Turken gida book 2 cmplete by janafty - Chapter 7
Turken gida book 2 cmplete by janafty Chapter 7: Turken gida book 2 cmplete by janafty Chapter 7. "Yusufa."
3,371 words
"Yusufa."
Yusufu wani suna ne da in Nene ta kira shi dashi ya san mgana ce mai muhimmanci. Ba ta kiran sunan shi sai dai ta kira shi da Tafida. Shi ya sa ya na jin haka ya ɗago da kansa ya na kallonta cikin dakiya ya amsa mata. "Na'am Nene" Ya amsa mata ya na tattaro dukan jarumtarsa a gabanta amma a ƙasan zuciyarsa ya yi rauni. Domin hasashen sa bai taɓa kawo sa ga wannan bingiren da Nene ta kawo shi yanzu ba.
"Ka taɓa fahimtar har yanzu Gimbiya ba ta daina sonka ba? Ko ka taɓa lura da cewa har yanzu ba ta cire tsammani da yaƙini da cewa za ka iya zama na ta ba?
Tambayoyin Nene sun yi masa tsauri da ya kasa cewa komai.. Sannan gashi ta ƙura masa ido ta na jiran amsarsa. In ya ce bai taɓa sanin Gimbiya na son shi ba ya yi ƙarya domin tun tana kunya har ta fito ma da alamomin da suke bayyana cewa ta na son shi, ba ma shi ba har mutanen da ke kusa da su sun fahimci irin soyayya da Gimbiya ta ke yi masa. Da farko shi ma ya ɗauka ya na sonta ne sai da ya haɗu da Sadiya anan ne ya fahimci ba so ba ne shakuwa ce kawai da haɗuwar jini. Sadiya ita ya ji ya na yi ma soyayyar da Ubangiji ya hallita tsakanin mace da namiji. Amma bai taɓa ƙin Gimbiya ba, sannan har gobe ta na daga cikin foverite ɗin mutane a wajensa amma bai taɓa tunanin ya saka tunanin auran ta a ran shi ba, ba kuma domin ba zai iya auranta na ta ba sai domin tunanin hakan bai taɓa shiga ƙwaƙwalwarsa ba ne.
"Shurun ka na nufin amsarka da E Tafida"
Nene ta katse masa tunani, ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce" Nene ba ni ba duk wanda ke tare da mu zai iya shaida akwai kyakyawan alaqa tsakanina da Gimbiya. Amma." Hannu ya ga Nene ta ɗaga mai tana kallonshi kafin ta je fa masa wata tambayar da ta ƙara rikita shi.
"Kana son Saudatu!?
"Za ka iya zaman aure da ita?
Sai ya kasa mgana bakinsa na rawa ya na so ya yi mgana ya kasa. Tambayoyin suna da girma da tsauri in aka ce ya amsa su nan take kamar ana so ya yi gaggawa ne. A bari ya samu kamar sati ɗaya daga shi sai zuciyarsa ya gani ko za ta iya amsar tambayoyin Nene amma ina Nene ba ta bashi wannan damar ba yana ƙokarin mgana ta ƙara tare shi da faɗin" Ba buƙatar dogon lokaci ba ne Tafida ka faɗamin shin za ka iya auran Saudatu kuma ka yi zaman aure da ita?
"E. Amma Nene.."
"Ka gama min komai Tafida. Na gode da afarman ka. Na gode da biyyarka. Na gode da kyautatawarka a gareni. Allah ya saka maka da gidan aljannah. Allah ya shirya maka zuru'a ya yi ma rayuwarka da duk abin da ka saka hannu a kai albarka Na gode." Nene ta faɗa ta na zare hannayenta daga cikin na shi sai kuma ta fara sharan ƙwalla ganin haka sai bakin shi ya mutu Nene na share hawaye ta na ta saka masa albarka da addu'o'in gamawa da duniya lafiya su suka haɗu suka ƙara kashe masa baki da zuciya gabaɗaya.
Ya ɗauka iya mamakin da Nene za ta gama bashi kenan ashe ba shike nan ba. Umarni ta bashi da cewa ya kira mata Zuwaira da Maimuna da Bahijja suma su taho gida yanzu tana son mgana da su. Ya ɗauka dai kan mganar da suka gama shi ya ke kiran su da wayarsa amma sai Nene ta karɓa ta yi musu mgana Zuwaira(Mimisco) ta fara zuwa tunda ita ce lokacin da aka kira ta ta na makaranta ta ce ma za su yi meeting ne amma ba ri ta saka a ɗaga zuwa anjuma sai ta taho. Sauran kuma suka ce yanzu za su shirya su taho suma dai hankalinsu ya tashi sun ɗauka jikin Nene ne sai da ta basu tabbacin ka da su damu ta na lafiya sannan hankalinsu ya kwanta suka ce ga su nan zuwa.
Lokacin da Mimisco ta iso gidan ta ɗan yi mamakin ganin Tafida zaune, amma sai ba ta yi mgana ba ƙila dai ya shigo gidan ne amma dai tana tunanin da akwai dalili acikin kiran na Nene. Kalaman da Nene ta furta ma Mimisco ne ya sa ɗan sauran gudun jinin da ke tafiya a jikin Tafida ya tsaya cak!
"Zuwaira Rano na ke so mu je a yau yau ɗin nan."
"Rano kuma Nene! A yau kuma?
Ta faɗa ta na kallon Tafida shima ita ya ke kallo amma ya kasa mgana sai ta maida hankalinta kan Nene ta na faɗin" To wani abu ya faru ne a can Nene? "Ba abin da ya faru sai Alheri. Aure na ke so yau a ɗaura a tsakanin Tafida da Saudatu."
Shi dai sai da ya ji yam! tsigogin jikinsa sun tashi. Numfashi ya yi sama sannan ya jawo shi ya dawo. Mimisco ko ido ta zaro ta na kallon Nene tana kuma kallon Tafida kafin ta ce"Wata Saudatun kuma Nene? Domin ita sai ta ji ma ta manta wacece Saudatun.
"Gimbiya ta mu."..
"Topha yau shi Tafidan da kan shi ya ce ya na son ita Gimbiyan! Sannan ya ce a yau ya ke son a ɗaura auran?
Mimisco ta faɗa cikin ƙarin mamaki, ta na kuma mai kallon Tafida da ya kasa mgana. Nene ce ta yi mata bayanin komai ta ƙara da cewa" Tunda har ya ce zai iya zaman aure da ita me za mu jira Zuwaira! A ɗaura kawai daga baya sai a yi mganar tariyan" Mimisco ta kasa mgana Tafida ta kalla sai taga itama ya kalleta yanayinsa kawai ta kalla ta fahimci a bazata mganar Nene ta zo masa in kiya ya yi mata ido itama sai ta yi masa alamun ya yi mgana mana.
Sai gani suka yi Nene ta miƙe tana faɗin" Bari na kira Hajiya na faɗa mata muna tafe." Ta faɗa cikin murna wanda har ya bayyana a muryanta. Mimisco ta yi saurin cewa"Nene dawo ki zauna." Sai ta juyo ta na kallonsu kafin ta dawo ta zauna ta na faɗin" Me ya faru ne? Mimisco ta kalli Tafida kafin ta ce" Ka yi mgana da Sadiya ne?
Sai a lokacin ma ya fahimci ƙura ne turƙe a gaban shi bai sani ba, sai ya girgiza kansa kafin ya ce" Yanzu yanzu Nene ta yi min mganar kuma a yanzun ta yanke wannan hukuncin." Sai Mimicso ta kalli Nene kafin ta ce" Nene ki yi hakuri ki ba shi dama ya je gida ya yi mgana da matarsa zuwa gobe sai a yi yarda kike so." Amma Nene ta ce ba ta amince ba, ya kira Sadiya a waya ya faɗa mata kuma ai yana da sauran lokaci.
"Waya kuma Nene? Gaskiya bai kyautu ya yi mata waya ba. Sai dai in haka kike so a je a ɗaura ɗin daga baya sai ya yi ma Sadiya bayani." Nene ta ce hakan za a yi kuma ta san Sadiya za ta fahimcesa. Ba yadda ya iya har Mimisco ba ta so gaggawan ba amma ba yarda ta iya Nene ta dake har ta Kira Hajiya ta ce suna nan tafe, Bahijja ta fara zuwa daga baya sai Maimuna suna jin ƙudurin Nene suka haɗa baki suna rangaɗa guɗa su lamarin ya yi musu daɗi matuka sannan Nene ta biya su. Da dai Tafida ya ga da gaske Nene ta ke sai ya roƙi su Bahijja da don Allah su yi shuru da wannan mganar kar Sadiya ta ji. Ya na so ne in ma za ta fara ji sai daga bakinsa har suka ɗan samu cacan baki da Bahijja domin ta ce bai isa ya hana su nuna farinciki ba.
Sai da Mimisco ta shiga tsakani ta ce ya na da gaskiya. Za su tarwatsa masa gida ne ai ya na da gaskiya kuma mganar aure ai ba mganar wasa ba ne. Da haka dai suka yi alƙwarin ba za su fidda maganar ba. A lokacin ko awa ɗaya ba su ƙara a Kano ba suka ɗau hanyar Rano da shi da Nene da Mimisco da Bahijja Maimuna ta koma gidanta. Suna kuma zuwa Nene ta isar da kudurinta sai da Hajiya ta tashi ta rumgumeta ta na mai nuna farincikinta a gidan Tafidan Rano ƙanin baban Gimbiya aka ɗaura auren Yusuf da Saudatu kan Sadaki naira dubu 100k. Kuma ba a ɗaura ba sai da shi Waliyin nata ya kira ta a waya ya tambayi izininta tunda bazawara ce kuma addini ya ba ta wannan damar ita kanta a ba za ta ta ji mganar wai ta na son Yusuf? Domin ga waliyanshi sun iso domin nema masa auranta. Da rawan jiki da na zuciya ta amince, a cikin office ɗin ta bayan Anty Bahijja ta kira ta ta ce an ɗaura auran ta da Tafida sai da ta faɗi ta yi sujjudar shukur ta na hawayen farinciki atleast dai yau burinta ya cika tabbas kar bawa ya cire tsammani duk abin da ya ke rabon ka ne ko ya hau sama sai ya faɗo a kanka. Alhamdulillah.
Bangaren Tafida Kawu Sa'adu ne da su Abba suka karɓa masa auran Sadakin kuma Nene ce ta biya da kuɗinta saboda yadda ta ke son Tafida da Saudatu. Bayan an gama ɗaura aure kuma acan gidan Hajiya aka fara ɗora girki na sadaka, bakinta har kunne ta kira sauran Ƴayanta a waya duk ta sanar da su kafin ka ce kwabo labari ya zaga Rano da kewayenta. Abba shi kan shi ya yi mamakin auran nan cikin gaggawa da Mimisco ya yi mgana ita ce ke yi masa bayanin yadda lamarin ya fara. Amma Yusuf bai iya ba, domin lamarin kamar a mafarki ya ke gani. Duk roƙon da ya yi musu sai da Bahijja ta ɗora a status a tunaninta ta cire Sadiya ko ta manta da Ma'u ne?
Ko Tariq da ya ji yadda asalin lamarin ya faro ya ji wani iri. Duk da Gimbiya ƙanwarsa ce kuma ya na yi mata murna, amma bai ji daɗin yadda Tafida ya amince aka ɗaura aure ba tare da ya yi mgana da Sadiya ba shima Abba haka ya ce amma sun yi ta ba sa shawaran da ya koma gida ya sanar da ita gudun samun matsala, amma sai ya ji ya kasa ya na gani ta na tura masa saƙon Anniversary ɗin su sai a lokacin ma ya tuna muhimmancin ranar a gare su, sai dai ina ranar kuma sai ta rikice ta koma rana mara daɗi ga Sadiya ba zai iya kashe mata karsashinta wannan ranar ba, shi ya sa har ya gama nuku nukunsa ya koma gida ya kasa iya faɗa ma Sadiya wai shi ya ƙara aure ba tare da ta sani ba. Ya kusa shafe sama da awa ɗaya a waje ya kasa iya shigowa ga shi dai ba abin kunya ya aikata ba amma yana jin tsoro da kunyar haɗa ido da Sadiya a wannan yanayin.
Lokacin da ya shigo gidan suka haɗa ido da Sadiya sai ya ji kunya kwataƙwacin kamar ya ci amanarta haka ya ji. Ya kasa iya sarrafa kansa a gabanta. Har aka wayi gari yana cikin wannan yanayin sai daga baya ne ya fara warwarewa. Bai taɓa tunanin Sadiya ta ji mganar auran shi ba, duk da dai mganar ta zagaya dangi tunda ana ta kiran shi ana masa fatan alheri. Ya yi ta mamakin duk labarin ya je ma kowa, a tunanin shi Sadiya ba za ta sani ba shi ya sa ya ke ta shirye shiryen yadda zai tunkare ta da maganar sai ga shi duka shirinsa ya rushe. Ga shi shagon da ya kama mata har ya biya kuɗin shekara key na hannun shi, kunya da nauyin sun saka ya kasa yi mata mgana, balle yanzu in ma ya nuna mata a zuciyarta za ta ce ba domin Allahya yi ba saboda ya yi mata kishiya ne shi ya sa ya kasa bata. Ya tuna jiya har sai da Musbahu ya yi masa mganar shagon.
"Yaya Tafida wai ƙasa za mu koma ne?
Sai ya girgiza masa kai a lokacin. Domin shi kan shi bai san mafitan shi a lokacin ba. Sanin da Sadiya ta yi ba tare da ya faɗa mata ba ya yi masa mumnunan duka, saboda yanayin da ya ke ciki tun da aka ɗaura auran sau biyu suka taɓa waya da Gimbiya gidan ma sau ɗaya ya je suka haɗu bayan kuma gaisuwa wata mgana mai tsawo ba ta shiga tsakaninsu ba, ya fi so sai ya gama da Sadiya sun samu daidaituwa kafin wata mgana ta biyo baya. Ya tsara a jiya zai yi mata mgana ya sanar da ita sai kuma Allah bai so ba ya yi tunanin yau ɗin in ya koma gida amma tun haɗuwarsa da Yaya Abubakar gabaɗaya tsarin sa ya ruguje mafita ya ke nema ya rasa mafitan. Shi ya sa ya kasa iya komawa gida da wuri ya kama hanyar gidan da dadaddren kenan kuma sai ga kiran Nene ya riskeshi.
******
Ya na cikin motan bai fito ba sama da mintina talatin. Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi. Wayar sa ya laluɓo a gaban Aljihunsa ya sake kiran Abba. Yana ɗauka bai ko jira sun gaisa ba cikin roƙo ya fara faɗin" Don Allah Kawu ka taimaka min ka zo gida gobe ka ta ya ni fahimtar da Sadiya don Allah."
Daga can bangaren Abba ya ce" Sai kuma ka yi. Wallahi ba in da zan zo. Kai ba ka da baki ne? Ko kai ba Namiji ba ne? A sanyaye Tafida ya ce" Kunyar ta na ke ji fa." "To ai sai ka murje kunyar ka sanar da ita. Duk da dai bakin alƙalami ya riga ya bushe. Sai dai ka yi gyaran mgana daga baya."
"Kai yanzu don Allah ba za ka zo ka yi mgana da ita ba?
"Wallahi ba zan zo ba. To ni me ye nawa! Ni ne mijinta? Kai ne mijinta kai ya dace ka zaunar da ita ka koyo kalaman haƙuri da kare kai har sai ta fahimceka. Kai fa namiji ne kuma ka fi ni sanin matarka sosai ka san kuma hanyoyin da za ka bi da ita har ta fahimceka. Amma ni dai na roƙe ka don Allah ka daina saka ni a cikin wannan mganar."
Ko ma ya jira cewar Tafida ya kashe wayarsa ya bar sa cikin damuwa da tararradi Ya daɗe zaune yana tufka ya na warwara amma duk in da ya kamo ya fara tufka sai ya warware ya kasa samun mafita guda ɗaya da zai kama. Dole dai ya buɗe mota ya fito a kasalance kamar mara lafiya ya wuce cikin gida saboda dare ya yi kowa na cikin ɗakin shi, ɗakin Maman Farko ya leƙa suka gaisa daga nan ya wuce shashen Nene falon shuru har sun rage haske alamun sun kwanta da ya yi sallama ne ya ji muryan Nene daga ciki ta na amsa masa, sai ya cire takalminsa nan ƙofar falo ya shiga har cikin bedroom ɗin Nene
Ya iske ta har ta kwanta ma ganin shi ya sa ta miƙe zaune bayan ta miƙe kafafunta ta na faɗin" Tafida sai yanzu? Ya na sosa kansa ya ce" Wallahi na tsaya gamawa da Office ne Nene" Ya faɗa dai dai ya na zama gefen kafafunta a gefen gadon. Gaisawa da tambayan iyalan shi ya ce suna lafiya kafafunta ya ɗauka ya ɗora a saman cinyarsa ya na matsawa.
"Suna ciwo ne yanzu?
Ya faɗa ya na kallonta lokaci ɗaya kuma yana ƙara matsa mata kafafun duka biyun.
"Ba sosai ba. Saudatu na shafa min man zafi in zan kwanta."
Kallonta ya yi kafin ya ce" Amma yau dai ba' a shafa ba ko? Ban ji zafin sa ba " Ya faɗa ya na shinshina hannunsa.
"E. Ba ta jin daɗi yau kanta ke ciwo ta ce min da wuri ma ta baro wajen aikinta." Cikin nuna jimami ya ce" Subhanallah ta sha mgani? "E. Ta sha da sauƙi ta ce bari ta kwanta ne. In ka tashi tafiya sai ka shiga ka duba ta." Sai ya amsa mata da toh sun ɗan fara taɓa hira ganin dare ya yi ya sa ta kalle shi kafin ta ce" Kan mganar Saudatu ne daman."
Sai ya maida hankalinsa a kan Nene ganin haka ya sa sai ta cigaba da faɗin" Na ga an kusa yin sati da ɗaurin auran ku kuma ban ga kana zuwa ba, ballantana ma ku yi mganar yadda za ku tsara tarewar na ta." Shuru na wani lokacin kafin ta ƙarƙare da faɗin" Shi ne daman na kira ka na ce ka zo na ji ko lafiya?
Shuru ya yi kafin ya sauke numfashi. "Nene." Ya kira ta amsa kafin ya ce" Daga ke har Gimbiya ku ɗan ƙaramin lokaci don Allah" "To shike nan" Nene ta faɗa ta na kallon shi a yanayinsa kawai ta gane akwai damuwa. "Akwai matsala ne Tafida? Sai ya gyaɗa kai da sauri ta sauke kafafunta ƙasa ta zauna dakyau ta na faɗin" Sadiya ce?
Sai ya ƙara gyaɗa mata kai ya ce" Ta ji labari Nene ta ji labari." Cikin mamaki ta ce" Ta ji labari? Ba ka gaya mata ba ne daman? Nan ma kai ya gyaɗa mata kafin ya ce" Na kasa faɗa mata ne. Ina ta riƙe mganar daman yau na ke shirin faɗa mata sai kuma na haɗu da yayanta wajen jana'iza sai gashi yana min murna kuma ya ce ita ta faɗa musu na ƙara aure." Ya karishe faɗa kamar zai yi kuka Nene ta dafa kanshi kafin ta ce" Ka kwantar da hankalinka. Kuna da fahimta kai da Sadiya. Yanzu ka tashi ka tafi gida ka zaunar da ita ka yi mata bayani na san za ta fahimta.'
Sai ya gyaɗa kanshi kafin ya kalli Nene ya na faɗa min" Nene abin mamaki a ina ta ji! Kuma wa ya sanar da ita? Nene ta ce" Sanin wanda ya faɗa mata sai Allah. Amma ba abin mamaki ba ne domin ta ji labari. Magana in ka iya rufe bakin wani, ba za ka iya hana wani mgana ba. Ka yi kuskure da tun lokacin ba ka faɗa mata ba, amma yanzu ma baka makara ba ka tashi ka je gida ka zaunar da ita ka yi mgana da ita cikin Sigar da za ta fahimcen ka ka ji ko? Sai ya gyaɗa mata ɗan shafa kanshi ta yi kafin ta ce" Tashi ka je. In sha Allahu ba matsala."
Da haka suka yi sallama bai fita ba sai da ya ga ta koma ta kwanta har ya ɗan rufa ma ƙafafunta bargo ya kashe mata fitilan ɗakin sannan ya fita. Har ya kai ƙofa zai fice sai ya tuna da Nene ta ce ya shiga ya Duba Gimbiya sai ya fasa fitan ya dawo zuwa ɗakin da Gimbiyar ke ciki ya ƙwaƙwansa sau biyu daga ciki ta ce a shigo sai ga shi ya buɗe a hankali ya shiga da sallama.
Ta amsa masa sallamansa tana zaune a gefen gado amma ta saka wani ƙaramin hijabi hasken ɗakin a kunne ya ke alamun ita ta kunna. Sun haɗa ido ita dashi sai ya yi mata mirmishi itama sai ta mayar masa. Tura ƙofar ya yi ta rufe kanta sannan shi kuma ya fara takowa zuwa gabanta da jikin wadrope ɗin da ke ɗakin ya Jingina wanda a baya babu shi a ɗakin ita Gimbiyar ne ta saka a ka yi mata anan garin.
"Sannu ya jikin? Kan ya daina ciwo?
Ya kauda shurun da ke tsakaninsu tun bayan gaisuwan da ya shiga tsakaninsu.
"Da sauƙi."
Ta faɗa a hankali, cikin sanyin murya. Sai ya yi mata fatan samun sauƙi kafin ya ce" Kin sha mgani? Sai ta ɗago ta kalleshi kafin ta ce" E. Na sha." Shuru na wani lokaci ba tare da tsammani ba kanta na ƙasa ta ga ƙafafunsa a gabanta kafin ta ɗago kanta ta ji tattausan hannunsa bi sa goshinta sai da ta runtse ido cikin wani yanayi.