Turken gida book 2 cmplete by janafty - Chapter 5
Turken gida book 2 cmplete by janafty Chapter 5: Turken gida book 2 cmplete by janafty Chapter 5. Kaye kaye na fara yi a kitchen ɗin saboda ina so na fara…
3,374 words
Kaye kaye na fara yi a kitchen ɗin saboda ina so na fara gyara shi bayan na gama sai in yi wanke wanke na goge kitchen ɗin a lokacin da Yallaɓai ya shigo ina kwashe dattin da ke cikin filet ɗin wajen sink ina zubawa a cikin leda na ji shigowarsa ni kuma ina ta bin karatun na yi kamar ban gan shi ba na gama tara dattin na ɗau ledan zan fitar can waje sai ya saka hanny ya karɓa ban tsaya masa jayayya ba na sakar masa na koma ina goge saman dirowers ɗin kitchen ɗin da wani ƙaramin towel saboda ma kar ya zo ya dame ni har ƙure volume ɗin wayata na yi da karatun na ji buɗe kofarsa da dawowarsa na kuma ji a jikina ni ya ke ta kallo amma ban juya ba ina cigaba da aikina lokaci ɗaya ina bin karatuna ga shi na tsuke cikin riga da wando amma jeans ɗin mai ɓudewa ta kasa ne sai wata ƙaramar riga amma na saka wani ƙaramin hijabi wanda ba zai dame ni ba saboda baƙon da muke dashi.
Ni ban ji lokacin da ya taho ba kawai jin kansa na yi ya ɗoramin a saman kafaɗata. Na ɗan tsaya haka sai kuma kawai na basar na cigaba da aikina kuma ban dakata da jin karatun ba, leƙa fuskata ya ke yi har ya na shafa mini kumatu saboda dai na kula shi amman ban yi ba. Domin ni Yallaɓai duk wani abu da zai yi ko zai ƙara yi ya daina burgeni tunda abin na shi duk munafunci ne, gani na yi yana saka yatsa ya na latsa min gefen cikina kamar ya na so ya yi min cakulkuli da sauri na ƙwace jikina ina kallon shi. Marairaicewa ya yi ya na min wani kallo wanda a da kallon nan ya ke rikitani amma yau wallahi ko kaɗan ban ji wani abu ba, sai ma na koma na cigaba da aikina lokaci ɗaya ina faɗin.
"Karatun Qur'ani ne fa."
Na faɗa ina cigaba da bin karatun, shi kuma sai ya ƙara biyoni sai ji na yi ya rumgume ni ta baya ya sagalo kansa ta tsakanin wuyana sannan hannayensa ya sargafe su ta cikina ya matse ni, kiss ya yi ta min a wuyana da gefen bakina amma na ki bashi wata dama kawai sai ya zura hannunsa ya ɗauko wayar dake gefena ya tsaida karatun na ɗago a zafafe zan masa masifa da sauri ya haɗe bakin mu waje ɗaya duk iya ƙokarina yau na kasa kwatan kaina domin ya yi min bake bake ne ya rufe ni ruf ɗin da na kasa ƙwatar kaina amma har ya yi kiɗan shi ya yi rawan shi ban yi ƙwaƙwaran motsi ba, yau sai na ji kwata kwata bakin Yallaɓai kamar miyansa ya koma mini maɗaci domin wata zuciyar na faɗa mini ya yi ma Gimbiya irin wannan shi ne kema ya zo yana yi miki tuni na ji kamar zan yi amai, na kasa haɗiye miyan bakina a gaban shi ya na kallona na saka hannu ina goge bakina kamar ya shafa min wani cuta.
Hannuna ya riƙe caraf ya na wani tsare ido. "Cuta na saka miki da kike goge bakin Sadiya? Sai na kalle shi, tunda ya aure na zama ba tashi ba sai dai ya rika kirana da sunana Sadiya kawai gatsal. Tun daga nan na san na fara ganin iskancin namiji tun kafin ma su tare su fara zaman auren.
"Sorry mana. "
Ya faɗa ya na riƙe duka hannayena cikin shagwaɓa har ya na wani karya wuya. Na yi masa banza ban yi mgana ba sai kawai ya sake ni ya riƙe duka kunnuwansa yana faɗin" Sorry. Haba mana Sadiya ta." Ya faɗa lokaci ɗaya ya na ƙara marairaicewa na kalle shi na ƙara kallon shi wai yau ni ce Yallaɓai ya kalla ya ce ya na dai dai da ni, to ai shi ne zan gani in zai iya da ni ganin ya hana ni aikina sai bina ya ke yi ya na min magiya dole na ce na haƙura sai ya rumgumeni ya na mai sumbatar goshina kafin ya sake ni ya kuma bi ni da kallo ya na faɗin" Za mu samu abin karyawa ni da kawun na ki?
Ya dai ci darajan Uncle Abba da ba zan yi ba amma saboda darajan mai daraja sai na amsa da toh duk zamansa a kitchen ya ga ina aiki bai tambayi ina Saude har sai da ya fita sannan ya ƙara dawowa. "Ina Saude? Ba za ta zo ba ne" "Ba ta da lafiya." Amsar da na bashi a takauce kenan sai ya juya yana mai faɗin Allah ya ba ta lafiya da harara na rakashi har ya fice sannan na yi ƙaramin tsaki ina mamakin halin maza na ƙara yarda da aka ce ba su da kunya tun daga ranar farko kunyar abin da Yallaɓai ya aikata min ya fita daga jikinsa ya daina nuna tsoro ko kunya ya yi aure ban sani ba, ban san tunanin shi ba, shi a tunanin shi ban sani ba sai ranar da ya ga dama sai ya faɗa mini ƙila ma bayan Gimbiyan ta tare, Ma'u ta cuceni da halin da na shiga cikin kwanakin gwara ma ban ji mganar ba sai a lokacin da ya ga damar faɗa min ga shi ta dalilinta sauran farincikina a kwanakin da ya kamata na yi shi ta yi silan ruguzamin shi, ni kam ai tsakani da Ma'u sai Allah ya isa kuma da ikon Allah duk wani sharrinta sai ya koma kanta.
Ina aikina ina tunane tunane baƙin ciki na kara samun muhalli a cikin raina. Dankali na fere na soya musu da kwai sai na sake dafa musu ruwan tea na kai musu Uncle Abba na ta yi mini sannu. A falon na bar su suna karyawa ni kuma na koma na cigaba da aikina sai da na gama wanke wanke sannan na yi sharan ɗakunan gabaɗaya na wanke Tiolet ɗin mu da na su Jidda duka kuma na yi mopping gidan amma ban da falon Yallaɓai kirchen na gyara shi na goge shi tas ban zauna ba sai da na ɗora girki gwara na yi hutun gabaɗaya. Shi ma girkin saboda Uncle Abba ne domin ya na gidan bai tafi ba har bayan azahar sannan suka fita tare da Yallaɓai bayan ya ce mini daga masallaci zai raka Uncle Abba anguwa ba su suka dawo ba sai bayan La'asar lokacin har na yi wanka tun ɗazu abinci kuma tuni na daɗe da gamawa Jalop ɗin shinkafa da Nama ɗan sauran da ya rage mana na saka a ciki. Sai kuma daman na haɗa zoɓo har ma ya yi sanyi shi na cika wani jug ɗina da shi kuma sai da suka shanye shi, Sai wajajen Biyar Uncle Abba ya yi mana sallama ya tafi bayan ya ba ni 10k ya ce na yara ne na karɓa ina godiya tare suka fita da Yallaɓai bayan tafiyar su ne na gyara falon na tattara abin da suka ɓata zuwa kitchen falon su Jidda na koma na kunna Mbc bollywood sai wani indian film da suke yi series ya ɗau hankalina mai suna Habibi da'im da kuma gargaliyan Labarci su ke mgana to ina ɗan tsinta sosai film ɗin ya ja hankalina tuni na fahimci a dai dai wannan lokacin suke saka cigaba film din sau shidda a sati ban da jumma'a da asabar a raina na saka cewa zan dinga bin shi dramar ta ɗau hankalina.
Ƙarfe bakwai a ka gama film ɗin sai na ga sun fara shima wani ban tsaya ba na tashi yin salla su jidda tun wajen shidda da kwata suka shigo gidan a kafa suke dawowa tun da makarantar ba nisa har sun sauya kaya sun ci abinci. Tare da su muka yi salla sannan na ce su ɗauko Qur'ani mu yi karatu muna cikin karatun ne wayata da ke kan kujeran da na tashi a kai ta fara neman ɗauki alamun ana kirana Baby ce ta yi saurin ta shi ta ɗauko min ta na faɗa min Abba ne, har za ta ɗauka na fizge wayar ina faɗin.
'"Ko ba Abba ba."
Na faɗa ina balla mata harara da sauri takoma kusa da ƴar'uwanta ta zauna ta na wani fiki fiki da ido. Na yi mamakin ganin Anty Zabba na kira a cikin raina na gane dalilin kiran kawai sai na mike sanye da hijabin da na yi sallah Jidda na kallah kafin na ce" Ku cigaba kafin na dawo." Sai ta amsa min ni kuma sai na bi ta ƙofar kitchen zuwa cikin ɗakin mu na barci.
Wayar ta katse lokacin da na kai zaune gefen gado amma cikin lokaci sai ga wani kiran na ta ya sake shigomin, sai na ɗauka ina mai dai dai ta yanayina. Gaisawa muka yi da tambayan iyalan juna kamar yadda muka saba. Sai kuma muka yi shuru na wani lokaci saboda gaskiya mu ba abokan mgana da juna ba ne sosai.
"Jiya ina ta kiran wayar ki a kashe."
Ita ta fara kauda shurun, sai na ce" E. Wallahi." Daga nan sai na yi shuru ina jin sautin mirmishinta kafin ta ce" Sadiya ya muka ji da wannan jarabawar rayuwar! Na ji shima Tafidan na ki an ƙaƙaba masa wata matar." Gimbiya ce ko? Ban yi mamaki saboda ni na san kowa ya sani a tunanin Yallaɓai ni ce kaɗai ban sani ba tunda bai sanar min ba.
"E. A ina kika ji labari hala?
Na tambaya sai ta ce min Jamila ta faɗa mata jiya suka yi waya suna cikin wayar ma sai ta katse ba ta ma karisa ba ta labarin ba, ina ga shi ya sa ba ta ji an ce a yi shuru kar na ji ba."
"Sadiya akwai zafi na sani. Ni kaina har yau ban fita daga wannan zafin da Usman ya haddasa mini ba."
"Uhmm."
Kawai na iya cewa zafi ai ba ma sai an faɗa ba. Ita kuma sai ta cigaba da faɗin" Kishi fa gaskiya ne Sadiya sai wanda aka yi mawa ya ke sanin haƙikanin zafin abin. In ka nuna damuwa a ce ka ɗaga hankalinka wane wane Alhalin ba wanda ya san irin zafin da kake ji acikin zuciyarka."
"Kwarai."
Na bata amsa sai ta cigaba da fadin" Ki daure Sadiya akwai zafi amma ki daure. Dangin mazajen mu suna neman ganin gazawarmu ce shi ya sa, shi na wajena ya auri yarinyar ogansa shi kuma na wajen ki ya auri yaruwansa duka fa domin a kaimu ƙasa ne kuma Allah ya fi su, ki daure zafin zai ta ƙaruwa barin ma in sun fara zama tare amma ki yi ta addu'a da ikon Allah za ki samu komai da sauƙi kin ji ko?
'"Na ji. Kuma in sha Allahu ba damuwa."
Mun dade muna mgana ta na ta bani shawarwari sai a lokacin ta ke faɗa min ashe a lokacin mganar auran ya Usman da ta dawo gida ba yaji ta yi ba ta ce kawai ta zo gida ne ta samu kwanciyar hankali amma dangin miji suka buga mata tambarin ta yi yaji, ni kaina na sha mamaki na ce mata mu ma haka aka ce mana wai kin yi tashin hankali har da su yin yaji.
"Uhm wallahi ni ban yi yaji ba. Da amincewarsa na taho gida Sadiya. Gwara mu yi nesa da juna sai na samu damar rage jin zafinsa domin a zauna lafiya. Ba gashi an yi ba kuma muna zaune gida ɗaya da ita ba sai dai tana bangarenta ina nawa, ni dai ina zaman musulunci da ita, itama haka amma ba zan yi zaman daɗi da kishiya ba Sadiya shima ai na faɗa masa matarsa ta yi rayuwarta nima na yi tawa ni da ƴaƴana."
"Shi ne alheri ma."
Domin ban ga amfanin haɗa kai da kishiya yanzu ba kai ya waye ban da mutanen da wa ke maida kishiya yar'uwa wallahi gazarwar ki ta ke nema in kuma ta samu sai ta yaƙe ki. Anty Zabba ta yi ta bani wasu labarai ta na faɗa min na zama jaruma. Shawarar da za ta bani kar na ce zan bibiye ta na ɗauke kaina a kanta sai na zauna lafiya amma kar na sakar mata kar kuma na ƙi ba ta dama a yi zaman musulunci wanda ba zai wuce jaje ko taya murna ba, ta yi na ta rayuwar nima na yi tawa a hankali a hankali zafin zai gushe har wata rana ma sai na manta ina da kishiya. Ina dariya na ce.
"Daman ana mantawa?
Itama ta na dariyan ta ce" Sosai ma. Barin ma in ba gida ɗaya za ku zauna ba" Sai na ce mata ban sanin masa ba nan na ke faɗa mata ni fa har yau bai faɗa min ba amma na ji yana waya ashe shi ne ya roke su kar su faɗa,min har sai bayan shi ya faɗa mini da kansa. Cikin dariya ta ce" Ya yi miki irin na Ɗan"uwansa nima ai bai faɗa min da farko a gari na ji. Ni ko na yi irin taki ban nuna masa na sani ba." Nima ina cigaba da ba ta labarin a wajen wata yar uwata na ji labarin. Anty Zabba ta ce na yi jarumta na cigaba da bin shi a haka na ga iya gudun ruwan shi. Hira ta ɗauke mana hankali har sai da aka kira sallar isha'i sannan muka yi sallama sai na ji zafin da ke taso min a saman ƙirjina ya na raguwa samun wanda mu ka yi hira ƙwatakwancin mai damuwa ko na ce gyambo irin nawa.
Muna gama wayar ban koma falo ba sai da na yi sallar isha'i sannan na koma falo wajen su Jidda sai na iske ma suna salla bayan sun idar nace Jidda ta ɗibo min abinci tun da ɗazu da rana ban ci ba. Da gaske ne na ji sauƙi sauƙi a cikin raina tunda har ban ma yi barci da wuri ba sai da na jira dawowan Yallabai wajen tara na dare, ina ta kallonsa ina tunanin daga wajen Gimbiya ya ke amma sai na yi saurin kauda wannan tunanin kamar yadda Anty Zabba ta ba ni shawara.
Shi kan shi na san ya ga chanji. Domin ni da kaina na haɗo masa ruwan lipto ya sha bai ci abincin ba ya ce cikinsa ya cika mun zauna da yara muna kallo har goma na dare sannan na ce su je su kwanta saboda makaranta gobe, mu kuma sai wajen sha ɗaya muka shiga kwanciya domin Yallabai ne ya ce sai ya ƙarisa kallon wani american film ɗin da muka fara kallo a MBC ACTION. Saboda ya ga na ɗan sake masa ya na ta ba ni labari ashe tun fitan shi suna tare da Uncle Abba sai daren nan suka je ya gaida Nene shi ya kawo shi gida sannan ya wuce. Ina gyara gashin kaina na ce" Allah ya kai shi lafiya " Su Yallaɓai an samu fuska ya na tarawan jiki duk da har ga Allah ba na cikin Mood ɗin haka nan na bashi dama, kuma daman al'adata kwana biyu ya yi ya ɗauke ni da na ke yi kwana biyar a baya. Yau ban san da me zan kare kaina ba. shi kan shi ya ɗan ga chanji domin ban yi masa wani rawan jiki ba, kar dai ya ce na yi masa kamar gunki ne ya sa na ɗan motsa masa kaɗan na ga mamaki a saman fuskarsa amma bai furta min ba ni kuma ban bashi damar mgana ba, domin niki niki na yi da raina ina ta faman sha masa kamshi.
Da asuba ma da na ga take taken shi na son ƙarawa sai na yi masa barcin ƙarya dole ya ƙyaleni. Bayan su Jidda sun tafi makaranta ni da shi ne kaɗai a gida, Marwa ta zo kwasan sauran kayanta ita na samu ta yi min gyaran gida muna ta hira da ita tana ma gidan sai ga Saude na ce ba na ce ta zauna a gida ta warke ba sai ta ce min ai ta ji sauƙi. Su suka ɗeɓemin kewa domin Marwa ta yi min abincin rana sai wajen ukun rana suka tafi. Yallaɓai kuma daman tun safe ya ce min yau da yamma ko da daddare ya na so zai yi mgana da ni, ina jin haka a raina na ce daga baya kenan. Sai na ji kamar ba na son jin ma abin da zai gaya min saboda ba zai zama wani sabon abu a wajena ba. Har na saka ma kaina dangana na ce zan tsaya na saurare shi ko domin na ji abin da zai ce min. Sannan ina son na san ta in da aka haihu a ragaya, to eh mana domin har yau ban ji labarin yadda wannan auran bazatan ta ya faru ba, shin daman can an shirya sa ne ko yaya abin ya ke! Bai ba ni wannan amsar ba mutum ɗaya ne ko zuwa biyu ko Yallaɓai ko kuma ita kanta Gimbiyar.
Wajajen ƙarfe biyar da wani abu na yamma muna falo tare da Yallaɓai shi ya na aiki a saman system ɗin sa ni kuma ina kallo a Mbc bollywood domin na fahimci suna series masu kyau da ma'ana. Jefi jefi muna hira duk da ƙarfin hiran na bakin Yallaɓai ne ya na ba ni labarin aikin su na kaduna da irin alherin da ya ke fatan samu kallonsa kawai na ke yi, a baya ne in ya na faɗa min haka na ke jin daɗi amma yau sai na ji ko kaɗan ban wani damu ba, in zai lura ma ni ina ta taɓe masa baki ne labarin duk ya gundure to Allah na tuba yanzu ai komai ya samu ba nawa ba ne ni da ƴaƴana ba, namu ne har da ita kanta Gimbiyar wa yasanin ma ko da kuɗin ya ke saka ran yi mata hidima da kuɗin ma ya kawo min kishiya.
Fitsari ya tashe shi nan tiolet ɗin falo ya shiga ya kama ruwa. Ya tashi kenan ba daɗewa wayarsa da ke gefensa a in da ya tashi ta fara haske kaamar tana silet ne ina zaune amma na kasa tashi domin na daina saka ido akan wayar Yallaɓai domin tsira da kwanciyar hankalina. Duk da ina ankare da shi ni dai tun bayan faruwan auran na su ban taɓa ganin sun yi waya ba kamar ta ɗan rage kiran shi a bisa baya. Wata zuciyar ta ce min ke Sadiya in suna wayar ma za ki sani ne! Balle ma suna gari ɗaya ai suna ma haɗuwa su yi abin da a waya ma ba za su iya ba.
Tunanin haka kawai ya sa na yi tsaki mai karfi na tashi da niyyar na bar masa falon. Amma sai zuciya ta rinjaye na ƙarisa wajen wayar ina ganin tana cigaba da hasken alamun mai kiran ya kasa haƙura.
"Daughter."
Gabana ya faɗi ya yi wani raga raga, kirjina ya amsa dum! Har sai da na dafe ƙirjinan nawa saboda na ji nauyin da ya yi min na neman rinjiya na. Dai dai lokacin Yallaɓai ya fito daga tiiolet ya na daura mazugin wandon shaddan da ke jikinsa.
"Sadiya ta a taimaka a wanke min tiolet ɗin mana."
Duk ƙokarina da nuna jarumta yau na kasa, me ya sa ta ke kiran shi? Ba kullum suna tare ba! Don kawai yau bai fita ba ta ganshi ba shi ne sai ta kasa sukuni sai ta neme shi! Ƙila ya fara ɗanɗana mata daɗin shi ne ba za ta iya hakura da shi ba, ina jin tahowar Yallaɓai ya na mgana amma turiri na ke ji na fitowa daga zuciyata har ina jin zafin a cikin bakina.
"Kawai kin yi ma tiolet ɗina tawaye shi sai a yi sati ba a kalle shi ba."
Ya faɗa dai dai yana ƙarisowa wajen da na ke tsaye.
"Na ga kina tsaye! Me ya faru?
Na so ne na juya cikin lumana na bar masa falon amma kishi ya sarrafa zuciyata domin a fusace na juyo, ko kallon Yallaɓai ban yi ba da wani uban sauri na wuce sa har ina bangazan kafaɗansa.
"Sadiya.."
"Sadiya.."