Turken gida book 3 cmplete - Chapter 8
Turken gida book 3 cmplete Chapter 8: Turken gida book 3 cmplete Chapter 8. Kamar wasa na yi ta samun odar masu siyan hijabai da inners barin ma da azumi…
3,335 words
Kamar wasa na yi ta samun odar masu siyan hijabai da inners barin ma da azumi ya ke tunkaro mu. Da ya ke a mota kawai ake saka mun ina tura masa bayanan da kololin na Hijabai inners kuma sara na yi da yawa na yara da manya na tura kuɗi a ka kawo minI har na cin kasuwar salla. hijaban dai sai na ƙaro tun da guda 50 na ce a akawo mini. Da suka iso duk wanda ya siya ni da Jidda muka yi zaman saka su. A leda muna manna sticker sai lamarin ya burgeni ni kaina komai da tsari kan ya fi burgewa Jidda ta yi Vadeo muna saka sticker ta kuma ɗora mini a status ta ce kaya sun iso. Nan da nan cikin sati ɗaya kaya suka ƙare sai na sake tura kudi ɓarin ma Inners ɗin sun tafi yadda ma ban yi zato ba daman su Hijabai ana siyan su sosai. Wannan karon sai na ce a sako mini da mayafai da kayan barci suma dai ba laifin ana ta siye da na gida da na waje.
Sana'ata na riƙe gadan gadan. In dai ka ganni da waya to ina can ina marketing. Yallabai har suna ya sauya min wai hajiyar Hijabai ni dai na ce ka ji da iyayin ka tun da karatun dai bai zo hannuna ba gwara na kama abin da ya zo hannuna. Ana cikin haka a ka kawo mana kayan saka ranar Suhailat ɗin Anty Bahijja bayan sallar azumi za a yi bikin kuma Kaduna za a kai Amarya. Ni da kaina na kira ta a waya na yi mata Allah ya sanya alheri. Ni ba na gaba da ita muna gaisawa in mun haɗu amma daga wannan gaisuwan kowa sabgan gaban shi yake yi tun da aka yi mana tsakani ni da ita.
Cikin ikon Ubangiji muka riski watan ramadana cikin lockdow abubuwa duk sai a hankali saboda yanayin zirgan zirgan gari duk da ba kamar lokacin gari na sake ba wannan karon ma Yallaɓai ya siya buhun gero da siga sai wake buhu ɗaya na alale da ƙosai na kai ma Maman Saude yin kunin ita kuma Maman Nana mai yi min kitso a ka ba ta yin ƙosai da alalen. Sannan ya rarraba ma matansa da ke aiki a ƙarkashin sa kayan abinci wasu kuma ya ba su kuɗi, daga can Rano Kawu Abba ya aiko mana da su ƙwai da dankalin turawa. Nima Yallabai ya ba ni kayan abinci har da kuɗi na kai gida duk da na san itama Gimbiya ya ba ta ta kai can Rano amma ni bai gaya mini ba, ban nemi da sai na ji ba kuma Azumi ashirin da tara muka yi kuma ban sha ko ɗaya ba ko da ban ga period ɗina ban damu ba, ko watan da ya wuce ma bai zo ba saboda an sha yin azumi ni ban sha ba sai ban saka tunanin komai a raina ba. Yallaɓai ya yi mana kayan alfarma ni da yara har salla ta wuce muna saka sabbin kaya sannan ya yi ma iyayena har Inna Mariya ya yi ma turmin atamfa wannan shekaran. Ni kuma na caɓa da cinikin hijabai da inears wannan sallar kaf su Ya Hamza wajena suka yi ma iyalansu siyayya kuma na ji daɗi a dangin Yallaɓai kuma su Musbahu ne da su Anty Zuwaira har Anty Maimuna ta siya ma yara. Gimbiya ma ta siya kuma ta kawo mini costumer kuma na ji daɗi na gode mata. Yallaɓai ma kuɗi ya ba ni na yara sai kawai na cire musu a ciki da ni kaina na saka kuɗin a ciki. Kuma ba abin zan ce ma Allah sai godiya ina samu ina yi ma kaina hidima sannan abu na ƴan uwa ya ta so ina ɗauka na yi ba sai na je ina yi ma Yallaɓai yar murya ba. An ɗaga bikin ɗiyar Anty Bahijja sai gab da babbar sallah a bakin Munnira nake jin wai uban mijin ne ya biya ma Sulaihait ɗin kujeran makka tare da mijin ana ɗaura auren za su tafi tare na ce Allah ya sa su je lafiya su dawo lafiya.
****
Kamar kar a yi salla sai na fara rashin lafiya. Kuma rashin lafiya irin a tsatsaye haka. Kasala ya riƙa damuna na dai na cin abinci komai ba ya mini daɗi ban da kunin tsamiya mai zafi ba abin da ke shiga cikina. Sannan ba na iya shan kowani ruwa. Ba ni da aiki sai kwanciya tun ina ganin abin wasa har dai na fara tunanin watakila ina da ciki. Tun da in dai na ci abinci sai na yi amai ga Yallaɓai ba ya nan ya je Dutse wajen kwanan su huɗu a can, karyata kaina nake yi da ba ciki gare ni ba saboda ko wancan da na yi ɓarin shi ban ga alamomin shi ba sai kawai na fi amimta da maleria ke damuna na saka a ka siya mini mganin maleria na fara sha. Ai duk ranar da na sha sai na yi amai sannan sai na fara miyau ba na iya haɗiye miyau. Sannan na yi ta kwana da zazzaɓi gari na wayewa sai na ji sauki. Jidda ta ce za ta rakani asibiti na ce ba zan je ba har waya ta sata ta yi ma Yallaɓai waya ta faɗa mai halin da na ke ciki sai ya ce ta ba ni wayar haka ya riƙa mini faɗa ya kuma ce umarni ne maza maza na tashi na shirya Jidda ta rakani asibiti na ga likita.
Ba yadda na iya haka na shirya. Sai a lokacin na fahimci na rame sannan na ƙara haske, wani asibitin kuɗi muka je muna zuwa suka yi mini tambayoyi na faɗa musu wajen wata uku kenan ban ga al'adata ba sun ɗibi jinina da kuma fitsari muka zauna jiran sakamako Yallaɓai kuma sai kira ya ke yi Jidda ce ke ɗaga kiran ni ina ta kaina sai kwanciya nake yi a kujerun asibiti. Lokacin da sakamako ya fito likita ya ba ni farar takarda sannan ya faɗa mini ina da shigar ciki ɗan kimanin wattani biyu da kwanaki. Duk da alomomin masu ciki sun bayyana a tare da ni ban saka ma kaina yaƙini ba. Hawaye suka zubo minibsai na sharce su a cikin raina na yi ma Allah godiya sannan na yi masa kirari. Jidda na wajen domin ita ta riƙe ni muka shiga da muka fito ina riƙe da takardan muka samu adaidaita da zai mai da mu gida. Amma sai da Jidda ta biya Pharmacy ta siya mini magungunar da ya rubutamin na ƙarin jini da na cin abinci. Da farko da Yallaɓai ya ce zai kira Salisu ya kai mu tun da motar na hannun shi in fita haka ta kama ina kiran shi ni na ce ya ƙyale shi mu fita mu hau adaidaita sahu. Har a cikin adaidaita kwanciya na yi da leda a hannuna ina tara miyau duk cikina da na yi da ga na Jidda har na Baby ban yi miyau ba, kai ban ma yi wannan laulayin mai wahalar wa ba. Tun kafin mu kai gida Jidda ta kira Yallaɓai tana murna tana faɗa mai likita ya ce Umma na da ciki.
"Jidda da gaske kike yi?
Ina ji saboda wayar an ƙure mata kara. A yanayin muryan Yallaɓai za ka san akwai zaƙuwa da zamuɗi.
"Na rantse da Allah Abba Umma za ta sake haihuwa."
Ta faɗa cikin har sai da mai adaidaitan ya juyo yana kallonta ina ganin shi sai da ya yi murmishi ya juya kai ya na faɗin" Hajiya yanzu daman wannan budurwan ƴar ki ce? Wallahi na dauka ƙanwarki ce ni dai dariya kawai na yi ba tare da na yi magana ba.
"Ma sha Allah. Allah ya inganta.'"
Na ce Amin ita Jidda ba ta ma jin sa ta na can ta na waya, ban yi mamakin kalamansa ba saboda ba shi kaɗai ya taɓa faɗan haka ba sau tari mutanen da ba su sani ba in suka ganni da Jidda sai su yi tunanin ƙanwata ce. Saboda na haifi Jidda da ƙananun shekaru shi ya sa muka ta so kamar ƴa da ƙanwa sannan na mori ƙaramin jiki.
Ji kawai na yi Jidda ta manna min waya a kunne ta ce ga Abba na mgana. Sai da na cire facemark na tofar da miyau a ledan da ke hannuna sannan na karɓi wayar
" Yallaɓai."
"Congratulations My Sady. "
"Congratulations Yallaɓai na."
Na faɗa a hankali ina murmushi.
"Alhamdulillah Allah abin godiya. Kin gani ko? Daman ni a jiki na na ke jin ba ki gama haifa min ƴaƴa ba Sadiya. Yanzu kin aminta da magana ta?
"Na aminta Yallaɓai."
Na faɗa a hankali saboda jikina gabaɗaya ba ƙarfi, faɗi yake yi yana cikin farinciki mai tsanani sai na katse shi da cewa.
"Yallaɓai ban da lafiya. Jikina ba ƙarfi ba na iya cin abinci ba na shan ruwa."
Na ce kamar zan yi masa kuka shi kuma sai ya ruɗe. "Sannu. Me likitan ya ce! Me ya sa ba su riƙe ki a can ba? Sai na kasa mgana domin maganar ma wahala take yi mini sai kawai na ce ya bari mu koma gida sai mu yi magana. Dalilin da ya sa ya katse wayar kenan muna ko komawa gida ya sake kira ya na tambayana yadda nake ji.
"Yallaɓai miyau ya yi ta taruwa a bakina. Ni komai ma baya mini daɗi ban iya zama fa sai kwanciya ban taɓa laulayi mai zafi irin wannan ba."
Yallaɓai duk ya damu sai lallashina ya ke yi, daga ƙarshe ya ce zuwa gobe zai dawo na kula da kaina. Sai da ya kashe wayar na ji taruwan kwalla ina tausayin kaina ina tausayin shi ban ɗauka bayan tsawon shekaru goma zan sake samun ciki ba. Amma na yi yaƙini da ubangiji mai bayarwa a lokacin da ya so da kuma wanda ya so. Na saka a raina in ina da rabo Allah zai sake ba ni sai ga shi kuma ashe ina cikin waɗanda Ubangiji ke yi ma Ni'ima in sun yi haƙuri ya ƙara musu a lokacin da ba su yi tssammani ba. Ban taɓa tunanin Yallaɓai zai yi mini rawan jiki in na samu ciki ba sai ga shi yana yi min bawan Allah ya na son haihuwa. Na ɗauka tun da Gimbiya ta haifa masa biyu duka maza yanzu ba ya zumuɗinta amma sai ya kore mini shakku. Lokacin da na faɗa masaa na yi ɓari da ya nuna da yakinin wata rana zan sake samun ciki na haihu bai ɗadani da ƙasa ba kamar yadda bayan samun cikin ya nuna farincikin sa. Kwana ya yi ya na kirana yana jin jiki. Jidda kam ya yi mata kashedin ta kula da ni ban san adadi ba. Baby da Jidda ta faɗa mata Umma za ta haifa musu wata Baby yini ta yi tsalle da ihu ni dai ina kwance zama ma ba na so ina yi.
Washegari da rana Yallaɓai ya dawo duk da ba gidana zai sauka ba, yana gidan Gimbiya ne tun da ni ranar da zai bar gidana ya yi tafiyar. Amma duk da haka gidana ya fara sauka ya duba ni ya iske ni kwance da gwangwani miyau da a ka cika min da ƙasa. Ya rumgumeni nima na lafe a jikimsa shi ina sauke numfashi. Yallaɓai ya yi ta shafa marata kamar ya buɗe ya ga abin da ke ciki. Shi kan shi ya ce na rame bakina ya bushe ya yi ɓawo to ko ruwa fa ba na sha sannan ban iya cin komai sai kunin tsamiya.
Duk bakina da surutu na bakina ya mutu. Allah ya sa Jidda na gida ita ke kula da gidan da yin abinci. Yallaɓai ya faɗa ma Gimbiya ina da ciki ya kuma kawo ta ta duba ni ita da su Khalipa, ina kwance ne ina fama da kaina a saman kujeran falon su Jidda. Ina kallon Gimbiyar tun da muka gaisa ta koma gefe ta tsume. Duk da ban da lafiya amma na fahimci kamar ranar ranta na bace ne, sai na danganta haka da ƙila ita da Mijinta ne. Ko jiran shi da ya ce ta yi ma ba ta yi ba, la'asar na yi ta ce min za ta ta fi wai za ta biya ta shago. Su Khalipa ma da Jidda ta ce ta bar su sai ta ce wai daga Shago Gwammaja za ta biya shi ya sa ba za ta bar su ba. Ni dai ina kwance amma sai da na tofa na ce ta bar su mana in Yallaɓai ya dawo sai ya mai da su amma sai ta ce kar wai su dame ni ba ni da lafiya. Ina jin haka ban takura ma kaina ba na ce su gaida Nene in sun je.
Tun kuma daga ranar sama da sati ba ta dawo ba na tuna lokacin cikin Khalipa da kwanciyar da ta yi ta yi a asiniti ina jigila da ita. A raina na ce da ban haihu ba da na ji haushin duniya. Munnira ce ta kira ni a waya tana faɗa mini haihuwar Salma Yayar Jawahir C.S a ka yi mata, a ranar da ta kira ni ta ce jiya da daddare ne ta haihun shi ne ta kira ni ta ji yaushe za mu je! Tun da anan Kano ne a Dala. Shi ne na ce mata ba ni da lafiya ma ina gida. A ranar ta zo duba ni kafin in faɗa mata ina da ciki ita ta fara cewa matar injinya ciki ne da ke na ce mata e sai ta buga shewa ta riƙe hanci ta rangaɗa guda ta kuma kira Hauwa tana faɗa mata sai Hauwa ta fara faɗa min an ware ta ba a faɗa mata ba. Ni ko na ce ba wanda na sanar ma wa, nan Munnira ta yini har da lissafin sai ta ɗauko DJ ranar sunan na yi dariya kawai a raina na ce Allah ya sa na rabu dai lafiya.
Washegari sai ga Hauwa ta zo duba ni. To su ne da aka haɗu ca gidan Salma ranar suna duk wanda ya ga bai ganni ba sai su ce ina gida ina fama da laulayi. Anan ne wasu suka ji, su Anty Bahijja kuma ina da tabbacin Gimbiya ta faɗa mata gwara ma Anty Maimuna in ta ce ba ta sani ba amma zai yi wahala Anty Bahijja ta ji abu ita ba ta ji ba musamman za ta kira ta a waya ta faɗa mata. Anty Zuwaira har gida ta zo ta duba ni ta ba ni dubu ashirin ta ce na siya gero tun da na ce kunu kawai nake sha ina son ta saboda wallahi tana da matukar kirki shi ya sa nake girmamata. Ita ta ce mini Nene ce ta faɗa mata ba ni da lafiya ta zo ta duba ni, Nenen kuma na san Yallaɓai ne ya sanar da ita. Mubeena na zuwa duba ni akai akai har Marwa ma ta zo ita kuma Kawu ne ya faɗa mata ita kuma ta yaɗa ma Ya Aina ta nan maganar cikina ya faso a dangin mu kowa ya ji sai ya ce ikon Allah lalle bayan wuya sai dai daɗi sannan ba a cire ma Ubangiji yaƙini in ka yi hakuri za ka ci riba. Sun zo dukkansu sun duba ni har da Ma'u Gwaggo ma ta zo har gida kuma na ji daɗi su Ya Hamza a waya suka gaishe ni da matan su. Zainatun Ya Abubakar ta zo yi min yini, ta yi mini wanki da girki ranar.
Ranar da Nene ta zo ita da Hajiya iya da Maman farko a raina na ce duk abin dake cikina ɗan gata ne. Tun da har su Nene suka zo duniya. Nene ko faɗi ta ke yi Allah ya raba lafiya. Amma ko su kan su sun yi ta ƙorafin rama ta da rashin cin abinci na ce komai na ci sai na yi amai kuni kawai ke zama a cikina shima mai zafi. Ruwa ko rabon da in sha har na manta. Yallaɓai tsausayina ya ke yi sai ya ce ya za a yi ɗan adam ya rayu ba ruwa na ce to ga shi dai ka gani. Gimbiya sau ɗaya ta dawo shima ba ta daɗe ba ta tafi sai na ga kamar ba ta murna da samun cikina. Amma sai na yi saurin cire tunanin haka a raina sai na yi mata uzuri na kuma saka mata kyakyawan yaƙini. Inna Mariya ni da kaina na kira ta na faɗa mata ta yi ta murna ta kuma zo har gida ta duba ni.
Ko da nake kwance in ana son Hijabai ko kaya Jidda ke mgana da mai ɗinka min daga Zaria a kawo kuma ta zauna duk ta saka musu sticker ta kuma saka su a ledojinsu shi ya sa ba ni da damuwa. Na shafe wata ɗaya da wani abu ina wannan zazzafan laulayi sannan na ɗan fara samuwa. Na fara cin abinci tuwo haka sai ɗanwake sai awara sai dambu, amma ban da su shinkafa da taliya. Duk sona da fura da kayan marmari na daina son su yanzu, ruwa kuma na fara sha amma sai mai sanyi ko na ce mai ƙanƙara ya na narkewa ina sha. Yallabai ya yi ta faɗa wai sanyi zai kamani amma shi kan shi da ya ga shi ne ruwan da na ke sha sai ya ƙyale ni. Na ɗan fara samuwa tun da na daina kwanciya kasalar sai dare ya yi yanzu ta ke nika min jiki, sannan tun da na fara laulayin nan ban yadda mun yi ɓarnan ruwa da Yallaɓai ba to ina ta kaina. Shima kuma bai matsa mini ba, kuma bai sani ba kwata kwata abin ne na ji ba na ma son shi. Na ɗan fara dan kiɓan kumatu amma fa kaya na duk sun yi mini yawa. Na faɗa a raina na faɗa asarari da cewa wannan cikin ɗan gata ne shi ya sa ya ke wahalar da ni. Amma dai na ji sauƙi sosai ba kamar kwanakin baya ba.
Cikina na wata uku cikin na huɗu aka fara hidiman bikin Sulaihat ɗin Anty Bahijja. Matar nan ba ta zo ta duba ni ba duk da ta san ba ni da lafiya. Amma dai Anty Maimuna ranar ta biyo Nasara sun taho tare. Da Anty Bahijja da Halima ba su zo ba daman ita Halima tuni ta koma bangaren Gimbiya. Yarinyar nan mun sha haɗuwa a Gwammaja ko sha'anin su ta yi kamar ba ta ganni ba. Wai ni ce Halima ta ke gani ta wulaƙanta, lalle na yarda rayuwa ta na cike da mutane masu abin mamaki. Yadda ba a saka ni a shirye shirye ba, ban tusa kaina ba an dai fidda ankon mother eve da na yinin biki. Yallaɓai ya siya mini tun da matarsa ce ta ɗauko Gimbiya. Jidda kuma Anty Zuwaira ta yi mata tare da sauran sa'aninta su Farhan Anty Maimuna Baby ma su suka yi mata, ni ina fama da kaina ba ma ta kan bikin na ke yi ba, bikin zai kama babbar salla saura kwana tara ne.
Na dai san Kaduna za a kai ta. Bikin kuma zai yi jama'a tun da har Anty Zabba da muka yi waya ta ce za su zo gabaɗaya har da yara tun da ba makaranta. Sannan kaf su mazan gidan da ke zaune ne sa za su taho da matan su. Matar Jafar ce kawai ba za ta zo ba ita za ta tarbi bakin nan in ji Anty Bahijja, nima duk a bakin Munnira na ke jin wasu labaran a bakin ta na ji su Gimbiya su ne ƙirjin biki sannan har list an yi na mutanen da za a tafi da su a kaduna. A dalilin ina fama da kaina ban ji a raina zan je kai Amarya kaduna ba, ko da ma ina lafiya ba zan tusa kaina ba.