da ke cikin gimbiya? Sannan waye dangin asiri? Kar dai ki ce da ni ki ke ?

Na faɗa ina kallonta domin har duhu duhu na fara gani, ni za a yi ma tijara a bainar na si, ni za a ƙulla ma sheri a ci mutumcina da mutumcin dangina

"Na ce ina fatan ba da ni kike ba ko?

"Da ke ake ko kina da mgana ne?

Sai kawai na ƙura mata ido ina kallonta.

"Kika ce da ni kike? Ni ce mai yin asirin?

"Ke ce mana. Kin so zubar da cikin Gimbiya Allah ya fiki. Ai duk mun san komai. Mun san cewa Yayar mamanki asiri ta yi ma abokiyar zamanta kaikayi ya koma kan masheƙiya ta mutu cikin hauka, kowa ya san wannan labarin saboda asirinta ya tonu."

Mamaki ya hana ni mgana, idanuwana sun kawo ruwa cikin rawam murya na ce" A ina kika ji wannan labarin?

"A bakin da ba zai yi min ƙarya ba. Ma'u ce ta faɗa min ko za ta yi miki ƙarya ne?

"Ma'u."

Na maaimata sunan a saman laɓɓana. Na kasa ma yin wani motai bakina na rawa na kasa mgana jikina ba in da baya rawa zuciyata ina jin kamar za ta faso ƙirjina ta fito saboda halin da na ke ciki.

"Ma'u fa?

Ma'u ƴar uwata da muka taso tare ita ce za ta zo dangin mijina ta yi min ƙazafi. Daman na san wannan bini binin na ta ba na lafiya ba ne. Sai ta ga na tozarta sannan hankalinta zai kwanta. Lalle ko akwai yaƙin duniya na uku tsakanina da Ma'u da duk wanda ke da hannu wajen yi min wannan mummunan ƙazafin.

*Janafty* *TKG017*

"Bahijja kina mata wani sanyi sanyi ke Sadiya har mganin asirin suke kawo miki har gida. Gimbiya ta gan ki lokacin da ƙanwar mamanki ta kawo miki su har gida ko shima za ki ƙarya ta ne?

Kalaman Anty Maimuna suka buga min kai kamar an dake ni da ƙarfe sai da na ji kaina ya yi dum na ɗago ina kallonta ba bakina ba har idanuwana suna rawa ne a lokacin.

"Haba Anty Maimuna me ya sa haka?

Hauwa ta faɗa kamar ta yi kuka Munnira kuma sai ta hau tafa hannu ta na faɗin" Yanzu me Sadiya ta yi muku da za ku yi mata wannan mummunan ƙazafin?

Ni kuma Gimbiya na ke kallo cikin mamakinta ina so na tabbatar da gaske ita ce ta faɗi ta ga ƙanwar Mamana ta kawo min asiri? sai na ga ta kauda kaita alamun kenan da gaske ne. Sai kawai na ji na fara jijjiga ni kaɗai saboda ɓacin rai ranar da Inna Mariya ta zo kawo min mganin na dawo min a cikin idanuwa. Oh shi ya sa daman ta ce min ta ga ta na ta kallon mu? Kenan zargin ta kawo min asiri ta ke yi min tun da gashi har ta kawo labarin gaba. Kuma tunda ina shige shige kuma ina baƙin ciki da cikin da ke jikinta tun da ni ban taɓa haihuwa ba shi ya sa na ba ta mgani ta ci a abinci cikinta ya zube sai Allah ya fini asirina ya tonu cikin bai zube ba. Shi ne aka zauna aka tattauna gwara a turke ni a ci min mutumci, duk a lokaci ɗaya na gama hango abin da ya faru shi ya sa ban san na yi wata dariya ba sai da na ga ina yin ta cikin mamaki suke kallona Anty Bahijja na nuna da yatsa na ina faɗin.

"Ba a haifi wani ɗa namijin da zan kauce ma Allah saboda shi ba Bahijja"

"Kuma kika kaucen?

"Tunda kin yarda na kauce kuma na yi asirin tun da kin ce ni yar na gada ce, sannan ma ai an ce an ga tabbaci me kike jira Bahijja? Na kira sunanta cikin tsawa kafin ta samu zarafin magana na zare mayafin jikina na ɗaure a kuguna ina faɗin

"Na ce tunda kin samu tabbaci me kike jira? Ba sai ki ɗau mataki ba Bahijja?

Na faɗa ina nuna ta da yatsa, Itama ta so min tana faɗin zan ko ga matakin da za ta ɗauka Hauwa da Munnira na rike ni ina fizgewa, ita ma Bahijja su Maimuna na riƙe ta Nene ma ta mgana ba wanda ya ji ta, Hayaniya ya sa har su Hajiya Iya da Maman farko sai da suka shigo lokacin Anty Bahijja na faɗin zan ga abin da zai faru.

"Ba abin da zan gani sai alheri me zan gani? Ya wuce ki saka ƙanin ki ya sake ni? To sai me? Kaina farau zawarci ke in ba ki saka shi ya yi min saki uku ba tabbas ke Bahijja ba ki haufu cikin uwarki da uban ki ba."

"Ke Sadiya ki yi shuru"

In ji Maman farko Suwaiba na ja na ita da su Hauwa ta na faɗin" Sadiya mu je mu je Sadiya."

"Ni kike zagi don uban ki Sadiya. Ni sa'ar ki ce?

"An zage ki ɗin ke uwata ce da ba za ki zagu ba? Har ni za ki yi ma kazafi na so zubar da ciki? To ni na zubar da cikin gimbiya na ci riban me? Ko haihuwa ce ban taɓa yi ba da za ta zame min baƙuwa? Amma ba laifin ki ba ne, laifin wacce ta faɗa miki ne. Amma ina so ki sani da ke da wacce ta faɗa miki na rantse da wanda raina ke hannun shi sai na yi ƙaran ku a wajen hukuma."

Daƙyar su Suwaiba suka fita da ni daga ɗakin Nene tana zagina ina zaginta. Itama ana riƙe ta tana cewa a sake ta, ta doke ni "Na ce ku sake ta mana ta zo ta ga in zan bugun mata ko wanda na ke aure bai isa ya doke ba ballantana ke banza a banza."

Itama ana riƙe ta tana fizgewa faɗi ta ke yi wai ai ba ƙarya aka yi min ba. Ina shige shige na wanke gaba na ba ma Tafida ya sha da ba ya ganin laifina, na shanye musu ɗan'uwa ko auran shi ma da Gimbiya Allah ne ya fi ƙarfina shi ya sa aka yi auren.

Ni ko na ce ita mijinta da yan'uwansa da ta shanye su sai abin da ta ce itama kenan gaban na na ta ta wanke ta ba shi ya sha kenan.?

Readers Also Read