Kenza eBookz

Turken gida book 2 cmplete by janafty - Chapter 33

Turken gida book 2 cmplete by janafty - Chapter 33

Turken gida book 2 cmplete by janafty Chapter 33: Turken gida book 2 cmplete by janafty Chapter 33. Sai ta fara haƙilon faɗin" Ai mu kowa ya san zuru'ar mu…

3,362 words

Sai ta fara haƙilon faɗin" Ai mu kowa ya san zuru'ar mu ba mu da tambarin bin bokaye kuma ba a ji labarin wata cikin ahalin ta mutu cikin hauka ba." Har ta na cewa na yi shige shige na na haɗa Kawu Abba da ɗiyar yayata saboda shima a shanye shi sai yadda aka ga dama dashi to na rubuta na ijiye ko ta ce bokan mu ya yi ƙarya Abba ba zai auri dangin masu asiri ba har ta na faɗin me aurena ya tsinana ma Tafida? Ni kuma na ce in ba ta saka ya sake ni ba, to ba ta haifu ba.

"Kuma dangin asirin su Kawu Abba ya gani ya ce ya na so in Allah ya haɗa ki raba in kin isa "

"Mata kin bi kwazzaba ma rayuwata a gidan aurene? Me na tsare miki? Zaman ki na ke yi! Ke da kika miƙe kafa a gidan na ki mijin wa ya takura miki? Ko kema shige shigen kike yi? Ke ki ce kina son ki ji daɗi a gidan wani da zuru'an wani amma kuma ke ce wata ba za ta zo na ku zuru'an ta ji daɗi ba? Ashe haka kike da son kan ki? To wallahi kin kure ni akan matakin da ba zan ɗauka ba tun da kin fito ta haka to nima zan fito miki ta bangaren da kika fito min ni da ke shege ka fasa Bahijja"

"Sadiya ba ki da kunya? Bahijja ba yayar mijin ki ba ce?

Anty Maimuna ke tare ni da faɗin haka har ta na shan gaba na, idanuwana sun rufe yadda bacin rai ke sarrafa zuciyata a wajen ko mari na ta yi sai na rama.

"Au ni ce ma ba ni da kunya daga ƙarshe kenan!? Ke ba ki ji duk mganganun da ta ke faɗa min ba ne! Me na yi mata? Kamar ta na jira. Ai ita ba ta kama girmanta na yayar mijina ba. Shi ya sa nima na bi girman nata na tattaka ni da ita wallahi sai mun cire renin da ke tsakanin juna."

Nene hankalinta ya tashi ta yi ta yi Bahijja ta yi shuru ba ta yi ba sai ta Umarci Maman farko da ta ja ni zuwa ɗakin ta tun da ita ma Bahijjan ta ƙi sauraranta har da Halima a masu jan Anty Bahijja amma ta na wani zillo ai nima na haukace musu ta na zagina ina zaginta itama.

Suwaiba da Maman farko da su Hauwa suka yi ta ja na Dakyar suka shiga dani ɗakin Maman farko na zame musu kamar mai aljanu sai da suka haɗa da rufe ƙofa Maman farko fadi ta ke yi" Innalillahi Sadiya ki yi shuru mana."

"Ku kira Tafida mana."

"Bari na kira shi" Cewar Suwaiba ta na wucewa cikin uwar ɗaki."

"Ki yi hakuri Sadiya."

In ji Munnira ta na kuka ganin na zaune saman cafet ɗin tsakar ɗakin Hajiya iya na rushe da kuka kamar wata yarinya.

"Kazafin fa suka yi min? Sun ci mutumcina ni da zuru'ata?

"Ki yi haƙuri amma tabbas an ci zarafin ki."

In ji Maman farko Hauwa kuma faɗi ta ke yi" To daga ina wannan mganar ta fara fitowa?

"Ko da ga ina ne ko waye wallahi ba zan bar wannan mganar ba sai hukuma ta ƙwatomin haƙƙin ƙazafin da suka yi min."

Na faɗa ina jin ƙuna a ƙasan raina lokaci ya yi da zan tauna tsakuwa domin a ya ta ji tsoro. Ba Ma'u ba ko Baaba ce sai na yi kararta ba Bahijja ba ko Nene ce ta yi min wannan ƙazafin sai na ji dalilinta wallahi. Ina kuka zuciya ta na wani irin zafi ina ma jin turarin zafin daga maƙoshina. Duk alherin da na yi ma Gimbiya ni ce za ta saka ma da sharri. Lalle na yarda da maganar hausawa da suka ce mai kishiya ba ya mutuwar Allah. To an kawo gabar da komai zai ƙare, zan yi abin da hankalin kowa zai koma jikinsa.

Jikina ba in da ba ya rawa kawai hasko kaina na ke yi na kama Ma'u na yi mata shaƙan da sai ta kusa zuwa lahira. Kawai sai gani na na yi na mike Munnira da Hauwa da suke ta jajanta lamarin suka mike suma, ganin na nufi hanyar barin falon na Maman farko ya sa Munnira ta ce.

"Sadiya ina za ki je?

Maganarta ya dawo da hankalin Maman farko a kan mu saboda itama wayarta ce a hannu ta na dannawa kamar neman wani ta ke yi a wayar. Kuma daga ma nan dakin muna jiyo hargagin Anty Bahijja da zage zagen da ta ke yi.

"Ina kuma za ki je?

Suwaiba ta faɗa ta na fitowa daga ciki.

"Jakata zan ɗauko da mayafina "

Na faɗa muryata a shaƙe sai Maman farko ta ce ba zan fita ba Hauwa ta je ta ɗauko min,sai na yi shuru amma ban zauna ba ina tsaye ina karkaɗa jikina in ba sumar da Ma'u a yau ba, ina jin ba zan huce haushina ba kafin na haɗa da jami'an tsaro sai na bar mata taɓon da za ta kiyaye ni har gaban abada. Ko raba ɗayan biyu ba zan yi ba Ya Murja ta faɗa ma Ma'u maganar Marwa da Kawu ita kuma ta zo ta fesa ma uwarta ai kuma komai ya zo karshe daga yau zan kawo karshen makircinta a kaina.

Hauwa ta buɗe falon ta fita dai-dai lokacin da Maman farko ke faɗin" Kin samu Tafidan?

"E ya ce ga shi nan a kan hanya. Ya ma ce Halima ta kira shi ta faɗa masa ba ki ji yadda hankalin shi ya tashi ba na ce ya taho a hankali Sadiya ta na ɗakin ki mun rufe ta."

"Wayyo bawan Allah."

Maman farko ta faɗa cikin wani yanayi ni dai ina tsaye kiƙam na kasa zama. Sai ga Hauwa da Hajiya jiya sun shigo, jakata kawai Hauwa ta dauko min da sauri na karɓa wayata na ciki da kuɗi lokacin biyu na rana har ta gota daman sai da na yi azahar na fito daga gida.

"Sadiya ki yi hakuri. Kai wannan lamarin bai yi daɗi ba"

In ji Hajiya Iya, Mama ko faɗi ta ke yi" Ni Bahijjan ce ta ba ni mamaki ko gaya mata abu aka yi ta yarda ba ta da shaida? Suwaiba ta karɓe da faɗin" Ita ko ke da shaida ba ku ji suna faɗin Gimbiya ta ce ta ga ƙanwar Maman Sadiya ta kawon mata magani ba! Itama ai ta haɗa fitina ita da wacce ta tari Bahijja da mganar wani tarihin wata ta mutu da hauka."

"Ma'u ce tare suka tashi da Sadiya. Da babansu da ita mahaiyar Ma'u uban su ɗaya uwar su ɗaya'

Hauwa ta faɗa sannan ta kora musu jawabin ta in da suka haɗu da Anty Bahijja. Hajiya iya na salati Maman farko na yi, Suwaiba ta ce" Na gane ta wata yar fara haka. Amma ko ta yi asara wallahi." Hankalinsu ya ɗauke da hiran su ba su san na zari mayafin da na gani a saman kujeran hanyar fita ba, na buɗe kofa na fice ko takalmi babu a kafata sai wani da na gani a ƙofar ɗakin na saka. Karan rufe kofa ta suka ji sannan suka far ga ga na fita sai suka biyo ni da gudu suna kiran sunana sun ɗauka ɗakin Nene zan koma sai su ka ga na fara sauka daga Bene Suwaiba da su Hauwa suka biyo bayana suna kiran sunana amma kamar wata hajijiya haka na rika sauri kamar zan kifa a haraba na ci karo da Mimisco ta iso itama ina ga kiranta aka yi. Har ta na tsayawa ta ɗauka zan yi mata mgana ne sai ta ga na wuce ta fuu kamar zan kifa.

"Sadiya tsaya. Ki tsaya na ce Sadiya."

Ko sauraranta ban yi ba mayafi a saman kafaɗa ina rike da ƙaramar jakata na fice da sauri kamar zan faɗi. Ba san ni ba ko sun biyo ni ni dai ina fita na fara sauri ina haɗa hanya har da gudu gudu ina hango bakin titi kawai na ga Motar Yallaɓai ta sha wo kwanar, yadda na dumfari in da zuciyata ke son zuwa ko waye ya tsaida ni ba zan tsaya ba ko da Alhajin mu ne kuwa.

Ya wuce ni, ni ma na wuce shi da sauri sai ga shi ya na dawowa da baya da baya a motar ya na kiran sunana bayan ya sauke gilashi ko jin sa ban yi ba ganin ya tsaya da motar yasa na saka gudu ina zuwa bakin titi na saka hannu mai adaidaita na zuwa ba kowa a ciki ya tsaya na shiga ciki da sauri na ce.

"Mu je Rijiyar zaki. Ka yi gudu da ni sosai."

Haka na faɗa ina haki, sai na juya baya ina ganin Yallaɓai ya koma mota ya yi riverse kenan ni zai biyo ni kuma ina azalzal ma mai adaidata da cewa ya yi sauri kawai hango kaina na ke yi a gaban Ma'u yadda zan makure ta sai ta kusa mutuwa ji na ke yi kamar zan iya yin bindiga ni kaɗai tsabar halin da na ke ciki na bakin ciki da ɓacin rai, kafin na fara kai su ƙara sai na ci uban Ma'u saboda in hukuma ta shiga ciki da farko ba zan samu damar cin uban ta dakyau ba gwara na fara nuna mata ina nan a Sadiyar da ta sani ban sauya ba kuma wallahi ni da zumunci da Ma'u har abada. Bahijja da sauran masu ta ya ta a kaina Yallaɓai zai shiga tsakanina da su, da ita kanta matarsa munafuka mai maida alheri da alheri sai an tuhuman min ita a gidan uban wa ta ga Inna Mariya ta kawo min asiri? Wallahi ko sama da ƙasa ne za ta haɗe ba zan bar maganar nan ba. Wato maganin nan da Inna Mariya ta kawo min ranar shi ne ta ke magana akai kenan lalle kar ka raina mutum duk wannan abubuwan da suka faru Ma'u ce sila ita ta ba ma Anty Bahijja daman cin zarafina. Shin wai da aka je asibiti an ce ne magani Gimbiyar ta sha? Ba ɗaya fa kawai ta tsane ne shi ya sa ta ke neman hanyar ci min mutumci, ban da haka ai ta san Gimbiyar na ta matsalan raunin mahaifa ko acan Abuja ma ta yi ɓari kuma ni da bakin Anty Bahijja na ji lokacin rasuwar mijin Gimbiyar ta na faɗin ai an nema mata maganin gargajiya na matsalan ciwon maran da ta ke fama da shi ke sa ta yi ɓari in ta samu ciki, amma yanzu sun manta Ma'u ta zo ta ɓata ni su kuma daman kamar su na jira sun far min da cin mutumci to komai ya zo ƙarshe daga wannan ba za a ƙara ba.

Muna tafe duk irin gudun da mai adaidaitan nan ya ke yi ni ba na gani, ji na ke yi kamar na karɓi tuƙin ƙila na isa in da na ke so a kan lokaci domin ji na ke yi kamar na yi tsuntsuwa na ganni a gaban Ma'u. Sai faman kiran wayata da ke cikin jaka ake yi amma ban bi ta kai ba, alokacin ni kaina ban san a yanayin da na ke ciki ba amma zan iya cewa tun da uwata ta haife ni ban taɓa jin irin ɓacin ran da na ke ji a yanzu ba. Ban taɓa jin nauyin ƙirji da na zuciya irin na wannan ranar ba, ban taɓa tsintar kaina a yayin fusata da fushi mai tsanani irin na yau ba. Abu ɗaya ke ƙara tafasa min zuciya in na tuna yau duk cin mutumcin da Anty Bahijja ta yi min ba kowa ya ba ta dama ba sai Ma'u. Ma'u fa ƴar'uwata ce da za ta iya tsaya min da jikinta da aljihunta in ta ga wani zai cutar da ni wani ko zai ci zarafina, amma sai gashi yau ita da kanta ta ba da damar da aka taru aka ci zarafina a ka zagi dangin mahaifiyata da ta ke ƙasa ba ta san ma abin da ke faruwa ba.

Ban san ina hawaye ba sai da na ji ɗigan su a saman hannuwana. Ban san ina kuka ba sai da na ji zuciyata na wani irin zafi, zafin kuma sosai kamar sheɗata za ta ɗauke min sai da na fara numfashi sama sama saboda halin da na ke ciki. Ina tuna labarin da ta je ta ba ma Anty Bahijja wani tsohon labari ne da mu muna yara ƙanana ma aka yi, da girman mu labari muka ji daga baya. Yayar Mama Inna Mandiya Allah ya jiƙanta mijinta ya auro wata bafullatana an yi auren ba daɗewa ta fara rashin lafiya aka yi ta yawon mgani anan ne aka ce wai asiri aka yi mata. Daga nan magana ta shiga gari aka yi ta cewa Inna Mandiya ce ta yi mata asiri ta kwanta jinya. Ƙwatsam kuma sai ta rasu bayan kuma mutuwarta ba daɗewa itama Inna Mandiya ta fara rashin lafiya na aljanu a yadda Mama ta faɗa ma na ana tunanin Gamo ta yi shi ne da wannan rashin lafiyan ta koma ga Allah. Magana ta za ga gari cewa ƙaiƙayi ne ya koma kan masheƙewa sama da shekaru amma mutane ba su bar maganar ba, an daɗe ana kiran gidan su Mama da gidan yan asiri, daga baya da mutane suka ga ji suka daina ni kaina na manta da labarin abin da ya faru sama da shekaru ashirin amma da ya ke ita Ma'u munafuka ce ta na tune da labarin shi ne ta zaunar da Anty Bahijja ta faɗa mata domin ni ta tozarta ni.

Ban san ma na buɗe muryata ina kuka ba sai da mai Adaidaitan da na ke ciki ya juyo ya na faɗin" Hajiya lafiya? Na kalle shi amma na ƙasa mgana sai danne laɓena na ƙasa na ke yi kar na fashe da kuka tsabar yadda na ke ji na a rikice kamar na fita daga hayyacina. Wannan abin da aka yi min shi ne abu mafi munin da ya taɓa ɓata min rai tun aurena da Yusuf duk da an yi wasu a baya amma bai kai wanda ni za a tozarta ni sannan a yi min mummunan ƙazafi ba.

"Ko rasuwa aka yi miki Hajiya? Sai haƙuri Allah ya jiƙan musulmi."

Shi ya yi kiɗan shi ya yi rawan shi amma ni kallo bai ishe ni ba, ni kaɗai na san yanayin da na ke ciki. Ma'u daman suna farko farkon Rijiyar zaki ne gidanta na bakin titi da kin shiga layi kaɗan haka, gani na yi ma in na tsaya sai ya shiga dani zan ɓata lokaci ya sa na sauka a bakin titi na buɗe jakata na ɗauko masa 1k na bashi ya na mgana ban ji sa ba domin tuni na yi gaba. Hango kaina kawai na ke yi a gaban Ma'u na maƙureta ina dukanta ko zan ji kaɗan daga abin da ke taso min a ƙasan zuciyata ya ragu. Gudu gudu sauri sauri ina tafe a hanya na ga wani ƙaton dutse na ɗauka na riƙe a hannuna ina zuwa bakin get ɗin ban jira komai na saka dutsen nan na riƙa buga kofar da shi ina jin megadin gidan na tambayan waye na yi banza da shi, ya na buɗe get ɗin ta ƙaramar ƙofa bakin sa ya buɗe da shirin mgana na tura shi baya da ƙarfi na shigo gidan.

Da idanuwana na ke kallon haraban gidan Allah ya ba ni sa'a na hango Ma'u tsaye a jikin mota da shirinta tsab na fita ta dukar da kai ta na duba wayarta. Ban jira komai ba da sassarfa na fara takawa zuwa gare ta megadi ya biyo ni ya na faɗin" Baiwar Allah lafiya? Bai sanni ba domin rabo na da gidan Ma'u tun haihuwan Alhaji ƙarami..

Hayaniyar Megadi ya sa hankalin Ma'u ya dawo kan mu yadda ta ke kallona na san ta yi mamakin ganina ne. Na dumfare ta da sauri dai dai ina fuskarta ƙofar shiga falonta. A kuma lokacin mijinta Alhaji Mustapha ya fito ya na saɓa babban riga da alama tare za su fita da Ma'u. Kafin ya ƙariso ni na riga shi ƙarisawa gaban Ma'u na saki jakar hannuna da mayafina lokacin da bakin ta ke motsi na ji ta ambaci sunana.

"Sadiy.."

Ban bari ta ƙarisa ba, saboda lokacin da na ganta ga ta a gabana sai na ji ɓacin ran da na yi kafin na zo gidanta ya ninka sama da sau saba'in ba tare da jira ba kawai na ɗaga hannuna da karfi na kwashe ta da wani mahaukacin mari ta bangaren damanta wanda sai da ta gicjiya gefe cikin razana da firgici. Adai dai lokacin da mijinta ya ƙariso ya na faɗin.

"Sadiya ke ce ta fe? Ah Subhanallah."

Sai maganarsa ta ƙare da kiran sunan Allah ganin na yi sauke ma matarsa marin diɓan mahaukaciya. Ganin ya na ƙokarin karisowa ya sa ta na ɗagowa cikin mamaki dafe da kunci na ƙara dagewa na sauke mata wani marin a bangaren dama da sai da wayar hannunta ta suɓuce a ƙasa ta ba da sautin ƙara kafin kuma ta yi wani motsi na saka hannuwana duka biyu na ɗago kafaɗunta na yo gaba da ita sai kuma da karfi na mai da ta baya gam! Na buga kanta da jikin motan da ta ke tsaye a gefenta, na ƙara ɗagota na ƙara maida ta gam sannan na saka duka hannuwana na shaƙe mata wuya kamar zan kasheta idanuwanta sun firfito waje ta na rike hannuwana domin ceton ranta amma a lokacin ni ba na ji ba na gani burina kawai na yi ma Ma'u dukan mutuwan da gaba ko sunana aka ambata sai ta razana.

Alhaji Mustapha ya yo kaina cikin tashin hankali. "Ke ke Sadiya me ye haka? Ya ke faɗa ya na neman ɓambare hannayena daga wuyan Ma'u amma ina ya kasa domin sai na ji wani karfi na shiga ta, hankaɗe shi na yi gefe ya ta ga taga taga kamar zai faɗi. Sakin mata wuya na yi na jawo mayafin da ke jikinta na matse mata wuya da shi, na ƙara jawo ta ta dawo na sake maida ta ta ƙara buguwa da jikin mota gam! Ban tsaya ba na saka duka hannuwana dama da hauni na riƙa yarfa mata maruka kamar Allah ya aiko ni . Sai ga Alhaji Mustapha ya yo kaina shi da megadin shi suna neman raba ni da Ma'u.

"Ke mahaukaciya ce! Yar'uwan ki ce fa?

Ya faɗa lokacin da suka ƙwaci Ma'u daga hannuna ta na bayan shi duƙe ta na maida numfashi, Megadi na gefe ya na salati shi kuma Alhaji Mustpha ni ya ke kallo ganin yadda na ke huci kamar zakin da ya daɗe a dawa bai samu abinci ba.

"Me ya same ki? Me ta yi miki za ki zo har cikin gidan ta kina dukan ta? Kin san me kika yi?

Na yi tsaye ban yi masa mgana ba sai ya juya ya na duba Ma'u ya na yi mata sannu ya mikar da ita tsaye fuskarta ta yi ja da shatin hannayena idanuwanta sun yi ja sai kuka ni kuma ina kallonta ta na kuka ina ji a raina ba ta daku ba so na yi na yi mata dukan da ba za ta iya ma mgana ba.

"Sadiya me na yi miki!l? Ni ce fa Ma'u yar'uwan ki?

Sai na ji kamar ta jona min shoking a jikina a fusace na nuna ta da yatsa ina faɗin" Ke dai Ma'u ke dai Ma'u wallahi ke tsinanniya ce." Gabaɗayansu suka zuba min ido, ita ko sai ta fashe da kuka ta na nuna kanta.

"Ni kike kira da tsinanniya Sadiya?

"Kin wuce tsinanniya. Ke sheɗaniya ce."

"Ya ishe ka haka fa Sadiya ina ganin girman ki"

A fusace na ce" Ka daina gani daga yau. Ba ruwan ka a wannan mganar ka matsa gefe ba dai kai na ke yi ba."

"Matata ce Asma'u ba ki da hurumin da za ki zo gidana kina tsine mata"

Readers Also Read