Kenza eBookz

Turken gida book 3 cmplete - Chapter 7

Turken gida book 3 cmplete - Chapter 7

Turken gida book 3 cmplete Chapter 7: Turken gida book 3 cmplete Chapter 7. Tun daga lokacin ya samu sara da na yi magan sai ya ce su Sadiyallle masu…

3,308 words

Tun daga lokacin ya samu sara da na yi magan sai ya ce su Sadiyallle masu degree da Masters ni ko na ce da ikon Allah, na gane in ina fushi ma ya fi jin daɗin tsokana ta sai na daina nuna na ji haushin shi, Maganar jari kuma tun da na ce ba na so bai ƙara mini mgana ba, ni kuma da gasken ba na so shi ya sa ma har su Ya Hamza na faɗa ma zan koma makaranta da na ce Yallabai ya amince fatan alheri kawai suka yi mini. Na gama shirina tsab saboda muna tunkaran sabuwar shekara da cewa ko Yallaɓai bai taimaka mini da sisin shi ba zan kwashe jarin hijabai na koma makaranta da shi.

****

*2020*

Da gaske na ke yi na nemi gurbin Masters a BUK Kano, kuma har na samu, har na yi cuku cuku, kuma ilai dai bangarena na farko na sake ɗauka na kula da tattalin arziki wato Economics Sannan Jidda na son ta biya Jamb tun da sai bayan sun rubuta Jam ɗin za su fara jarabawar su ta WAEC. Ko lokacin da Jidda za ta cike Jamb tare da Musbahu suka je ni ban san ina ta cike ba sai da ta dawo take faɗa minI a first chioce ABU Zariya ta cike.

"Ni dai ba ruwana kin san dai Abban ku ya ce a garin nan za ki yi karatu ba ya son nesa."

"To ni Umma ina son ABU ne kuma ai ba ga Kawu Hamza a zaria ba"

Kallonta na yi kafin na ce" Ya san da shi ɗin ya ce ba za ki je ba"

Za ta fara mini magiya na katse ta faɗin" Ba ruwana na ma faɗa miki." Ai ko da ya dawo ta faɗa masa ta sha faɗa ya kuma ce mata ta ma cire rai ba anan za ta yi ba BUK za ta yi domin ba ya so ta yi nesa. Jidda na ji ta na gani dole ta cire rai tun da Ya ce ba za ta je ba to mgana ta ƙare.

A she ya je sun yi mgana da Gimbiya itama ta roƙe shi, amma ya ce ya gama mganar sa. Ni daman ban saka baki ba sabo da tun da ya kafe da wahala ya sauya ra'ayi infact nima shirin nawa karatun nake yi Yallaɓai tun ya na ɗauka wasa ne har dai ya ga na miƙe ga kaina. Wasu abubuwan duk ta online Datti ya yi mini su sauran kuma na shiga cikin makaranta na ƙarisa. Da dai Yallaɓai ya ga tabbas na samu addmission har ya na zuga ni wai na yi part-time.

Ni ko na ce full-time zan yi. Ɗa gare ni ko jika da zan yi part-time sai ya yi shuru. Ina shirin yin rigistration ne Yallaɓai ma ya ba ni kuɗi ya ce na hidimar makaranta ban tambaye shi ba kuma da bai ba ni ba, ba zan tambaya ba. Kwatsam kawai aka fara cutar corona a Negeria, daman tun december 2019 cutar ta fara ɓulla a na mganar ta a kafafen sada zumunta. Kafin a motsa ta fara yaɗuwa a Nigeria kafin ka ce me an shiga lockdown wannan hutun na corona shi ya ruguza burina na komawa makaranta Yallaɓai sai ya koma yana mini dariya har wani suna ya saka mini wai mai kwalin masters zaman gida dole.

Sai ga shi da ga ni har yara mun koma mun dafe a gida. Jidda ke ba ni tausayi su da ke da shirin zana jarabawar fita an yi musu tsiya.

*Janafty**TKG0B30D4*

*Littafin TURKEN GIDA 1K ne on Telegram. 09069067488.*

Kina buƙatar kayan kitchens domin ƙawata Kitchen ɗin ki? Ya ke Uwargida kina buƙatar chanza ma megidan sabbin kwanukan cin abinci? Ko kina buƙatar sauya masa kofin shan ruwa? Ko kina so ki burgeshi da farantai masu kyau da yarari? Ko Amarya ce yar ƙwalisa da ke son ƙawata gidanta da kayan alfarma? To ku matso kusaa domin JANAFTY EXLUSIVE AVAILABLE Muna kawo muku ko wani nau'in kayan Kitchen da na kwalliya gida domin farincikin ku, kuma akan farashi mai rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina daga in da muke, ku tuntuɓemu ta wannan lambar domin ƙarin bayani. 09069067488 +234 706 234 9732

Ban ji daɗin ɓullowar cutar corona ba, sannan ban ji daɗin lockdown ɗin da a ka san ya mana ba gabaɗaya ƙasa ta tsaya waje ɗaya cak. Ba makarantu ba zuwa aiki komai ya tsaya, in fita ta kama ka dole sai ka saka takumkumi kamar wani ɓarawo kana tsaka tsan tsan. Shikenan Burina na son komawa makaranta ya tsaya cak shima amma duk da haka ban karaya ba faɗa ma kaina nake yi na san na ɗan lokaci ne kasa za ta daidai ta na cika burina na komawa makaranta.

Kowa na cikin takura da wannan lockdown ɗin amma sai na ga kamar Yallaɓai shi murna ma yake yi, ko don ba aikin gwammati yake yi ba ne wataƙila domin ya ga na shi ayukan ba su tsaya ba ne shi ya sa. Sai daga baya na fahimci har da zama na a gida ban samu tafiya makaranta ba kamar yadda na ci buri saboda ba shi da aiki sai tsokana ta har wani suna ya saka mini yanzu Hajiya Saadiya mai kwalin mastes. In kuma ya tashi tsokana ta da cewa masu masters dai an koma zaman gida tun ina nuna jin haushina shi kuma ya yi ta dariya har wani jin daɗin tsokana ta yake yi ranar dai na gaji na ƙufulu na ƙudirta a raina in ya sake tsokana ta sai na mayar masa da martani kamar ya ko san ina jiran shi sai ga shi ranar ya kwana a gidan Gimbiya sai ya biyo nan gidan da safe mu gaisa sai ya iske ni na ci gayu na cikin riga da wando ina zaune a saman kujeran falon ina danna waya ta lokaci ɗaya kuma ina ɗan kallon talabijin ɗin da Baby ta kunna cartoon a ke yi a MBC3.

Da Surraya Dee mai kyan ɗa'a muke chart na tura mata ciko kuɗin ta domin satin da ya wuce na siya mganin sanyi da haɗin kaza. Tana ta mini tsiya saboda sai da ta ƙara kirana ta ce ta ji shuru ba ta ji ni ba, ni kuma na ce mata lokacin muna ɗan hatsaniya ne da megidan da ya ke ta san yanayin tun da itama matar aure ce. Ta ce Mazan ne sai a hankali su yi tutsu in sun so a yi daɗi ana yi in suka so tsiya ma sun san ta kan shi. Shi ne fa muke ta hira da ita a kan matsalolin rayuwa na yau da gobe.

Jidda na ɗaki tun da suka daina zuwa makaranta in dai ba aiki za ta yi ba tana cikin ɗaki tana karantu Baby ce yar falo mu yi ta hidiman mu, itama ɗin yau ta na can falon Abban na su ta na zane zane a takardu ta bar ni, ni kaɗai ina ta danna waya ta. To tun da an kulle mu a gida sai kafafen sada zumunta suka zama ababen debe mana kewa. Na ji shigowarsa suna mgana da Baby a falo ban tashi daga zaunen da nake ba sai ga shi ya shigo cikin shigar ƙananun kaya ni Yallaɓai har mamaki ya ke ba ni shi bai son ya girma ba ne? Ko don jikinsa ba ya nuna shekarun sa? Ya kama kafar wajen shekaru arba'in da bakwai amma kuma yana jin kansa kamar ɗan shekaru talatin.

"Wannan kallon fa Madam?

Ya faɗa lokaci ɗaya yana jan hancina. Ashe ya ƙariso har gaba na ban sani ba.

"Ko na yi miki kyau ne?

Ya sake faɗa yana mini murmushi har yana kashe mini ido ɗaya.

Sai na yi dariya kafin na ce" Wani kyau? Ina kallon ka ne, a raina ina cewa Yallaɓai na ya fara tsufa"

Yana zama gefena yana faɗin" Ko? Ke dai ce da mganarki amma ni har yanzu ji na, na ke yi kamar ɗan saurayi mai shekaru talatin." Sai na buge kafaɗansa ina dariya kafin na ce" Jidda fa ƴ'ar ka ce? Ko ka manta ne? Sai ya jawo kafaɗata saman tashi ya saka hannunsa guda ɗaya ya zagayo ƙuguna da shi.

"To sai me! Ke in ba fa na faɗa ba ɗan Saurayi a ke kallona. Kuma tsab in na tsai da budurwa yar sha za ta tsaya mini"

Hararan sa na yi kafin na ce" Wai ko dai ƙara aure da za ka yi da yarinya ƙarama ne Yallaɓai?

"Me kika gani?

Ya faɗa yana dariya ƙasa ƙasa.

"To na ga da an fara mgana sai ka ce ko yanzu za ka iya auro yarinya yar sha sa'ar Jidda."

"To in ma da gaske ne Haramun ne?

Ai sai na buɗe baki ina kallon Yallaɓai. Ganin na kasa mgana ne ya sa ya rufe mini baki yana mini dariya sai na ture shi gefe ina hararan shi. Shi kuma ya na ƙara naniƙe ni ina ture shi yana minidariya.

"My Sady kishi"

"Ina ruwana ai ba a kaina za ta zauna ba kuma ai ni ka gama mini kishiya. Gimbiya ce a kan layi "

Dariyan nishaɗi ya yi kafin ya ce" Ka ji ta kamar gaske" Na yi masa banza saboda na ga alamun ya na so maganar ya yi dariya ya na jin nishaɗi. Da gaske nake yi ai ni ya gama mini kishiya ko wata zai aura sai dai Gimbiya ta ji ƙwatan ƙwancin yadda na ji a lokacin da ya auro ta. Kallon sa nake yi yana tambaya ta Jidda na ce ta na ɗaki sai ya tashi ya shiga dakin na bi shi da kallo. Yallaɓai bai taɓa ce mini yana sha'awan tara mata ba amma ni a ƙasan raina na ke jin giyar kuɗi za ta iya ɗibar sa ya ji mun yi masa kaɗan kuma wannan wargajenjen filin da na ji labarin ya siya ba, ba iya ni da Gimbiya ba ne. Wataƙila shashen mata huɗu ne zai gina a hasashena tun da bai taɓa furta mini haka ba. Ya ce sai an gama ginin kamfanin shi an buɗe shi sannan zai fara ginin gida can kwanaki ma da muka bi ta hanyar na ga Kamfani ya yi nisa kaɗan ya rage a ƙarisa.

In ana misalin maza jajirtattu masu jajircewa da juriya to sunan Yallaɓai zan fara kamawa a shekarun da na san shi sama da shekaru goma sha takwas ya jajirce domin mafarkinsa ya tabbata na gina kamfanin shi, domin ya taimaki matasan da aikin yi to ko a haka ya tsaya wallahi ya cigaba domin matasan da suke aiki a ƙarkashin shi shi kan shi bai san iyakar su ba. Da masu ilimin da ma waɗanda ba su da ilimin duk na shi ne, masu ilimin suna aiki a bangaren ma'aikatan shi mara sa ilimin kuma suna aiki a bangaren kwangilan gine ginen shi. Kuma ya na da tausayi da kyautatawa ga kuma mu yadda ya ke kyautatama mu da iyayen shi, shi ya sa Allah ba zai bar shi ya taɓe ba.

"Ke wai me ke damun ki kike yawan shiga tunani ne?

Na ji yana faɗa lokaci ɗaya ya na mai zama a gefe na. Har ya na wani jawo ni jikinsa yana shafa bayana zuwa kuguna sannan ya cigaba da faɗin. "Uhm mene ne. Faɗa mini damuwarki yanzu na yi miki mganin ta." Kamar abun arziƙi na ɗago ina kallon shi kafin na marairai ce ina faɗin" Yallaɓai wai yaushe za a buɗe gari ne? Tsakani ga Allah ba a kyauta mana ba da yanzu fa mun yi nisa da lectures"

Me Yallaɓai zai yi in ba dariya ba, har ya na ƙyaƙyatawa. Ni kuma sai na haɗe rai na koma gefe na yi bakam. Ina jiran ya taɓo ni sauke masa jin haushin shi da nake ji.

"Ai in za ki shirya zaman gida ki shirya. Domin cutar ma ƙara yaɗuwa ta ke yi ba ma maganar a buɗe gari."

Kallona ya ke yi fa yana tsintsira min dariya.

"Hajiyar Masters. Ki yi wannan master ɗin ki a gidan auren ki, taho mu je ciki ni ma ai malamin ne sai na baki karatu"

Ya ma miƙo hannu ya kamani na bige hannun shi ina hararan shi amma bai saka ya daina dariya ba.

"Yallaɓai."

Na kira sunan shi a tsume.

"Na'am My Sady masu kwalin masters"

"Ni dai ko murna kake yi da faruwan wannan abin ne? Ko daman can da ka ce ka bar ni na koma makaranta ba har zuciyar ka ba ne?

Na ƙarishe ina mai kura masa ido. Ya na danne dariyarsa ya ce" Wallahi har raina na amince miki. Ya za a yi na yi murna da haka? Ya ƙarishe faɗa yana daga hannu sama amma bai daina mini dariya ba.

"Na ga kamar murna kake yi. Wato gara da a ka yi haka ko?

"Murna kuma! Da girmana Sadiya?

Ya faɗa yana sosa sajensa amma bai daina dariya ba kawai sai na miƙe fuu da wayata ina faɗin"Ohon in ma ka na murnan gwara da a ka yi ne gwara ka daina saboda ba ni kaɗai ba ce a gidan har da ƴaƴan ka"

"Kuma haka ne fa."

Ya faɗa yana kuma cigaba da dariya.

"Kuma in sha Allahu, za a buɗe gari kuma zan shiga makaranta Ehe."

Na faɗa ina mai barin masa falon sai ya biyo ni yana faɗa mini. "In sha Allahu wa ya isa ya hana ki zama mai kwalin masters" Gabaɗaya Yallabai ya mai da ni abar nishaɗinsa na so ina shige ɗaki na rufe ne sai ya shammace ni ya biyo ni yana faɗin shi fa ba dariya yake yi mini

"Wallahi in na tuna yadda kika ci burin karatun nan sai na ji duk ba daɗi. Sorry My Sady in sha Allahu zaman gidan ba zai yi tsawo ba."

Wani kallo na yi masa saboda yana faɗa ne amma yana danne dariyan shi kawai sai na fusata na jawo filo na wurga masa ina faɗin. " Ka fita Yallaɓai" "Na je ina? Har tsayawa yake yi yana tambaya ta, sai na ƙara rarumo ɗayan ina ƙokarin jifan sa da shi sai ya mamayeni ya rumgumeni yana mini dariya ni kuma ina fizge fizge sai ya fara min cakulcakuli a dole sai na yi dariya. Yallaɓai akwai mugunta wallahi sai da na yi hawaye, har fa sai da na ce masa zan yi fitsari a wando in bai daina ba sannan ya ƙyaleni. Bai bar gidan ba sai da na dai na fushi na dawo ina dariya ni ce har haraba na raka shi muna soyewar mu.

*****

Tun ina saka ran za a buɗe gari na yi registration ɗin makaranta har na cire rai ganin har mun shiga wata biyu muna kwararan na uku, sai na ce gwara na zauna na yi ma kaina tunanin mafita. Tun da karatu dai ba zai yuyu ba gwara na mai da hankalina kan sana'ar hijabai na da yadda zan ƙara ingata shi, sai na fara tunanin sunan da sanya ma kasuwancina. Da ƙwaƙwalwar ta ƙi sai na nemo Jidda na ce ta sama min suna. Haka muka zauna muna ta zaɓe har sunana ta haɗa ni da Yallaɓai SADYUF na ce ba na so da a baya ne zan iya haɗawa dashi amma tun da ya yo mini kishiya na fahimci Yallaɓai ba nawa ba ne ni kaɗai. Ta haɗa da haruffan sunanta da na Baby na ce ba na so sunan ya yi kama da na ma'aikatan Yallaɓai ne. HM TAFIDA AND SON'S LIMITED. Sai na ce a samu dai wani ganin zai yi wahala na ce kawai ta haɗa min da sunana, mun yi kwanaki ba a samu wanda ya yi min ba sai da na ce mata ina so na saro inears wear sai ta ce to bari a haɗa gabaɗaya. Da ƙyar dai Jidda ta samo min SADY S YASHE HIJABS AND MORE. Sai na ji sunan ya kwanta min arai nan take na ce bari mu tafi da wannan sunan kawai.

Musbahu na nema tun da shi ne ɗan gida ne kuma idon gari ne kusan ya san ko'ina. In da Allah ya taimake ni kuɗin da Yallaɓai ya tura mini na hidimam makaranta da na ce zan mai da masa sai ya ce na riƙe na ƙara jari ya bar mini, da su na yi amfani domin ƙara bunƙasa kasuwancina. Musbahu ya shige mini gaba a ka buga mini ledojin da tambarin logona na SADY S YASHE HIJABS AND MORE. An yi manya da ƙanana sannan an yi na kwali su na manya costumer ne Sannan an yi min sticker na mannawa a jikin kaya bayan na siya ledoji farare da zan riƙa saka hijaban da kayan in an siya. Tun dai an samu zaman gida bari mu kama sana'a zama bai ganmu ba. Musbahu ya saka cikin masu zanen su na kamfani ya zana min logo mai kyau na saka shi a duka handle ɗina na kafafen sada zumunta.

Kuma kowa ya gani sai ya ce sunan ya yi kyau. Ya Hamza sai da ya ce bai ga sunan Yallaɓai ba ina dariya ban ce komai ba har Ma'u da muka daɗe ba mu yi mgana ba da na ɗora a status a ƙasa na yi caption da cewa.

"SADY HIJABS AND MORE. Muna siyar da nau'in hijaban da kuke so sannan za mu fara kawo muku inners wears, kamar su pants, bra, sikat, mini trouser and more. Please potonorize your Sister. Sadiya Sulaiman Yashe C.E.O"

A nan Yallaɓai ya gani ya yi tagging ya turo mini dariya. Na shaka na auna masa naushin hannu na sticket kawai sai ya yo mini Vn ranar ma ba a gidana ya kwana ba yana gidan Gimbiya amma a daran zai dawo gidana.

"Daman shawaran nan na kawo miki tun farko kiƙa ƙi karɓa. Duk wanda ya tuba don wuya ba lada."

Haka ya ce min fa sannan ya ƙarishe da dariya. Ina masa Typing sai ga shi ya sake turomin mgana.

"Congratulation My Sady. Duk abin da kika saka ma suna ko hannu sunan shi Nasara. I wish you the best"

Kalamansa suka wanke mini zuciya na fasa tura masa abin da na yi niyya.

"Thank you Mijin Sadiya."

Kamar ya ijiye wayar amma dai ya tafi bai kashe data ba. Mutane sai fatan alheri suke yi mini har Anty Maimuna sai da ta ce yana da kyau kam na ƙara da wani abun Anty Zuwaira kuma ta yi tagging da zamu siya in sha Allahu. Daman ita ai ba ta da matsala Anty Bahijja ne ta gani ba ta yi mgana ba. Amma har Gimbiya ta yi mini murna sannan ta ce za ta yi mini talla a status ɗin mutanenta su gani ko za su siya na ce Na gode. Daga nan na kashe data na sauka sai zuwa can an juma Sameena ta kira ta ce ta na son hijabai da na pant da bra shi ne take faɗa min a status ɗin Yallaɓai ta gani ya ɗora sai da muka gama waya sannan na buɗe data na gani.

Ya saka ne amma bai yi wani rubutu ba. Na ga kara domin sun ta sakawa a status suna yi mini tallah. Marwa ma ta saka Hauwa ma da ta yi waya Munnira ma haka yan gidanmu Ya Balki sai Amina har da Datti Ya Auwal dai da Ya Hamza ba a saka su a lissafi su waɗanan ba su damu da saka statua ba irin Yallaɓai ne. Ya Abubakar kuma shi wannan ɗan buga buga ne bai ma cika hawa online ɗin ba. Gidan su Yallabai su Musbahu ne da su Adnan sai Jawahir da su Suwaiba sune daman nawa. Duk kuma wanda ya ga logon zai ce zane ne, ma su abu da abin su kura da kallabin kitse.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull