Turken gida book 2 cmplete by janafty - Chapter 6
Turken gida book 2 cmplete by janafty Chapter 6: Turken gida book 2 cmplete by janafty Chapter 6. Haka ya riƙa kirana, amma ko juyowa ban yi ba, da wani…
3,375 words
Haka ya riƙa kirana, amma ko juyowa ban yi ba, da wani irin zafi na buga masa ƙofar falon bam! Na kuma san sai da ƙaran ya shiga kansa ina tafe ne zuwa ɗaki amma ina ganin nisan shi a yau, ni dai kafata kawai ke tafe da ni ban san ya aka yi ba na ganni zaune saman cafet ina kuka bayan na shigo ɗakin barcin mu na rufe ƙofa duk ƙoƙarina na kar na yi kuka sai da na yi. A raina ina faɗin Yallaɓai ya cuce ni da ya yi auran nan a lokacin da ban yi zato ko tsammani ba.
Ni dai tun da na shige ɗaki ban buɗe ba, ban kuma fito ba ina jin Yallaɓai ya gama bugun duniya da kiran sunana na yi masa banza. Sai da na ji fitarsa masallaci sallar mangariba na buɗe nima na shiga tiolet na yi alwala na zo na yi salla a lokacin su Jidda suka shigo sun dawo daga makaranta tun ɗazu wai Abba ya ce ba na jin daɗi, sai amsa musu da eh tunda ya ce ban jin daɗi ai shikenan zama na yi kan darduma ina ta salatin Annabi har sai da na samu natsuwa ana kuma kiran sallar isha'i na miƙe na yi ina idarwa na yi shirin barci na koma na kwanta. Ni yanzu ma waya ba ta gabana saboda na fahimci ita ke barazana da kwanciyar hankalina.
Yallaɓai sai bayan isha'i ya dawo ya kuma shigo ɗakin sai na fara nishi kamar ban da lafiya. Sai ya ruɗe ya ƙariso gare ni yana tambayata meke damuna na dafe kaina na ce kaina ne, ya ce zai bani magani na ce ai nasha. Bawan Allah ya bani tausayi haka ya zauna a kusa dani ya na ta min sannu ni fa daman guje ma mganarsa ne a yau ya sa na yi haka ganin yaƙi tashi a kusa dani ya sa na fara barcin ƙarya, ganin haka yasa ya gyaramin kwanciya ganin ina zufa sai ya kunnamin fanka ya fice bayan ya rage min hasken ɗakin gabaɗaya.
Yana fita na mike zaune ina mai harɗe hannayena a saman kirjina. Na daɗe ban yi barci ba ina ta tunanin wai yau Yallaɓai ba nawa ba ne ni kaɗai kai lamarin akwai girma. Tun ina jiyo ƙaran tibi daga falon yara har barci ya ɗauke ni sai asuba na tashi, da rawan jiki ya fara min sannu har ya na taɓa goshina.
"Ya kan na ki? Ya yi sauƙi?
Sai na gyaɗa kai ina faɗin ya yi sauƙi saboda na ji yana faɗin in ba zan iya ba na ɗaga zuwa asibiti sai wani sati da sauri na ce zan iya. Yallaɓai ranar ya yi ma yara da mu kan mu abin kari, doya ya soya mana sai abincin jiya da ya ɗumama duk tare za mu fita shima ya na da zuwa jana'iza baban wani yaron shi ne ya rasu a can sheƙa. Su Jidda suka fara tafiya mu kuma takwas da rabi muka fita ni da Yallaɓai sai da ya fara kaini asibiti sannan ya wuce jana'izan da za a yi ƙarfe tara na safe ya na ta ma sauri, ni kuma har muka rabu ban iya ce masa daga asibiti Ɗorayi zan wuce ba na bari sai na gama da asibitin sai na kira shi na faɗa masa.
Yau ban samun ganin Dr.Aisha Bukar da wuri ba, saboda ba ta zo da wuri ba , sai 12pm na rana na baro asibitin. Daman na je mata da Test ɗin da ta rubutamin a ƙarshen zuwana tun da yanzu bayan sati uku na ke dawowa. Yau ma ta ƙara rubuta mini wani amma tace shi ne na ƙarshe, daga shi za ta ɗora ni kan mganguna.
"Dr kina ganin zan ƙara samun ciki har na haihu?
Na faɗa cikin karaya saboda ni dai na gama sarewa.
Sai da ta kalleni kafin ta maida hankalinta kan fayel ɗina ta na rubutu.
"E mana. Me zai hana? Likitoci ai ba Ubangiji ba ne, duk abin da muka faɗa hasashe amma ba gaibu ba ne. Balle ni ban ce miki kina da wata matsalan da ba za ki sake haihuwa ba. Za ki sake haihuwa haife haife ma in sha Allahu."
Haka aka sha faɗa mini amma kuma kalaman Dr Aisha ya sa na samu sukuni, na yi mata godiya da ya ke mun saba sosai da ita. Sai da na fito bakin asibitin na kira wayar Yallaɓai bai ɗauka ba sai na ƙara kirana har sau uku amma bai ɗauka ba.. gani a bakin hanya ina son hawa adaidaitan da za ta kaini Ɗorayi.
Dubaran tura masa saƙo ya shiga kaina. Da sauri na shiga bangaren saƙonni na lalibo Yallaɓai tun saƙon Anniversty da na tura masa bai ko ba ni amsa ba, ban damu na shiga yi masa rubutu.
"Ina so daga asibiti na je gida na gaida Alhajinmu."
Na daɗe fa a bakin hanya raina har yafara ɓaci har na yanke shawaran ƙarisawa Office ɗin sa tunda ya ce min daga wajen jana'iza office zai zo, da ya ke ba nisa offishin na su na can gaba ne ko a ƙafa ma zan iya takawa. Ina wannan tunanin sai ga saƙon sa.
"Ok."
A takaiçe haushi ya kama ni na yi ja dogon tsaki na maida wayata jaka na samu adaidaita da za ta kaini ɗorayi. Ina sauka a a bakin layi na tako zuwa cikin layi na haɗu da wasu matansa anguwa muka gaisa. Na shiga gida ana ta kiran sallar azahar na samu Gwaggo a tsakar gida ta na alwala gidan shuru.
Ina sallama Gwaggo ta ɗago ta na amsawa. "Ah maraba Dubu ke ce tafe? Na amsa mata ina gaisheta ta amsa lokaci ɗaya tana tambayan Yallaɓai da yara, nace suna lafiya. Ɗakinta muka shiga ina tambayan Alhajinmu ta ce jiya ya je can yashe sai yau zai dawo.
"Topha lafiya ko Gwaggo?
'Lafiya lau. Kan auran autan su Muntari ne kinsan bikin saura kwana goma."
Gwaggo ta amsa min.
Shaf na manta da bikin kuma daman na yi alƙwarin sai na je wannan karon. Nima sauke jakata na yi na tuɓe hijabi na fita na ɗauro alwala na zo na yi sallah bayan na idar Gwaggo ta ce ɗanwake ta yi na je na zuba na ci, ina son ɗanwake jikina na rawa na tashi na je na zubo na dawo ɗakin ina ci muna hira sai da na gama na sha ruwa sannan na ce mata daga asibiti na ke.
"Allah sarki ina fatan dai ba matsala ko? Sai na amsa mata da " Muna saka ran haka Gwaggo." Sai ta yi min fatan Allah ya sa a dace ta ce min akwai na gargajiya a can gida ta yi mgana za ta karɓo min na ce to bari in na gama shan na asibitin tukkuna. Tun da Alhajinmu baya nan Gwaggo na faɗa ma ƙarin auren Yallaɓai itama ta sha mamaki har sai da ta furta..
"Topha aure haka bagatatan Sadiya?
Ni kuma sai na ce mata an ɗaura ne amma ba a yi tariyan ba, duk da ban sani ba amma alamu sun nuna mini haka. Gwaggo ta yi fatan alheri nima kuma ta yi min nasiha ta ce sai na yi hakuri na kauda kai na ce mata in sha Allahu. Ina gida tare da Gwaggo muna ta hira sai gabda la'asar na yi ma Gwaggo sallama na ta fi gida bayan na ce a gaida Alhajinmu in ya dawo.
Ina komawa gida na yi salla na shiga kitchen kuskus na dafa mai kayan lambu da hanta. Sai na yi lemun ginger na saka a fridge ya yi sanyi, Yallaɓai ya ba ni mamaki ko ya kirani? Har wayata na dinga dubawa amma bawan Allah bai kirani ba sai kuma abin ya dameni ai ya ga saƙo na ko? Wata zuciyar ta tunaar da ni yanzu fa ba ke kaɗai gare shi ba bai zama lalle sai ya damu da ke kamar baya ba. Ina ta so yakice tunanin haka a raina amman na kasa gaskiya kishi akwai wahala gabaɗaya har na fara rama a tsaye saboda zullumi da tunani ban sani ba.
******
Gwammaja.
Wajajen takwas da wani abu na dare ya shigo anguwan gwammaja a motar shi. Ko a cikin gidan ma ya daɗe a mota ya kasa fitowa bayan ya kashe motar. Gabaɗaya jikinsa ya yi sanyi ko na ce ya mutu. Ƙwaƙwalwarsa ta tsaya cak ya kasa ma wani tunani tun safe ya ce tun bayan barowansa wajen gaisuwan nan ya ji kamar zazzaɓi zai kama shi, ya je office ya yini amma ya kasa taɓuka komai kamar mara lafiya.
Ya na gani Sadiya na kiran shi ya kasa ɗaga kiranta to me zai ce mata! Akwai wasu kalaman da zai iya kare kanshi ne da su ne? Ya ga saƙon ta ok ɗin ma da ya tura mata hannunsa na rawa ya tura mata, domin gani ya ke yi duk abin da ya ce ko zai ce a baya da yanzu Sadiya ba za ta daina masa kallon maƙyarci ba kuma ma ci Amana ba, duk da ba haramci ya aikata ba. Amma dai ba daɗi shi kan shi ya sani bai kyauta ma Sadiya ba
Sai a lokacin lda suka haɗu da Yaya Abubakar a wajen jana'iza bayan sun gaisa ya yi masa murnan aure ya kuma ce Sadiya ce ta sanar dasu. Tun daga lokacin ya ji jikinsa ya mutu. Ashe ashe tuni Sadiya kallonsa kawai ta ke yi bai sani ba! Sai a lokacin ma ya riƙa tunano attitude ɗin da ta riƙa bashi tun ranar Anniversary ɗin su, bai taɓa kawo ma kansa labarin auran sa da Gimbiya ta ji ba, Bai taɓa tunanin roƙon da ya yi ma ƴan'uwan shi da alfarman da ya roƙa ba su yi masa ba. Ya a ka yi sadiya ta ji wannan mganar? Sai a lokacin ya tuna abin da ta yi jiya lokacin da ta ga Gimbiya na kiran wayarsa a she duk a lokacin ta na dannewa ne amma ta sani kawai kallon shi ta ke yi.
Ya tuna a lokacin ya na hanya zai koma office daga wajen jana'iza ya kira Abba ya na faɗa masa Sadiya ta sani ba tare da shi ya faɗa mata ba.
"Laifinka ne Tafida me ya sa ka yarda ma aka ɗaura auran ba ka koma gida ka faɗa mata ba?
"Na so haka Abba amma Nene ta ce yanzu yanzu mu tafi Rano."
Ya bashi amsa cikin karaya. Kalmar ɗaya Abba ya sake faɗa masa sai ya ji ya ƙara jin mutuwar jiki.
"Kai ba ka jin shawara. Da tun tuni ka ji shawaranmu ni da Tariq da a bakin ka Sadiya za ta ji wannan mganar gashi yanzu an ɓata komai sai dai ka yi hakuri ka zuanar da ita ka yi mata bayani "
"Ba zan iya ba Abba. Ina jin kunya."
Tafida ya faɗa a marairaice.
"To sai wa zai iya faɗa mata in ba kai ba?
"Kai mana. Don Allah ka taimake ni ka zo ka yi magana da ita."
"Mtseww. Ni na ce ka yi auran? Can ta matse maka " . Daga haka Abba ya katse wayarsa ya bar Tafida da tattaradi.
Bayan tasowarsa daga office har gida ya koma amma wallahi ya kasa shiga ya kasa iya tattara kalaman da zai yi amfani da shi wajen kare kanshi a wajen Sadiya. Kawai sai kuma ga Kiran Nene da cewa ya zo gida tana son ganin shi, gaban shi ya faɗi domin a irin wannan kiran ne ya na zuwa a ranar bai yini ba sai da ya zama mijin Gimbiya abin da bai taɓa hasashe ba, ko ma yana hasashen bai kawo shi nan kusa ba.
*Janafty* *TKG*
04.
FHB CLOTHING Muna Dinka kowanne irin nau in dinkunan yara na zamani,Muna bada sari ga masu bukata haka Muna maraba da masu sayen dai dai Muna turawa ko Ina cikin sauki a Nigeria da makotan kasan mu . Amana shine taken mu . wtsapp no.08080266674 or call @08034109622
RANAR ƊAURIN AURAN GIMBIYA DA YUSUF.
Ya ji tsoro da kiran Nene shi a tunanin shi kiran gaggawan da ta yi masa ko jikinta ne ya tashi, kuma ta ce ya zo gida da gaggawa tana neman shi sai ya firgita shi ya sa ya fita ko ƙaryawan da Sadiya ta matsa ya tsaya ya yi bai yi ba ya ce sai dai in ya dawo. Bai taɓa kawo ma kansa hashashen ga in da kiran Nene ya dosa ba saboda a yana hanya ma kafin ya ƙariso gidan sai da ya kira lambar wayar Gimbiya amma ba ta ɗauka ba sai ya ƙara firgita a tunanin shi jikin Nenen ne ya yi tsanani. Hankalin shi bai ma kawo masa a muryanta bai ji alamun ciwo ko wani abu ba.
Karfe takwas da rabi na safe ya shigo gidan, ya haɗu da Hajiya iya a ƙasa suka gaisa kuma ya ga ba ta ce masa komai ba, bai dai ji hankalinsa ya kwanta ba sai da ya shiga falon Nene ya ganta zaune a kan kujera ta yi wankanta tas da ita kuma cikin ƙoshin lafiya sannan ya iya sauke ajiyar zuciya na samun salama da natsuwa. Bayan ya zauna a gefenta ya shiga gaisheta cikin ladabi ta amsa masa cikin fara'a da soyayyar da ta ke yi masa wacce ba ta iya ɓoyuwa a cikin idanuwanta.
"Ya wajen ita Sadiyan? Ina takwarata da Maimuna? Ina fatan duk kuna nan lafiya."
Kansa na ƙasa ya ce"Duk lafiya lau Nene. Su Jidda kuma suna makaranta sun koma tun jiya."
Kai ta gyaɗa kafin ta ce" Allah ya taimaka. Allah ya yi musu albarka gabaɗaya." Ya amsa da Amin Amin shuru na wani lokaci saboda ya ji falon shuru sai ya ɗan waiwaya ya kalli ɗakin da Gimbiya ta ke kwana ya gansa a kulle sannan ba alamun ta na ciki sai ya juya ya na kallon Nene lokaci ɗaya ya na faɗin" Ke kaɗai ce Nene? Daugther ta fita ne?
"E. Ta fita yanzu ba daɗewa an kirata daga wajen aikinta."
Sai ya jinjina kai kafin ya ce" Ina hanyan zuwa nan ma na kira wayarta ba ta shiga. Ni fa hankalina ya tashi da kiran ki Nene na ɗauka ko jikin ne ya tashi."
Sai da ta yi mirmishi kafin ta ce" Ko ɗaya lafiyata ƙalau Tafida." Sai kuma ta yi shuru shi kuma sai ya bi ta da Allah ya ƙara miki lafiya da tsawon kwana Nene." Ta amsa masa da Amin Allah ya sa.
Shuru ya sake biyo baya na tsawon mintina biyar. Ya na kallon Nene ya ji ko za ta ce wani abu. Amma ya ga ta yi shuru kuma ya san tun da ta kira shi akwai mgana. Sai ya gyara zama shi ya kauda shurun kafin ya ce" Nene akwai damuwa ne? Ko wani abu kike so na yi miki? Sai ta kalleshi, ko acikin ƴaƴanta Yusufa na dabam ne. Shi ne ya ɗibo kusan hallayar marigayi mahaifinsu. Shi ne kawai in ta yi shuru ya ke fahimtar ta na buƙatar wani abu amma ta na jin nauyin tambaya.
"Nene ki yi mgana mana. Komai kike so nan duniya zan iya miki shi ko da ya gagareni zan nemi taimako a wajen wanda zai iya yi mini alfarma domin na faranta miki."
Ya faɗa ya na matsowa kusa da ita. Sai ta ɗago ta kalleshi kafin ya ji ta saka hannayenta duka biyu ta kama duka hannayensa lokaci ɗaya ta na faɗin" Alfarma na ke so na roƙa a wajen ka Tafida. Amma kar ka ji a ranka ko na tursasa ka ne, ina so komai da zai faru ya zama da amincewarka da yardan ka ne."
Cikin mamaki ya kalleta kafin ya ƙara jimƙe hannayenta ya na faɗin" Nene ni ne fa Tafida! Umarni kawai za ki ba ni na cika miki shi ai tsakanin mu ba alfarma Nene." "Akwai Tafida. Akwai alfarma a tsakanin uwa da ɗanta. Nima yau albarkacin wannan alfarman na ke so na ci a wajen ka Tafida." Da sauri ya ce" Faɗi ko miye Nene, ni ko zan cika mganarki da sunan umarni ba alfarma ba."
Ta na mai kallonshi hannuwansu sarƙe cikin na juna ta ce" Tafida ka san a shekarun baya da ka kawo mganar auran Sadiya na goya maka baya a lokacin da ƴan'uwanka suka ƙi fahimtar ka ko? Sai ya gyaɗa mata kai amma gabanshi na faɗuwa domin bai gane in da mganar Nene zai dosa yanzu kuma ba.
"Har ga Allah tun ganin farko da na fara yi ma Sadiya a cikin falon nan nawa a shekarun baya na yaba da hankalinta na kuma san ka yi dacen samun mata tagari. Sadiya ba ta gazamin ba kuma ba ta yi min komai ba wallahi sai ma tarin alherinta zuwa gareni." Ta ɗan dakata tana kallonshi kuma shi har ga Allah ya ƙosa ya ji in da mganganun Nene suka dosa. Ajiyar zuciya Nene ta sauke kafin ta ce" Tun muna ƴan mata ni da Hajiyar Tafida muka yi alƙwarin da fatan in mun yi aure mun hayayyafa za mu yi haɗin auran zumunci a tsakanin y'aƴaƴyanmu domin ƙara karfafa zumuncin da ke tsakanimu, sai ga shi kuma mun auri mazaje abokai, sai amintan mu ya yi girman da mutane ma suna kwatance damu. Tafida tun da na haife ka na ji a raina kai ne za ka iya cika mini wannan alƙwarin. Zaman ka a Rano a gidansu Gimbiya da shaƙuwar da ke tsakaninku sai muka sakankance za ku dai dai ta kanku har burin mu ya cika kwatsam sai ka zo mini da mganar Sadiya."
Zuwa yanzu kam jikinsa ya yi sanyi shi ai ba yaro ba ne tuni ya fara fahimtar in da maganganun Nene suka dosa amma bai katse ta ba, gwara ya ji ta har ƙarshe domin ya san a ina za ta dire mganganunta. Ita kuma kallon shi ta ke yi ta na ƙara nazarta yanayin sa. Amma ko a fuska bai nuna mata wata alama da za ta ce mganganunta ba sa yi masa daɗi ba. Sai kawai ta cigaba da faɗin.
"Na so ka da Saudatu Tafida kamar yadda Hajiya itama ta so hakan sosai wanda har sai da ta furta mini tun a wancan lokacin. Amma saboda kai ka kawo Sadiya kuma ka nuna ita kake so a lokacin in na ce ka bari za ka bari kuma za ka yi min biyayya ka auri Gimbiya sai dai na yi tunanin na zama azzaluman uwa tunda na hana ka abin da kake so domin ni na wa cikar burin shi ya sa ban taɓa yi maka mganar ba na taka ma su Bahijja burki a kan ƙin auran ka na ce su yi maka fatan alheri, domin ko suma a lokacin da Gimbiyar suke hangenka. Amma suka danne saboda na ce su bar mganar matan mutum ai kabarinsa. A lokacin da mganar auranka ya samu Hajiya ko da ba ta furta ba, ni na san ba ta ji daɗi ba amma sai ta yi fatan alheri a gare ku gabaɗaya. Na yi ta zura ido na ga ko za ka fahimci Gimbiya na sonka amma sai na ga ba ka nuna wata alama ba, wataƙila ka fahimta amma sai ba ka ba ma hakan muhimmanci ba. Gimbiya ta yi ta zaman jiranka ta na ture manemanta a yaƙininta cewa wata rana za ka iya fahimtar irin ƙaunar da ta ke yi maka. Amma sai ka kasa fahimtar ta, duk shekarun da ta ɓata ba ta yi aure ba ta kasa fidda yaƙini be a kanka ne, sai daga baya da ta fahimci ka fahimceta kawai dai ra'ayi ne a kanta ba ka dashi sai iyayenta da ƴan'uwanta suka yi mata faɗa har ta fidda wannam mijin ta aura sai ga shi cikin hukuncin Allah zaman bai yi tsawo ba ya rasu ya barta. Ta dawo gida ta yi idda ta gama gashi yanzu ta dawo nan wajena da zama."
Sai Nene ta dakata ta na sauke numfashi har kuma lokacin Hannayenta na hannun Tafida ya damƙe sanyin da jikinsa ya yi ya sa gabaɗaya ya kasa motsi ya na ji zufan hannun shi na jiƙa tafukan hannayen Nene da ke cikin na shi.