Turken gida book 2 cmplete by janafty - Chapter 34
Turken gida book 2 cmplete by janafty Chapter 34: Turken gida book 2 cmplete by janafty Chapter 34. Sai na kalleta ta na ta kuka kamar mutuniyar ƙwarai…
3,374 words
Sai na kalleta ta na ta kuka kamar mutuniyar ƙwarai kafin na nuna da yatsa ina faɗin" Ma'u Allah ya tsine miki albarka munafuka mai fuska biyu."
"Yar'uwan ki ce fa kike tsine mawa?
Ya faɗa ya na mai daka min tsawa, ni ma a fusacen a tsawacen na ce" Ni ba yar'uwta ba ce domin na raba jinin da ke tsakanina da ita har abada. Domin abin da ta yi min jinina ba zai taɓa yi shi ba. Kuma ki sani wallahi sai hukuma ta shiga tsakanina da ke Ma'u."
Sai ya kasa mgana ya tsaya ya na kallona.
"Me ya faru?
"Ka tamnayi annamimiyar matar ka. Wacce ba ta ramin ta sai dai ramin wani."
Sai kawai ya fara lalubo waya daga cikin aljihun rigan shi lokaci ɗaya ya na faɗin" Ni dai ban san me ya faru ba amma ba ri na kira Injiniya." Megadi kuma megidan ya ce ya tafi abin shi amma ya daga can gefe ya na kallon abin da ke faruwa hankalin shi ya tafi ga kiran waya na shammace shi na ƙara yin kan Ma'u wannan karon ta so kare kanta sai muka fara ƙoƙowa amma duk da haka sai da cire mata ɗankwalin kanta na damƙi shegen gashinta mai kama da hammatan ɗan iska na fara ja sai ta fara ihu da gudu ya rugo ya shiga tsakaninmu burina kawai na bar ma Ma'u taɓon da duk lokacin da ta kalle shi sai na faɗo mata a rai shi ya sa na riƙa waige waige ina neman dutse ko sanda na rotsa mata kai dashi ta haka ne ya samu damar saka ta cikin mota ya rufe na ɗauko dutse da na gan shi a can gefen na rika bugun gilashin motar da shi, shi kuma ba ya son riƙe ni sai dai ya na ƙare wa kuma ya na kiran sunana da faɗin na shiga hankalina.
Ita kuma ta na cikin mota ta na kukan munafunci amma na ga lokacin da ta yi min wannan mirmishin nata ita a tunaninta ta yi nasara ne. Ƙarya ta ke yi ba ta yi nasara ba sai ma faɗuwa.
"Wallahi yau dubin ki ya cika Ma'u daga yau karshen ki ya zo domin sai na tabbatar da kowa ya san wacece ke. "
"Haƙuri koma me ya faru a zauna a tattauna?
Na kalle shi da jajayen idanuwana kafin na ce" Shari'a ce za ta shiga tsakanina da matarka." Ina mgana ya na kiran waya sai ji na yi ya na cewa injiniya ga matarka a gida ta zo ta na jan Asma'u da faɗa ban san me ya ce masa ba na ji dai ya ce sai ya zo, ni kuma na kasa na tsare na ce ko ya fito da Ma'u ko na fasa gilashin motar ni na fito da ita.
"Haba Sadiya ki natsu mana "
"Yadda ta haifar min da rashin natsuwa. Nima wallahi sai na haifar mata da fiye da abin da ta yi min."
Shi dai ya babbage bakin mota ya na ta ba ni haƙuri domin ya ga yadda na ke a rikice zan iya aikata duk abin da na ga dama. Ɗamara na ci da mayafin jikina ina girgiza kamar zan yi bi iska shi fa ya tsorata ya ɗauka ina da aljanu ne har Ma'u ma ta tsorata kuma ta bugu domin har fuskarta ta kumbura, da dai na tuna in Yallabai ya zo zai hana ni ƙarisawa ofishin yan sanda ya sa na karɓi jakata da Alhaji Mustpha ke miƙamin tun ɗazu ban karɓa ba. Sai da na karɓa sannan na ce.
"Mu haɗu a gaban hukuma."
Ya biyo ni ya na ce min injiniya na hanya na yi banza ds shi megadi tun kafin na ƙarisobya buɗe min kofa ina fita sai ga motar Yallaɓai na karisowa ina ganin shi sai na juya na nufi bangaren yamma shi kuma da sauri har da gudu ya fito ya taka ya na bina lokaci ɗaya ya na kiran sunana Allah ya sa layin ma ba jama'a da mun zama ƴan kallo.
"Sadiya."
"Sadiya magana fa na ke yi miki. Ki tsaya don Allah."
Ban saurare shi ba sai da ya yi gudu ya sha gaba na, na kauce masa zan wuce ya riƙo ni da ƙarfi ya na kiran sunana.
"Ka ba ni hanya na wuce ko?
Na faɗa ina masa wani kallo da jajayen idanuwana da ina da tabbacin yanayin da ya ganni ya daɗe bai ganni a cikin sa ba.
"Ina za ki je? Kin ga yadda kike kuwa?
Sai da ya faɗa na kalli kaina da ɗamara. Kamar wata yar dambe sai na warware mayafin na yafa a kaina amma Yallaɓai ya ƙi sakina.
"Ka sake ni na ce ko?
Na faɗa a fusace ina kuma ƙokarin kwace kaina amma riƙon Yallaɓai ba na wasa ba ne na kasa.
"In na sake ki ina za ki je?
"Offishin yan sanda."
Na bashi amsa ina huci kafin na cigaba da faɗin"Wallahi ba zan ƙyale duk wanda ya nemi ya tozartani ba. Sai hukuma ta bi min kadin kazafin da suka yi min ni da zuru'ata." Na karishe faɗa ina fashewa da kuka sai ya rike ni a jikinsa amma ina ta fizgewa ina faɗin ya sake ni domin ni ba zan bar wannan mganar ba.
"Na ji nima ai ban ce ki barta ba. Mu je ki shiga mota sai mu je police station ɗin tare da ke."
Sai na kalle shi sai ya gyaɗa min kai ya na ƙara rike duka hannuwana ya na jinjina min kai, ban san me ya sa na yarda da shi ba na bi shi zalau zalau har bakin mota ya buɗe ya sakani a ciki ya rufe sannan ya taka ya isa bakin get ɗin gidan Alhaji Mustapha bai shiga ba amma shi ya leƙo sun yi mgana ba daɗewa ya dawo ya buɗe mota ya shiga ya ta da ita ya yi riverse muka bar layin tun da muka fara tafiya na ke kuka kuma da karfi ina yi har da jiniya bai kuma hana ni kukan ba.
"Ni Ma'u za ta tozarta? Ni yayarka za ta kalli idanuwana ta ce dangin uwata dangin asiri ne?
"Ki yi hakuri"
Yallabai ya faɗa a marairaice, ga shi sai kiran wayarsa ake yi bai ɗauka ba.
"Yusuf lokacin da ka ce min matarka za ta zo ta zauna da mu me na faɗa maka? Ba sai da na ce ina tsoron wani abu kar ya faru daga baya ba! To yau ni matarka ta saka ma da sharri sakamakon alherin da na yi mata. Ita wai ta ce ta na gidan kanwar mamana ta kawo min asiri. Ita ce fa ta faɗi haka Yallaɓai"
Na ƙarishe faɗa ina kallon shi ina kuka har da majina.
"Ita Saudatun ne ta ce haka?
Ya tambaya cikin mamaki.
"Abin da ya fi min ciwo Anty Bahijja ta zubar da abincin da na kawo ma Nene ta ce ba zan kashe muku uwa kamar yadda na so na zubar ma da Gimbiya cikin jikinta? Yusuf a zama na da kai na taɓa kwatanta wani abu na cutarwa gareka ko yan'uwan ka?
"Ba ki taɓa ba Sadiya"
"Na taɓa zagin su! Na taba musu wani abu na rashin ɗa'a? Tsakaninmu sai girmamawa amma yau duk alherin zaman shekarun aurena da kai ya koma na sharri da ƙazafi?
"Ki daina kuka don Allah Sadiya raina na ƙara ɓaci."
Ya faɗa cikin wani yanayi ya na kuma gudu a mota sosai daga gani ran shi ya na ɓace ne.
"Yusuf yau fa Anty Bahijja ta ce min ba ta ga abin da aurena da kai ya tsinana maka ba. Ta ce wai na wanke gaba na baka ka sha na mallake ka, shi ya sa na shiga na fita zan liƙa ma Kawu Abba ɗiyar yayata saboda shima a maida shi shanyayye kamar ka."
"To ina ruwanta in kin shanye ni? Sannan uban wa ya faɗa musu labarin Kawu da Marwa."
In kuka na ce" Munafuka Ma'u ce, shi yasa na ce maka sai na haɗa su da hukuma"
"Ban ɗauka haka ta ke ba. Ma'u nan ta ba ni mamaki ".
Ya faɗa cikin bacin rai kafin ya cigaba da faɗin" Me ya sa na ki kirani da abin ya faru ba? Kin san dai ba zan zura idi a ci miki mutumci ba. Duk wanda ya ci miki mutumci to tamkar nawa mutumci ya ci." . Na kasa mgana sai kuka kawai na ke yi ina faɗin ya kai ni offishin yan sanda.
"Ki yi hakuri mu koma gida a zauna a yi mgana."
A fusace na ce" Ba zan zauna da kowa ba Yusuf hukuma ce za ta tuhume su."
"A'a."
"To ka sauke ni na tari adaidaita"
"Na ce a'a."
Ya faɗa a fusace cikin tsawa, kamar zai dake ni daga gani ran maza ya ɓaci.
"Babu wani hukuma. Ni nan zan tsaya miki sai na ji dalilin wannan kazafin da cin mutumci. Ki daina kuka ki bar min komai a hannuna kawai."
"Ni dai a'a ka bari na kai su ƙara."
"Na ce a'a ba za ki bi umarnina ba ne Sadiya?
Ya yayyaƙomin kamar zai dake ni ai sai na yi shuru
"Ko ba ki yarda da ni ba ne? Ko domin Anty Bahijja na yayata sai na zauna na zura ido a ci zarafin ki? Ba zan bar wannan mganar ba sai na ji dalilin wannan tozarcin. Na rantse da wanda raina ke hannun shi sai na tada ma duk wanda ya yi silan a taruwa a ci miki zarafi ki hankali shima"
Ya faɗa a fusace har ya na dukan sitayari duk fusata ta sai da na koma na yi shuru saboda na ga Yallaɓai ya harzuka. Daman ya kan daɗe ran shi bai ɓaci ba in kuma ran shi ya ɓaci to ba shi da kyau. Sai na koma gefe ina maida numfashi ina jera ajiyar zuciya.
"Na maida ke gida ko gidan Alhaji?
"Mu je gidan Ya Aina."
Na faɗa ba tare da wani tunani ba sai ya yi shuru bai yi mgana ba ana ta kuma cigaba da kiran wayarsa
"Nene ina tare da Sadiya. Zan taho gidan yanzu in sha Allahu."
Na ji ya na faɗa sai na ɗaga kai na kalle shi, ya na waya ne kuma Nenen da ya ambata ya sa na gane da ita ya ke waya.
"Nene gidan Yayarta zan kai ta. Yanzu zan dawo gida, ki kuma sanar da Bahijja ba Sadiya ta tozarta ba ni ta tozarta na kuma gode mata."
Sai na zo."
Ya faɗa kafin ya kashe wayar haka muka yi tafiyar nan shuru ni ina ta sauke ajiyar zuciya shi kuma ya na ta tsula gudu ba daɗewa muka iso gidan Ya Aina ya sauke ni kuma bai ce min komai ba ya juya motar a fusace ya bar layin ni kuma na taka na shiga gidan Ya Aina da sallama cikin muryata da ke shaƙe saboda kukan da shaƙa kamar an yi min mutuwa.
*Janafty* *TKG018*
*Littafin TURKEN GIDA, 1k ne akan manhajar Telegram.* 09069067488
Na shiga gidan Ya Aina ko gani ba na yi saboda tashin hankali da damuwa. Tafe na ke ina jefa ƙafuwana ba tare da na san in da za su faɗa ba. Ya Aina na hanga a ɗan karamin madafinta dake tsakar gida sai ƙannen Marwa na gefen ɗakinta a kan tarbarma suna cin abinci. Ko sallama ma ban yi ba ni dai kawai na shigo kuma na dumfari ɗakin Ya Aina so na ke yi na samu waje ni kaɗai na fashe da kuka na yi kuka mai ƙara mai sauti ko zan ci ɗan sauƙi sauƙi abin da ke taso min daga ƙasan zuciyata.
"Laa Mama ga Umma Sadiya."
Na ji wani cikin yaran ya faɗa amma ba zan iya gane ko waye a cikin su ba. Ni dai ƙafafuwana na taka suka shigar da ni falon Ya Aina sannan lokaci ɗaya na zube a saman cafet ɗin ɗakin tare da fashewa da kuka mai sautin da har a tsakar gida ana jiyo kukana.
Da gudu Ya Aina ta shigo ina jin salatinta. "Innalillahi me zan gani Sadiya? Ta faɗa lokaci ɗaya ta na zama kusa da ni ta saka hannu ta ɗago ni ta na mai kiran sunana.
"Sadiya"
"Ke Sadiya me ya faru?
Ta ke faɗa cikin tashin hankali da damuwa. Ban buɗe idanuwana ba amma na ɗora kaina a saman cinyarta ina cigaba da rera kukana, sai na ji kamar jikina ya na wani irin yam tsikar jikina sun tashi yam! Zuciyata na ji ta buɗe ina so na yi kuka mai yawan da na daɗe ban yi irin shi ba. Sannan ji na a saman cinyar Ya Aina ya ƙara raunana raunina da ya sa na ji kamar tsawon shekaru ban samu kafaɗan da zai tallafeni ba, shi ya sa na daɗe ban yi kukan da na ke jin yau ya na tahowa daga ƙasan zuciyata ba.
"Kai ku koma ku cigaba da cin abincin ku."
Na ji ta na faɗa, sai na ɗan buɗe idanuwana da suka kumbura saboda kuka sai na gansu sun yi jere a bakin kofa suna kallon mu. Maganarta ya sa suka fara fita ɗaya bayan ɗaya amma fuskokinsu dañkare da mamakin ganina ina kuka.
Sai da suka fice sannan Ya Aina ta ƙara maida hankalinta a kaina. "Sadiya me ke faruwa ne? Nan ma na yi mata shuru ina ta kuka hawaye da majina na zuba lokaci ɗaya.
"Ko wani abu ya faru tsakanin ki da Baban su Jidda ne?
Sai na ƙara ma kukana Volume amma na kasa mgana.
"Sadiya ki bar kukan nan ki yi min bayani. Duk kin ɗaga min hankali."
Ina shassheƙa na ce" Ki bar ni na yi kuka Ya Aina.. ki bar ni na yi kukan da zuciyata za ta samu natsuwa." Na ƙarishe faɗa ina mai ƙara fashewa da kuka sai ta ƙyaleni ina ta kukana amma ta saka hannunta guda ɗaya a bayana ta na bubbugawa alaman lallashi mun fi karfin sama da mintina ashirin sannan kukan ya fara ɗaukewa sai shessheƙa da kuma jan majina.
"Sadiya me ke faruwa?
Ta faɗa ta na kallona dai-dai lokacin da na tashi daga saman cinyarta ina faman goge hawayena da ɗankwalina da ya zame daga saman kaina.
"Ya Aina Ma'u ta ba da gudummuwa an tozartani yau a dangin su Yusuf"
"Ma'u kuma?
Ya Aina ta maimaita sunan ta cikin mamaki. Kawai sai na ji sabon kuka ya taso min ina kukan ina labarta ma Ya Aina abin da ya faru tun daga farko har ƙarshe.
"Innalillahi wa'inna alaihirraju'un"
"Anty Bahijja ta ci min mutumci ta kirani dangin bokaye da asiri. Ta ce aurena da Yusuf ba ta ga amfanin shi ba, Ya Aina wai ni suke zargi da ƙoƙarin zubar da cikin Amaryan Yallaɓai? Duk ta dalilin Ma'u. Domin ita ce ta ba su damar duk abin da suka yi min Ya Aina."
Na ƙarishe faɗa ina gunjin kuka da ƙarfi saboda sai na ji kamar a alokacin ma abin ya ke faruwa.
"Innalillahi. Ita Ma'un ce ta aikata haka? Amma ta ba ni mamaki matuƙa ban taɓa tunanin haka daga gare ta ba."
"Ba in ina cewa munafuka ba ce sai a riƙa ganin laifina ba? Yanzu dai kun yarda ko? to Ma'u ta daɗe ta na ci duduniyata a dangin Yallaɓai ta daɗe ta na son rana irin ta yau ta faru sai yau burinta ya cika."
Na faɗa ina goge idanuwana da hannuna kamar wata yarinya.
Ya Aina ta kasa mgana saboda lamerin ne ya zo mata cikin ba za tan da ba ta taɓa tunani ko tsammani ba. Salati kawai ta ke yi ta na ɗaukowa ta na direwa.
"Ma'u ce ta je ta faɗa ma Anty Bahijja dangin mahaifiyata yan asiri ne, sannan ita kuma Amaryan Yallaɓai ta ƙara da cewa ta na gidan ma Inna Mariya ta kawo min asiri. Sannan kuma ta ce wai yadda na gama shanye Yallaɓai haka na ke so na tusa ma Kawu Marwa domin shima a shanye shi da asiri tun da mu ƴan na gada ne ba na haya ba."
"Na shiga uku ni Aina. A ina suka ji labarim Marwan? Ko shi Abban ne ya faɗa?
"Ma'u ce ta fasa maganar. Ita kuma Ya Murja ce ta faɗa mata. Ba ina faɗa muku munafuka ce kuna ganin kamar ban da haƙuri ba? Uhm ni kaɗai na san wace ce Ma'u da kaidin ta."
Na faɗa ina mai ɗaura ɗankwali na rufe kaina kukan ya tsaya amma zafin da ke cikin zuciyata ya kasa raguwa.
"Ma'u. Lalle ko Ma'u ta ba ni matuƙar mamaki."
Ta fada ta na mai yin tagumi cikin ɗimuwa.
"Shi ya sa na ce an zo ƙarshe wallahi tallahi sai hukuma ta shiga tsakanina da su Ya Aina. Ba zan bar wannan kazafin da suka yi min ya tafi a banza ba."
Sai ta kalleni kafin ta ce" Shi Babansu Jidda me ya ce? "Me kuwa? Ya ce shima zai ɗau mataki amma ba shi zai hana ni ɗau nawa matakin ba."
"Alhajinmu ya sa ni?
"Ke kaɗai kika san abin da ya faru."
Na bata amsa ina kallonta sai kawai ta miƙe tana faɗin" Ya zama dole ya sani domin magana ce da ta shafi zumunci. Kuma ni kaina ba zan so a bar maganar ba gwara a ɗau mataki tun da ya shafi zuru'armu ya kuma shafi auran ki da mutumcin ki, ya zama wajibi a shiga wannan mganar domin a yi min lamarin tufkan hanci."
"Wa za ki kira?
Na tambayeta ganin ta na ɗaukan wayarta.
"Hamza zan kira. Shi sai ya kira Alhajinmu."
Sai na yi shuru saboda na san Ya Hamza zai ba ni dukkan goyon baya har sai ya ga an ƙwatamin haƙƙina. Da dai Ya Abubakar ne daman ba zan saka ran ya goyi bayana ya bar Ma'u ba amma kuma ya sani wannan karon ba gudu ba ja da baya ni da Ma'u har abada sannan sai hukuma ta shata mana layi a tsakaninmu.
A gabana Ya Aina ta zauna ta labartama Ya Hamza duk abin da ya faru ta ƙarishe da cewa" Sadiya ta zo min ciki kuka na fitan hayyaci. Hamza Ma'u ba ta kyauta ba, kuma tun da ta taɓa auren Sadiya bai kamata a yi shuru ba. Ka kira Alhaji ka faɗa mishi sai a san yadda za a shiga mganar. Domin Sadiya ta ce ba za ta yarda ba sai ta kai ta ƙara hukuma."
"Ta yi min dai-dai. "
Ya Hamza ya faɗa kafin ya cigaba da faɗin" Ni ban yi mamakin abin da Ma'u ta aikata ba daman can halinta ne ta na wani muƙu muƙu na munafunci ba Sadiya ni nan Hamza Muhamamad Yashe jinin Sadiya ba zan bari cin zarafin da a ka yi mata ya tashi a banza ba. Sannan duk wanda ya taɓa zuru'an Mama kamar zuru'an Gwaggo ya taɓa. Sannan duk wanda ya nemi tozarta zuru'an Gwaggo kamar zuru'an Alhaji ya taɓa. Kuma taɓa waɗanan zuru'an dai-dai ya ke da ka taɓa mana mutumcin mu da darajan mu, kuma taɓa darajanmu dai-dai ya ke da ka nemi faɗa damu. Saboda haka wannan lamarin ba Sadiya kaɗai ya shafa, har damu gabaɗaya."
"Gaskiya ne wannan."
"Sabo da haka, yanzu zan kira Alhaji a waya na faɗa masa abin da ke faruwa. Ya kamata ya sani saboda abu ne da ya shafi auren Sadiya. Sannan za a yi zama zan kira Auwalu jibi asabar mu shigo Kano. Ba Ma'u ba har Baaba sai an kira. Za ta ci ubanta sai mun ji in yayar Yusuf ita ce jininta ba Sadiya ba. Kuma daga wannan a yi mata iyaka da komai yadda za ta fahimci Sadiya ma ta na da gata."
"Haka ne gaskiya ne. Haka yakamata a yi."
Nan take ya ce ta ba ni wayar da ya ke a speaker ta saka wayar shi ya sa na ji komai. bayan na amsa mun gaisa ya ce" An ce kina ta kuka? To ki share hawayen ki, mu ƴan'uwanki za mu tsaya miki har sai gaskiya ta bayyana. Shi Yusuf ɗin me ya ce? Ko wani mataki ya ce zai ɗauka?
"Ya ce zai ɗau mataki amma bai faɗa min matakin da zai ɗauka ba."