Turken gida book 2 cmplete by janafty - Chapter 43
Turken gida book 2 cmplete by janafty Chapter 43: Turken gida book 2 cmplete by janafty Chapter 43. Ranar daman ya bar gidana kuma har ya koma gidan…
3,370 words
Ranar daman ya bar gidana kuma har ya koma gidan Gimbiya ya gama kwanakinsa bai kirani ba, sau ɗaya ya zo gidan daddare shima wasu takardu ya zo ɗauka. Yadda ya basar da ni nima haka na basar da shi, tun da har na bashi haƙuri da farko ni kuma a raina na ƙudiri niyyar ba zan ƙara bashi haƙuri ba kuma. Kar ma ya haƙura shi ya sani. Ga shi ina son na tambaye shi maganar zuwa Rano amma ba fuska. Cefane ma Salisu ya kawo min kuma da in zai kawo Yallaɓai na kiran waya ta ya faɗa min amma ranar bai kirani ba, ni kuma da ya zo gidan ban yi masa mgana ba.
Ranar da zai dawo wajena ranar Matar Musbahu ta zo min yini Mubeena mai kirki da ita. Yadda Musbahu ya ke ɗan gidana itama haka ta ke a wajena domin shi da kan shi ya nuna mata ta daraja ni shi ya sa ta ke girmanani. Ta na zuwa gidana sosai ta yi min yini. Ni ko bai fi sau biyu na taɓa zuwa gidanta ba da lokacin bikin su sai kuma da muka je tare da su Hauwa, na ji daɗn zuwanta da ya ke ta na da wayewa ta na ma karatu ne anan BUK Kano sai dai ta na shekaran karshe ne, ga ta ba ta son jiki in dai ta zo tare muke yin ayyukan mu, ita da bakinta ta ke faɗa min acikin hira Anty Bahijja har gida ta je ta na yi mata faɗan wai ta kama ni kamar ni ce yayar mijinta. Su za ta kama domin su ne dangin mijinta ni ma bare ce kamar ita. Da ta faɗa min dariya kawai na yi ni yanzu ai sun daina ba ni mamaki harkan gabana kawai na ke yi, tun da aka yi mana tsakani ba ta ƙara haɗo mu ba, duk da dai suna yi ta bayan fage. Yanzu har Halima na daina ganinta a gidana ta koma yar tsagin Gimbiya.
Ƴaƴansu daman ba sa zuwa gidana amma gidan Gimbiya har truruwa suke yi mata ni wannan bai dame ni ba. Amma nima ƴaƴana sun daina zuwa musu hutu tun da abin na su ya koma wariyan lautin fata kowa ya riƙe na shi, ko da ya ke yanzu sun daina mararin su sun koma mararin su Khalipa yanzu su ne komai suka samu na su ne ni na manta rabon da su yi ma su Jidda ma wani abun ma ban damu duk da na san a baya sun yi daga baya da suka samu waɗanda suka maye musu gurbinsu sai suka manta da su. Ban lura da wannan domin babu abin da ƴaƴana suka nema suka rasa. Yallaɓai mai yi ma iyalan shi ne shi ya sa ban cika damuwa da wasu abubuwan su ba.
Waina na yi ranar Mubeena ta ta yani muka yi aikin wainar. Har dare ta na gidana sai da Yallaɓai suka taho tare da Musbahu sannan suka koma gida tare bayan shima ya ci wainar a nan na kuma saka musu a kula su ka tafi dashi. Yallaɓai ya ɗan sake amma ba sosai ba har yanzu da sauran cin mgani a muryansa da ayyukansa ni kuma sai na nuna kamar ban ma san yana yi ba zuwa washegari sai ya saki ya dawo ya na min magana kamar ba shi ne ya ke ci min mgani ba. Fuskar da na gani ya sa na yi masa mganar bikin Rano nan ta ke ya amince ya kuma turamin 30k ya ce na yi na mota da guddumuwa. Da ya yi maganar yara na ce ga Jidda za ta iya kula da gida. Shi fa a ganin shi har yanzu Jidda yarinya ce ita kanta ta na bukatar kulawa sai na ce to ya kwashe su zuwa gidan Gimbiya kafin na dawo sai ya ce sai abin da ya gani.
Ko Munnira ban kira na sanar mata an bar ni ba. Sai dai na faɗa ma Hauwa muna tafe ranar jumma'a ta na ta murna. Ita tun ranar litini ta na can, da na tura mata kuɗin da muka haɗa kamar ta yi kuka da ta kirani ta na min godiya na ce mata ai mun zama ɗaya. Marwa na kira ranar al'amis ana gobe tafiyarmu na ce mata muna tafe ta buga tsallen ihu ta na murna daman ai ta san da bikin tun da ni da kaina bayan bikin na su na je Rano na ɗauki Marwa na kai ta har gidan su Hauwa na yi ma ta uwar ɗaki da mamansu Hauwa da ƙannenta.
Su ka kuma karɓeta hannu biyu suna zumunci yanzu bayan gidan iyayen mijinta ba ta da kamar gidan su Hauwa duk da har gidan su Gimbiya ta na zuwa amma sai wani abu ya faru na jaje ko na murna. Kawu Abba kulle gare shi ba ya son yawo ko Kano tun da Marwa ta yi aure sai da ta yi wata biyar sannan ta zo ganin gida daga nan kuma sai da ta dawo gida jego da ta koma ba ta dawo ba sai bikin Antin Ya Murja na su Jawahir ba su kwana ba a ranar suka zo tare da matan su Kawu Sa'adu a kuma ranar suka koma.
Kafin safiyar jumma'a na shirya kayana tsab don ma telana ya ɓata min lokaci akwai kala ɗayan da bai gama min ba sai da na jira. Munnira ta biyo min, ba mu tafi ba sai da su Jidda suka dawo makaranta sannan muka ɗau hanyar Rano. Yallaɓai ba gidana ya kwana ba a waya muka yi sallama. Mun isa Rano da wuri shi ya sa ko su Anty Bahijja acan suka iske mu, mun baje ana komai damu a ka gaggaisa kusan ita Anty Bahijja ko yaya ne sai ta taɓa hali sai da ta ce ma Munnira wai ka ga Aminan yayar amarya har an hallara akan lokaci Munnira ta ce tabbas dole mu hallara akan lokaci domin ta Hauwa shirye shirye a matsayin mu na Amininta.
Marwa nan gidan su Hauwa ta so muka haɗu da mangariba ta tafi za ta ce gida ta shirya ta na da aikin dare ne ranar. Mu kuma nan gidan su Hauwa muka kwana washegari aka tashi da yinin biki da ɗaurin aure, ni kwata kwata tun bayan saukan mu ba mu yi waya da Yallaɓai ba kuma bai faɗa min zai zo ba, duk da na san zai zo ɗin amma ban ɗauka tare da matarsa za su zo da yara ba sai ganin su Jidda kawai na yi wa ya kawo ku? Wai tare muke da Anty Gimbiya da Abba. Sai ga Khalipa da ita kanta Gimbiyar ɗauke da Anwar kenan shi ya tuko su alhalin ni bai nuna min ma za ta zo ba. Ban nuna mata wani abu ko a fuskata ba muka gaisa. Lokacin ni ban ma yi wanka ba sai daga baya ankon less ɗin da muka yi mu uku muka saka gabaɗayanmu wani marroon da baƙi yi yi mana kyau duk in da muka gifta sai an ce kai leshin nan ya yi kyau. Har cikin gida su Yallaɓai suka shigo Allah ya sanya alheri da shi da Kawu Abba da Tariq sai Musbahu sai Nasir da Muttaka. Sannan a ɗakin samarin gidan su Hauwa suka zauna aka kai musu abinci ni dai ban je ba domin na ga Gimbiya ce ke kai da kawo sai na bar mata amma dai mun je dukkan mu mun gaishe da mazajen namu.
"Madam kin fa samu duniya"
In ji Yallaɓai ya na kallona ni ko sai na kalle shi ina yi masa fari kafin na ce.
"Allah ko! In ma duniyar ce ai kai ka ba ni ita a hannuna Yallaɓai."
"Wannan gaskiya ne Uwargidan Alaji Tafida ba."
Tariq ya faɗa ya na dariya Kawu kan cewa ya yi." Ba dole ya ba ta duniyar ba. Saboda ita ce ta san shi tun kafin duniyar ta same shi."
"Tariq ya su Farida? Sai ban gan ta ba." Na faɗa ina kauda maganar Kawu Abba tun da na ga Gimbiya ta shigo lokacin Yallaɓai sai fama da yara ya ke yi, Khalipa ya manne masa ga Anwar a jikinsa duk sun ƙi bari ma ya ci abinci ni dai ina gefe a raina na ce can ku ƙarata.
"Wallahi ba ta samu zuwa ba saboda makarantar yara."
Tariq ya ba ni amsa, zan yi magana Munnira ta ja ni muka fita waje ta na min raɗa. "Ke na ga matar nan sai wani rawan kafa ta ke yi ne" Sai na kalleta ban ce komai ba na wuceta ina faɗin" Ta yi ta gama Munnira." Daga haka na koma cikin gida na bar su, can ma aka fara ƙidan ƙwarya muka je can muna chasewa da aka ce filin na yayyen amarya ne, muka shige fili ni da su Hauwa muna ta rawa ana yi mana liƙi sai can da yamma su Jidda suka ce za su tafi Gimbiyar ma ba ta min sallama ba a raina na ce a gayas, to uban gayyar bai min sallama ba ballanta ita. Amarya cikin garin Kano za a kaita a daran aka tafi da ita amma mu ba mu je ba. Tun da muna gari muka ce sai mu sa rana mu je daga baya. Ranar a gidan Marwa muka kwana washegari muka yi shirin dawowa gida. An ba mu kayan biki su cincin da dublan da kayan robobin da aka raba can muka bar Hauwa sai ranar talata za ta dawo. Amma tare muka taho da wasu dangin su kuma za su je gidan Amarya.
Ko da na koma gida ba kowa, sai da na buɗe ashe suna can sharaɗa gidan Gimbiya. Yallaɓai bai kirani ba sai ni da kaina da na kira shi na ce na dawo. Shi ne da daddare sai gashi sun taho da yaran har da Khalipa da na ke murnan kwana biyu ya bar ni na huta ashe ba haka ba ne. Ranar ga gajiyan biki hayaniya ta yi yawa a can ba mu wani samun barci, amma yaron nan haka ya hana mu barci a ɗakin su Jidda na kai shi ya kwanta saboda ya fara barci a falo amma sha biyu saura muna kwance a ɗaki muka ji ihun shi dole Yallaɓai ya je ya ɗauko sa ya saka shi a tsakiyarmu kamar wani yaro haka ya tashi cikin dare daga ya ce zai sha ruwa sai ya ce zai ci abinci. Gabaɗaya ya hana ni barci, ni ƴaƴana ba su hana ni barci sai ɗan kishiya. Yaro kamar an haife shi da makirci da kissa a daran Yallaɓai ya tashi ya haɗa masa tea. Ban san yadda aka yi ya cire masa pampers ɗin jikinsa ba, kawai sai farkawa na yi da asuba na ga Khalipa ya kelayamin fitsari a sabuwar katifa ta.
Tsabar baƙin ciki ma na kasa mgana. Wallahi ko su Jidda ba su yi zaman yi min fitsari a kan katifa ba domin tun zamanin napkin shi na ke yi musu in zamu kwanta. Kuma ba na bari su sha ruwa daddare ko su sha tea amma saboda iskanshi shi Yallaɓai cikin dare ma ya ke tashi ya na ɗura ma yaro ruwa ba dole ya yi fitsari ba da na ga kalli wajen har sai da ya yi shaida a zanin gado kawai sai na kalli Yallaɓai lokacin ya dawo daga sallar asuba Khalipa na can ɗakin su Jidda.
"Yallaɓai cire ma Khalipa pampers ka yi? Ji fa yadda ya yi min fitsarin kwance."
Kai tsaye ya ce" E jiya ne ya na ta rigima sai na cire masa sai na ga ma duk ya cika shi da fitsari." Ban sake magana ba sai shi ne ya ɗago ya kalleni kafin ya ce" Ba komai ai fitsarin yaro ne. Ki kuna fanka kawai ni bari na je can ɗakin na ɗan runtsa." Daga haka ya fice ya bar ni ina bin shi da kallon takaici. Sai da na cire zanin gadon sannan na saka ruwa da omo na goge wajen na saki fanka zanin gado kuma na fita waje na jiƙa shi ina ta ɓata rai da sassafe ya sakani wahala, ba fitsarin ne abin haushi ba na ga dai ba jariri ba ne, ba zan hana shi kwana a gidana ba amma ba a ɗakin da na ke kwana da mijina ba har kuma ya kwanta ya yi min fitsari.
Shi ya sa ko su Jidda ba su ga fara'ata ba har shima ko da ya fito na haɗe rai na. Amma bai hana nai yi ma Khalipan wanka na sauya masa kaya ba. Ni kuma na je na wanke zanin gadon da ya yi min fitsari na shanya. Duk da Yallaɓai ya siya mana in ji min wanki amma da hannuna na wanke shi tun da guda ɗaya ne. Da Yallaɓai zai fita nan ya bar min shi wai maman shi ba ta nan za ta je asibiti Anwar ne ya kwana ya na ciwon ciiki. Ya fita ya bar ni ina ta aikin a kitchen ina can ina wanke wanke bayan na gama gyara duka ɗakunan na saka turaran wuta. Cartton na kunna ma Khalipa na yi masa jan ido da cewa in ya sake ya tashi sai na yi masa bulala ashe yaron nan bai ji ba ina can ina wanke wanke shi kuma ya samu dispanser ya danna ya yi min ta min ɓarin ruwa har ya gangaro ya jiƙa min cafet ruwa ne cike fa sai da ya yi rabi da shi kamar an ce na leƙa falon na ci karo da mummunan aikin da ya aika ta min
Na ko kama shi na yi masa bulala biyar, saboda haushi ko ɗana ne ya yi min ɓarnan nan sai na dake shi sai kawai ya fashe da kuka ko tsayawa bi ta kan shi ban yi ba haka ya ja min aiki sai da na naɗe cafet ɗin nan na fita dashi na shanya. Sannan na koma na sake goge wajen yaro nan neman ya yi ya saka min hauka ranar ina can ina aiki amma ina fargaban abin da zan je na tarar na ƙudira a raina zan yi ma Yallabai magana sai dai duk abin da zai ce ya ce. Ga barcin gajiya a idanuwana amma ban isa na kwanta ba domin in na kwanta na san abin da zan ta shi na tarar shi ya sa bayan na gama aikin jikina da zuciyata na son na kwana na huta amma na kasa, tun da in dai na bar shi na kwanta sai ya jawo min gagurumin aiki shi kuma ga shi ba ya barcin rana ballantana mu kwanta tare.
Ba ni na samu na huta ba sai da yamma shima ba barci ba tun da yamma ta yi. Dawowar su Jidda ya sa na shiga ciki na kwanta na dai samun natsuwa kawai. Allah ya sa in da ya yi fitsarin ya bushe sai na shimfiɗa wani sabon zanin gado, saboda gajiya ana sallar isha'i na kwanta tun kafin Yallaɓai ma ya shigo. Na dai haɗa masa abincin sa a dining, ni ban san yadda aka yi ba tun da da wuri na kwanta can cikin barci na ji kuka sannan da muryan Jidda ta na kiran sunan Abba sai na farka a firgice lokacin har Yallaɓai ya farka shima kuma ya kunna hasken ɗakin ma.
Waya ta na jawo a gefen gado na duba lokaci ɗaya da rabi na dare. Hankalina ya tashi na ɗauka wani abu ne sai da na ga Yallaɓai ya buɗe ƙofa sai ga Jidda ta ɗauko Khalipa ya na kuka ya na ganin uban ya maƙale masa ya na kuka, shi kuma Yallabai sai ya rumgume shi ya na faɗin.
"Shii ga Abba nan shii."
"Abba ya tashi ne ya na ta kuka ya na cewa sai an kawo shi wajen ka."
"To Jidda je ki kwanta. Sai da safe."
"Sai da safe."
Ta faɗa kafin ta juya, shi kuma sai ya rufo ƙofar ya ɗauko Khalipa, ina zaune sake da baki ina kallon abin mamaki yau ɗin ma wataƙila kamar kullum ya fara barci ne aka kai shi ɗakin su Jidda shi ne ya na farkawa ya ga bai ga Uban ba shi ne ya saka musu kuka. Na kasa magana ganin Yallaɓai ya kwantar dashi a tsakiyar mu, har ya na lulluɓe shi da bargo. Zuciyata ta ciwo ni yau ko ɗana ne sai na yi maganinsa ballanta ɗan kishiya. Ina iya ƙoƙarina amma yau kam an zo ƙarshe.
A fusace na miƙe sanye na ke da doguwar rigar barci hulan kaina ma ta saɓule. Kitson kaina shiko ne har ya ɗan fara ma tsufa tun da ban yi kitson bikin nan na Rano ba.
"Me hakan ke nufi Yallaɓai?
Na faɗa ina kallon shi, ƙoƙarin kwanciya shima ya ke yi kafin ya ce" Zai kwana tare damu. Me ya sa kike tambaya? "Saboda ban gane ma'anar abin da kake yi min ba." Sai ya kalleni kafin ya ce" Me ye ba ki gane ba? Kwanan Khalipa tare da mu?
"E."
Na faɗa afusace saboda na fara harzuƙa ma da tambayoyin shi.
"Miye a ciki? Ai ba yau aka fara ba ko? Kin san ai Khalipa ba ya iya barci sai tare da ni ko can gidan ne ita kanta Daugther ta san haka."
Ya na gama faɗin haka ya koma ya kwanta ya na faɗin" Ki rage mana haske." Sai na ga yaron ya yi shuru Yallaɓai na kwanciya ya wani maƙale shi, baki na saki ina kallon shi, na ma kasa magana amma na ji a raina yau dai sai dai Yallaɓai ya zaɓa ko kwana da ni ko kwana da ɗansa.
"Yallaɓai ni ce zan fita na bar maka ɗakin ko kai da ɗanka ne za ku fita ku bar min ɗakina?
Na faɗa kai tsaye ina kallon shi, sai ya yi shuru bai motsa ba. Ina ganin haka a fusace na fizgi filo na kuma janye bargon da suka rufu da shi da ƙarfi ina faɗin" Zan bar muku ɗakin." Sai kawai na ga Yallaɓai ya miƙe a fusace ya riƙe bargon da na fizge ya na faɗin.
"Sadiya me kike shirin aikatawa haka?
"Abin da ka ji ka gani mana "
Na bashi amsa a fusace saboda raina tuni ya gama ɓaci. Kawai sai ya fizge bargon ya shimfiɗa ma Khalipa. Yaron ya lumshe ido ban sani ba ko barci ya ke yi, har gabana ya tako ya na kallona kafin ya ce.
" Sadiya yaushe kika koma haka? Yaushe kika zama haka?
"Yaushe dai ka zama haka dai Haba ba ka yi min adalci. A ina ne aka ce dole sai da yaro zamu riƙa kwana? Ko ƴaƴana ka fi kowa sani suna shekara uku da wani muke raba shimfiɗa da su. Me ya sa shi ba za ku koya masa hakan ba?
"Na faɗa miki a can ma haka ya ke. Ba ki ga yaro ba ne? Zuwa gaba zai daina."
"To ni ina ruwana da can ma haka ya ke yi, ai can ɗin in ya yi wajen uwarsa ne, haba ni fa na gaji na yi kara na yi kawaicin amma ba ka gane ba. To daga yau ta kau in za ka kwana da ɗan ka, ka sauya ɗaki ko ni na bar maka daƙin gabaɗaya amma ba zan ƙara kwana da Khalipa ba."
Har na gama faɗa na ya na kallona. Sai kawai na ga ya yi mirmishi kafin ya ce" Ba sai kin bar mana ɗakin ba, tun da ɗakin ki ne mu za mu fita mu bar miki ɗakin."
"Beter."
Na amsa masa ina girgiza jikina.
"Amma kin ban mamaki, ban taɓa tunanin haka kike ba Sadiya. Ashe gudan jinina ba jinin ki ba ne? Ashe Khalipa ba ɗaya ya ke da Jidda da Baby ba?
"Ɗaya suke domin ko su ba ka ga ina kwana a gado ɗaya da su ba."
Hannu ya ɗaga min ya na cigaba da faɗin" Sai yanzu na gano ki. Baƙin ciki kike yi a kan yara nan Sadiya ba tun yau ba, sai dai ban saka abin a raina ba saboda ina ƙaryata hakan sai ga shi yau kin tabbatar min.'