Kenza eBookz

Turken gida book 2 cmplete by janafty - Chapter 4

Turken gida book 2 cmplete by janafty - Chapter 4

Turken gida book 2 cmplete by janafty Chapter 4: Turken gida book 2 cmplete by janafty Chapter 4. Sai na ga ta kalleni bayan ta ga na yi mgana da sauri na…

3,277 words

Sai na ga ta kalleni bayan ta ga na yi mgana da sauri na ce" Na idar ne." Sai ta wuce zuwa kitchen ta duba ta dawo ta ce saura guda ɗaya ina daga zaunen na ce ta kira shi ta faɗa masa har da siga ma ya siyo mana ta mu wacce ta rage ta yi ƙasa da ya ke ta san password din wayar ta buɗe ta kira shi ta faɗa masa ya ce to zai taho da shi haka Jidda ta faɗa min bayan sun gama wayar sai na gyaɗa mata kaina. Ina nan zaune Baby ta kunna cartoon jifa jifa ina kalla sannan wani bangaren kuma ina can ina tunani. Sai da Jidda ta gama aikin makaranta sannan ta kwashe jakarta ta maida ɗaki bayan ta dawo falon na ce ta sako musu abinci akwai kaza a fridge ta ɗauko ta ta ɗumama su ci ta amsa da to bayan ta ɗumama kazan ta ɗibo abincin taliya ce jalop mai kifi tun wanda Marwa ta yi ne suka yi min ta yi na ce ba yanzu zan ci ba. Gabaɗaya na rasa ɗanɗanon bakina tun yinin yau daga ruwan tea na safe sai ruwa kawai na ke sha na kasa cin komai.

Jna ji Jidda na ce min" Umma shima Abba taliya zai ci? Sai na kalleta yarinyar nan da iyayin tsiya wato har ta san babanta ba ya son cin taliya. A raina ko na ce ita zai ci in ya ga dama in kuma ya tsaya gidan amaryansa ya ƙoshi shike nan a fili kuma ban ta amsar ta ba shurun da na yi kawai ai ya faɗa mata E ne ita zai ci domin ni ba zan ƙara yin masa wani girki ba bala'in haushin shi na ke ji wallahi na rasa yadda zan yi da raina. Saboda ma kar ya dawo ina falon ya tare ni da mgana na ce musu zan je na kwanta Jidda ta kalleni kamar za ta yi mgana sai kuma ta fasa ina lura da ita sarai na san a ranta za ta ga abin da ba ta saba gani ba ne. Yallaɓai ko ƙarfe nawa zai kai bai dawo ba sai na jira ya dawo zan kwanta amma yau ɗin nan sai na ga in ma na tsaya jiransa ni ce sakara saboda ai wajen Amaryansa zai biya sai ya gama zamansa sannan ya dawo sai ni kuma da ban san ciwon kaina ba sai na zauna ina jiransa ai ko ya yi kaɗan.

Shigewata ɗaki na yi, na yi shirin barci na koma na kwanta ina juye juye marata ce ta ɗan fara min ciwo ya sa ma na tashi na je kitchen na zuba ruwan lipto na sha saboda marata ta ɗaure ban tsammaci zuwan al'ada ba saboda ni family planing ya gama lalatamin al'ada ba na iya gane zuwansa sai dai kawai duk lokacin da ya ga dama ya ke zuwa wannan ciwon maran daman ina fama dashi lokaci bayan lokaci. Ɗaki na koma na kwanta kuma cikin ikon Allah sai ya lafamin, barci ne a idanuwana saboda akwai bashin sa a kaina a cikin raina na riƙa addu'ar Allah ya sa barci mai nauyi ya sace ni Allah ko ya amsa addu'ata barcin da na yi mai nauyi ne domin har dawowar Yallaɓai ban sani ba sai dai muka haɗu da asuba shi ne ya ke ce min ya dawo ya ga ina ta barci ya na fatan lafiya? A yatsine na ce masa marata ce ta ke ciwo a jiyan sai na sha mgani na kwanta.

"Ayya Sorry.."

Kaina na gyaɗa masa lokacin ya ɗauro alwala ne ya na saka riga ni kuma tashina kenan na fita zuwa Tiolet na duba Al'ada bai zo miin ba sai kawai na kama ruwa na ɗauro alwala sanda na fito baya nan ya fita masallaci sai da na yi raka'atul fajir sannan na gabatar da sallar asuba. Ko da na fita zuwa ɗakin su Jidda har sun tashi ina jin Yallaɓai ne kafin ya fita masallaci ya tashe su barci ne a idona suna cewa karatu na ce Jidda ta yi ma Baby su karanta azkar zan je na kwanta kuma ina komawa ɗaki na kwanta ga casbaha a hannuna sai barci kuma ya sake ɗaukana ban farka ba sai wajen tara saura na safe har su Jidda sun tafi makaranta Yallaɓai kuma na can falo yana aiki a kan system ɗin sa.

Ina ganin haka sai kawai na fara yin wanka na shirya cikin riga da wando. Sai na leka kitchen ɗin na ga sun soya dankali da buredi da ƙwai, saboda kar in koma can falo mu haɗu da Yallabai ya sa na sake dafa wani ruwan tea lipto ne kawai da gnyen shayi ko siga ban saka ba na ɗibi dankalin anan kuma kitchen ɗin na zauna na ci kaɗan ba da yawa ba, ina tunanin ko Yallaɓai ya karya ko bai karya ba? Amma kuma na kasa zuwa falon na ga ni ko hakan ta faru ina wanke hannuna na koma tiolet na kuskure bakina sai na sake komawa bedroom ɗin mu na shige bargo ina jin sanyi sanyi na shigana kamar zazzaɓi zai kamani. Ina nan kwance sai ga Yallaɓai ya shigo ya riga ya kamani idanuwana biyu ba zan iya masa alaye da na saba masa kwana biyun nan ba.

"Ina kwana."

Na faɗa daga kwancen da na ke, sai da ya sauke kayan a hannunsa a saman dirowan gado sannan ya tako har gabana ya duka ya sumabci goshina lokaci ɗaya yana faɗin" Yaushe muka fara irin wannan gaisuwar Sadiya ta? Kallonsa na yi ba tare da na yi mgana ba sai na ga kawai ya ware min hannuwana alamun na taso wallahi wani turriri na ke ji a ƙasan raina ina tunanin yanzu fa yadda ya ke yi min nan tuni ya fara yi ma Gimbiya ko? Idanuwana suka ƙanƙance da kishi ina shirin na ce ni ya ƙyaleni ina jin barci ban samu dama ba ko ya fahimci niyyata ne ya sa kawai ya sunkuyo ya ɗago ni zaune yana faɗin"Oya ta so nan."

Ba yadda na iya haka nan na miƙe a kasalance na faɗa jikinsa ya ƙamƙame na wani lokaci ya na sauke ajiyar zuciya kafin ya ce" Kwana biyu nan duk an daina min kirki Sadiya ta. Ko na yi miki laifin ne? A raina na ce babban laifi ma kuwa sai dai ban ce ba sai da na fara ture sa sannan ya sake ni ya na kallona hancina ya lakace kafin ya ce" Kwana biyu ba mu yi ɓarnan ruwa ba ko? Kafin na yi wani yunƙuro ya haɗo haɓata ya haɗe bakim mu waje ɗaya ban taɓa sanin akwai ranar da za ta zo Yallaɓai na taɓa ni ina jin ƙuna a cikin raina ba domin sheɗan ne ke haskomin su tare da Gimbiya ya na yi mata kwatankwacin irin abin da ya ke yi min tuni na ji wani ƙarfi ya shige ni da hannu na saka iya karfina na ture Yallaɓai baya ina mai ƙwace kaina daga gare shi.

Cikin mamakin da na gani a saman fuskarsa ya kalleni. "Me kika yi hakan? Ya faɗa a ɗan zafafe amma cikin sanyin murya kai tsaye ina goge bakina kamar ya saka min cuta na ce" Ka ga Yallaɓai please." "Please mene? Ya katseni da sauri ya na kallona kirjinsa na ɗagawa sama da ƙasa alamun ranshi ya fara ɓaci.

Ina yarfa hannu na ce" Ka ƙyaleni kwana biyu nan am not in the mood." Ina gama faɗin haka na koma kan gado na kwanta ina jan bargo kenan na ji ya fizge da karfi ya cilla dashi a kasa da gajiya a cikin idanuwana na kalle shi kafin na ce" Na ce ka yi hakuri ka ƙyale ni ko? Ban jin daɗi ne."

"Ƙarya kike yi Sadiya."

Ya faɗa ya na kallona sai na ware ido cikin mamaki ina kallonsa sai kawai ya yi wani mirmishi kafin ya ce" Kin ɗauka ban lura dake kwana biyu nan ba. Sam ba ki son ina taba ki in kuma na kusanto in da kike a fuskarki kike nuna ba ki son hakan sai na ɗaga miki kafa ina tunanin fushin da kike yi a kaina ne ba ki sauka ba! Amma Sadiya ji fa abin da kika yi yau ni ne na zo gare ki kika ture ni? Ture ni fa kika yi to me kike nufi?

Ya ƙarishe faɗa a fusace kaina kawai na dafe saboda ni ba na son damuwa. "Na yi miki laifi ranar Anniversary ɗin mu na yi dare ban dawo ba. Yes na ji kuma na karɓi laifina sau nawa zan ce ki yi hakuri Sadiya? Ni kawai tsayawa na yi ina kallon ikon Allah don kawai ya ga ban buɗe baki na yi mgana ba shi ne zai wani tsaya a kaina ya na min masifa.

"Ki ba ni amsata ina miki mgana me hakan da kika yi ya ke nufi?

Ya faɗa a fusace har ya na daka min tsawa na kai makura na ga ba zan iya ɗauka ba a fusace na sauko daga kan gado ina ƙokarin barin masa ɗakin da zafi ya riko ni ya yo baya da ni har ya na yaga min hannun rigar jikina saboda da ƙarfi ya jawo ni ta baya. "Kar ki sake ina mgana da ke kina barina a wajen zan saɓa miki Sadiya." Na ƙanƙance idanuwana ina kallonsa kafin na ce" Ni me zan ce? Na ce ka yi hakuri wannan faɗan ne kuma ban san dalilin shi ba"

"Amsa tambaya za ki ba ni malama"

Ido cikin ido yake kallona sai na fahimci ranshi ya ɓaci ya na ta sakin huci ni ko domin na ƙara kunsa masa takaici sai na ce" Me ka ke son sani? "Abin da kika yi yanzu? Me hakan ya ke nufi? Ya faɗa ya na wani taso min sai na ja baya ina faɗin" Me kuwa? Ni ba na nufin komai" "Na yi miki wani laifi ne bayan laifin ranar?

Kawai saboda ya ga na yi shuru. Lalle nema Yallaɓai nima ko ina kallonsa na ce" Laifi! Sai ka tambayi kanka Yallaɓai." Na faɗa ina ƙoƙarin wucewa wannan karon da karfi ya jawo hannuna ya tamke har sai da na ji zafi ina kallon shi cikin mamaki kafin na samu zarafin mgana ya ce da ƙarfi" Ina tambayarki kina tambaya na Sadiya? Ihu Yallaɓai ke yi min a saman kaina saboda ina guje ma ɓacin raina kar nima na haukace masa.

"Me na yi miki kike ba ni wasu attitude da ban gane musu ba ne? Ko akwai wani abu a zuciyan ki ne! Ki fada min na ji.!" Yadda yaƙarishe tsawan ne har ya na neman ɓallamin hannu ya sa a fusace na make hannunshi nima cikin ihu na ce" Sakar ni. Ban sani ba. " Na faɗa nima cikin hargowa ina mai ɓalla masa harara idanuwana har sun kaɗa sun yi jajir Wucewa na yi ina faɗin" Na ce ka yi haƙuri ka kyaleni amma ka ƙi so ka ke yi raina ya ɓaci na haukace maka?

"To ki haukace mana. Ina dai dai da ke."

Ya faɗa ya na wani sakin tsaki Yallaɓai na kallah wannan abun na ƙirjina na taso min har wani duhu duhu na ke gani wato wannan shi ne halin maza in sun ƙara aure yau wai ni Yallaɓai ke faɗa ma ya na dai dai da ni. Kallon shi na yi idanuwana sun cika da kwalla sai kawai na nuna kaina cikin sanyin murya ina faɗin" Yau ni ce Yallaɓai ka ke faɗin kana dai dai da ni ko?

Sai na ga jikinsa ya yi sanyi saboda ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce" To ya kike so na yi miki Sadiya. To taho ki ji." Ya faɗa ya na tahowa wajena da sauri na ɗaga masa hannu sai ya dakata kafin na kalleshi na jinjina kai ina faɗin" Ka guji haukacewan tawa domin na rantse da Allah kai ba za ka iya da ni ba sai ka yi gayya "

Ina gama faɗin haka na fice daga ɗakin na bar shi nan. Ina jin kuka na taso min ɗakin su Jidda na shige na faɗa saman gadon Baby sai na ji kawai na fashe da kuka, sanin Yallaɓai zai iya biyo ni ya sa na tashi na rufe ƙofa ilai ya zo ya na ta kiran sunana na yi masa banza sai yau na samu damar yin kuka wato har na fara fuskantar wulakanci daga wajensa saboda ya ƙara aure ina kuka mai sauti amma kuma zafin da ke zuciyata ba ya raguwa sai ma ƙaruwa. Yallaɓai ya yi ta bugun kofa ban bude ba sai can kuma ya dawo ina jin sa ya na faɗin.

"Sadiya ki yi hakuri raina ne ya ɓaci. Na shirya zan je kaduna in na dawo yau in sha Allahu za mu yi mgana"

Ina jinsa ya gama mganganunsa ya fice ya bar gidan Ranar Saude ban san abin da ya hanata zuwa ba ni kuma kwance na yini ɗakin su Jidda salla kawai ke ta da ni ban komai ba hatta girki da suka dawo ne na ce Jidda ta dafa musu indomie ni kuma sai na sha ruwan zafi saboda cikina ya tanmke ga marata na matsannancin ciwo. Su kansu yaran sun san yau ba kanta Jidda ta ce" Umma ba ki da lafiya ne? Sai na amsa mata sannu ta yi min, yadda na yini kwance haka ma har dare ina kwance can bayan isha'i al'ada ta zo min sai na tashi na sake wanka na gyara jikina ranar ma da wuri na kwanta su Jidda ma na saka su barcin wuri. Wayata ko a yinin ranar ma kashe ta na yi saboda ba na so damu na fi son a bar ni na gama ji da abin da ke damuna wannan duka dukan da Yallaɓai ya yi mini ba.

Ban ɗauka a daran ya dawo ba sai farkawa na yi cikin dare na ganshi kwance kusa da ni. Da safe kuma na dai gaishe shi na addinin da ya ce mace ta gaida mijinta ya amsa a daƙushe shima, muryata ta shaƙe da safe tunda kukan da na yi ta yi jiya ya saka min mura mai zai shi ne ma ya yi min mgana.

"Sannu Mura kike yi?

Ya faɗa lokacin da ya dawo daga kai su Jidda makaranta an saka su wata tahfiz can gaba damu kaɗan asabar da lahadi. Salisu na gida ba ya jin daɗi. Ya ji ni ina ta attishawa ne sai ya yi min sannu na amsa kuma shi da kanshi ya je ya dafo min shayin citta ya kawo min na sha sai na ɗan samu sauki sannan ya duba cikin box ɗin mu na mganguna ya samo min mganin mura ya ba ni na sha sai ya ce na kwanta na huta har yana gyara min kwanciya ya na rufamin bargo da ya ke kuma mganin kamar ya na saka barci sai barci ya ɗauke ni sai wajen sha ɗaya na farka na tashi ina mutsike ido wayata na kunna na ga 11 na safe ta gota gashi yau ɗin asabar. A kasalance na sauko daga kan gado ina hamma tiolet na shiga na kama ruwa yunwa na ji ina ji sai na tafi kitchen sai na ga Yallaɓai ya soya doya ya rage min ita na diɓa zuwa falon yara daga nan na ke jin tashin muryoyi kamar ba ta Yallaɓai shi kaɗai ba sai da na gama cin doya na kora da ruwan shayi sannan na kai kofin da filet kitchen ni kaina wajen duk ya yi min kazanta jiya Saude ba ta zo ba ni kuma ban yi ba.

Bedroom na koma na sako hijabi da takalmi na yi sallama a falon Yallaɓai suka amsa min sannan na tura ƙofa na shiga.

"Uncle Abba kai ne tafe ba labari."

Na faɗa ina karisowa cikin falo, lokaci ɗaya ina ɗan tari kaɗan.

"E. Na shigo duba wani fili sai na kira Yallaban ki ya ce yana gida na ƙariso. Ina zuwa ke na fara tambaya ya ce ba ki jin daɗi kin kwanta "

Ina zama saman kujera mai zaman mutum ɗaya na ce" E wallahi sannu da zuwa." Na faɗa ina kallon Yallaɓai ta gefen ido ya na zaune a gefen Kawun na shi ya duƙar da kai ƙasa.

"Sannu ya muran to?

Sai na ce da sauƙi ina tambayan ya mutanen gida. Mu ɗan yi hira saboda ni dai muna shiri da shi kuma har muka gama Yallaɓai bai saka mana baki ba, ban daɗe ba na tashi na koma falon su Jidda. Daga Yallaɓai har Uncle Abba sun bi bayan Sadiya da kallo har ta fice kafin Yallaɓai ya sauke ajiyar zuciya ya na faɗin" Ka ga abin da na ke faɗa maka ko? Kwata kwata na kasa gane kanta."

"To daman ina za ka gane kanta ka yi mata kishiya."..

Yallaɓai ya ce" Ai ba ta sani ba."

"Ko?

Uncle Abba ya faɗa ya na kallon Yusuf. Shi kuma sai ya gyaɗa kai kafin ya ce" Yes. Domin na roƙe su kar su faɗa mata sai ta faraji daga bakina."

Jinjina kai Abba ya yi kafin ya ce" Ni kuma sai na ke tunanin kamar ta sani Tafida." Ido Yusuf ya saka masa kafin ya ce" Ta sani? To wa ya faɗa mata? Abba ya zaƙuda kaffaɗa kafin ya ce"oho amma ka yi tunanin me ka yi mata da ta sauya maka haka? Ni kaina na ga duk ta yi wani iri kamar ba Sadiya ba."

Yusuf ya yi shuru ya na tunanin kai bai yarda ta sani ba in ta sani me ya sa ba ta yi masa mganar ba. Sai dai ya fi yarda ƙila ta na ji dai a jikinta domin an ce mata in za a yi musu abokiyar zama suna ji a jikinsu.

"Ba ta sani ba gaskiya rigimarta ce kawai ta tashi."

Ya faɗa cikin jadaddawa.

"To sai ka sanar da ita da wuri kafin ta sani a wani wajen."

Sai ya jinjina kai kafin ya ce" In sha Allahu. Daga nan suka cigaba da tattaunawa duk a kan ba tun dai.

*Janafty* *TKG*

03.

FHB CLOTHING Muna Dinka kowanne irin nau in dinkunan yara na zamani,Muna bada sari ga masu bukata haka Muna maraba da masu sayen dai dai Muna turawa ko Ina cikin sauki a Nigeria da makotan kasan mu . Amana shine taken mu . wtsapp no.08080266674 or call @08034109622

Ni ko ina barin falo ɗaki na koma na ɗau wayata na kunna na kira Saude sai balaraba ta ɗauka tana faɗa mini Saude ba ta da lafiya zazzaɓi ya rufe ta. Amma ta ji sauƙi, fatan samun lafiya na yi mata sai ta ce min ko ina buƙatar ganin ta ne? Ai sai ta rarrafo ta zo tunda ta ji sauƙi.

Da sauri na ce" A'a ta bar shi kawai in ta ƙara jin sauƙi sai ta zo."

Sai muka yi sallama bayan na ce ta haɗa ni da Sauden na yi mata sannu sai ta ce mini ta shiga makewayi mun rabu akan zan sake kiranta in sha Allahu. Ajiyar zuciya na sauke ina mai riƙe ƙuguna aikin da ke gabana kawai na ke hasashe jiya ba a gyara gidan ba ga wanke wanke mai yawa ba a yi ba in dai ba ina so a zo gidana a tafi da ni a baki a bangaren kazanta ba ne. Dole na sauke son jiki na gyara gidana wayata na ɗauka zuwa kitchen na kunna karatun Qur'ni cikin suratul Maryam saboda ina son suran sosai ta na yi mini daɗi.

Readers Also Read