Turken gida book 2 cmplete by janafty - Chapter 9
Turken gida book 2 cmplete by janafty Chapter 9: Turken gida book 2 cmplete by janafty Chapter 9. Kalamanta ya sa na kalleta, tabbas ta san kishi, ita da…
3,260 words
Kalamanta ya sa na kalleta, tabbas ta san kishi, ita da aka auro ma uku. Kenan itama ta san irin zafin da na ke ji a cikin zuciyata sai na ji na godema Allah a cikin raina ko banza za ta fahimci kwataƙwacin irin ɗacin da na ke ji a cikin zuciyata. Kaina na ƙara maidawa ƙasa lokaci ɗaya ina share hawayen saman fuskata da gefen hijabin jikina muryata har ta fara chanzawa na ce.
"Bakomai Nene. Allah ya ba mu zaman lafiya da juna."
Ta amsa da Amin Amin cikin mirmishi kafin ta ce" Sadiya wallahi ban yi ma Tafida ta yi auran Saudatu domin na ga kin gazamin ba. Ko na ga shi kin gaza masa ba, sai dai kamar yadda na faɗa miki tsohon kuduri ne a zuciyarmu ni da Hajiya ina kuma son na cika shi kafin na bar duniya shi ya sa auran ya zo bagata tan. Amma wallahi Allah ɗaya kenan ba ki taɓa min wani abu cikin sanin ki ba ko ma kin yi min a cikin rashin sani na yafe miki na sha faɗa a gaban idon ki a kuma bayan idon ki bakomai a tsakanina da Matar Tafida sai mutumtawa da Darajawa saboda haka kar ki saka a ranki ko kin gaza ne, ko kuma na ware ki, da ke da Tafida da Saudatu ɗaya kuke a wajena, ba bu bambamci a tsakaninku kamar yadda Saudatu ta ke ƴa a wajena kema ƴa ce domin iyayenki ranar da kika zama ɗaya daga cikinmu ni suka ba ma amanarki suka kuma ce min ni uwa ce a gare ki na yi miki gyara in kin yi kuskure tamkar yadda zan yi ma ƴaƴana na cikina ko kin manta Sadiya?
Kai na gyaɗa ai ba zan manta wannan ranar ba. Inna Mariya ce ta riƙa jadaddama Nene ƴa suka kawo mata ba suruka ba. Kai na ƙara jinjinawa kafin na ce" Haka ne Nene." Sai kuma na kalleta kafin na ce" Na gaza Nene. Na gaza wajen ba ki jikoki masu yawa daga tsatson Tafida kamar yadda kike so." "Kul kar ƙi ƙara wannan mganar Sadiya. Ba ki gaza ba kin kuma biya ni domin kin haifa min takwara kin kuma haifa min ƴa. Ni ko me na ke nema a duniya da Allah bai ba ni ba? Allah na tuba ni jika wanne ne ba a haifa min ba Sadiya! Ki godema Allah kina da biyu wata ɗayan ma ba ta samu ba shi ta ke nema. Ki kuma gode ma da Allah da ya baki har biyu sai ki yi ma Allah butulci da cewa gazawa ce? Maza ki nemi gafaran Allah domin ya yi miki kyauta ba ki gode masa ki nemi gafaran shi ki gode masa sai ki ga ya ƙara miki da ni'imar da ta fi irin Ni'imar da ya baki a baya."
"Astagafurilla. Astagafrilla."
Haka na shiga furtawa da sauti, domin sai na ji tsoro kar na batulce ma Allah ya ƙi ƙara min wata haihuwar domin nan duniya ba ni da wani buri sai na ganin Allah ya sake ba ni haihuwa ko da guda ɗaya ne. Zuciyata har rawa ta ke yi in na yi hasashen ƴaƴa biyun da Allah ya ba ni wata rana in ya so zai iya ɗauke kayansa sai na ji jikina har ƙwaƙwalwata ya na amsawa cikin wani yanayi wanda ba ki ba zai iya misaltawa ba.
Nene ta ga yanayina ina ta rawan jiki sai ta ce na yi ta kiran sunan Allah har sai na samu natsuwa innalillahi na cigaba da maimaitawa a cikin zuciyata cikin ikon Allah sai ga shi na dawo cikin natsuwa Nene ta durkusa da kanta ta buɗe ruwa ta zubamin a kofi ta ba ni ta ce na sha da bismillah. Ban yi musu ba na karɓa na sha da yawa na miƙa mata kofin ta karɓa ta maida shi saman farantin sannan ta koma ta zauna ta na kallona ina ta sauke numfashi. Sai da ta fahimci na samu natsuwa sannan ta shiga yi min nasiha mai ratsa jiki da cewa duk abin da na ga ya faru da bawa daga Ubangiji ne kuma duk abin da ya aikata dai dai ne shi ba ya kuskure, mu ƴan adam mu ke kuskure amma shi Ubangiji duk abin da ya yi a garemu mai kyau ne. Ta umarce da shawaran da daaina tunani na fauwalama Allah komai. Wataƙila jinkirin alheri ne nan gaba Ni'imar za ta fi ta baya yawa. Ina gyaɗa kaina cikin gamsuwa ina faɗin.
"Allah ya sa. Allah ya sa. Na gode Nene Allah ya saka da alheri"
Ta amsa da Amin kafin ta ce" Ina fatan kin fahimce ni. Sannan a mganganuna kin fahimci irin matsayin da kike da shi a zuciyar Tafida ko? Sai na kalleta alamun bangane ba sai ta gyara zama kafin ta fara da kiran sunana. "Sadiya ba ki fahimci irin martaban da ubangiji ya yi miki a acikin zuciyar mijin ki ba? To ko kin fahimta ba ki gane ba. Ni bari na warware miki irin taki baiwar da ubangiji ya yi miki ba ki sani ba."
"Sadiya."
Ta ƙara kiran sunana na amsa ina kallonta sai ta nuna kanta kafin ta ce" Kin san kishiyoyi uku Marigayi mahaifinsu su Tafida ya auro kafin rasuwarsa? Ba ta damu da mganata ba ta cigaba da faɗin" Zan faɗa miki wani sirrin da ban taɓa faɗa ma ko ƴaƴana ba. Ina yar yarinyata ya ƙara aure a lokacin cikin maimuna ƙarami ne a jikina. Maman farko da kike gani bashi ita a ka yi abokin mahaifinsa ne ya bashi ɗiyarsa. Da maganar da auren tsakani wattani huɗu ne, amma ya kasa faɗamin saboda ya na tsoron tashin hankalina gashi ina da ciki kar wani abu ya samu cikin jikina kar na ɗaga hankalina wani abu ya same ni ya sa bai iya faɗamin da kansa ba sai amininsa marigayi Tafidan Rano ne ya zo ya same ni ya sanar da ni a lokacin sai da ya kalleni kafin ya ce" Hauwa'u ki godema Allah kin yi dacen samun nagartatten mijin da ya ke gudun ɓacin ranki da tashin hankali. Yususa ya ƙi sanar da ke labarin matar da aka bashi ne saboda ba ya so ya tashi hankalinki wani abu ya same ki, ya na jin kunyar ki matuƙa duk da ba haramci zai yi ba, a lokacin ya ce min Hauwa ba duka maza ne irin Yunusa ba, ba duka maza ke iya jin kunyar matansu kamar yadda Yunusa ke jin kunyarki ba ya sake sanar da ni cewa ba duka maza ke tsoron tashin hankalin matansu ba, saboda haka ki daure ki kuma yi haƙuri ki ba ma mijikin goyon baya kar ki ɗaga masa hankali, ki yi masa alfarman guje ma tashin hankalinsa kwatanƙwacin yadda ya guje ma na ki." Sadiya tun daga waɗanan kalaman da ya yi mini har ya bar duniya da gangan ban taɓa ɗaga masa hankali ba, in ma na ga hankalin shi ya ɗaga ni ce zan zama sillar kwantar masa da hankali, har ya yi duka aure aurensa ban taɓa ɗaga masa murya ba, na yi hakuri na danne saboda wannan nasabar da Ubangiji ya yi min a zuciyar mijina ba na so na bashi kunya. Na ci riban hakurina na zauna lafiya da shi da matansa tun yana rage ni ce giwarsa a cikin gida da waje har kuma ya koma ga Allah hakan bai sauya matsayina a wajensa ba sai ma ya ƙara hauhawa ninƙi ba ñinƙin, faruwan wannan lamarin ya sa kawai in na kalli Tafida sai na ga kamar na ga makwafin mahaifinsa ne a tare da shi, Sadiya ba wai ina faɗa miki wannan ne saboda tausan baki ba. A'a ina faɗa miki ke ma Allah ya yi miki wannan nasibin. Ba kowacce mace ba ce za ta samu miji na jin nauyinta ba, ba kuma kowace mace ba ce ke samun darajawa da mutumtawa a wajen mijin auranta ba. Ba kuma kowacce mace ke iya samun namijin da ke gudun tashin hankalinta da damuwarta ba. Ke Allah ya baki wannan nasibi na kawo miki wanman labarin ne saboda na ankar da ke wasu abubuwa guda biyu zuwa uku."
Ta ƙarishe faɗa ta na kallona. Na kuma natsu na ba da duka hankalina a kanta ina sauraranta. "Sadiya." Na amsa da "Na'am Nene." Sai kawai ta yi mirmishi kafin ta ce" Kin ga duk sanyin halin Hauwa na sha yin shari'a tsakaninta da muttaƙa." Ido na zaro ina kallon Nene sai ta gyaɗa min kai kafin ta ce" Ba tonon asiri ba ne Sadiya Nasabar da Ubangiji ya yi miki na ke son ƙara tunasar da ke. Sadiya tun auran ku da Tafida bai taɓa kawo min ƙaran ki ko da rana ɗaya ba. Bai taɓa zama ya kushe ki ba sai dai ya yabeki, ke ma haka ba ki taɓa kawo min ƙaran Tafida ba,duk da na san kuna samun matsala domin babu auran da bashi da matsala sai dai ku binne shi ku kaɗai ba tare da sanin kowa ba. Sadiya wannan ma wata Nasaba ce da Ubangiji ya yi miki, kuma a cikin idanuwana ina karrama wannan ƙimar ta ki."
Sai na ji kaina ya yi girma cikin alfahari Nene ba ta bani damar mgana ba ta cigaba da faɗin" To ba na so saboda wata ta zo ki sauya Sadiya. Kin zama turken gidan Tafida duk matar da ta zo daga bayanki sai dai ta ɗora igiyanta a kan wannan turken da kika riga kika kafa shi Sadiya. Kar ki sake da wannan matsayin da Allah ya ba ki na uwargida kan gida, kar ki yi sake da shi ya tashi a banza. Akwai zafi amma ki daure ki gani ƙi ƙi gani, ki ji kuma ki ƙi ji, a zo a gaya miki ki toshe kunnen ki in kika yi haka za ki zauna lafiya, ki ba ma mijinki dama damar da ya ke so daga wajen ki, ki yi ta addu'an zaman lafiya da salama Sadiya wallahi tallahi ba Saudatu ba ko Tafida bai isa wata rana ko halin su na maza ya motsa masa ya tozartaki ba saboda kin tsare mutumcin kan ki, na san Saudatu ke ma na san ki Sadiya in kuka yi hakuri za ku ba da shaidar kyakyawan zurua anan gaba. Ina roƙon ki da ki riƙe wannan nasabobin da na sanar da ke Ubangiji ya yi miki, ko an yi miki wani abu in kika tuna su sai ki danne zuciyarki ki yi haƙuri in kika yi haka tabbas wata rana sai kin ci riba in sha Allahu."
Kamar hadda haka na haddace kalaman Nene a cikin kaina kuma cikin ikon Allah da kalamanta sai na ji zafin da ke cikin zuciyata ya na raguwa. Ina jin haushin ta da na fara ji ita da Yallaɓai ya na raguwa. Duk da an ce tsakanin miji da mata sai Allah gaskiya ne zan kalli Nasabar da na ke da shi a wajen Yallaɓai na lulluɓe duka sharrinsa a gareni kamar yadda shima ya ke kallon alherina ya lulluɓe sharrina ba kuma wai domin ba ni da shi ba, kowani ɗan adam ya na da na shi alherin kuma ya na da na shi sharrin.
Sai kawai na kalli Nene ina murmishi kuma tabbas murmishi daga ƙasan zuciyata ya fito ba a iya saman leɓena ba ne. "Na gode Nene. Kuma na yi miki alkwarin ba za ki ji saɓanin tunanin da kike da shi a kaina ba in sha Allahu." Sai ta jinjina kai kafin ta ce" Amin. In sha Allahu na gode nima da samu abin da nima na yi tsammani daga wajen ki. Na gode Allah ya yi muku albarka Allah kuma ya zaunar da ku lafiya ya kuma kaɗe fintintunu." Na amsa mata da Amin Amin sai ta ce za ta wuce amma kafin nan na yi ma Yallaɓai mgana kafin ta wuce, ni na tashi na leƙa falon da suke zaune shi da Musbahu na kira shi muka dawo tare wannan karon kasan cafet muka zauna ni da shi gabaɗaya ta kallemu kafin ta ce.
" Na ƙara tunasar da Sadiya abin daman ta riga ta sani na auranka da Saudatu. Tafida sauran aikin na ka ne, ka zauna da matarka ku yi mgana ku fahimci juna ku tattauna rayuwarku tare. Dukkanku ina fatan tsamanin abin da na ke tsammani daga gare ku. Allah ya ƙara muku zaman lafiya da fahimtar juna. Dukkanku da ku da yayanku Allah ya yi muku albarka gabaɗaya." Muka yi ta amsa mata da Amin sannan ta yunƙura ta miƙe ta na faɗin" In ina da rai wata rana ina fatan alheri ya sake dawo dani gidan ku." Muka ƙara amsa mata da Amin. Yallaɓai ya shiga ƙwalama Musbahu kira ni kuma na je na kwaso mata takalmanta na jera mata ta zo ta saka ta na faɗin" Allah ya shi albarka. Allah ya ba ku zaman lafiya."
Ni na buɗe mata kofa muka fita har haraba sannan sai ga Yallaɓai da Musbahu, sun fito na buɗe mata gaban mota ta shiga sannan na rufe ina ɗaga mata hannu Yallaɓai kuma ya tafi buɗe musu get har Musbahu ya fita da mota na ga ya tsaya Nene na mgana da Yallaɓai ta window na ga ya na gyaɗa mata kai sannan suka wuce shi kuma ya rufe get ɗin ina tsaye na harɗe hannu a kirji ina kallonsa sai yanzu da na ƙare masa kallo na fahimci ba ni kaɗai na yi raman tsaye ba Yallaɓai ma duk ya rame sai karan hanci kamar bashi ba.
Ban san ya ƙariso gabana ba sai da na ji yana shafa kumatuna sannan na fahimci ya ƙariso kusa da ni.
"Ya dai?
Ya faɗa ya na kallona sai kawai na sauke ajiyar zuciya. "Bakomai." Na sauke hannayena na juya zan tafi sai ya riƙo hannuna na dama, na juyo ina kallon shi. Sai kawai ya wuce gaba ya na riƙe da hannun nawa, nima ban kwace ba sai na bi bayan shi. Bai direni ko'ina ba sai a kan kujeran mai zaman mutum ɗaya shi kuma sai ya durkusa a gabana ya na mai riƙe duka hannayena biyu a hannayensa ina kallon shi ya na kallona sai na ji rauni ya na kama ni. Zan iya fashe masa da kuka sai na yi saurin kauda kai, shi kuma sai ya kai yatasun hannuna ɗaya bayan ɗaya a bakinsa ya na sumbata. Kallon sa na ke yi da duka zuciyata ina jin ta na sake buɗewa a karo na biyu na yarda da kaddara wataƙila zantu kan Nene ne suka farkar da ni, wataƙila ba za ta ga laifina ba domin itama ai ta san kishi ta kuma ce ya na da zafi sai an daure.
"Sadiya ta."
Ya kira sunana cikin raunin murya sai na ɗaga ido na kalle shi kwarmin idanuwana suna mai cika kwallah. "Sadiya wallahi ban ɓoye miki wannan auran da wata manufa ba, sai domin na kasa. Na Kasa jarumtar sanar da ke na ƙara aure. Ban san da wata kalma zan yi amfani da shi ba,ban kuma san ta yadda za ki karɓi mganar ba. Ba na so na faɗa miki wani abu da zai ɓata farincikin ki na wannan ranar. Ban san dalili ba sai na ji ina jin kunyarki. Ina jin kamar ban kyauta miki ba, har ma a cikin kwanakin nan Sadiya sai na riƙa ji a ƙasan zuciyata kamar na ci Amanarki ne, don Allah ki yi haƙuri ki yi haƙuri ki ya fe min don Allah SADIYA TA."
Ya ƙarishe faɗa ya na mai ɗora fuskarsa a saman tafukan hannayena ba kuka ya ke yi ba amma ina jin hucin numfashinsa lokaci ɗaya da bugawar zuciyarsa. Yau fa ban san me ya faru dani ba, kamar ruwa ruwa da an fara mgana sai na ji kamar na fi kowa rauni a duniya sai na fara kuka yanzu ma ɗin ma hawaye na ke yi, ina danne abin da ke taso min a cikin zuciya ta. Kai na ƙara yarda da cewa kishi cuta ne kishi masifa ne da bala'i domin a lokacin ji na ke yi ko na ce gani na ke yi yadda ya kwanta a jikina yana lallashina wata rana fa zai kwanta a jikin Gimbiya itama ya na lallashinta ko? Kawai sai na ji zuciyata na rufewa da kanta, ƙuncin da ya fara barina na ƙara ziyarta ta.
Bai san ina kuka ba sai da ya ji ɗigan hawayena a saman hannunshi na dama da ya sauke shi a saman cinyata. Da sauri ya ɗago ya na kallona ai sai ya ga ina hawaye wasu na koran wasu da rawan jiki ya miƙe zaune ya samu hannun kujeran ya zauna ya mai sanya yatsun hannunsa ya na share min hawaye amma kamar sun sani ya na share min wasu suna ƙara ɓulɓulowa.
"In kina kuka Sadiya ta. Ni me kike so na yi?
Haka ya faɗa ya na share min hawaye, kawai sai na fashe da kuka har da buɗe murya saboda ji na yi kamar in ban fittar da kukan ba zan iya mutuwa, tashi ya yi a ruɗe ya cicciɓeni shi ya koma ya zauna ya ɗora ni bisa jikinsa ya rumgume ya na ta share min hawaye, ya na kuma lallashina ni bai ma san ma lallashin na shi ke ƙara sakani kuka ba, ina shessheƙan kuka na ƙwaɓe hannun shi daga saman fuskata ya ƙara kawowa na ƙara kwaɓewa sai ya tsaya ya na leƙen fuskata da na ke boyeta a saman ƙirjinsa.
Sai kawai ya daga hannayensa sama ya na faɗin" To na bari tunda ba ki son lallashin." Saki na ya yi sai gashi na zamiye kamar zan faɗi kasa kuma shi bai riƙe ni ba, gani zan sha ƙasa ya sa na ƙamƙame shi ina kallon shi ya na murmishi ya ce" Na kawo hannu ki ture ni? Ya faɗa ya na kallona wani abi ya soki zuciyata a raina na ce ai in Gimbiya ce ba zai bari ta kai ƙasa ba. Kawai sai sai na ƙara saka masa kuka lokaci ɗaya na saka duka hannayena ina dukkansa a ƙirji bai hanani ba sai da na yi har na gaji sannan na koma na lafe a saman kirjinsa ina maida numfashi hannayena suna zagaye a wuyansa. Sai da ya ga na yi laushi sannan ya saka hannuwansa ya tare ni sosai a saman jikinsa bai sake yi min mgana ba amma hannunsa guda ɗaya da ke bayana da shi ya ke ɗan bubbugamin bayan alamun lallashi, ina ta jan majina da jan numfashi cikin lokaci kuma sai kukan nawa ya ɗauke na koma ina ajiyar zuciya, har kuma na koma na yi lamo idanuwana suna lumshe amma ba barci na ke yi ba. Mun zauna a haka sama da awa ɗaya na san hannayensa da kafafunsa sun gama sandarewa da gangan na ƙi sauka a raina na ce gwara duk na gama more jikin ko ta zo sai dai ta samu saurana.
Kuma na samu natsuwa sosai fiye da tsammani na. Ba tare da ya nuna ya gaji ba na sake shi ya saka hannu zai riƙe ni na ce" Zan ta shi.' Sai ya taimaka min na miƙe hijabin jikina duk ya bushe da ruwan hawaye shima miƙewa ya yi ina gani yana juya wuya da hannayena. Sai da na yi dariyan mugunta a raina, ban ce masa komai ba ya ga na fara ta ku zan bar falon sai ya biyo bayana ya na faɗin"
"Sadiya ba mu karya ba fa yau"