Turken gida book 3 cmplete - Chapter 10
Turken gida book 3 cmplete Chapter 10: Turken gida book 3 cmplete Chapter 10. Ta faɗa tana mini yatsina. Na ga rainin hankali a lamarin Gimbiya fa ya fara…
3,367 words
Ta faɗa tana mini yatsina. Na ga rainin hankali a lamarin Gimbiya fa ya fara yawa tun ina hakuri tana ƙure ni daman kuma tun da na samu cikin nan a wuya na ke abu kaɗan ke ɓata mini rai ina kiyaye mata sabo ni ba sa'ar yin ta ba ce wanda ya ijiye mu ni shi ne daidai da ni tun abun na mu na mu uku ta ja sai da mutane su ka far ga da abin da ke faruwa domin ni dai ba zan yi shuru ina kallonta ta na so ta ci kasuwa a kaina ba.
"Ba ko a yi mini laifi ba. Amma ina tunanin wata ƙila ni na yi miki laifi tun da tun shekaranjiya in muka haɗu a gidan nan in na yi miki magana sai ki yi kamar ba ki jini ba yau ma ban dandara ba ina ganin ki na yi miki mgana kika yi banza da ni. Ni ko Gimbiya me na yi miki da zafi haka? Me na yi miki da ya sa kike jin haushina?
Kawai sai matar nan ta fara ɗaga murya tana faɗin" A a malama ɗan dakata ba na son sharri ni yaushe kika yi mini mgana ban amsa ki ba? Ai ko sai dai in ban ji ki ba. Ni dai ki tsaya da mganar nan a nan ahto domin kar ta je gaba. Yanzu sai ki ji magana a gaba ana ƙokarin ɗora min jarkar tsaba."
Naja na yi mata mgana amma tana mini rashin kunya har ta na wani ƙara yarfa hannu tana cigaba da faɗin" To Naja haka kurum ina cikin zaman lafiyana ta jawo mini wani masifan. Yanzu nan sai ki ji mgana ta kai kunnen Daddy shi kuma da yake ba ta laifi a wajensa ya hau ni da faɗa. To ba na so mganar ta tsaya iya nan, maganar kin yi maganar na yi banza da ke ban san an yi haka ba wataƙila lokacin da kika yi mini maganar ban ji ba ne."
Ai sai na ma kasa mgana sabida mamaki lokacin har su Munnira sun zagaye mu suna tambayan ba'asi ita kuma Gimbiya Naja na janye ta tana ba ni haƙuri tana ce ma su Suwaiba ba wani abin faɗa ba ne na ce ne na yi ma Gimbiya mgana ta yi banza da ni sai ita kuma Gimbiyar ta ce ba ta ji ba ne. Amma ba faɗa ba ne.
"Ba faɗa ba ne ta ke faɗa minI kar na kai mganar gaba? Wato ga munafuka ko me? Kin taɓa jin wani abu ya faru Yallaɓai ya ce daga bakina ya ji? Ina ruwana da sha'aninki da za ki tsaya a gaba na balle na riƙa hirar ki da miji? Kina gidan ki ina gidana me ye haɗina da ke! Ni ma sha'anin gabana ya isheni ba ni da lokacin wannan sannan ban gane kin ce wai ni daman ba na laifi a wajen shi ba? Me kike nufi? Sannan kina nufin ni zan yi miki ƙarya ne Gimbiya? Na ci riban me? Ke ma kan ki kin san ba ki isa na yi miki ƙarya ba domin isar ki ba ta kai har haka a wajena ba"
"Sadiya me ya faru?
Maman farko da tambayeni lokacin da ta ƙariso wajen ina ƙoƙarin magana kawai sai Gimbiya ta buga shewa tana faɗin" Ahayye. Shi ya sa na ga kin yi ƙutun ƙutun kin tafi Kaduna. To ina fatan kin je kin ciwo abin da ba ki taɓa ci ba ko?
"Ke Gimbiya me ye haka?
Anty Maimuna ta faɗa tana shiga tsakanin mu.
"Ba dai rashin kunya za ki yi ma Sadiyar ba ko?
Anty Zabba ta faɗa. Hauwa ko rike ni ta yi tana cewa kar na ce komai Munnira ko faɗi take yi" Jaruba wallahi kika ce za ki yi ma Sadiya rashin za ki daku a falon nan wallahi."
Wata shewar ta buga kafin ta ce" Ko ita ba zan da kun mata ba. Ballatana ku yan koren ta."
"Haba Saudatu"
Maman Farko ta faɗa kamar ranta ya ƙara ɓaci Anty Bahijja ba ta wajen daga baya a ka kirata ta zo dai dai lokacin da Munnira ke sa'in sa da Gimbiya.
"Ni kaina ba kai isar da zan yi sa'in sa dake ba. Ballanata Sadiya ta fi ƙarfin ki. Kuma Kaduna ta je ke ma ya sa ba ki je ba? Kin ga kenan isar ki ce ba ta kai ba ita kuma da na ta isar ya kai miji ya sahale mata ta je duk shi ne haushin na ki? Sorry ki yarinya mijin wata kika aura dole ki zamo ta baya ko kina so ko bakya so. Kuma na san duk wannan kumfar bakin da kike yi ba a kan tafiyar mu Kaduna ba ce, haushi ne baƙin ciki kin ji labarin Sadiya na da ciki sannan Tafida na ririta ta shike nan sai hassadarki ta motsa wato kin so ne ke da kika zo kika aure mata miji sannan kuma ki zama ke ce ke ta haihuwa ita kuma ko oho ko? Sai ga shi ba ke kaɗai ke da Allah ba. Ubangiji na kowa da kowa ne. Ta samu ciki kin kasa ɓoye hassdarki shi ya sa kika zo za ki yi ma mutane rashin kunya. To ba sa'an ki anan kuma duk tsiya dai a baya kika zo sai da aura ta rage sannan kika samu."
"Ke Munnira"
In ji Anty Bahijja. Maman Farko ba ta yi magana ba Anty Maimuna ce ta ce" Munnira ke ba za ki ba da haƙuri ba sai hura wuta! Wallahi kar na ƙara jin bakin ki"
"Ta yi magana dole fa a mayar mata da martani domin rashin kunya ce za ta yi ma mutane."
Munnira ta faɗa a fusace. Anty Zabba sai ta yi aikin hankali ta kama hannuna tana faɗin" Ta ho mu je Sadiya kin ga ba ke kaɗai ba ne. Ɓaçin rai kaɗan zai iya shafar abin da ke cikin ki. Munnira ai ta gama mgana taho mu je." Har na bi ta, saboda raina ya ɓaci har wani duhu duhu na ke gani amma tabbas Munnira ta faɗa masu zafi shi ya sa ta kasa magana amma Gimbiya ba ta so mganar ta tsaya nan ba sai ta fara masifa har tana fizge hannunta a cikin na Naja da ke riƙe ta, tana faɗin kar ta tanka mgana ta mutu har Maman Farko sai da ta roƙe ta da kar ta ce komai a bar mganan hakanan
"Ahayye. Nanaye baƙin cikin me zan yi niSaudatu! Ai duk haihuwan da za a sake yi ma Daddy sai dai ta biyo bayan haihuwar da na yi masa. Biyu ne amma kamar da goma ne. Irin kuma haihuwar da ba a taɓa masa ba sai da ya auro ni sannan na haifa masa.'"
"Ke Saudatu me ya sa ke b a ki jin mgana ne?
Maman Farko ta faɗa a fusace tana cigaba da faɗin" A na cewa a bar mganar kina ƙara magana?
"Kyaleta Mama ba riba za ta ci ba domin kowa a nan wajen ya san ba ta da gaskiya."
In ji Suwaiba saboda kowa ran shi ya ɓaci da mganganun Gimbiya. Har na ci burki da zan juya na bata amsa Munnira ta ƙara fansana
"Wallahi ƙarya kike yi. Ai am gama yi ma Tafida farar haihuwa tun haihuwan Jidda. Kin san soyayyar a haifa ma ɗa kana tashen samartaka! Kin san girman soyayya auran saurayi da budurwa? Wallahi ko goma za ki ta haifa maza sai dai ki biyo baya amma ba dai ki zo a gaba ba. Kuma in Sadiya ta haihu ki rubuta ki ijiye sai kin gane cewa ke dai kin yi irin na ki haihuwan amma ba dai ki yi irin na Sadiya ba."
Na so na yi shuru amma sai na kasa saboda na biyu kenan ta na faɗin ta yi haihuwan da ba a taɓa yi ma Tafida ba saboda ta haifi maza ni kuma ban iya haihuwan namiji ba shi ne ban iya farar haihuwa ba. kawai sai na juya na fizge hannuna daga na Anty Zabba na isa gaban Gimbiya ina kallonta kafin na ce.
" Sau biyu kenan ina jin kina nuna bambamci tsakanin su Khalipa da su Jidda. Ban yi miki magana a farko ba amma yau na kasa haƙuri sai na tanka. Gimbiya ni fa Yusuf kaɗai na aura kuma soyayyace ta sa na yarda da shi har ma iyayena suka aminta da shi muka zama a ƙarƙashin inuwar aure. Yau ko mata dubu zan haifa da ɗigon jinin Yusuf wallahi ni Allah ya gama mini komai Gimbiya. Ya tsamoni cikin duba ya yi mini ni'imar da ba kowa ya yi ma wa ba. Haihuwan namiji ko mace ni ban ɗauke shi a wani abu ba. Ɗaya na ɗauke shi. Mata suna da matuƙar tasiri a rayuwar mu da addininmu. Kin manta cewa mace ce ta fara karɓan addinin musulunci a mata? Kin manta da tarihin matar Firauna? Hasiya da irin gwagwarmayan da ta yi domin addinin Allah. Ko kina da labarin Allah ya gina mata gida a Aljannah? To kamar yadda Maza suke da tarihi a cikin addininmu haka ma Mata ke da wannan tarihin. Saboda haka ni in mata Allah zai ba ni ina so in ta haihuwarsu ina roƙon Allah ya shirya mini su. Ya kuma sa su yi ma addininsu hidima. Ke kuma da kike son Mazan saboda tunanin su ne ke da gidan Allah ya yi ta baki ko dubu za ki haifa wallahi tallahi ba zai tsole mini gefen ganina ba Gimbiya. Gargaɗin da zan yi miki shi ne ki daina ƙoƙarin mayar da ƴa'ƴana a baya. Suma ƴa'ƴa ne dai-dai da irin haihuwan da kike tunanin kin yi a kan su Khalipa."
Ina gama faɗin haka na wuce. Maman farko ta jinjina kai tana na faɗin" Shi kenan Sadiya kin gama mgana." Kowa sai ya yi shuru ya yi sanyi ita ko Gimbiya sai ta fashe da kuka jin yadda har Hajiya iya da ba ta san farkon faɗan ba ta na salla sai da ta ce Gimbiya ce ba ta da gaskiya.
"Ko ba ta girme ki ba ai tana gaba da ke a aure."
"Balle ma wallahi Sadiya ta girme ta. Sai dai ta yi sa'ar ƙanwar ta Amina."
In ji Munnira, Suwaiba ta karɓe da cewa" Tsaya tsaya ma ko da ma a ce ba ta girme ta a shekaru ba a gidan aure ita ce babba. Kuma bai kamata ta girmama ta ba? Ai kowa ya ji wannan abin da ya faru a san ba ki ta ki gaskiya ba Gimbiyan"
Ni dai ban tsaya ba na ce zan tafi gida. Yau ma tun safe rabon da mu yi waya da Yallaɓai. Anty Maimuna ta ba ni mamaki har da ita a masu ba ni haƙuri Anty Bahijja kuma ta rufe Gimbiya ta faɗa tana kukan munafunci. Tare da Marwa da Munnira muka fita Hauwa ta ce Muttaƙa zai zo ya ɗauke ta. Anty Zabba kuma gidan su ta ce za ta je ta kwana. Amaryan ta ma tun da suka sauka daman gidansu ta sauka bikin ma daga can ta zo. Muna cikin adaidaita Munnira sai jaraba take yi tana ce mini wai ina yi ma Gimbiya sanyi sanyi shi ya sa ta raina ni.
"Wallahi ta ba ni mamaki ko kunya ba ta ji ba."
Marwa ta faɗa cikin mamaki. Munnira ta ce"To daman tana da kunyar ne! Wallah ba ta da kunya ta daɗe tana neman da man da za ta ci kasuwa a kan Sadiya." "Sai me? Don Allah ku bar mganar ni wallahi raina ma ƙara ɓaci yake yi "
Na faɗa ni a ƙokarina su bar mganar amma Munnira ba ta bar ta ba sai masifa take yi tana cewa na faɗa ma Yallaɓai domin ya dauƙi mataki. "Ni ba ruwana ba ki ji ta ce kar na kai ta gaba ba." "Ki kaita ɗin domin ta san kin isa."
Shuru na yi ban yi magana ba. Saboda ni ba halina ba ne wannan surutun, abubuwa da dama sai dai ya ji su can a bakin ƴan gidan su. Ni bar ni da mgana in na ga za a cuce ni ko magana kan lamarin da ya shafe ni amma ba ruwana da mganar kishiya. Ko kafin ma ya yi aure ko hatsiyar mu da yayyen shi ban taɓa faɗa masa sai dai in ya ji labari ya zo ya tambaye ni amma ba dai ni na kwashi jiki na je ina ce masa an yi kaza an yi kaza ba. Shi ya sa yau ɗin ma na yi shuru amma har a ƙasan raina ba zan faɗa masa ko da kuma ba zai ji labari ba amma dai ina da yaƙinin tabbas zai iya sani.
Mu mai adaidaita ya fara saukewa sannan ya wuce da Munnira. Allah ya so ni ga Marwa ina komawa gida na kwanta sai zazzaɓi ita ce na samu ta dama min kuni na sha ya zauna a cikina. Ni saboda bacin rai ko Baby ban nema ba da zamu taho. Sai kawai na ce gobe sai su dawo tare da Jidda. Haka Yallaɓai ya zo ya same ni a kwance ya yi ta faɗan sai da ya ce ba ya son na je Anty Zuwaaira ta matsa sai an je da ni gashi nan na dawo ba ni da lafiya sai da na ce masa ba fa komai ba ne aman da na yi a can sai ɗan zazzaɓi kuma ya san ina yin zazzaɓi haka daddare sannan ya ɗan sarara da faɗan da ya fara
Paracetamol ya ba ni na sha na yi sallah na kwanta sai na ji daɗin jiki na zuwa safe kuma sai na ji ya sake ni. Marwa ta gyara minI gida ta yi mana abin kari itama da safen ta wuce Ɗorayi za ta gai da su Gwaggo. Daga can ta wuce gidan su ta kwana da safe ta wuce Rano. Iya kwanakin da Kawu ya ba ta kenan. Ni kaɗai a gida domin Yallaɓai da hantsi shima ya fita, sai can bayan la'asar dai ga shi an kawo su Jidda. Ita na samu ta yi girki ni kuma na ce ta dama mini kuni domin wanda Marwa ta dama min tas na shanye shi kuma shi kaɗai na ke samu ya na zama a cikina sai ganye haka irin su Kabeji, latas da allayahu. In a ka sanya su a cikin abinci ina samu na ci sosai. Amma wani kifi wani nama ko warin shi ba na so balle su ƙwai da sauran nau'ikan abincin da ba na so ma na ji warin su in ana dafawa. Ni warin ma maggi mai star ne kwata kwata ba na so shi ya sa na daina ma giftawa ta Kitchen ɗin na bar ma Jidda ne ban san yadda yake ciki ba, domin na daɗe ban shiga cikin sa ba.
Har a ka kwarari kwana huɗu da dawowata gida ban ji Yallaɓai ya yi mini wata mgana ba. Sai ranar jumma'a ranar ma ba a gidana yake ba yana gidan Gimbiya ne. Yau Mubeenan Musbahu ta zo ta yinin mini ita ta yi girki da gyaran gida. Tun da ya ga ba ni da lafiya yana yawan turo ta gidana kuma ina jin daɗin haka. Sai dare Musbahu ya zo ya ɗauke ta shi ya sa na koma ɗaki na kwanta saboda na ji na fara jin sanyi sanyi. Ina cikin bargo ina shafa kasan marata cikina ya shiga wata na huɗu kuma har ya fara turowa. Ina jin ƙaunar abin da ke cikina sosai wata ƙila don irin wahalan laulayin da na ke sha ne na tuna kafin bikin Suhailat maganar da muka yi da Yallaɓai.
"Yallaɓai in na mace na haifa sunan Mama za mu saka mata."
"In kuma Namiji ne to sunan Alhajin Ɗorayi za mu saka masa ko?
Ya ƙarishe mini yana dariya. Nima dariyan na yi kafin na ce" Ka yi gaskiya. Tabbas haka ne a raina." A lokacin jawo ni jikinsa ya yi yana faɗin" Kar ki damu fata na ki sauka lafiya duk sunan da kike so shi za mu sanya kin ji ko? Sai na ji daɗi har ina ba shi sumba.
Vibration ɗin waya ta ne ya dawo da ni daga tunanin da na faɗa. Ta na gefen in da na ke kwance ne na saka hannu na ɗauko ta sai na ga Yallaɓai ke kirana. Ban kawo komai a raina a tunanina sallama zai yi mini kamar yadda ya ke yi in bai samu zuwa ba.
"Zan taho da Daughter yanzu ina so mu yi mgana gabaɗaya."
Abin da ya ce minI kenan bayan mun gaisa. Sai na ce masa sai sun taho. Har muka gama wayar tunanina bai hasaso mini kan abin da ya faru ba ne sai daga baya na fara tunanin wataƙila kan haka ne amma kuma a ina ya ji? Ko wa ya faɗa masa? Watsar da tunanin na yi saboda ba ni da mai ba ni amsar su.
Sai da suka zo gidan sannan na fito daga ɗakin na saka hijabi amma duk wanda ya gani ya san ina fama da azaban laulayi duk na yi fari na lashe na kuma rame. kullum ina fama da bushewar baki da maƙogwaro. Ina ganin Gimbiya sai na tuna da faɗan da ya shiga tsakanin mu da ita shi ya sa na yi kamar ban gan ta ba kamar yadda itama na ga ta yi, sai wani cin magani take yi tana wani hura hanci.
Shima gogan ransa a ɓace na gan shi da ga gani sun yi ta ne kafin su ƙariso. Jidda ya haɗa da yaran gabaɗaya da cewa su koma falon su za mu yi mganam ita ta tattara su suka bar mana falon. Shi yana saman kujera mai zaman mutun uku ni kuma ina zaune a mai zaman mutum biyu a gefen sa ita kuma sai ta zauna kan mai zaman mutum ɗaya muna fuskatan juna ni da ita. Ai ni tun da ta yi mini wannan wulakancin na yi alƙwarin duk in da za mu haɗu in ba ta ce sannu ba ba zan tanka ta ba. Da mutumcina ba zan zauna wacce ba ta isa ta zubar mini da ƙima ba.
"Ba ku gaisa ba?
Ya faɗa bayan ya kore shurun namu gabaɗaya.
"Tsakanin ni da ita wa ya zo ya samu wani?
Na tambaye shi ina mai kallon shi da idananuwa da suka ƙanƙance.
"Ita ce "
Ya faɗa yana kaɗa kai, ni ban yi magana ba sai shi ne ya kalleta kafin ya ce" Ki gaishe ta mana." Ta yi shuru taƙi mgana ni dai kaina na ƙasa ina wasa da gefeb hijabina da ya sani bai ɗauko mini ita ba. Ta zo har falo na tana yi mini Taƙama.
"Ba da ke nake mgana ba."
Na ji ya da ka mata tsawa.
"Ina yini."
Ta faɗa kamar dole. Ko da ya ke ai dolen ce ya saka ta.
"Ke kuma ki amsa tun da ta gaishe ki."
Ya faɗa muryansa a sama daga gani yau an taɓo zuciyar ƴan maza.
"Lafiya lau."
Nima na faɗa a tsume saboda ni ba gan amfanin wannan zaman ba tun da wacce ta yi laifin ba ta ji a karan kanta ta yi nadamar abin da ta yi ba.
"Hakan da kuka nuna shi ne ya ƙara tabbatar mini akwai wani abu da ya faru a tsakanin ku wanda kuka rufe ni ba ku gaya mini ba. Ban sani ba ba domin Kawu Abba ya kirani ya faɗa mini ba, sannan Maman Farko ma ta kira ni ta ce na tara ku kun samu yar hatsaniya ranar a gidan Bahijja amma cikin ku a ka rasa me faɗa mini wani abu ya faru? Me ya sa haka?
Dukkan mu muka yi shuru. Ni sai da ya faɗa sannan na gano in da ya fara samun labari. Wato Marwa ce ta sanar ma da mijinta shi kuma ya kira Yallaɓai ya faɗa masa. Sai Maman farko da ta yi masa mgana ashe ita ma mara kunyar ba ta faɗa masa ba.
"Daku fa na ke mgana?
"Me ya sa ba ku faɗa mini ba?