Turken gida book 3 cmplete - Chapter 9
Turken gida book 3 cmplete Chapter 9: Turken gida book 3 cmplete Chapter 9. Ban je gidan bikin ba ma sai ranar laraba da a ka yi mothers eve ɗin. Yallaɓai…
3,305 words
Ban je gidan bikin ba ma sai ranar laraba da a ka yi mothers eve ɗin. Yallaɓai ma cewa ya yi in ba zan iya ba na yi zama na su Jidda su tafi sai na ce zan iya. Tare da su Hauwa muka tafi can muka iske matar Muhammad Kabir Nafisa har Faridan Tariq ta zo Marwa ma ta zo muna tare da ita tun da gidana ta sauka. Anty Bahijja ta sha gayu ka ce ita ma Amarya ce da ƙawayenta suma yan gayu su Gimbiya ana ta shiga da fita har makeup ta yi su Khalipa ma an sha gayu. Anwar ne ma na gan shi a hannun Baby ta na fama dashi, Ni dai na je na gaishe da uwar biki na yi mata fatan alheri shi ne ta ke ce mini an ce ba ni da lafiya na warke kenan na ce mata Alhamdulillah.
Kowa ya ganni sai ya ce na rame amma fa na yi shar da ni. Suwaiba kam har sai da ta ishe ni wai ban ga kyan da na yi ba ne ko Tafida ya ganni kafin na fito na ce ban sani ba. Mun haɗu da Gimbiya amma ba ta minI mgana ba da cewa ita ta na fama da jama'a ba ta ganni ba ni ko na ce ba zan bi ta domin mu gaisa ba. Ita da Najan Anty Zuwaira ne akan komai kuma suma sun ui gayyar ƙawayen su irin su yan gayu kirari kawai suke yi mata tun da kusa damu suka zauna a haraban gidan in da aka saka kanofi da kujeru. Su Ma'u ana gefe ba karsashi to ta ga iyayenta a kinibibi dole ta koma baya.
Gimbiya suke ta raba takeaway da snack a ciki da naman kaza sai ruwa da lemu. Da ta zo wajen ƙawayen na su sai shewa ya hau ta shi ana yi mata kirari. "Ka ga Saudatu sa'ar mata. Gimbiya kike sunan ki ne. Kuma kin cika Gimbiya a zuciyar Injiniya Yusuf Tafida. Takawarki lafiya giwar Tafida. Takawarki lafiya Amaryan Tafida. Takawarki lafiya uwar maza a gida ko da kika je an haihu amma ke da kika tashi sai kika yi irin haihuwan da ba a taɓa yi ba. Ka ga uwar maza a gidan Alhaji Yusuf Tafida. Ko gobe aka sake masa haihuwa ba za a kwantata irin ta ki ba"
Sai suka buga shewa ta miƙa hannu suka tafa ta jiya musu kugu kafin ta ce" Wallahi ko gobe aka sake masa haihuwa ba za ta kama kafar irin tawa haihuwar ba faɗi ki ƙara." Ta faɗa ta na wani fari da ƙara juyawa. "Takawar ki lafiya ki juyi dai Gimbiya a girman ki ne. Kin ci lokacin kuma za ki ci na wasu in sha Allahu kuma daga kanki ba ƙari kin cika duka gurbaben mata huɗun nan" Sai kawai ta ɓalle jaka ta fara zazzaga ma mai yi mata wannan kirarin kudi suna ta ihu da shewa sai hankula duk ya koma kan su.
Duk da Maganar suke yi amma ko waye ya ji ya san magana ce mai harshe damo ko na ce habaici. Hauwa ta kalleni ganin na yi shuru kawai ina zaune. "Kamar fa da ke suke. Wai ko da ta zo an haihu amma ba a yi kamar irin ta ta ba" "Kuma wai ko da an sake haihuwan ba za a sake irin ta ta ba" Munnira ta amshe itama.
"Da Sadiya fa suke yi. Shi ya sa na tsani Gimbiyar nan munafuka ce baƙn ciki take yi kin samu ciki ta so ne ita ta yi ta haihuwa ke kuma ki zama yar kallo."
Hauwa ta saki tsski kafin ta ce" Wallahi haka ne ma. Sai kin ji mganganun da take zuwa gida ta na yi. Ta yi ma Tafidan da Dangin sa haihuwan da ba a taɓa yi masa ba. Tun da ta haifi maza har ji fa na yi wai ta ce yadda ya ke son su Khalipa ko su Jidda albarka."
"Ka ji sakarya. Ya fara samun su Jidda? Ai wallahi ƙarya ta ke yi.'
Baƙin ciki suka hana ni mgana amma na daure jin Munnira ta ce wallahi za ta tashi ta je ta yi musu mgana sai na riƙe ta ina faɗin" Rabu da su so suke a tanka a yi wani abu kuma ace ba mu da gaskiya ku ƙyaleta. In za ta je ta faɗa ma duniya cewa Yallabai ma ya fi son ta a kaina ni bai dame ni ba. Fatana na sauka lafiya."
"Allah ya sa ki haifi namiji na ga ta tsiya."
Sai na yi mirmishi ina tuna wayar da na yi da Dr. Aisha AKTH. da na faɗa mata ina da ciki ta yi murna karshe ta ce Allah ya kawo boy ni kuma na ce mata ko boy ko girl duk wanda ya Allah ya bani ina iso. Yanzu ɗin ma cewa na yi.
"Ko namiji ko mace duk wanda Allah ya ba ni iso."
Suna kallona sai na kaɗa kai kafin na ce" Ni ba ruwana da jinsi Ni ko duka mata zan tara ina so. Ita haihuwan maza ke gabanta."
Daga nan na kashe maganar. Amma har Suwaiba sai da ta zo wajen mu ta na zagin Gimbiya a cewarta ni ban yi kishi da ita ba ita da ta aure mini miji sai ita. Ant Zabba ba ta wajen da ya ke so sun iso har da Amaryan Usman ɗin itama da tsohon ciki za ta yi haihuwa na uku kenan itama kamar Gimbiyar gwarne take yi. Da ta zo wajen mu ta ji ana mai da zence ta yi ta mini masifa ta na faɗin ina da sanyi na daina sanyi da kishiya za ta rika cin kasuwarta a kaina na yi dariya kawai ban ce komai ba.
Sun yi fa abubuwa Gimbiya da gayya ta ke komai amma ni ban biye mata, sai mangariba a ka tashi sai a lokacin Ant Zuwaira ta zo tana zuwa kuma ta nemo ni ni da Munnira da Anty Zabba ta ce mu shirya da mu za a je Kaduna kai Amarya.
"Anty Zuwaira ina fama da kaina'"
"Ai kin ji sauƙi ko ba za ki iya zuwa ba ne?
Sai na kasa musa mata sai ta buga kafaɗata da cewa" Ku ne matan kawunne manya saboda haka da ku za a je." Sai na ce to Allah ya kai mu Hauwa a ka ce ba za ta je su sai daga baya ba a son a je da yawa ne. Anty Zuwaira ta ce ba da ita ba Anty Maimuna ce da Nasara sai Suwaiba da Halima a yayyen uwa iyaye kenan sai Maman farko da Hajiyar Tafida da ƙanwar baban Sulaihat ɗin a kakkanin Amarya. Sai ƴaƴan yayyen baban ta guda biyu ƙawayenta. Sai a nan aka zaɓo ɗiyar Anty Maimuna sai yar makarantar su guda ɗaya ƙawarta. A Rano kuma an saka yayar Gimbiya amma ita ban ji an saka ta ba sannan har da Faridan Tariq Marwa ma an saka ta ita kaɗai a ce a matan kawun ne. Ana so a yi lamarin da tsari ne kamar da angon ya bukata ba su son cikowa abun ka ga masu kuɗi. An ce matukin jirgin kasa ne Captain akwai kuɗi a hannun shi sannan zuru'an su suna da kuɗi nima duk a bakin Munnira nake ji tsuliyan gari.
Da na koma gida ni kaɗai yara duk suna can na baro su za su kwana. Sai ga Yallaɓai ba a gidana yake ba sai ya ce Gimbiya da yara can za su kwana sai washegari jumma'a ranar walima muna karyawa ya ce.
"Za ki iya zuwa kaduna kuwa? Ya Zuwaira ta matsa mini sai ke dai kin je."
"Nima haka ta faɗa mini jiya. Ni da Munnira da Anty Zabba."
Yana kurɓa tea ɗin dake hannun shi a mug ya ce" Na ce ga Daughter tun da ita ce ta ce minibza ta je kai Amarya amma sai ta ce a a dole sai ke tun da ke ce Babba."
Ban yi magana ba amma ni kaina na san Gimbiya za ta ce sai ta je kaduna kai amarya yadda ta ke rawan jiki da bikin nan.
"Shike nan tun da za ki iya zuwa sai ki shirya. Amma please ki kular mini da kanki da Baby na."
Ya faɗa ya na mini murmishi. Nima sai na yi masa murmushi kafin na ce" Da na ce ko ita Gimbiyar ta je? "A'a gaskiya Ya Zuwaira ta faɗa ke ce Babba kuma ke ɗin ce wakiliyata so ke ɗin ya kamata ki je tun da kin ji sauƙi." Sai na gyaɗa kaina ban saka aka ba wallahi. Ranar mun je walima ban san me ya faru ba mun haɗu da Gimbiya a ƙofar shiga falon Anty Bahijja ina washe mata baki ta yi kamar ba ta ganni ba ta ɗauke kanta. Har ta na ture kafaɗanta sai da muka shiga ciki ne Suwaiba ke faɗa mini kan tafiya kaduna ne an ce su bari sau ranar lahadi sai su je tare da wasu kayan ita da Naja shi ne ta ce ita tuni su yi mgana da Tafida kuma ya ce za ta je Kaduna. Ita kuma Anty Zuwaira ta ce ni ce zamu tafi da Amarya gobe shi ne ta fita tana ƙunƙuni
"Topha."
Na faɗa a fili a raina na ce ni ban ga abin ɓacin rai ba. Munnira ta ce ta raina wayon ta akan kai amarya sai kace zuwa madina? Ni dai Allah ya kyauta kawai na ce kuma a ranar sai da Anty Zuwaira ta tabbatar mini da na shirya da ni za a je. Ranar ma ba ta yi mini mgana ba sai fushi take yi tana cika ta na batsewa. Ma'u ta ba ni tausayi da bikin nan kamar ba a santa ba, ita kanta Anty Bahijja ta na fama da mutane ba ta bi ta kanta ba, sai dai tana raɓe wajen dangin mijinta da a ce muna zaman amana ne ni da ita za mu haɗe to da yake ba ta da hali sai ta zama kamar mujiya ga shi Shema ta yi aure da a da ne tare za su zo.
An sha wa'azi malamai uku aka gayyato mata suka yi ma amarya wa'azin zaman aure da zamantakewa sai mangariba a ka tashi. Yallaɓai ya zo ya ɗauke ni wajen taran dare kuma ko gidan bai shiga ba. Bayan mun koma na ga ya na ta waya abin da ya sa na fahimci da Gimbiya yake mgana saboda maganar da ya yi mata.
"Me ya sa kike da taurin kai ne Saudatu? Na ce miki ba za ki je ba Sadiya ce babba ita za ta je kuma hakan ne ya kamata."
"Ok to ki yi yadda kike so"
Ya faɗa a fusace ya kashe wayar. Ban taɓa jin ya kira sunanta ba sai ranar, ta kwaɓe musu saboda zuwana Kaduna ni ko da karambani bayan mun kwanta na ga har lokacin bai huce ba sai na ce masa na hakura ya bar ta ta je kawai.
"Wallahi ba za ta je ba. Ke ma in ba za ki je ba fine amma na riga na rantse ba za ta je ba kuma kin san ba macen da isa ta saka ni na yi kaffaran kan aikin banza da wofi."
Ai ina jin haka sai na koma na lafe a kan filo na ji shuru. Shi da kan shi da ya hucen ya matso ni jikinsa lokacin na ma ɗan fara barci ina ƙoƙarin motsawa na ji yana mini raɗa a kunni.
"Sai da safe"
Ban amsa mishi ba saboda barcin ya fara fizgata. Na dai ƙara shiga jikinsa sosai na lafe shi kuma ina jin sa yana rufe mana jiki da bargo.
*Janafty**TKGB30E05*
Washegari asabar muka tashi da shagalin biki. Sha ɗaya na safe a ka ɗaura aure kuma sun ce a lokacin za su tafi da amarya. Shi ya sa duk nuƙu nuƙun da a ka tsaya yi ɗaya da rabi motacin ɗaukan Amarya suka miƙa hanya. Ni mota ɗaya muka shiga da Munnira da Anty Zabba sai Marwa. Faridan Tariq tana motar Amarya a gidan gaba.
Da yake motocin sabbi ne sannan kuma masu lafiya ne a na gudu ma sai ka ji kamar ma ba a yi. Zuwa huɗu da rabi biyar saura mun sauka a gidan Amarya. Mun iske matar Jafar Nauwara, sai ƙawayen Anty Bahijja ina ga su ƴan Kaduna nan ne da wasu dangin angon su suka tarbe mu. Ma sha Allah gida ya yi kyau ƙwarai. kuma iyayenta sun kashe mata kuɗi kayan ta kaf ba na Nigeria ba ne a ƙasar waje a ka siyo su kuma ba a sauke su ko'ina ba sai Kaduna. Kuma da ya ke akwai ma'aikata maza su suka gyara komai, mu kan mu kayan kitchen ne muka zo da shi sai su cafet da labulanya sai ɗan abin da ba a rasa ba. A nan muka yi sallar la'asar muka ci abinci sannan muka kama a ka ƙarisa gyaran daƙun nan. Muna gidan har dare dangin mijin na ta zuwa a nan ne ma mu ke jin jibi jibin nan za su bi jirgin yawo zuwa Madina, mai son ganin ɗakin Amarya sai dai ya jira bayan salla kuma in sun dawo daga Hajji.
Ba a gidan Amarya muka kwana ba. Ni da Munnira da Anty Zabba har da Marwa gidan Faridan Tariq muka kwana. Ita ma Nauwaran Jafar ta diɓi wasu ƴan'uwa. Daga ƙawayenta sai kakkaninta a ka bar Amarya da su ta kwana. Kuma bayan mun kwana can muka hantse sai wajen sha ɗaya muka dawo gidan Amarya da ke anguwan malali. Da yake abin na yan gayu ne ba wani cikowa sannan an gyara ko'ina tsab. Muna komawa ba daɗewa sai ga Naja ta zo ita da Suwaiba da Halima sai Anty Maimuna jiya ba su samu tafiya ba. Ni dai ban ga Gimbiya ba, ban kuma Tambaya ba amma Munnira sai da ta tambayi Suwaiba ita kuma ta ce Gimbiyar ce ta mata musu lokacin a na ta jiran ta daga baya ta ce su ta fi ba za ta je ba. Zuwa kai Amarya kamar wani kayan gabas ni Sadiya? Sai da muka yi azahar muka ci abinci sannan a ka kawo mota muka ɗau Amarya da su turamen atamfa da shadda sai kayan abinci da su cincin ɗin da su Naja suka taho da shi.
Gidan Iyayen mijin muka je da ke NDA. Muka kai musu Amarya sannan da kayan da muka ta ho da shi. Amarya ta samu tarba da kuɗaɗe sosai. Da ya ke suna da kumbar susa ko su gidan iyayen na shi ma a abin kallo ne. Sai a lokacin suke faɗa mana tafiyar su Madina jibi in sha Allahu a ka yi ta fatan alheri. Muna gidan har wajen uku saura sannan muka yi shirin tafiya daman kowacce da shirin ta tun da sun faɗa mana daga nan Kano za a wuce da mu. Nan muka bar Nauwaran Jafar da Farida sai Hajiyar Tafida da Tariq ya riƙe ta wai ta jira shi zuwa gobe zai saka a mai da ita gida. Mu kan mu an ba mu turamen Atamfa kowaccen mu sannan da kuɗi cash 10k sannan a ka ɗauke mu zuwa Kano cikin motocin alfarma kamar yadda a ka ɗauko mu.
Ba mu isa gida ba sai bayan Mangariba kuma suna ijiye mu suka juya zuwa Kaduna. A gidan Anty Bahijja muka sauka tun da ita ce uwar biki ya kamata ta ga dawowar mu, amma ba domin haka ba gidana zan wuce na gaji sannan kasala duk ya rufe ni, tun da muka je ban ci wani abincin kirki ba. Na yi amai duk na galabaita barin ma yau ɗin amma ban ƙi sauka ba. A na ta yi ma na maraba da dawowa muna zaune dukkan mu a falon Anty Bahijja a na ta mai da yadda a ka yi a can Kaduna. Maman Farko na ta faɗin Sulaihait ta yi dacen surukai masu dattako sai fatan zaman lafiya sannan ga labarin kyautar ban girman da a ka yi ma na Anty Bahijja sai faman washe baki take yi. A raina na ce wato kowa na son na shi ya je ya ji daɗi. Amma ta na takura ma wasu in ta ga suna jin daɗi lalle wanzami daman a ka ce ba ya son jarfa.
Tun da muka sauka kowa na ta zuwa mana sannu da zuwa. Tun da akwai sauran jama'a a gidan har Hauwa a gidan muka same ta. Ni ban ma san Gimbiya tana gidan ba sai da na fara ganin Khalipa. Ban ga Jidda ba sai Baby ita ke faɗa mini Jidda na gidan Gwaggon su Zuwaira. Bedroom ɗin da ke falon Anty Bahijja na shiga domin na kama ruwa na yi salla ina shiga na ga Gimbiya ta fito daga cikin tiolet ɗin cikin ɗakin ɗauke da Anwar kamar ta wanke masa kashi ne tun da na gan shi ba pampers. Ina ganinta na washe mata baki ina faɗin.
"Maman Khalipa ashe kina gidan?
Amma sai matar nan ta yi kamar ba ta ji ni ba, gani ni da ita a cikin ɗaki ban dandara ba na sake faɗin.
"Mun dawo yanzu ba daɗewa a na ta hira a falo ban gan ki ba."
Na saki baki kawai ina bin ta da kallo domin zuwa ta yi ta raɓa ta gefe na ta fice daga ɗakin kamar ba ta san Allah ya yi ni a tsaye a wajen ba. Har ta na banko ƙofar a saman fuskata bam! Jikina ya yi sanyi ban san adadin sakannin da bakina ya yi a buɗe kafin na rufe shi ba. Jikina a sanyaye na shiga tiolet na yo alwala na zo na yi salla da hijabin da na samu a cikin wardrope ɗin ɗakin ina jin na Suhailait ne domin ɗakin nata ne kafin aure ya tashe ta.
Ina idarwa na fito da niyar na ce ma su Munnira ni zan ta fi gida. Sai kawai na ga Gimbiya suna mgana da Naja. Kamar zan wuce na ƙyaleta sai kuma wata zuciyar ta ce na yi mata mgana na ji ko na yi mata wani abu ne da zan yi ta mata mgana tana mini wulaƙanci.
"Anty Sadiya ba dai tafiya ba?
Naja ta faɗa ganin na taho in da suke tsaye a gefen falon suna mgaana. Tana ganina ta wani haɗe rai kamar ta ga mutuwarta.
"E yanzu na ke son tafiya ba na jin daɗin jikina ne."
"Gaskiya sannu. "
Ta faɗa sai kuma ta juya tana ce ma Gimbiya."Amai ta yi ta yi a can wallahi." Ban san ko maganar ta suɓuce mata ba ne, ko kuma daman da niyya ta faɗa ban sani ba sai ji kawai muka ji ta ja wani ubn tsaki kafin ta ce.
" Mtswww to ina ruwana ni dai mu cigaba da zencen mu. "
Ba ni kaɗai ba hatta Naja sai da ta ji wani iri ina kallonta ta na ma Gimbiyar mgana da ido. Ni ko da farkon da na zo wajen har na sauya shawara na wuce kawai ba tare da na yi mata mgana ba tun da na ga da ta ƙara ganina ta haɗe rai amma kalamanta na yanzu su suka ɓata mini rai ya sa na ce sai na yi mata mgana.
"Amma ko dai ba ruwan ki ai mgana mai daɗi ma Sadaka ne in ji Annabi(SAW)"
Na ma yar mata da martani ina kallonta sai ta wani ɗauke kanta sama jikinta na jijjiga irin ƙiris take jira ɗin.
"Don Allah ki yi haƙuri Anty Sadiya." Naja ta faɗa ta na kallona na so na danne zuciyata na yi haƙurin amma sai Gimbiya ta ɓata komai.
"Mi ye na wani ba ta haƙuri an yi mata wani laifi ne?