Kenza eBookz

Turken gida book 2 cmplete by janafty - Chapter 8

Turken gida book 2 cmplete by janafty - Chapter 8

Turken gida book 2 cmplete by janafty Chapter 8: Turken gida book 2 cmplete by janafty Chapter 8. "Uhm na ji kan na ki ba zafi sosai."

3,359 words

"Uhm na ji kan na ki ba zafi sosai."

Haka ya faɗa ya na yin baya kaɗan. Ajiyar zuciya ta sauke a hankali saboda yanayin da ta ke ciki. Ya juya kamar zai fita daga ɗakin ya na faɗin. "Allah ya ƙara lafiya. Ki kwanta ki huta kin ji ko? A ƙasa ƙasa ta amsa da Amin.

Har ya saka a hannu a jikin handel ɗin ƙofar sai kuma ya juyo daman itama kallon shi ta ke yi sai suka haɗa ido. "Daughter." Ya kira sunanta kamar yadda ya saba. "Na'am Daddy." Shuru ya yi na wani lokaci kafin ya ce" Na faɗa ma Mamanki ke da ita ku ɗan ƙaramin lokaci kaɗan. Ina so na ɗan gama da wasu abubuwan ne first daga baya sai na zo mu yi mgamar tarewar ki ko?

Ya faɗa ya na mai kallonta da sauri ta sunkuyar da kanta kafin ta ce" To." Ta na mirmishi, shima mirmishin ya yi mata sannan ya juya ya na faɗin" Sai da safe." "Gud night." Itama ta bashi amsa har ya fita ya rufe mata ƙofa ba ta daina mirmishi ba ya na fita ta faɗa gado ta na tsalle da kafafunta lokaci ɗaya ta na rufe bakinta. Ta ji shigowarsa falon Nene tun farko har leƙensa ta yi bai sani ba ta na ta Allah Allah ya shigo ta gan shi ko za ta ji daɗi sai ga shi Allah ya amsa roƙon ta. Wani irin rawa zuciyarta ya ke yi na soyayya da ƙauna har yanzu ba ta daina godema Allah ba domin ya gama yi mata komai. Ubangiji ya gama ba ta komai anan duniya tunda har ya mallaka mata Yusuf. Za ta iya jiransa ko nan da shekara ne ba dai an ɗaura ba ai an gama mai wahalan.

*****

10:50pm

Goma da minti Hamsin Yallaɓai ya shigo cikin bedroom ɗin mu. Ina kwance da waya a hannuna ina dannawa shi ya sa ma na duba lokacin. Na so na yi barci kafin ya dawo barcin ne ya ƙi zuwa dole na ja wayata na kunna data ina ta shige shige. Mun yi chart da Amina sai Munnira. Sannan kuma mun yi waya da Sameena ƙanwar Gimbiya yadda ba ta min mganar auran Yallaɓai ba, nima ban yi mata ba na san ta sani kawai ba ta so ne ta fara ɗauko min mganar amma mun yi hira da ita sosai.

Ni Munnira ke ba ni mamaki ta ƙi yi min mganar ni a tunanina ko wani zai ɓoye min su sai su ɓoye min amma ina jiran su wallahi sai na yi musu wankan soso da sabulu. Datti ma da daren nan ya kira ya na ce min ashe Yallaɓai ya yo amarya Amina ke faɗa masa shi bai damu ba dariyan shi ya ke yi to daman su maza ina ruwan su ko uku Yallaɓai ya ƙaro min lokaci ɗaya na tabbata cewa za su yi ya yi dai dai. Ko a jikinsu tunda daman duk halinsu ɗaya na son kansu.

Kafin ya dawo ba tunane tunanen da sheɗan bai gayyato min ba, in na runtse ido sai na riƙa hasko shi da Gimbiya a cikin yanayin da kan iya haifar min da hauhawan jinina sama. Lokacin da ya shigo da sallama na yi niyyar ne na ƙi amsswa amma sai na taushi zuciyata na amsa masa ta gefen ido ina kallon shi, domin ni kawai na saka a raina ya na wajen Gimbiya wato tun kafin ta tare ya fara raba ma na yini saura kwana kenan. Wanan malolon abun da ya ke cikin ƙirjina tun san da na ji labarin auran sa da bai wuce ba har yau shi ne ya taso min. Daƙyar na iya daurewa a shaƙe na yi masa sannu da zuwa sai na ga shima bai kalleni ba ya amsa kawai.

"Ya gidan ne? Ya kika je kika samu su Alhajin?

Ashe ya tuna in da na je. Ba ya kallona kayan jikinsa ya ke tuɓewa. Nima sai na kauda kai kafin na ce" Duk suna lafiya." Daga haka na cigaba da duba waya ta a IG har Volume na ƙure da gangan saboda haushi bai kalleni ba, kuma bai ƙara mgana ba bayan ya bar gajerun wando na ga ya fita sai na ji ƙaran ƙofa kenan ya shiga Tiolet wanka ya yo ya fito ina nan in da ya barni kwance, ina ta nazarinsa ta gefen ido, har ya gama shirin barcinsa na ga bai yi min mgana ba kuma ya na shirin kwanciya sai na daure na waiwaya ina kallon shi kafim na ce"

Abinci fa na Dinner."

Sai ya kwanta a can gefensa sannan ya ce" Ba na jin cin wani abu yanzu." Daga haka sai na ga ya juya min baya kawai ya yi kwanciyarsa. Mamaki ya kamani amma na kasa mgana sai nima ma juya masa bayan ina sakin ƙaramin tsaki kuma na tabbata ya ji ni. Amma bai yi wani motsi ba, da gayya na yi ta shiga Yuotube ina shiga waƙoƙi ina ji domin na dame shi amma har na gaji bai motsa ba, ba ni na kwanta ba sai 12pm sannan na ijiye waya da na ji barci, ina yin addu'an barci na runtse ido sai barci.

Zai da ya tabbatar da ta yi barci sannan ya juya yana kallon bayanta. Dole ne ya sa ya yi avoiding ɗin Sadiya ya rasa da idanuwan da zai kalleta abin da ya yi shi ne dai dai. Bai ma ɗauka zai zo ya same ta idanuwanta biyu ba. Ajiyar zuciya ya sauke ya yi kwanciyar rigingine ya na kallon rufin ɗakin na POP. Ya na kuma tunanin ta ina zai fara? Duk in da ya yi tunanin zai fara ta can sai ya ga hanyar ba mai ɓullewa ba ce, ya daɗe bai yi barci ba ya na faman juye juye amma har garin Allah ya waye bai samo mafita ba.

****

Saboda rashin barcin da bai samu a daram jiya ba ya sa tun bayan da ya dawo sallar asuba ya ke kwance ya na barci sai kiran wayarsa ce ta tashe shi. Sai ya ga Nene ce ke kiran shi da sauri ya miƙe zaune ya na daidai ta yanayinsa. Sannan ya ɗaga kiran. "Tafida." Ta kira shi bayan ya yi mata sallama.

"Na'am Nene ina kwana."

"Lafiya lau. Kana gida ne? Sai ya amsata mata da E. "Ka yi mgana da Sadiya jiya! Cikin kasala da muryan barci ya ce" Ban yi ba Nene." "To ka jira ni. Kar ka yi mata mgana."

Cikin mamaki ya ce" Me ya sa Nene? "Akwai dalili. Ka jira ni." Daga haka ta yanke wayarta sai ya bi wayar da kallo yana mamaki bai koma ya kwanta ba amma ya kishigiɗa da gado ya harɗe hannayensa a ƙirji ya na hasoso tunanin Nene na cewa ya jira ta. Bai taɓa tunanin shirin Nene na zuwa gidan shi ba ne sai bayam mintina talatin da wayarsu da Nene ya ji kamar ana buga get duk da ya san Sadiya na can cikin gida baya tunanin za ta ji, shima domin ya na cikin bedroom ne kuma window ɗin su na haraban gidan ne. Sai ya miƙe daga shi sai bakin wando da singleti ya fita falo sai ya ga Sadiya kwance a falon yara kallo take yi ko kawai ta na kwance ne bai sani ba.

Ina daga kwance na ga fitowarsa sai na yunƙura na miƙe zaune ina faɗin" Ina kwana." Sau ɗaya ya kalleni sai kawai ya yi gaba ya na faɗin" Lafiya lau.' Bari na je waje na ji ana buga get." Ya na gama faɗin haka ya buɗe kofa ya fice na rasa shi da kallon mamakim to wai har na fara masa baƙi a ido ne da ya sa Yallaɓai daga jiya zuwa yau ba ya son haɗa ido da ni? Zaune na ke ina mamakin shi, ni ko shigowar mota ma ban ji ba sai dai na ji kamar mgana daga falo sai na miƙe na kawo gabda ƙofa zan buɗe sai ya rigani turowa ya shigo sai muka haɗe ya kalleni na kalle shi.

"Nene. Nene ce ta zo."

Cikin mamaki na ce" Nene fa? Saboda ni dai tun da muka dawo gidan nan sau ɗaya ta taɓa zuwa shima rashin lafiya Baby ta yi shi ne ta zo duba ta. A wancan gidan kuwa har muka tashi ba ta taɓa zuwa ba.

"E. Ta ce ta na son mgana da ke."

Haka ya faɗa min kafin ya wuce. "Magana da ni? Na maimaita a cikin raina. "To wata mgana ce? "Ta wuce ta auran Yusuf da Gimbiya" Kamar wahayi haka na ji zuciyata na saƙa min magana. Uhm kawai nace a saman leɓena sannan na bi bayan shi domin na ɗauko hijabina ina shiga na ganshi ya saka riga zai fita ya raɓa ta gefena ya fice ni kuma na shigo ciki na ɗauko hijabin sallah na saka nima na bi bayan shi amma ni sai da na fara biyawa ta kitchen na dauko mata ruwa da lemu lokacin safe ne domin tara ma ba ta yi ba, bayan tafiyar yara makaranta ne ba daɗewa na kwanta a falon da Yallaɓai ya fito ya ganni kwance.

*Janafty* *TKG*

05.

Da sallama na shiga falon hannuna ɗauke da farantin da na ɗora ruwa da lemu tare da ƙananun kofunan glass a saman shi. Gabaɗayansu a tare suka amsa sallamata ashe Musbahu ne ya kawo ta ya na zaune gefen Yallaɓai a saman kujera mai zaman mutum ɗaya ɗaya. Ita kuma Nene ta zauna akan mai zaman mutum huɗu ne.

Sai da na ja center table ɗin da ke wajen na ɗora ruwan a kai sannan na durƙusa a gaban Nene ina gaisheta ta amsa cikin fara'a lokaci ɗaya ta na ba ni umarni na koma kan kujera na zauna sai na koma na zauna kan kujera mai zaman mutum biyu da ke gefen in da Nene ta ke zaune.

"Anty Sadiya ina kwana."

Musbahu ya gaisheni yana kallona na amsa ina faɗin kwana biyu idon sa kenan ya na yar dariya ya ce" Yallaɓan na ki ne har yau bai cire min ranar hutu ba shi ya sa bakya ganina" Mirmishi na yi amma ban yi magana ba, yadda Yallaɓai bai kalleni ba nima ban damu da na kalle shi ba domin tunda na shigo falon kansa na ƙasa ya yi shuru kamar wani mara gaskiya. Ko da ya ke ai mara gaskiyan ne tunda menene maraban dambe da faɗa?

"Ina takwarata da Maimunatu? An tafi makaranta ko?

Kaina na ƙasa na amsa ma da Nene da cewa" E Nene.' Sai ta rausayar dakai kafin ta ce" Allah ya ba da sa'a. Allah ya sa a samu karatu mai albarka." Muka amsa da Amin gabaɗayanmu. Shuru na wani lokaci domin shi Musabahu wayarsa yake ta latsawa ganin haka ya sa na gyara zama ina faɗin" Nene a kawo abun karyawa?

Da sauri ta ce" A'a Alhamdulillah. Sai da na karya a gida na fito sai dai in Musbahu ga shi nan." Ta faɗa ta na kallon shi, sai da ya ɗan yi shuru kafin ya ce" Tea kawai matar Yallaɓai." Sai na miƙe ina faɗin bari na je na haɗo masa, har na fice daga falon ba wanda ya ce mini komai, daman already akwai ruwan lipton a cikin fulas, sai kawai na soya masa ƙwai guda uku ina cikin soyan ma ya leƙo ya ce gashi a falon su Jidda sai na ce to ina gama soya kwan na kai masa nan tare da mug da fulas ɗin ruwan zafi sannan na kwaso masa kayan tea ɗin har da buredi.

"Sannu da aiki Anty Sadiya."

"Yauwa."

Na amsa masa ina ɗan mirmishi hannuna na wanke sannan na koma falon wajen Nene na koma na zauna kenan Nene ta kalli Yallaɓai da ke zaune jugum kamar wani marayan da ya zo neman abin sakawa a bakin salati.

"Tafida."

Ta kira sunan shi sai ya dago ya na kallonta lokaci ɗaya kafin ya ce" Na'am Nene." "Ba mu waje. Zan yi mgana da Sadiya daga ni sai ita." Da ni da shi gabaɗaya mun kalli juna sannan muka juya muna kallon Nene sai ta gyara zama kafin ta gyaɗa kanta lokaci ɗaya ta na ƙara jadadda mganarta.

"E haka na ce. Ka ba mu wuri mu yi mgana Tafida."

"To Nene."

Haka ya faɗa sannan ya miƙe a hankali kamar wanda ƙwai ya fashe ma a ciki haka ya fice daga falon lokaci ɗaya ya na mai rufe mana ƙofar falon a sannu kar ta yi ƙara. Da ga ni har Nene da kallo muka bi shi ni kuma da ita kowa a cikin ranshi ya na da nashi tunani, ni dai ko tausayinshi ban ji ba domin a ganina wannan shi ake kira daga baya kenan an yi sadaka da bazawara.

Shuru na ɗan wani lokaci kaina na ƙasa ina wasa da gefen hijabina na ji Nene ta kira sunana.

"Sadiya."

Sai da na ɗago na kalleta kafin na ce" Na'am Nene." "Na zo ne mu yi wata mgana da ke. Kuma kar ki yi tunanin ko mijinki ne ya turo ne" Na kalleta sai ta gyaɗamin kai kafin ta cigaba da faɗin" Ko ɗaya bai ma san zan zo ba. Bai kuma san da abin da na zo da shi ba, ni ce kawai na yi tunanin na ga lalle ya dace na zo na same ki mu yi mgana baki da baki."

"Haba Nene don wannan shi ne sai kin zo da kanki? Ai da kirana kawai za ki yi a waya na je gida na same ki " Na faɗa cikin sanyin murya amma cike da biyayya. Ko ban ɗauketa a matsayin uwata ba na ɗauketa a matsayin uwar mijin da ta haifa min miji na aura sannan uwar mijin da ban taɓa samun matsala da ita ba. Tsakanina da ita akwai girmamawa da mutuntatawa mai yawan gaske.

"A'a maganar ta ki ce, shi ya sa na ce gwara na zo da kaina."

Ta faɗa ta na kallona, sai na jinjina kai ban yi mgana ba. "Sadiya kan mganar auren Tafida da Saudatu ne." Duk da na san maganar, kuma daman a cikin wani shashe na zuciyata na faɗa min ƙila dalilin zuwan Nenen kenan amma a yadda na ji maganar a bakinta ya sa sai da gabana ya amsa. Wannan abun da ya tokaremin a ƙirji na ji ya taso min amma sai na danne ban nuna komai ba illa kai da na gyaɗa mata amma na kasa iya furta wani abu.

"Na san kin ji labari. Tun da jiya Tafida ya je cikin damuwa ya na sanar da ni kin ji labari ba tare da shi ya sanar dake da bakin sa ba."

Kaina na sunkuyar domin na rasa ma abin da zan ce, Au ashe daman ya san na sani? Na rasa ma wani suna zan kira Yallaɓai da shi a dai dai wannan lokacin ba ma, kawai kai na rausayar ina jin kamar duk duniya ko marayu ba su kai ni zama a bar tausayi ba.

"Ba ki ce komai ba Sadiya."

Nene ta ƙara katsemin tunani da maganarta na ɗago na kalleta itama ni ta ke kallo cikin karantar yanayina rasa abin da zence ne ya sa na gyaɗa mata kai kafin na ce" E. Na sani." "Tun yaushe kika san da labarin? "Tun a ranar da aka ɗaura auren." Na bama Nene amsa kai tsaye sai ta jinjina kai kafin ta ce" Ba zan yi mamaki ba. Domin mgana in ta wuce mutun ɗaya ta fara kirga uku to ba ka isa ka rufe bakin kowa ba, in ka rufe na wani, na wanin ba za ka iya dakatar da shi daga mgana ba. Ba kuma zan matsa sai na ji daga wajen da kika ji ba, zan je kai tsaye kan batun da ya kawo ni wajen ki Sadiya."

Kaina dai na ƙasa ina ta wasa da gefen hijabina amma zuciyata zafi ta ke yi, kiran sunana ta sake yi na amsa sannan ta ce" Zan ba ki labarin yadda lamarin ya faru, ba domin ki yarda Tafida ba da gangan ya ƙi faɗa miki ba sai domin na ƙara samar da kyakyawan fahimtar juna a tsakanin ku."

Ba tare da ta jira cewata ba ta fara gaya min yadda komai ya fara, ta in da aka hau da kuma ta in da aka sauka ta karishe da faɗin" Wallahi Allah ɗaya ne Tafida ya so na bashi ko kwana daya ne domin ya samu damar sanar da ke, ni kuma na ga duk ɗaya ne, ko ya sanar da ke kafin a ɗaura ko bayan an ɗaura tunda sai daga baya za a yi tariyan. A gabana kuma ya roƙi yan'uwansa da cewa su yi shuru da bakinsu ba ya so ki samu labari a bakin kowa sai daga bakin sa ba ki ga yadda ya ɗaga hankalinsa a jiyan da ya zo ya sameni ya na faɗa min ya haɗu da yayanki har ya yi masa murna sannan ya sanar masa ke kika faɗa masa. Ya damu ya ce ya na jin kunyar ki shi ya sa tun kwanaki ya kasa iya faɗa miki ba kuma domin don ya aikata haramci ba, a'a sai domin ke ɗin kina da daraja da ƙima a wajensa kina da mutumcin da ya ke tsoron ya sanar da ke labarin da zai ɗaga miki hankali, ya na jin kunya da nauyin faɗa miki ya yi aure ba tare da ya sanar da ke kafin auran ba. Yau da safe na kira shi ya sanar da ni bai faɗa miki ba sai na yi tunanin ya kasa shi ya sa ba tare da sanin kowa ba na ce Musbahu ya kawo ni domin ni na zaunar da ke na warware miki dukkan abin da ya faru na kuma ƙara tunatar da ke abubuwa ma su girman gaske da Ubangiji ya ba ki wanda nan gaba kar kishi ya rufe miki ido ki manta da su ko kuma ki kasa kallonsu a wani baiwa ko nasabar da Ubangiji ya ba ki Sadiya."

Nene na magana amma idanuwana sun cika da ƙwalla ina ƙoƙarin hana su zubowa a saman fuskata. To bayanin na menene! Ba ta saka shi ya auri ɗiyar ƙawarta ba to ni kuma me ta ke so ta faɗa min? Wannan fa shi ne an cuceka amma ana so a hana ka yin ihu da kuka, har ga Allah na ga baƙin Nene me ya sa ba za ta bari Yallaɓai ya yi mgana da ni kafin a ɗaura auren ba? Sai na ji zuciya ta sosu kuma a ganina ta yi min rashin adalci da za ta ce a yi min kishiya kai tsaye ba ta re da shiri ko tsammani ba."

Runtso idanuwana na yi, hawayen da na yi ta riƙewa suka zubomin shar! Duk Nene na kallona amma sai na kasa gefen hijabina ina sharewa a lokacin in za a tona zuciyata daga Uwar har ɗan duk haushin su na ke ji amma ina ƙoƙarin dannewa kuma a saman fuskata ina karyata abin da na ke ji a cikin zuciyata.

"Ki yi hakuri Sadiya. Ki yi hakuri."

Nene na bani haƙuri ina jin kamar ta na ƙara ma ciwo na barkonu ne, ina ta danne kuka na amma ina share hawaye ne wasu suna ƙara sauka kamar an buɗe famfo tun kuma da labarin auran nan ya zo min ko Yallaɓai ban taɓa zubar da hawayena a gabansa amma yau sai na ji na kasa iya wannan dauriyan ganin hawayen sun riga sun taho kai tsaye sai kawai na barsu suna ta zuba sharr, in suka kwaranya a saman fuskata har suna gangarowa a saman hijabin jikina, Idanuwana suna mai kallon zanen cafet ɗin da ke falon, ina jan hanci irin na masu kuka, so na ke yi na samu keɓewa ni kaɗai na fashe da kuka na yi birgima ko domin na ji sauƙi sauƙin abin da ke suka na acikin zuciyata.

"Ki yi haƙuri Sadiya. Daure na san kishi. Na san kishi ya na da zafi Sadiya amma in aka yi haƙuri za a ci riba wata rana."

Readers Also Read