Kenza eBookz

Turken gida book 2 cmplete by janafty - Chapter 42

Turken gida book 2 cmplete by janafty - Chapter 42

Turken gida book 2 cmplete by janafty Chapter 42: Turken gida book 2 cmplete by janafty Chapter 42. A lokacin da ya dawo daga Saudiya na ga uwar tsaraban…

3,365 words

A lokacin da ya dawo daga Saudiya na ga uwar tsaraban kayan wasan da ya kwaso musu sai da na yi magana da cewa Yallabai hala dai ba ibada ya kai ka saudiya ba. Siyan kayan wasa ka je yi ko? Ai daga wannan maganar ya fara min masifa wai ina mgana ba ta taunawa ko Baby ai ba za ta yi wannan mganar ba, sai da na yi nadamar yi masa mgana kwana biyu ya yi ya na gaba da ni. Daga faɗin gaskiya domin jaka ce shaƙe da kayan wasa ba dole na yi tunanin daman abin da ya kai sa ba kenan ni kaina gidana ga su nan da yawa ballantana gidansu da Jidda ta ce min ɗaki ne guda da kayan wasa na khalipa da Anwar. Na yi ta haƙuri ina kauda kaina yanzu haka Gimbiya sunan da su Anty Bahijja ke kiranta da shi shi ne Uwar maza. Shekaranjiya ma mun haɗu gidan Naja suna ta haihu ana ta yi mata kirari da Giwar gidan Tafida uwar maza mace mai kashin arziƙi domin a cewarsu tun da Tafida ya aure ta ya ke ta ganin buɗi na arziƙi ni dai ban tanka ba tun da daman ai tun bayan faruwan lamarin nan sun sanni na san su, shi ya sa in suna abin su ba na biye musu suma kuma sai dai habaici da shakuɓe amma ba sa yi da ni kai tsaye.

Munnira ce ma ta ce ita uwar mata ba uwa ba ce? Anty Maimuna ta ce uwa ce amma uwar maza ita ce da gida. Sai da muna adaidaita za mu tafi gida ni da Hauwa bayan mun rabu da Munnira ta ke min mgana wai kar na damu da mganganunsu ni ko sai na ce yau a ka fara? ai sun daɗe suna fadin haka ban taɓa nuna na damu ba, ita kuma Gimbiya ta na hura hamci ta na iyayi ita matar arziƙi ni ko na ce in ma tsiyar ce to Yallaɓai ne ya shafa min tun da ni kam da arziƙina ya aure ni ya tsiyata ni yanzu da ya samu duniya sai suka manta. Yanayin rayuwa ya sa na daina ma damuwa da wasu manganganun saboda ai jiya ba yau ba ne. Kuma girma ya ƙara kamani da ya sa lamarin ya zame min jiki ba komai in na ji ko na gani na ke mgana ba amma tabbas an kusa kai ni bango akan lamarin Khalipa na zura ido na yi kara na yi kawaicin duk a banza ko ƴaƴana suna tasawa na ke daina kwana da su ballantana ɗan kishiya. A raina na ji ko me zai faru sai dai ya faru amma sai na yi ma Yallaɓai mgana.

****

Tiolet na shiga na kama ruwa sannan na fita falo. Jidda ce kawai ke gida ba ta jin daɗi Baby kuma ta tafi Tahfeez. Falon su Khalipa duk ya kama kaca kaca da shi ya watso min fillows ɗin kujera a ƙasa. Jidda na falon ta na karatu a ipad ɗinta tun da Abbansu ya ce a wannan shekaran za ta yi jarabawar fita da Jamb.

"Jidda kina zaune Khalipa ya hautsina min falo haka?

Sai ta ɗago ta na kallona kafin ta yatsina fuska ta na faɗin" Na gaji da gyarawa ne Umma da na gyara sai ya ƙara watso su." Hararanta na yi kafin na ce" To ni ne kike so na kwashe? Ina mgana na ji ina taka ruwa na fara mata faɗan ta bari ya jiƙa min gida sai ta ce wai ita ba ta sani ba.

"To ke za ki yi min gyara gidan ko yarinya."

Na faɗa ina shiga falon Yallaɓai nan ko sai da na kusa kuka ya watsa duka kujerun dining sannan na iske shi ya na feshe kujeru da ruwan bindigarsa ai saboda takaici ban san lokacin da na masa tsawa ba, kuma ga shi ba shi da tsoro, ke gizau Jidda na ƙwalama kira ta na zuwa na ce ta natsar da shi kuma ta gyara min gidana ko ranta ya ɓaci.

"Umma wallahi na hana shi ya ƙi bari ne."

Na wuce ina mai jan tsaki kafin na ce" Wannan ke ya shafa. Ni dai na fito na ga gidana ya yi tsab ya na tashin ƙamshi." Kitchen na shiga na haɗa tea daman akwai ruwa a fulas na dawo falon na zauna. Ina jin su ta na gyarawa ya na ƙara ɓatawa ita kuma ga shi ba ta da zafi shi ya sa ya ke ba ta wahala da Baby ce da yanzu an fara kokuwa. Da na ga ba zai bari ba sai na fito da bulalata na na nusa masa na ce ko ya natsu ko na zane shi, bai ko natsun ba sai da na chau la masa biyu sannan ya fara kuka daga nan sai barci shi ne fa Jidda ta samu ta yi min gyaran gidan. Ita ba ruwanta ta na son aiki ga wacce sai na yi da gaske ta ke aiki nan Baby in na yi magana sai Yallaɓai ya ce ai gado ta yi kuma daman an ce magaji ai mafiyi ina jin haka zan yi shuru. Allah sarki Saude ita na ke tunawa in su Jidda na makaranta aiki ya yi min yawa. Tuni an yi mata aure shekara ɗaya kenan a jigawa yanzu haka tsohon ciki gare ta. Duka masu zuwa su tayani aiki yanzu suma sun kama ɗaku nan kansu. Jidda dai ke ƙoƙari domin in dai ta na gida ba na aiki girki kam ba abin da ban koya mata ba.

Yau Yallaɓai a gidana ya ke amma gobe zai koma gidan Gimbiya. Sai dare ya shigo gidan ya ce min ya ɗan tsaya a Gwammaja ne, da ya ke Nene yanzu ta samu lafiya sai dai ɗan ciwon kafa da ke matsa mata lokaci bayan lokaci haka. Ko da ya dawo Khalipa ya yi barci amma kamar ana masa wahayi da ya ji muryan ubab zai tashi nan fa ya maƙale masa har cikin gaurancinsa ya ke faɗa ma uban wai na dake shi, shi kuma ya ce ka yi ma Umma laifi kenan ko?

"Ɓarna ya yi min bayan na saka Jidda na gyarawa ya ƙi barin ta ta yi aiki shi ne na yi masa bulala biyu."

"Kai sarkin rigima ba za ka daina yi ma Umma ɓarna ba ko?

Ya faɗa ya na shafa kumatunsa. Kallon Yallaɓai kawai na ke yi in ya na wani abun, faɗa ya ke yi itama Gimbiya haka ta ke fama da shi. A raina na ce muna fama dai ni fa sai dai na bar Yallaɓai da Khalipa domin a daran ma wasa suka fara yaron na bin shi da bindiga shi kuma ya na ɓoyewa shi da Baby saboda ita ce mai son wasa. Jidda kam ba ruwanta da wannan shanshanci shi ya sa na ke sonta ta na da aji sosai.

Ɗaki na koma na yi kwanciya ta ban ma san shigowarsa ba, sai cikin dare na farka na gan shi maƙale da Khalipa wani abu ya kawo min wuya amma ban yi wani abu ba, ji na yi kamar na koma ɗayan ɗakin na kwana amma sai na fasa. Da safe muna karyawa bayan yara sun tafi makaranta. Yallaɓai ya siya sabuwar mota wata bakar benz tsohuwar tashi kuma ta na hannun salisu shi ke kai yara makaranta a ciki sai cefane.

"Daughter ta ce a saka Khalipa a makaranta na ce laa ba yanzu baa"

Kallon shi na yi lokacin ina tura dankalin a bakina. Ko a yanzun ma Khalipan na kan jikin shi ya na bashi dankalin a baki, ko fa fita Yallabai zai yi in ba da shi zai fita sai da dubara in kuma ya duba bai gan shi ba haka zai ta rigima to ya riga ya sabar masa.

"Gaskiya kam a saka shi a Baby cllas ba."

Na faɗa ina haɗiye abin da ke bakina. Amma sai Yallaɓai ya ce ba yanzu ba sai ya shekara biyar.

"To me ya sa? Na ga dai da bakin shi ko? Kuma ko Baby ta na da shekara huɗu ka saka ta a makaranta."

"Da Khalipa da Baby ba ɗaya suke ba. Shi fa ya shaƙu da ni kina tunanin zai zauna a makaranta?

Wani kallo na wurga masa kafin na ce" Tabbas ba ɗaya suke ba na ga alama." Daga haka ban ƙara kula sa ba har ya gama mganganun sa. Tare suka fita da Khalipa ya ce zai kai shi gida a raina na ce a gayas daman na gaji ina so na kwanta. Bayan kwana biyu da ya dawo gidana bai zo da Khalipa fa a cewarsa uwar ce ta ce ba zai biyo shi ba.

"Ta ce wai ana takura miki. Ni kuma na ce mata duk ɗaya ne da nan ɗin da can duk in da Khalipa ya ke so zai zauna."

Kallon musulunci ma bai samu ba ya gama gyaran zencen sa ya yi shuru. Da safe kuma again muna ƙaryawa ya fara isa ta da labarin shagon Gimbiya na yi masa kasaƙe kawai ina jin sa kuma ina kallon shi.

"Shagon ma fa ta ce ya yi kaɗan kaya ba sa wata suke ƙarewa yanzu fa har jiran oder ta ke yi "

"Uhm Allah ya sa albarka."

Na faɗa ina son kauda mganar amma ina shi a dole sai ya faɗa min.

"Ina gaya miki ana siya kayan ta sosai duk abokaina da abokan kasuwancina wajenta suke ma matan su siyayya."

"Ka kyauta Marketing manager."

Na watsa masa mgana amma sai na ga ya yi dariya kafin ya ce" Haka Daugther ta ce ta naɗa ni markerting manager a shagon ta na iya talla." Kamar wani shashasha ya na ta dariya ji na yi kamar ina make sa da kofin hannuna amma sai na basar gani na yi ya dameni abu kaɗan ya ce Daugther daman ni sunan nan wallahi ya daɗe ya na ba ni haushi kawai yau na ce bari na yi masa mgana.

"Yallaɓai kana da abin mamaki."

"Na me fa?

Ya tambaya ya na kallona.

"Ka auri mace har ka yi mata ciki ta haihu sau biyu amma ka na ta wani kiranta da sunan Daugther don Allah miye ma'anar wannan sunan? Ƴa? To kai yarka daman ka aura ka ke yi ma ciki tana haihuwa?

"Ban gane ba"

Ya faɗa bayan ya rage fara'aran fuskar shi.

"Ka duk gane abin da na ke nufi."

"To sunan Daugther ɗin ke kuma ya tsaya miki a rai? Kike kishi da sunan?

Ya faɗa ya na kallona kafin in samu zarafin mgana a fusace ya cigaba da faɗin" Kin ba ni mamaki me ya sa yanzu kwata kwata ba ki tauna mgana in za ki faɗa min ne? Ai kin san matsayin ta a wajena da matsayin sunan tun kafim mu yi aure haka na ke kiranta kuma ya kama bakina. Sai a ka ce kuma haramun ne don ta na matata kar na ce mata Daugther?

"Ba haka na ke nufi ba."

Na faɗa ina ƙoƙarin kare kaina ganin ya taso min

"Haka kike nufi mana. Sai an yi magana ki ce ke kin girma kaza da kaza, kin girman ne kike yin abin da kike yi? Sunan mai sai kin yi masa wata fassaran? Ashe ita Allah ya jiƙanta ba domin ta mutu ba da sai ta haɗiye zuciya ta mutu. Wani irin suna ne ban kira ki da shi a gaban ta ba? Wallahi ba ta taɓa mgana ko ta nuna rashin jin daɗin ba, ban taɓa kiran ta da sunan soyayya ba ke fa! Ba sunan ƙaunar da ban kiraki da shi ba karshen ta dai to ke ɗin ce na ke kira abar ƙaunata a gaban ta, ba ta taɓa mgana ba sai ke? Don ina kiran ta Daugther? Ba ki son ji ne? To sai dai ki toshe kunnuwanki domin ba zan iya daina kiran ta da wannan sunan ba."

"Ka yi haƙuri."

Na samu kaina da furtawa a cikin raina ina mai nadaman fara yi masa mganar. Daga mgana sai kawai cibi ya zama ƙari.

"Ba maganar haƙuri ba ce. Ki gyara a matsayin ki na babba kar ki yi abin da za ta ji ko ta gani girman ki ya zube a wajen ta."

Ya na gama faɗin haka ya miƙe a fusace ya shige ciki sai ga shi ya dawo da key ɗin mota daman a shirye ya ke ya fice ya na faɗin.

"Sai na dawo."

"A dawo lafiyan"

Ko amsa ni bai yi ba ina jin tashin motarsa da ya dawo ma zai rufe get ɗin da ƙarfi ya tura shi har sai da ina daga falo na ji wani garam! Na riƙe baki ina faɗin ikon Allah!

*Janafty* *TKG020C20c*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LgZezgwmkmy8ZCuNsHiNxX

Assalamu Alaikum Fanmily, mun fara saro muku kayan Kitchen ko wani nau'i, duk abin da kuke bukata na gyaran Kitchen ɗin Amarya da uwargida duk za ku same su a JANAFTY KITCHEN ITEMS, kayan mu masu kyau ne da inganci sannan za ku same su akan rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina a falin Nigerian nan. Domin karin bayani ku tuntuɓe mu ta waɗannan lambobin kamar haka. 09069067488. +234 706 234 9732

Muna maraba da masu siya ɗaya ko sari🥰

Sama da mintina goma da fitar Yallaɓai amma na kasa ko da motsa ɗan yatsa na saboda da al'ajabi daga mgana sai cibi ya zama ƙari.? Har ya na min wani gorin ya na kirana Abar ƙaunarsa ni na saka shi? Ban da ma gulma yaushe ne ya fara kirana da wannan sunan? Ba sai da ya yo min kishiya ba ne ya fara min sanaben kirana da sunaye kala kala. Sannan in zai kirani da wannan sunan sai in zai min yaudaran su na maza ko ya na so ya raina min wayau amma shi ne har ya na yi min gori.

Abin fa ya tsaya min a zuciya cikin sanyin jiki na miƙe ina tattara tarkacen abubuwan da muka ɓata zuwa kitchen. Na gaji baya na har ciwo ya ke yi na saka anemin wata ƴar aiki, amma ba a samu ba can kwanaki na yi ma Inna Mariya mgana ta kawo min wata yar anguwan su amma ko sati ba ta yi da fara zuwa ba na ce ta bar shi kawai saboda ba ta iya aikin ba in ma ta yi sai na sake yi, in za ta yi shara bara da bana in mopping ne ta jiƙa min gida da ruwa. In kuma wanke wanke ne duk ta haɗe masu karni waje ɗaya kuma su yi ta warin omo ba ta wankewa da kyau ballantana ta ɗaureye su da kyau shi ya sa kawai na haƙura amma ni kaina na san zai yi wahala na samu mai aiki kamar Saude.

Ɗaki na koma na zauna a gefen gado cikin sanyin jiki. Na rasa me ke min daɗi haka kurum zuciyata sai ta cunkushe, na zauna shuru kawai ina ta nazarin rayuwa ƙaran wayata da ke gefena ya dawo dani daga tunani mai zurfin da na faɗa ina dubawa sai na ga Munnira ce amma har wayar ta katse sai na kira ta daga baya. Duk da ban san dalilin kiran ba amma ina tunanin kan batun bikin autar su Hauwa ne Sakina da za a yi nan da sati biyu. Mun yi ankon can Rano sannan mu ma mun fitar da anko mu uku.

Saboda duk duniya Hauwa ba ta da wasu ƙawaye makusanta ta a Kano irin ni da Munnira. Haka nima duk da dai ga su facololina amma kuma sun riga sun zama aminaina ma su taya ni kuka in dariya ne mu yi tare in kuma na baƙin ciki ne su ta ya ni su ne mutane na farko bayan iyayena da ƴan'uwana ma su zama kusa da ni a duk yanayin farinciki ko baƙin ciki. Nima shi ya sa in sha'anin su ne na ke ɗaukan shi da muhimmaci yanzu ma muna maganar gudummuwar da zamu haɗa ma Mamansu Hauwa mu aika da shi kafin lokacin bikin ne.

Nima har wayar ta katse ba ta ɗauka ba sai na ƙyaleta na miƙe kenan zan bar ɗakin sai ga shi ta sake kirana sai na koma na zauna. Cikin fara'a na ɗaga kiran ina faɗin. " Mata a gidan Nasiru." "Uwargidan Alhaji Injiniya Tafida ba"

Sai na ƙyalƙyace da dariya, itama ta na taya ni ina ji Samir na kuka yaron da ta ke goyo. Yanzu haka daga ita har Hauwa goyo su ke yi sun sake haihuwa. Ni ce dai Allah bai kawo karshen lamarin ba in kuma shi ne na ƙarshe to ina masa godiya domin ya yi min ni'ima ni'imar da ya tsame ni a cikin waɗanda ma bai taɓa ba ma haihuwan ba.

Bayan mun gama gaisawa da tambayan yara sai muka gangara kan mganar mu. Mun tsaya akan cewa za mu haɗa ma Hauwa 50k Munnira za ta turo min sai na haɗa na tura ma Hauwan mu ce gudummuwar ce ba yawa. "Hakan ya yi. Zan tura miki zuwa anjuma. To mganar tafiyar mu fa? "Mu je ana gobe biki. Sai mu dawo ranar lahadi ko? Na ba ta amsa, sai ta ce hakan ma ya yi itama daman ta riga da tambaya ni ko na faɗa mata ba ma mu yi mganar ba.

"To sai ki yi ƙokari ki yi masa magana duk da na san ba zai hana ki ba."

"Uhm yanzu nan ya gama ƙare min tanadi Munnira."

"Me ya faru?

Munnira ta tambaya ban ɓoye mata komai ba na sanar da ita duk abin da ya faru na ƙarishe da faɗin" Kin ji yadda ya ta so min Munnira? Har ya na ce min wai ni wani irin suna ne ba ya kira na da shi a gabanta ita ba ta taɓa nuna damuwa ba sai ni. Har ya na ce min na kama girma na." Munnira ta bushe da dariya har da ƙyatatawa. Har sai da na ji haushin ta ina faɗin.

"Ban son iskanci fa Munnira."..

Da ƙyar ta tsagaita da dariyarta ta na faɗin" Wallahi abin ne ya ba ni dariya. Lalle an nuna miki iya duniya Sadiya ke ma me ya kai ki? Ina ruwanki da sunan da ya ke kiranta? Ba Daugther ba Allah ya sa ruhinsa zai kira ta bai ma kamata ki nuna kin san yana yi ba, ballanta har ki nuna damuwar da zai samu damar faɗa miki mgana"

"Ni fa haushi ya ke ba ni. Abu kaɗan ya ce Daugther."

"To ina ruwan ki? Ke ma wallahi laifin ki ne, ke kika jawo duk maganganun da ya faɗa miki maganar gaskiya fa kenan" A daƙune na ce" To na ji ai shike nan" "Ba maganar shike nan. Gaskiya ce. Ke ma yadda na san ki da kama kanki me ya kaiki shiga abin da bai shafe ki ba wannan karon? "Ttsautsayi." "Allah ya raba mu da tsautsayi to." Munnira ta faɗa ta na min dariya sai na ji haushi na kashe wayata na bar ta ta na min dariya.

Nima sai daga baya na yi ma kaina Allah ya ƙara da ban yi magana ba, da bai samu damar faɗa min maganganu son ran shi ba, da haka na yaƙice tunanin haka na shiga ayyukana amma a ƙarƙashin zuciyata ina ta auna maganganun Yallaɓai ba wasa ba ya faɗa min mganganu masu zafi amma tun da ni na shiga huruminsa duk ma abin da ya faɗa min ai ni na jawo shi. Ɗan wannan maganar ashe shi Yallaɓai ya ɗauka da zafi da ya dawo gidan ina masa sannu da zuwa, da ƙyar ya amsa ni kamar na faɗa masa cuta ina ganin haka na kama kaina domin nima ina da zafi ba zan bari ya ɓata min rai ba, in hakan ta faru to ni da shi ba za ta yi mana kyau ba. Abinci ma da na haɗa masa nan ya bar min kayana bai taɓa ba da safe ma tea kawai ya sha ya fice jira ya ke yi ƙila na sake bashi haƙuri bayan duk haƙurin da na bashi jiya ai ko sai da a yi zama a haka.

Readers Also Read